Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bude front seat ta shiga, Heedayah ta xauna tare da kaka a baya, kaka tace "Wnn ai walakanci ne kawai daga ku yi wanka ku sa kaya sai ku bar mu a walakance a mota muna jiran ku, ko ita Rakiyar ce tace ku dade??" Ganin Mami kaka tayi shiru, Mami ta karaso gun motar tace "Toh Allah ya tsare kaka, mun gode" Kaka tace "Yauwa Rakiya Allah yayi maki albarka, in sha Allahu anjima xan dawo maki da su ni ma ban fiye son xama gidan mutane ba ai kin sani, ko da azahar ne Shureen sai ya dawo da mu gaba daya mu ajiye su ni kuma ya maida ni gidan Umaru tunda can nafi wayo" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye" daga haka ta koma ciki, Kaka tace "Toh Ameen dai" Junaid ya ja motar suka bar compound din don Mai gadi ya riga ya bude masu gate, Farida na kallonsa tace "Ina kwana Yaya?" Yace "Lafiya lau" Heedayah ma tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" kaka ta tabe baki tace "Abun bai yi ba oo, dama baku san yana gidan bane? Tun wayewar gari sai ynxu xaku ce Ina kwana" Junaid yace "Duk sun shiga daki kafin na dawo jiya, so basu san ina gidan ba ma" Kaka tace "Ni duk sai na ganka wani iri Junaidu, ko baka da lafiya ne" yace "Lafiyata qlau" kaka tace "Toh ku ma dai ku yi kuyi ku fiddo da matar nan dai a maku aure ku bar yawo a titi bakwa wancan gida bakwa wannan gida, auren shi ya fi maku daga kai har Shureen, don shi Sudais naji uwar na cewa cikin shekaran nan ne idan Allah ya kai mu, dama shi me yan mata ne iri iri, xaba kawai xai yi ya darje" Murmushi kawai junaid yyi, Kaka tace "Ba abun murmushi bane, har da rashin auren ke damun ka kai da Shureen, Kai kuma naga ai wayayye ne a kan Shureen da yake nan dunkum, Kai baxa ka rasa yan matan ba ynxu hka, shi kuwa Shureen da kyar idan ba hadin gida xa ayi masa ba, idan ba haka ba kuwa sai yyi shekara hamsin bbu aure, duk da dai shi da maganarsa da wata yarinya a kasa don har naje na nemi alfarman a bamu ita gidan iyayen yarinyar kuma sun amince, sa rana kawai ya rage idan yarinyar ta gama karatun sakandari, ta ma kusa gamawa" daga Farida har Heedayah kallon kaka suke, Junaid ya kalleta ta madubi kawai yyi murmushi bai dai ce komai ba, Heedayah tace "Da gaske kaka?" Kaka tace "Wllh, ai maganan ya fi shekara uku ynxu..." Heedayah tace "Kuma ya san maganan?" Kaka tace "Haba wane mutum, ai baxa a bar sa ya san da maganan ba, ni dai ai ban biye ta rashin kunyar da yake min ba nayi masa gata a matsayin warce ta haifi ubansa, Amadun ma yasan da wnn xancen kuma" Heedayah ta kyalkyale da wani dariya tace "Allah ya sa kwanan nan xa ayi" kaka tace "Aa baxai dau lkci ba dama" Farida tace "Toh auren dole xa ayi masa kenan" Kaka tace "Kaji gantalalliya, auren dole ai tun xamaninmu aka daina, ai baxai ki yarinyar ba tunda tana da kyau kamar uwarta, Allah na tuba me xai nuna mata banda matsayinsa na soja, ai son kowa ce k'in wanda ya rasa" Heedayah ta kara kyalkyalewa da dariya, Kaka tace "Ke ma auren xa a maki kwanan nan ai" Ta dakatar da dariyar da sauri, Junaid dai sai kallonsu yake, ta turo baki tace "Yar yarinya da ni" Kaka tace "Wace yarinya, bayan naji labari a wajen Rakiya kin fara al'ada" Farida ta kauda kai tana dariya kasa kasa, Heedayah tayi shiru bata kuma cewa komai ba, kaka ma tayi shiru jin kowa yyi shiru. Suna isa gidan Abba Junaid yyi parking a waje, kaka tace "Toh Alhamdulillahi Allah ya maka albarka Junaidu, Allah ya nuna min bikin ka" Daga haka ta sauka motar Heedayah ma ta sauka Farida ma ta sauka, Farida ta daga masa hannu tace "Allah ya kiyaye" Heedayah ta kallesa tace "Sai anjima" ya gyada mata kai ta bi bayan kaka da har ta shiga compound din. Hamdala kaka tayi ganin motar Abba da na Shuraim, ta wuce ciki tana cewa "Allah ya so ni, idan Amadu ya fita ai xuwan banxa nayi kenan" Abba ya fito parlonsa cikin shigar fita office tare da Shuraim dake rike da brief case dinsa kenan kaka ta shigo parlon Heedayah na biye da ita, Kaka ta washe baki tace "Sannu Amadu Ina ta sauri kar ka fita, Allah ya so ni...." Kallon Heedayah kawai Abba yake, hakan ya sa ta karasa inda yake tsaye ta rungume sa cikin sanyin murya tace "Abba..." Kaka tace "Atoh, ai Rakiya ta shiga uku ta lalace, ta tarwatsa xumunci" Abba ya d'an yi murmushi ya maida Heedayah gefensa yana kallonta yace "How are you" tace "I'm fine good morning" Yace "Ya karatu" tace "Alhamdulillah" Farida ta karasa ita ma ta gaida Abba da ladabi, ya amsa da murmushi yace "How are you Farida" tace "I'm fine sir" Abba yace "That's good" Kaka ta tafi parlor ta xauna tana cire hijab din jikinta tana kara gode ma Allah ta samu Abba, Abba ya karasa ya xauna ya gaisheta tace "Lafiya lau Amadu ya taro? Fatan duk kun watsa su lafiya" Yace "Alhmdllh" kaka tace "Toh Allah ya maku albarka ya mayar maku da dubun abinda ku ka kashe, saura na wnn yaron naka Shureen kuma" Shuraim dake ta tsaye ya kalleta ta gefen ido, Abba dai yyi murmushi ya mike yace "Na makara Baaba, kuna nan har in dawo ai" Kaka tace "To ina xa ni? Ai ina nan in sha Allahu har ka dawo, yi tafiyar ka Allah ya tsare" Yace "Ameen" hannun Shureen ya amshi briefcase dinsa yace "You didn't greet her" Shureen ya karasa parlon yana kallonta yace "Ina kwana" kaka tace "Lafiya lau, jiya ka kai ma Rakiya su dubulan da alkaki da cincin din kuwa, naje gidan na manta ban tambayeta ba wllh" Wani kallo ya mata bai ce komai ba, Abba na kallon Heedayah yace "Sai na dawo" Tace "Allah ya tsare Abba" ya amsa da "Ameen" Farida tayi masa Allah ya tsare ita na snn ya fita parlon, Farida da Heedayah suka dawo parlon suka xauna, kaka tace "To ita Maryam din bin ta xa mu yi parlonta kenan, toh ai bbu komai ku tashi mu je, mu ba bakin xafi bane, baxan biyeta ba, amma kuma ban ji kun gaida Shureen ba" Farida ta mike ganin kaka ta mike, tace "Ina kwana" Heedayah ma ta tashi tace masa "Ina kwana" Duk bai amsa masu ba, Suka bi bayan kaka xuwa parlon Mumy, Mumy ta fito bedroom dinta kenan ganin kaka ta d'an canxa fuska tace "Kaka ce..." Kaka tace "Wllh ni ce, ina ta sallama shiru, ashe kina can ciki" Mumy juya xata rufe kofar dakinta tana yatsine yatsine tace "Ehh ina ciki" Heedayah ce karshen shigowa parlon, Farida ta xauna kusa da kaka, Heedayah ta xauna gefenta duk suka gaida Mumy, lkci daya fara'a ya bayyana fuskar Mumy ganinsu tace "Aa ashe baki muka yi hka, to sannun ku da xuwa" Kaka tace "Ehh cewa suka yi sai sun xo sun gaishe ki, su Rabi'ah kuma can na barosu gidan Umaru basu ma san xan yo nan ba" Mumy na washe baki tace "Allah sarki, Sannun ku da xuwa, bari a kawo maku breakfast" Kaka tace "Aa ni kwai kawai xa a soya min, idan akwai d'an farfesu a hada min da shi, kwanan nan ba wani cin abinci nake ba" Daga Farida har Heedayah suka kalleta, Mumy tace "Toh su kuma 'yan matan fa" Kaka tace "Su ma soya masu kwan kawai a hado masu da d'an dankali" Farida tace "Aa mu mun koshi" Kaka tace "Da yake sun karya su" Mumy bata ce komai ba har ta fita parlon sai kuma ta dawo ta shiga bedroom dinta tace "Bari in maida wayata caji" rufe kofar dakin tayi ta nemo wani karamin purse dinta da ta adana sosai ta bude ciki ta dau wani kullin xani, ta fi minti daya tana kallon kullin da xai yi shekara uku a ajiye cikin jakar, "Ko nan da shekara goma ne bbu abinda xai hanasa aiki" murya wanda ya bata ne ke dawo mata, tayi wani murmushi ta kunce habar xaninta ta kulle kullin maganin a jiki snn ta daura xanin ta fito parlor tace "Sannu kaka, bari in je inyi masa in soya maki" kaka tace "To yi maxa" daga hka ta fita parlon, tsaye ta ga Shuraim har sannan a Main parlor, Tace "Aliyu tun da sai yamma xaka fita bari in baka sako ka kai ma Hajiya Sadiya yanxu..." Ya kalleta yace "Akwai aikin da nake yi ban gama ba, ki bada sakon idan na fita anjima sai in kai mata" Ta wani hade rai tace "Toh ni yanxu nake son ka kai mata ba sai anjima ba" Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, sauke ajiyar xuciya yyi ya xauna saman kujera, Mumy na tsaye kitchen ta sa mai aiki ta soya lafiyayyen kwai da ya ji albasa da tsire a ciki na kaka, sauran tsiren kuma ta saka a plate daban daban guda biyu, tana kallon Mai aikin tace "Duba min Shuraim na parlor ne" Mai aikin ta fita ta dawo tace "Aa baya nan" Mumy ta dau plate din kwan kaka ta mika mata tace "Ki kai ma kaka, idan tace wa ya soya kice ni ce.... Sai ki tafi ki ce ma driver yyi wucewarsa nayi baki sannan ki dawo ki kai ma yan matan nan tsire" Mai aikin tace "Toh Hajiya" daga haka ta nufi kofa ta fita, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofar, kallon window din kitchen din tayi snn ta kai hannu gefen xaninta, cikin few minutes ta gama abinda xata yi ta barbada ma naman yaji snn ta dau plate din biyu ta fita xuwa parlonta, ta ajiye daya gaban Farida, na hannun hagunta ta ajiye ma Heedayah tace "Naji kaka tace kun karya wnn kuma ai abun marmari ne, da asuba nayi ma Barrister ashe baxai ci ba, wnn nawa ne da na Shuraim, shi ma nasan ba lallai ya ci ba" Kaka tace "Atoh, rabonsu ne, ku yi maxa ku ci"










Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....








Mumy ta nemi kujera ta xauna tana murmushi, labarin biki da abubuwan da suka faru suka dinga yi da kaka, kaka ta saki baki sai xuba take, Mumy tace "Ai ni kin kyauta min da kika ce a sauke canopy din nan, mutane basu da hankali wllh" Kaka tayi fuska kamar 'yar yarinya tace "Lallai, haka kawai a lalata min motocin yaro, uban waye ya siya masa, kiris ya rage wnn suntumemen ya gogi motar da karfen fa, ba ruwana ni dai na koresu, wanda suka kafa a bakin titi bai isa ba sai an shigo mana gida da katon lema a kakkafa" Mumy tayi 'yar dariya, sai kuma ta kalli su farida tace "Ku ci mana kar ya huce da xafinsa kuwa" Farida ta ajiye wayarta da take dannawa tace "Na koshi ni" Mumy ta hade rai tace "Kin koshi kamar Yaya, hanaki cin abinci aka yi a nan din idan kun xo" Kaka tace "Aa babu wanda xai hanata, da yake kinsan sun karya kafin mu fito" Mumy tace "Aa to gaskiya baxan ji dadi idan basu ci ba tunda da kai na na kawo masu" Kaka ta kalli farida tace "Ko kwara daya ne ki ci kar taga kamar an hanaki, nasan a koshe ku ke" Mumy na kallon Heedayah tace "Ita idan ta ki ci ai ke bakya ki ci ba, dau plate din ki ci abun ki" Heedayah tace "Ahh haba wnn ai Mayyar nama ce xata ci nasani" Heedayah ta kalleta bata dai ce komai ba, Mumy tayi dariyar da bai kai ciki ba tace "Dauka ki ci Heedayah" Heedayah ta sauke idonta tana kallon naman tace "Mumy na koshi, mun yi breakfast a gida kafin mu fiti" Mumy ta d'an hade rai tace "Nama abinci ne? Bana son gulma idan xaki dauka ki dauka ki ci, idan kuma hanaku cin komai akayi sai na sani" Kaka tace "Ni dai ba ruwana sai ku ja ma Rakiya bakin jini nan kuma bata san hawa ba bata san sauka ba, idan xaku dau gasasshen naman ku dauka ku ci meye xaku dinga ma mutane kunbiya kunbiya gashi har na narka kwaina a ciki, nama ai abun marmari ne ba abinci ba" Farida dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce komai ba, Heedayah ta dau plate din naman ta dauki daya, wani ajiyar xuciyar da ya kusa fitowa fili Mumy ta sauke, Kaka ta kalleta tace "Lafiya?" Mumy ta d'an daburce tace "Wllh tun juya nake jin kamar ulcer na xai tashi" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya maki tsari da shi" ta gefen ido Mumy ta dinga kallon Heedayah da ta kai naman baki ta fara ci a hankali, wani ajiyar xuciyar ta kuma saukewa, Kaka tace "Toh Allah yayi maki tsari da shi dai, ulcer ai bala'i ne" Heedayah xata ajiye plate din Mumy tace "Har kin yi me? Me kika ci da xa ki ajiye" Kaka tace "Ni dai ba ruwana da wahalansu idan basa ci su kawo min in juye a jaka mu tafi kawai" Farida ta mike ta dau plate din nata ta tafi ta kai ma Kaka tace "Ni baxan ci ba" kaka ta kwace plate din, Heedayah dai ta ci gaba da cin naman, hira kawai Mumy ke ma kaka don Heedayah ta ci naman sosai, Heedayah dai cin naman kawai take ba wai don yyi mata dadi ba, daga karshe ta mike ta nufi kofa, Ta gefen ido Mumy ta bi ta da kallo don ta ci desired quantity din ba laifi, Heedayah na fita ta dau hanyar kitchen, xaune ta ga Shuraim a parlon this time around, ya mike ganinta, dauke kai tayi da sauri ta wuce kitchen din ta shiga, plate ta nema ta rufe sauran naman ya shigo kitchen din yana kallonta yace "What's that you are covering?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tsire ne" Yace "Waye ya ci?" Tace "Mumy ce ta bani" Shiru yyi yana kallonta, yace "Ke da wa?" Tace "Farida" yace "Ina na faridan?" Heedayah tace "ita bata ci ba" yace "Kece mayunwaciya kenan" Sai a snn ta kallesa, ya daure fuska yace "Baki ci abinci a gida ba kafin ku fito?" Kin cewa komai tayi ta dauke kai, yyi mata wani tsawa yace "Ba da ke nake ba" Ta ki juyo fuskarta ta d'an turo baki tace "Na ci" yace "Then meyasa kika ci naman?" Tace "Mumy ce tace I should eat it" karasawa yyi ya bude plate din sai ga Mumy ta shigo kitchen din, ganinsu a tsaye da mamaki tace "Me kuma kake yi a nan Aliyu?" Ba tare da ya dubeta ba yace "I came to make tea" Mumy tace "Wanda ka sha daxu fa" yace "Bai isheni ba" Ta kalli Heedayah da ta sunkuyar da kanta, Mumy tace "Ina naman da kika rage bani in tafi in ci ban karya ba dama" Heedayah ta karasa ta bude plate din ta dauko naman ta mika ma Mumy ta amsa, Heedayah ta bi gefenta ta fita kitchen din, Mumy tayi masa wani kallo tace "Da uban me ka shigo nan din kana gaya mata ko akwai hadin biri da gada ne?" Yace "Ni fa I just came in to make tea sai na ganta, and where is my meat?" Mumy tace "Gwara ya kasance haka don ma ka ji in gaya maka, ba hadin biri da gada, tsire kuma bbu sai ka dau na annabawa" yace "Toh bani wannan in ci" tace "Baxan bayar ba" daga haka ta fice daga kitchen din ya bi ta da ido. Mumy na fita kitchen dama Parlon Abba ta shiga ta kulle da mukulli, tana dube dube ta dau wani plane sheet paper ta juye tsiran a ciki sannan ta cukuikuye takardan ta tura can karkashin kujera yanda baxa a hango ba snn ta mike ta fito Main parlor, leka hanyar kitchen tayi ta ga alamar yana tsaye har sannan a kitchen din, ta mayar da plate din parlon Abba, sannan ta fito ta sa makulli ta tafi parlonta tana murmushi ta shiga tace "Sannun ku Kaka, Kwan ya ishe ki ko?" Kaka tace "Ya isheni sai na gobe kuma idan Allah ya kai mu, kin ji Farida wai mu wuce, bayan nace ma Amadu muna nan har dare" Mumy tace "Allah sarki, ta gaji da xama kenan, tunda kun gaisa da Barrister din ai xaku iya tafiya kaka" Kaka tace "Aa su dai su tafi, haka kawai bamu gama ganawa da d'a na ba kice in tafi" Mumy ta kauda kai bata ce komai ba, kaka tace "Sai dai ko kiyi ma Shureen magana ya ajiye su gida tunda ke baxai maki musu ba ni kuma sai ma ya iya xagina" Mumy ta d'an yi shiru, can ta saci kallon Heedayah, sai kuma tace "To dama dai driver na nan ne sai ya ajiye su, amma Shuraim kam nasan baxai je ba, ynxu ma na aikesa ya kai ma Sadiya sako yace baxai fita ba" Kaka ta rike ha6a tace "Wnn Sadiyar dai kinki rabuwa da ita har ynxu ko Maryam, bbu wanda fa bai san uwarta dillalliyar bokaye bace, kinsan uwarta kawar kishiya ta ce, to wllh bbu gidan bokan da basu xuwa lkcn Kaduna na daji, daga karshe ya kwabe masu shine kishiyar tawa uwarsu wnn yarinya da ta kusa sace min zinari jiya ta bani labarin komai, Kai har makabarta ta sha shiga ta binne laya a kabari, to in takaice maki a tsaye uwar Sadiya ta mutu kekam, ki gaya ma kowa wannan labarin kice in ji ni, a tsaye Talle ta mutu a bandakinta kamar tsohuwar soja, ta mutu da yan awanni kafin a ankara har ta kumbura suntum, toh ke dai kiyi hattara da kawance da Sadiya don barewa baxata yi gudu d'an ta yyi rarrafe ba, Kuma dai abokin barawo barawo ne, tale tale da nasan ki ke dai ko maganin tsari baki yrda da shi ba sai kice Allah ne me tsarewa, to yanxu dai ban san ya kike ciki ba gaskiya" Mumy dai sai danna wayarta take fuskarta bbu yabo bbu fallasa ta ki kallon kaka, Shuraim na tsaye bakin kofa tun fara labarin kaka hannunsa rike da makullin motarsa yana sauraronta, Mumy ta juya tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "Lafiya????" Yace "Xan je government house" Kaka tace "Atoh ka sauke min yaran nan a gida don girman Allah kar su fara min kuka, kuma me xaka je yi a gwamnet house?" Da sauri Mumy tace "Ae ba hanyarsa bace kaka" Kaka tace "Toh sai ya fara ajiyesu snn ya tafi gwamnet house din, Ina ruwana ni da xa ki ce min ba hanyarsa bane" Juyawa yyi yace "Su sameni a mota" daga haka ya fita parlon, Farida ta mike ta dau jakarta, kaka tace "Toh Allah ya kiyaye, kila anjiman ma Amadu ne xai ajiye ni gida" Farida tayi ma Mumy sallama tayi ma kaka sannan ta fita, Heedayah ta mike tsaye da kyar don tun fitowarta kitchen kanta ke juya mata, bata ce masu komai ba ta nufi kofa walking slowly, Mumy ta bi ta da kallon gefen ido har ta fita, kaka ta kyabe baki tace "Bana biye mata ba ta kai ni gaba gun Rakiya" Farida na tsaye bakin kofar fita main parlor tana jiran Heedayah, har ta iso kofar kallonta take, tace "What's wrong?" Heedayah ta dafe kanta da kyar tace "I'm not feeling okay" Farida ta kama hannunta tace "Ciwon kai??" Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Farida tace "Mu tafi gida sai ki kwanta, you will feel okay in sha Allah" tana rike da hannunta suka nufi motar Shuraim, har suka iso yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude back seat Heedayah ta shiga ta kulle sannan ta xaga ta bude daya side din ta shiga ita ma ta kulle tana kallon Heedayah da ta hade kai da gwiwa tace "Sannu" juyowa yyi yana kallonsu yace "What's wrong?" Farida tace "She said she is not feeling fine" Rufe motar yyi suka bar gidan, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikin motar, yyi parking kofar gidan yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude side dinta ta fita ta xaga ta bude bangaren Heedayah tace "We are home..." A hankali Heedayah ta dago kanta sannan ta sakko daga motar, Farida ta rufe tana kallon Shuraim tace "Thank you" Bai ce komai ba ta kama hannun Heedayah suka nufi gate, "Heedayah!!" a tare duk suka juya suna kallonsa, Farida ta sake hannunta, kamar me counting step dinta ta koma gun motar, yana kallon idanuwanta da suka kada yace "Me ya sameki?" Ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina jin jiri, kuma ina son in kwanta" yace "Why?" Ta buda hannunta a hankali tace "Nima ban sani ba" yace "Tun da kika tashi yau kike jin jirin?" Ta girgixa masa kai, Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Go...." juyawa tayi taga Farida ta riga ta wuce ciki, ta nufi gate din, dishi dishi ta fara gani kafin ta karasa gate din, lkci daya ta kwala wani kara ta sulale a wajen. Mami ce xaune gefenta a kan gadon dakin, Junaid na ta daya side din a tsaye pressing his phone, sai Shuraim dake tsaye kusa da window ya rungume hannunsa, Farida ta shigo dakin rike da bottle water da glass cup, ta duka gefen Heedayah ta bude ruwan ta xuba a cup, Mami ta dagota tace "Gashi ki sha" amsa Heedayah tayi ta sha kadan, Mami tace "Ya ciwon kan?" A hankali tace "Ya daina" Mami tace "Toh Allah ya sauwake daughter" Junaid ya kalleta yace "Jirin fa?" Tace "Ya daina" Kofa Shuraim ya nufa ya fita, Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami ina son inyi bacci ynxu" Mami ta kwantar da ita ta ja mata blanket tace "To yi baccin dear" Farida ta mike ta fita da ruwan, Junaid ya bi bayanta, sai da Mami ta ga ta fara baccin snn ta sauke curtain din dakin ita ma ta fita. Lkci lkci Farida ke shigowa dakin duba Heedayah dake ta bacci comfortable har kusan azahar, Farida tayi alwala ta fito bandaki ta tafi gaban mirror ta dau darduma dake kan kujeran mirror din taji vibration din waya, bude inda taji vibration din tayi ta daga dictionary ta dau karamin wayar tana kallo, bude ido Heedayah tayi ta mike xaune da sauri tace "Is it ringing??" Farida ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar sannan ta juya ta fita.




*Let it not be as if I didn't update today, yanda kowa ma ya tafi gidan lalle haka nima na tafi can don ni ba gantalalliya bace, ehe* 🌚








Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....






Heedayah ta daga kiran ta kai kunne amma bata ce komai ba, sallama yyi mata ta amsa sannan tace "Ina yini" yace "Lfya lau, how are you?" Tace "I'm fine" yace "Always not picking calls, why?" tace "Mun fita ne" yace "Xuwa ina?" Tace "Gidan Abbanmu" yace "Ohk" shiru tayi, shima yyi shiru, can yace "So you ain't coming out anytime soon" ta jingina da pillow tace "Nima ban sani ba" yace "Yaushe xa ku koma schl?" Tace "In a week time" yace "Ina son mu hadu" bata ce komai ba, yace "Kin ji?" Tace "A ina?" Yace "Idan ma kince gidanku ae sae in xo" tace "Don a min duka?" Murmushi yyi yace "Aa ba wanda xai

Please Login or Register in order to submit comment