Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take ™anwar ™anwar bayana?"

Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa da kuka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan Wan ta? Ko ci kanku bata ce ba.

Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yake faruwa ita bata gane komai ba, Sabrina ta sau™o tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta Wora mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba.

"Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?"
Mommyn ta faWa cikin mamakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin?
"Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama wani iri ga faWa da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai yanzu?"
Samha ce me maganan zuciyarta har lokacin yana bugawa
"Nima na kasa ganewa Samha kaina ya kulle tamau, kwakwalwana ba ya tunani daidai... Amma bari iyayen nata su zo mu ji me kenan?"

A parlorn suka cigaba da zama chan kuwa sai ga Gaje da Yaya sun shigo, yanayin shigar tasu ma ba yadda suka saba zuwa ba a raSe a raSe a baya suna tsoro kar su yi ma mommyn ba daidai ba, kai tsaye suka zauna cikin kujerun parlorn yaya yana cewa
"Hajiya Hussaina ashe ana nan, barka da gida"

"Sannunku da zuwa"
Ta faWa tana ta kallonsu kaman sabbin halitta yadda suka shige cikin kujera duk ba haka suke yi a baya ba, bata gama mamaki ba sai da Sabreena ta zo da gudu ta rungume Gaje tana musu oyoyo

"Masha Allah, Amarya kin sha kyau da kamshi"
"kai Gaje, Baba sannu da zuwa"
Ta faWa tana daga jikin Gaje dake ta riritata.
"Barka dai 'yar arziki irin albarka, ya sabon wuri? Babu takura ko?"
"Ah baba wa ya isa ya takura ni ni da gidan mijina"
Suka yi dariya.

"Yana zuwa ya gaishe ku, sa kaya yake yi"
"Ah ba komai ai muna nan"

Mommy tana zaune tayi tsamo tsamo kaman ruwa ya daki babban zakara har Saleem ya sauko ya zo ya tsuguna suka gaisa da su Gaje sai albarka suke sa mishi kan ya mi™e ya kalli Sabreena yace
"Na fita"

Da sauri ta mi™e ta bishi muryarta na fita a lokacin da take cewa ka zo min da... Sai dai bata ™arasa da karfi ba, bayan ya fita ta dawo ta saka su Gaje gaba banza suka yi da su Mommy kaman Allah bai halicce su a wurin ba, wasu irin hawaye ne ke zubowa Sameera tana ambaton sunan Allah kan ta tashi ta shige Waki tana fashewa da kuka.

Samha dai da mommy sun kasa magana, suna kallo har ta musu iso dining suka ci suka yi nak suka dawo parlorn, mommy ta kasa shiru tace

"Yaya...!"
Kallonta yayi
"Menene yake faruwa ne? Na rasa gane kan Sabrina tunda aka yi auren nan, Wazu fa har sa wa tayi Salim ya daki sadiqa abin da ba halinshi ba, ba haka na saka shi ya aureta su zauna ba ba zan zuba idanu mu cigaba da tafiya a haka ba, Salim ko kallon mutunci ya daina min daga aure? Me hakan ke nufi?"

"Hajiya Hussaina ke fa kike Waukar abu da zafi, yaro yayi sabon aure ai ba za'a saka musu ido ba, tarbiya daidai gwargwado mun ba Sabrina kuma idan Sadiqa tana mata gani gani da a matsayin ta na yayarta yanzu yayansu take aure ya kamata su san maganan da za su dinga faWa mata ina ga hakan sai a zauna lafiya"

Mommy ta saki baki da hanci tana kallonsu. Sabrina tayi murmushi tace
"Abin da mommy ta kasa ganewa kenan, mu ajiye batun nan ku tashi mu je ku kalli sashena"
Basu bi ta kan 'mommy ba suka bi bayan Sabrina, numfashi ne taji bata iya ja da kyau Samha ta ri™e hannunta

"Mommy...! Mommyyyy!!"
Hankali tashe take kiranta kiran ya fito da Sadiqa da Sameera ruwa suka dauka suna shafa mata a fuska har ta Fara sau™e numfashi da ™arfi, me su Yaya suka yiwa yaronta? Sai yanzu tunanin za su iya cutar mata dashi ya zo mata innalillahi kawai take ta maimaitawa a tsananin tsorace.

Su kam suna hawa Sabrina tace
"kun yi min komai iyayena, ba ni da abinda zan saka muku kun ba ni wannan daula da dukiyar sai yadda naga dama zan juya shi, a yanzu ma ina ragarwa uwar ne saboda wani dalili nawa amma itama nan kusa za ta gane ta Wauki goruba ne ta damkawa kuturuwa don kwace saleem a hannuna sai mutuwa"

Dariya suka sheke dashi Gaje tace
"Ke gidan nan fa duk na mijin ki ne kina da ikon yin yadda kike so, sai na ga kaman wannan sashe yayi muku kadan kenan ku suka raSa ba ku kuka raSa su ba"
Hakane kuma gaskiya Gaje, kai Sabrina ta gyaWa
"Zan san abin da zan yi akai, amma ko za ku dawo nan Win ne?"

"Ta ya kenan 'yar albarka?"
Baba ya faWa, ta saki murmushi
"Kar ku damu na san yadda zan yi saleem yayi musu korar kare a gidan nan"
Hira suka cigaba da yi wane sa'anninta ba iyayenta ba duk wani tuggu sun haWa shi a ™arshe baban ke cewa
"Ai duk yadda za mu yi mu yagi rabon mu kan a je lahira za mu yi, ko a gaban Allah laifin mu kadan ne ita ta ga dama ta bamu hanya zuwa cikin gidanta shekara nawa ina faWi tashi akan ya kula ki sai da na hakura na cire rai kwatsam ta dawo da zancen ashe muna da rabon dangwalar arziki mu ma, bari mu je mu fara tattare"

Sallama suka mata suka bar gidan ransu kal...

****

"Saleem..."
Ya kira sunan yana zama gangar shi, buWe rinannun idanunshi yayi ya zuba su kan Rayyan Win ba tare da ya ce komai ba, duk wannan Win ba halin Saleem bane na Rayyan ne hakan ya sa Rayyan Win ya Wan damu.

Yana zaune kawai ya ga Shigowar saleem Win office Win kuma bai ce mishi komai ba bayan sallama ya samu wuri ya kishingida.
"Menene? Me yake damunka?"
"Ni ma ban sani ba Rayyan, kawai ina jin ™unci ne raina babu daaWi zuciyata na mini zafi ba na iya bacci"
"Saleem kana karatun Alqur'ani?"
Ya girgiza kai don ya fi 2weeks rabon da yayi karatu in ba a sallah ba.

"Alqur'ani wani dafa'i ne na yaye ™uncin zuciya saleem, idan ka ga ba zaka iya bacci ba kayi ta nafilfili kana karatun za ka ji sau™i, ka fi kowa sani na har a yanzu bana bacci kaman na mutane amma da na ri™e ibada ban zauce ba... Ka ro™i Allah ya yaye maka dukkanin damuwowinka"
Kai ya gyaWa, Rayyan bai kara cewa komai ba ya tashi yayi playing karatu a office Win ya je ya Wauko ruwa ya kawo mishi ya Wan sha tare da kwanciya a three seater abin mamaki tun karatun na shigar shi har bacci mai tsananin daaWi da natsuwa ya Wauke shi ba tare ma da ya san yayin ba.

Saleem ya yi baccin Awa biyu cip kan ya farka har lokacin Rayyan na office Win yana wani aiki a system ganin ya farka ne ya mishi sannu, kai ya gyaWa ya mi™e ya shige toilet da ke ta tashin kamshi wanke fuska yayi tare da alwala don ana ta kiran la'asar, bayan ya fito Rayyan ma ya rufe duk abin da yake yi don baya tunanin daga masallaci zai dawo office Win ya shiga bayin yayi alwala ya fito yana gyara hannun lafiyayyar farar shirt Win shi da ya Wora akan navy blue wandon jeans, rigar suite Win ya dauka da briefcase Winshi suka fice yana kulle office Win. Sai da ya zube abubuwan a mota suka isa masallaci suka yi sallah.

"Za ka iya driving Win ko in mayar da kai"
"No zan iya"
Ya faWa a hankali.
Da kallo ya bishi har ya shiga motar shi ya bar wurin, ™asa natsuwa yayi da yanayin saleem Win duk sai ya tsaya mishi, da wannan 'yar damuwar ya nufi gida horn yake dannawa a kofar gidan da gudu aka wangale mishi gate ya cusa motar ciki, idanunshi ne suka faWa kanta sanye take da wani stylish crepe Adire ta haWa shi da matching colour purple na Jersey, daga inda yake yana hangar labbanta dake shekin man baki sossai tayi kyau amma shi ba kyaun yake gani ba.

Dr. Sulaiman dake tsaye yana mata magana ya Wan zubawa idanu kan ya ™arasa parking Win ya sau™a sai ya Wauke kai kaman bai san akwai halittu wurin ba, tafiya yake kaman ba zai taka ™asa ba har ya Wan gota su Dr. Sulaiman ya taso

"Assalamu Alaikum warahmatullah Dr. Rayyan"
Sai da ya Wan lumshe ido ya buWe kan ya Wan waigo ya kalleshi ba don ya san muhimmancin sallama ba babu abinda zai sa ya amsa, hannu ya mi™a mishi suka gaisa ya juya ya shige ciki fuskar nan kaman an mishi mutuwa.

Sai da ya Sace ta sauke numfashin da ta ri™e Dukda ko kallon inda take bai yi ba, kwarjinin shi ya matu™ar cika ta ta tabbatar haka Sulaiman ma don babu wanda baya shan jinin jikinshi a duk sadda Rayyan ya matu™ar tsumewa, ita dai ta san Rayyan ba ya rasa nasaba da sarauta.

"Afeefah me kika ce?"
Dr. Sulaiman ya faWa
"Zan tambayi Mammi in shaa Allah in ta amince tunda gobe half day juma'a sai ka zo mu je in na tashi school"
"Toh shikenan, ga wannan"
Ya mi™a mata leda kin karSa tayi sai da ta ga ranshi ya Saci kan ta amsa don bata yadda ta iya.

Kai tsaye wurin Mammi tayi don ta bata ledar ba ma ta bukatar buWewa kan ta kai mata, da kuwa ta san abinda zata tarar da bata shiga ba faWa sossai Rayyan ke yi na shi baya son tarukuce idan abinda zata yi kenan ta tattara ta bi samarin nata yaushe har ta tafasa da zata ™one? Haka ta ga Abeeha na yi? Toh shi ba irin tarbiyar da yake ba ™annenshi ba kenan in kuma tana gidan dole tayi abinda ta ga su Abeeha na yi.

Jikinta rawa ya Wauka, Mammi ta ri™o hannunshi
"Duk faWar nan na Sulaiman ya zo ba tare da ka sani bane? Kayi hakuri ni ce na mata izinin fita ba haka kawai tayi fitan gaba gadi ba kuma ko mintuna biyar bai kai ba idan nima na yi laifi sai in ji..."
Shiru yayi bai ce komai ba.

Tana tsaye a gefe kaman yajin kosai kafafunta kaman za su kayar da ita saboda yadda suke rawa don mugun kallon da ya aika mata, ledan hannunta ya kalla
"Ba kin ga kalar rainin da bana so ba Mammi? Mun ce ba mu dashi ne da zai kunso koma menene a leda ya kawo mata? Ko ta tambayi abu ba'a yi mata ba?"

"Saraki...! Bana so! ka ga bana so don Allah, ka duba yadda ka firgita ta? In kuma hankalina kake so ka Waga ka cigaba"
Da Wan faWa tayi maganan, haushin kanshi ya ji ina ma ruwan shi da zai damu da tarbiyar ta? Shi ba wani tsiyar yake dubawa ba sai kar ta lalace da tara samari tun bata kai lokacin ba, Mi™ewa yayi ya nufi fita daga Wakin ranshi a haWe fuskar nan murtuk, wani irin chill abu ne ke bin jikinta na tsoro, bata san me yasa shi baya wani damuwa da damuwarta ba a ranta take jin kaman bai yi na'am da zamanta a gidan nasu ba, ita idan ba don mammi ba wlh ko inuwa ba zata so haWawa da shi ba bare har magana, gashi nan tana ta aikata laifin da zai ji haushinta.

Kamshinshi ne ya daketa a sadda ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba ta lumshe ido sai da ta tabbatar ya tafi ta sauke numfashi ta isa wurin Mammi tana jin hawaye na tsinke mata

"Mammi ki yi ha™uri ban san ba'a haka anan ba, na fita ne ba don wani abu ba sai don Ro™on da Dr yayi ta min a kan ko ba zan Wauke shi Masoyi ba in Wauke shi wa da zan iya neman abu a wurinshi yayi min, ya ce min Mamanshi ta damu tana so in je ta ganni ta ji lafiya ta don kaman 'ya itama ta Wauke ni wlh ba ni na ro™e shi ba Mammi kin ga da kyar na karSa har saida ranshi ya Saci..."
Dafa ta Mammi tayi

"Natsu Afeefah! Ki natsu kar masifar Saraki ya dame ki, haka yake wlh kin ga su jidda basu isa su kula saurayi ba sai ya fara zuwa ya ganshi yayi bincike ya amince mishi kan ya zo idan yayi bincike bai mishi ba ko wayanshi suka sake Wauka mai karbar su a gidan nan sai ya shirya, na sani a yanzu babu zancen aure tsakanin ki da Sulaiman shiyasaŭ˙˙˙ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ na bari kika fita, kuma ai ba'a mayar da hannun kyauta baya... Goben ki shirya sai ku tafi da Abeeha in ta dawo school ku gaishe da mahaifiyar tashi kinji?"
Tsoro ne ya sake rufe ta jin yana duka, itama kenan zai iya bugun ta in tayi ba daidai ba

"A'a Mammi ba sai na je ba, zan bashi uzuri..."
"Kar ki wani damu zan mishi magana"
Ledar ta ajiye don ji take ko abin ciki bata sha'awar gani, hankalinta ba'a kwance ba ta tashi tayi Wakinta ko da ta shiga sai da ta sakawa kofar key don ji take kaman zai biyo ta ya cigaba da faWa.



=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*FATIMA A MUHAMMAD Sirikata kuma namecyna ina so in yi amfani da wannan dama in mi™a sa™on godiya da kuma jinjina bisa irin kokarin da kike yi a kan wannan littafi, ha™i™a ba ni ma da kalmar da zan nuna miki jin daaWi na da kuma yabawa mai tarin yawa wannan shafin naki ne kiyi yadda kika ga dama da shi... Jama'ar gidan haihuwa da hanji conversation room ina ganin tarin comments naku sai dai lokaci baya bani dama a kullum na shiga a sha fira da ni amma ina matukar jin daaWi kuma ina yabawa ku sani muddin Aminiyar ango(Fatima A Muhammad) ta amsa wallahi kaman ni ce nan na amsa. Ina kuma yi muku albishir gobe public holiday za mu samu damar jero shafuka biyu in Allah ya yardar mana. Na gode sossai*

*27*

Washegari friday har ta je school ta dawo bata daina tuna irin faWar shi na jiya ba, ita kam ba don mammi ta tabbatar mata da sai ta je ai shi zumunci yake so da ita ba tsiya ba, wanda yake sonka da arziki kuwa ya gama maka komai da babu inda zata je ai zama lafiya ya fi zama Wan sarki.

Ko da ta dawo da Wakin Mammin ta fara ta duba jikinta suka Wan yi hira kan ta wuce Wakinta aka biyo ta da abinci, sai da ta ci kan ta shiga tayi wanka da alwala ta zo tayi sallah, a gaban mirror ta zauna tana kallon kanta a yanzu ko ita ta san ta yi kyau, ta Wan yi ™iba skin Winta na wani irin yalki don man da Abeeha take shafawa ita ma shi ta saya mata kuma skin tone Win su Waya, ta sake cika tayi kumatu kaWan sai ya mata kyau, kwalli ta zana a idanunta bata cika sakawa ba amma ta san yana mata kyau kawai dai bata son sakawa ne don yana sa idanunta hawaye sai wani ruwa ya kwanta ciki kaman mai, dama gasu da girma masha Allah, lip gloss ta shafa ta mi™e ta tafi gaban wardrobe.

Abaya ta Wauko wani blue da adon fari egyptian ne ya amshe ta sossai ta saka farar hula don farin gyale yake da shi sai ta yafa gyalen ta yi kyau sossai sai ta ji nishadi a ranta, wa zai ganta ya ce Afeefar Dutsen-wai ce, Mayya kuma annoba? Wa zai ce tagayyara aka so tayi Allah ya dube ta ya tallafi rayuwarta? Malamin islamiyyarta na makaranta na cewa Allah zai buWe ma bayinsa kokafofin rahama da sau™i cikin ko wani tsanani muddin ka saka tsoronshi da tawakalli cikin ranka, sannan zai buWe maka kofofin arziki ta inda baka yi zato ko tsammani ba ko a mafarki bata zaci ganinta cikin irin wannan gida tana rayuwa ba, tayi tunanin za ta tabbata a bauta da wahala a kasakance amma da Allah ya ce ba hakan bane ga inda ya kawo ta a yanzu.

Da kyar ta bar gaban madubin wurin Mammi ta nufa.
"Masha Allah Daughter ta tayi kyau tabarakallah!"
Murmushi tayi tana zama gaban Mammin
"Mammi zolaya ta fa kike ina kyau anan? Ko fa powder ban shafa ba"
Mammi za ta yi magana kenan Abeeha ta shigo kaman ta jima da Dawowa don ba da kayan da ta fita ta shigo ba.

"Afeefah Dr. Sulaiman ya kira yana harabar gidan nan"
Mammi tace
"Abeeha gobe dai tunda saturday ne ku je ki nema mata waya mai kyau"
Murmushi Afeefah tayi tana Mi™ewa
"Sai kun dawo a gaishe su, sannan a kula. Abeeha kar ku jima kin san Yayanku"
Da Toh duk suka amsa suka fice daga parlorn.

Ta jima sossai tana tuna Afeefah a ranta kan ta sauke ajiyar zuciya tana Mi™ewa da kyar cikin yanayin rashin ™arfi da cikakken lafiya ta shiga cikin Waki.

A harabar gidan kuwa suna fitowa Rayyan na parking, gaban Afeefah ne ya faWi zuciyarta ya shiga doka wa da ™arfin gaske, a natse ya buWe murfin motar ya sanyo jikinshi waje Farar jallabiya ce da daga ganinta zaka san tana da tsada sai mai™o take yi kirar Kasar dubai don tana da wani ado mai yanayi da rubutun larabci daga gefen kirjinshi kaWan har karshen hannun hagunshi, hirami ne ba™i mai layi layi fari ya mishi wani Wauri a kai yadda Larabawa suke yi ya zauna mishi sossai yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano ba™a, hannunshi na daure da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ™arshe ke ta daukar idanu.

Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake, ba™ar shade na ma™ale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da yake ba ya shige gidan kamshinshi na buso musu, Abeeha ce ta iya yi mishi
"Sannu da dawowa"
Hannu kawai ya Waga mata wai shine amsar ya shige abunshi.

Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan suna sake gaisuwa.

Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ™asa ta zube tana gaishe da mahaifiyar shi Umma ta mi™a mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta zaunar da ita gefenta tana Wan rungumeta kaWan
"Ina ta jin labarin Wiyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa"
Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daaWin irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da su drinks aka cike musu gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake.

Sun jima sossai har aka yi la'asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka fito shirye don wucewa islamiyya suka yi sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da wani girman jiki a shekaru kuma da kaWan za ta iya fin Afeefar kila su yi sa'a da Abeeha, zama tayi tana ce musu sannu.

Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin Afeefar da bata santa ba amma ta yi matu™ar haddace sunan saboda yawan Ambaton da Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau ta fita ko ado ba haWiye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice.

Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru ta Wan yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ™arshe, Baaba da Umma sun sha kuka umma ta sake rungumeta tana cewa
"Sannu Afeefah... Sannu! Allah ubangiji ya ™ara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk wannan wahalhalun"
Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu'a da tayi ta bin iyayenta da Aunty zee.

Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a Wakin shi a yanzu matsayin matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani yake lokaci ya riga ya ™ure, Dukda haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga yanzu.

Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da ta dinga zuwa mata, har cikin gida ya dawo dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.

****

Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado, da Wan hanzari ya isa gareta

"Mammi! Lafiya kike kuwa?"
Ta Wago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ™arfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa haWe da gajiya, a idanunta wani abu mai wuyar fassara yake karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu Suya ba sam don a kan Mammi baya iya danne damuwarshi.

"Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana"

A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake malale tsakar Wakin.

"Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma'aikinmu sannan akwai wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mutuwar mutum komai nashi zai tsaya chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai Wa nagari mai mishi Adu'a ashe baka Fatan ka ajiye 'ya'yan da za su yi maka Adu'a bayan baka nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka taSa aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin rashin sanin nagarta da kyaun halinka... Ba duka aka taru aka zama Waya ba"

Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam baya so baya son jin zancen wani aure daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san mummunar taSonshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za'a iya kallon cikin kwayar idanunshi a faWa mishi kalmar da har abada ba zai taSa mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.

"Mammi..."

"RAYYAN...!"
A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata taSa ™ira ba... GabaWaya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce

"Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba? Kana so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in barka ban cika alkawarin da na Wauka wa rayuwarka ba?"

"Yaaa ilaihil alameen..."
Ya faWa a rikice sai ya mi™e tsaye don wani irin tashin hankali yake ji, taku biyu yayi gaba ya juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya

Please Login or Register in order to submit comment