Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

always be there for you... Ka yi kuka just let your worries our this will be our Lil secret ka ji?"
Har lokacin bata daina shafa suman kanshi ba cikin wani irin kulawa, sake ™am™ameta yayi kaman zai Sallata jikinshi na sake Waukar rawa zuciyarshi na wani irin tsitsinkewa Dukda irin yadda take ji da zafi dake ratsa ta haka ta sake hugging nashi, she hugged him until his soul melts into tears sai ji tayi yana sauke wani irin numfashi mai tafe da zafafan hawaye masu rikitarwa.

Lips Winta ta datse tana runtse ido a sadda sautin shi ke shiga cikin kunnuwanta a hankali yana samun masauki a cikin zuciyarta, bata daina shafa shi ba shi kuma bai daina sake kankanmeta ba ya fi mintuna talatin cikin wannan yanayi kan a hankali ya fara sassauta ri™on, gefe gefe tayi ta kwanta yayinda ya bita har lokacin kanshi na kan chest Winta dake beating so so fast tana shafa shi da hannunta tana jin jikinshi na sauyawa daga zufa zuwa zafi dake shiga har cikin jikinta, sai da suka kai kwance ta iya jin ruwan hawayen shi na sauka a kan silk maroon rigan baccinta Yana taSa fatarta ta runtse ido kawai. Basu san iya adadin lokutan da suka Wauka a hakan ba har bacci ya Wauke shi itama baccin tayi.

˜arfe biyu da wani abu ya sake farkawa, shiru yayi yana shakar fitinannen kamshinta yana jin hannayenta a jikinshi, Waya a cikin tattausan gashin kansa Waya a bayan wuyanshi, a hankali ya zame ya mi™e zaune wutan Wakin a kunne har lokacin amma ba tarrr ba mai Wan duhun yana iya kallon fuskarta a haka, idanu ya zuba mata yana aikin kallo her caramel skin, dogin lashes Winta pointed nose Winta zuwa thin beautiful lips Winta he just felt lost a kallon nata moments Winsu na Wazu na dawo mishi kaman yanzu, he can't believe that it happened.

It really happened! he cried in this little Girl's arms, the way she caresses him, pet him like a Lil boy ya tsaya mishi sossai a rai. Sau™a yayi daga gadon ya ja duvet Win ya rufeta zuwa kirji sai ta Wan gyara kwanciya kaman dama a takure take ya shiga toilet yana jin wannan nauyin na cikin zuciyarshi ya ragu, ruwa ya kunnawa kanshi ya jima a ciki har lokacin kuma duk motsinshi kallon kanshi yake akan chest Winta tana bashi utmost kulawa, wanka yayi ya fita ya zo ya nemi jallabiya ya saka ya fara nafilfili har sai da ya ji zazzabi na neman fin karfinshi ya mi™e ya zare jallabiyar ya saura daga shi sai guntun wando da karamar vest da ya bayyana duk wani kakkarfar sura mai cike da zati da Allah ya mishi gadon ya hau ya ja bargon shima ya Wan rufa tare da juyawa ya zubawa face Winta idanu tana baccinta peacefully har bacci ya sake sace shi a haka.

Ita ta fara farkawa da asuba ta sauke idanunta akan kyakyawar fuskarshi, ta Wan jima tana kallonshi kwakwalwarta na tuna mata abin da ya faru a daren, nauyi da kunyarshi suka lallaSo suka rufeta amma ta kasa Wauke idanu daga kallonshi he's just handsome so so handsome da bata san ya zata kwatanta shi ba, yana baccin kaman ba shi bane Saraki mai zuciya a kusa, wannan masifaffen marar fara'a da son Magana murmushi ta tsinci kanta da yi Alhamdulillah atleast ta samu riba a kanshi wani abin dole ta san ya ragu mishi hakan kaWai ya faranta mata, sau™a tayi daga gadon tare da Waukan hijabinta ta saka ta shiga toilet don yin alwala tana jin ko me ta mishi bata ragu ta kowani fanni ba saboda he's her life savior ba don shi Win ba da yanzu tana cikin matattu matattun ma cikin sahun masu gingimemen laifi wa ubangijinta.

Tana rufe kofan bayin ya buWe idanu sai dai bai motsa ba don zazzabi ne sossai a jikinshi har numfashin da yake fesarwa na fitar da zafin hucin zazzabin, bayan tayi alwala ta taho gadon ta taSa goshinshi sai taji shi rau a hankali ta shiga kiran sunanshi

"Ya Saraki..! Ya Saraki...!!"
Ya rasa wani irin effect sunan ke dashi a zuciyarshi don wani irin tsalle zuciyar tashi tayi a sadda ta ™ira sunan cikin tsiririyar muryarta
Idanu ya buWe ya kalleta
"Sannu! Na ji jikinka zafi sossai za ka iya tashi ka yi sallah? Ko in idar in kawo maka ruwan nan?"
Idanunta kawai yake kallo hakan ya sa ta kawar da idanun yace a hankali
"Zan iya"

Daga haka ta koma baya ta tada sallah kar ya ga kaman ta cika za™ewa, shi kuwa ya Wan jima a haka kan ya yunkura ya mi™e zaune yana dafe kanshi, a hankali yake tafiya har ya isa bayi yayi alwala ya dawo sai ya kasa Sallar a tsaye duk kafin halinshi a zaune ya gabatar bayan ya idar ya mi™e ya koma gadon tare da lullubuwa, bayan ta idar ta mi™e ta ninke sallayar tana shirin fita wayanshi ya Wauki ™ara sai ta koma taje ta Wauka ganin Likitarshi yasa ta Waga suka gaisa take tambayarta ya ya kwana nan ta mata bayanin zazzabi ne a jikinshi sossai Dukda ya samu ya zub da hawayen.

Hamdala tayi da farko kan tace za ta turo yanzu collegue Winta zai zo ya saka mishi drip da wasu allurai in shaa Allahu zuwa yamma zai samu lafiya don Allah ta kula dashi ta amsa tare da godiya ta sau™e wayan, ficewa tayi zuwa kitchen ta ga abinda suka fara a lokacin gari ma ya fara haske taje ta watsa ruwa don duk yadda ta motsa kamshinshi kaman tayi wanka da turarenshi kamshin na sakata jin kaman har lokacin yana kwance ne a jikinta rungume da ita Dukda ba don soyayya ko wani romance suka yi ba taimako ne ta mishi amma hakan ya mugun tsaya mata,bayan ta fito ta shirya cikin atampharta riga da siket da ya zauna mata chass ta Waura dankwali sai ta nemi gyale mai girma da kauri ta yafa ta fita parlor tana shirin shiga side dinshi aka yi mata sallama.

"Mery ya dai?"
"Wai wani likita ne ya zo duba Oga Rayyan"
"oaky ki ce ya shigo"
Tana nan tsaye har ya shigo suka gaisa kan ta mishi jagora har ciki, har lokacin yana kwance ba bacci kuma yake ba don zafin zazzabin bai barshi ba, tana daga chan gefe har likitan ya haWa drip ya mishi allura ciki ya saka mishi canular yayi wani a canular kan ya Waura ruwan sai Sata fuska take kaman ita ake Sula wa.

"Toh madam za ki iya samun ruwa masu Wan dumi kaWan da towel ™arami a shafa mishi a kan nan da Goshi zafin jikin zai ragu Dukda na mishi allurai amma hakan ma na da kyau don temperature Win shi is very very high"

"in shaa Allahu mun gode kwarai Dr"
"Mention not"
Daga haka ya fice, bayi ta tafi ta haWa ruwan ta samo ™aramin towel ta dawo bakin gadon ta zauna ganganshi ta cire gyalen ta ajiye tare da matsa ruwan ta Wora mishi a Goshi ya buWe ido ya kalleta saboda sanyin da ya ratsa shi yana sau™e ajiyar zuciya mai nauyi, wani iri take ji da kallon nashi amma ta dake ta cigaba da shafa mishi da kanshi ya gaji ya mayar da idanun ya rufe sai ta sauke numfashin da ta ri™e tuntuni, idan ta zo daidai kwantaccen sajenshi sai ta tsinci kanta da zame towel ta bar fatar hannunta na shafa lallausan gashin wurin a hankali.

Jin abin nata na so ya fi karfinshi ya Waga hannu ya ture hannunta, ta Wan tura baki ta mi™e ta nufi bayi tana mita
'Mutum bama shi da lafiya amma hali ba zai chanza ba!' Sarai ya ji ta a maimakon ya ji haushi Sai Wan murmushi da yayi a cikin zuciyarshi wanda ko alama bai fito fili ba, bata ma fito ba bacci ya Wauke shi don akwai allurar bacci ciki daga nan ta Wauki gyalenta ta yafa ta nufi cikin gidan, Wakin su Abeeha ta shiga inda ta samu suna zaune sun yiyyi wanka Mommy da mama da suna nan tun rasuwar basu tafi ba suma suna Wakin da alamu sun zo duba kwanansu ne.

Har ™asa ta du™a ta gaishe su suka amsa cikin kulawa kan ta dubi jannah ta gaisheta tare da mata sannu da jiki suka gaisa da Abeeha a karshe, wata cousin Winsu Aaliyah ce tace
"Na ga likita yana shiga wurin ku da safen nan Allah dai ya sa ba wani abu bane?"

Kanta ™asa tace
"Wlh Ya Saraki ne ya kwana da zazzabi amma Alhamdulillah an saka mishi drip yanzu haka bacci yake"
Cike da jimami suke mishi Allah ya kara sau™i ta Wan jima anan har aka gama fito da kayan kari ta karya anan suna hira kaman dama chan ita ma she's part of the family don basu ware ta ba sam.

Sashensu ta koma ta le™a ta samu har lokacin bacci yake ta koma parlor tana kallon time, a chan kuwa fitan ta ba jimawa sai ga su mommy sun shigo babban parlor aka dawo da gaisuwar makota dai kan shigo a yi gaisuwa da su ˜awayen su Afeefah har ma da dangin mijin jannah ita dai Samha sai baza ido take ta ga ta inda Afeefah za ta Sullo amma bata ganta ba.

Ko da Saleem ya shigo suka gaisa Abeeha ya tambaya Rayyan fa don ya ta kiran wayanshi ba'a picking nan ta faWa mishi ai bashi da lafiya an ma saka mishi drip kila bai tashi ba har lokacin, bai shiga ba don ya san akwai bambancin da da yanzu ba zai yiwu ya je har Wakin ba sai fita yayi akan yana parlorn waje.

Sai karfe sha Waya da rabi da Afeefah ta le™a ta samu baya kan gadon alamar ya shiga wanka, gadon ta gyara tsaf kaman ba'a kwanta ba ta fice chan sai gata rike da tray mai dauke da dafaffen dankali sai wani curry chicken soup da ta mishi da kifi gasashe a gefe sanin yana so sai tea da ta haWa mishi, ya gama shiryawa cikin riga da wando masu taushi don ba jeans bane wandon cotton ne mai Wan faWi Brown, shirt Win burnt orange ya karSe shi sossai ya sake zama pale kana kallonshi zaka san yana ciwo.

A kan table na gaban couches na Wakin ta ajiye ta kalleshi shima ita ya kalla sai suka haWa idanu ta Wan rausayar da nata tace
"Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?"

Bata zaci zai wani amsa ba sai kuma taji ya ce
"Alhamdulillah da sau™i"
Dukda a hankali yayi magana amma ta ji ta Wan murmusa
"ka karya sai ka sha magani"
Ya nufo inda take sai da ya Wan wuce taji ya ce
"Thank you!"
Zama yayi ya ja abincin ya shiga ci hakan ya faranta ranta sossai ta juya ta fice, a parlor ta zauna tana kallo kusan mintuna talatin sai gashi ya fito ya fita waje.

Sai lokacin hankalinta ya kwanta ta mi™e itama ta nufi wurin su Jannah tana shiga babban parlorn da sallama suka hada idanu da Mommy...




=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*


*41*

"Sannunku"
Ta faWa tana Wauke kanta daga cikin idanun mommyn da ta kusa daskarewa a wurin a zaune.

Bata ™ara firgita ba sai da taji matar uncle sanusi na cewa
"Sannu Afeefah, jigilar nan ba zai haifar miki da ciwon jiki ba? Kece nan ke ce chan ya kamata kina hutawa fa"
Matar uncle Mansur tace
"Gaskiya kam ya kamata ki dinga ji da mijinki kawai su jannah duk ba ga mu nan ba, shima ba don baudadden halinshi ba ai da duk sai mu kula da ku don kema na tabbatar raunin tafiyar Mammi na nan Wanye a zuciyarki."
Murmushi ta Wan saki tana zama za tayi magana Sameera ta mi™e tsaye don tun dazu duk su huWun kaman an kafa su ne idanunsu ™urrr a kanta.

Nuna ta take hannunta na rawa
"Afee...fah?"
"Ita ce ko Ya Sameera? Ita ce ba gizo na gani jiya ba ashe!"
Samha tayi saurin faWa kaman jira take wani ya fara magana cikinsu.
Mommy ta kasa ma magana tsabar yadda taji da ganin Afeefar ™are mata kallo take yadda ta wani sauya tayi mugun kyau ko atamphar jikinta ka gani ka san bata cikin wahala sai hawaye suka fara zuba mata ta tuna ranar auren Saleem inda take ce mishi a lokacin Afeefah na chan tana raba wa maza kanta tana samun na cin abinci idan zai mantata gyara ya mantata.

"Kun santa ne?"
Mama tayi tambayar da mamakin irin shock da ta gani a tare da su ga mommy ta fashe da kuka.

Jannah ce da daman ta kasa sakewa dasu saboda har lokacin bakinsu take gani akan abinda suka yi wa Afeefah tace
"Sun santa Mama, mommy kin ga ta sauya ko? Kun ga yadda Allah ke ikonshi ko? Ku kun ™i ta mu mun so ta mun karSeta hannu bibbiyu, kun muzguna mata hakan bai hana ta muku taimako mafi girma ba a rayuwarku... Ita ce ta taimaka da ayoyi da ruwan tofi ba ji ba gani har saida ta tabbatar asirin da aka yiwa Ya Saleem ya karye, gata nan yanzu haka ana dawowa makaranta exams na karshe zasu rubuta tana kan karatu. Nasara mafi girma da daraja shine tayi aure ta auri namijin nunawa sa'a wanda ko cikin maza sai an tara dubu a samu tamkarsa Waya. Afeefar da kuka sani ce dai ita ce matar Ya Rayyan ta sunna a yanzu haka"

Afeefah ta mayar da kanta ™asa hawaye na taruwa a idanunta sam bata san sun zo gangarta ba sai jin mommy tayi ta ri™e hannunta tana sake ™ara fashewa da kuka mai tsuma rai, Abeeha ma bata yi shiru ba ta kara da labarin irin yadda ta taimakesu akan Saleem.

"Don Allah ki yafe mana Afeefah, ha™i™a ba mu da bakin neman yafiyarki saboda mun aikata miki ba daidai ba, mun kasa duba kasantuwarki mace mun kasa yarda cewa Allah ke komai a sadda ya so na bi dare na raba ki da Saleem karfi da yafi na aura mishi wacce nake ganin ta fi cancanta ashe ban sani ba ™abari na ha™a mana... Ha™i™a na so na ganki ba tare da aure ba nayi adu'ar Allah ya bayyana mini ke ko ta wani hali in nemi yafiyarki in kuma gyara kuskurena ashe ke kam Allah ya dubeki ya Musanya miki da alkhairinki... Don Allah ki yafe mana ki yafe mana Afeefah!"

Sossai duk suke kuka suna neman yafiyarta sai ta nemi rudewa Dukda tayi mamaki amma ta sani duniya aka ce makaranta.
"Mommy ku daina neman yafiyata wlh tun kafin na bar gidan duk na yafe muku Yaya Saleem ya wuce yadda kuke zato a wuri na. Ban ri™e ku a zuciyata ba ku daina wannan kukan don Allah".

Samha ta fi kowa bata ha™uri sai Mommy, duk ta nuna ita komai ya wuce a wurinta suka koma gefe suna ta kallonta ko motsi tayi burgesu take, basu taSa sanin haka take ba sai a yanzu yinin da suka yi a ranar suka kara sanin wacece ita kunyar duniya duk ya rufesu na tunanin duk irin wulakancin da suka yi mata, lallai da gaske ne da aka ce mai ha™uri shi yake dafa dutse har ma ya sha romonta.

Mommy ta tabbatar Saleem bai san da wannan labarin ba, gab za su tafi ta kira shi a waya akan ya zo ciki duk jama'ar sun watse a babban parlorn sai Afeefah dake zaune tana duba abu a waya mommyn ta fito daga Waki ganinta yasa tace
"Yauwa ashe kina nan dama ke zan je dubawa kitchen. Yanzu Saleem zai shigo ku gaisa..."

Gabanta ne ya faWi rabon da su hadu kusan watanni bakwai zuwa takwas kenan, ya rabu da ita cikin kuna da zafin zuciya tare da hawaye a yanzu zai haWu da ita matsayin matar aure, matar ma ta abokinshi me zata ce mishi? Ta san akwai laifin mahaifiyarshi a rabuwarsu amma ta san dole zai ji zafin samun wannan labari, anya ma zai yi farin ciki da ganinta? Bata gama tunanin ba ta ji sallamarshi gabanta ya sake faWuwa ta mi™e tsaye sai suka haWa idanu a lokacin da take amsawa da iyaka lips Winta.

"A...Afeefah? Ke..ke ce nake gani? Afeefah ba gizo idanuna suke min ba kece tsaye a gabana?Ta yaya kika zo gidan nan? Ina kika shiga Afeefah? Ina kika shiga...?"
A ruWe yake maganan idanunshi na cika da kwallah kaman yadda nata ya cika fal da hawayen ganinshi.

"Ya Saleem...!"
Ta faWa a sanyaye sai ta kama hawaye.
Sake matsowa yayi kaman zai taSa ta tayi saurin matsawa baya sossai tana girgiza mishi kai.

"Ka gafarceni Ya Saleem yanzu da baya ba Waya bane..."
"Afeefah na san akan mahaifiyata ne wlh yanzu duk sun yi nadamar abin da suka aikata miki, na tabbatar za kuma su nemi yafiyarki don Kullum adu'arsu shine mu ganki mu nemi yafiyarki...ko babu komai a yanzu za mu cika burinmu za mu cika alkawarinmu na mallakar juna..."
Daidai lokacin Rayyan ya sanyo kai parlorn he just stood there fuskarshi kadaran-hadaran yana kallonsu.

Hawaye take yi sossai
"Lokaci ya riga ya ™ure ya Saleem, kayi hakuri Allah bai nufa na zama rabonka ba. Ni din yanzu matar aure ce."

Jikinshi yayi wani irin sanyi wani tashin hankali da damuwa na lallaSo wa ya rufe shi murya na shaking yake furta
"A..a..aure Afeefah? Aure kika yi? Da waye? Me..me yasa?"

Idanunta ne suka shiga cikin na Rayyan da sauri ta kawar heartbreat Winta na kara gudu ganin kallon da yake mata.

"Ka sa a ranka ™addara ce ta zo haka, amma ni matar aure ce don Allah ka ajiye zancen ala™ar da ta riga ta wuce Ya Saleem"
Daga haka tayi saurin wucewa sashensu ta barshi kanshi a matukar kulle, idan bai ce ya matu™ar kaWuwa da wannan zance ba yayi ™arya zuciyarshi raWaWi ya shiga mishi, saboda rauninshi tuni hawaye suka shiga zubo mishi ha™i™a ya so Afeefah kaman ranshi har gobe yana ™aunarta amma gashi ™addarar su ya zaSar musu rabuwa aure tayi a sadda yana chan ya rasa hankalinshi, me yasa bata yi ha™uri ba? Meyasa bata jira ba? Me yasa yayi jinkiri? Tun da ya dawo hayyacinshi a neman ta yake ko Allah zai sa ya ganta ashe ita kam tana chan tare da mijinta tana rayuwa mai kyau don ko skin Winta ya bayyana hakan.

Mommy ce ta fito ganin yanayin da yake ciki ta kalli Rayyan dake tsaye har lokacin a bakin kofa hannunshi harde a kirjinshi wanda da alama Saleem Win bai kula da wanzuwar shi ba tayi saurin kama Saleem Win ta zaunar taje ta kawo mishi ruwa bai karSa ba sai ma maganganu da ya fara

"Mommy ta ya kika ga Afeefah? Me ya kawo ta gidan nan? Mommy wai da gaske Afeefah aure tayi? Aure tayi? A yanzu haka Afeefah ta haramta mini?"
Mommy ta kalli Rayyan ta mayar da idanunta kan Saleem.

"Saleem Afeefah ta yi aure laifina ne duka, laifina ne ta subuce maka ka yafemin ciwon da nake sakawa zuciyarka ka Wauki dangana da ha™uri. A gidan nan muka samu Afeefah tana kuma auren abokinka ne Rayyan..."
Da ™arfin gaske ya mi™e har yana Buge ruwan hannunta ya faWi ™asa
"Rayyan?? Mommy all this while Rayyan na tare da Afeefah? Har ma ya aureta? Rayyan dai Rayyan Moh'd Khamis??"
GabaWaya wani duhu ne ya taso ya rufe mishi gani tsabar wani irin bacin rai da ya zo mishi juyawa yayi zai fita yaje ya samu Rayyan Win sai suka haWa idanu nan ya nufe shi ya tsaya a gabanshi.

"Rayyan da gaske Afeefah ka aura?"

Shi karan kanshi ya san yayi mugun ™o™ari a sadda ya buWi baki ya furta

"Saleem Afeefah matata ce idan har ka san darajar aure da kuma martabarsa za ka kiyaye irin kalmanka a kan matata... ˜addara ta riga ta raba ku ta bani ita a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba don haka don't Look at me with those eyes dake nuna kaman I betrayed you or something like that, you should questioned yourself nd your family not me..."
Yana kai nan ya wuce don har ga Allah bai san dalilin da yasa yake ji kaman zai kama da wuta ba, mommy ya kalla har kaman zai wuce ya tsayar da idanunshi kanta ba zai iya yi mata magana kai tsaye ba ba kuma don komai ba sai don uwa ce ya juyo ya kalli Saleem dake kallonshi rai a tsananin Sace yace in a respectful manner.

"Rasuwa aka yi mana ko ba rasuwa ba muna da darajar da ba za'a tako har nan a ci mana mutunci ba Saleem, idan ba zaka taya mu ba™in ciki da jajen rasa wani sashe na bangonmu ba za ka iya zama da kai da familyn ka a gida. Mun gode"
Daga haka ya nufi sashensu ya bar su nan tsayŭ˙˙˙ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~e calmly kaman ranshi ba suya yake ba.

Wani irin duka Saleem ya kaiwa bangon wurin yana yin baya tare da zuba yatsun shi cikin gashin kanshi kaman zai fashe haka yake ji, su Samha ne duk suka fito a tare da Abeeha jin salatin mommy.

Ganin yanayin da suke ciki suka shiga tambayar me ya faru? Menene?
Mommy tana zubar da hawaye tace
"Na sake wani kuskuren, da na san hakan zai kasance Saleem da ban nemi ku gaisa da Afeefah ba! Na zaci zaka yi farin cikin ganinta idan ka ji kuma tana da aure zaka taya ta murna da Adu'a ka karSi kaddara amma me kayin nan? Abokinka ne fa Rayyan abokin da ya zama Wan uwa ya kuma tsaya mana duka a sadda muke neman tagayyara. Rasuwa fa mahaifiyarshi tayi ko lafiya bai samu ba me kake yin nan?"

"Rayyan ya ci amanata mommy, ashe ya san inda Afeefah take ya zaSi ya Soye min? Ashe aurenta yake shirin yi ko da na matsa ya nemo min ita a sadda ba ni da daman hakan saboda kalamanki ya san inda take ya dinga zurma ni akan ya neme ta ya rasa? Meyasa tun farko bai ce min sonta yake in sakawa zuciyata hakan ba? Idan ba da wata manufa yayi hakan ba Meyasa ina zuwa gidan nan bai taSa nuna min tana nan ko ya bari na ganta ba?"

Abeeha da ranta yayi mugun Saci tace
"Ya Saleem baka kyauta ba sam...! Ban zaci ko Ya Rayyan amanarka ya ci zaka iya aikata hakan kuma ka jefe shi da irin kalaman nan ba. kar hankalinka ya gushe mana... Toh wallahi Yaya Rayyan ya auri Afeefah ne bisa umurnin Mammi, ya karSi auren cike da tunanin mai zaka Wauki hakan a duk sadda ka dawo hayyacinka... Idan ma ya faWa maka a lokacin kake nemanta cewa coincidently sun haWu a sadda ta taimaki Mammi Mammi ma ta taimaka mata ta kawo ta gidan nan me zaka yi? Kar ka manta a sannan Allah ya isan mahaifiyarka ke kanka muddin ka mata magana? Idan da yana da mugun nufi kanka da ba zai ba da gudummawar dinga kawo ka gidan nan kana ci da sha daga ayoyin Allah ba har ka dawo cikin hayyacinka...idan da yana da wata manufa ta daban da ba zai bari ku kasance tare da ita a zaman makonkin nan ba don kaima ka san zai iya kaita ko ma inane... Wallahi ko ni bayan labarin da Afeefah ta bamu na ji har abada ban bata goyon bayan aurenka ba, Mammi ta zaSa mata miji kuma ta karSa hannu bibbiyu kuma take ibadar aure... Ko da Yaya Rayyan baya sonta a baya bai kyamaceta ba Dukda ya san labarinta kaman yadda kaima baka kyamaceta ba bambancin kawai mu da mahsifiyarmu muna sonta kuma muna so rayuwarta ta inganta ashe idan baka godewa Ya Rayyan ba ba zaka ga ba™in shi ba. Ka je kayi nazarin kalamaina kan ka sake yanke kowani irin hukunci ne"

Tana kai nan ta juya ta koma ciki cike da jin haushinsu dukkansu, tunanin ta ya tsaya akan ya Rayyan da banzar zuciyarshi Allah ya sa kar ya sauke akan Afeefar.

Tana zaune bakin gado ta toshe bakinta

Please Login or Register in order to submit comment