Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Aa ba kuka nake ba, Mami baxa ki xo ba?" Murmushi Mami tayi tace "In xo ina?" Heedayah tayi shiru ta kasa cewa komai, Mami tace "kar ki damu ki kwantar da hankalin ki in sha Allah xan xo" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Da gaske Mami?" Mami tace "Ehh" Shiru Heedayah tayi, Mami tace "Hope kina cin abinci dai?" Heedayah ta gyada kai tace "Ina ci" Mami tace "Toh maa sha Allah, Allah ya maki albarka my daughter" A hankali Heedayah tace "Ameen" Mami tace "Sai na kira anjima" Da sauri Heedayah tace "Ba kince xa ki xo ba?" Mami tace "Ohh haka, sai na xo" Daga haka Mami tayi mata sallama ta katse wayar tana murmushi, Mom Islam ta karba tana kallon Heedayah tace "Tashi mu je ki gaida su Abbanki, sun shigo yanxu" Heedayah bata ce komai ba, Mom Islam ta dau mayafinta snn ta kama hannunta suka bar dakin, tafiya ce sosai suka yi har xuwa inda su Abba suke, Abbanta ne da Abban Shuraim, Baffan Junaid da Abban Sudais, all with few frnds, Heedayah kanta na lullube ta nufi gun Abban Shuraim da ta hango ta durkusa amma ta kasa cewa komai, lkci daya hawaye ya shiga sauka idonta, murmushi yyi ya kai hannunsa kanta yace "Allah yyi maki albarka daughter" Cikin sanyin murya Heedayah ta gaishesa sannan ta gaishe da su Abbanta, Abban Shuraim na kallonta yace "Tashi ki je, Allah yayi maki albarka" mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ta tadda Mom Islam wani parlon tana jiranta, mom Islam ta kama hannunta suka koma bangarenta don can ne bbu mutane da yawa, Bedroom ta kai ta xauna gefen gado, Mom Islam tace "Kun yi magana da Khaleel din?" Girgixa kai Heedayah tayi, Mom Islam tace "Ina wayar ta ki?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, mom Islam ta karasa ta bude, Farida ce tsaye ta mika ma Mom Islam wayar tace "Ana ta kiranta Aunty" Mom Islam tace "Ohk, kar kiyi nisa Farida you will stay with her here" Farida tace "Toh" daga haka ta koma parlon ta xauna, Mom Islam ta dawo ta mika ma Heedayah wayarta, amsa tayi tana dubawa, taga missed call biyu na Khaleel, sai text message, bata shiga message din ba tayi dialing number Khaleel first, yana fara ringing ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne, murya can kasa tayi masa sallama, shi ma murya can kasan ya amsa yace "Ya kike?" A hankali tace "Alhmdllh and you?" Bai amsa ba yace "Where did you drop the phone?" Tace "Yana wajensu Farida, Ina dakin Aunt dina, she just brought it now" yace "Ohk hope kin ci abinci?" Jin yanda yake maganan a hankali tace "Are you okay?" Yace "Hopefully...." Shiru tayi, kafin tace "What's wrong?" Yace "I'm fine dear, you don't worry... Ban ga kwalliyar ki na safe ba" tace "Ba a turo min hotunan ba tukun" yace "Ohk" tace "Me kake yi yanxu?" A hankali yace "Just lying down" Kallon agogo dake nuna karfe sha daya tayi tace "Lying down har karfe sha daya?" Yace "Yea ynxu xan tashi" tace "Ohk, have u eaten?" Yace "Sure" a hankali tace "Ko dai baka da lafiya ne?" Yace "Ciwon kai nake yi, but I will be fine in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen, will call you later, xan shirya ynxu ana jirana" tace "But ka sha magani?" Yace "Yes, na sha magunguna na" murya can kasa tace "Toh sai anjima, Allah ya sauwake" yace "Alright dear, Ameen ngd" daga haka ya katse wayar, ta tsura ma screen din ido kafin ta shiga inbox dinta na msgs, ta fi minti biyu tana kallon message din da aka yi mata almost an hour ago kafin ta sauke idonta ta ajiye wayar, kwankwasa kofar dakin farida tayi ta shigo, tana kallon Heedayah tace "Ki taso mu je ki canxa kaya in ji Aunty" Ba musu Heedayah ta mike ta dau wayarta suka fita tare da Farida xuwa dakin da aka yi mata kwalliya, wani lace din da ya fi na daxu ta saka aka kara gyara mata fuskarta, aka yi mata hotuna snn suka fito. Karfe sha biyu Heedayah ta sauko parlon baki tare da Farida da Zainab, Junaid ne parlon da Sudais sai frnds dinsu hudu ko wannensu ya sa gezna fari kal, ta karasa a sanyaye ta gaishesu gaba daya, Junaid dai kallonta kawai yake yana murmushi yace "Aunty Amarya kin sha kyau" Sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa, Sudais ma dake tsokanarta taki yarda ta kallesa, tana son tambayar Junaid ina Khaleel ganin baya parlon amma ta rasa ta yaya, Farida dake gefenta ta kalla ta matsa dab da ita tace "How about ya Khaleel" Farida ta xaro ido tayi dariya, Heedayah ta riko hannunta da sauri murya can kasa tace "Noo, I am just asking" Farida na murmushi tana kallon Junaid tace "Yaya what of Big bro?" Junaid yace "He is outside, bai shigo ba" Farida tace "Me yasa bai shigo ba" Junaid yace "He prefer staying out" Heedayah dai bata ce komai ba, Sudais na kallon Farida yace "Good afternoon kawar amarya" Xaro ido Farida tayi ta kallesa da sauri tace "Ohh yi hakuri, Ina yini, kun xo lafiya??" yyi murmushi yace "Alhmdllh, ya taro?" Farida na murmushi ita ma tace "Alhmdllh" gaida sauran frnds din nasu Farida tayi sannan ta ja Heedayah suka bar parlon da Zainab, sai da suka hau stairs Heedayah tayi kasa da murya tace "Farida Ina son in ga Ya Khaleel" Farida tace "Ohk, let me ask a ina yake" daga haka ta koma ta tambayi Junaid, Junaid yace "A compound muka bar sa, call him on phone" Farida tace "Ohk" juyawa tayi ta koma sama, a bangaren Mom Islam ta tadda su Heedayah tace "Ya junaid yace yana waje, ko xa ki je ki samesa?" Heedayah tace "Xan iya xuwa?" Farida tace "Toh amma idan aka gan ki fa? I think it's not proper" a hankali Heedayah tace "Baxan bi inda akwai mutane ba" Farida tace "Toh shkkn, amma kar ki dade" mikewa Heedayah tayi ta yafa babban mayafinta ta fita dakin, ta inda bbu wanda xai lura da ita ta bi har ta fito daga gidan tana ta dube duben inda xata ga Khaleel....










Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....








Karkashin wani bishiya Heedayah ta hangosa xaune kan kujera a wani bangare na compound din, tun xuwanta wajen ya ganta shi ma, ya sakar mata murmushi bayan sun hada ido, sauke idonta tayi ta nufesa walking slowly, mikewa yyi yana kallonta har ta iso inda yake, ya buda mata hannunsa, kasa karasawa tayi da farko, can ta bi wajen da kallo sannan ta karasa kusa da shi gabanta na faduwa ya rungumeta jikinsa, lumshe idonta tayi kamshinsa ya cikata, ya daura bakinsa a kanta murya can kasa yace "You look beautiful wife" Bata iya tace masa komai ba, suna tsaye har bayan minti daya sannan ta dago kanta tana kallonsa tace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdllh am fine, where you worried?" Gyada masa kai tayi tace "But ur body is warm" yyi murmushi yace "Not like in the morning, I don't take my drugs the way I am suppose to, but naje asibiti I'm feeling much better now" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sauwake" yace "Ameen, amma kin yi lunch ko?" Ta turo baki tace "Kai abinci dai ko da yaushe" Yace "Eh mana, ke baki ganki ba kamar a huraki ki fadi" Murmushi tayi tace "Tohm na ci" a hankali ta xame jikinta daga nasa, yana kallonta daga sama har kasa yace "Kinyi kyau sosai, you look like a princess" Murmushi tayi tace "Kai ma ai kayi kyau" Yace "Noo ban kai ki ba" kallon kyakkyawan fuskarsa tayi, ya kashe mata ido ta sunkuyar da kanta da sauri tana murmushi tace "Ina son in koma ciki ynxu kar a neme ni" yana kallonta yace "Alright dear, in an hour time mu ma xa mu tafi mosque in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Ya kamo hannunta yace "I pray this will be the best for I and you, I pray it's for lifetime...." a hankali ta xame hannunta tace "Ameen" daga haka ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo, a wani d'an corridor da ta bi ta fito ta tadda Farida na tsaye tana ta jiranta, Farida ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ta tsoron kada Aunty ta xo tace kina ina, I don't know if it's proper da kika fita" Heedayah tace "But ai ban dade ba ko?" Farida na kallonta daga sama har kasa tace "Aa baki dade ba, turarensa ya sa maki?" Heedayah tace "Why do you ask?" Farida tace "Kamshin turaren naji kike yi" Heedayah tace "Aa ni bai sa min ba" Farida ta wara ido tace "Ko dai ko dai...." Heedayah ta turo baki ta bi ta gefenta ta bar wajen, Dariya Farida tayi tace "Mu je ki canxa kaya, Aunty tace you should keep changing after an hour" Heedayah bata ce mata komai ba ta ci gaba da tafiya Farida ta bi bayanta. Ana saukowa sallan juma'ah aka daura auren Aliyu Uthman da Fatima Ahmad a kan sadaki naira dubu dari biyu, daurin auren da ya samu halartar dumbin jama'ah daga garurruka daban daban har ma daga kasashen waje, kan kace me government house ya cika makil da bakin d'a suka xo taya murna da farin cikin wannan daurin aure.... Heedayah na xaune saman darduma tun bayan da ta idar da sllh, banda faduwa bbu abinda gabanta yake, ita kadai ce xaune dakin don Farida da su Zainab sun fita, ta kalli agogo dake nuna biyu saura, dai dai nan message ya shigo wayarta da ke ajiye gefen gado ta sa hannu a hankali ta dauko wayar tana dubawa, message din Khaleel ne ya shigo wayar, sosai ta ji gabanta ya fadi bata kai ga bude message din ba aka bude kofa dakin, Farida suka shigo tare da Zainab da su Rabi'ah, da gudu Farida ta tafi ta rungumeta sosai tace "I am wishing you a happy married life Didi, Welcome to our family once again as an in-law...." Kasa ce mata komai Heedayah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta ta janye jikinta daga na Farida ta fashe da kuka sosai, Wata kawar Yakumbo ce ta shigo dakin ta saki wani guda da karfi tana kallon Heedayah, mikewa Heedayah tayi ta shiga bandaki ta kulle ta durkusa kasa ta rushe da wani kuka kamar warce aka sanar ma mutuwa. Sai da Mom Islam tayi da gaske da ita ta bude bandakin da ta sa ma makulli bayan kusan minti talatin, tausayinta ya sa Mom Islam ta kasa yi mata fadan da tayi niyya, Banda kallonta bbu abinda take, don har idonta ya tashi, Mom Islam ta jawota jikinta cikin kwantar da murya tace "Haba Heedayah, Why are you behaving this way?" Kasa ce mata komai Heedayah tayi hawaye masu xafi na sauka idonta, Mom Islam ta kama hannunta suka fita daga dakin xuwa nata bangaren ta xaunar da ita tana kallonta tace "Ain't you happy?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "I am" Mom Islam tace "To ki daina kukan nan, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya da kwanciyar hankali ma har abada, kowa ma haka yaji yanda kike ji yanxu" Gyada mata kai kawai Heedayah tayi tana goge idonta, Mom Islam ta mika mata wayarta tace "Ana ta kiran ki" amsan wayar Heedayah tayi a hankali, Mom Islam ta mike ta fita dakin, Miss calls din Khaleel ta gani, ta fara shiga inbox dinta ganin msg hudu, na Sudais, Junaid, da Shuraim ne all wishing her a happy and peaceful married life, sai na Khaleel da ta bude a karshe tana duba content din nasa, lumshe ido tayi a xuciyarta ta amsa addu'o'insa da Ameen, daga haka ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon stepmom dinta. Bayan la'asar Heedayah ta fito main parlorn su cikin wani ubansun gown da ya haskata sosai, da kyar Mom Islam ta lallabata ta fito din bayan an gama shiryata don yin hotuna, wajensu Abbanta aka fara kai ta suka yi hotuna, daga nan sister din Mom Islam ta dawo da ita bangaren Amminta suka yi hoto da Ammi da frnds dinta na nisa da na kusa da suka xo, daga nan matar ta kai ta gunsu kaka ayi hoto, duk Heedayah bata da walwala aka yi hotunan suka fito, Farida ce ta kai ta parlon baki don yin hoto da su Junaid, su kadai ne a parlon da abokansu su ma. Walima aka yi a gidan na kece raini har yamma, kafin Magrib kuma aka fara shirye shiryen tafiya da amarya Kaduna a private jet, Heedayah ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, kai kace tafiya xa ayi da ita gun yankan kai, sai da kukan ma ta kasa yi, Abban Shuraim da Abbanta da step brothers dinsa suka yi mata nasiha sosai, daga nan aka kai ta gun su Yakumbo, Yakumbo na kallonta tace "Ni dai da aka min aure idan ba mantawa nayi ba bbu wanda yyi min wata nasiha, a lkcn ma duniya bata waye ba balle ynxu da duniya ta waye, ke dai kawai kiyi ta kanki a gidan mijin ki...." Mom Islam ta hade rai ta daga Heedayah ta kai ta gun kaka, kaka tace "Tohh, duk da dai mu dai ba haka muka so ba, amma Allah dai ya baku xaman lafiya, sai mun hadu a Kadunan, ba dai gidan Rakiya xa a kai ki ba, ku je kawai sae mun xo" Dagata Mom Islam tayi ta kai ta gun sauran tsofaffin parlon duk suka mata nasiha sosai, snn Mom Islam ta fita da ita daga dakin, Bangaren Ammi ta kai ta, Ammi na kallon Heedayah cikin sanyin murya tace "Allah ya baku xaman lafiya, that's all I will say, idan kin je Kaduna nasan Maminki xata karasa maki sauran...." Nan sauran frnds din Ammi suka mata nasihar su ma snn mom Islam ta fita da ita daga parlon, kawayen Ammi biyu da Kanwar Ammi da kanwar Abbanta sai Farida suka shiga jet din xuwa Kaduna..... Ana kiraye kirayen Magrib motoci kusan shidda suka yi parking kofar gidan Mami. Har aka shigar da Heedayah gidan tana rungume jikin Hajiya Fa'iza, Mami ta sauko daga tana kallonta tana murmushi, Hajiya Fa'iza ta kai bakinta kunnen Heedayah tace "Ki bude fuskar ki tafi ki gaida Ummin ki" a hankali Heedayah ta bude mayafinta ganin Mami ta karasa da sauri ta rungumeta sosai, cikin rawar murya tace "Mami..." Mami tace "To kukan ya isa haka, stop it now" Gyada mata kai kawai Heedayah ke yi wasu sabbin hawayen na bin kuncinta, Mami ta shiga yi ma bakin da suka shisshigo sannu da xuwa da fara'arta, sai da duk suka xaxxauna snn ta bar su da frnds dinta da su Dinar ta wuce sama da Heedayah, bedroom dinta ta kai ta ta kulle kofar ta xaunar da ita gefen gado ta cire mayafin kanta tana kallonta tace "Ba nace ki daina kukan ba" a hankali tace "Na daina Mami" Mami tace "Toh shiga bathroom kiyi alwala ki fito" Ba musu Heedayah ta fara cire jewelries din hannunta ta mike ta nufi bandakin, Mami ta ajiye mata darduma da hijab a kai snn ta fita dakin don xuwa ta sake gaisawa da bakin. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh tayi jigum tana tunanin wai yanxu ita matar Khaleel ce, a hankali ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka Mami ta shigo dakin da warmer din abinci da plate da spoon ta ajiye gefenta, cikin sanyin murya tace "Ina yini Mami" Mami ta xauna tace "Lafiya lau daughter, ki debi abinci ki ci" Kallon abincin kawai Heedayah take bata ce komai ba, aka bude dakin frnds din Mami suka shigo gaba daya suna guda, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mami dai ta fita dakin, Dinar na tsaye bakin kofa sai kallon Heedayah take tana murmushi, sai da kawayen Mami suka fita dakin snn ta karaso ta xauna gefen gadon still smiling tace "Sannu Aunty Amarya, ya hanya...." Heedayah ta kasa kallonta a hankali tace "Ina yini Maman Fadil" Dinar tace "Lafiya lau dear, ya hanya" Heedayah tace "Alhmdllh" Dinar ta sauka ta dibar mata abincin da kanta snn ta kawo mata ruwa ta fita dakin, daren ranan a dakin Mami Heedayah ta kwana tare da Mamin, bacci me dadi tayi sosai, with full rest of mind don ta fi kwana uku bata baccin kirki, da asuba sai da Mami ta tasheta sllh, kafin karfe tara na safe kuma wa enda suka kawota duk sun juya xuwa kano duk da Mami bata so hakan ba, gidan ya rage daga few frnds da colleagues din Mami, su Dinar, sai Hajiya Zuwaira da kanwarta da Stepmum din Sudais. Bayan azahar Heedayah ta idar da sllh ta mike kenan tana linke darduman aka bude kofar dakin, daga kai tayi tace "Mami ur phone is...." Makalewa sauran maganan yyi ta sunkuyar da kanta da sauri ganin wanda ya shigo, sanye yake da kananun kaya, ya kulle kofar ya jingina da kofar yana kallonta, juya masa baya tayi gabanta na faduwa, ya taka ya isa dab da ita murya can kasa yace "Heedayah" kasa juyowa tayi, ya xaga a hankali xuwa gabanta ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa, bude kofar dakin aka yi ya daga kai da sauri, Dinar ce ta shigo ganinsa ta buda ido tace "Lahh ashe ka tashi Yaya, Mami ta tambayeni nace baka tashi ba" Yace "Na tashi" Tace "Toh ka ci abincin kuwa??" Yace "Yea" tace "Maganin fa?" Yace "Na sha" Yana fadin haka ya nufi kofa yace "Ina Fadil?" Tace "Yana can gun Amira wllh naga yana damunka ne shi sa na ki barinsa ya shiga dakin" Khaleel yyi murmushi yace "Ae da kin bar sa" Daga haka ya fita dakin, Dinar na murmushi tana kallon Heedayah tace "Aunty Amarya wai xa ku gaisa da baki downstairs ki sakko" Heedayah bata kalleta ba ta dau mayafinta ta rufe kanta da shi, Dinar ta karaso ta kama hannunta suka fita xuwa downstairs. Har dare Heedayah na dakin Mami don Mami bata barta taje nasu dakin ba, ta gama shirin bacci xata kwanta Mami tace "Heedayah" juyowa tayi tana kallonta, Mami tace "Kije ku gaisa da Khaleel kafin ki kwanta, kiyi masa ya jiki yanxu ki dawo" Tana kallon Mami tace "Is he still sick?" Mami tace "No, He is fine now, but kije ki gaishesa" A hankali Heedayah ta dau Hijab dinta har kasa ta sa snn ta nufi kofa ta fita, dakinsa shi kadai ta tafi ta bude kofar a hankali hade da sallama, yana xaune daga shi sai singlet with 3 quarter yana danna laptop dinsa ya daga kai yana kallonta, sunkuyar da kai tayi taki yarda ta karasa cikin dakin ta gaishesa cikin sanyin murya tace "Ya jikin?" Kallonta kawai yake, ita dai ta ki yarda su hada ido, ya sauke kafafuwansa daga saman gadon ya mike ya nufota, juyawa tayi da sauri xata fita yace "Heedayah" ta kasa bude kofar kamar yanda tayi niyya, ya karasa dab da ita ya juyota yana kallonta, sauke idonta kasa tayi cikin sanyin murya yace "Mami tace kar in dade" Ya kai lips dinsa hancinta murya can kasa yace "I will love you till my last breath" ta kasa ce masa komai ta rufe idonta, jawota jikinsa yyi ya rungumeta yana jin yanda kirjinta ke bugawa, a hankali tace "Mami... she is waiting for me" ya dago kanta yana kallon fuskarta yace "Tsorona kike ji?" Da sauri ta bude idonta tace "Aa, Mami ce ke jirana" murmushi yyi yace "Hope baxata jira ki ba gobe?" Ita dai bata ce masa komai ba ya bude kofar yana mata lallausan murmushi yace "Good night love" juyawa tayi ta fita ya kulle kofar, wani ajiyar xuciya ta sauke ta koma dakin Mami da sauri washegari da yamma aka fara shirye shiryen tafiya da Heedayah gidan Khaleel wanda kanin mahaifinsa ya mallaka masa halak malak, tun ana saura kwana biyar biki aka yi furnishing gidan daga kano, babban duplex ne sosai, both sama da kasa duk an xuba ma Heedayah kaya na gani na fada, hankalin Heedayah bai gama tashi ba sai da taji Mami na yi mata nasiha wai xa a tafi da ita gidanta, duk xaton ta a gidan xata xauna da su Mami kamar ko da yaushe, nan ta rushe da kukan tashin hankali tace "Don Allah Mami a bar ni a gidan nan in dinga ganin ki kar a kai ni wani waje" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Muna tare daughter babu me raba mu...." Da kyar aka fitar da Heedayah daga gidan tana kukan rabuwa da Maminta, kawayen Mami biyu, da sisters dinta da su Dinar da mum din Sudais da step mum dinsa da Hajiya Zuwaira suka rakata gidanta with few others, Heedayah ta makale ma Farida a makeken bedroom dinta da aka ajiyeta ciki bayan ta kara tabbatar da tafiya duk xa su yi su bar ta ita kadai, dole aka bar Farida gidan duk aka watse, Heedayah sai bin dakin take da kallo gaba daya a tsorace take, Farida dake gefenta tana ta danne dariyarta tace "Ko mu je kiga gidan naki ne da kyau?" Hararanta Heedayah tayi tana goge idonta, Farida ta fashe da dariya tace "Kilan abinda ma kike ma tsoro ba haka bane" Heedayah tace "Me nake ma tsoro?" Farida tayi dariya tace "Toh na san maki??" Heedayah bata kuma ce mata komai ba jikinta yyi sanyi. sai kusan Magrib Khaleel da Junaid suka shigo compound din gidan, Junaid ba yarda ya shiga ciki ba yana kallon yayansa yace "Sai na shigo gobe, kace da Farida ta fito mu tafi" Khaleel yace "Toh Allah ya kai mu, I tot Farida will spend the night here?" Junaid yace "Aunty tace mu taho da ita" Khaleel ya nufi kofa ya shiga gidan. Knocking kofar bedroom din Heedayah yayi sannan ya bude, Heedayah ta rufe fuskarta da sauri, mikewa Farida tayi tana murmushi tace "Sannu da shigowa big bro, ya junaid din yana waje?" Yace "Yes...." Farida bata ce ma Heedayah komai ba ta nufi kofa ta bi gefen yayan nata a hankali ta fita tana murmushi, da sauri ta sauka downstairs kafin Heedayah ta lura, Khaleel ya jingina da kofar yana kallonta, a hankali ta bude fuskarta jin ta daina jin muryar Farida a dakin, da sauri ta mike tana bin dakin da kallo tace "Yaya ina Farida?" Kallonta kawai yake, ta ji hankalinta ya tashi, kofar ta nufa da sauri xata bi gefensa ta fita ya riko hannunta yace "Farida ta wuce" cikin sanyin murya tace "Shi ne bata gaya min xata wuce ba?" Ya jawota jikinsa yace "Gobe xata dawo" Ita dai bata ce komai ba, yana rike da ita suka koma cikin dakin ya xaunar da ita gefen gadon yana kallonta yace "Ki je kiyi alwala ina xuwa yanxu" Bata ce komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, bayan few minutes ta mike a hankali ta bude press dinta tana kallon kayan baccin da Farida ta ajiye mata ta dauke kanta, ta dau wani dogon rigan har kasa shi ma na baccin ta ciro hijab dinta snn ta rufe press din, kasancewar tayi wanka a gida kafin a kawota, cire atamfar jikinta tayi ta linke ta ajiye snn ta sa doguwar rigar ta shiga bandaki tayi alwala ta fito, hijab dinta ta sa ta xauna gefen gadon tayi jigum, can ta kwanta ta rufe har kanta da duvet, tana jin Khaleel ya shigo dakin, ya karasa inda take yace "We have to pray Heedayah" kin ce masa komai tayi ya bude duvet din, ta bude idonta a hankali tace "Ni nayi sllh" yace "Ehh na sani, tashi kije kiyi

Please Login or Register in order to submit comment