Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gigice ta juya ta nufi sashensu don gaisuwar ba zata iya shi ba cikin wannan hali ta tabbatar da za'a bincika jininta yayi mugun hawa ko ya zu™e tas yayi ™asa tsabar tashin hankali
Yana zaune kawai ya ga faWowarta don yau din Asabar ne bai fita ko ina ba da kyar ma ya kyaleta ta fita gaisuwar, ganin halin da ta shigo ya sa yayi saurin Mi™ewa yana rike kafaWunta.

"Afeefah! Afeefah menene? Me ya faru?"
Ta kasa magana ma, girgizata yayi
"Me ya sameki? Afeefah!!!"
Da ™arfi yayi maganan yana bin jikinta da kallo sai dai bai ga komai ba.
"A wurin Ammie ne aka Sata miki rai? Ko wurin Mama ne? Me ya faru kika shiga cikin wannan yanayin? Ki yi min magana mana!"
Kuka mai sauti ta fashe dashi kaman wacce aka rufe da duka sai ta sake Waga mishi hankali ya juya da sauri zai fita ya tambayo uban da ya taSa ta tayi saurin ri™o hannunshi tana kukan sossai duk ta ruWa shi.

"Sakeni in ba zaki faWa min abinda aka yi miki ba Afeefah, Sakeni nace in je in ji dalilin da kaina...!"
Da tsawa yayi maganan yana kokarin fusge hannunshi tayi saurin rungumeshi kamkam tana cigaba da kukan da ya ™arasa cire mishi natsuwa.

"I thought ina da muhimmanci a rayuwarka, a zatona duk wani abu da ya shafeka ya shafe ni Meyasa zaka min hakan? Meyasa Ya Saraki?"
Sakinta yayi yana ri™o fuskarta idanunshi cikin nata
"wa yace miki ba ki da muhimmanci a rayuwata? Kin kuwa san yadda nake jinki Afeefah? Meyasa za ki yi irin wannan tunanin?"
"Ba gashi ba, idan har ka daukeni da muhimmanci ba zaka binne ni ba, ashe aure zaka yi nan da sati biyu? Aure Ya Saraki irin wannan baka iya ka sanar min ba?"
Kukan da take na shaketa ta ™arasa, sossai fuskarshi yayi Red ainun jijiyoyin kanshi duk suka mi™e kukanta tamkar saukar tafasashen ruwa ne a zuciyarshi shi kadai ya san irin abinda yake ji, a ina ta ji? Zai yi magana ta ture hannayenshi ta nufi Waki da gudu tana cigaba da kukan ya ri™e kanshi yana ambaton sunan Allah, bayanta ya bi da sauri sai dai ya tarar ta rufe kofan da makulli hankalinshi ya sake tashi ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta cikin damuwa...




=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*55*

https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c

Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!=ĜOÜ<Ĝûß

********

Yayi yayi ta buWe kofar ta ™i, har spare key ya Wauko sai dai dayake ta bar key jikin ™ofan ya ™i shiga, cike da damuwa ya koma ya zauna a kan kujera hannunshi dafe da goshinshi sama da mintuna goma yana nan shiru kan ya mi™e ya tafi Wakinshi yayi wanka ya shirya cikin wani jumpha ba™i dinkin zamani, ya saka hula da half cover duk ba™ake ya fito kai tsaye ya nufi motarshi su GaabWo na mi™a gaisuwa ma babu wanda ya amsawa ganin yanayinshi yasa basu nuna za su bishi ba don kallo Waya ya musu suka koma suka natsu.

Tafiya ba mai nisa ba sossai ya kai shi shiyyar da Galadima yake duk a cikin masarautar, parking yayi ya sauka ya nufi ciki hadiman Sangaren na ta mi™a gaisuwa bai amsawa ko Waya ba ya isa babban parlorn Galadiman, ya kuwa same shi zaune suna ma tattaunawa ne da Ameer, ganinshi ya sa duk fuskokin su suka cika da fara'a
"A'ah yau Satan kai ka yi ne Ciroma?"

Da kyar ya Wan sake fuskan ya zauna
"Baba Barka da rana"
"Barka dai, ya iyalin naka?"
"Alhamdulillah"
Mi™awa Ameer hannu yayi suka gaisa kan ya dubi Baba.
"Baba dama na zo ne akan maganan Zarah da mai martaba ya tayar, idan da hali ina so ka mishi magana Baba a dakatar da maganan nan zuwa gaba duk yadda zan mishi bayani ya kasa fahimtata, na amince mishi ne kawai saboda na san girman alkawarin wannan masarauta kuma ba na so ko kadan a ga gazawarshi ka san yadda su Makama suke... Na ji na amince amma ba yanzu ba kaman yadda suke so"

Galadima ya sau™e numfashi ya ce
"Sameer da safen nan muka gama wannan magana da mahaifiyarka, ta kirani akan a ja maganan ba yanzu ba duba da baka ma wani jima da dawowa ba abubuwa dayawa baka gama sabo dasu ba, ga matarka da bata rufa shekara ba Dukda ba hujja bace tunda anan muna aurawa namiji ma mata biyu a rana Waya amma abin a duba ne zancen naku, Mahaifiyarka ba iya jayayya take da mai martaba ba a wanchan Sangare kuma akwai Fulani da 'yan uwanta har biyu suna uzzura mishi duba da yarinyar ta isa auren shiyasa abin ya zo a hagunce. Zan gwada yi mishi magana idan ya amince sai a bar maganan for now amma da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa"

Idanunshi ya runtse ya san dama aikin su Fulani Adama ne they will be on his fathers neck har sai sun ga sun samu abinda suke so, shi wlh ba ma zai iya wassafa yadda zarahn take ba Dukda bata dameshi ba amma tashin Hankalin Afeefah shine abinda ba zai iya jurar gani ba a abinda ya shafi auren.
"Baba don Allah a yi min wannan ™o™arin, mai martaba yayi rantsuwar ba zai karSi wani uzuri daga gareni ba muddin ba mai ™arfin da zai iya haramta auren bane a yanzu duk abinda zan fada mishi gani zai yi excuse nake kawowa na watsa mishi ™asa a idanu"

"Hakane. Dukkanmu ba za mu so ganin an yi ™aranta ba don ba girman wannan masarauta bane, zan gwada mu gani"
"Na gode sossai Baba bari na koma"
Ya mi™e Ameer ma ya mi™e suka fito a tare a jikin motan shi suka tsaya yayi shiru.

"Lafiya dai kam Sameer? Ko duk maganan auren ne ya saka ka cikin damuwa?"
Numfashi ya sauke yana fesar da iska daga bakinshi
"Ameer damuwana Waya ne tak tashin hankalin Afeefah, bana son zancen auren nan kwata kwata don na san ba zata ji daaWi ba wace macece ce zata so a mata kishiya? Irin wannan kam ma Gani zata yi kaman don ita ba yar cikin gidan nan bane za'a ware ta ko a ba ni zarah, tunanin sakata a damuwan ya sa ban iya na yi mata maganan ba amma sai gashi ta ji a wani wuri yanzu haka tana chan tun dazu tana kuka ban san ya zan yi ba!"
Cike da damuwa ya ™arasa maganan.

KafaWar shi ya dafa
"Ban taSa sanin haka rauninka yake ba sai akan Afeefah, kuma gaskiya baka kyauta ba ya kamata duk abinda yake faruwa ta fara sani daga wurin ka zata iya fahimtarka ba wai taji a wani wuri ba da ake maganan kila saura sati biyu...! Yanzu kai za ka kwantar da kai kayi rarrashin ta hanyar da zata fahimceka ko don gaba duba da kaine magajin wannan jaha ta mu ko a rana Waya ana iya baka mata a Waura bambancinta kawai zai iya zama kana sonta fiye da kowa kuma hakan ma wani makami ne a gareta"

"Dole na Ameer don ba zan samu natsuwa ba muddin tana cikin damuwa, bari na je. Na gode"
Da kallo Ameer ke Binshi har ya shiga motar ya bar wurin, murmushi yayi lallai So So ne hmm idan ba son ba wani abu ne zai taSa zuciyar Sameer haka? Juyawa yayi ya koma ciki don basu gama tattaunawarsu da Mahaifin nashi ba.

Sai da yayi azahar ya dawo Sangaren ga mamakin shi ya samu abincinshi jere a kan dining kuma ya san bata taSa bari hadimai su mishi girki ba kenan ita ta fito tayi, Wakin ya nufa ya murda handle Win sai dai a rufe still goshinshi ya dafe bai taba sanin tana da fushi haka ba, ya san kalar ha™urinta lallai ya kaita ma™ura.
Dakinshi ya nufa don abincin ba zai shiga ba ya rage kayan jikinshi ya kai zaune yana lissafi.

Wasa wasa har dare ta ™i bude kofan, ko da ya fita Magrib da isha kan ya dawo ya samu ta Wauke abincin dazu ta ajiye wani daban, shima bai bi ta kanshi ba ya sake komawa kofar Wakin yana kiran sunanta amma ta ™i ta buWe daren tea ya sha daga ita har shi baccin su rabi da rabi don tunda suka shirya basu taSa kwana ba tare da juna ba cikin bargo Waya skin to skin sai ranar.

angaren Afeefah Da asuba bayan ta yi sallah ta Wan yi azkar kan ta mi™e ta saka wani silk fabric gown ta Waura dankwalin fuskarta har lokacin da alamun kuka don kukan da ta jima bata yi ba tayi shi a jiya a ™arshe ta yi finalizing solution Winta, ta sakawa zuciyarta ha™uri da juriya don ba zata taSa hana shi ba idan Allah ya rubuta, haka ba zata saka ya ™i bin umurnin iyayenshi ba ta riga ta sakawa zuciyarta cewa ko ba jima ko da bai auri zarah ba zai iya yin wani auren don haka za tayi Adu'a Allah ya kawo wacce za su zauna lafiya, za ta kuma yi iya kokarinta na ganin ta cigaba da zama ta farko a zuciyarshi har abada sai dai ba zata Wauki ya dinga binne ta a komai ba, don yawan fushin nata ma na rashin faWa mata akan lokaci ne.

Ta zubawa dining Win idanu ganin bai taSa komai ba ta tattare ta nufi kitchen ta saka a microwave don bai lalace ba, kokarin Wora mishi wani abin take don ta san shi kam ba zai ci wanchan ba kawai ta ji an rungumeta ta baya, daga ita har shi sai da suka sau™e wani nannauyan numfashi, shiru tayi bata ce komai ba ta cigaba da kokarin aikinta ya Waga ta chak yayi Wakinshi da ita ya sauketa a kan gado yana zama ya ri™o hannayenta duk biyu.

"BoWWi am...!"
Idanunta ta kawar yayi murmushi mai sauti ya ce
"Na tuba ki yafe ni Afeefah, ba zan iya jure fushinki ba Allah kaWai ya san wani hali kika jefa ni daga jiya zuwa yanzu... Please lets talk kin ji?"
Idanunta suka cika da kwallah bai ankara ba ya ji ta fashe mishi da sabon kuka a fili ya furta
"Yaaa Salaam Afeefah...."
Rungumeshi da tayi ya saka maganan yankewa, ya rufeta cikin jikinshi yana shafa bayanta idanunshi a rufe yana jin zafin kukan nata har ranshi.

"Ki yi ha™uri na saka ki cikin wannan hali, it wasn't intentional ban san yadda zan iya fuskantarki da maganan bane but am sorry kin ji?"
"Promise me Ya Saraki, ka min alkawarin cewa ba za ka taSa juya min baya ba, ka yi min alkawari cewa ba zaka sake Soye min duk wani abu da ya shafe mu gabaWaya ba, i felt hurt zuciyana ya kwana yana zafi da raWaWin jin zancen aurenka ba tare da na sani ba"
Šago fuskarta yayi yana share mata hawayen da hannayenshi biyu cikin karyayyen murya yace
"I promise Afeefah, na miki alkawari in shaa Allahu. Ki yi ha™uri i didnt meant to hurt you that badly dubi fuskar ki yadda yayi looking so tired and pale sbd zubar da hawaye"

Wani hawayen ne ya gangaro sai ya runtse ido yayi shiruu.
Shesheka ta ja ta sa bayan hannunta ta share wani ya sake zuba ta sake sharewa looking cute nd sad at the same moment.
"Ka yi ha™uri i couldnt control my emotions ba laifina ba ne, am jealous kishi nake ji in na tuna nan da kwanaki kadan zan raba ka da wata, za ka shaki kamshinta ba nawa ba, za ka hada jiki da ita.... Am sorry"
Duk ta rasa yadda zata yi bata san tana da irin wannan kishin ba kuma ruwan kaunar da ya zuba mata ya sa take jin shigo da wata duniyar su zai yanke mata wannan ™auna.

Jikinshi ya janyota zuciyarshi na tsananta zafi ya kasa magana, ita kuma ta zaci shirun da yayi ita ce take Sata ranshi cikin kuka tace
"ka taya ni Adu'a Allah ya sassauta min abin da nake ji Ya Saraki, am just jealous because I love you, angry because all i care about is you a lokaci guda kuma am scared because am afraid of losing you"

Šagota kawai yayi ya haWe bakinsu don kukan ya gama hawa kanshi, wani irin deep Kiss yake yi mata da tun bata amshi signal Win ba har ta amsa, a iya romance ya tsaya sai da ya tabbatar jikinta yayi laushi ainun fatarshi da nata na a manne da juna yana shafa bayanta a hankali suna sau™e numfashi zai yi magana ta riga shi muryarta chan ™asa tace
"I wanted to be the only one to tells you I love you, wacce za ta haWa miyaun baki da kai, touches your skin and feel you inside me sai dai kash! kana naka ne Allah na nashi, Kana da damar auren mata har huWu tunda kana da halin hakan kuma kana da lafiya, abu daya zan roka daga gareka Ya Saraki kar ka daina so na don Allah zuciyata fashewa zata yi".

Yana shafata tana sake yin lub jikinshi ya shiga furta
"Afeefah ki yarda da ni, babu wata kishiya da zuciyar Ryan zata iya yi miki a soyayya domin ke Waya jal ta sani kuma ke kaWai ta aminta da ki ja ta duk inda kike so, da ke kaWai ta aminta a matsayin Abokiyar rayuwa ba ni da yadda zan yi ne da babu dalilin da zai sa in amince da batun zarah amma ba zan iya watsawa mahaifina ™asa a ido ba alkawari ne da aka yi tun ban san kaina ba, amma in har za ki cigaba da wannan kukan komai zan iya yi ciki har da barin wannan gid..."

Šagowa tayi ta haWe lips Winsu da kanta sai da ta bashi kyakyawar Kiss kan ta kalli idanunshi hannunta na a fuskarshi shima idanunshi zube cikin nata da suke a rine tace
"Kar ka ce komai, ni da kai duka karkashin ikon mai martaba muke dukkanmu uba ne shi a gare mu da magana kawai zai yi mu cika, sannan aure ba haramun bane idan yana cikin ™addararmu ina ro™on Allah ya ba ni ha™uri da juriya ya kuma kawo mana ta gari wacce za mu haWe kai mu zauna mu kula da kai gabaWaya, don haka Allah ya nuna mana lokaci ya bamu zaman lafiya gabaWayanmu"
Ta ™arasa tana komawa kan kirjinshi ta kwantar da kanta tana mayar da hawayen da suka cika mata ido.

Matseta yayi a jikinshi kawai bai ce komai ba, sun jima a haka don bacci ne ma ya Wauketa shi kam bai iya yayi baccin ba damuwar da ta shiga ya tsaya mishi ainun ya san ba komai bane sai zallar soyayyar da take mishi, lumshe ido yayi kawai sai ranar da take ba Mammi da Abeeha labarinta ya faWo mishi the way she was deeply hurt nd depressed anya ta chanchanci raba farin cikinta guda Waya jal da wata? Yayi adalci kenan idan ya iya haWa jiki da wata mace ba ita ba? Numfashi ya sauke mai nauyi ya mirginata kwance ya ja mata bargo kan ya sauka ya dauki shirt ya saka ya nufi kitchen.

Breakfast ya samar mata bayan ya gama ya kai har kan gado ya ajiye kan ya shiga shafa kanta zuwa fuskarta cikin tattali da kulawa har ta buWe ido, murmushi ta mishi ya mayar mata
"Tashi ki ci abinci BoWWi"
Mi™ewa tayi zaune tace
"Brush tukuna bakina babu daaWi"
"Ba dole ba na tabbatar through out jiya baki ci komai ba"
"kaima ai na ajiye maka baka ci ba i was disturbed"
"Toh ba fushi kika yi da Sarakinki ba..!"
Yayi maganan cikin muryarta ta saki dariya ya Wauketa zuwa bayi tare suka yi brush suka dawo tana bashi yana bata har suka koshi.

Wanka ma tare suka yi abin su yana ta takalarta tana ture shi, suka fito ta shirya shi kan suka je Wakinta ya taya ta shiryawa.

"Bari na je nayi gaisuwa na dawo"
"Ki bar gaisuwan nan babu inda zaki a sake bata miki rai a banza"
Idanu ta ware
"An taSa fushi da iyaye ne Ya Saraki? Iyaye musamman uwa ita kaWai ce take mantawa da kanta yayin da take yiwa danta Adu'a ita a wurinta idan danta yayi nasara itama ta yi, Na san ka rasa Mammi ka kuma tabbatar babu zafi da ciwon da ya kai na rashin mahaifiya. Ciwo ne da baya taSa goguwa har abada, zaka yi fata za ka yi adu'ar ko da ganinta sau Waya ne a yayinda kasa ya rufe idanunta a sannan kuma babu halin hakan, Uwa garkuwa ce ga dan da ta haifa, Ya Saraki in na ce maka ga kalar kukan da nayi na maraici ba zaka yarda ba, duk raWaWin da zan fada maka akwai ba zaka fahimta ba wani lokacin Allah ya sanya albarka daga bakinsu kawai kake nema ba zaka samu ba, Allah ya umurcemu da kyautata musu iya iyawa a sadda suke raye ni ka ga ban samu wannan damar ba, ko sanin su ban yi ba tsakanina da su Adu'a ashe ba zaka amfani wannan damar ba? Don Allah Ya Saraki ka sake tunani akan hukuncin da zuciyarka ke aikatawa, Allah ya sasanta tsakaninku cikin sau™i"
Shiru yayi ganin kaman zata Sata mishi rai ta tashi ta fice tana ce mishi sai ta dawo ya bita da kallo kawai bai ce komai ba.

Sashen Ammi ta fara zuwa suka gaisa ta Wan jima suna hira da Zarah da Aisha kan ta wuce sashen Fulani Adama.
"Barka da safiya Mama!"
Tana hakimce ta amsa idanunta na scanning Afeefar ciki da bai kallon da ya sa taji duk ta tsargu kan ta amsa.
"Lafiya ™alau, shi mijin naki kam isar shi ta kai ya share sama da watanni a Masarautar nan bai taSa zuwa inda muke ba sai dai mun haWu a hanya ko? Uhm ko da shike ba ke ya kamata na yiwa zancen ba mai martaba ne ya Waure mishi kugu dole"

Shiru tayi don bata san me zata ce ba, kiran hadimarta tayi
"Ke Rahane kawo mata abin taSawa"
"Ai mama da ta barshi yanzu na karya kenan na fito"
"Dama na lura baki taSa cin komai na Sangaren nan ba, ashe kema baki daukeni uwa ba kenan... ai shikenan sai gaisuwar ma a barta kawai Allahn da bai bamu 'ya'yan ba yana sane da mu, na ji labarin babu abinda bakya ci a sashen FaWimatu nan ne ba zaki ci komai ba? Yayi kyau"
Bata san Meyasa take mata maganganu haka ba, duk sai ta rikice ma tana tuna gargaWin Rayyan akan kar ta ci komai na gidan kuma dai tana cin na Ammi, wani zuciyar yace ta gudarwa kanta matsalar Fulani Adama ta ci kawai ai Rayyan ba zai sani ba kuma ma kindirmon da aka kawo mata fari tas kwance a ™warya yayi matukar bata sha'awa don haka ta janyo ta dauki ludayi ta shiga sha, sai da ta sha dayawa ta ture tayi godiya kan ta mi™e ta bar sashen.

Yinin ranar suna tare da Rayyan yana sake nuna mata ita kaWai ce tauraruwar zuciyarshi yana cika ta da kauna don ko girkin rana da dare ma ba ita tayi ba, bayan sun gama cin abincin dare tana kwance kanta akan kafafunshi suna ma kallon wani movie ne yana wasa da gashinta ya shiga jin hannunshi na jikewa musamman in ya kai ga goshinta, shafa goshinta yayi yana kiran sunanta ta amsa
"Lafiya kike zufa haka? Duk irin Ac dake aiki a parlorn nan?"
Tace
"Nima ban sani ba kawai dai cikina ke dan murda min kadan kadan ba sossai ba"
"Mp ne? Amma ai bakya ciwon cikin priod pain tashi mu gani ko mu tafi asibiti?"
Ta girgiza kai
"Ba wani sosai bane ba fa zai daina Yaya"
Ganin ta ™i tashi ya sa ya kai hannunshi yana shafa mata cikin a hankali.

Mutsu mutsu ta fara duk ta kasa kwanciya wuri guda ita kaWai ta san azabar da take ji wanda rashin son tada mishi hankali yasa take ta daurewa, yana kula da motsinta sai gani tayi ya Wagata ya kai hannu ya kunna hasken parlorn tarrr, ganin idanunta ya tabbatar mishi da ba ciwon wasa take ji ba.

"Tashi mu tafi Asibiti"
Ya mi™e yana ri™o ta bata yi musu ba ta mi™e tsaye sai dai abin da taji yana bin kafan ta ne yasa tayi saurin kallon wurin shima ganin yadda ta razana sai ya kai idanunshi wurin.

"Jini??"
Yayi maganan a Wan rikice kaman kuwa ana jira su gani cikin nata ya shiga kartar da bai yi ba da farko, damke hannunshi tayi tana jin azabar na shirin kasheta tuni ta fita hayyacinta a rikice ya Wauketa suka fice daga parlorn da gudu GaabWo ya je ya buWe mishi mota ganin yadda suka fito ko tukin ba zai iya ba yana rike da ita a baya yana shafa cikin yana mata sannu sai juye juye take tana zub da hawayen da bata san suna ma zuwa ba, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba jinin da bai san daga ina ba kuma na me na ta wanke su sai sannu yake maimaita mata kaman ya taya ta kukan a haka suka isa asibiti aka yi emergency da ita don har ta fara sumewa.

A masarauta kuwa Ammi na zaune da su Aisha aka kawo musu labarin dukkansu hankalinsu ya tashi suka mi™e tsaye suna tambayar
"Me ya sameta?"
Babu wanda ya san amsar sai kiran me martaba da Ammi tayi tuni ya bata umarnin tafiya suka fito a ruWe sai ga Ameer tare da shi da wasu securities suka bi bayan su Afeefar cike da adu'ar Allah ya sassauta koma menene ya bata lafiya cikin gaggawa..







=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ


HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Don Allah ku yi min uzuri na so in bi comments in amsa kowanne amma na kasa, bana jin daaWi ne kar ku yi expecting biyu gobe in na iya na yi Wayan ma Alhamdulillah!*

*56*

Afeefah ta matu™ar jiggata kan aka samu aka shawo kanta da kyar, shi dai ba zai ce ga abin da yake yi musu a Wakin ba yana tsaye ne kawai saboda matsayin shi na likita kuma mai mu™ami da ba zasu iya kora ba, hannunshi na rike da nata yana tsaye kyamm idanunshi na zube kan fuskarta wani irin ciwo ne wannan lokaci Waya? Me ya sameta? Babu kalar sake saken da bai yi ba.

Kalaman da ya ji likitocin suke yi cikin harshen turanci cike da ™warewar aiki ya ™ara daure mishi kai ya jefa shi cikin tunani da damuwa lokaci Waya.

"Sir da ka je ka sauya wannan kaya saboda duk sun yi stains, za tayi bacci sossai kila sai zuwa midnight ta farka sai a sake running wasu tests"
Wani likitan ya faWa bayan ya dafa kafaWar Rayyan da ya jima cikin duniyar tsoro, mamaki da kaWuwa.

Hannunta ya zame yana kallon kayan da aka kawo za'a sauya mata da wasu towels da za'a goge mata jikin da ya Saci Dukda mata ne karSa yayi suka fita, shi ya goge mata jikin tas ya sanya mata kayan asibitin riga da wando ne kan ya gyara mata kwanciya ya duba tafiyar ruwan har lokacin fuskarshi Jajazir, kwakwalwarshi ya ™i hutawa da sa™e sa™e a haka ya fito daga Wakin sai ya tsaya chak yana kallon Ammi da take kallonshi itama a zaune.

Jikinshi ya bi da kallo yana tuna jinin Wan shi ne nan ko Wiyar shi, wani irin zafi da bai san ya zai fasalta ba na taso mishi a cikin zuciya bai san ya nufi Ammin ba ya samu wuri a gefenta dab ya zauna bai ce komai ba kanshi a ™asa, dukkansu sun yi mamaki har ita kanta amma ta danne tace
"Sameer ya jikin Afeefahn?"
Ya yi shiru na seconds yana hadiye wani irin

Please Login or Register in order to submit comment