Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an nemo na ™asan akwati don ma™on shi ma bai barshi yayi sabon Winki cikin dubu hamsin din chan ba bai tashi jin kunya ba sai da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na ma™ale saman katangu ana kallon ikon Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo...

Fara haramar Waurin aure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman
"Nawa ake bayarwa?"
Sulaiman ya Wan juya hannu alamar mene kenan?
"Sadakin?"

"Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ™arancin sadaki yana dubu Wari da tamanin da uku ne"
A lokacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir Win dubu-dubu guda biyar ya mi™awa Uncle Sanusi aka mi™awa liman an Waura auren Afeefah Kamal da Rayyan Moh'd Khamis akan sadaki naira Dubu Wari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin yanayi ne yake ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da dabino da sweets.

Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin da yake ji baya misaltuwa mishi, kawu sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a fina-finan ma wannan ko ya aka yi kuWinshi daban ne, limami ne yake rike da kuWin sadakin kawu yaje ya fara kokarin karSa sai uncle Musa yayi interrupting Winsu

"Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?"
Limamin ya gyaWa kai
"Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata"
Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya karSi kudin gabaWaya wani irin kullutun bakin ciki ne ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception 'yan kauyen sun ga abinci da kaji iya gani, yana ta mamakin ya aka yi Mammi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk kauyen babu gidan da ba'a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi.

Karfe goma sha Waya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo shi
"Malam Labaran na ga kana kokarin shiga mota?"

"Eh wai dama in je ne in kalli inda 'yar tawa za ta zauna"
"Ah ai ba'a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin salama"
Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun haWa ta da ™addarar ta rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma sun shaida a yanzu ta shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da hantar kura.
Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi za™in baki har motocin suka watse illa Sulaiman da Rayyan wanda yake jingine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha'awar kallon kawun baya yi don ko da kawun ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya haWe fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin kwarjini dole kawun ya kyale shi.

Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka Waura mata aure kwatankwacin na Afeefah, sadakinta kaWai yayi sadakin mata ashirin a kauyen kaf... Inna Larai na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan kawun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja baja.

Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi.

Ko da suka iso Kaduna shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye karamin parlorn Mammi ya le™a sai ya ga wata cousin Winta tace mishi
"Tana sashen ka Rayyan"
Bai amsa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi sara mishi yake.

A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka cikin leshi blue doguwar riga ta Wora gyalen da ya shiga da leshin a kanta da aka yi wa dauri mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye suka shiga zubo mata

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da Wana a rana mafi muhimmanci cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiya Allah ka sanya musu tausayi, jin kai, bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sau™e duk wani hakki nashi na aure... Rayyan..."
Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu'o'in nata har a cikin zuciyarshi ya sa hannu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta kira Abeeha

"Ku zo da ita"

Daga haka ta kashe.

A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai suke yin kyau don shine yake ba ta kulawa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana Waukar su, suka kalli cameran suka murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin murmushin Mammi yayi yawa ya sa ya kai idanunshi inda take kallo.

Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ™aya, tayi masifar kyau cikin wani exlusive luxery lace da aka yi wa Winki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da fuskarta makeup da aka mata ya matu™ar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah.

Mammi ta mi™e ta tarbota
"Masha Allah, Tabarakallah Wiyata you made a beautiful bride"
Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idanun har suka zo suka zauna Mammi tana tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya Wan tsayar akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun shi ta kamo na Afeefah ta haWe a tare suka Wago sai zuruf idanunsu suka faWa cikin na juna, idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta du™ar da kanta daidai Mammi ta Wora nata hannun a kan nasu camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga Waukar hotuna.

Ko da za'a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta mi™e ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma Win amma har lokacin da space tsakanin shi da Afeefah mai hoton ya kalleta yace
"Amarya ki Wan matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi"
Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana so ya tashi don ya gaji hakan ya sa ya Wan matsa kaWan Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta haWe sai suka kalli juna don duk sadda jikinsu ya haWu su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani ma'ana na daban nan aka shiga daukar hotuna. Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi.

Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na taSa bayan nata babu zato ta ji hannunayenshi duk biyu ya zagaye cikinta, a Wan razane ta Wora nata biyu a kan nashi
"Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??"
Da Wan faWa yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin su ma suka fice.

An yi yini an ci an sha an yi hidima har la'asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi kaWai ya bayyana tsadar shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima aka ci aka sha kan mutane suka fara watsewa don bayan isha aunties Win su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai taSa tafiya ya kyaleta a gidan ba, kuma parts dake gidan kenan don a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi part Win da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi.

Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah tayi sallah aka shirya ta again cikin atampha aka Wora mata lafaya aka mi™a ta wurin Mammi, sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, ta rungumeta ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya Waya jal da Wan ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee na nan ta ga wai Afeefah ce a Wakin miji? A haka aka kaita Wakinta da Adu'a a Bakinta.

Mammi waya ta Waga ta kira shi, ba'a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi yawa ya saukar mishi da ciwon kai sossai.

"RAYYAN...."





=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*33*

"Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ™annenka, na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba zaSi shi kuma ya zaSa maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwarka, idan har ka ci amanar ta ko ka ha'inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda Allah, idan ka so ta ka so ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar Wa kunya. Ka zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami"

A hankali ya Wan Wora kanshi a gefen kafaWarta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sau™a Mata, hannunta ya kama
"Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce"
Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai a yanzu haka wanda bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba.

"Ka tashi ka sha magani Saraki"
Ta faWa, da kyar ya buWe lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya mi™e zaune, karbar pills Win yayi ya sha wanda ta haWa da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin, Mi™ewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace
"Sai da safe"
"Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da Amin kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi ha™uri ta kara juriya kafin ta samu yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta Wan saki kan ta sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi ba™i kam duk babu kowa.

Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi Wauke da sallamar da iya shi kaWai ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana Wora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da zai iya da kuka zai yi da ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa yayi ™asa kan carpet ya Wora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan yanayi sai da ya Wan samu relief ya mi™e ya nufi Wakinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora uku kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci Waya yana dan buga glass Win wurin wankan da hannunshi.

Sai da yaji zai iya faWuwa idan bai bar wurin ba ya fito Waure da towel ya hau gadon ya kwanta ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo.

Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya tafi ta mi™e tana kallon Wakin har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so, a hankali take bin Wakin da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar ba ita dake fama da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da ubangijinta.

A haka ta shiga bayin shima ta ™are mishi kallo komai na 'yan gayu, bata yi wanka ba don sai da tayi wanka ta saka kaya aka kawo ta karamin akwatin da Abeeha tace mata kayan bacci ne ciki ta buWe ta duba silk riga da wando cream Color yana da adon Black lace daga kirji da kuma ™asan kafafun wandon ta saka, kamshinta da kamshin Wakin har ya so yayi mata yawa ga sanyin Acn dake busawa kashe wutan tayi ta hau gado ta kwanta tana sake jin salama a ranta sam bata wani sa damuwar rashin ganin Sarakin ba don ta riga ta sakawa kanta ha™uri da juriya har Allah ya kawo karshen komai Dukda bata san yaushe ba bata san ko karshen zai zo ba amma she have her trust in Allah zai mata komai ba sai ta damu kanta ba Adu'a ne babba kuma zata cigaba.

Washegari da safe bayan tayi sallah ta Wan koma bacci, ™arfe tara ta farka ta sau™a daga gadon da kaman kar ta tashi tsabar daadinshi da take ji ta wuce bayi ta yi wanka ta fito ta fara neman kaya cikin sababbin dinkunan da telan Jannah ya chanchada mata, wani atampha doguwar riga A shape ta fitar ta shirya ciki tayi kyau sossai ta feshe jikinta da turarukanta sababbin waenda kamshin suka yi mata ta kafa Wauri, bata sa kwalli ba sai ta saka lipstick kawai accesories da tayi anfani na silver sai suka ™ara haskata tayi kyau ainun gidan ba ba™onta bane amma sai ta fara tunanin ta saka gyale ne ko kar ta saka?

Tsoro take kar ta fita su haWu don yanzu ba kaman da bane da ba lallai ma su hadu ba in ba wurin Mammi ba, a hankali dai ta sa hannu ta buWe kofan Wakin ta sanyo kai cikin parlorn, ko taku biyu bata yi ba idanunta suka sau™a kanshi a farko ta tsorata sai kuma ta fahimci kaman bashi da lafiya ne don ga matar da take matsayin likitarshi zaune a kujeran dake fuskantar shi, yayi relaxing sanye da wasu blue pjamas riga da wando complete, kafafunshi babu takalmi suna lume cikin tattausan carpet Win dake shimfide parlorn, fuskarshi yayi ja sossai haka gashin kanshi a hautsine.

Wani iri taji a ranta sai taji tausayin shi na bin jikinta kaman ruwa, ta riga ta san dalilin da ka iya kawo mishi ciwon a hankali ta shigo cikin parlorn Likitar na kallonta ta saki murmushi itama ta mayar mata a hankali ta Wan du™a ta gaisheta ta amsa da kulawa tana tambayarta Ya Rayyan da jiki? Ita dai ta amsa da da sau™i amma bata ma san bashi da lafiyan ba sai yanzu.

A hankali ta kalleshi idanunshi na a lumshe har lokacin, matar ta mi™e
"Allah ya baka lafiya zan zo gobe da safe, please make sure ka ci abinci ka sha waennan pills Win"
Ta karashe tana ajiye mishi wasu pink pills a roba.
Sai a lokacin ya Wan buWe ido
"Thank you"
Tayi murmushi ta yiwa Afeefah sallama ta fice.

Sai aka bar su su biyu a parlorn, yatsina fuska yake don kamshinta har kanshi yake ji ba tun yanzu ya fara ji ba tun ranar da suka same shi a dining da Abeeha ya iya bambance nata kamshin da na Abeeha, yanzu ma gashi ta zo ta tsaya mishi sai hawa kanshi yake tsaki ya Wan ja ya buWe ido sai karap suka hada idanu don kallonshi dama take tana tunanin ta inda zata fara gaishe shi ganin ya kalleta sai tayi saurin cewa

"Ina..kwana!"

Ya yunkura ya mi™e zaune da kyau, bata yi zaton zai amsa ba sai jin deep and calm voice Win shi da bai yi matcing da situation da yake ciki ba ya ce
"Good Morning!"

Daga haka ya mi™e ya wuce ta ya shige Wakinshi, ta sauke numfashin tsoro tana nufan kofa saboda knocking da ake, masu aiki ne rike da baskets na abinci kai tsaye suka jere mata su a dining suna gaisawa don sun saba da juna dama, plates, cups da spoons taje ta Wauko ta zo ta ™arasa haWa dining Win amma bata sani ba ta kirashi ne ko ta kyale shi, ta san ba zai so shisshigi ba in ta dameshi ya iya karyata don ya sha ambata kalan ya zo ya faru ta shiga uku, abincinta ta zuba ta ci har ta gama karyawa bai fito ba don haka tayi sashen Mammi don ta duba ta.

A zaune ta sameta ta gama karyawa tana shan magani tana ganinta fuskarta ya washe da fara'a
"Šiyata ni da nace yau za ki huta sossai sai ga ki da sassafe? Sannu da zuwa"
Yadda take mata sai ya saka kunya kamata kaman wacce ta fito daga wani unguwar, a ™asa ta du™a ta gaisheta tana mata ya jiki.

"Alhamdulillah dawo nan gefena Afeefah, ina shi Sarakin?"
Wani kunyar ne ya sake lullubeta ta kasa magana Mammi tayi dariya kawai ta janyo wayanta ta kirashi
"Jiya ya tafi anan ban gamsu da yanayinshi ba, kun gaisa da safen nan?"
Kai ta gyaWa
"Eh na fito na same su da likitan shi suna magana"
"kin ga ko, sai in rasa Meyasa yake ajiye damuwar da baya bayyanawa yanzu baya so in sani ne ya ™i zuwa nan tun sassafe na kira ban same shi ba je ki ce ya zo"

Gabanta ne ya faWi rassss, ta ya zata fara kiranshi? A hankali ta mi™e ta fice zuciyarta na racing har ta shiga parlorn inda Allah ya taimaketa ma ta samu yana parlor a zaune kan dining yana karyawa wayanshi na a speaker alamu waya yake, a gefenshi ta ja ta tsaya sai ta ji Muryar dake tashi kaman ta san Muryar kuka me Muryar take har tana shidewa a hankali take cewa

"Ya Rayyan bakin cikin Ya Saleem zai kashe mana Mommy, duk abubuwan da ya dinga yi a baya mai sau™i ne yanzu ya kore mu ya saka surakanshi a gidan, bai damu da mun ci ko bamu ci ba, mun yi karatu ko ba mu yi ba muna lafiya ko babu tun muna zuba ido yanzu wata kenan da ko mun je gidan ba'a bari mu shiga, ga mommy kwance a asibiti saboda damuwa da hawan jini...!"
Dukda maganan da take yi Win ya shige shi sossai, damuwa ya nuna a kan fuskarshi sai dai bai tanka ba har ta gama ta cigaba da kukan.

"A wani asibiti take?"
Ya jefa maganan a hankali

"Tana 44 ne, anan muke da file"

Kai ya gyaWa kan ya katse wayan, Afeefah dake tsaye jikinta ne yayi wani irin sanyi a hankali zuciyarta ke motsawa da wani irin yanayin damuwa ba dai saleem da ta sani ake magana akai ba? Amma ai wannan Muryar ta Sadiqa ce, saleem ne har ya kori mahaifiyarshi a gidanshi? Ko jikinta duka kunnuwa ne ba zata yarda yana cikin hankalinshi yayi hakan ba, Wani irin tashin hankali ne ya zo mata har ta kasa boyewa ta manta waye a gabanta tace

"Yaya Saleem ne cikin wannan hali? Shi ne ya kori mahaifiyarshi da kanshi? Su Samha ne ke cikin irin wannan damu..."
HaWa idanu da suka yi ya sa maganar ta katsewa idanunta har sun cika da kwalla suna shirin zubowa, gani irin kallon da ya mata ya sa ta saukar da idanun ™asa, ajiye spoon Win hannunshi yayi ya zari wayan bai mi™e ba yana nuna ta da wayan ya ce

"Kika kuskura kika sake hawaye Waya ya zubo miki a kan fuska za ki gane ba ki da wayo...!"

Mukut haka ta haWiye kukan zuciyarta na cigaba da racing cikin mixed feeling ga idanun da ya zuba mata yana jira ya ga zata yi kukan ne ko ba zata yi ba ga damuwar halin da ta ji wai saleem na ciki.

"Mam..mi na ™iran ka"
Ta faWa a Wan tsorace. Kwafa yayi ya mi™e ya fice daga wurin da sauri ta dafa dining Win tana jan kujera ta zauna....




=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*34*

*Don Allah readers ina Wan so ne in ja hankalinmu a kan wani abu da na fahimta, zan Wan yi magana ne da miyaun marubuta. A duk sadda marubuci ke rubutu ba duba iya zallar nishadantarwa yake ba ko da kuwa littafin akan nishadi ne, ba son rai ake dubawa ba saboda ba shi ne ake son isarwa ba, duk sadda marubuci ya Wora alkaminshi a kan Littafi tunanin farko da zai fara shine me ya

Please Login or Register in order to submit comment