Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gyalen ta tana kuka kawai taji an turo kofan an shigo, da sauri ta Waga idanunta dake zub da hawaye sai suka shige cikin nashi da ya jirkice, wani irin kallo ya mata da ya sa tayi saurin mayar da idanunta ™asa tana Mi™ewa tsaye.

"Kin raina ni ko? Ni za ki wula™anta??"
A hankali yayi maganan. Sai ta Wago tana cewa

"Kayi ha™uri ban san zai shigo ba, ban san mahaifiyarshi ta kira shi ba da na nemi izini..."

"Shuttt up!! Just shut up Afeefahh"
Ya daka mata tsawa har saida ta tsorata tayi baya baya zata faWi ta dafe jikin gado kirjinta na sama da ™asa. Yau ne karo na farko da taji sunanta a bakinshi Dukda kaWuwar da tayi hakan bai hana sunan sake amsa kuwwa cikin kunnuwanta ba da muryarshi.

Shiru yayi yana sauke numfashi idanunshi a tsaye a kanta ya ce a zafafe
"Ko babyn roba na aura, ko 'yar tsana ce ta amsa sunan matar Rayyan Moh'd Khamis wallahi billahi na fi ™arfin ta wula™anta min aure... A gabana kike cewa aurena dake ™addara ce??"

"Ka yi ha..kuri ba haka..."
Juyawa kawai yayi ya fice yana buga kofar da karfin gaske sai da ta sake razana.

"Na shiga uku!"
Ta ambata tana zama bakin gadon.





=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Yauwa. Ga Page Win ku na yau, it's monday already! ba ni da tabbacin zama available through out.*

*42*

Zaune kawai yake a kan couch bayanshi na jingine da jikin kujerar idanunshi a lumshe, tun da ya dawo daga Sallar isha haka yake.
Wani iri yake ji lokaci lokaci ya kan buWe idanu ya kalli kofan ko za ta shigo amma shiru babu ita ba alamunta, sai wuraren sha biyu ya mi™e ya Wan yi shirye-shiryen shi na bacci ya koma gado ya kwanta sai ya tsinci kanshi da kallon wurin da take kwanciya a kwana biyun yadda inuwarta ke yi, irin rikicewar da tayi ta rungumeshi a daren jiya hannayenta na yawo a cikin sumanshi da bayan wuyanshi ya tabbatar da ana lafiya ne ba za ta taSa iya hakan ba, sai yaji emptiness da ya rasa na menene, da kyar yayi bacci bayan ya yi overdosing magungunanshi.

Ta Sangaren ta tana so taje Wakin amma tana tsoro, kila bai huce ba kar taje kuma ya hau ta da faWa ko ya make ta, haka ta shirya ta kwanta a kan gadonta sai ta dinga tunanin moment Winsu na jiya sautin numfashinshi na dawo mata har heart Winta na racing a haka bacci ya Wauketa.

Karfe goma na safen Washegari ta fito a shirye cikin half boubou da skirt na lace cream colour da mix of dark pink yayi mata kyau sossai ta yafa pink gyale bayan dan kunne da wani zoben gwal dake yatsanta bata wani saka acessories ba ta fito zuwa babban kitchen ta karbi abincin su ta kai ta shirya a dining kan ta koma wurinsu jannah da Uncle ya kira mijinta ya zo ya dau™eta yau duk su mama ma yau za su koma gidajensu.

Shi kam tun da ya dawo Sallar asuba bacci bai Wauke shi ba yana zaune kan kujera inda kaman nan ne wurin zamanshi a Wakin, as usual idanunshi a rufe ruf bai motsa ba har sai da Abeeha ta kira shi a waya akan su Mama za su koma gidajensu ya mi™e ya fito suka sake mishi gaisuwa da ban ha™uri kan suka tafi bayan sun raka su har waje, ya kalleta amma bai tsawalla kallon ba don haushin ta har lokacin yake ji barin ma da ya kalli yadda idanunta suka zama saboda kukan da tayi jiya Dukda ba kowa zai lura ba amma shi with a single gaze ya fahimci lids Win are swelled up a little.

Bai koma ciki ba motar Sulaiman ya shigo gidan sai suka isa kan kujerun da aka shirya don hutawa a chan gefen gidan suka zauna.
"Ya dai? Na ga kaman ranka a Sace sossai?"
Sulaiman yayi tambayar don a hankali Sulaiman Win yayi mugun karantar shi har ma ya zama kaman Saleem a wurinshi Wan zaman da suka yi daga aurenshi zuwa yanzu rasuwar Mammi.

"Hakane am just worried sick about one or two things."
Sulaiman ya gyara zama
"Toh fa, menene kuma?"
Nan ya bashi labarin duk abin da ya faru Sulaiman sai yayi murmushi
"Are you jealous?"
"Menene hakan?"
Yayi tambayar kaman bai san me ake nufi da kishi ba.

"Rayyan kana kishin Afeefah ne sossai kayi adu'ar sassaucin zafin kishi, anan dai zan baka laifi Saleem ko da bai auri Afeefah ba kaman Yaya yake a wurinta sannan Saleem yana da fahimta am very sure bai san reasons naka bane yasa ranshi ya Saci, shima fa mutum ne kaman kai yana da zuciya a kirji, your words are harsh gaskiya kenan.."

Ya gyaWa kai
"I know, tun jiyan i wanted to call him amma sai na bari ya huce tukuna. I just lost control tunda ta furta wai aurena kaddara ne kalaman sun min zafi"

Dariya Sulaiman ya fara
"Kana wasa da So Surgeon General Ryan Khamis, kuma fa babu wani abin zafi a maganan nan kishi ne kawai irin naka... Ai komai ma mukaddari ne daga Allah ta wani mawaki yace Nufin Allah ne! HaWin Allah ne ko da basa so su gani sai anyi! Ka ga kenan dole da kaddara a komai. I'am advicing kaje ka samu Saleem ku yi resolving issue Win nan"

"Kai! ka fa dameni da zancen kishin nan idan ma kishin ne ai ban yi laifi ba a gaban ka na cire kuWina na biya sadaki!"
Yayi maganan da iyakan gaskiyarshi yana sake kame fuska Sulaiman yana ta dariya.

Basu jima ba ya wuce, shima ya shiga ya zari key bai ko bi ta kan abin kari ba ya fice daga gidan kai tsaye gidan su Saleem Win ya tafi, bai shiga ciki ba ya kirashi a waya akan yana waje mintuna kaWan sai ga Saleem Win ya zo ya buWe kofan motar ya shiga ya zauna ba tare da ya ce komai ba.

"Ka tashi lafiya?"
Rayyan Win ya faWa, bai jira amsar Saleem ba ya Wora da.
"Na zo ne in baka ha™uri akan abin da ya faru tsakaninmu we are not perfect in everything sannan a zaman tare dole watarana a saSa. A koyaushe kai ke ha™uri da ni I really respect and appreciate you Saleem kuma ka fi karfin duk abinda kake zato a gareni! Saleem...Billahi ban Soye maka wanzuwar Afeefah a gidanmu saboda son zuciya ko wata soyayya ba don har yanzu ban sani ba shin ina sonta ko ba na sonta na dai san ban tsane ta ba"
Ya Wan yi shiru kadan kan ya cigaba
"A lokacin da muke waya da kai akan Mommy ta kore ta na ganta amma ban zaci saboda kora ne take tsaye a kan titi ba, jin irin damuwar da ka shiga ya sa nayi deciding in koma in Wauko ta kafin ka samu masalaha da mahaifiyarka, ko da na koma ban sameta ba a sannan aka kira ni ba'a ga Mammi ba cikin damuwar rashin ganinta na tafi asibiti ka san halina farin sani damuwa na ba komai bane illa kar a samu wasu su cuceta ko su zalunce ta sanin bata san gari ba. ko da na isa asibitin sai na samu ashe ita ce ta taimaki Mammi, from there Mammi ta fara ™aunarta har ta mayar da ita gida ba tare da na ce musu komai akan labarinta ba Dukda na san Mammi da su Abeeha amma ba zan so ta samu matsala a gidan yadda ta samu a naku ba, nayi tunanin faWa maka sau ba adadi ina tsoron saka ka cikin wani damuwar don na san in har ka san inda take ba lallai ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya ba, zai iya zama ka saSa umarnin ta saboda mace ko kuma shaidan ya ja ka ga fushintan ta hanyar yarinyar, na bari akan daga baya idan kayi settling komai sai na faWa maka. Unfortunately abun nan ya zo ya faru tsakaninka da ex wife Win ka da i even called her name to your ears ka nuna baka santa ba kana da mata..."
Daga nan ya bashi labarin duk yadda aka Waura aurensu da Afeefah.

"Na karSi auren ne saboda Mammi Dukda ta rokeni ya zama saboda Allah zan yi wa Afeefah komai ko da bata nan zata samu peace of mind na cewa ta barta inda ba zata wula™anta ba, na san Afeefah ce tayi adu'o'in duk da kake using na seven days a gidan mu ban damu ba saboda na san ka cancanci fiye da hakan daga gareta, ko da ka samu lafiya kafin mu yi maganan Allah ya kawo ajalin Mammi... Wallahi idan da za ta zaSe ka Saleem ta tabbatar min za tayi farin ciki a tare da kai zan iya sakinta ka aureta... Saboda burin Mammi shine ta samu farin ciki da natsuwa a duk rayuwar da zata yi. I am terribly sorry da kalamaina na jiya i hope you forgive and forget ban san me ya hau kaina ba."

Ya sau™e numfashin wahala don ya gaji matu™a da maganan, Saleem ya Wauki ruwa dake tsakiyar su ya buWe mishi ya mi™a mishi sai ya karSa ya kurba kaWan ya mayar mishi sai suka Wan murmusa.

"Kishi ne ya hau kanka ba komai ba"
"Ana kishi haka siddan ne? Dazu Sulaiman ya gama ranting about that!"
Saleem yayi dariya yace
"Lallai kai sabon shiga ne, ai ba'a kishi babu So irin nakan nan ma mai zafi ne ™anwata ta ma zuciyarnan dabaibayi ba zaka farga ba sai ka gama zurmawa saura mu saka ™asa kawai mu binne"

Murmushi mai sauti Ryan yayi bai ce komai ba. Saleem ya dube shi yana sau™e numfashi
"A ha™i™anin gaskiya nima a sadda na dawo na kwana da tunanin actions Wina na jiya, kawai na saka a raina cewa ban samu labarin bane ta yadda ya dace hakan ya haddasa saSanin da muka samu. Tun a jiyan tun da na fita daga gidanku na riga da na sakawa raina har Abada Afeefah matsayin ta Waya da su Samha a gareni, ban san wani irin rabo bane ya haWa ku ban san me Mammi ta hanga ba ta haWa ku but i believe har karshen rayuwarku Afeefah ba zata yi kuka da kai ba muddin ta iya tafiyar da kai! Menene burina dama?"

Ya Wan ja numfashi
"Burina Waya da Mammi shine ta samu rayuwa mai kyau and am very sure tunda ta karSi auren take zaune lafiya she accept it with all her heart and soul to na me zan damu? Abeeha... She's so brave kalaman ta sun shigeni sossai da sossai am also sorry for what happened Ina yi muku Fatan alkhairi i also hope and prays za ka bani daman zama Wan uwan da ba ta da shi a rayuwarta"

Murmushi Ryan yayi ya Wago ya kalleshi
"Anya zan amince? ai sai ku haWe min kai Thats the role that Sulaiman is playing fah"
Saleem yayi dariya.

Kallon gidan Ryan yayi
"Why are you guys still here ba ku takura ba?"
Saleem ya Wan yi tsaki yana sake kallon gidan shima
"Mun takura fa kawai rasuwar nan shi yayi delaying Wina da yanzu mun koma Nan gidannan nawa na Malali already an gama komai maybe gobe we move out"
Kai ya gyaWa suka sake hira kaWan a kan aiki kan suka sallami juna Rayyan ya fice Saleem ya koma ciki hankali kwance.

Ya dauki hanyar unguwar su kenan aka kira shi a waya ya duba ya ga uncle Musa ne, dagawa yayi cikin ladabi suka gaisa
"Ina so dama na ganka ne Ryan idan ka samu dama ko yanzu ka zo."
"In shaa Allahu Baba gani nan zuwa"
Juya motar yayi ya nufi Unguwar sarki inda nan ne gidan uncle musan yake.

Yana zuwa ma ana kiran azahar yayi alwala suka shiga masallacin tare suka yi sallah kan suka dawo ciki, an kawo mishi abincin rana don haka a tare suka ci kan uncle Musa ya dube shi
"Ryan ka san idan mamaci ya mutu ana so a yi gaggawar sau™e mishi duk wani nauyi har gado, Toh zaman dai ya kamata mu yi da Abeeha da jannah ne amma sanin kana gaba da su kuma kai uba ne a gare su yasa na fara kiran ka, wannan takardu"
Ya mi™a mishi ya karSa yana dubawa Dukda komai na Mammi ya sani, haka komai na su Abeeha da jannah na wurin babansu dake hannunshi wanda Mammi ta sakar mishi yake kula musu da shi duk ya sani.
"Mamanka ta ce in tabbatar maka ita ta baka halak malak har abada baya cikin abinda za'a
raba nata"
Da sauri ya kalli Uncle Musa.

"Rabin dukiyar ta ne fa anan"
"Eh, ta saka hannu zaka gani lawyer Winta ya saka akwai kuma shaidu akan hakan. Ta mallaka maka rabin abinda ta mallaka wanda gado ne daga wurin mahaifinta kyauta"
Dukda arziki baya gabanshi kyautar ya kaWa shi sai yana jin sabuwar Soyayya da kuma tsananin kewa na Mammin, idanunshi suka sauya sossai ya kalli uncle da ya sake cewa

"Wannan kuma sauran rabin abinda ta mallaka ne na su jannah shima ta ce ne in bari a hannunka kai zaka zauna da su idan suna bukata ka basu idan sun bar maka ajiya ta tabbatar za ka juya musu yadda ya kamata"
KarSa yayi yana jin wani iri sossai da sossai. Da kyar ya haWa natsuwar shi wuri guda yayi godiya wa uncle Win kan ya fice daga gidan ya nufo gida.

Yana parking wayanshi ya Wauki ringing ganin ogansu ne yasa yayi picking tare da saluting maganan mintuna biyar suka yi ya sauke wayan tare da bude media group dinsu, news dake yawo ya zubawa idanu sama da mintuna goma ba tare da ya sani ba kan yayi baya baya ya jingina da kujera wani irin abu na tsaya mishi a tsakiyar zuciya, sossai news din ya jijjigashi amma yana iya kokarinshi wurin ganin ya danne don in ka kula har jikinshi rawa yake sai lumshe ido yake yana buWewa lip dinshi na ™asa a Wan datse tsakankanin hakwaranshi.

Sai da ya gaji ya buWe murfin motar ya fita ya nufi cikin gida, a babban parlor ya samu jannah da Abeeha suna zaune shima ya zauna suka gaishe shi ya amsa da kulawa ya dubi jannah
"Yaushe kike shirin komawa ne kam?"

"Dama yau ne to kuma ya tafi Abuja Wazu yace in zauna kawai gobe zai dawo in ya dawo zai biyo ya daukeni sai mu wuce gida"
Cikin girmamawa tayi magana. Ya gyaWa kai
Nan ya musu bayanin gadon su tare da fitar da papers Win ya ajiye.

Abeeha tace
"Ni dai Yaya bana bukatar rike komai a hannuna gaskiya, babu abinda ka rage mu dashi ko da Mammi ke raye baka barta ta mana komai da kuWinta ba don haka ka haWa duka ka ri™e a wurinka kawai."
Jannah ma tace
"Gaskiya nima dai babu abinda zan yi dashi a yanzu, kana min ko da nayi aure baka daina ba shima kuma bai rageni da komai ba for now ka bar wannan a hannunka yaya"
Kai ya gyaWa ya dubi Abeeha

"Gobe zan tafi wani aiki chan Gabas maso yammacin ™asar nan ban san adadin kwanakin da zan yi ba don haka ki duba ki rubutu duk abinda za ku bukata da safe zan kaiku shopping sai a saya"
Godiya ta mishi da Adu'a. Ya mi™e ya nufi sashensu.

Afeefah na zaune shiru cike da tunaninshi, bai karya ba hakan ya dameta sossai har take jin babu daaWi sai tunani take ko ina ya je? Ko yana lafiya? Tsoronta ma ya sha magani? Kar zazzabi ya dawo mishi yana ta yawo a rana duk ita kaWai dai ta yanke dole zata bashi hakuri ta kuma fahimtar da shi ba da wani manufa ta aikata abinda ta aikata ba.

Ta mi™e zata fita wurin su Abeeha kenan shi kuma ya shigo, kallo Waya ya mata ya Wan Wauke kai sai yayi sallama yadda zata ji ta amsa tare da cewa
"Sannu da dawowa Ya Saraki"
Ya Wan lumshe ido ya buWe kan ya ce
"Yauwa"
Daga haka ya wuceta ya nufi Wakin shi bai bata daman magana ba kenan har yanzu fushi yake, jiki a sanyaye ta fice wurin su Abeehar anan take jin labarin wai zai tafi wani Assignment gobe ba lallai ya dawo kusa ba jikinta ya sake yin sanyi ™warai har bayan Magrib bata san me zata yi ba, luckily ko da ta ajiye mishi abincin dare ya ci.

Bayan tayi isha ta gama shiryawa cikin cotton Light blue riga da wando dogo na kayan bacci ta Wora navy blue hijabinta har ™asa ta nufi Wakinshi don ta yanke zuwa kawai ta bashi hakuri kar ya tafi yana fushi da ita.




=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Tsakani da Allah ba ni da abin da zan ce da masoya sai na gode, ina ganin irin ™aunar ku gareni. Na gode kwarai da gwalagwalan adu'o'inku. Ta Baba Makkah kin faranta min kwarai, sai masoyinka na ha™i™a ne zai tuna da kai a gaban Wakin Allah har yayi maka Adu'a da Fatan alkhairi don haka wannan Page Win sadaukarwa ce gareki Allah ya bar zumunci har a aljannah, Allah duk ya dube mu ya biya mana bu™atunmu na alkhairi.*

*43*

Ta Wan jima tsaye jikin ™ofan tana tunanin ta shiga ne ko kar ta shiga? Da kyar ta tattaro kuzarinta ta Wan yi knocking kan ta tura kofar ta shiga gabanta na tsananta faWuwa.

Hasken Wakin ba shi da wani yawa don haka tsaf take kallonshi zaune tsakiyar gado jingine da pillow gabanshi system ne yana kallo, idanu ya Wan zuba mata tana tahowa a hankali har ta isa jikin gadon ta Wayan side Win inda shi kuma yana jingine ne da side Win da ya saba kwanciya.
Muryarta na fita a hankali cikin tsoron faWan shi ta shiga furta
"Na na..zo ne mu yi sallama na ji wai za kayi tafiya, kuma ina so ne in baka ha™uri wlh ban san kalmar ba zata yi maka daaWi ba. Don Allah kayi ha™uri."

Tun da ta shigo ya Wauke kanshi daga kan system Win ya zuba mata ido sau™ar muryarta a kunnuwanshi ya sa Ya Wan lumshe idanun ya sake buWewa a kanta. chan ™asan muryarshi yace
"Zo nan."
Bai cigaba da kallonta ba sai ya mayar da idanunshi kan system dake aiki gabanshi wanda kallo yake na wani horror movie, tun da yayi shirin kwanciya tunaninta ya so ya dameshi sam shi bai ma san me yake damunshi ba daga dan kusancin da suka samu kwana biyu shikenan kuma sai a ta shiga lokacin hutawarshi ta hana shi hutawa da tunaninta? System ya jawo ya fara kallon dole sai kuma Allah ya jefo ta.

A hankali ta hau gadon kamshinta na dukan shi har yana jin bugun zuciyarshi na sauya wa.
Idanunshi ya kai ga kallonta ganin tana chan nesa ya ce
"Matso nan"
Ya taSa gefenshi, a Wan tsorace cikin bugun zuciya ta matsa tana dana sanin zuwanta Wakin don ji take kaman zuciyarta za ta fito daga madaukarta don tsabar bugu, inda hannunshi yake ta matsa kaman an ce ta kalli fuskan computern aka nuno wani abin tsoro da ya firgigita don ta tsani film mai abin tsoro za ta gudu ya ri™o tsintsiyar hannunta babu zato sai gata bisa kirjinshi daga gefen kafadanshi ya mayar da hannunshi na wurin ta bayanta inda tayi saurin binne kanta a kirjin nashi sihirtaccen kamshin shi na sake shiganta yana ™ara bugun zuciyarta, baya baya yayi ya jingina da gadon yana sake kara kusantar da ita jikinshi.

Bai ce komai ba ya cigaba da kallon yayinda tayi shiru kawai tana sauraran bugun zuciyarshi, sun kwashe sama da awa guda a haka ko da ya gama ya Wan Wago ta zai yi magana kawai ya ga tayi bacci, ya san kwanakin tana ™o™ari kuma bata samun isashen bacci yadda baya yi itama bata yi, gwara ma shi da safe ya kan taSa amma ita ko da safen baya ganin tana yi sai zirga zirga.

Hijabin ya zare mata ya jefar ya zubawa fuskarta idanu yana kallo, bai san me ya ri™e shi a fuskar ba ya dai tabbatarwa kanshi da she's Drop-dead gorgous wanda bai taSa fahimtar fuskar ba irin yau, kallon natsuwa yake binta dashi da ya rasa dalili a hankali ya furta
"what's wrong with me?"
Ya kai hannunshi Waya yana jin zuciyarshi na pounding har sound Win na iya shiga kunnuwanshi...

Yana so ya kwantar da ita akan pillow amma sai ya ji ba zai iya ba don haka ya gyara kwanciyarshi ya gyara mata ta yadda rabin jikinta na a nashi ya lumshe idanu ga mamakinshi tunaninta ya cigaba da yi Dukda gata jikinshi da kyar bacci ya Wauke shi.

Basu farka ba har aka shiga masallaci suratul Fatiha da ake karantawa shi ya farkar dasu duk su biyu lokaci Waya ta yi saurin Mi™ewa zaune tana Wan matsawa kanta ™asa, ya Wan kalleta kadan yadda tayi kaman wacce aka kama tana sata ya sa ya Wan yi murmushin da bai fito ba ya sauka ya shige toilet, hijabinta ta Wauka ta sau™a ta gudu.

A bayi ta tsaya tana kallon kanta, bacci fa ta sake yi a jikinshi comfortably? Wayyoo Allah ta ayyana a ranta tana dafa zuciyarta, gashinta da tayi parking cikin messy burn ribbon Win ya fice bata ma san ta baro a Wakin ba, da kyar ta haWa tunaninta wuri guda tayi alwala tazo tayi sallah ta kwanta a wurin, sai Eight ta fito a shirye cikin Abaya Grey da yayi mata kyau sossai hula ne a kanta kai tsaye taje ta dubo abincin taga wanda zai iya ci ne ta kwaso ta kawo sashen nasu ta shirya dining ta saka turaren wuta a parlorn don a gyare yake tsaff yana kyalli ta juya zata koma ya buWe kofa ya fito, kallonshi tayi yana sanye da wani Army Green riga tare Black wando da ya amshe shi, rigan ya kama shi ya fitar da kirarshi sossai bai mishi ruwa ba sam sai taji wani nauyin shi ya rufeta ta mayar da kanta ™asa, ya kalleta ya Wan shafa gashin kanshi kaman zai yi magana kuma sai ya nufi dining kawai.

Binshi tayi sai da ya zauna tace
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
Ya bata amsa ko numfashi bai bari ta ™arasa saukewa ba idanunshi na akan fuskarta sai kawar da ido take daga kallonshi wanda hakan ma dariya ya bashi amma ko a fuska bai nuna alamu ba, ta haWa mishi abin kari da yau English breakfast suka yi a gidan ta tura mishi, bata so ta tafi tayi laifi don haka ta Wauki omlet Waya ta haWa tea ta ja kujerar da take zama chan nesa dashi ta zauna tana karyawa, bai ce mata komai ba itama bata ce ba.

Bayan ya gama ya mi™e ya koma Waki ta bishi da kallo tana Wan taSe baki mutum kaman hawainiya, tattare wurin tayi tsaf kaman ba'a ci abinci yanzu ba ta wuce nata Wakin, monday za ta fara waec don haka dole ta fara duba takarda kafin taje ta faWi sai ta fara lalabo takardunsu na makaranta ta Wauko wayanta ta fara bincike akan past questions da take son fara dubawa.

Shi kam kusan sai da ya gama haWa duk abin da zai bu™ata lokaci lokaci yana dan daakatawa ya tafi nazari kaman wanda baya kaunar tafiyar kan ya Wauki keyn mota da wallet Win shi ya fito sanye da wata White sneakers da ta sake fito da shigar tashi idanunshi ya rufe da ba™ar space sai ya zama kaman wani model ya san kan wanka ba laifi, a babban parlor ya samu su Abeeha suna ganinshi kuwa suka mi™e tsaye don dama sun shirya saboda sun sanshi yadda ya washi jira sai dai a jira shi...

Har sun nufi kofa yace
"Ina take?"
Duk tsayuwa suka yi Abeeha na so ta tambayi ita wa amma fuskar shi da ba'a sake ba yasa tace
"Afeefah ina ga bata san da ita za'a yi fitan ba bari na ™irata"
Ta ™arasa tana nufan sashensu a ranta tana

Please Login or Register in order to submit comment