Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin na nuna mishi yaron

"Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?"
"Hajiya yadda kika ganshin nan haka mu ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin wando idan ya bushe zai saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai taSa barin wurin ba sai wanka ko wanki da ya kan zo nan"

Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin na koma wurin mota na tafi na je na sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai bu™ata na dawo na bashi ya ™i karSa a ™arshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya samu gurbi a zuciyata, a ranar takalmina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin zafin ranar minti minti sai ya Wan waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba, har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da Sangaren mata abin da ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa wurinshi a na huWu ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya kalleni kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa

"Me ya same ki?"
Numfashi mai nauyi na sau™e ashe ba kurma bane
"Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana"
Ga mamakina sai ya mi™e ya kama hannuna muka koma inuwa duk muka zauna bayan nan duk yadda zan yi yayi magana ya ™i na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya kalleni ya ce

"Me kike so?"
Ina mamakin yadda yake magana wane babba
"Kai nake so in taimaka kai nake so in Wauke daga wannan jujin in kaika gidan mu kayi rayuwa mai kyau, za ka bi ni?"
Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya Waya ba zan so rayuwar shi ya ™are a kan titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.
Kai ya gyaWa min na yi farin ciki kwarai na kira babıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿana ina mishi albishir don ya san labarin yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a lokacin na je Makka so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.

Ban barshi cikin ma'aikata ba na kaishi Waki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min
"Na gode"
Murmushi nayi a raina ina raya wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za'a yi ba don bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.
"Ya sunanka?"
"Ban sani ba"
Abin da yace kenan na yi mamaki ™warai kuma kaman akwai abinda ya Soye min amma ban bincika ba nace
"Zan saka maka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni kaWai ce sai babana a gidan nan ka Waukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan cika maka shi ka ji?"
Ya kalleni nayi murmushi
"ban kai in haifeka bane? Shekarunka nawa?"
Ya Waga min yatsu shida nace
"To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba'a kai hakan"
Ya Wan yi murmushi daga nan na fahimci shi mai Wabi'ar miskilanci ne tsantsa babana na samu da shawara shi ya ba da sunan Rayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki bana tunanin ya kai shi sarauta..

A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da zan kaishi makaranta tare muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga tashin hankalin da Saraki ne kawai ke iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai taSa kirana ba ko zai yi magana sai dai kawai yayi na ce ko Aunty ya ce min ya ™i, Rayyan bashi da lafiya don yadda yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye yana haWa gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ™arami muka fara ganin likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.

Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban sake yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina da Ciwon ™oda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ™odar shi yayi offering mini Mahaifinsu Jannah ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba'a dace ba, a lokacin da nake jinyar Baban su Jannah ma ya rasu ga rashin lafiya ga rashin miji na yi ciwo sossai duk Rayyan ne yake tsaye tsayin daka a kaina ga ™annenshi Jannah da Abeeha bai bari na tagayyara ba, yana mini son da iyakaci kenan ko da ni ce na haife shi.

Saraki ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana ma bata dame shi ba don ko abokai bashi da su, sannan yaro ne da idan yana abu dole ka kalleshi yana da jin ™ai ko magana yake dole ka kalleshi, dalili na ya tafi short service a harkar lafiya don dama science ya karanta a secondary school, ba'a fi shekara biyu ba na matsa mishi da zancen aure ya nuna akwai wacce yake gani zai iya aure, magana ta fara nisa ranar ya je wurinta babanta ya zo ya same shi ya ce mishi

"Ina so in ka koma ka tambayi asalinka sai a fara batun neman aure amma ba zan ba da auren Wiyata wa marar cikakken asali ba"

Wannan magana ya dake shi sossai, wanda ni na Wan lallaSa shi na tura uncle Musa sai ce mishi suka yi ba za su bada auren ba basu sani ba ko ba Wan sunna bane ko an same shi ta gurbattacciyar hanya, magana ce mai girma a gareshi wanda ya tado ciwon baya da kyar muka samu ya dawo daidai bayan tsawon wata shidda baya bacci kuma ya ki faWa mini wani irin mafarki yake ko wa Dr Winshi, gashi Rayyan baya taSa zubar da hawaye, tunda ya girma rabon da in ga hawayenshi kila da wani abu zai ragu a zuciyarshi, daga nan yayi alkawarin ba zai sake neman aure ba don duk wanda ya sake kallonshi ya mishi gorin asali sai ya kashe mutum har lahira.

Afeefah kin ji waye Rayyan, kin ji cewa bashi da cikakkiyar asali sai dai yana da tarin nagarta, ilimi, natsuwa da sanin ya kamata ga ibada tsantsa, yana da ni matsayin uwa da na bashi duk tarbiyar da uwa za ta iya ba yaro daga yarantarshi har girmanshi, ya samu gatan iyaye both uwa da uba don baban su Jannah har ya rasu bai taSa nuna ko da da second daya cewa ba shine Uban Rayyan ba, kin ji cewa bashi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ba na hauka ba sai na tsantsar damuwa akan abinda ya shafi rayuwarshi da ciwo a zuciyarshi wanda ya mayar dashi mai irin zafi da faWan nan, tun yana yaro ba za ki taSa ganin dariyar shi ba sai murmushi shima sai ya kama, shin za ki iya auren Rayyan a haka? Afeefah za ki iya yi min wannan alfarmar??





=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*30*

**Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sau™i ga bawa a duk sadda ™addara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?"**
Da wani irin amo sautin muryarshi ke dawo mata a sadda yake faWa farkawarta daga shan piya-piya, ashe da biyu yake yi mata irin wannan faWan? Ashe shima duniyar ba daaWi tayi mishi ba?

Wasu irin ruwan hawaye ne ke bin fuskarta babu kakkautawa, sai taji har gwara ita ma da shi kaman ™addarar ta ya fi nashi sau™i tunda tana kwanciya tayi bacci lafiya ™alau, kuka kawai take yi duk yadda mammi ta so tayi shiru ta ™i, sai da tayi ma'ishi Mammi ta bata ruwa ta sha kan ta Wago ta kalli Mammi bata ce komai ba.

"Za ki iya cewa Meyasa ban bashi Abeeha ko Jannah ba ko? Har raina na Wauki Saraki Wan da na tsuguna na haifa ne shiyasa har abada na haramta mishi auren 'ya'yana, uba yake a gare su a yanzu da basu da wani uba shi ya raine su bayan yana jinya na, shi ya basu tarbiya cikakkiya da har in sun fita ana sha'awar su. Wannan dalili ya sa ko da wasa wannan tunani bai taSa darsar min ba don har in mutu bana fata ko sau Waya Saraki yayi tunanin don ba ni na haife shi ba zan iya Sata mishi..."

A hankali Afeefah da idanunta suka sauya ainun ta ri™e hannun Mammi
"Ke mutumiyar kirki ce Mammi, kina daga cikin sahun 'yan aljanna in shaa Allah... Hakika kina da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona"
Murmushi kaWan kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa

"Mammi ki bar ro™o na kin yarda da ni ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so"
Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.

****

Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Saleem gida bayan yayi ta mishi tuni akan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu'a yana kuma da yakinin duk abinda yayi farko yana da ™arshe musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.

Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta buWe sai ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya shiga ya samu wuri ya zauna, cikin mintuna kaWan ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna

"Barka da juma'a Yaya"
"Barka dai ya gidan?"
Ta amsa da farin ciki
"Lafiya ™alau ya su Mammi?"
"Alhamdulillah"
Ya faWa yana shan zobo don yana matu™ar kaunar zobo bayan ya sau™e cup Win ya kalleta

"ba ki da wani damuwa ko?"
Kai ta gyaWa
"Babu komai Yaya"
Ya ce
"Masha Allah"
Mi™ewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota ya tafi ta dawo tana murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.

Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la'asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya fita yayi sallah sai ya dawo ya huta gabaWaya, ko da ya shiga yanayin wurin ya Wan zubawa ido Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya Wan ji wani yanayi da har bai Suya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya Wauke kai sai ta mi™e ta zo zata fita muryarta na cracking tace
"Sannu da dawowa"
Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi kaWai tausayi yake bata.

Šan shiru yayi kan ya taSe baki yana Waga Kafada ya isa wurin Mammi
"Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?"
"Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?"
Bai ja zaren zancen ba yace
"Eh, hope baki ji yunwa ba?"

"No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin you should rest"
Kai ya gyaWa ya Wan jingina da kujera yana lumshe ido
"Ni ko ina son yin wata magana da kai"
BuWe idanun yayi yana kallonta
"Saraki ka tuna kai ka ce in zaSa maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na zaSa?"
Šan shiru yayi kan chan dai ya gyaWa kai.

"Toh mun samu Mata Saraki"
Bai wani nuna ya ji daaWi ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya Wan buWe.

"Baka tambayi wace ba kuma a ina?"
"Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda ya dace kawai"
"haka za ka aureta baku fahimci juna ba? Ai ba'a haka dole za ka nuna mata itama macece kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga tsakanin saurayi da budurwa"

Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin zai iya yin ko abu guda cikin wanda ta lissafo.

"Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba"
"Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan zaSa maka wacce na san bata dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ™arbar ta yadda take ko?"
Ya Wan matsa kaWan ya ri™e hannunta
"Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda na Wauki girman alkawari wallahi zan amince, wacece?"
Yadda take ta zagayen ne yasa ma yaji yana son sanin wacece haka.

"Afeefah ce!"
Šan shiru yayi yana tunani don sai ya ji kaman ma bai san sunan ba, amma duk inda ya zagaya a kwakwalwarshi mace Waya tak ya sani da wannan suna, mace Waya da ya sani kuma buduruwar abokinshi ce salim.

Da sauri ya kalli Mammin yana girgiza kai
"A'a Mammi ki samo wata ba wannan ba"

Da zuciya Waya yayi maganan kuma kai tsaye.

"Ban gane in samo wata ba, Meyasa?"

"Mammi ni wannan ta yi min yarinya wlh ba na son hauka da raini, sannan Mammi buduruwar saleem ce fa! Ta ya zan fara zaman aure da ita?"
Murmushi Mammi tayi a maganan nashi na farko

"Ina saleem Win? Ina yana chan yayi aure yana zaune da matar shi? Ko ma bai yi aure ba ba zan amincewa Afeefah ta auri saleem ba ba kuma don shi a karan kanshi ba sai don mahaifiyarshi ba zan so ta koma inda zata sha wahala ba shiyasa na zaSa mata kai ina da yakinin za ka kula da ita har karshen numfashi"
Tayi maganan cikin tabbatarwa, duk ya Wan ruWe mata kaman zai yi kuka ya fara magiyar ta chanza wata shi dai wannan yarinya bata mishi ba.

"Ba fa zan fasa ba Saraki sai ka bani kwakwarar hujjar da zan gamsu ban da buduruwar saleem, ban da kuma baka sonta itama bata son ka dukkanku za ku koyi son juna idan zama ya haWa ku, banda kuma tayi yarinya don kaima ka san ba yarinyar bace"

Hangota kawai yake a idanunshi yana son tuna menene kuma aibunta wannan idanu farare manya da take zarowa duk sadda yayi magana yake hangowa kawai, da Wan sauri yace

"Mammi ba™a ce!"


Dariya Mammi ta fara tana girgiza kai ya kwaSe fuska shi da gaske yake
"Yaushe kuma ka fara zaSar kala? Kenan ni da babanku bai aureni ba kenan ko kuma da Su Jannah ba za su auru ba"

"To ai ku daban ne ita daban Mammi"

"Ka san Allah idan ba legit hujja zaka kawo ba, maganan nan babu fashi ka fara shiri... Saboda yanayin jiki na ba za mu Wauko wani hidima ba Waura aure kawai za'a yi ayi walima kowa ya shaida ta tare"

Duk yadda ya so ya zamewa Mammi ya kasa, don komai ya ce tana da amsa har aka kira la'asar ya tashi ya tafi, ta bishi da kallo tana murmushi idan ta ga yana hira da ita haka hakan na yi mata matukar daaWi a rai, ta kan rasa Meyasa baya son Magana alhali ya iya ba bai iya ba, kawai dai ya zauna shiru ya fi mishi ko mahaifin su Jannah da yana raye sai dai ya ji dariyar ta ba zai ji maganan Sarakin nata ba yayi ta tsokanarsu kenan tana shigarwa Sarakin don shi bayan ita wasa da sakin fuskanshi babu mai gani gwara ma saleem da suka shaku sossai shima don salim Win ya karanci halayenshi ne tsaff kuma ya iya zama dashi.

Tana fata ko ba yanzu ba ya so Afeefah ya sake mata fiye da yadda ita take ganin wannan side Win nashi, hannu ta Waga tana ro™on Allah ya nuna mata wannan rana da zata mi™a shi Wakin matarshi.

Daga nan ta mi™e ta shige don alwalar la'asar, bata yi ™asa a gwiwa ba da daren ta sa driver ya kaita gidan ™anin mahaifinta Uncle Musa dattijo ne sossai shima kuma natsatse mai tarin ilimin boko da arabi yana da zuri'a kuma duk zaman lafiya suke da su Mammi, sossai ta mishi bayanin Afeefah ta kuma ro™i da su je su nema mata aure a wurin dangin mahaifinta don a fita hakkin su, bata so su bada komai amma tana son A karSi auren Afeefah daga shakikanta. Ya gamsu shima kuma yayi na'am da hakan sun yi hira sossai don tana kwana biyu bata je ba sbd jikinta shi ne ma ya kan zo har gida ya duba ta haka yaranshi da wasu jikokinshi, bata bar gidan ba sai da suka tsayar zai yi tattaki da kanshi da babban danshi su tafi Dutsen-wai su nemi a basu ranar auren daga nan sai a fara shiri.

****

Mommy ce kwance a kan gado tsabar damuwa da tunani da ta sakawa kanta ne ya sa jininta hawa sossai, su Samha ke zagaye da ita a yanzu Win ma hawaye take zubarwa na tausayin Saleem da damuwar halin da yake ciki wanda ta yarda laifin ta ne amma me yasa su Yaya za su rama alkhairinta da mugunta? Me ta musu da zafi haka?

Bata gama tunanin ba Sabrina ta shigo Wakin ta samu wuri ta zauna
"Sannu Hajiya mommy ashe kuma jiki ya ™i?"
Mommy ta danne tace
"Eh amma Alhamdulillah"
"Toh Allah ya kara sau™i dama Saleem ne ya aiko ni"
Yadda ta kira sunan sai da suka daga kai duk suka kalleta.
"Wai cewa yayi ku koma wanchan tsohon gidan na gado ya riga ya tashi 'yan hayan yana son yayi renovating nan, kin ga yanzu mun yi yawa ga iyali zai fara tarawa ga su Gaje gininsun ya tsofe cikin ko wani minti zai iya rufta musu suma dai duk nan za su dawo"

Galala suke kallonta da kyar mommy ta iya cewa
"Saleem Win ne yace haka?"
"Ai kin san ban san yan hayan ba bare in tashe su, shine yayi komai kuma ya tabbatar min kar ku wuce yau don gobe masu aikin za su fara zuwa"

Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sulmiyo wa mommy da su Samha, Sameera ce ta iya daurewa ta mi™e tsaye ta fara hada kayan mommyn don ba zasu zauna ba, gwara su tafi Win babban matsalar dukkansu babu mai aiki cikinsu karatu suke yi, mommyn sai kallonta take tana jin tururin zafi a zuciyarta tuni Sabrina ta fice, mommy tashi tayi ta fito kai tsaye ta haura saman su ta buga, su Samha duk suka bi bayanta jikinsu a matu™ar sanyaye sai da tayi mintuna biyu kan aka bude saleem ta ™ura wa ido sama da seconds goma kan tace

"kai ka ba matarka sa™o ta ba mu?"
Kai ya gyaWa
"Duk abinda tace haka ne!"
Jiri ne ya kwashe ta ya yunkura zai tare ta ta ture hannunshi ta juya da sauri ta sau™a su Samha ta cewa su hada kayansu duk suka hada suka fito a motar sadiqa suka zuba duk abubuwan bu™atar su ta ja suka fice daga gidan dukkansu suna kuka, basu sake jin tashin hankali ba sai da suka iso gidan duk 'yan haya sun lalata shi komai dai sai a hankali kuma dakuna biyu ne da parlor sai kitchen duk jiki a sanyaye suka zauna a parlorn mommy na dafe da kanta har lokacin kuka take yi.

"Mommy..!"
Sameera ta kira sunanta.
Sai ta Wago ta kalleta
"Kina jin zafi a ranki ko? Kina jin ciwo da raWaWi ko? Kina jin ba™in ciki da tsantsar damuwa da tashin hankali ko?"
Mommy tace
"Ba sai na faWa ba Sameera abin da nake ji ba zai misaltu ba ni saleem ya Waga daga gidan shi zai dawo da surukanshi? Ni fah? Ko a mafarki ban taSa zato ko tsammanin saleem zai iya juya min baya a kan mace ba"
"Mommy in faWa miki gaskiya? Laifin ki ne, dukkanmu muna da laifi a abin da ya faru... Mommy kin yi tunanin inda Afeefah ta nufa da muka kore ta? Gwara mu muna da nan kuma ko ba komai muna da junanmu amma ita kaWai ta fita bata da kowa bata da inda zata je, kin tuna irin wulakancin da muka mata? Ashe alhakin da muka raina zai iya bibiyarmu, kin tsane ta ne saboda saleem yana son ta kina ganin son nan da yake mata zai sa ya bijire miki kika zaSa mishi wacce kike ganin ke ce da riba sai kuma akasin hakan ya faru. har yanzu kina ganin laifin Yaya da kika mishi dolen karbar wacce bai taba so ba? Kina ganin laifin Yaya da ™arfi da yaji yana kuka yana komai kika raba shi da Masoyiyar shi? Mommy ina jin zafi ina jin ciwo ina ji a zuciyata cewa duk wannan abinda ya farun alhakin yarinyar nan ne, Allah ya jarabceni da azabar so na ji yadda itama ta ji a sadda muka raba ta da nata savior Win, na ji kwatar abinda yaya ya ji a kanta amma muka hadu muka nufeta da sharri har da ™agen lalata da samari wlh idan ba mu neme ta mun nemi yafiyarta ba to kadan kenan muka fara gani"

Dukkansu maganganun sameeran sun shige su barin ma mommy da Samha dake ta kuka, gaskiya Sameera ta faWa bata kyauta ba kuma duk laifin ta ne da tun farko ta kwaSe su ba zasu yi ba amma bakin al™alami ya riga ya bushe sai dai su tari gaba, tana tuna irin abubuwan da suka mata tana tuna irin yadda taje ta haWa ta da maza don tayi rayuwa saboda kawai an ce ne ita Mayya ce sai ka ce jahilai waenda basu yi karatun islama ba sun ci zarafinta baiwar Allah, sai gashi Allah ya nuna musu Wan Adam ko ya yake mai daraja ne a gareshi, ya nuna musu ikon shi a kan bayinsa.

"A ina za mu sameta mu nemi yafiyarta a ina zan ganta Sameera?"
"Wannan sai Allah mommy, yanzu ina so ki daina yiwa yaya kuka mu dukufa Adu'a da sadaka Allah ya karkato da hankalinshi mommy adu'ar ki karSaSSiya ce a gareshi ke kika Sata ke ya kamata ki dukufa ki gyara"
Ta gamsu sossai kuma ta fahimci karatun duniyar, ta fahimci ayar da Allah ya nuna a kanta don haka gwagwalanta ta cire ta ba sadiqa akan su je su sayar su musu sayayyan

Please Login or Register in order to submit comment