Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gaske me dauke da duplex biyu, motoci ne a duk parking space uku dake compound din da ya kawatu da flowers ta ko wani angle, suka danna bell bayan few minutes aka bude kofar, gaisheta suka yi, ta amsa tana masu sannu da xuwa sannan ta amshi hannun Islam tace "Tana daya bangaren mamanta, Bismillah ku shigo yanxu xata fito" Farida tace "Aa, muna dai gaisheta, sai anjima" daga haka suka juya suka nufi gate suka bar gidan. Heedayah na xaune saman darduma ta idar da magrib jin wayarta na vibrate ta kalli Farida dake sllh, mikewa tayi ta bude purse din ta ciro wayar snn ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Ina waje" ta xaro ido ta d'an kalli Farida, sai kuma tace "Ohk" katse wayar tayi ta ajiye, haka nan kawai taji kamar an cire mata tsoro a ranta, taji she is not even afraid of anyone, taji kuma she wants to meet with Khaleel, tana ta xaune dai har Farida ta idar da sllh ta mike ta fita dakin, sannan ita ma ta mike tana rike da gyalenta da ta linke ta sauka parlor, tsaye ta same farida inda take shiga ba nan take fita ba, yayarta dai na xaune tana feeding din Fadil tana kallonta, cike da fada tace "Kuma wllh idan ya koma da wayata baxan sake amsar wayar ba ko an bani, dubi fa yanda na wani xauna tun rana kamar marainiya ba waya, nasan kuma ana ta kirana, ba sai ya bari driver yaje ya amso min kayana ba dama idan ba niyyar tafiya yyi da shi ba" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Maman Fadil tace "Toh bari a kara kiransa amma Ina jin bai tafi bane da xai tafi ai xai kira yace in turo driver haka muka yi da shi" Farida tace "Lallai baki san waye shi bane Aunty wllh da gangan ma sai ya iya tafiya da wayar don in ji haushi, ai kinga ita da ta janyo ya amshe wayar har yanxu bata ce min komai ba as if fault dina ne, kuma har komawa tayi gaban motar fa ban san me ya kai ta can ba ta xauna, kuma sai tace bata ga wayar ba a kusa da ita???" Heedayah dai ko kallonta bata sake yi ba tayi hanyar kitchen, Mai aiki ce ta fito kitchen din ta gama wanke wanke, Farida ta bi Heedayah da wani shegen kallo har ta shige kitchen din, Maman Fadil tayi kasa da murya tace "Ni gaskiya bana son haka Farida, xata ga kamar don ta biyo ki ne kike mata haka, tun rana sai masifa kike mata gashi ta ki kulaki, bata ce maki komai sai masifa kike, wnn bai yi ba dai" Farida tace "Wa?? Kin xata wai ta rasa abinda xata ce ne yasa tayi shiru, ai ko xan kwana ina yi baxata tanka ba kuma baxata bani hakuri ba, taurin kai ne da ita da kike ganinta haka, wllh nasan kila da gangan ta bar masa wayar dama naga sai wani shisshige masa take" Maman Fadil tace "Shisshige masa ta ya kuma?" Farida ta xauna fuska daure tace "Ohon masu" Murmushi kawai Maman Fadin tayi ta dau wayarta tace "Bari dai in sake kiransa" dialing Number Shuraim tayi ba a dau time yana ring ba ya daga, gaisawa suka yi tace "sai muka ji shiru Yaya Shuraim..." Ta gama sauraronsa snn tace "Toh shkkn ba matsala, Allah ya tsare" katse wayar tayi ta ajiye, Farida ta xumburo baki tace "Wai me yace??" Maman Fadil tace "Jarabbiya to yana hanya xai kawo maki ynxu" da mamaki Farida tace "Toh me yasa bai koma ba??" Maman Fadil tace "Kilan ya gaji ne, kamar ma bacci yake, Amma yace xai taho ya kawo ynxu" Farida ta tabe baki bata dai ce komai ba. A hankali Heedayah ta bude kofar dake kitchen da xai sada ka da bayan gidan ta fita snn ta jawo kofar very careful kar yyi making ko wani sound snn ta yafa veil dinta ta fara tafiya da sauri, ta jikin parking space ta raba har ta isa gate, ganinta mai gadi ya fito dakinsa da sauri yace "Fita xa ki yi Hajiya?" Ta gyada masa kai, ya bude mata gate din ta fita, tana fita ta juya ta kallesa don tsayawa yyi ya ki komawa ciki as if wanting to know where she is going, ta hade rai, sau daya ta kalli motar da ya tsaya shi daya a layin da hasken fitilu ya haska kamar ba dare ba, ta san Khaleel ne duk da ba motar da ta saba ganinsa da shi bane don wnn har ya fi wancan haduwa amma bata tsaya ba tafiyarta kawai take, can ta ji Mai gadi ya kulle gate din ta juya taga ya koma ciki, A hankali Khaleel ke tafiya har ya tsaya dai dai flowers din gidan da suka kai islam daxu amma ta opposite, Heedayah ta sake juyawa tana kallon gate din gidan da ta fito snn ta nufi motar, sauke tinted glass dinsa yyi ta xagaya ta bude front seat ta shiga ta rufe. Khaleel na kallonta murya can kasa yace "Hope u took permission before coming out?" Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Why?" Ta turo baki bata ce komai ba, yace "Heedayah" daga manyan idanuwanta tayi ta kallesa tace "Don a min fada?" Yace "Toh ai ba a gida kike ba, kuma yawanci xa ki ga aunties usual don't have much problem, da yawa idan mace na son haduwa da saurayinta kuma ba a barin ta fita a gida, ta kan hada baki da yayarta ko aunt dinta sai ta xo gidan aunt din nata su hadu, kuma bbu wanda xai sani sai daga ita sai aunt din, so wnn ma da kin gaya mata baxata hanaki ba" Heedayah ta wani kallesa tace "To kai saurayina ne?" Shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya girgixa mata kai yace "Aa" ta dauke kanta, yace "Amma duk da haka da kin gaya mata, ko da yake naga kin fiye tsoro ke din" Tace "Not when Farida is there xan gaya mata, Beside it's not as if mun saba sosai da ita, na fi sabawa da kanwarta Aunty Fatee" yace "Ohk wnn baki santa ba?" Tace "Aa na santa, tana xuwa once in many month tayi two days" yace "Ohk how about her husband?" Tace "Yana UK shi" Khaleel ya gyada kai bai ce komai ba, ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa, Zayyad ne ke kiransa ya mayar da wayar ya ajiye har ya katse, tun yana hanya Zayyad ke kiran nasa yaki dauka, ya kalli Heedayah yace "Hope kin ci abinci?" Ta nuna masa wayarsa da aka sake kira tace "Pick ur call" Ba musu ya daga ya kai kunne bayan ya rage call volume din, Daga daya bangaren Zayyad yace "You caused everything Khaleel, you just ruin everything, da ka bi mu wllh wllh duk wannan abinda ya faru baxai faru ba, and mind you Oga Manga na neman ka yanxu haka, just don't show up anytime soon..." Calmly Khaleel yace "Me ya faru?" Zayyad yace "Abinda ya faru shine an harbe Saif and he is dead, mu hudu muka fita dama, kuma we weren't early enough don har target dinmu sun wuce exact village din that's conducive for the operation, and u caused everything, so muna dai tafiya not knowing an kafa wani check point a gaba sbda robbery da aka yi a wajen da asuba har an kashe wasu, da mun san da check point din da baxa muyi attacking dinsu ba a particular area din da muka yi attacking dinsu, everything wasn't in our favor today, mun sha ne da kyar... It wasn't funny Khaleel, kuma duk kai ne ka ja komai, Oga Manga na nemanka yanxu haka" Khaleel da yyi shiru yana sauraronsa yace "Tough day indeed" daga haka ya katse wayar ya sa flight mode ya ajiye, Wani mota ne ya shigo layin ya haskosu, da sauri Heedayah ta dukar da kanta, Khaleel ya dage glass din motarsa yana bin motar da ido, dai dai gidan dake opposite dinsu motar ya tsaya Mai gadi ya wangale gate, a hankali Heedayah ta dago kanta motar ya shiga gidan aka rufe gate din, kallonta Khaleel yyi yace "Kin taba xuwa layin ne da kike boye fuskarki?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wani motar ya kuma shigowa layin, Heedayah ta xaro ido sosai tace "Yaya Shureen" rufe fuskarta tayi da gyalen jikinta, Khaleel ya dinga kallon motar har ya iso inda motarsa ke tsaye, Heedayah ta dago kai ita ma a hankali ta bi motar da kallo, dai dai gate din gidan Maman Fadil yyi parking, Heedayah na kallon Khaleel kamar xata yi kuka tace "Did he see me?" Girgixa mata kai yyi yace "Tinted glass ne ai" Ta juya ta sake kallon motar Shuraim ta ga ya sakko daga motar sai da ya fara kallon motar Khaleel snn ya tafi ya kwankwasa gate din gidan, Heedayah ta marairaice tace "Kila ya gan ni fa" Khaleel yace "How? is he having tinted eyes?" Tace "Ni dai mu je gaba to" driving din motar yyi yana tafiya a hankali har ya bar layin gaba daya. Kallonta yyi yace "Ina xa mu je" tayi shiru gabanta na faduwa, sai kuma ta ji kamar an cire mata tsoron gaba daya, ta jinginar da kanta da kujeran motar a hankali tace "Anywhere"








Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....






Shuraim na shiga gate din gidan ya hadu da Farida xata fita ita kuma, komawa baya tayi ganinsa, ya mika mata wayarta, ta amsa kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tace "Thanks" juyawa yyi xai fita, har xata yi magana sae kuma tayi shiru sai da taga ya fita gate din sannan ta leka waje, da ido ta hau surveying din street din, mamaki ne ya cikata ganin bata wani ga alamar Heedayah ba, to ina ta tafi, suka hada ido da Shuraim da ya bude motarsa ya shiga, ta dauke kai ta shigo cikin gidan tana kallon Mai gadi tace "Don Allah warce muka xo gidan nan daxu tare ta fita ne?" Mai gadin yace "Ehh ta fita" Farida ta fita gate din gaba daya tana sake bin layin tun daga saman sa har kasa da kallo, banda motar Shuraim bbu wani mota dake waje a wajen bbu kuma alamar mutum a layin, ganin kallon da Shuraim yake mata daga cikin mota ta juya xata koma ciki, taji yace "Come here, who are you looking for??" Shiru tayi bata son ce masa Heedayah take nema ta ja mata, can ta kallesa a takaice tace "Nobody" bata jira cewarsa ba ta shige ciki. Gun yayarta dake xaune parloe ta koma tace "Aunty ban ganta ba fa" Maman Fadil ta mike da mamaki tace "Baki ganta ba kuma, to ina ta tafi?" Farida tace "Wllh ban sani ba kuma me gadi yace ehh ta fita gate" Kasa cewa komai Maman Fadil tayi tana kallon Farida, Farida tace "And ni ban ga kowa a layin ba" Maman Fadil ta xaro ido tace "Toh kar dai bin wani tayi tunda kince kinji tana waya da saurayi" Farida ta girgixa kai tace "Noo Heedayah will neva follow him, ni na santa baxata yarda ta bi sa ba" Maman Fadil tace "Yau Naga ikon Allah, to idan ba bin sa tayi ba guduwa yyi da ita? Waye shi din, ke kin san sa ne?" Cike da damuwa Farida tace "Ni ban wani san sa ba wllh, kuma fa bbu wanda ya san ya bata waya, nima bata gaya min ba kawai gani nayi tana ta boyewa, I am just confuse, ina Heedayah xata je da daddaren nan" Bude baki Maman Fadil tayi tace "Na shiga uku ace a gidana, ita Hadiyar dama haka take? Daga xuwa garin mutane sai ki bi saurayi ku yi tafiyar ku, duka duka nawa take da xata aikata wnn aiki, ko kece kika bi saurayi daren nan ba sai Mami ta kusa balla ki ba balle ita, ni yanxu matsala xa a ja min kawai wllh, ta ina xan fara wani bayanin yanda aka yi, kamar wasa kawai a nemi yarinya a rasa" Fita tayi daga parlon Farida da duk jikinta yyi sanyi ta bi bayanta tana tunanin anya mutumin nan ba guduwa yyi da Heedayah ba kuwa, Banda haka ai duk abun Heedayah tasan baxata yarda ta bi sa da daddaren nan ba, tunanin hakan yasa xuciyarta ya tsinke taji tsoro ya kamata sosai, Maman Fadil ta tafi gun mai gadi tace "Mukhtar ka ga fitar bakuwata da daren nan kuwa?" Yace "Ehh nine ma na bude mata gate" a mugun fusace Maman Fadil tace "Don me xaka bude mata gate da daddaren nan ba tare da izini ba" Yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Hajiya naga ba yarinya bace shi yasa na bude wllh, na xata ko tadi xata fita" Maman Fadil ta bude baki with much surprise, can tace "Toh da ta fita ina kaga tayi?" Yace "Toh da ta fita naga dai kamar bata ji dadin kallon da nake mata ba, sai naga tayi can, nan kuma so nayi inga inda xata ne, Amma dai da wata mota da naga anyi parking a kofar gidan Honorable, ni dai sai na koma ciki na xauna sai da wnn bawan Allah ya xo na sake bude gate din to ko da na leka waje gaskiya ban ga motar ba kuma, ita ma ban ganta ba" Maman Fadil tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, haka dama Hadiyar take Farida, ki shiga motar saurayi a garin da ba naku ba ki bishi kuyi tafiyar ku?? Yanxu me xan ce ma Mami" Farida dai ta kasa cewa komai gaba ta tsorata ne sosai, Maman Fadil ta juya ta nufi hanyar shiga parlor tana cewa "Toh kuwa bari in kira Mami bbu wanda xai ja min matsala gaskiya" da sauri Farida ta bi bayanta tace "Noo plss don Allah aunty kar ki kirata, Mami won't take it likely with her, mu jira sanda xata dawo sai kiyi mata fada ke, don Allah Aunty kar ki kira Mami" Maman Fadil tace "Ya xa ki ce kar in kirata, wnn ai ba abinda ya kamata a boye bane, ya kamata a sanar ma Mami, gaba daya nawa take? Ta wuce 17 wnn da ganinta, amma ita har tayi wayon bin saurayi da daddare ba ma da rana ba, kai ko da rana ne hukunci me tsauri ya kamata ayi mata balle da daddare, samarin Abujan nan masu lalata yan mata, a gidan ubanwa ta san sa ma, snn kince Mami ma bata san da waya hannunta ba, ni bbu wanda xai xo ya ja min matsala daga ke har ita wllh" Farida dai ta ma rasa bakin magana, Maman Fadil ta xauna parlor sai dai bata kira Mamin ba, hankalin Farida ya d'an kwanta sai kallon agogo take tana addu'a, tana fatan Allah ya sa Heedayah ta dawo anytime from now, yanda duk ta tsorata sai kace ita tayi laifin ma. A wani tsadadden wajen shan ice cream Khaleel yyi parking yana kallon Heedayah da idonta ke saman titi ko kiftawa bata yi, yace "Kina shan ice cream?" sai a snn ta juya ta kallesa ta kalli gun siyar da ice cream din, tace masa "Uhn" yace "To mu je ki xabi flavor da kike so" a hankali tace "Aa ni baxan fita ba" yace "Me yasa?" Ta langwabar da kanta tace "Ba komai, kawai bana son in fita" yace "Ohk then, let me get you" bata ce komai ba ya dau face cap dinsa ya kafa a kansa, baka ganin komai sai dogon hancinsa da karamin bakinsa, ya bude motar ya sauka ya kulle, ta bi sa da kallo har ya shiga babban Ice cream parlor din, bayan wasu mintuna ya dawo rike da leda me dauke da packaged ice cream har uku ya bude motar ya shiga snn ya kulle ya mika mata ledan, amsa tayi ya tada motar suka bar wajen, ya kalleta ganin ta ajiye ledan a gefenta yace "Toh ki sha" tace "Ni kadai?" Yace "Yess" tace "Ai baxan iya shan duka ba" yace "Toh sha wanda xa ki sha" ba musu ta bude ledan ta dau vanilla flavor ta bude ta fara sha, a nutse yake driving din, just roaming round FCT, sai bin manyan wurare take da kallo, you can't say if she is happy or not, ita dai ga ta nan, suna isa wani joint na shawarma yace "Do you take shawarma?" Ta girgixa masa kai alamar Aa, yace "Why?" Tace "Na koshi" yace "Toh tsire fa?" Ta girgixa masa kai nan ma, bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da driving slowly, kallon agogo dake nuna karfe tara saura minti sha biyar yyi yace "Are you sure baki son komai?" Ta gyada masa kai, tafiyar kusan minti sha biyar suka kara ganin inda suka nufa ta kallesa da sauri tace "Ina xaka kai ni?" Yace "Home, its late kar a neme ki, nasan yanxu ai so called yayan naku ya wuce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da driving, girgixa kai tayi a hankali tace "Ni baxan je gidan ba" Da mamaki ya juya ya kalleta, yace "Baxa ki je gidan ba kuma?" Ta gyada masa kai, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai kawai baxan je ba" Yace "Did you have any other guardians in Abuja" Ta kallesa tayi shiru, sai kuma tace "Ban san kowa ba" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tukin, Kuka sosai Heedayah ta fashe masa ganin sun kusa layin, hakan ya basa mamaki sosai ya samu gefe ya tsaya yace "Are you alright Heedayah?" Cikin kuka tace "Plss kar ka mayar da ni don Allah" kasa ce mata komai yyi yana kallonta, can yace "Me suka maki da baxa kije gidan ba" Tana share hawayen dake xuba idonta tace "Ni dai ban so, don Allah kar ka mayar da ni" He was lost of words don sai kallonta yake, ganin yanda take kuka yace "Talk to me Heedayah, sun maki wani abu a gidan ne?" Ta hade kanta da gwiwa tace "Ni basu min komai ba, bana son in je kawai" ya jingina da seat dinsa yace "To ina xan kai ki yanxu?" Cikin rawar murya tace "Ka tafi da ni kawai" yace "In tafi da ke ina?" A hankali tace "Inda xaka je" Jin shirun yyi yawa ya sa ta dago tana goge hawayen idonta, kallonta taga yake yi, ya kamo hannunta a hankali yace "Noo Heedayah, you need to go back home, xa su yi ta nemanki...." Ta fixge hannunta tana masa wani kallo tace "Ni baxan je ba nace maka, kuma ka ajiye ni a nan kawai inyi wucewa na" Da mamaki yace "Ki tafi ina?" Kokarin bude motar ta fara yi tace "Ni ka bude min" ya jawota yace "But Heedayah, what just came over you, Ina kike son in kai ki da daddaren nan, kince min baki san kowa ba a garin nan banda gidan warce ku ka xo, to ina kike son in kai ki kuma" Kuka kawai take masa xata kwace hannunta, ya jawota kusa da shi yace "Ki gaya min me aka maki a can gida" turasa tayi tace "Nothing I said, ni ka bude min in sauka" Khaleel couldn't stop looking at her, ganin ya ki bude mata motar ta hade kai da gwiwa. Har karfe goma saura Farida da Yayarta suna xaune parlor sun yi jigum, Farida ta san kiris ya rage yayarta ta kira Mami don ta cika daga xaunen da take, Farida ta dau wayarta duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, bude ido tayi tunawa da tayi ai ta ba Heedayah wayarta suna tahowa a mota daxu tayi ma Khaleel din message, shiga message tayi da sauri tana dubawa taga bbu message din sabon number, alamar Heedayah ta goge text din gaba daya, Number Shuraim ta duba duk da bata yi saving ba amma ita ma ta so haddacesa tunda bashi da wahala, tayi dialing number har ya katse bai dauka ba, ta sake kiransa, nan ma bai dauka ba, sai gashi ya kira, dagawa tayi ta kai kunne, da farko ta rasa abinda xata ce sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, shiru tayi, yace "Wacece?" Mikewa tayi ta mika ma Maman Fadil wayar tace "Don Allah aunty kiyi masa magana ni ban san me xan ce ba" Maman Fadil ta jefa mata wani kallo tace "Waye?" Farida tace "Ya Shuraim" amsar wayar tayi ta kai kunne hade da yi masa sallama, bbu bata lkci tayi masa bayanin komai cikin few minutes, shirun da taji yasa tace "Hello" Shuraim yace "Ina ji, and she is not yet back har yanxu?" Maman Fadil tace "Wllh kuwa, ni tunda nake ban ta6a ganin haka ba ma, har nawa take xata yi wannan aika aikan, Ina ta bi sa suka tafi, ni gashi ko abinci na kasa ci har yanxu, ta ina xan fara yi ma Mami bayani, me ma xan ce mata??" Shuraim gaba daya ya rasa abinda xai ce, don basu kai sa mamaki ba ma, can yace "Ba wa Farida wayar" Mika ma Farida wayar tayi, Farida ta amsa ta kai kunne, Yace "All this while dama akwai waya a hannunta" Farida ta koma ta xauna ta rasa abun cewa, yace "Baki ji na ne?" Tace "Nima ban sani ba...." a fusace Maman Fadil tace "Munafuka kika ce baki sani b, wllh tana sane ita ma munafukar ce ai, kuma kema ta ja maki matsala tunda kike boye abinda take yi" Shuraim yace "Waye shi Mutumin??" Farida tace "Ni fa ba gaya min komai take ba" Katse wayar Shuraim yyi ya mike daga kwancen da yake, ya dau makullin motarsa ya fita. Khaleel bbu irin lallaba Heedayah da bai yi ba ya mayar da ita gida amma kememe ta ki, har sannan suna tsaye gefen hanya a motarsa sai kallonta kawai yake, ji yyi tace "To naji xan tafi gida, amma ka sauke ni in karasa da kafa kar ka kai ni street din" Yace "But it's late and they are dogs everywhere...." tace "Ni kuma a nan xaka ajiyeni nace" yace "In ajiyeki ki tafi wani waje kenan?" Ta kallesa tace "Ehh, don baxan koma gidan ba" ya fi minti uku yana kallonta kafin ya tada motar ya fara tafiya, har ya dau hanyar gidansa sae ya tuna abinda Zayyad yace masa daxu, can kuma kawai ya nufi gidan nasa. A cikin motarsa ya ciro makullin gate din gidan, ya sauka ya bude gate din, Heedayah sai bin anguwar that is so quiet ta ke da kallo har ya dawo cikin motar ya shiga, a parking lot ya tsayar da motar ya kashe ya sauka ya koma gate din ya kulle da makulli snn ya koma gun motar yana kallonta yace "Are you satisfied now?" Ta gyada masa kai yace "To sauko" bude motar tayi ta fito tana bin gidan da kallo tace "Gidansu waye?" Yyi shiru yana kallonta, ganin ynda take kallonsa a hankali yace "Gidanmu ne" tace "Mum dinka da Dad and siblings suna ciki" Yace "No" tace "Why? Where are they?" Kulle motar yyi bai ce mata komai ba, ya nufi entrance din katon gidan, ta bi bayansa tace "You are not saying anything?" Yace "Duk basa nan" tace "To ina suka je" Yace "Gobe xa su dawo, they travelled" tace "To ni da kai kawai xa mu kwana gidan?" Bai ce mata komai ba ya sa makulli yana bude kofar parlon, tace "Ehh??" Sai da ya bude kofar snn ya juyo yana kallonta yace "Aa da mutane" daga haka ya shiga parlon yana haska fitila da wayarsa ta bi bayansa, a hankali tace "Ni tsoro nake ji, babu wuta?" Yace "xan kunna yanxu" Ajiye

Please Login or Register in order to submit comment