Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a yadda take a yanzu, haka islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee Win ke nuna ta matsayin Wiyarta.

Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag Winta, fuskanta ya fito fess a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin Winta har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga Wakin uncle usman ta samu ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta Wan duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa

"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci"
Afeefah tayi murmushi
"Toh shikenan na wuce makaranta"
"karSi"
Ta matsa ta karSi Wari biyu da yake mi™a mata
"Sai kin dawo a mayar da hankali"
Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.

Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu programs na makarantar, bata da ™awa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams ake don haka yau revision ™arfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.

Sai dai ta samu babu kowa, ta karSi key a ma™ota ta shiga sai da ta zare uniform Winta ta sauya da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta Waura dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta Wora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san suna da dangin nesa nesa ta Sangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee Win ba ta su take ba abinda ke gabanta ma ya fi karfinta.

Tana sau™e faten doyar sai ga su sun shigo
"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"
Aunty zee ta le™o kicin Win tana tambaya
Dariya Afeefah tayi
"Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"
Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta mi™awa Afeefahn, Afeefah ta karSa ta shiga saka mata kan tace
"Eh Afeefah ban jin daaWi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ™ani"
Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee Win sai ta hau hawayen murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta a duniya?

Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace
"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle Winki da ma Wayar Auntyn taki da suka tasa ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana yasa"
Tana murmushi ta ™arasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa a cin abincinta.

Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term Win don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee Win ba, ko tsinke in ta ga zata Waga za ta karSe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani Sangare, kishiyar Aunty zee Win ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haWu da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba tunda babu abin da ya haWa su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan so bata damu ba sam.

Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta
"Aunty ki taya ni murna"
Result Win ta mi™a mata
"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"
Kai ta gyaWa tana ta dariya.

****

Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa Aunty zee Win hira kaWan kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huWu kenan.

A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah Win tana da matu™ar buri a kan rayuwar Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah
"Wai kuwa kin san kamanninki har ya Saci da Yaya Aisha?"

Afeefah ta Wago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin Aunty zee Win
"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"
Mi™ewa Aunty zee ta yi ta shiga Waki ta Wan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da cikinta har ya turo sossai ta zauna.

"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin bikinta ne da babanki"
Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na Wan rawa ta sanya ta karSa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar ta irin na mamanta ne, ba™in fatarsu mai she™i, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su, karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda Waya da maman nata ke dashi a gefen hagu itama tana da shi.

RaWaWin maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici? Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk duniya idan da za'a ce me take bu™ata ayi mata ko da abu na ™arshe ne za ta zaSi su yi rayuwa na har abada amma ake mata ˜azafin kashe su, anya zuciyarta za ta taSa warkewa? Anya za ta iya yafewa masu alhakinta?

Šago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee
"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaSi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuWi ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba? Yanzu wannan pure soul Win ni na kasheta ko?"
Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ™asan zuciyarta na ciwo da raWaWi...






=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku yi ta Adu'a mu ™are a haka ina jin karsashin typing, ina jin daaWin comments Win ku Allah ya bar ™auna*

*005*

Hannunta ta ri™e cike da tarin tausayinta da kuma ™aunar da take jin tana mata fiye da ™ima ta shiga cewa
"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ™age ne kawai da ˜azafi irin da jahilai daga cikin al'ummar mu, ™arancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a ™ar™arorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuSe bawa yayi sai an faWi dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.
Afeefah Kowacce rayuwa akwai ™alubale ciki ke kuma ta ki kalar ™alubalen kenan, amma fa na faWa na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ™are ne ko da sanadi ko babu dole babu ma™awa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ™aunar da kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ™untatawa kan ki saboda ™addarar da ba ke kika Worawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassa™a ba su isa su hana ki toho ba"

Jikin Aunty zee kawai ta faWa tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta Wago
"Na miki al™awari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taSa kuka a kaina ba"
"Allah ya amince hajiya ta"
Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar 'yar kasuwa don tana so tayi kuWi saboda wani dalili nata. ˜aurin kamawar leda da suka ji ya sa ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta
"Aunty alele na so yayi mana bu™ulu"
Aunty zee na dariya tace
"Hira ta yi daaWi ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"
Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ™asan guda biyu da ledar ya ™one nan ta zuba musu tare da Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata
"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"
Murmushi ta saki kan ta karSa tana godiya.

Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta Sangaren Afeefah tana nan tana ™o™arin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta Wauki na Waya kuma 3rd term nan suna ™are ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee Win ta shigar da Afeefah cikin business Win ta, wani lokacin ta kan aike ta ita kaWai ma kasuwa wurin customers Winta kuma ta zo ta raba wa clients Winta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da kayanta idan bu™atar hakan ta taso.

A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi, hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ™irata, ta fi kowa shiga damuwa an ™arbe ta zuwa Wakin haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruWewa babu abin da take tunawa vividly sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ™arshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba zata taSa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaWa a yanzu Allah kaWai ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.

Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes Win da suka karSi haihuwar suka fito suna musu albishir na ta samu 'yan biyu mace da namiji faWin kalar murnar da suka yi Sata baki ne. Karo na barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin sha'awa kaman ta HaWiye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta
"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"
Da sauri ta juyo tana dariya
"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"
Ta Wan saki murmushi.
"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"
Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sau™a sai da ta ji Wuminsu kan wannan wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe ta da ganin ™wanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta ba don ko yau ta faWi ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a, bata san daaWin haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da ba™in ciki har abada matukar suna kusa da ita.

A hankali Afeefah take kokarin Waukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn
"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike Waga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki Waga su?"
Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da hankali ba don Aunty zee ta amsa mata
"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"
"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taSa su bare wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"

Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta Wago ta kalleta
"Me kike nufi Hamdiyya?"
"Gaskiya nake faWa Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya koma ba™in ciki ba"
Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi Aunty zee ta Wora mata yaran duk biyu a kan kafafunta
"Afeefah ga su nan ™annenki ne, ki ri™e su yadda kike so"
Juyawa ta yi ga hamdiyya
"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taSa zuba ido ki tozarta Wiyata a gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaWin su ko? To wallahi zan iya zaSar Afeefah sau dubu kan in zaSe su sau Waya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"

"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"
Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe da kuka mai ™arfi tana yun™urin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ™warai wurin haWe kawunansu ba zai so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin farin ciki tsantsa.

"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haWa ku?"
Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta
"Ka yi ha™uri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk Waya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"
"Zainab!"
Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaWi
"Gori kika yi mata?"
"Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taSa yi mata ba don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye

"jita-jita bai taSa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a kan Afeefah amma na Wauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ™aunarta, abin da nake tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi ha™uri da daukar su har su yi kwari shikenan na yi laifi...? Ku yi ha™uri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faWa mishi abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaWin reaction na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.

"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sau™e mu raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raWaWin zuciya tun ranar da uncle ya amince ta zauna da su sai yau.

Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi haWe da rashin imani zai sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce ta rungumeta ta cicciSota ta zaro ta daga cikin bala'i da ™uncin rayuwa?

"Afeefah..."
Auntyn ta ™ira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin Wakin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare abin hawa ta faWa mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana tuburewa, maganganu take gayamishi cikin Waci da nuna kaman shi ne ai ya zaSi ya ba Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.

"Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".

"A'a Usman ai ka fi ™aunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.





=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*006*

"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi ha™uri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani Auntyna ta faWa miki magana ne saboda irin ™aunar da take mini amma ni na san gaskiya kika faWa, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba da jira har lokacin da ya kamata a ce na Wauke su Win"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da hawaye ba. Uncle Win tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taSe baki ta ce

"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare Waya a yi abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sau™e ki a babur na"
Mi™ewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haWa su ba ta sau™a ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin.

Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta Wora girki marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta Wan kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai

Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haWa su ba don ta matu™ar jin zafin abin da ta yiwa Afeefar.

Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran
"Afeefah! Afeefah!!"
Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta, Auntyn ta Wago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya
"Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?"
"A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaWi, da missing Win mu da zai yi sai yayi mishi yawa"
Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma ma™ota da abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma Winkewa da jama'a nan Afeefah ta shiga jeka ka dawo.

Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko satan kallon yaran ta yi sai ta yaSa mata ba™ar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin son su tamkar jini da tsokarta ta sha Suya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu duk Aunty bata sani ba.

Auntyn Ta yi matu™ar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka ta

Please Login or Register in order to submit comment