Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta ro™e shi ya taimaka mata ko da ya haWa ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaiman ai bai san wacece ita ba idan su ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake faWa hawaye na silalo mata daidai ya sake kallonta idanunshi suka sau™a kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar wurin.

Juyawa tayi ta cigaba da jan trolley Win dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin saleem ma a duniyarta shi kaWai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta faWi Afeefar tayi hanzarin sake akwatin ta ri™e ta
"Subhallah! Ki yi ha™uri"
Ta faWa cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta
"Lafiya Aunty? Ko baki da lafiya ne?"
Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.

Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani tunani ne ya faWo wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa
"Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan taSa jakanki ba"
BuWewa tayi ta samu Wari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki itama ta shiga mai machine Win ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi
"Asibitin dake kusa don Allah"
"Sannu, Sannu"
Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a haka suka isa wani private hospital ya shiga da su har ciki aka dau™eta emergency zuwa lokacin bata numfashi.




=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*018*

Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac Win shi ya ™are, hakan ya Sata mishi rai don baya son buWe glass na mota yana tu™i, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren sha biyu ya bar asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai Wauki hanyar cikin unguwar su na Barnawa hold up ya ri™e shi, a dole ya sau™e glass saboda zafin da yake ji.
Karon farko da idanunshi suka sau™a a kanta bai gane ta ba sai da ya Wan yi focusing na seconds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya taSa ceta from poison, wannan yarinya da saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da ya mayar da idanunshi wurin suka sau™a a kan trolley dake gabanta, idanunta ya sake mayar da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai Waga ba shi da ya tsani kira sau biyu ya kan ce ai duk uzurin da mutum ke yi in ya zo ya ga na farko zai bi ba sai ka ta jera kira kaman marar aikin yi ba, a kira na uku saleem ya Waga sai dai ya kasa magana.

"Saleem are you Okay? Whats wrong with ur voice?"
Saleem ya kasa magana don shi kaWai ya san me yake ji, Ryan bai taSa jin Muryar abokin nashi a haka ba, dole ya nemi wuri yayi parking
"Saleem Mommy ce?"
Yayi uttering
"Uhmm Ryan Mommy ta kori Afeefah ban san wani irin hali za ta faWa ba, mommy tayi alkawarin tsine min na sake ko da magana da Afeefah ne bare yunkurin taimako aure ko soyayya, she's too young Ryan she's too young! Na san tana chan all alone, scared and disturbed idan wani abu ya same ta fa? Its all my fault da na fara son ta Its my fault..."
Hawayen da yake yi ne ya sa ya datse lips Win shi da ™arfi sai kawai ya katse wayan.

Kunna motar rayann yayi yana jin wani abu a ™asan ranshi, tausayin Saleem ya rufe shi haWe da damuwan jin halin da yake ciki bai taSa jin abokin shin haka ba, saleem da ko haWe rai baya yi. Fuskarta yake gani a idanunshi ashe kallon taimako take mishi, steering ya Wan buga da tafin hannunshi yana zagayowa inda ya barta sai dai neman duniya bai ganta ba, har parking yayi ya sau™a yana takawa da kafa ya zazzaga bata nan. Bakinshi ya Wan taSe kaWan yana shirin juyawa wayanshi yayi ringing.

Zarowa yayi sai ya ga Driver Win Mamminshi ne, dagawa yayi
"Ado ya aka yi?"
Ya fitar da maganan yana lumshe ido sam ba zaka san yana da damuwa ba ko hankalinshi ya Wan tashi don fuskar bai nuna ba ko da wasa.
"Oga akwai matsala ne, Hajiya ce!"
Tuni ya ware idanun a take suka sauya ya fara nufar motanshi yana ji Ado na mishi bayani wai ya kaita sayayya kuma yayi ta jira bata fito ba ya shiga ciki kuma yayi neman duniya bai sameta ba.
"A ina ne?"
"Galaxy mall"
Yana kusa da wurin ™arasa wa kawai yayi
"Ka ™irata?"
Ya jefawa Ado tambayar Ado yayi saurin du™ar da kanshi don ya san fushin Rayyan a take sai ya haukace, idanunshi sun yi mishi kwarjinin da ba zai iya kallon cikinsu ba
"Ban fito da waya ba"
Wani irin kallo ya watsa mishi lip Win shi ma sun yi nauyin buduwa bare su sake furta ko da kalmar A.

Wayanshi kawai yake dannawa ya shiga ™iran layinta sai dai ringing na duniya ba'a Waga ba, tracker ya shiga na Find my Iphone tuni ya ga location da take, a maimakon hankalinshi ya kwanta sai hankalinshi ya sake tashi ba za ka sani ba amma in ka ™ura mishi ido zaka ga hannayenshi har rawa suke idan kuma ka taSa za ka ji sun yi sanyi tamkar ™an™ara to baya cikin lafiya kenan.

Mota kawai ya shiga ya ja tafiyar mintuna goma ya isar da shi asibitin yayi rough parking ya sau™a ya nufi ciki, a gaban nurses station ya tsaya
"An kawo wata elderly woman yanzu! Where is she?"
Da Wan karfi yayi maganan don ya ga mace Waya ce kawai ta mayar da hankali kanshi tsawar da yayi ya sa duk suka juyo, kofan emergency kawai ta nuna mishi ya nufi wurin kawai ya tura ya shiga.

"Excuse you! Baka san ba'a shiga nan bane?"
Id card Win shi ya fitar ya nuna musu idanunshi na kan Mammi da suke ta ™o™ari wurin ganin sun ceceta ya furta a hankali
"The patient is experiencing end-stage renal disease(ESRD) nd she's diabetic i hope ba ku yi kuskuren komai a kanta ba"
Ja da baya wanda ke rike da drip yayi don ba ruwan masu sugar bane, Id card Winshi kuma ya tabbatar musu da waye shi. A tare da shi aka cigaba da ™o™arin ceton Mammin kusan awa Waya da wani abu kan suka fara fitowa aka barshi shi kaWai.

A kan kujera ya zauna ya sa hannu ya ri™e nata Waya ya gimtse a duka hannunshi biyu ya Wora goshinshi a kai yana jin jininshi na cigaba da tsitstsinkewa rauni mai girma ne da ba zaka Wauka irin shi mai dakakkiyar zuciya zai nuna ba bayyane a fuskar shi da ma idanunshi, ™iran sallah ne ya sa ya Wago a hankali ya zuba mata idanu sama da mintuna uku kan ya mayar da hannun a hankali ya ajiye mata ya mi™e ya fito Fuskarnan babu Wigon walwala, a kan trolley idanunshi suka fara sau™a ya Wan kalli Ado da ke ma™ure gefe kaWan kaman zai yi magana kuma sai ya fasa yayi gaba, sallah yaje yayi bayan ya idar ya dawo yana shigowa reception Win tana Wagowa suka haWa idanu, handbag Win hannunta ya Wan kalla kan ya nufeta.

Yana matsowa dukar zuciyarta na ™aruwa gabanta sai dukan uku uku yake tamkar za ta rasa numfashinta take ji don bai daina kallonta ba kuma bai daina nufarta ba kamshinshi ya riga shi isa, ko kan ya iso aka ™ira shi
"Sir the patient, ta farka"
Numfashi kaWan ya sau™e ya juya ya nufi Wakin, bata san ta kama numfashi ba sai da ya Sace mata taji tana kokarin mutuwa ta sake shi da ™arfi tana dafe kirjinta, Allah ya gani tsoron shi take bata sani ba ko tun ihun da yayi mata ne tayi developing wannan tsoro ko yaya amma muddin ya sau™e ido a kanta sai ta ji wani tension na building inside her.

Idanu kawai ya zuba mata ta Wago ido ta kalleshi cikin ™arfin hali ta sakar mishi murmushi tare da mi™a mishi hannunta, ya taka a hankali yaje ya kama yana zama
"Mammi..."
Sai yayi shiru ta sake yin murmushi mai kyau
"Saraki na ji sau™i ka kwantar da hankalinka, sannan am sorry na ji ina son Wan shan iska ne ya sa na fita not knowing hakan zai faru am sorry na Waga maka hankali"
"Mimmi stop it please, am sorry i wasn't there to take you out myself da kin faWa min zan bar duk abin da nake zan zo na kai ki na kula da ke har mu koma, Its my fault da nake emphasizing akan zaman gidan am sorry you get bored"

Hannunshi ta Wan matse tana murmushi har lokacin, Wago ta yayi ya buWe ruwa ya bata ta karSa babu musu ta sha sossai kuwa don masu ciwon su na bu™atar enough ruwa a jiki.

Basu wani jima ba suka fito yana ri™e da ita, har lokacin in har ka san shi sosai za ka hangi akwai damuwa a fuskar shi, Afeefah da har lokacin tana zaune a wurin tayi saurin Mi™ewa ganin su tare, dama ya san matar?
Menene ala™arsu? Ta ya aka yi ya san tana nan? Su ne tambayar da ta tsaya yi tana daga tsaye tana kallon su.

Idanun Mammi ne ya kai kanta, sai ta dakata tana tunani ga jakanta dai hannun stranger a hankali take tuna abin da ya faru yarinyar ce ta taimaketa, ta yi mamaki ™warai ganin yarinyar har lokacin kuma ri™e da jakanta da alama ko ajiye shi bata yi ba, tana tuna kalaman yarinyar na ban ha™uri a sadda ta Wauki Wari biyar ciki.
"Saraki wanchan yarinyar ita ta taimakeni ta kawo ni nan, da ban san me zai faru ba"
Kaman bai fahimta ba ya sake kallon Afeefah, chan ™asan ranshi ya ji daaWi kuma ta samu wani ™ima a idanunshi saboda duk wadda ya kaunaci Mammi ko da bai kaunaceshi ba shi ya bashi daraja na musamman, sai dai har lokacin fuskar shi bai nuna ba sai nufanta da Mammin ta sa suka yi, ita abin da ya kaWa ta ma tahowarsu tare, ita dai ta rasa wannan irin razani da take shiga da kwarjinin wannan bawan Allahn, ko da suka tsaya gabanta sai ta ga ya cike wurin gabaWaya, kuma kallonta yake don Mammi ta sake shi ta kama hannunta.

"Šiyata yaya Sunanki?"
"Sunana Afeefah, Aunty ya jikin ina fata komai lafiya?"
Tayi maganan kaman mai tsoron wani abu zai kama ta
"Alhamdulillah Afeefah, na gode ™warai da kyakyawar tunanin ki ba kowa ne zai iya irin taimakon da kika yi min ba, Allah ya saka da alkhairi"
Afeefah tayi murmushi
"Babu komai Aunty, ga jakarki ki yi ha™uri na cire Wari biyar a ciki mun hau adaidaita saboda ba ni da ko biyar"
Murmushi Mammi ta saki ta Wan kalli Rayyan da bai ce komai ba ya zuwa yanzu ya kawar da kai daga kallonta sai dai yana sauraren su.

"Gaskiya samun irin ki a wannan zamani sai an tona"
Idan ta tafi da jakar nan ba karamin abu za ta samu ba don bata tantama har zobunan gwagwalanta suna ciki amma bata ko buWe ba bare tayi tunanin yi mata sata, hakan ya matu™ar burgeta.

"Saraki mu kai ta gida ko? Ina so in ga gidansu in yi ma iyayenta godiya kuma in basu hakurin rashin ganinta kan lokaci"
Ta kalleshi shima ita ya kalla bakinshi ne yayi mishi nauyi, kuma ba ya son dogon bayani sai ya kalli Afeefar da kanta ke ™asa kaman daga sama ta ji ya ce

"Kina da gida?"
Yayi maganan yana Wage gira Waya.

Mammi ta Harare shi
"Wani irin tambaya ne wannan akwai wanda ya faWo daga sama ne?"
Ita dai tambayar ya zo mata wani iri sai hawaye suka cika idanunta a lokacin ta tuna ashe bata da inda za ta je, da alamu kuma ya sani don maganar shin ya fi yi mata yanayi da gatse, a hankali ta kalli Mammi

"ba sai kun kaini gida ba Aunty, kina bukatar hutu saboda jikinki daga nan zan koma da kaina"
Tayi saurin juyawa amma duk da haka ya ga hawayen da ya silalo mata, Ado ya kalla

"Šauki akwatin nan mu tafi"
Yana kai nan ya fara kokarin kama mammin

"She has No where to go, for now za mu tafi tare"
Cike da tausayi Mammi take kallonta, so take ta ji karin bayani me ya sa bata da inda zata je? Ina dangin ta in bata da iyaye? Amma sanin duk ba yanzu bane lokacin maganar ta saki Rayyan ta ri™o hannun Afeefar galala yayi yana kallonta ko ta tsaya don ta san rigimar shi, haWe fuska yayi sossai ya biyo bayansu.

Sanin halinshi ya sa Mammi ta zauna gaba Afeefah ta shiga baya, ya ja motar a hankali ya fita daga asibitin, Ado ma ya bi bayanshi har yanzu zuciyarshi bai dawo daidai ba yana tantamar ko Rayyan ya barshi ko sai ya Wauki mataki a kanshi don abin da duk ya shafi Mammi baya wasa da shi sam kaman yadda ita ma bata da kaman Rayyan a duniyarta.

Shiru motar yayi don Mammin na bu™atar hutu so ganin ma kaman ta gaji da zaman ya nemi wuri yayi parking, ya Wan koma baya ta yadda ya sake birkita Afeefah dake zaune saitin kujeran shi ya sa hannu ya kwantar da seat Win mammin a hankali, ta buWe ido ta kalleshi ta Wan yi murmushi kawai ta sake lumshe ido ya furta
"Sannu"
Cikin tsantsar kulawa, sai kallonsu Afeefah take yi. A iya zaman nan ta fahimci matar tana da matu™ar muhimmanci a rayuwarshi Dukda bata ga kama ba don matar ba™a ce kaman ita shi kuwa farin shi har ya Saci, ba zaka taSa cewa bai hada dangi da Larabawa ba barin ma kasumba da gemun da ya ajiye Wan daidai da shi ba™i sidik.

Motsin kirki bata iya yi kamshin motar har yana hawa mata kai a haka suka isa wani tsararren unguwa shiru ne unguwar kaman ba titin da suka baro ke Wauke da hayaniya da jama'a ba, nan Win gidajen manya manya ne, sai dai ka hangi su dawisu da su jimina a gidajen da gininsu ma na zamani ne, gaban ko wani gida kuma akwai securities zaune kusan kowanne sanye da uniform ko yellow ko blue, a hankali ya gangara gaban wani golden gate mai girma fuskar sai sheki take horn yayi, sai gashi an le™o wannan Win ma na sanye da blue riga da bakin wando, Gaisuwa ya shiga mi™awa Ogan nasu ya Waga mishi hannu kawai don Window na sau™e saboda rashin Ac. Tamfatsetsen gida ne don yayi na su Saleem sau uku ko biyu da rabi, gidan tamkar ginin sarauta saboda fari ne kal an mishi ado da golden paint har kwanon golden Color ne, harabar na shimfide da interlocks Wauke da shukoki masu tsananin kyau da Waukar ido, Dukda akwai parking lots har uku jere da motocin alfarma bai yi parking a ciki ba sai da ya je dab kofar shiga yayi parking ya sau™a ya zagaya ya buWewa Mammin kofa.

Ita dai Afeefah na ta mamaki don bata zata akwai wanda wannan mai zafin ran ya dauka da muhimmanci ba haka, bata taSa zaton zai iya buWewa wata macen kofa ba kila dai mahaifiyarshi ce, kila kuma kamannin mahaifinshi yayi shiyasa basa kama ko ta wani Sangare.

"Afeefah sau™o mana kin zauna ciki"
Ta faWa a hankali, buWe murfin tayi ta sau™a tana jin kanta dake sara mata na ™aruwa saboda tsabar kukan da tayi yau, kunyar hijabin jikinta take don onion colour ne kuma duk gaban da ya jike da hawaye ya bushe sai yayi wani jirwaye jirwaye,
A baya ta bi su har suka shiga cikin tsararren parlorn mai girman gaske sanyi ne ke ratsa ko ina ga kamshi, parlorn kal kal kaman a zuba maka abinci a ™asa ka ci komai na parlorn royals ne golden and milk, tana kuranta kyaun gidan su saleem wannan gida ya fi nasu tsaruwa nesa ba kusa ba.

A cikin kujera suka samu wata budurwa ganin Mammi ya sa ta tashi da gudu ta nufeta sai dai hararar da Ryan ya sakar mata ya sa ta fasa isa da gudun ta Wan natsu
"Mammi are you Okay? Me ya same ki? Na dawo daga school wai kin fita Mammi jikinki yayi kyaun da za ki fita? M..."

"Will you shut up and let her rest?"
Ya faWa ba da tsawa ba sai dai ba kuma da wasa ba, mammi ta Wan yi murmushi
"Abeeha ga Afeefah ki kai ta Waki na musamman a kai mata abinci tayi wanka ta kwanta ta huta sossai please she's exhausted daga alamunta"

Kallon Afeefah Abeeha tayi sai ta juyo zata fara jero wa Mammi tambayoyin ina ta samo ta sai suka haWa ido da Ryan tuni ta wuce ta kama akwatin da Ado ya shigo da shi suka yi wani Sangaren daga cikin parlorn.

A hankali suka isa wani matakala uku suka hau zuwa wani corridor da ya ji interior kan suka shiga wani parlor madaidaici kuma tsararre grey ne da Black colour, bai barta nan ba sai da ya sadata da cikin bedroom Winta duk ko ina suka bi kalkal yake gidan kaman kullum ake wankewa, a bakin gadon da shima Grey ya ji shimfida White ya ajiye ta ya buWe wani frigde dake gefe ya fiddo ruwa marar sanyi sossai ya bata ta sha sossai kan ta Wan kwanta
"Sannu Saraki Allah yayi maka albarka"
Idanu ya lumshe ya buWe tuni suka Wan sauya, a hankali ya amsa da Ameen kan ta Wan kwanta tana sau™e numfashi.

"Mammi ki huta sossai please, bana so in tafi in barki amma Saleem bashi da lafiya i need to go and see him, ba zan jima ba zan dawo"
Tayi murmushi
"Su fa Maryama suna nan kar ka damu take your time, kuma ma Abeeha ba ta dawo ba na san tana gamawa da Afeefah zata zo"
"Ta ishe ki da surutu dai"
Yana kai nan ya mi™e tana mishi sai ya dawo ya gaishe mata da saleem ya fice.

Wani motar daban ya Wauka mai Ac ya fice daga gidan bayan ya umurci Ado da ya fita da wanda ya dawo ya kai a saka Gas na Ac, kai tsaye gidan su Saleem ya nausa bayan ya isa ya bi ta baya ya haye saman zuwa Wakin saleem Win komai a kashe ya samu kaman ba mutum, hasken ya kunna ya nufi cikin Wakin sai ya samu saleem lullube da bargo, kanshi ya nufa ya janye bargon ya sa hannu a goshinshi ya janye
"Subhallah! Saleem you are burning up tashi mu tafi hospital"

"Ryan Afeefah, ban san wani irin hali zata faWa ba am scared kar Allah ya kama ni da laifi... Please help me find her please"
Da kyar yake maganan saboda zazzafar zazzabi dake kassara gaSoSinshi.
"Za mu same ta, In shaa Allah i will find her lafiyarka First ur temperature is very high"


=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku min uzuri da rashin amsa comments please matsalar wayata ta saka sai na nemi wani wayan nayi connecting hotspots saboda gidan sim din ta ™i gyaruwa, please bear with me idan na tara comments ina bi in karanta na gode sossai da sossai. Anjima zan samu in duba idan na ga an zuba yadda ya kamata in shaa Allah za ku ji ni da dare*

*019*

Ko sanar da mutanen gidan bai yi ba suka tafi asibiti kai tsaye Amenity ya sa aka kai shi ya fara bashi taimako saboda abin ya Buge shi sossai, tausayin Saleem Win ne ya rufe shi mahaifiyarshi bata yi mishi adalci ba amma uwa ce ya suka iya?

A chan gida kuwa Mudi ne ya shiga ya same su duk suna zaune a parlor fuskokin su babu walwala.
"Hajiya Oga saleem ne..."
Da sauri Sameera ta katse shi
"Yayi me?"
"Babu lafiya yanzu Oga Rayyan ya fita dashi jikin dai babu daaWi ban gan ku ba nake tunanin baku sani bane"
Samha ta ce
"Mun shiga uku, duk akan Afeefar ne?"
Shi dai mudi shiru yayi karshe ma ya bar parlorn, Saıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿmeera ta Wauki mayafi tana kallon mommy dake zaune har lokacin, sadiqa da Samha ma suka mi™e Sameera tace
"Mommy ki tashi don Allah mu je muga ya jikin nashi, mommy kaman ba a yi mishi adalci ba wallahi..."

"Ba zan je ba ki ja ni ki kai ni, babu inda zan je ya gama ciwon ya dawo ya same ni, ba dai a kan wanchan Mayyar ba ce? Zai yi ya gama Rabuwa kam sun rabu na har Abada"

"Amma mommy ya kamata dai ki je ciwo ai ya kore komai"
Sadiqa ta faWa, Samha tayi fuskar tausayi bata san haka abin zai kasance ba da bata janyo wannan rigimar from First place ba, suna son dan uwansu basa son ganinshi cikin wani hali.

Duk yadda suka yi da mommy akan ta je ta ™i haka suka tafi su uku, suna ficewa ta sabi gyale itama ta dauki mota ta bar gidan.

Tafiya mai nisa tayi kan ta iso inda ta nufa, wani gida ne tayi parking gidan dai daga gani Talaka ne mamallakinshi don ya tsufe har ya gaji, ta sauka ta shiga ciki da sallama.

"Ah Hajiya Hussaina ce tafe? Maraba sannu da zuwa sannu da zuwa"
Matar da daga ka ganta ka san suna cikin wahala daidai gwargwado ta faWa tana Wauko taburma sabuwa ta shiga shimfida mata zama tayi suka shiga gaisawa, bayan sun gama tana Wan kallon cikin gidan tace
"Yaya fa? Allah ya sa dai bai yi nisa ba"
Tace
"Yanzu kuwa ya fita amma babu jimawa zai dawo don abu ya je karSo wa nan kusa da mu"
"Ina yaran? Ina sabreena?"
"Duk fa sun tafi Allo, ita sabreena suna bukin ™awarta ta fita"
Bata gama magana ba kuwa sai ga Yayan ya shigo.

"Hajajju ke ce a gidan maraba sannu da zuwa"
Gaisawa suka yi Dukda yayanta ne sai dai shi ke bata respect duk saboda kuWi masu gidan rana.
"Ina soja marmari daga nesa? Sati biyu kuwa da ya shige ya aiko mana da kayan abinci wane Allah dai yayiwa rayuwa Albarka ya cigaba da buda mishi"

"Ameen yaya, dama maganan da ta kawo ni kenan ma akan shi... Ka san akwai batu a kanshi da sabreena da take ta mutuwar sonshi shi kuma yana nuna baya so, to yanzu zancen da nake maka wata yaje ya Wauko chan wani kauye ta asirce shi tun kan ma ayi auren sai maganarta yake ji yanzu haka saboda na raba su yana chan kwance gadon asibiti"

Gaje da Yaya suka hada baki suka ce
"Eyeee ka ji min yaran zamani ki samu mutum da uwar shi ki so raba su? Amma Saleem dai yayi ragon azanci ina shi ina irin waennan matan?"

"Shiyasa nake so a tado magananshi da sabreena da na Wauka wata mai hankali zai Wauko mana ashe dai shima hankalin bata ishe shi ba, na kuma ga gida bai koshi ba ai ba za'a kai waje ba, idan ba damuwa ma bana son auren nan ya Wauki lokaci ko wata bana so ya rufa ta zo tayi jinyarshi"

Gaje ta washe

Please Login or Register in order to submit comment