Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga akurkinta ta faWi bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.

Ko mintuna biyu bata yi da shiga Wakin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar ana ya™i, idanunta sun kumbure ko iya buWewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu Wa matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba'a fita da ita ba gidan gabaWaya za su ™ona, tashin hankalin da bata taSa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya aka yi 'yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na ihun kar su ™ona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka wulla ta motar 'yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita...



=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*003*

Bayan tsawon lokacin da ba za ta iya cewa gashi ba ta ji sau™ar ruwan sanyi a kanta duk da ta farka sai dai bata da kuzarin Waga ko da yatsar hannunta ne.

" In ba kema da ja wa kai ba ina ke ina cin maita don janyowa mutane bala'i ki mutu a ce ai ba ma aikinmu ne yadda ya kamata. tashi my friend"
Ya ™arasa yana kai mata kafa.
LaluSe take har ta samu ta mi™e zaune gajimare ya rufe mata ido bata iya ganin komai. Ma™ogoronta da ke bushe ko miyau ba ta iya haWiyewa sai kartar ta yake da kyar ta buWe baki ta ce
"R..ruwa..a don Allah"
Ruwan ya tura mata ta Wauka ta afa a baki har kwarewa take sai da ta sha sossai cikinta ya murWa don dama babu komai ciki ai sai amai tana jin Wan sandan na zaginta amma ba za ta iya tsayarwa ba ya riga da ya zo, a lokacin idanunta sun washe tana gamawa ya tasa keyarta ta kwashe ta share wurin cikin layi.

A lungun cell Win ta raSe tana ta aikin ri™e ciki saboda yunwa, Waya dan sandar ya taso yana ™are mata kallo
"Ya dai?"
"Yunwa nake ji"
Murmushi yayi yana gyaWa kai yana sake ™arewa halittarta kallo Dukda rama ya yi mata yawa ainun albarkatun jikinta na daidai shekarunta ba su Suya ba sam.
"Zan sayo miki abinci amma kin san gomnati ta hana aikin banza ko? Nima za ki rama min"
Sam bata wani fahimta don yunwa ba ta da hankali samm kai kawai ta gyaWa ya fice chan sai gashi da filate ya mi™a mata ta fusga ta shiga ci hannu baka hannu ™warya sai da ta fara koshi tukuna ma ta fahimci ashe gari ya waye kenan a cell ta kwana gashi har ana batun ™iran sallar azahar tsabar rashin gata babu wanda ya neme ta, ta tabbatar ko shekara zata yi nan kawu ba zuwa zai yi ba bare ya cire kuWin shi yayi belinta don sun ce sai an ba su kuWin mai za su sake ta...

Bayan ta gama ta ro™i za tayi sallah basu hanata ba ta rama duk waenda aka bi ta. A nan ta cigaba da zama ita daya har dab Magrib wani matashin Wan sanda ne ya shigo yana dubanta
"Ya Sunanki?"
"Afeefah"
"ba ki da kowa ne da zai zo yayi belinki?"
Ta girgiza kai
"Ni marainiya ce kawu na kuma na san ba zai taSa zuwa ba ko shekara zan yi"
'dan shiru yayi
"Afeefah za ki iya komawa gida da kan ki?"
Ta gyaWa kai
"tashi ki tafi to zan biya kuWin belin naki, bana so dare ya sake samunki a nan muna da gurSatattun 'yan sanda bare har kin bari kin ci abin hannun kopur DanJuma sai ya dawo, kuma ba ni da ™arfi ko ikon kare ki"
Hawaye ne suka cika kumburarrun idanunta ashe akwai masu zuciyar imani da tausayi a cikin 'yan sanda? Godiya tayi ta mishi har da kuka a lokacin da zata fita ta ce
"Menene sunanka?"
"Sa'adu. Sa'adu Rabi'u"
"Allah ya dube ka ya shiga cikin lamuranka ya dafa maka"
Amsawa yayi ta fice da sauri lunguna tayi ta bi a tsorace kar ma ta haWu da kopur Danjuma har ta isa gida.

"Uban wa yayi belinki?"
Kawu dake kofar gida ya daka mata tsawa
"Su...su suka sake ni"
Takalman shi ya wuwuro ya jefa mata
"shegiya natacciya dama shiyasa ake cewa mutum maye mana in ya cika naci, kin rantse sai kin kasheni ko? To kafin nan sai na yi ajalinki marar anfani kawai"
Da gudu ta shiga gidan don ya mi™e ya biyo bayanta kaman zai faWi.
Šakinshi ya shiga ya haWo tarkacen da ya karSo na kare kai daga sharrin Mayu yayi Wakinta dorinarshi ya samu ya rufeta da duka wai na hawan jinin da ta saka mishi jiya ta kusa ja mishi asarar rai da dukiya babu wanda ya kula su duk ihu da neman agajinta sai da ya gaji ya kyaleta. Ya sa aka kawo mishi garwashi ya turbune su da uban haya™i mai bala'in ™auri bayan ya gama ya tafi ya barta nan yana cigaba da sababi.

Bata san iya adadin lokutan da ta Wauka a kwance cikin yanayin ba, tun tana kuka da hawaye har suka ™afe sai dai zuci na cigaba da zubar da kwalla cikin ™unci da raWaWin da bata san ranar tsayuwarshi ba, yunwa ne kaman zai yi ajalinta hakan ya sa ta dole ta lallaSa ta fito, yadda garin yayi shiru sossai za ka san cewa dare ya riga da ya tsala murhu ta isa akwai sauran gawayi ta dibo ruwa tana layi ta Wora, a wurin ta zube tana kallon kicin Win babu alamar an ajiye mata wani abu da zata iya ci, busashen miyau da ya ™afe a Bakinta ta lalaSo da kyar ta HaWiye.
Sai da ruwan ya tafasa ta juye hadari ne sossai a garin don har an fara iska da walkiya sai dai dayake zuciyarta a kafe yake yasa babu tsoron komai cikin ranta ta shiga ta gasa jikinta sossai ta fito, kicin Win ta koma da kyar ta samu wani kanzo ta Wan bubbuga ta zuba ruwa yayi laushi ta Wauka ta nufi akurkinta tana da Wan maggi da yaji da mai kaWan ta saka a ciki ta ci bata ma gama ci ba taji sau™ar ruwa kaman da bakin ™warya, ko da ta kwanta baccin sai ya ™i zuwar mata sai tunanin rasuwar yaron jiya take ko wani hali iyayenshi ke ciki? Tana kuma tambayar kanta da gaske ita Win Mayya ce? Da ™yar bacci da ya fi kowa iya sata ya lallaSo ya sace ta...

Rayuwa ya Wauki yi mata zafi a gidan fiye da baya saboda a yanzu tallar bata yi inna larai ta yi mugun tsanarta don ta karya mata kasuwa hakan yasa ko abin da zata ci a girkin inna larai gagararta yake, ba'a isa a aike ta ba haka zata dawo da hawaye saboda maganganun mutane da ma yunkurin illata ta da wasu kan yi, bautar gidan duk ya dawo kanta yanzu har girki ita ke yi musu su zo suyi rabo kuma a hanata don daga an sau™e za'a aike ta kan ta dawo an raba in ta tambaya su ce sun manta da ita, ita dai gata nan amma rayuwar baya yi mata daaWi ko ta wani Sangare.


''Ina ma mutum na da zaSi kan rayuwarsa! Ina ma a ce bawa ke da ikon rubuta ™addararsa! Da ban zaSi maraici ba. Duk bala'i na san ko da kowa zai guje ni su Win ba zasu taSa guduna ba" a hankali take furta hakan wani irin kewa da maraici na taso mata, har ™asan ranta bata son yadda ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, bata son wannan suna na Annoba da yanzu kowa ke ™iran ta dashi... Kanta a du™e ™asa ruwan hawayen da bata rabo da su na sulmiyowa cikin ruwan kunfar wanke-wanken da take yi wani irin zafin da zuciyarta ke yi kaman zata fito daga madaukarta
"Wai zama kika yi kina maitar da kika saba na shanye kurwuwowin mutane ba za ki yi ki kawo mini kwanuka in raba abinci ba?"
Inna larai ta watso mata kalaman cikin hantara.
sharSe hawayenta ta yi, cikin mintunan da ba su wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikinta gefe ta tsaya tamkar ji™a™™iyar kaza da ta rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
KuWin da ta wullo mata a wula™ance ta sanya hannu ta Wauka ta juya tana jefa singallin kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje, ko da ta dawo zaune ta tadda zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan Wumamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da take tsoron ji ita Win dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin raWaWi ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani ba ba kuma ta tunanin za ta sauya Win abu ne da ta riga ta sani a kullum idan har za a raba abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya faWi ™as.

Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ™wa™walwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta da shi ba ta kuma da wanda zai ba ta babu mai Wigon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.

Sau™ar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ™arar azaba a firgice ta mi™e daga dur™uson da ta yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta Waile, daidai lokacin inna larain take faWar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shesshe™a ta fara ro™on su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina murWa suke, yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ™afafu ta hamSare ta ba tare da ta ko damu da raunin ™unar da ke jikinta ba.
"Ba za ki taSa samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin Waura mini abincin rana."
Jiki a saSule ta mi™e ta nufi wurin murhu, a haka cikin raWaWin gangar jiki da zuci ta fara aikin. Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanukan mawanki kowa ya nufi Wakinsa don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ™arfin mi™ewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar dake dawainiya da rayuwarta.

Šan sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta haWe da tukunyar ta kankare ™asan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula inna Larai dake mata gargaWin kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta mi™e ba don ta ™oshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ™arasa ta kwalfi ruwa ta afawa cikinta. A gindin randar ta raSe cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.

"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sureıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿ ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta tare da kiran sunanta.

"Lafiya kike bacci a nan?"

Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai maganar da muryarta yayi kama da wacce ta sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta. Sanyin farincikin sanya mace guda da ta rage mai ™aunarta kaf faWin duniya a idanunta, tashi ta yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ™arewa fuskarta da ma jikinta kallo ne ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ™ai™ayi. Dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da ™yar Afeefah ta yi shiru kan matar ta buWe jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ™warewa, matar ta Wibo ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da kawu ya fito shirye da alama kasuwa za shi..


"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ™arfin ™addara ba. Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ™ar™ashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka, a yau za ka iya faWuwa ka mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"

Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi Sacin Sacina kuma ki daina haWa yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko Waya ba, ban kuma shirya mutuwa ba. Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya sake kallon ta.
"Af! Idan ™arshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Mi™ewa tsaye ta yi a zuciye.

"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a saman dami, idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tashi mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta Aunty zainabu da ita kaWai ce ™anwar mahaifiyarta ta so karSar ta sai dai kakarta ta ™i har ma ya kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau Waya ta taSa zuwa ta duba ta a gidan kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo sau biyu sai dai bata taSa wuce awa Waya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani kauye gaba da su sossai take.

Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a yanayin da ta sameta ya matukar Waga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su faWo ta saisaita ta mi™e da sauri ta shige akurkin Wakin nata. Wani tunani da ya Warsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ™arewa Wakin kallo cike da tausayawa ta du™a gangarta tare da dafa kafaWarta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da tunanin da zuciyarta ke yi.

"Sau tari ™addarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sau™i. Mu tafi."
Taya ta tayi suka haWa yar Ghana most go Winta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ™eya suka bi su da shi don yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.

Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya matu™ar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya haWu da bata taSa shiga mota ba a rayuwarta don bata taSa barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata san akwai titi kwantacce irin hakan ba sai da suka Wauki titin cikin garin Anchau daga kauyensu chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sau™a ba ma su isa tasha ba don Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sau™a suka yi ta Wauki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan ™arfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai dai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida da take da tarin shuke-shuke.

A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta buWe karamin frigde Winta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na Wora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai takura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gyaWa tana ya™e dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ™i tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka shiga yi tare tare har suka gama, shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"Wauka ki koma ™asan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.

Aunty zainabu dai na ta kokarin haWa na mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai har yanzu babu wani labari na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.

Tana ™o™arin kai loma yana sallama, ta amsa ya Wan yi turus yana kallonta gabanta ne ya Wan faWi don ganin fuskanshi ya Wan sauya ko da ta gaishe shi da kalma Waya ya amsa kan ya nufi ciki yana kiran zainabu...



=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls bear with me ku ri™e wannan as na chan anjima Win tunda Its already friday.*

*004*

A wurin ta cigaba da zama jiki a saSule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har ya Wuri ruwa saboda ™una daga gefe zuwa ™asan idanunta, Allah ya ta™aita ma bai taSa idanun ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"

"Eh Aunty na gama"
Ta faWa a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle Winki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ™unar kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta mi™e ta shiga parlor zuwa Wakin da ta ajiye mata kayanta daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika Wauko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ™ira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta Waga mishi murya ba sai yau. Kuka ta fara
"Haba Usman na fa faWa maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah Wiyar yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."

Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki Wauko ta ki kawo min cikin gida?"

Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taSa yarda Afeefah zata yi maita ba, babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ™are idan ko don ka zauna da mutum kwana ya ™are ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar da ita gidan labaran ba wallahi"

Numfashi mai karfi ya sau™e
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"

A lokacin Afeefah ta sulale ta ma™ale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta Wago kai
"Aunty don Allah ki yi ha™uri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye

"bawa baya taSa wuce ™addarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taSa iya sake barinki ki zauna wurin 'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ™una a wurin kan suka dawo.

Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke ma™otaka tana saya kuma ta sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba tela akan zai Winka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar yadda zata so mahaifiyarta.

Da kaya sossai suka dawo niki niki, a Wakin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu Wan dama suka tafi da su kasuwa aka rarrage mata yadda zai ™arbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.

Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo, natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi

Please Login or Register in order to submit comment