Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san kowa zai mutu idan ajalin shi ya zo amma kuma ta taya ta duba raunin da yake danne wa a cikin zuciyarshi he was already traumatized, yana fama da insomia for so long ciwon Mammi kuma ya haifar mishi da anxiety tsoro da fargabar barin shi da zata iya yi.

LallaSa shi tayi tayi har ya Wan sake, maganin da ta bashi kuma ya taimaka mishi don kafin ta tafi ma yayi bacci a kan kujerar, Mammi ta samu
"Don Allah Maman Rayyan ki taimakeni a kan Rayyan, ki daina mishi maganganun da zai ji a ranshi kaman wasiyya ne, kin san matsalar shi kin san da ya ya girma in ba Allah ba babu mai iya kawo Rayyan matakin da yake kai yanzu"

"Dr. Ya zan yi ne? Ina faWa mishi hakan ne saboda ya shirya, ya kamata ya shiryawa hakan dole zata kasance amma bana Fatan hakan ya kasance bashi da wani kafaWar, bana Fatan hakan ya kasance ba shi da inda zai iya bayyana damuwarshi shiyasa nake so yayi auren"
"Amma kin san matsalar da niyyar auren nan ya jawo a baya, a maimakon ya gyara sai tabargaza da yayi mana har ya zama for months Rayyan baya aiki baya kuma fita ko ina, bakya tsoron abin da ya faru ya sake faruwa?"
Shiru Mammi tayi itama duk damuwa a kan fuskanta kan ta ce a hankali
"Zan san yadda zan yi likita, na gode sossai da taimakon ki ina fata zai Wore ko da bana nan"
Murmushi kawai tayi ta taso ta dafa kafadar Mammin ta Wan bubbuga kan ta fice bata iya ta ce komai ba.

Hawaye ne ya silalowa Mammin, ita kadai ta san me take ji, ita kaWai ta san tsoro da fargabar da bawa kan shiga a duk sadda aka ce maka ga wa'adin mutuwarka Dukda bata yarda ba amma hakan ya tsaya mata a rai tun shekaru bakwai baya, Dukda ta wani gefen hakan ya matu™ar bata kusanci da ubangijinta sai dai tsoronta yadda zata tafi ta bar Rayyan, bata jin yaranta matan saboda basu da matsalar komai amma Rayyan fa? Raunin shi sabo zai dawo bata son hakan bata Fatan hakan don haka dole ne a gareshi ya nemi abinda zai tallafeshi a bayanta.

****

Ta Sangaren Dr. Sulaiman neman duniya ya saka an yi wa Afeefah sai dai babu ita babu alamunta, police station har uku daban daban ya kai report sai dai babu ko duriyarta.

Tun yana ciwon kai a tsatsaye har sai da ya kwanta don da gaske ya matu™ar damuwa, a ™arshe ha™uri umma tayi ta bashi akan ya fawwalawa Allah ya karSi auren da aka bashi don Abba ya nuna mishi babu gudu babu ja da baya.

A dole daga ita har ™annenshi suka fara shirye shiryen auren tunda sati biyu kachal ya saura a yanzu.

****

A Sangaren saleem ma duk ya ™are a tsaye saboda damuwa da tunani, a kullum adu'ar shi a kan Afeefah ne Allah ya tallafeta ya hanata faWawa halaka Allah yayi ri™o da hannayenta ya bata uwar Waki na ™warai, har yanzu iya gaisuwar ™annenshi kawai yake amsawa wanda abin ya dame su sossai ya zura musu ido kawai musamman mommy da ke ta shirye-shiryen aure ka'in da na'in ita uwar amarya kuma uwar ango.

Sameera na zaune a kan plastic chair a wurin parking lots saleem ya shigo da motar shi ya zo yayi parking ya sau™a, bai mata magana ba don ta gaisheshi da safe kuma ya amsa har zai wuce tace
"Yaya!"

Ya juyo ya kalleta duk tayi wani iri da ita
"Yaya don Allah kayi hakuri da abubuwan da muka yi maka, wallahi na gane kuskurena tun da jimawa na tuba don Allah"
"Me kuka yi min Sameera? Ai ni dan uwanku ne ba zaku iya min komai ba ko? Sai bare ne zaku iya yi wa... Babu komai Allah yana gani"

Kuka sossai take yi.
"Allah ya riga ya nuna min iyaka ta ko a haka na gane kuskurena, Yaya in na tuna abin da muka yi wa Afeefah sai Naji tamkar jayayya muka yi da ubangiji... Za ka yi mamaki yaya idan na ce maka na san abin da kake ji a ranka, na san zafi da raWaWin rashin masoyi domin Allahnta ya saka mata, a sadda take nan ina samun sau™i ne kawai da kallonshi amma a yanzu ko arzikin kallon babu tunda Afeefah bata nan haka kawai ba sakayya bane?"

Idanu ya zura mata duk ta zama wani iri ta rame,
"Sameera wa kike so? Rayyan?"
Ta girgiza kai
"Sulaiman?"
Tayi shiru ya Wan yi jimmm, kan ya matso ta.
"a haka kawai Allah ya barki ya rama mata, ba yafiyata za ki nema ba ita za ki nema ta yafe miki"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta saukar da kai tana hawaye, tana bibiyar Sulaiman sossai Dukda bai sani ba a haka ta san auren shi wadda hakan ya sake daga mata hankali amma ya zata yi? Jarrabawarta kenan, ashe Afeefar ma ba laifi tayiwa ubangiji ba ya zaSi jarabtar ta ta hanyar da ya so, ba zata taSa cewa Sulaiman tana son shi ba amma zata yi Adu'a Allah ya sassauta mata ya kawo karshen shi.

****

Rayyan yayi kwana biyu yana jinya kan ya Wan sake Dukda ba sossai ba, sam ko a hanya basu sake haWuwa da Afeefah ba don bata zauna ba shima kuma ba shiga mutane yake yi ba idan bashi da lafiya, Abeeha ta Wauke ta suka yi sayayya sossai wadda Mammi ce duk tayi mata, suka je aka sama mata makaranta sun ma ™i karbar ta sai da kyar aka barta SS1 za ta yi waec kawai SS2, idan tace hankalinta ya taSa kwanciya irin na kwana biyun nan tayi ™arya, wani irin so da kulawa suke nuna mata.

Bata aikin komai don gidan ma'aikata har sun yi yawa sai ka ga daman zuwa kitchen, uniform da ake jira Winka mata bai samu da wuri ba saboda uniforms Win school din ba'a Kasar nan ake yi ba kuma tsakiyar term ne ya ™are already wanda suke dashi ba'a kawo wani ba, don haka kullum suna tare da Abeeha kusan duk wanda ya san Abeeha sai ya san Afeefah matsayin 'yar uwarta.

Gidan Jannah suka je suka sha yinin su itama bata da damuwa kaman dai Abeeha don duk sun samu nagartaccciyar tarbiya daga mahaifiyarsu.

A yau monday Afeefah ta fito sanye da uniform Winta mai dauke da bajin KIS(Kaduna international school) tayi kyau sossai a uniform din sai kuma tayi kankanta, murmushi ne sossai fuskarta tana yiwa Mammi sallama Abeeha ce zata sauketa in an tashi sai Driver ya je ya Wauko ta, har tana shirin fita Mammi tace
"Afeefah kin mance lunch box Win ko kunyar dauka kike?"

Abeeha tace
"Ana kunya da ciki ne? Oya maza yi sauri ki sameni a mota"
Da sauri ta juya bata ankara da akwai mutum ba kawai ta ji ta buga goshinta a kan kirjin shi, kamshin turarenshi ya sanar da ita waye tun bai Wago ba a razane tayi baya baya tana Wago ido sai suka sar™e cikin nashi fuskar nan tamau, uban Harara da yake zabga mata ya sa ta nemi rikecewa...

"Ba ki da hankali ne? Ko ba kya abu da natsuwa ne?"
Dakakkiyar muryarshi ya sauka a cikin kunnenta ai sai....







=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*23*

"Ba ki da hankali ne nace!"
Ya sake faWa da Wan ™arfi, in za ta iya tunawa kalaman shi na farko kenan a gareta, kila to bata da hankalin ne don yanzu ma rikice wa tayi ta rasa me zata ce Bakinta ya kasa furta ko A sai baya baya da tayi da sauri idanunta da suka firfito farare tass a kanshi.

Ganin Hararar da ya watsa mata yana cewa
"Daina kallona!"
Ya sa tayi saurin Wauke idon, Mammi ce ta ceceta
"Haba Saraki! Bata san kana wurin bane za ka tasa ta gaba kana zazzare mata ido, kayi ha™uri"

Mammi yake kallo, itama Afeefah jin abinda Mammi tace ya sa tayi ™o™arin har haWa kalaman ha™uri tace
"Ka..yi ha™uri"
Tsaki ya ja ya wuce ta ya barta da fitinannen kamshin shi, kitchen ta wuce ta Wauko lunch box Win mai kyau dashi ta fito a sanyaye tacewa Mammi

"Mun tafi Mammi"
Daga haka ta fice a parlorn da sassarfa don tana fitowa ya zuba mata ido, tsaki ya ja bayan fitan ta ya dubi Mammi
"Meyasa kuka sakata makarantar da ba'a sa hijab kamar ba musulma ba?"
Mammi ta kalleshi
"Yanzu menene aibun uniform din nan?"
Sky blue shirt ne da navy blue blazer da skirt Dukda a gwiwa ne sai dai ta saka socks da ya haura mata har cinya, cover shoe Black ne kafafunta sai navy blue cap da ta rufe kanta kirip dashi, neck tie ne me layi layi sky nd navy blue sun yi mata kyau kayan kuma babu inda ke bude jikinta banda hannayenta da fuskarta.

Baki ya taSe bai sake cewa komai ba, abin kari mammi ta kira aka kawo mishi ya fara karyawa a hankali, bayan ya gama ya dube ta
"Mammi auren salim next week friday"
"toooh aure haka kwatsam babu sanarwa babu shiri?"
"Nima jiya ne yake faWa min"
"Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi"
Ya amsa da Ameen.

Daga nan wani hirar ta shiga yi mishi yana bata amsa a hankali hankali har suka gama ya mi™e ya bar gidan.

˜arfe biyu sai ga 'yan makaranta an shigo, bata samu Mammi a babban parlor ba kawai sai ta shige Wakinta tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Abaya onion colour mai kyau, hula ta saka ta fito ta nufi Wakin Mammi jinta take very fresh nd healthy, wani sa'in ta kan tuna salim da halin da yake ciki sai kuma tace kila ma ya manta da ita, Sulaiman ma kan zo mata rai ko yaya yake oho bata sani ba.

Da sallama ta tura parlorn Mammi ta shiga ta sameta zaune gabanta abinci ne, farin shinkafa ce basmati aka dafa amma dibawa aka yi kaman na jinjiri da alama ma da measurement cup aka gwada don ba zai wuce 1/2 cup ba, sai wani wake green, akwai salad Wan kaWan shi ma daga lettuce sai cucumber da lemon tsami, kaza ce gasashiya 'yar kaWan itama a gefe sai ruwa.

Murmushi Mammi ke yi tana amsa sallamar
"Barka 'yan makaranta an dawo?"
"Eh Mammi mun dawo, ya jikin?"
"Alhamdulillah, Ki karSi abinci ki ci sai ki huta ko?"
"Toh Mammi"
Abincin Mammin ta zubawa idanu sama da seconds biyu kan tace
"Mammi idan ba damuwa zan iya tambayar me yake damun ki?"
Mammi tayi murmushi tace
"Babu damuwa Afeefah, ciwo biyu ne ke damuna an haifeni da diabetes na gado don tun ina shekara biyu aka gane cewa na gaji Sangaren mahaifina ne da ciwonsu na sugar, matsalar ciwon sugar idan yayi tsanani yana iya affecting koda to wannan dalilin ne ya janyo na samu damuwa da koda shekaru tara zuwa goma baya, an ma yi min aiki an chanza duka ba'a dace ba Afeefah har ma an ba ni wa'adin wata uku shine ™arshen rayuwata sai kuma gashi da yardar ubangiji na shekara bakwai bayan nan"

Afeefah damuwa ne sossai ya nuna a fuskarta tace
"Toh Mammi shi ciwon ™odar yaya yake? Ba'a warkewa ne?"
"Allah ya halicci mutane da koda biyu, wani halitta ne kaman wake akwai wasu ma da suke da Waya jal kuma suke iya rayuwa amma kowa biyu Allah yayi mu da su, waennan kodar amfaninsu kuma su tace jininmu ne idan ruwa yayi yawa su cire ta ta hanyar fitsari, suna taimakawa wurin hana jini ya hau sannan suna kuma sake wasu kwayoyin halitta na hormones su hana ™arancin jini suna kuma haWa vitamin D dake ™ara karfin ™ashi. Akwai abubuwan da suke kashe koda ba sai ciwon sugar ba wani ma abu mai sau™i kan iya janyoshi kaman rashin shan isashen ruwa, ri™e fitsari ki ga mutum yana jin fitsari ya matse shi sai lokacin da ya maka tukuna zaka tafi da gudu, yawaitar shan pain killers baya na Wan ciwo a sha diclofenac, wani yatsa ma na ciwo ki ga an apka feldin yawaitar shan su akai akai to su suna zuwa ne su rufe jijiyar da yake kaiwa koda jini, a cikin jikin mu kuma koda na daga cikin organs da suka fi kowanne bukatar jini, Sai kuma hawan jini ya fi yawa ma a ™asar mu yana taimakawa sossai wurin kashe koda waennan dalilan bayan ciwon sugar su kan iya haifar da ciwon ™oda, a kan iya chanzawa a dace amma ni an chanza min duk biyu ba'a dace ba yanzu haka ina zuwa dialysis ko wani wata."

Tamkar Afeefah za ta zubar da hawaye take juya maganganun Mammin
"Mammi Allah ya baki lafiya ya sa kaffara ce duk kika yi ta yi"
Mammi tayi murmushi tace
"Ameen, kila Allah ya ajiyeni ne don ™addarar haWuwarmu kila alkhairi zai haifar, bana fita kwata-kwata sai da Saraki ranar kawai na ji ina son fita ashe da rabon mu haWu ne"
Afeefah tace
"Na ga Yaya..."
Sai ta kasa cewa Rayyan a hankali tace
"Ya Saraki! Ya damu sossai da rashin lafiyar naki"
Mammi ta Wan murmusa Allah ya sa kar Rayyan ya ji tana ce mishi Saraki don baya so, shiyasa ko su Abeeha ma Ya Rayyan su ke cewa
"Afeefah ba zan iya misalta miki yadda hankalin Saraki ke tashi a kan ciwo na ba, ko kin san hatta me dafa min abinci ta karantu ne sossai akan cimar masu ciwon mu? Saraki ya tafi yayi courses akan likitanci ne bayan ciwon sugar na ya haifar min da wannan ciwon ™odar in ba haka ba burin shi ya zama soja ne kawai ba Army medic ba, duk don ya san irin taimakon da zai bani a cikin gida ba sai mun yi ta zarya asibiti ba sanin bana so"

Jinjina irin kaunar da yake mata take yi, lallai Rayyan na son mahaifiyarshi.
Cigaba da mata hirar irin gudumawar da Rayyan yake bayarwa a rayuwarta take yi. A yadda dai ta gansu kaman babu wani namiji a gidan bayan Rayyan to mahaifinsu rasuwa yayi? Bata da wannan amsar sai dai ta san idan har tana gidan za ta sani ne.

Abeeha ce ta shigo
"'yan makaranta ashe an dawo?"
Tayi maganan tana zama hannun kujerar da Afeefah take
"Na dawo Adda Abeeha, makarantar akwai daaWi they are all nice to me basu yi min dariya ba"
"Ai na faWa miki babu mai miki dariya, wasu da girman da suka fi naki ma suke zuwa suyi karatu bare ke da jikinki ba nuna girman yake yi sossai ba"

"Aikam na gani kuma na ji daaWi, ga malaman sun iya karantarwa komai fa fahimta nake kaman na sani tun da chan"
Mammi da Abeeha suka murmusa, za ta sake magana kenan Ya shigo parlorn da sallamar da shi kaWai yake sanin yayi kayanshi.

Kai tsaye kusa da Mammi yaje ya zauna, da ita da Abeeha suka haWa bakin ce mishi
"Sannu da dawowa"
Kai ya Wan gyaWa bai kalli kowaccensu ba, mammi ma ta mishi sannu da dawowa yake tambayarta ya jikinta ta amsa da da sau™i.

"Yauwa Mammi Wazu na haWu da Samha a school ashe auren ya salim wani sati?"
Abeeha Tayi maganan da Wan mamaki, Dukda da ta kalli Samha sai da ta tuna abubuwan da suka yi wa Afeefah kuma haushin su take ji har ranta ko da samhar tayi mata magana da kyar ta daure ta amsa, wurin kokarin janta da hira ne take sanar mata auren salim Win kuma suna gayyatarta.

Wani irin faWuwa gaban Afeefah yayi
"Aure Ya Saleem zai yi?"
Bata san a fili tayi maganan ba sai da ta Wago idanunta suka faWa cikin nashi da a lokacin ya Wago ya kalleta jin furucinta, da sauri ta Wauke ido gabanta na dokawa sam bata son suna haWa ido bata san me yasa ba, sai dai yanzu maganar auren saleem Win sai ta ji shi wani iri duk ta ji babu daaWi, Abeeha ma sai da tayi maganan kan ta tuna da Afeefar.

Mammi ce tace
"Eh aure zai yi Afeefah wani sati, kar ki wani sa damuwa a ranki in shaa Allahu Allah zai musanya miki da abin da ya fi alkhairi"
Kunya ne ya rufe ta sai ta du™ar da kai tana kallon yatsun ta sautin tsakin shi ne ya shiga kunnenta, Mammi ta fara mishi faWa akan yawan tsakin kaman wani tsaka, Abeeha ce ganin yanayinta ta ja Afeefar akan su je su ci abinci suka fice daga parlorn.

****

Hidima fa ya kankama Sangaren Amarya sai shiri ake wane, tun saura sati aka fara bikin 'yan karya don Mommy sossai ta ajiye musu kuWi Dukda ma angon ya ja mata gargadi akan duk abin da za su yi kar su sake su saka shi, bai ma je gidan ba ko sau Waya sai ranar da suka yi kauyawa bayan Magrib yana zaune harabar gidan su da dangi suka cika, shiru kawai sam ba ya jin daaWin komai kuma komai ba ya burgeshi kaman daga sama ya ji Muryar Mommy.

"Saleem yanzu ka rantse sai ka nunawa duniya duka ba ka son auren nan dole na maka ko?".

Shi bai san me yayi ba, kaman zai yi kuka yace
"Me nayi kuma mommy?"

"Ko sau daya ka je kofar gidan su Sabrina da sunan zance? Ko ita ba mutum ba ce? Ka hana ta saka ka cikin duk hidimar ta da kyar ma na bugi cikinta ta nuna min kai ne baka so ba ba bata sanar da kai bane, baka bata komai ba haka ake yi?"

"Amma mommy ni nace tayi wani hidima ne?"
"Au in kai kana ™unci da ba™in hali a kan wata chan da na tabbatar yanzu ta rabarwa maza kanta sai aka ce ita ma ta biye ka kuyi ™uncin tare?"
Runtse ido yayi ya buWe tuni suka sauya Meyasa mahaifiyarshi ke yin abu kaman bata je islamiyya bane? Ya subhallah maganar da ta faWa ya mugun ™ona mishi rai amma ya zai yi ne? Uwa uwa ce.

"Zan je, zan ba ta kuWin"
Abin da kawai ya iya faWa kenan ba tare da ya kalli mahaifiyar tashi ba, sai da ta wuce ya bita da kallo yana jan Astagfirullah don yana tsoro, 'ya'ya mata ne garesu yana tsoron Allah ya hukunta mahaifiyar tasu da daya daga cikin yaranta, yana tsoro ta fahimci kuskurenta in a Hard way.

A lokacin ya mi™e ya nufi mota kan ya shiga aka wangale Gate, motar Rayyan ne ya shigo cikin gidan dole ya fasa tafiyar sai ya nufi wurin Rayyan Win suka gaisa.
"Fita za ka yi ne?"
"Eh wai zan je ne in ba Sabrina kudaWen da ya kamata su yi hidimar bikin"
Kai Rayyan ya gyaWa yana furta
"zagayo mu tafi"
Zagayawa yayi ya shiga motar, shiru yayi dama shi ne mai hirar muddin suna tare da Rayyan to shi ma baya cikin yanayin hiran, hakan kuma sai yake sa Rayyan ke jin wani iri sai ya ga kaman bai kyauta mishi ba Soye mishi da yayi Afeefah na gidan su amma zaman lafiyanshi kenan tunda mahaifiyarshi ba amincewa zata yi ba ko ya faWa mishi Win.

Har suka isa unguwar da saleem ne ke ta mishi kwatance hira ba sossai ya hada su ba, a cikin Layin aka yi kauyawan ana ta shirye-shiryen kiran sallahn isha su kam suna nan suna chasewa 'yan mata sai zuba rawa suke, Rayyan ya samu wuri yayi parking yana kallon arean da abin da suke yi a ranshi ya ja tsaki yayi dubu, auren saleem ne ake yi ake wannan haukan? Babu natsuwa a lamarin nasu babu kama kai, ba'a hana hidima ba amma sai a yi shi da tsari ba irin wannan ba ko daga rawar da ake ka san an zubar da mutunci.

Wayanta ya shiga kira ringing na karshe ta Waga
"Hello Ya Saleem"
Ta faWa da Wan ™arfi saboda kida dake tashi
"Ki zo ina daga bayanku kaWan"
Babbar kawarta ta janyo jiki na tsuma suka nufi motar, baya suka bude suka shiga suna gaishe su.

"Amma mun yi fushi sai yau abokanan ango ke neman mu?"
Ci kan ku Rayyan bai ce ba, arzikin kallo ma basu samu ba yana wurin ne kawai saboda Saleem ne da wani ne waennan Win sun mishi kaWan ya haWa numfashi da su a mota guda.

Bundles na 'yan dubu dubu guda uku ya buWe dashboard ya fiddo ya ajiyewa saleem a kan kafafunshi dole ya Wauka ya juya ya mi™a mata
"Ku yi hidima."
Jiki na rawa suka karSa sai kamshi kudin ma ke fitarwa na sabunta.

"Akwai wani abu?"
Ya tambaya saboda kawai mommy ta mishi dole
"A'a ya saleem wannan ma ya isa mun gode sossai"
Daga nan suka fice don shi maganan soyayya ma ba wai hada su yake da ita ba.

"Ka ga abin da mommy ta ja min ko Rayyan?"
Saleem ya faWa bayan sun fice daga unguwar.

Hakika shima ya ga wautar mommy, da ya ga yarinyar sai ya hasko Afeefah a idanunshi ko a kusa bata da abin da za'a haWa ta da Afeefah bai ce komai ba dai har ya mayar da saleem gida.

Su Gaje sun yi shiri matu™a na wannan aure, yayinda amarya tayi shagali sossai kuma ta kullaci kannen angon da babu wanda ta gani a hidimar ta har aka Waura aure ranar Juma'a, Dukda aure ne da babu wani sanarwa ko hidima saleem ya ga mutane kwarai an mishi kara, saboda shi ma na jama'a ne Rayyan na a gefenshi yana yi ne kuma saboda saleem ne don baya son harkar hidima da hayaniya har aka ci bikin aka watse, amarya dai ta tare a sashen saleem na gidan inda duk mommy ce ta tsara hakan sai fatan Allah ya basu zaman lafiya.





=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*24*

Da misalin ™arfe Waya na dare ta jefar da mayafin kanta tare da dira daga saman gadon tana jan tsaki, me salim ke nufi ne? Babanta ya tabbatar mata shirin da aka yi akan shi ba mai sau™i bane da zai iya resisting amma me ya faru har yanzu bai shigo ba? Šaukan maganin da Gaje ta bata a gefen bedside tayi ta jujjuya
"To bai ma zo bama bare in sha wannan Win" ajiyewa tayi ta janyo wayanta kaman ta ™ira su Gajen kuma sai ta fasa ta nufi parlor, kasancewar sashen nashi Waki daya ne da parlor sai kitchen in har dai ya shigo to ba zai wuce yana parlorn ba sai dai idan a waje zai kwana.

Shi kuwa salim tun karfe tara ya shigo gidan yanayinshi baya mishi daaWi sam, fuskarshi babu walwala haka ya tura kofan da sallama ya shigo, yana taka door mat Win ya ji kanshi yayi wani diimmmmm jiri na shirin kwashe shi a hankali ya furta
"Subhallah!"
Ya tsaya a wurin sama da mintuna biyu kan ya sau™e numfashi ya nufi three seater ya kwanta hannunshi dafe da goshinshi, duk yadda zai yi ya samu sauki ya yi sai dai wani irin tension yake ji, sai juye juye yake Sabrina da a chan ™asan ranshi ya san bai damu da ita ba sai kai komo take yi a ranshi, bai san adadin lokacin da ya dauka ba shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba, ko matse shi zaka yi ba zai ce maka ga abin da ke damunshi ba sai jin Fitowar ta yayi.

Ganinshi ya sa ta nufe shi.
"Ya salim dama ka shigo? Shine kayi kwanciyarka anan ina chan duk tsoro ya rufe ni?"
Bai ce komai ba sai ido da ya Wan zuba mata.ıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿ
"Ka tashi mu je ka kwanta a ciki idan baccin ne ma"
Ta faWa tana ri™o hannunshi, kasa mata musu yayi haka ya bi bayanta kaman rakumi da akala, a bakin gado ta ajiye shi ta shiga rage mishi kayakin jikinshi, wani sashi na zuciyarshi tsantsar mamaki yake na wannan bushewar idon wani sashen kuma na faWa mishi ba laifi bane, har ta gama cire mishi kayan shi dai bai tanka ba kuma bai motsa ba, hannunshi ta ja wai tunda ba ya jin daaWi su je ta mishi wankan, tana tura shi bayi ta dawo da baya ta sha wannan maganin da

Please Login or Register in order to submit comment