Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta san ta isa gabanshi tare da ri™e hannunshi

"Mammi...! Mammi.."
"Me ya sameta?"
Ya faWa hankalinshi na tashi lokaci Waya, ganin duk ta ruWe yace
"Je ina zuwa"
Fita tayi da sauri shi kuwa ya Wauki boxers kawai ya saka da jallabiya tare da zaran keyn mota kafafunshi ma silifas ce ta wanka ya fice da hanzari, yanayin da ya sameta sai da ya ™ara Waga masa hankali haka ya Wauketa Afeefah na ta kuka suka nufi Asibiti duk ma'aikatan hankalinsu ya tashi da sauri aka karSeta sai oxygen aka sanya mata sun yi iya kokarinsu har numfashinta ya Wan daidaitu, Rayyan dai ya kasa aikata komai don ba karamin girgiza yayi ba duk tashin ciwonta bai taSa ganin kaman wannan ba, bai zaci za su iso asibitin da ranta ba jikinshi rawa kawai yake yana tsaye daga gefe yana kallonsu a sadda zuciyarshi ke cigaba da bugawa kaman zai fashe, idanunshi sun rine sai adu'a yake yana ro™on Allah akan ya bata sau™i a ranshi.

Ganin ta dawo daidai oxygen Win na tafiya a hankali ba kaman daga farko ba da in ta ja kaman ba zata sau™e ba ya isa gangarta ya ri™e hannunta kawai ya zauna, a jikin gadon ya Waura kanshi yana danne abinda yake ji na taso mishi, ina ma da zai iya kuka da yayi ko don samun sassaucin abinda yake ji a ranshi da ma kwakwalwanshi!

Ba zai ce ga adadin lokutan da ya Wauka zaune a wurin cikin wannan yanayi ba chan dai ya ji kaman ana shafa suman kanshi da Wan hanzari ya Wago sai suka haWa idanu tana ta kallonshi, gyara zama yayi yana kirkiro murmushi mai nauyi ya ce
"Mammi na! Kin farka? Ya jikin?"
Ta sake yin murmushi a hankali ta nuna mishi oxygen na hancinta sai ya cire yana jin yadda take sauke numfashi a kai akai
"Mammi ki yi saving energy Winki kar ki yi magana kin ji?"
Ta sake yin murmushi
"Ina so na ji abin da ke bakin ka! Ka ba ni labari...tun jiya na lura kana son min magana amma kana ri™e wa menene?"
Shiru ya Wan yi
"Speak up Saraki, yanzu ne kake da lokacin magana da ni anjima kaWan kila sai dai matarka ko 'yan uwanka"
Da sauri ya Wan kalleta tana ta murmushi, kanshi ya du™ar a hankali ya fara furta

"Mammi ki daina irin wannan maganan don Allah"
"Toh na daina Saraki!"
Ta faWa tana lumshe ido, hannunshi dake cikin nata ne ya ™ara yin sanyi she can feel the nervousness a cikin tafin hannunshi zata iya cewa yana cikin yanayi ne marar fasaltuwa sai dai da yake namiji ne kuma jarumi yana iya shanye damuwarshi kaman babu komai.

Idan Mammi ta tafi ba tare da ya sanar da ita menene a ™asan Ranshi ba tabbas zai yi nadama mai girma, tunaninsa ya dinga rarrabuwa har yana jin kaman zai zauce idan ya cigaba da zurfafa a cikin muguwar tafiyar rayuwarshi...iya tunanin kaWai kan karya duk wani guntun karsashinsa.

*****

A hankali yake buWe idanunshi har ya ware su akan Mommy da su Sadiqa dake zaune a Wakin jugum jugum.
"Saleem! Ka farka? Sannu ko mu je asibiti ne?"
Girgiza kai yayi yana Mi™ewa zaune jikin gadon ya kalli mommy da ita ma take kallonshi a hankali yace
"Mommy na tuba! Mommy ki yafe min wallahi...."
"Shhhh Saleem na sani, na san ba da saninka ka aikata hakan ba na san baka cikin hankalinka a lokacin da komai ke faruwa, laifina ne wlh laifina ne ka yafe min Saleem son zuciya Sacinta, hakika na yi amfani da son zuciyata wurin WaiWaita maka rayuwa don Allah ka gafarceni"
Ta roka yafiyarshi tana kuka su ma duk su sadika suka shiga bashi hakuri, anan ya zauna yana jin yadda komai ya kasance... Hakika mommy ta yi kuskure Afeefah ce ta faWo mishi a rai ko tana cikin wani hali yanzu? Ko ya rayuwa yayi da ita? Allah masani


******

"Mammi..!"
Ya sake ™ira a karo na biyu ba tare da ta buWe ido ba tace
"Uhmm"
"Zan faWa miki ne, zan faWa miki wanene ni..."
Da sauri ta buWe ido ta kalleshi cikin yanayin jin jiki ta zura mishi idanun a hankali ya cigaba da cewa
"Ban manta komai ba, na ™i faWa ne saboda wacce daraja da ™imarta suka zama ™ololuwa a gare ni ta yi fatali da hakan ta Wauke ni ta yasar tamkar tsumma a cikin al'ummar da ba ni da masaniyar yaya suke bare ya rayuwarsu take, ya al'adarsu take ko ya imaninsu yake, ba tare da ta damu da zan ci ko bazan ci ba, shin rayuwata za ta inganta ko za ta yi lalacewa marar iyaka? kafin na haWu da ke na zaci uwa masifa ce ga 'ya'yanta ta kan nesanta su da farin ciki ta saya musu wahala, ta kan zama tamkar ginin ™asa da muddin Wa ya jingina da ita sai ya faWi, a maimakon ta kasance garkuwata sai ta zama ita ce a farkon cutar da rayuwata, na kasance a koyaushe bana rufe idanu na buWe ba tare da na ga sadda take cire hannayenta daga cikin nawa ba tare da tura ni cikin dattin juji...ta tafi! Ta tafi da rayuwata da dukkan farin cikin da ya taSa wanzuwa cikinsa ta tafi da rai da ruhi na..."

Shiru yayi yana cije lip Win shi na ™asa da har su ma rawa suke yi.
"Ke ce kika ba ni hope na rayuwa, a kan ki na yarda uwayen ma suna suka tara Mammi kin zame min gata a sadda na kasance cikin wahala, kin ba ni duk wani kulawa da gata ba tare da tsammanin lada ba kin bani kaunar da bata taSa yankewa ba, kin zame min rayuwa, rahama da kyautatawa da bata da iyaka. Mammi Sunana Sameer..."
Lumshe ido tayi a hankali hawaye na sauka mata ya sa hannu ya share mata.

A hankali ya cigaba da bata labarin da kafin ya gama jijiyoyin kanshi sun yi raWa-raWa, idanunshi tamkar garwashi muryarshi har yankewa yake amma Dukda haka jarumtarshi ta ™i barin ruwan hawaye ko guda ya diga bisa fuskar shi ko zai samu salama cikin rai da ruhinshi, ba zata iya Mi™ewa ba da zata iya da ta rungumeshi ta rarrasheshi da ta nuna mishi komai na duniya mai wucewa ne, da ta tuna mishi da irin girma da darajar da Allah ya ba uwa don kalamanshi sun yi tsauri sossai a kanta, bata san dalilin ta na yin hakan ba amma ta san babu uwar da zata so tagayyarar Wan ta, Wan ma mai tarin gata, daraja da martaba irin Rayyan.

"Ka zama mai ha™uri da rayuwa! Ka zama mai afuwa Saraki ha™i™a an cuce ka an kuma Wauki alhakinka mai yawan gaske amma ina ro™on ka da ka bari komai ya wuce kaman ba'a yi ba, ka yi uzuri ga mahaifiyarka ka waiwayi gida..."
Shiru tayi sai ta Wan yunkura kaman zata tashi ta koma ta kwanta tana sha™uwa.
"Ka min al™awari Rayyan!"
Girgiza kai yayi yana Wago rinannun idanunshi gareta sai ya ji tana ambaton Allah da salati Wauke a Bakinta a kan idanunshi, hannunta na a cikin nashi Mammi ta ja numfashinta na ™arshe da ya tafi da duk wani ™warin gwiwanshi, ya tafi da duk wani haske da yake tunanin da shi yake amfani wurin haskaka tarin duhun dake mamaye da shi, gigice wa ya nemi yi sai ya manta da cewa shi Win ma likita ne, ya kasa yanke hukuncin cewa ta tafi ya kasa yardar wa kanshi cewa da gaske ta tafi ta bar shi...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Shine kalaman da ya fito da kyar ya ratsa harshenshi har ya fita sarari.

Ya fi mintuna ashirin a zaune a haka baya iya ko da kifta idanun kirki, kila mafarki yake, kila bacci tayi za ta buWe idanu kila zai iya ganin kirjinta ya motsa ya cigaba da bugawa kila za ta ja numfashi ta ce mishi wasa take... Shigowar wani likitan ne ya tabbatar mishi da cewa da gaske ya rasa Mammi rasawa ta har abada ha™i™a Waci da raWaWin mutuwa ba za su faWu ba ba kuma za su misaltu ba.

A chan reception kuwa Su jannah da Afeefah ne zaune cikin damuwa mai yawa don tunda suka shigo Afeefah bata daina zubar da kwallah ba, ta san mutuwa kuma ta ga mutuwa daban daban bata fata ya kasance a kan Mammi nan kusa Dukda ta san da cewa mutuwar dole ce ga dukkan mai rai, su uncle Musa da iyalan shi da Abeeha ta ™ira ta sanar musu jikin Mammi babu daaWi duk suna cikin asibitin a lokacin da wannan likita ya fito ya sanar musu da rasuwar gigice wa suka yi suka fice daga hayyacinsu, Jannah ce ta yanke jiki ta faWi sai jini ya fara fita mata Abeeha kam rasa ma ya zata yi tayi sai da uncle Sanusi ya ri™o ta yana ta maimaita salati ta kankanmeshi ta fara kuka mai tsuma zuciya shikenan sun zama marayu babu uwa babu uba, Mammi ta tafi lallai dukkan mai rai mamaci ne.

Afeefah kam ba zata ce ga yanayin da take ciki ba, Dukda ta kaWu iya kaWuwa sai dai ko motsi ta kasa yi daga inda take hawayen idanunta ma kafewa suka yi, wata cousin Win su Abeehar ce ta ri™e mata hannu sai ta firgita tana kallonta idanunta duk a waje...
"Wai cewa suke Mammi ta rasu? Ko kunnuwana ne basu ji da kyau ba?"
"Sai ha™uri Afeefah, sai ha™uri..."
Wasu irin hawaye ne suka shiga zubo mata masu zafi da raWaWi, da kyar take iya maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun....

A lokacin Rayyan ya fito hannunshi na tura gadon da mammin take kai a hankali yana tafiya ne ba tare da ya san inda yake jefa kafafunshi ba, Uncle Sanusi ne da matarshi suka taho da sauri suka saka mishi hannu don kaman zai kifa, idanunshi sun zama wani iri jikinshi na rawa zuciyarshi a bushe haka suka fice yana gaban motar da Mammi ke ciki wacce amblance ce aka dauko ta a baya har cikin gida, a Wakinta aka sanyata babu wani jinkiri Matar uncle Musa dattijuwar malama da taimakon wasu malamai mata aka yi mata wanka aka yi mata sutura, kan kace mene gidan ya dinke da mutane masu kuka na yi masu yabon kyaun halinta na yi, Jannah dai tana asibiti don Sari tayi ba tare da ta sani ba.

Abeeha da Afeefah banda kuka da du'a babu abinda suke yayinda Rayyan na a parlorn shi a zaune wane mutum-mutumi tasbihi yake yi amma ba zai iya cewa ga abin da yake cewa a ciki ba, Saleem ne ya shigo Dukda ba ™arfin jiki ya samu ba sai dai labarin mutuwar ya dugunzuma hankalinshi.
"Rayyan!"
Ya kira sunan.
Jajayen idanunshi ya buWe ya zura mishi ba tare da yayi magana ba
"Sannu! Allah ya gafartawa Mammi Allah ya haskaka makwancinta ya sadata da annabin rahama"
Da kyar ya iya furta
"Ameen"
Idanunshi na kan hawayen da Saleem Win ke yi ina ma zai iya? Ina ma ya san ta yadda zai nemo hawayen? Ina ma zai iya cire zuciyarshi ya yasar? Da yayi hakan ko zai huta raWaWin da ke gasata wane wuta.

"An gama shirya ta ayi alwala a fita gabatar da sallah don samu a kaita makwancinta!"
Wannan kalma ta Uncle Mansur ya zama kaman zuban wuta a jikinshi, shikenan fa yanzu ko? Shikenan zai rabu da Mammi rabuwa ta har abada? Saleem ne ya ja hannunshi har zuwa bayi yayi alwala suka fito a tare zuwa Wakin Mammi aka Wago makarar aka nufi fita da ita haraba inda kuka ke tashi, kowa idanunshi na kan Rayyan ne da yake ta focusing akan hanyar da yake takawa kar ya faWi ri™e da gawar Mammi da yayi mata sallama na ™arshe da qulhuwallahu ahad!

A tare da shi aka yi mata Sallah aka kaita makwancinta na gaskiya, shine ya ba da ghdumuwa wurin sakata a rami kuma shi ne ya fara zuba mata ™asa kan yayi baya baya zai faWi aka tare shi su Uncle Mansur ne da Saleem, Wagowa yayi yana kallonsu kila su basa jin abinda yake ji tunda gashi suna hawaye! Har aka gama binne Mammi aka kamo Rayyan zuwa mota baya gane fari ko ba™i don duk wanda zai ji mutuwar Mammi a bayan Rayyan ne.... Innalillahi wainna ilaihi rajiun =Ĝ-Ŝ
Allah ka sa mu yi kyakyawar karshe!






=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*38*

"Dakata!!"
Wata murya mai amo tayi maganan.
Chakk suka tsaya daga Wora wukan a ma™ogoron kawun.

"Mecece ala™arshi da ™ungiya?"
Yayi tambayar a kausashe.
"Babu mai girma shugaba"
"Ku kyaleshi jinin shi bai halalta mana ba"
Suman daaWi ne ya tafi da kawu Dukda azabar da yake ciki, dunkule shi suka yi suka tura cikin buhu aka saSe shi kaman kayan wanki aka fitar sai haushi suke ji bai musu amfani ba tsabar lalacewarshi, a booth na mota aka saka shi sai da suka yi tafiya mai uban nisa kan suka buWe booth Win suka cilla shi ™asa suka yi tafiyarsu.

Ya fi awa nawa yana mutsu-mutsu ga zafin rana Allah ya kawo wani mai ruwa ya taimake shi ya buWe buhun sai ya fara tari da mayar da numfashi sama sama, da kyar yake ambatar
"Ruwa! Ruwa!!"
Mai ruwan ya bashi ruwa a gora ya sha sossai yana sauke numfashi kan ya fara kalle kallen wurin da yake, wani kauye ne na daban
"Me ya saka ka cikin buhu bawan Allah?"

"Sace ni aka yi 'yan yankan kai ne suka sace ni Allah ya kubutar da ni"
Abin mamaki ya Wauke shi har gidan mai garin garin suna da karamci aka bashi wuri yayi wanka ya wanke najasar jikinshi ya rama sallaolin da suka hau kanshi, har abinci ya ci aka ba shi kuWin mota ya nufi Dutsen-wai cikin zuciyarshi sa™e-sa™e ne mai yawan gaske ga bakin cikin abin da su larai suka yi mishi ga yadda ya sha jinin jikinshi da abin da ya riska a kwanakin wanda har abada ba zai taSa mantawa ba, yana isa Dutsen-wai gidan mai gari ya nufa yana neman iso aka mishi iso ya ce

"Toh dama na zo ne in sanar kuma in nemi a gargaWi duk jama'ar garin nan cewa duk wanda ya sake cewa Šiyata Afeefah Mayya sai mun yi shari'a har kotun koli don Afeefah ba Mayya ba ce, ita kuma ba Annoba ba ce"
"Toh fa da kanka Malam Labaran? Kana lafiya kuwa?"

"Lafiyata ™alau kawai dai na san Afeefah ba Mayya ba ce kuma kar a sake ce mata haka don abin da Mayu suke yi ko a mafarki ba zata iya ba wannan abu ne da ya shallake dukkan tunanin mai tunani."
Ya ™arasa cikin tabbatarwa da jimami.
"Dama tun farko tsantsar jahilci da son zuciya ya sa kuka lakaba mata abinda ba shine ba, ashe kenan mutum ba zai taSa mutuwa haka siddan ba? Har fa tambari kuka buga na cewar tun tana ciki ta cinye Wan uwanka amma Alhamdulillah tunda ka gane gaskiya kuma kana shirin tsayawa a kanta sai ka yi wa kanka faWa ka nemi tsari da jahilci don wallahi mugun ciwo ne kuma shi ke Wawainiya da mafi yawanku cikin wannan ™auye".
Malam liman ne ya jero wannan jawabin, kawu ya gamsu har ya ji jikinshi na Wan sanyi barin ma da malam liman ya sake nusar dashi akan Allah shi ba ruwanshi, da ya turo mu duniya yayi mana umarnin mu nemi sani a kanshi kafin mu bauta mishi, ba ka da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin Ubangiji matukar baka tashi ka nema ba.

kan ya dawo gida labarin dawowarshi ya riske su bai damu da zancen mutane ba da wasu ke cewa kila ta cika shi da kuWi ne wasu na zaton ko don ta auri mai kuWi yanzu ai dole ya ja ta jiki. Shi kuwa hankalinshi ya fi tafiya ga jan hankalin da liman yayi mishi na neman ilimi Dukda a yanzu wani tataburzun ne gabanshi don saurin da yake zabgawa yana so ya tabbatar babu kowa ne a gidanshi kafin faWuwar rana.

Kaman daga sama suka ganshi ya faWo Asabe murfin tukunya ce a hannunta sai da ya subuce ya faWi ™asa ya tsaya kyamm yana kallonsu
"Toh ban mutu ba! Kuma dama an ce sai abu ya same ka kake sanin masu sonka ashe dukkanku ma™iyana ne na tara? Ashe za ku iya bari na in mutu? Toh an gama wallahi gwara in zauna ni kaWai na da in cigaba da zama da ku don haka kowaccenku ta tattara ya nata ya nata ta bar min gida na sake ku saki WaiWai..."

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Malam ka tsaya ka saura..."
Ya katse ta da masifa
"Babu abin da zan saurara Asabe! dole ku bar min gida a yau ba sai anjima ba kuma ku tattaro yaranku kaf ku fice min daga gida a tabbatar kuma an dawo min da kudade na mugayen banza mugayen wofi"
Sai masifa yake ko ya tsaya ya saurare su abin ya mishi zafi rigima fa sossai ya kachame don suma sun ce in zasu tafi ba zasu tafi da yara ba tunda ba da su suka zo a kullin gararsu ba ko hutawa bai yi ba aka sake komawa gaban manya ya rantse shi ya sake su su tafi kuma baya bukatar ko wani Wa don za su iya saka wuyanshi gabas su yanka tunda suka iya watsar da rayuwarshi alhali yana chan cikin tsaka mai wuya.

"Labaran!"
Malam liman ya kira shi ya amsa
"ka san ko ma menene suka yi laifinka ne?"
"Ta yaya? Ina fa chan gaban azzalumai mutanen nan don basu da imani suka ™i daukar waya alhali ga abin da nace su yi da kuWina ba nasu ba su kubutar da ni, ba don Allah na so na da sauran numfashi ba da na jima da mutuwa yanzu zaman makoki ake"

"Labaran ka yarda kaso mai girma na abin da ya faru laifinka ne"
"shiyasa na ce ina so in ji ta yaya?"

*****

A Sangaren Rayyan ba zai ce ga yadda yinin ya kasance mishi ba don baya gane komai, kawai yana so ya ji an daina ko magana a gangarshi ya ji shiru na ratsawa don ya samu damar gamsar da kanshi cewa da gaske ya rasa mace Waya jal mafi muhimmanci a rayuwarshi, wacce ta cire shi daga wahala ta bashi so da kauna ta raine shi fiye da yadda ta raini 'ya'yan da ta haifa da cikinta, ko gaisuwa aka mishi sai dai ya gyaWa kai don baya magana, idanunshi har tsoro yake ba wa wasu idan ya buWe, An yi an yi ya ci wani abu tun safen har dare ko ruwa bai yarda ya sha ba don raWaWin da yake ji daga zuciyarshi har akan harshen shi baya tunanin zai iya cin wani abin don cikin nashi ma jinshi yake a cushe, ganin yana shirin yi wa kanshi illa ya sa Sulaiman yi mishi allurar bacci don daga ™arshe numfashi wahalar fita ya fara mishi.

Su basa yarda da wani zaman makoki daga yinin da aka binnetan duk na waje suka watse, Afeefah tsabar yadda ta kasa yarda cewa Mammi ta tafi a Waki ta cigaba da zama hakan ya mata hijabi da haduwa da mutane dayawa ciki har da su mommy da Saleem, don Saleem yayi niyyan kwana a tare da Rayyan mommy ta sanar dashi yayi aure ai, ya shiga tsantsar mamaki ya kuma ji babu daaWi a lokaci guda, yana mamakin yadda Rayyan yayi aure cikin kankanin lokaci alhali shi bai taSa ji Rayyan ya furta sunan wata macen a matsayin buduruwa ba, ya kuma ji ba daaWi yadda bai kasance tare dashi a bikin ba amma ya mishi Fatan alkhairi ya Wauki su mommy suka koma gida don har yanzu a tsohon gidansu suke har shi, ya ce ba zasu koma chan inda ya zauna da Sabrina ba wani zai saya musu don bai san me suka binne ciki ba.

sai dare ta fito ta nufi Wakin Abeeha dake kwance rib da zazzabi, a gangarta ta zauna tare da rike hannunta
"Afeefah da gaske Mammi ta tafi ko? Idan na je Wakinta ba zan ganta ba ko? Yanzu shikenan ba mu da uwa ba mu da uba?"

Ta danne hawayen da ke shirin ziraro mata tace
"Haka Allah yake lamarinshi Adda Abeeha, dukkan mu da muke rayuwa a yanzu kwananmu ne bai kare ba idan ya ™are dole za mu tafi"

"ba za ki gane raWadin da nake ji ba Afeefah"
Ta girgiza kai
"Duk wanda za ki ji Adda Abeeha na ji shi, kar ki manta ko da aka haifeni ba ni da uba, ban kuma buWi ido na tarar da mahaifiyata ba sai a hoto kin ga ko zafi da raWaWin maraici na fara dandana, shi ne tun a cikin cikin mahaifiyata har zuwa zanin goyona. Adda Abeeha ku gode Allah kun rayu da iyayenku har girman ku..."
Kuka ne ke shirin kwace mata amma ta dake ta danne.

"Don Allah ki daure ki daina yi wa Mammi kuka haka! Mu bita da Adu'a shi ta fi bu™ata a halin yanzu"
Matar uncle Sanusi dake Wakin tace
"maganar Afeefah gaskiya ce Mahaifiyarku Adu'a take bu™ata Abeeha ba kuka ba ita ai tata ta yi kyau! Allah ya sa jinyar da ta sha ya zama kankarar zunubanta ne"
Suka amsa da Ameen.

"Mommy ya Adda Jannah?"
Afeefah tayi tambayar a sanyaye.
Matar uncle sanusi tace
"Ta farka amma tana under kulawar likitoci don Sarin ya zo ne bagatatan ga cikin ya fara girma, ta dai ji jiki kam sai dai Allah ya kawo na moro suna chan tare da su mamanku"
Ta fahimci da su matar uncle Mansur take nufi don haka Adu'a suka mata na samun ingantacciyar lafiya.

Abeeha ta dubi Afeefah
"Yaya fa?"
Shiru Afeefah tayi don bata san me zata ce ba, a lokacin mommyn ta fita daga Wakin
"Yana Wakinshi Adda Abeeha"
Mi™ewa zaune Abeeha tayi ta ri™o hannunta.
"Afeefah na san zaman ku da yaya babu daaWi, na kuma san kina tsoron shi da kuma tsoron kasancewa inuwa Waya da shi amma wallahi a yanzu babu wanda Yaya zai fi bu™ata kaman ke! Mammi za ta yi farin ciki idan kika kular mata da shi at his worst moment irin wannan..."

"Ta yaya Adda Abeeha? Mutumin da bai taSa min kallon matsayin abu mai muhimmanci ba, wanda bai taSa Waukata da kima ko daraja ta mace ba macen ma matarshi?"
Tayi maganan cikin sanyi, tun Wazu ya™i take da zuciyarta akan Rayyan, tana so ta je inda yake amma tana tsoro ta san yana bu™atar wani amma bata san ta yadda za ta rarrashi mutum irin shi mai dakakkiyar zuciyar da baya bayyana rauninshi a fili ba.

"Trust me Afeefah za ki iya, na san kema kin san me ya fi bu™ata a yanzu tunda duk waennan abu kin yi going through a rayuwarki... A lokacin da muka rasa Abbu akwai Mammi Dukda bata da lafiya ta tsaya mana dukkanmu har saida muka zama daidai muka amshi ™addararmu amma a yanzu bata nan ita da ta fi kowa sanin Ya Rayyan a duniya, na sani a kwanakin nan bacci sai dai idan da allura ko magani hakanan zai yi ta ciwo amma ba zai nuna ba, ba zai yi magana ba ba zai ci abinci ba don Allah ki taimakemu ki kula dashi matsayin ki na matarshi"

Kai Afeefah ta gyaWa ganin Abeehar ta fara hawaye, tun dazu take so taje gareshi har cikin zuciyarta amma bata san me zata yi ba in taje Win, Mi™ewa tayi tana kallon Abeeha
"Ki yi bacci zan kula da komai in shaa Allah"
Godiya Abeeha zata yi mata amma tayi saurin ficewa Abeeha ta mayar da idanun ta rufe hawayenta na gangara.

Afeefah na barin sashen tayi Wakin ta wanka tayi saboda yanayin zafi da ake dan yi tayi Sallar isha ta jima tana yiwa Mammi Adu'a tana hawaye kan ta yi shafa'i da wutiri ta nemi riga da wando na bacci jajaye ta saka ta Wora hijab har ™asa a kai sai ta fito ta nufi Wakinshi, sai da tayi knocking ta buWe ta shiga hasken a kunne don haka ta hange shi kwance kan gadon Wakin idanunshi a rufe ya Wan dukunkune kaman mai jin sanyi amma kuma bai rufa ba, kamshin shi da ya kama Wakin na

Please Login or Register in order to submit comment