Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a yanzu hijab ne jikinta har ™asa, daidai yana shigowa take cewa Sa'ade
"Ki tattare kitchen nan please ban yi shafa'i da wutiri ba bari na gabatar"

Bata ma kula da Shigowar tashi ba don ciki ciki yayi sallama ta wuce Wakinta ya bi bayanta da kallo hannayenshi zube cikin aljihu, a natse ya ™arasa dining Win daidai Fitowar Abeeha da Jannah suka mishi sannu suma suka zauna suka shiga cin abincin, ganin ta jima ya sa ya dubi Abeeha
"™ira min Afeefah"

Ta mi™e ta nufi Wakin ta samu ta idar tana zaune ne kawai, jin yana kiranta ta mi™e ta nufi parlorn zuwa dining.

"Zauna ki ci abinci"
Ganin fuskarshi ba fara'a yasa ta zauna ta zuba abincin kaWan tana ci kaman bata so, karamin kwalin da bai jiman nan ba GaabWo ya zo ya ajiye mishi ya tura mata.

"Na gode"
Ta faWa tana jan paper bag Win ta buWe ciki sai ta ga waya ne dall a cikin kwali Iphone 17 Air ce, bata nuna zumudi ko farin ciki sossai ba sai ma su Abeeha ne ke ta santin wayan ta sake ce mishi ta gode ya bi fuskarta da kallo.

Bayan sun bar dining Win su sa'ade suka zo suka tattare wurin tsaff.
Šakinta ta koma ta bar su Abeeha da wayan a parlor suna mata setting ta yi wanka, ta duba wani orange and Black nigty silk ne mai hannun shimi ya bi jikinta sossai don Black lace Win ya kara haske kayan, hijabi ta saka a kai ganin yadda ko motsi tayi komai na jikinta na motsawa cikin kayan musamman hammatan dake bayyana tudun na shanunta time ta kallah almost nine.

Fitowa tayi Abeeha ta bata wayan don jannah ta gudu waya da mijinta a Waki, Wakinshi ta nufa kai tsaye da sallama ta kutsa kai rike da wayan a hannunta don tana so su yi magana.

A tsaye take bisa kanshi yana kishingide cikin tattausan Italian cushion a hankali yake Wan taune lip Win shi kaifaffun idanunshi zube bisa kanta
"am...am just fed up, ba na tunanin zan iya cigaba da zama a haka i've had enough na san ba ka aureni ba ne saboda kana so na, ka aure ni ne out of pity da kuma am... Mammi. Muddin na cigaba da zama a haka zan iya mutuwa a yanzu bana jin zan iya cigaba da kasancewa matsayin ma..matar k..."
"It's pretty!"
Ya furta chan ™asa cikin deep voice Win shi da ya sa ta kame, duk maganar da take yi ba idanunta yake kallo ba lips Winta da take motsa su a hankali ya ™urawa lumsassun idanunshi yana wani kashe su yana buWewa...
"W...whatt?"
"Ur lips... They are pretty"
Ko kan ta farga ya yunkura ya fusgo hannunta guda ta tafi gabaWaya kanshi tayi masauki a kan kafafunshi fuskarta ya sau™a kan wuyanshi a tare suka Wauke numfashi. A Wan razane ta shiga mutsu-mutsun sau™a ya sa hannunshi na hagun ya zagaye kwankwansonta yayi pinning Winta jikinshi, na daman ya sanya ya zare mata hijabin idanunshi na sauka kan jikinta, ya bi damtsen hannunta da yatsa biyu cikin wani salo har cikin tafin hannunta kar yayi baya ya ri™e wrist Win hannun ya Wora saman heart Win shi da ke beating very very fast. A take nata ma ke ™o™arin sauya bugu numfashi na neman kwace mata idanunshi a saman fuskarta kaman zai tsagata da su ya furta

"sa™on zuciya baki ne yake furta wa sai dai kuma wani lokacin yana iya fin ™arfin harshe ya bar wa idanu nunawa, Lil angel saurari bugun zuciyata ki kalli tsakiyar kwayar idanuna na tabbatar sun isa sanar miki da cewa Ryan na ™aunarki ba zai iya rayuwa babu ke ba, kuma yana tsananin bu™atar ki, you are like a Light in my darkness. You are not just my wife Afeefah you are my safe space, my solace...you are the key to my salvation..."
Wani irin birkicewa ta nemi yi saboda nauyin zantukan nashi ga idanunshi masu kaifi da yake zagaye fuskanta da su yana wani lumshe su, maganar ma har cikin Sargonta take ji saboda yadda muryarshi ke fita very deep nd husky.
"A haka kike cewa in rabu da ke? Uhmm? Ki fahimta rashin ki a gareni masifa ne Afeefah"
˜uri tayi da idanu kalamanshi suna samu matsuguni daram a cikin zuciyarta, sakinta yayi ta koma zaune kawai akan kafar tashi, kanta ta mayar ™asa tana neman dulmiyewa tsabar yadda kalaman suke zuwa mata a bazata Rayyan ne fa gabanta shine yake fitar da waennan tsadaddun kalmomin daga cikin bakinshi?

Anya ta ji da kyau? Ko dai yaudararta yake shirin yi ganin irin kallon da yake mata ba tare da ya sake furta uffan ba, shi ne zai so mace kamarta? Sake Wago kai tayi ta kalleshi suka hada idanu. Sarai ya san kokonto take akan kalamanshi kuma hakan bai mishi daaWi ba, ya kai hannunshi ya kama haSarta ya Wago fuskarta yana kallon cikin idanunta cikin karantar yanayinta bai furta komai ba.

Idanunta ta mayar kasa zuciyarta na bugawa da tsananin karfi har tana jin kaman cikin ko wani lokaci zuciyarta zai iya yin bindiga ta mutu, amma shi ko a jikinshi kuma fuskar a kame yake magana idanunshi na yawo bisa jikinta ya
ce
"Idan kuma kin matsa da sai na rabu da ke, zan iya yin hakan ne kawai under 2 conditions Afeefah sai ki zabi wanda kike gani ya fi miki sauki ni kuma i promise zan rabu da ke!"
A razane ta dago ta zuba mishi idanunta da har sun fara zubar da kwallah lips dinta dake rawa ya bi da kallo kan ya dauke idanu yana lumshe wa ya bude
Da ma na sani baya so na tunda gashi zai iya rabuwa da ni amma me yasa nake jin zafi?
Meyasa nake jin kaman karshen rayuwata ne ya zo? Abinda take ayyanawa kenan a ranta..
Da kyar ta iya furta
"Menene conditions din?"
Tana ji gwara ta sani gwara ta hakura ta nemi daidai ita.

"It's either ki mayar da lokaci baya ki goge ranar da na fara sanin ki a rayuwarta don daga ranar ne zuciyata ta fara bugawa da ˜aunarki ko kuma ki tsaga zuciyata ki sauya min da wata zuciyar don wannan ta jima tana sakar da jini mai dauke da kaunarki zuwa ko wani sashe na jiki da jijiyoyina...."
Baki kawai ta saki hawayenta na zuba sossai da sossai, ya kai hannu ya janyota suka samu kusanci ainun, ya Wago babbar yatsarshi ya shafa soft lips Winta dake ta rawa idanunshi na cikin nata yayi leaning a hankali ya Wora bakinshi kan nata zuciyoyinsu na amsa ba™on yanayin nasu da karfin gaske.......







=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Babu lallai ku ji ni da daddare manage this please, and na ga ruwan comments da Adu'o'i na gode kwarai Allah duk ya faranta mana ya hada mu da masu kaunar mu saboda Allah*

*51*

A hankali ya raba bakin nashi da nata, ya zuba mata idanunshi da suka matukar sauya ko da ta buWe idanu sai suka sarke cikin nashin, ya ri™e natan sama da mintuna da suka fi biyu kan ya saukar da kanshi wuyanta yana goga mata gemunshi zuwa karan hancinshi a gefen kunnenta cikin wani irin salo da bata san ta mayar da hannayenta biyu bayanshi ta yi grabbing wuyanshi ba tana sau™e numfashi.

A hankali yake haurawa numfashinshi na sauka da zafi yana ™arasa hautsina mata natsuwarta har ya isa cikin kunnenta cike da wani shau™i mai dauke da mayen son da ba za ta iya resisting ba ya shiga whispering into her ears
"Afeefahhh ke ce ta farko a zuciyata, ke kika buWe shafin farko a soyayyata, a kanki jikina da zuciyata suka fara gamsuwa da cewa ni din namiji ne cikakke kuma ina bu™atar Abokiyar halitatta, ki amince min mu zama daya, ki yarda na baki ragamar rayuwata! dama Waya tak nake so ki ba ni...ni kuma zan killaceki a cikin zuciyata tsawon rayuwata, zan zama bawa a gareki mai hidimarki tsawon rayuwarmu zan tabbatar wa da duniya ke ce farin ciki na kuma hasken zuciyata..ina fata ba za ki hanani raSa daga ni'imarki ba?"

Hawaye ne ke zuba mata na rashin Makama, yanayin ya mata zafi kalaman sun mata tsauri ainun ta yadda take jin kaman tana duniyar halwa ne na soyayya ba duniyar mutane ba, bata san ta gyaWa mishi kai ba yayi murmushi mai nauyi wanda sautinshi ya fita kaman numfashi, bata ankara ba taji ya tashi da ita a hannunshi ya isa ya mayar da hasken Wakin dimmm sossai kan ya nufi gadon ya shimfiWeta za ta yunkura ya bi bayanta his hands started to move inch by inch na jikinta, yana squezing Winta gently bakinshi is slowly kissing her and driving her nuts especially wuyanta da ya fi ko ina motsa shi, da baki yayi amfani ya saukar da sleeve na riganta cikin salon da bata taSa sanin akwai shi ba, heavy breathes Win shi na sake birkitata.

cikin natsuwa yake komai, Sai da ya tabbatar tayi laushi shima ya fara rasa kanshi a duniyarta kan ya nufi yin mai gabaWaya, a sannan ne ya birkice ya gigice tunaninshi ya Sace, jinshi yayi nisa bashi da buri a lokacin illa na ganin sun zama daya ta zama shi shima kuma ya zama ita, ko da ya ji shi a duniyarta ™arasa haukace wa yayi a sannan ne ita kuma ido ya raina fata ta fahimci that pleasure da irin tarin iya sarrafa mace da yake dashi ne ya ruWe ta har ta zaci abin mai sauki ne, duk irin magiya da ro™on da take mishi haWe da kuka duk baya ji, idan hannunta ya sauka jikinshi ma sai yaji kaman zaburarwa ne cikin salonta.

Bai sarara mata ba bai kuma saurara ba don yayi haukacewar da ko sunanshi ka tambaya a lokacin ba zai iya tunawa ba ita kaWai ya sani, ita kaWai kuma yake gani...Tsammmmm haka ya rukunkumeta yana binne kanshi a wuyanta a sadda ya samu cikakken natsuwa, Dukda irin halin da take ciki na fitar hayyaci da raWaWin azabar da bata taSa fuskantar irinshi ba a rayuwarta tana iya jin Wumin hawayenshi dake bin wuyanta, chan kaman daga wani uwa duniya take jin sha™a™iyar muryarshi na furta

"Allah ya gafarta miki Mammi, Allah ya yafe miki kurakuranki Allah ubangiji ya sadaki da rahamarsa Allah ya jiyar da ke daaWin aljannah fiye da yadda kika yi sanadiyar jin wannan daaWi nawa na duniya....Thank you! Thank you Mammi"
Sossai yake hawaye har numfashinshi na seizing ya mata ri™on da kaman ya tsaga jikinshi ya chusata yake ji ko zai samu saukin abinda ke shirin zauta shi, bai iya ya motsa ba kaman yadda itama bata da kuzarin Waga ko da yatsar ta ne, yana so ya Waga ta ya ji lafiyarta yana so ya gwada buWe baki ko zai iya furta mata tarin irin kaunar da yake mata sai dai ya kasa, ya kasa sarrafa kanshi bare ya sarrafa jikinshi abu daya ya sani ta gigitashi a duniyarta ta goge mishi haddar da baya tunanin har abada akwai wacce ta isa ta kaishi inda ta kaishi, ta kashe mishi duk wani laka na jiki kaman ba tsayayye kuma jarumin sojan nan ba, ™asusuwanshi sun yi laushin da ya kasa ko da lankwasa su bare ya sarrafa su har su mi™e a dole ya sake binne ta ya ja bargo ya rufa musu a haka wani irin bacci ya Wauke shi ba tare da ya san halin da take ciki ba.

Sautin kuka da turirin zafin dake fita daga jikinta zuwa nashi ne yayi sanadiyar farkawarshi, gaining courage yayi ya yunkura da ita a jikin nashi har lokacin banda bargon nan babu komai jikinsu duk su biyu, juyata yayi ta koma kwance yayi pecking goshinta a hankali ya fara ambaton sunanta

"Afeefah... Bebe!"
Bata amsa ba sai kananun kukan da take na zazzafar zazzabi idanunta a rufe kirib
"Am so sorry...am sorry"
Ya faWa yana sake pecking goshinta kan ya sauka ya nemi wandonshi na bacci ya saka ya nufi toilet shi karan kanshi kafafunshi rawa suke kanshi ya mishi nauyi ainun, gefen cikinshi ya ri™e mishi sossai amma sanin dalili tunda shi likita ne bai wani damu ba ya haWa mata ruwa mai zafi, ya dawo gadon ya Wauketa kaman 'yar baby.

"Matar Saraki..! Afeefah... Kina ji na? Zan saka ki a ruwa compose yourself kar ki ji zafin a bazata! Am so sorry Ya Saraki bai kyauta ba, Yafam boWWi am"(ki gafarceni kyakyawata)
Da wani irin sloww tune yake maganan a kunnenta kan ya saukar da ita a hankali cikin ruwan, wani irin ™ara ta saki tana rirrikeshi za ta tashi ya shiga ciki ya danneta kawai ta kife kanta kirjinshi tana girgiza wa cikin azaba da kuka mai ratsa zuciya, hautsinannen gashinta da ya gama wargaza wa yake shafawa zuwa bayanta yana hura mata iska a kunnen yana whispering
"sorry, am so Sorry My love."

Sai da suka yi ruwa uku a tare tana li™e bisa kirjinshi idanunta a rufe rufff kan ya sakata tayi niyya suka yi wankan tsarki, a towel fari ™al yayi wrapping Winta ya sake Waukar ta zuwa kan cushion ya ajiye ta, har lokacin bata buWe ido ba kuma bata bar kananun kuka ba shi kuma bai bar lallashi da ban ha™uri ba, gadon yaje ya chanza musu bedsheets.

A gabanta ya tsuguna bayan ya Wauko magani, bata ma san ya zo ba don har bacci ya fara fusgarta na wahala kawai taji hannunshi cikin towel Win ya shafa cikinta ta Wan zabura sbd har lokacin hannunshi da sanyi ta buWe ido sai suka haWa ido tayi saurin rufewa yayi murmushi

"Tashi ki sha magani 'yar albarka..!"
Bata motsa ba shi ya Wago ta zata fara kananun kuka ya sanyata jikinshi ya shiga bata tea din da ya saisaita zafin ta sha sossai kan ta sha maganin, a maimakon tayi shiru ma sai ta sake fara wani kukan.

"Am sorry My love, har yanzu baki ji sassauci ba?"
Ta gyaWa kai tana hawaye don ita kaWai ta san me take ji, shima kuma ya san jarumar mace yake tare da ita tayi matukar ™o™ari, a hannu ya dau™eta bai damu da su sa wani kaya ba suka koma kan gadon ya shimfiWeta bisa kirjinshi
"Sannu Chéri am(My darling) in duba in gani ko kina bu™atar stiches?"

Ta ma™e kafada za ta fara kuka yayi murmushi mai sauti kan ya shiga shafa wet gashinta da yayi mishi laushin taSawa saboda bai bushe ba, a kunnenta yayi whispering
"Afeefahh kin san Bugawar zuciya alama ce ta mutum na raye ko? Toh kece bugun Zuciyata wanda hakan ke nufin idan babu ke a zuciyata babu ni zan iya amsa kowace irin tambaya a game dake saidai tambaya daya da ba zan iya amsawa ba ita ce wane irin so na ke miki, wannan tambaya ba zan iya amsata ba domin ni kaina ban san wane irin so nake miki ba abin da kaWai na sani game da yadda nake jinki cikin jinina shine ba zan iya cigaba da rayuwa ba idan har ba'a tare dake ba. Afeefahhh idan har rayuwa ba za ta yiwu babu iska ba haka nima ba zan iya zama mai rai ba tare da ke ba, ke ce rayuwata Gimbiyata"

Duk giyar soyayyarta ya saka yana jin kome ya faWa mata yayi kadan wurin bayyana abin da yake ji, kuka take ba na bakin ciki ko ciwo ba kukan farin ciki take, tana kukan alfahari tana kukan isar ta macen da aka iya macewa a cikin begenta, tana kukan mallakar wannan gwarzo namijin da bakinshi bai yi nauyi ba wurin shimfide mata sirrukan zuciyarshi, rungumeta ya sake yi tsamm yana shafata cikin bege
"Allah ubangiji ya kula min da dukkan lamuranki na rayuwa, yadda kika shayar da ni garWi da za™in zumanki ubangiji ya shayar da ke ruwan alkausara... Thank you so much Habeebty a yanzu you are not just the part of my life you are the owner of my heart, ki yi bacci Habeebty kiyi bacci cikin salama"

Da wannan kalamai haWe da tarin lallashinshi mai tsadar gaske bacci ya Wauketa. Ya jima sossai kawai yana kwance in ta motsa sai ya sake shigar da ita jikinshi kaman za'a raba su ne ya yi pecking tsakiyar kanta, sun so su makara don ™arshen ta a gida ya ja su sallah bayan ya kaita tayi alwala, wani ba™in Oman jallabiyarshi mai adon gold ya saka mata sossai ya mata tsawo ya Wauko mata hijab Winta ya saka mata shima ya saka jallabiya ya ja su sallah, suna idarwa ya janyota ta kwanta a kan kafafunshi ya zare hijabin yana shafa gashinta yake musu azkar duk su biyun don da kyar tayi Sallar saboda bacci da zazzabin da bai gama sake ta ba, tuni ta yi baccinta peacefully har ya gama ya dau™eta ya mayar da ita gadon yana kallon pale fuskarta.

Idanu ya lumshe yana sauke numfashi, a duk sadda zai ganta wani sabon ™auna da mararinta yake ji yana kwarara cikin zuciyarshi, hannunta ya ri™o yayi pecking ya sake yi mata peck a Goshi kan ya mi™e ya fito, hadiman da suke share share da goge goge suka zube ™asa suna kwasar gaisuwa, ya Wan shafa kanshi ya ce

"Ammm yau gabaWaya na baku hutu, ina so ku koma sashenku kuyi duk abinda kuke so sai dare ku dawo"

"Godiya muke Yariman Matasa! Godiya muke Ciroman fombina Allah ya kara girma da arziki Allah ya biya bu™atu"
Kai kawai ya gyaWa suka mi™e suka fice shi kuma ya nufi kitchen.

Abeeha da zata fito kenan ta ji yana koran hadimai ta koma ta buga jannah da ke shirin komawa bacci
"Wallahi barin sashen nan ya kama mu Addah jannah... Me afkuwa ta afku ga Ya Rayyan chan kitchen zai dorawa gimbiyarshi breakfast "

Da sauri jannah ta mi™e zaune cike da zumuWi tace
"Keeee Ya Rayyan Win?"
"Shi fa wallahi, hmmm ai na san jiyan nan ba lallai a wanye ™alau ba, bawan Allah Saraki a waje Hadimin Afeefah a gida"
Suka kwashe da dariya jannah na cewa
"Kin ga irin su Yayan nan hmmm ki bar su kawai... Maza shirya bari nima na shirya mu koma sashen Ammi for today mu bar su su ™one in sun ga dama"
Abeeha na dariya ta shiga toilet wanka ji take zuciyarta kal kal, basu fi mintuna talatin ba suka bar sashen abin su.

Shi kam bai ma sani ba yana kitchen, plantain yake frying amma minti minti zai saki murmushi yana tuna moments Winsu na jiya, ji yake ma yana kewanta a jikinshi daga Fitowar shi Wakin zuwa yanzu, sai da ya gama ya haWa mata spicy egg sauce mai Wan yawa, ya yi toasting bread with butter very soft and simple kan ya shirya plate Win with so much love don burin shi kawai ya ga tana murmushi burin shi ya ga ta ji daaWi kuma tayi alfahari, clean tray mai kyau garai-garai ya samu ya ajiye plate Win ya hada da tissue ko za ta bukata wrapped with cutlaries.

Dube dube ya fara har ya samu wani drawer mai dauke da notepads masu yawa da Pen sbd specifying objects, rubutu yayi a jiki ya manna a gefen tray Win ya hada tea mai kauri sossai ya ajiye kan ya Wauka ya nufi Wakin.

A gefen bedside ya ajiye ya yaye mata duvet Win har lokacin riganshi ne jikinta, ganin tana baccinta peacefully ya shafa fuskarta motsi ta fara a hankali har dai ta buWe idanunta da suke kumbure ta sauke bisa kanshi ya sakar mata kyakyawar murmushi
"Good Morning My Queen, My greatest blessing and the reason i believe in love..."

Duk yadda bata so murmusawa ba sai da yayi escaping ta tsinci zuciyarta da dumbin farin ciki wane takarda.

Mi™ewa tayi zaune tana sau™e kanta ™asa haWe da fara wasa da hannunta tace
"Good Morning"
Bai matsa mata ba ya san kunya ke Wawainiya da ita shi ko a jikinshi ya Wauko tray Win ya ajiye mata a kan cinya zai yi magana wayanshi ya shiga ™ira ganin mai martaba ne da kanshi ya sa yayi picking yana fita daga Wakin don dole zuwa parlor.

Note Win da yayi rubutun ta Wauka ta shiga karantawa.
"Na shirya miki wannan karin kumallon ne da tarin soyayya, kina da muhimmanci sossai a rayuwar Ryan. Allah ya albarkaceki da farin ciki da lafiya kullum, Ina ™aunar ki!"

Zuciyarta ta sa hannu ta dafe, kaunar ya mata yawa ji take ta ma rasa me zata yi sai sake karantawa take tana murmushi. Adanawa tayi ta dauki fork ta fara cin abincin da ya shirya mata da hannayenshi, loma biyu tayi sai gashi ya dawo yana zama gefen ta
"Afuwan mai martaba ne ya kira ni ko yau zan samu fita ran gadi da shi"

Kai ta gyaWa tana sakar mishi cokalin bata ce komai ba don ya riga ya sanya hannu cikin nata ya karSa ya cigaba da bata cike da kulawa yace
"Kin san me na ce mishi?"
Kai ta girgiza
"Ce mishi nayi yau yini na, magana na da duk wata kulawa tawa naki ne ke kaWai saboda kin bani abu mafi daraja a rayuwarki..."
Da sauri ta kalleshi tana zaro idanunta waje gabaWaya ya saki murmushi mai kyau har hakwaranshi na bayyana tace kaman za ta saki kuka
"Da gaske haka ka faWa mishi?"

Hancinta ya lakace
"Gashi na saka ki kallona da waennan idanun da suke kashe ni, kuma na ji wannan murya taki mai kaman sarewa..."
Bata san tayi murmushi ba shima ya cigaba da yi har ya gama bata.

"Mu je in miki wanka..!"
Ta zaro ido
"Zan iya wlh"
Tayi saurin faWa a ShagwaSe ya kalleta
"Ya daina zafi? Kin tabbatar za ki iya tafiya?"
Kai ta gyaWa ya dage tray Win ta sau™o tana Mi™ewa tsaye ta ri™o shi jin tana shirin faWuwa wani Sharp pain na shigarta, ya ajiye tray Win yana saSarta

Duk rigima da ShagwaSar da tayi ta mishi dole suka yi wankan ta lura ita ce ke mutuwa da kunya shi ko a gyalen shi tattalin ta yake wane ™wai, shi ya dubo mata wani kaya ta saka Dukda ma ba masu nauyi ba a parlor ya ajiye ta ya kunna mata Tv wai tayi kallo bari ya zo, har ya tafi ya koma yaje ya Wauko mata popcorn ya zo ya bata yayi pecking goshinta kan ya koma Wakin nashi ta bi bayanshi da kallon ™auna tana murmushi cike da tarin farin ciki....






=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*52*

https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c

Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!=ĜOÜ<Ĝûß

*****

Ga mamakinta bai fita Win ba ya tabbatar mata da gaske yake ya cewa Abeey bata da lafiya ba zai iya yin nesa da ita ba, kunya ya rufe ta amma shi ko a gyalen shi da kanshi ya gyare Wakin tsaff ya wanke beddings da suka Sata kan ya dawo yayi joining Winta a parlor hannunshi da mug yana sipping tea, da kanta ta kai kwance jikinshi ya mayar da hannunshi Waya bayanta ya rungumeta suna kallon a tare hasken parlorn a kashe Dukda hantsi ce amma yadda curtains suke rufe kirib rip hasken duk a kashe sai ya ba da wani yanayi kaman cinema.

Film din ya ™are amma bata sani ba saboda ta yi nisa cikin tunani, hawaye kuma na bin fuskarta har take ji kaman zazzabinta zai dawo sabo, kula da hakan da yayi ya Waga mishi hankali ya Wago fuskarta yana kallon ruwan hawayen da take yi
"Afeefah lafiya? Me yasa kike kuka haka?"

Yana maganan ne yana Wauke hawayen da palms Win shi wasu na gangarowa, a hankali tace
"Twins na cikin film din nan sun tuna min da Suhail da Suhaila ne, ko ya suke? Na san yanzu sun girma, ko suna maraicin uwa kaman yadda nayi? Ko suna samun farin

Please Login or Register in order to submit comment