Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsala ihu ko zai fahimtar da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.

Zama yayi ya kalleta
"Mammi saboda ke don ke kaWai zan amince da zancen aure! Amma ban san kuma ta yadda zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba kuma... Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai karSa ne"

Shiru tayi tana kallon shi, ya ri™o hannunayenta

"Mammi kin san yadda na Wauki al™awari, na miki al™awari zan yi iya kokarina a duk abinda za ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko wacece zan zauna da ita yadda kike so matu™ar hankakinki zai kwanta, matu™ar za ki daina yi min zancen tafiya ki bar ni... Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa"

Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko babu komai zai tuna da ita ta zaSar mishi mata, zai tuna da ita ya yi mata adu'ar alkhairi a duk sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi zaSin nan da kanta ba za ta bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta ro™i ubangiji yayi mishi zaSi da kanshi ta san sai ya fi dacewa duniya da lahira...

Anan suka bar maganan ya mi™e ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai yi hannu ta Waga sama tana cewa
"Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah ka sada shi da duk wani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ™iyama..."
Ta shafa.

Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu'ar neman zaSin Allah, ko sau daya bata yi tunanin wata mace ba damuwarta kawai Allah ya zaSa mishi mafi alkhairi cikin mata, ya zaSa mishi matar da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman yaro ™arami da kan ri™e hannunta yayi kuka yayi kuka matu™a idan an faWa mishi abin da ya taSa zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da ™arfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.

Ta Wauki tsawon sati biyu tana wannan ro™on Allahn a cikin uku bisa Wayan dare lokacin da Allah ya ce mu ro™e shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na Waya yana neman bayinshi masu ro™on shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma'a bayan ta gama nafilfilunta ta kwanta kaWan saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lallaSa ya dau™eta ana ™iran farko na assalatu ta farka a Wan firgice ta mi™e zaune, a hankali ta saki murmushi mai kyau kan tayi Adu'a ta mi™e ta nufi bayi don gabatar da Alwala.






=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Comments Win ku shi zai yi determining Page na dare>Ĝ8Ŭ
@&ŝ*

*28*

Tun ™arfe goma sha Waya na safe Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma'a don yana so ya fita da wuri yana so ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.

A shirye ya fito cikin shigan manyan kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya Win, governors yard ne da aka yi wa dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito Wakin Mammi ya fara yi ya sameta zaune tana azkar Winta da bata rabo da shi.

"Sannu da hutawa Mammi"
Ya faWa yana zama gefenta
"Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka"
Ya gyaWa kai
"Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim"
"kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke Suya ko?"
Murmushi kawai ya Wan yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta ri™e da tray mai dauke da plate na abinci.

Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai haWa ta dashi kiyayewa take saboda yadda bata samun natsuwa a area Win da yake gashi abin laifi baya mishi kaWan yanzu ya hau faWa da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray Win ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi dake godiya ya ce

"Ba dai wannan abin za ki ci ba?"

Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci ne ya zama abu?
"Me yayi?"

Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace
"Kashe ta kike son yi?"
Wani irin faWuwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro waje tana so tayi magana amma Muryar rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind Winta ta yadda ko ya aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.

Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke razana ta
"Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?"

Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.

"Saraki...! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a hankali ai za ta fahimta ba sai ka yi mata faWa ba, kuma ni na saka ta dafa min ba gaban kanta tayi ba"

"Mammi ina Merry?"
Yayi tambayar ranshi a hasale, idan da bayanan sai Mammi ta ci abincin nan don ya tabbatar ko don wahalar da wannan yarinyar tayi ta dafa zata iya ko loma kadan ne don yarinyar ta ji daaWi, Dukda Couscous ne amma akwai abubuwa masu yawa da bai kamata ta saka mata ba ciki.

"Merry bata ji daaWi ba jiki da jini, Abeeha na school shiyasa nace ta dafa Win amma na tabbatar bata gane bayanin da na mata bane ba da gangan tayi hakan ba"
Tsaki ya ja ya Wauki tray Win ya fice.

A ™asa ta zube tana sau™e numfashin tsoro yadda yake zaro mata ido kawai take gani, Mammi ta dafa ta
"Ki yi ha™uri Afeefah duk ya firgitaki"
"Mammi ban san akwai abubuwan da bai kamata ki ci ba ciki kiyi ha™uri laifina ne"
"ba wani laifin da kika yi na kirki Alaiyahu da kuma tomatoes da kika saka ciki duk are high potassium veggies da bai kamata in ci ba su ne fa kawai sai zubin da yayi yawa kasancewar Couscous Win daga wheat ake samun shi, amma ai ina da ido kuma zan iya miki gyara shi dai kawai zafin kanshi ne dayawa"

Dukda halin da take ciki sai da ta Wan murmusa kaWan, yau public holiday shiyasa bata je school ba itama Abeeha wani research take yi shiyasa ta tafi Merry wacce ke da karatu na musamman akan nutrition Win irin masu ciwon Mammin bata da lafiya shiyasa ta shiga kitchen Win ta girka ba wai don gwaninta ko nuna iyawa ba, jikinta ya yi sanyi bata ma zauna wurin Mammin ba ta fice kar ya dawo ya sameta.

Shi kam kitchen Win ya koma, a hankali masu aikin suka zame suka fice sanin kila da kanshi zai yi girkin kaman kuwa sun sani, a take ya fara shirya abincin Mammin, idan ka ga yadda yake aiki za ka zaci wani professional Cook ne cikin taka tsantsan da tsantsar tsafta da Allah yayi mishi, wanke hannu kuwa ko me ya taSa sai ya je ya wanke hannu da handwash ya dawo, ko sau Waya kayanshi bai taSa komai ba har ya gama Wan small portion na chicken salad wanda da breast Win kawai yayi amfani duk wani ™ashi babu ciki, babu gishiri ya gasa da herbs kawai da lemon, ya haWa salad din wanda lettuce ne sai cucumber da Bell peppers da albasa kaWan, ba mayonaise ko cream ya saka ciki ba sai ya zuba man zaitun pure one a cikin dan karamin bowl ya saka 1 tsp na vineger ya kaWa da 'yar habbatussauda kaWan ya juye a cikin salad din ya gauraya ya zuba a cikin wani bowl mai kyau. Shinkafa ce 'yar kaWan ya dafa mata half cup ya haWa da ruwa don bata shan wani sugar ko juice ya Wauka ya nufi Wakinta.

Murmushi ta saki tana mishi godiya, ita bata yi mamaki ba don kafin yayi hiring merry da kanshi yake yi mata duk abinda zata ci shi ya uzzurawa su Abeeha har suma suka iya duk cimar ta da yanayin awon duk sun haddace, godiya ta mishi yace
"Mammi babu fa wannan tsakanin mu har Abada, abin da ya zama min dole ne nayi"

Daga nan ya mata sallama ya koma Waki ya sake gyara jikinshi kan ya kara turare ya fice daga gidan.

Kai tsaye gidan su Salim yayi, kasancewar yanzu ba kaman da ba ta babban parlor ya shiga da sallama, Mommy da ke zaune ta zabga tagumi ta Wago ta amsa a hankali, ya zamu wuri ya zauna yana gaisheta

"Lafiya ™alau Rayyan ka shigo?"

Samha dake kuka ya Wan kalla kan ya kalli mommyn
"Lafiya kam mommy?"

"Ba ™alau ba Rayyan, ban san me zan ce ba ban kuma san ta ina zan fara ba amma tabbas Salim baya cikin lafiya da natsuwar shi... Rayyan ko za ka bashi shawara? Ko zaka mishi faWa? Don saleem bai Wauke ni uwa ba kuma, saleem ya fi gane maganar matarshi akan nawa yanzu ya bar nan bayan ya fasa bakin Samha don kawai ta ro™e shi kuWin makaranta suna shirin exams bata biya ba matarshi ta sa baki sai tace mata ba da ita take ba da Wan uwanta take shikenan har ya kai abin duka kuma yace ba zai biya Win ba rashin kunyarta ya biya mata? Saleem dai ina mishi magana ya Waukeni banza? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."

Wasu irin hawaye masu zafi take zubarwa bata taSa zato ko tsammanin irin wannan butulcin daga Sabrina ba, shi karan kanshi Rayyan yayi mamaki don kowa ya san saleem ya san yadda ya Wauki mahaifiyarshi da ™annenshi, shi Win mai biyayya ne ko da ko baya so zai yi don ya faranta ran mahaifiyarshi, ya san dai saleem ya chanza mishi amma bai zaci har mahaifiyarshi da yan uwanshi ba, sai ya kira shi ba zai Waga ba kuma ba zai kira shi back ba, sau biyu yana zuwa headquarter baya samun shi shiyasa ma ya yanke ya zo gida ya same shi, Dukda shi namiji ne kuma ba kaman sauran maza ba amma daga maganan mommy ya fahimci akwai ayar tambaya mai girma akan saleem.

Bai gama tunanin ba aka fara sallama, sameerah dake zaune shiru gefe ta mi™e ta nufi kofar.

"Mun zo daga companyn gadaje da kujeru ne mun kawo order Win da aka sanya wannan address Win..."

"Anya gidan nan ne? Ko zaka kira Layin da aka yi order Win?"

"Toh bari na ™ira"

Kira yayi cikin mintuna biyu sai ga saleem da Sabrina sun sau™o, ganin Rayyan ya sa ya je ya bashi hannu suka gaisa
"Saleem kana lafiya?"
Yayi tambayar yana sake nazartar abokin nashi da ya ji wani irin tausayinshi ya tsarga mishi.

"Lafiya me ka gani?"
Girgiza kai kawai yayi ya ce
"Zauna za mu yi magana"
Babu musu saleem ya zauna Sabrina za tayi magana ya Waga idanu ya zuba mata haka kawai kwarjinin shi ya wani irin cika ta, duk yadda ta so tayi magana kasawa tayi sai ta nufi kofa ta fice tana kwafa.

"Me ya sameka? Me ke damunka abin da baka yi ba tun kana ™arami zaka yi shi yanzu da ka mallaki hankalin kanka? Saleem uwa ba Abar wasa bace ba kowace uwa ba, ba irin mahaifiyarka da tayi dedicating lafiyarta, karfinta da kuruciyarta don ganin ta gina rayuwarka ba... Ta gina ka ne don ka girma ka tallafi kannenka, yau idan baka biyawa su Samha kudin makaranta ba wa kake tunani zai biya musu? Me ya hau kanka haka saleem?"
A tausashe yake maganan, saleem bai ce komai ba ya zauna shiru duk yadda Rayyan ya buga ya kaWa akan ya faWa mishi menene matsalar bai ce komai ba, daga karshe Rayyan ya ce

"Saleem ka ba Samha kudin makaranta yadda ka saba bata"
Šago ido yayi ya kalleshi shima shi yake kallo zuciyarshi na rawa, tabbas akwai ayar tambaya akan dabiun saleem sai dai ba zai yi saurin yanke hukunci ba, yana zaune nan sai da saleem ya dauki tsawon mintuna biyar kan ya zaro wayanshi yayiwa Samha transfer Win kudin yadda ya saba bata, mommy ta du™ar da kai tana kuka mai ciwo. Da zafi abin da zafi kana gani a sauyawa danka rayuwa daga yadda yake zuwa wani abu daban.

"Je ka shirya mu tafi masallaci"
Bai ce komai ba ya mi™e ya haura sama, Rayyan ya runtse ido a hankali sama da seconds goma ya buWe sun dan sauya, Mi™ewa yayi ya fice bai kula godiyar da mommyn ke mishi ba, a gaban motar shi ya tsaya yana kallon Sabrina da ke tsaye ana sau™e wasu kwalaye cikin store nazarin ta sossai yake yi chan ya Wauke idanu ya sau™e kan saleem da ya fito, yana kallo sai da yaje wurinta suka yi magana ta Waga ta kalleshi kan ta gyaWa kai saleem ya wuce ya zo ya shiga motar suka fice daga gidan.

"Saleem idan ka ga Afeefah a yanzu za ka iya aurenta?"

Shi karan kanshi bai san ya jefawa saleem Win tambayar ba don ya jima yana mishi yawo a rai kuma yana son tabbatar da zarginshi kan Sabrina. Sunan Afeefah ya sake maimaitawa a ranshi don dai bai taSa ambatar sunan a fili ba ma sai yau.

"Aure? Ai ina da aure"
Ya amsa shi muryarshi babu wannan karsashin idan yana maganar da ya shafi Afeefah, kaman ma wata ce chan daban da bai wani sani ba.

Bai ja maganan ba ya yi shiru, dole su tashi tsaye akan Saleem da alama zautar da shi ake shirin yi, amma yayi matukar mamaki irin mamakin nan da bai taba zaton hakan zai iya faruwa da saleem daga aure ba, auren ma na dangi ba bare ba.

****

Zaune take gaban Mammi don sai da ta tabbatar ya fice kan ta dawo, abincin ta tsurawa idanu yadda ya tsara shi kaman wani chef tana mamakin yadda ya iya girki haka, Mammi bata ce komai ba ta shiga cin abincin sai da ta gama tsaf ta dubi Afeefah tace

"Afeefah akwai maganar da nake so mu yi da ke ko kuma in ce akwai alfarmar da nake so na ro™e ki ban san ko za ki iya yi min ba, ba abu bane da ya saSawa shari'ar musulunci abu ne da muddin kika amince min Afeefah zan yi matu™ar farin ciki fiye da zaton ki"

Afeefah ta gyara zama jin maganar serious ne, kuma a yadda Mammi ta Wauke shi da muhimmanci ya sa itama ta ji ta bashi muhimmanci itama
"Tashi ki dawo nan Afeefah"

Mi™ewa tayi ta koma kusa da ita yadda ta ro™a hannayenta duk biyu ta ri™e

"Afeefah na dauke ki ne tamkar Abeeha, ba zan taSa yin wani abu da zai cutar da rayuwarki ba amma ban san yadda za ki Wauki maganar ba.."

"Mammi yanzu fa kika ce ni tamkar Abeeha ce a gareki nima kuma ba ni da uwar da ta wuce ki, wlh duk abin da kike so matu™ar zai faranta miki kuma bai saSawa shari'a ba ni mai amincewa ne Mammi, faWa kawai za ki yi in cika shi na san ba za ki taSa cutar da ni ba."
Afeefah ta katse ta ganin kaman contemplating take na gaya mata abin da take so, ita kuma tana da yakinin koma menene Mammin za ta ro™a ba sharri bane.

"Afeefah za ki iya auren Saraki??"

Afeefah ji tayi kaman kunnenta bai ji mata daidai ba, bata motsa ba don bata gama fahimta ba jin Mammi ta yi shiru tana kallonta yasa tace
"Mammi ina sauraranki in shaa Allahu zan yi duk abin da kike so"

"Afeefah abin da nake so shine kafin na mutu in ga na haWa aurenku ke da Saraki...! Shin za ki iya auren shi? Za ki iya yi min wannan alfarmar?"

Wani irin shock ne ya ratsa Afeefah daga kanta har cikin tafukan sawayenta, a matu™ar razane ta zare hannunta daga na Mammi ta mi™e tsaye zuciyarta na wani irin bugawa kaman zai ratso kirjinta ya fito

"a..ure? Ni Mammi? Ni... Ni Afeefah da Wanchan mutumin...??"
Don ji tayi ba zata iya ™iran sunanshi ba ma ko Rayyan Win ko Saraki idan tayi hakan kaman wani zunubi ne da muddin ya ji ta sai ya sauya mata kammani, kallon kanta take yi daga sama zuwa kasa ta Wago ta kalli Mammi kaman wacce ta zauce...




=Ĝ¤ŬGureenjoh=Ĝ¤Ŭ

https://chat.whatsapp.com/BuI7cmoy3ed3C3IimZKZA0

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*29*

Hasaso Rayyan Win ta shiga yi a majigin kwakwalwarta, kallo Waya tak za ka yi mishi ka san cewa shi Win soja ne a sojojin ma na daban, yana da lafiyayyar jiki murWaWWe kuma a tsaye yake fatarshi babu Wigon ba™i ko guda Waya, Dukda ba zata ce ga yadda yake cikin khaki ba amma ko daga maganar shi zai tabbatar maka jajirtacce ne kuma gwarzon namiji wanda ko daga kallonshi za ka sha jinin jikinka.
Zaman shi, tafiyar shi da yanayin dabi'unshi kuwa za ka zaci wani babban sarkin ne na wani yanki na daban, yana da wasu irin idanu kyawawa da ko tuna yanayinsu tayi sai ta ji tsikar jikinta ya zuba kaman ba namiji ba, fasalta kyaun fuskarshi da sauran halittar da Allah yayi mishi ma wani tulin bayani ne na daban, don Allah ina ita ina irin gawurtaccen nan? Ta ina ma Mammi ta fara wannan tunanin?

Tazarar da ke tsakaninta da Rayyan kaman tazara ne da ke tsakanin sama da ™asa ko ta amincewa aurenshi ita ce zata wahala daga karshe saboda ba zai taSa son irin ta ba, ba zai taSa kaunar mace kamar ta ba wacce ta fito daga kauye cikin tsantsar jahilai, wacce take da tambarin Maita kuma annoba, wacce ko wucewa ta zo yi gidajen mutane sai an zuba tafarnuwa, ˜ashin kifi da garin kukan miya a wuta don haya™in Mayu.... Ai ko da gami wane ita da Rayyan.

"Mammi kaman ban ji abin da kika faWa ba"
Ta sake maimaitawa har yanzu a kidime.

Mi™ewa tsaye Mammi tayi ta ri™o hannunta suka koma zaune.
"Ki natsu Afeefah kin ji? Ki ba ni hankalinki kar ki yi wani tunanin fin ™arfi, namiji bai taSa fin karfin mace ba in har ta amsa sunanta mace, ke kyakyawace kar kyaun Rayyan ya ruWe ki, ke yarinya ce mai hankali, ladabi, natsuwa da kuma biyayya kina da zuciya mai kyau, you are the purest soul i've ever met... Afeefah ba zan hada ki da Rayyan bane saboda wani ra'ayi nawa ko buri eh ina da buri a kan ku duk biyu, sai dai burin ba na komai bane sai na son ganin rayuwarku duk ya inganta kun tabbata cikin farin ciki"

"Mammi shi ya ce miki yana so na?"
Ta tambaya a sanyaye don ba fahimtar kalaman Mammin take ba don abu ne da take ji ba zai taSa yiwuwa ba.

"Ba shi ya ce ba, ni ce na ga cancantar kasancewarku inuwa Waya kar ki damu da halinshi ko yanayinshi na fushi da dacin rai Saraki na da wani tabo ne da ya mayar da shi hakan wanda dole zan faWa miki Afeefah... Ina so in fada miki ba don tonon asiri ba, sai don ya zama dole ki sani kan ki yanke shawarar za ki aure shi ko ba za ki aure shi ba? Ba zan miki dole ba wlh kuma ba na so ki dube ni a yayin yanke hukunci ki yanke duk abinda ke ranki ni me karSa ce don sai da na nemi zaSin Allah kan na tunkareki"

Shiru Mammi tayi idanunta sun rine sossai har suka tara hawayen da ya fara bin ™uncinta, Wacin maganan da zata faWa take ji har kan harshen ta maganan da bata taSa faWa da Bakinta ba bata taSa ambata ba sai a yau da ya zame mata dole, idanunta na kallon gefe ta furta

"Rayyan ba Wa na bane!!!"

Wani irin bugawa zuciyar Afeefah yayi da har sautin shi na fitowa fili ta zaro idanu gabaWaya tana kallon Mammi dake ta zubar hawaye

"Eh Afeefah ba ni na haife shi ba, hasali ma babu abin da ya haWa ni da shi na jini ko na kusa ko na nesa... Ni sunana Khadija ni haifafffiyar wannan gari ce ta Kaduna, mahaifina Alhj Isma'il mai rasuwa mutum ne mai tarin dukiya mai yawa a gaske kuma su biyu Allah ya ba wa iyayensu Wan uwanshi ma na da nashi arzikin don gada suka yi, mahaifina mutum ne da dukiyar shi bai taSa rufe mai ido ba, yana da kyauta tsantsa haka yana da taimako don haka ko da na zama ni kaWai 'yar shi yana da ´a´a dayawa da suke karkashin shi don lakabinshi ma shine Uban marayu da masu uba... Yaran da ya biyawa suka karatu basu kirguwa sai dai in baki zo wurinshi da kuka ba sai ya share miki hawaye, wannan dalili ya sa nima na taso da irin zuciyarshi Dukda rashin lafiyarmu don shi ma ciwon sugar ne ya kashe shi kaman yadda ya kashe baban shi, ™annunshi ma Uncle Musa haka yake don suna da nasaba mai kyau suna da ilimi boko da arabi.

Akan irin rayuwar da na tashi kenan har na kamallah jami'a ta ina da shekaru ashirin da Waya a duniya, wata rana ina driving na zo daidai wurin ba da hannu sai na hangi wani kyakyawan yaro da ba zai wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana'ar da yake yi kenan a wurin ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matu™ar haWe ko alamun dariya babu kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini, wannan yaro ™arami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da bai wuce a ce yana gaban mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi, sau™e glass din nayi muka haWa ido na sakar mishi murmushi
"Yaya sunanka?"
Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda idanu da ya tsura min yana kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na mi™a mishi kaman ba zai karSa ba sai ya karSa ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.

Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da shi haka na Wauki mota na koma inda na fara haWuwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman shi da ™afa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya haWa kai da gwiwa Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi da yanayin sumanshi na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na du™a na taSa shi ya Wago ya kalleni da idanunshi da suke a matu™ar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi da na sauran yara ba don idanunshi na nuna wasu al'amari da na kasa fahimta, maganan duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na mi™e na je wurin wani mai wankin mota a kusa da

Please Login or Register in order to submit comment