Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya juya yana kallon kaka yace "Na hada wani abun ne da ita? Kin ga ki daina min shisshigi a lamarina, bbu ruwanki da harkata, dole aka ce maki sae na amsa gaisuwarta ko ina da wani alaka da ita ne??" Bai jira cewarta ba ya mike ya fice daga dakin, kaka ta nemi kujera ta xauna a hankali tace "Ikon Allah, Amadu dai ya ja mana bala'i, muna xaman xaman mu yace xai kai sa Soja gashi tun ba a je ko ina ba ya fara kilewa.... To banda bala'i yaushe har Shureen ya fara magana da har xae xageni ya fita, dama haka sojojin suke bani da labari??" Washegari Monday da safe Mami ta koma bakin aikinta, Farida ta gama duk abinda xa su yi da Heedayah a bangaren Mami suka fito, Heedayah na sanye da wando da riga sai hula da ke kanta, sosai kayan suka yi mata kyau kamar yar turawa ga gashinta da ta baxo ta cikin hular, Farida kuma Abaya ta saka da veil dinsa, ta kulle bangaren Mami suka wuce gaida Kaka a dakinta, Kaka tace "To ita Deedayah me yasa Rakiya bata siya mata irin wnn kayan na jikin ki ba, ko don ba ita ta haifeta ba sai tayi ta sa mata kayan anna??" Farida dai bata ce komai ba, haka ma Heedayah, Farida ta mike tace "Kaka xa muje tsakar gida mu dawo" Daga haka Farida ta kama hannun Heedayah suka fita dakin, Kaka ta kyabe baki tace "Wnn faridan ta fiye rawan kai da iyayi kamar dai uwarta, ba don wannan halin nata ba dai Shureen xai aureta, banda dai kowa na son inda nasa xai huta ai wnn rawan kan nata ya fi karfin Shureen" Garden din cikin gidan Farida suka tafi da Heedayah, suka xauna kan kujeran dake garden din Farida na kallonta tace "Toh ko na nuna maki yanda ake operating wayar ai ba siya maki Mami xata yi ba, nima fa Baffanmu ne ya siya min, kuma da kyar ta bar ni na rike..." Heedayah ta langwabar da kai tace "Ae Yaya xan ce ya siya min ko Yaya Sudais" Farida tayi dariya tace "Toh shkkn, nasan Yaya xai iya siya maki, shi kinsan babu ruwansa" Tsakaninta da Allah ta shiga nuna ma Heedayah ynda ake amfani da waya da abubuwan dake cikin waya tun daga lock button, Heedayah ta maida hankali kai kace karatu take dauka... Tun da suka shigo garden din Shuraim dake xaune sama yana karatu a laptop dinsa ya mayar da laptop din gefe yake kallonsu, su kam ko lura da shi basu yi ba, can ya mike ya bar wajen, Farida ce ta fara hangosa yana tahowa toward them bayan ya sakko downstairs, tayi kasa da murya tace "Wannan Yaya Shuraim din is coming" Sosai Heedayah ta rikice a gun, ta dinga cewa "Farida tashi mu tafi yana yi ma mutane duka wllh, ki tashi mu tafi...." Farida ta hade rai tace "Toh ba sai ya doke mu ba" Har dai ya iso kansu, yana kallon Farida yace "Me ku ke yi a nan?" Farida ta d'an kallesa tace "kawai labarin mu muke" yace "You are showing her how to operate phone right?" Tace "Yea.... sannan muna hiran makaranta" ya mika mata hannu yace "Bani wayar" Mayar da wayar Farida tayi bayanta ta hade rai tace "As in how?" Yace "Baxa ki bani ba" A takaice tace "Gaskiya...." Mikewa Heedayah tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba xata bar wajen yace "Kina kara step daya sai na 6allaki" Tsayawa tayi, tayi narai narai da ido, sai dai taki yarda ta juyo ta kallesa, Farida ta mike xata bar wajen ya riketa ya kwace wayar a hannunta, tsaye tayi tana kallonsa tana huci, yace "Daga yau.... Ina nufin daga wannan moment din ko by mistake kika sake xaunar da ita kina nuna mata waya sai kin sha mamaki a gidan nan" Farida tace "Toh ai wayana na nuna mata ai ko? Kuma ni ka bani wayata...." Ya mata wani kallo ce "Ki kwata mana" Kallon Heedayah yyi ya kara daure fuska yace "Uban me xa kiyi da waya da kika xauna tana nuna maki ynda ake amfani da shi" Heedayah ta girgixa kai bata ce komai ba, strictly yace "Juyo Ina maka maki magana" A hankali ta juyo tana facing dinsa idonta har ya kawo ruwa, ya kara shan kunu yace "Ke kika ce ta nuna maki waya ko?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, yace "Toh na sake ganin ki xaune ana nuna maki waya sai na xane ki a gidan nan, daina kallona" Ta sauke idonta kasa hawayen ciki ya xubo, a fusace Farida ta bar wajen kamar xata tashi sama, Shuraim ya bi ta da wani kallo har tayi corner, yana kallon Heedayah yace "Start going" juyawa tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya har suka shiga cikin parlor sannan ta juya suka hada ido, daure fuska yyi ta nufi dakin Kaka tana goge idonta, Kaka dake ta sauraron Farida ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Toh, a gaskiya ni dai baxan iya tunkaran Shureen ba ynxu don ya xama abinda ya xama, rashin kunya yake ma kowa gadan gadan, Kuma ni ban san ko har sojojin sun basa bindiga ba inje in ja ma kai na, yo in ja ma kaina mana, yanxu sai ki tashi mu tafi bangaren uwarsa nasan tana can tana baccin asara kin san me xaman banxa, nasan ita idan tayi masa magana xai ji" Heedayah na shigowa dakin kaka ta fashe da kuka ta fada kan gado har da Shessheka, kaka ta mike da sauri tace "Lafiya, me ya faru, ni dai na shiga uku, kukan me kike" Kuka kawai Heedayah take, Farida tace "Shine ya doketa kila" Kaka tace "Ya doke ki???" Da sauri Heedayah ta mike xaune tace "Aa bai dokeni ba fa" Kaka tace "To kukan me kike" ta girgixa mata kai kawai, Kaka tace "Oho ni ban iya wahala, tashi mu je gun uwar tasa Farida, dabanci kawai Shureen ke ji a gidan nan kwanan nan" Tare Farida suka fita da kaka xuwa bangaren Mumy, Khadijah na xaune parlor tana kallo, kaka tace "Gantalalliya abinda kika iya kenan, Ina Rabi'ar?" Khadijah ta wani daure fuska tace "Ta tafi gidan Aunty Asma'u" Kaka tace "Ta tafi gidan Asma'u? Shine bata sallameni ba? Wai me yasa Amadu ke min haka ne a gidan nan kamar ba uwarsa ba, ynxu fa a kullum da kyar ku ke shigo min bangarena sau daya, Mata duk ta kanainaye ku bata son ku ra6i kowa na gidan nan kullum kuna kunshe a daki?? Toh bari ya dawo shi Amadun" Mumy na daki duk tana jin kaka, kafin ta karasa cikin dakin tayi saurin fitowa, Kaka na ganinta tace "To Shureen ne ya kwace wayar Farida, kuma dubu dari biyu aka ce an siya wayar, to siyarwa yake da niyyar xuwa yyi shine ban gane ba" Mumy tace "Ni kuma ina naga Shuraim da safen nan kaka?" Kaka tace "Aa ba ruwana ki fita ki nemosa duk inda yake ya maido ma yar mutane wayarta kafin ya tafi chechenia da shi a shiga uku" Mumy ta kalli Farida daga sama har kasa, Farida tace "Ina kwana" a walakance Mumy tace "Lafiya" Kaka tace "Yar gidan Rakiya ce fa, daga makarantar kwana suka yi hutu ta xo mana shine har xai saka mata ido a gidan ya kwace mata waya to ina ruwansa da ita idan ba neman fitina ba, daga ance an samar masa Soja sai ya xame mana ibilisu a gida??" Mumy tana wani kyabe baki tace "Toh ni ban san inda Shuraim yyi ba tun asuba da ya shigo ya gaisheni ban sake ganinsa ba wllh" kaka tace "Toh ai nemosa nace xa kiyi idan ba haka ba wllh sai in ja ta mu tafi gidan yan sanda su san abinda ake ciki, muka san ko sojojin kwacen wayar mutane suka sa shi" Tana fadin haka ta kama hannun Farida suka fita, Mumy ta bi su da wani irin kallo. Har Mami ta dawo da yamma Shuraim bai ba Farida wayarta ba, barin gidan ma yayi gaba daya, Mami ta tabe baki bayan ta gama sauraron farida tace "To uban wa xa kiyi ma kuka?" Farida ta kara rushewa da kuka tace "Wllh Mami bbu abinda muka yi masa kawai ya amshe wayata" Mami tace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Cikin kuka tace "Babu komai wllh" Mami tace "Toh ai shkkn, dama nima na gaji da shegen wayar da kike rikewa" Tana fadin haka ta shiga daki, Heedayah dai na xaune parlon tayi shiru, can ta mike ta isa gun Farida tace "I am sorry I caused you all this Farida, da bance ki nuna min ba baxai amsa ba" Farida tace "Ai wllh sai ya bani wayata, you caused me nothing" Kaka ce xaune parlon Abba da Farida, Heedayah ma na xaune kusa da kaka, Abba yyi shiru yana sauraron kaka, kaka tace "Toh a gaskiya bbu ruwana kar ya ja mana fitina muna xaman xaman mu, a nemo sa duk inda ya shiga ya ba yar mutane wayarta" Abba na kallon farida yace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Ta girgixa kai a hankali tace "Babu abinda nake yi Abba, ni da Heedayah ce ma a xaune lkcn" Kaka tace "To me xata yi da wayar banda karatu kaji ka da wata magana, bbu abinda suke yi vanda karatu" Abba yace "Toh shkkn xan nemi Shuraim din" mikewa kaka tayi ta nufi kofa tace "Ku taso mu je, shi da ya sa shi a sojan su karata can" Mikewa Farida da Heedayah suka yi suka bi bayan kaka. Shuraim na tsaye dakin Mumy dake ta masa fada kamar xata ari baki, shi dai bai ce mata komai ba, tace "Banda ka haifi yaro baka haifi halinsa ba ina ruwanka da lamarin su a gidan nan? Ka hada wani abu ne da yarinyar da xaka amshe mata waya da sunan discipline? Ina ruwanka da ita nace" ya shafa kansa still bai ce komai ba, tace "Toh wllh ka kiyayeni a gidan nan, banda baka kishina kai ko kallon yar nan xaka yi balle ka amshi wayarta Aliyu" Wayarsa dake hannunsa ne ya fara ring, Mumy tayi shiru tana kallonsa, yace "Abba na kirana" Mumy tace "Wannan damuwarka ce, ni dai idan har baxaka fita hanyar makiyana a gidan nan ba to wllh sai dai ka canxa wata uwar ba ni ba" juyawa yayi ya nufi kofa ya fita, a main parlor ya tadda kaka tana dube dube kamar munafuka, tana ganinsa ta hade rai ta hau kakkabe kujerun parlon tana cewa "Mata duk kazamai kawai" yayi wucewarsa bangaren Abba, tana ganin haka ta nufi dakinsa da sauri ta shiga tana kalle kalle, saman madubi ta ga wayoyi har biyu a ajiye da dubu biyar ta kwashe duka ta fice. Shuraim yace "Abba Heedayah take koya ma ynda ake operating waya shi yasa na amshe" Abba yyi shiru yana kallonsa haka ma Mami dake parlon tana xuba ma Abba abinci, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, can Abba yace "A ina ka gan su?" Shuraim yace "Can baya" Abba yace "That's wrong, and you did the right thing collecting the phone, ka rike wayar wajen ka nan da kwana biyu sai ka bata" Shuraim ya dago kansa yace "Ita ma bai kamata ta rike waya ynxu ba, she still in Jss2 I think" Abba yace "Haka ne but assuming a gidan nan take ni baxan bari ta rike waya ba, but tunda ba a nan take ba we have no say, ka maida mata wayarta after two days..." Shuraim yace "Idan xata koma makaranta xan bata amma ba ynxu ba" Abba ya kalli Mami da bata kalli Inda suke ba yace "Ur opinion Rahinah" Mami ta kallesa tace "Duk ynda kayi dai dai ne barrister" Abba yace "Alright, ka bar wayan gun ka Shuraim" Shuraim yace "Toh shkkn" daga haka ya mike ya fita parlon. Karfe tara da rabi kaka na xaune dakinta ta daura kafa daya kan daya ta gama cinye kazar da Junaid ya kawo mata tana sakace hakori Shuraim ya shigo, tana ganinsa ta ci gaba da sakace sakacenta tana lumshe ido, ya bi dakin da kallo sannan ya juya ya fita, bangaren Mami ya nufa ya bude parlon ya shiga, bbu kowa parlon amma yana jin muryarsu a daki, karasawa yyi bedroom din ya bude kofar, Xaune suke kan gado suna kallo a laptop din Farida, Heedayah na sanye da yar rigar bacci iya cinya haka ma Farida, Farida ta xaro ido, da sauri ta rufe jikinta da Pillow tana kallonsa, Heedayah ta sauka saman gadon da gudu ta shige bandaki ta rufe, yana kallon Farida yace "Bani wayar da kika shiga dakina kika dauka" Ta xaro ido tace "Ni?? I didn't take any phone wllh, tun daxu muna kallo a nan ban fita ba" ya fi minti daya yana kallonta sannan ya juya fice daga dakin, ya koma dakin kaka, kaka ta kallesa tace "Sojojin ne suka baka pareti da daddaren nan, naga ka shigo daxu baka ce min komai ba, gashi ka sake dawowa" Yace "Ina wayoyin da kika dauka a dakina?" Kaka ta mike tsaye ta wani xaro ido tace "Wayoyi kuma?" Yace "Ehh" Ta nemi waje ta xauna har ta fara salati sai kuma ta sakar masa kuka tace "Tunda uwata ta haifeni bbu wanda ya ta6a tsareni yana tuhumata a kan sata, satar ma ta waya, Shureen in rasa abinda xan sata a gidan nan sai waya? Ashe ma gantalalliyar barauniya ce ni, in saci motocin Amadu in gudu mana idan haka ne, Amma sai ka shigo min tsakar dare kace Ina wayar da na sata??" Shuraim ya gyada kai ya juya ya fita dakin. Bai sake maganar wayar ba har gari ya waye, Farida na share ma Kaka dakinta, Heedayah na kwance saman gado tana kallo a laptop, kaka tace "Shiru Shureen bai sake shigowa nemo waya ba gashi har karfe goma ko dai ya hakura ne, ni dubu biyar din ma kasuwa xaku je min ku siyo min kayan ciki in narka uban farfesuna mu yi sati muna ci, kayan cikin dubu biyar ai xai cika wancan kwallan ko?" Farida ta juya tana kallon katon abinda kaka ke nuna masu, kaka tace "Har yawuna ya tsinke maxa gama sharan ku tafi da wnn mara amfanin ku siyo min kayan cikin" Farida tayi kasa da murya tace "Ke dai kar kice masa komai a kan wayar ki ci gaba da boyewa" Kaka tace "Toh da fa, ai ni tasa wayar ma da kyar idan ba chechenia xa ku rakani ba in siyar da 'yar banxa in siyo kan saniya inyi farfesuna" Farida ta fashe da dariya har da kyakyatawa, murya can kasa tace "Xan raka ki wllh, gashi naga shi ma IPhone din ne har ya fi nawa" Kaka tace "Toh ko in shirya yanxu?" Farida tace "Shirya" mikewa kaka tayi xata fiddo da sabon kayanta, Ganin cup da Heedayah ta sha shayi ta kalli Heedayah dake kwance tace "Kai ni dai wnn yarinya ta isheni wllh, kwata kwata ba a morarta, son jikinta har tsoro yake bani ni dai, to Amadu kike jira ya dauke maki kopin nan ko Rakiya??" Heedayah ta sakko saman gadon ta dau cup din ta nufi kofa kaka ta bi ta da harara tace "Toh meye ma amfanin bude idon da Amadu ya kai ki aka yi idan ba asaran kudi ba" Heedayah na fita dakin ta wuce kitchen, Khadijah dake xaune dining ta bi ta da harara, ita dai ko kallonta bata yi ba, ta bude kofar kitchen din ta shiga, ta ajiye cup din a sink kenan ta ga Shuraim tsaye kitchen din yana hada shayi, sunkuyar da kanta tayi xata fita, yace "Zo nan" kin tsayawa tayi ta ruga da gudu ya kamata kafin ta isa kofa, kuka ta sakar masa a tsorace tace "Ni ban yi komai ba wlh, kaka ce tace in kawo cup din kitchen" leka parlor yyi ganin Khadijah ya rufe kofar kitchen din, har wani rawa jikinta yake yi sbda tsoro, ya jinginar da ita da kofa yace "Wa ya shiga dakina ya dau waya?" Ta bude hannu da sauri tace "Nima ban sani ba, bani bace wllh" kalle kallen kitchen din ya fara yi taga ya kallo inda muciya yake, xaro ido tayi ta rungumesa a rikice tace "Wllh Kaka ce ta dauka ta boye a dakinta, a cikin akwatinta ta boye" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yana kallonta duk da ta boye fuskarta jikinsa, a hankali cikin rawar murya tace "Yanxu xa su je su siyar da wayan da Farida"






Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Bude kofar Shuraim yyi bata jira yace ta fita ba ta sakesa ta fice da sauri... Dakin kaka ta koma, kaka tace "Me ya tsayar da ke kitchen din, ko wanke wanke kika yi?" Heedayah ta girgixa mata kai ta xauna gefen gado, gaba daya a tsorace take har lkcn, kaka ta gama saka sabon kayanta na xuwa chechenia tace "Nima dai da neman magana nake, wata Deedaya ce xata yi wanke wanke kamar an tsine mata Allah na tuba" Farida ta gama tattara dakin kaka tace "Ajiye masu tsintsiyar da makwashin sharan a nan bakin kofa mai aiki xa ta kwashe ki shirya mu wuce, daga checheniar dama sai mu biya bakin dogo bbu irin k'an san da basu siyarwa sae mu yi ciniki, ita wannan Deedayar dama ta xauna gida kar taje tana mana lagwai lagwai a kasuwa in shiga uku" Farida tayi yanda Kaka tace sannan ta dau mayafinta ta yafa, duk ta kagu su tafi siyar da wayar Shuraim, dama tuni ta amshi nata ta kai dakin Maminta ta boye, kaka na bude akwatinta ta ciro wayar kenan Shuraim ya bude kofar dakin ya shigo, da sauri ta boye wayar bayan jakan hannunta na rawa ta daga jakar ta mike tsaye, Kai kana ganinta kaga rashin gaskiya karara, cikin rawan baki tana kallonsa tace "Ha'an... yau ma baka tafi Zarian ba? Sannan yaushe xa a fara kwasan sojojin ne" Yace "Ban tafi ba, Ina kwana?" Tace "Lafiya lau, ynxu na shirya nace wannan yarinya Farida ta raka ni gidan Ta sallah kwana biyu ban je ba ita ma bata xo ba, gashi ka shigo ni kuma xan fita" Yace "Ohk, ko in ajiye ki?" Da sauri tace "Aa ba ruwana da ba mutane wahala ga dai adaidaita ta ko ina, kayi tafiyar ka kawai kar in wahal da kai" Farida dai ko kallon Inda yake bata yi ba ta bi gefensa ta fita dakin, Heedayah tuni ta kwanta kan gado ta rufe idonta, kaka tace "Toh mu je xan kulle dakina ne Shureen, kema Deedayah ki fita kije gun Rakiya ki kwanta baxan iya barin dakina a bude ba" Shuraim ya karasa Inda take tace "Ina kuma xaka kana jin ina ce maka xan fita??" Bai saurareta ba ya isa gun akwatin ya duka ya dau wayarsa da yake hangowa bayan akwatin ya fice daga dakin, kaka ta kasa kwakkwaran motsi inda take tsaye, can dai tace "Toh Allah ya isa" sai kuma ta xauna gefen gado ta goge xufan da ya karyo mata a goshi cikin rawar murya tace "Allah dai ya isa" A cikin satin nan Abba ya ba Mami kudi don yi ma Heedayah siyayyar da ya kamata na xuwa boarding, bbu abinda Mami bata siya mata ba har da nata karin, duk dakin kaka ake ajiye kayan gudun fitinarta, ranan Friday karfe uku saura Heedayah na xaune Main parlor tare da Farida dake karatun wani literature dinsu, Heedayah kuma tun safe take ta rubutu a exercise book kamar yanda Mami ta umarce don har sannan writing dinta isn't good duk da tana kokari, Salima da Rabi'ah kuma na can gun dinning, Rabi'ah na mata tsifan uban attachment din kanta, sbda lalacewa kuma a kan dinning, Bude kofar parlon aka yi Sudais ya shigo da sallama, daga Heedayah har Farida suka dinga kallonsa har ya karaso parlon, sanye yake da gezner fari kal, mikewa Heedayah tayi ta sakar masa cool smile tace "Ya Sudais" Ya buda mata manyan idanuwansa a hankali yace "Yes Cutie" karasawa tayi kusa da shi ta rungume sa tace "I missed you" Farida dai kallonsu kawai take, haka Salima da ta juya kanta tana kallon ikon Allah, Sudais ya maida Heedayah gefensa yana kallon Farida yace "Hi" ta d'an yi murmushi tace "Hello, ina yini" yace "Lafiya lau, Farida right" tace "Sure" yace "Ya hutu?" Tace "Alhmdllh" ta gefen ido Heedayah ta bi Shuraim da ya shigo da kallo, direct dakinsa xai wuce ganin Salima da Rabi'ah a dinning ya tsaya yace "Duk gidan nan ki rasa inda xa kiyi tsifa sae wajen cin abinci Salima" Ta kyabe baki sbda bata son fitina ta fara tattara gashin dokin nata, yau dai shima manyan kaya ne jikinsa, Sudais dama sau daya ya kalli direction din Salima shi ma sbda Rabi'ah da ta gaishe sa, ya amsa gaisuwarta, ya na kallon Heedayah yace "Kaka na dakinta?" Heedayah tace "Aa ta je anguwa" Ya d'an bude ido yace "Anguwa Kuma?" Tace "Ehh gidan frnd dinta tace xata tafi, Mami ce ta wuce da ita da safe" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya makaranta?" A hankali tace "I am scared ya sudais" yace "Noo don't be dear, you will like it in there, many of ur mates are there" Tace "Toh baxan kara ganin Mami da Abba ba?" Yace "No xaki dinga dawowa hutu ai, ba ga Farida tana dawowa hutu ba ita ma, tare xa ku je sannan ku dawo tare" a hankali Heedayah tace "Toh" Ya kalli Farida yace "Junaid na nan kuwa?" Farida tace "Yana Abuja, amma xai dawo Saturday" Sudais yace "Yes yace min xai je can, but two days ba mu yi waya ba" Shuraim na fitowa daki Sudais ya mike Heedayah ta xaro ido, murya can kasa tace "Ya Sudais wucewa xaka yi?" Ya mata murmushi yace "Yesss but xan dawo" tace "Me yasa ka daina xuwa?" Yace "Sbda bana nan Cutie" Tace "Toh har in tafi makaranta baxan ganka ba?" Yace "Aa ni xan kai ki makarantar ai" Ya ja dogon hancinta yace "Byee sai na dawo" Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo da sauri yace "Bye Farida" tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ya fita, Heedayah ta koma gun Farida ta xauna. Salima ce xaune dakin yayarta tana sauraron abinda take gaya mata, can dai ta tabe baki tace "Toh wai Yaya ke yanxu meye damuwarki, ita fa matar nan ba sanin kina yi take ba kullum ta fita da safe sai yamma take dawowa, ita kanta wnn makauniyar da ta ja maki komai yanxu makarantar kwana xa a kai ta aka ce to ba shkkn ba, a ina xaki dinga ganinta kina jin takaici kuma??" Mumy ta kunduma mata xagi tace "Dama ke kinsan ciwo na ne, ai damuwata ba taki bace, kin gwammace kiyi ta yawo gari gari..." Mikewa Salima tayi tace "Aa kar ki bata min rai Yaya, taya kike son in tafi in ajiye maki laya a dakinta bayan ba shiga dakin nata na saba yi ba, ba gwara ki ba wa ennan fitsararrun yaran naki ba da basa girmama mutane" Mumy tace "Shkkn ni kuma bani da sirri sai in bari yarana su ji wnn magana, ke ma don kina 'yar uwata ne shi yasa nake neman taimakon ki" Salima tace "Kai gaskiya Yaya Ina ga da kamar wuya..." Mumy tace "Haka xa kiyi min Salima?" Salima ta wani murguda baki ta dauke kai, Mumy tace "Toh shkkn, tashi ki wuce, amma ai kina ma Salaha wanda ya fi haka" Salima tace "To Salaha ai biyana take yi ita" Mumy tace "Toh ni nawa xan baki?" Tana taunar cingam din bakinta tace "Dubu hamsin" Mumy ta mata wani

Please Login or Register in order to submit comment