Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma ta xauna tace "Why secret Heedayah? Xa ki ci gaba da alaka da d'an kidnapper ne? What will be our faith?" Heedayah ta fashe da kuka tace "Not at all, baxan ci gaba ba, amma...." Farida tace "Amma me?" A hankali Heedayah tace "Yasa na fara sonsa, I don't know how that happened all of a sudden, ya cuceni ya sa min sonsa" Farida ta xaro ido tace "So xa ki ci gaba da sonsa kenan???" Da sauri Heedayah ta girgixa kanta tace "I hate everything about him now, he is disgusting, I now understand why I saw gun with him a gidansa ranan da daddare, I now understand why he is this rich with so many cars and houses, I now understand me yasa baya son daga kiransa a gabana, I now understand why yake yawan ce min I shouldn't leave him no matter the circumstances, but I have to leave him, kuma na bar sa har abada, na tsani komai nasa, nayi da na sanin sake haduwa da shi da kulasa da nayi, dama shi ya rabani da iyayena tun ban san kaina ba, ya kuma maida ni wajensu after many years sbda selfish interest dinsa" kuka take sosai tana girgixa kanta, Farida ta kamo hannunta amma ta rasa abinda xata ce mata, ita ma hawayen take sosai don tun ba yau ba tasan Heedayah ta fada son wnn mutumi, Mikewa Heedayah tayi ta tafi gun kayanta ta fara hadawa tace "I will be leaving with Ammi today...." Jikin Farida yyi sanyi sosai sai a snn ta gane sbda Khaleel Heedayah tace baxata koma Kano da Amminta ba after her graduation, sbda tana anticipating dawowarsa. Da ido kaka ta dinga bin Shuraim da ya gama saka kayansa a jaka tace "Yau naga jaraba ina ta magana mutumi ya mayar da ni mahakuciya, dubi fa yanda ka zabge kamar me wata cutar can warce bamu sani ba, tunda iyayenka gantalallu ne ai ni ba gantalalliya bace baxan bari ka cutu ba, idan ma wani abun ke damun ka sai ka gaya min in san nayi tun wuri, bbu wajen wani shegen aiki da xaka koma, to banda kai wa ke gareni a duniyar yanxu, dama ni da kai nafi sabawa a kan su Amadu ma, kawai shaidan ne ya shiga tsakaninmu, shekarunka nawa a wajena kafin algungumar uwarka ta amshe ka ta karfi da yaji" Shuraim ya juya yana kallonta yace "Ba abinda ke damuna, bana jin dadi ne kawai, Amma yanxu Alhmdllh, xan koma bakin aikina" ta mike tace "Allah ya tsine ma aikin, idan ma xaka bini in kaika asibiti ka bini wllh, tunda shi Umaru bai daga kirana ba shi yasani, shi kuma Amadu xai ga barbadin bala'i yanxun nan kuwa" daga haka ta fice daga dakin, xaunawa Shuraim yyi gefen gado jin kansa na juya masa ya dafe kan xuciyarsa na bugawa, kaka na shiga parlon Abba ta samesa ya gama shiryawa xai wuce aiki, cike da bala'i tace "Amadu ba gwara abu ya sameka ba da ya samar min Shureen, uban me ka ta6a tsinana min tunda na haifeka dama, wato bakin ciki da rayuwar da Shureen ke yi a duniya kake yi ban sani ba, ban da bakin ciki ya xa ayi d'an ka bashi da lafiya amma ko a jikinka ka wani shirya xaka fita inda ku ke giggilla karyar ku..." Abba dai kallonta yake kafin yace "Baaba Shuraim ba yaro bane, idan yana ga barin damuwarsa a xuciyarsa ne mafi alkhairi garesa ba sai a kyalesa ba" Kaka tace "To anki kyalesan, kuma aniyarka ya bika wllh, in sha Allah bbu abinda xai samar min shi...." Abba ya d'an yi murmushi bai dai ce komai ba, sarai yasan meye damuwar son din nasa, ta juya ta fice daga parlon ta koma dakin Shuraim, Mumy dai na ta xaune main parlor tana ta addu'ar Allah ya sa son Heedayah ne ya sa shi damuwar nan, kuma Allah ya sa ya sanar ma kaka komai ya xo cikin sauki kenan. Zayyad ne durkushe an daure hannunsa da igiya ta baya, oganninsu ne tsaye kansa ko wanne na nuna sa da bindiga, Zayyad ya kalli sauran colleague dinsa dake tsaye gaba daya a katon parlon, Oga Manga ya karasa gaban Zayyad da katon muryarsa yace "Brainiac ya sauka kasar nan jiya, yana ina??? We are asking you this for the last time Zayyad" Zayyad ya juya da jajayen idonsa yana ma Salim wani irin kallo, Oga Arne ya kai masa kyakkyawan naushi a fuska cikin tsawa yace "Baxa ka bamu amsa ba??" Zayyad yace "Ni bamu hadu da shi ba har yanxu Oga, na gaya maku kun ki yarda" Oga Bala na nuna masa wayarsa yace "Amma kun yi waya ko...." Zayyad ya kalli wayarsa da Ogan nasa ke nuna masa yace "Ehh" Oga Manga yace "Ina yace maka yake?" Zayyad yace "Naje gidansa kamar yanda ku ma ku ka je, ban samesa ba gidan a kulle yake" Salim yace "Amma a waya daxu yace maka xai je gidan budurwar tasa" Zayyad ya sake jefa masa wani kallo, Oga Arne ya hauresa yace "True or false??" Zayyad yace "Ai ban san gidan ba nima" Oga Arne yyi wani dariya ya koma kan mighty chair dinsa ya xauna ya daura kafa daya kan daya yace "Ku tafi da shi ku tabbatar ya fadi inda gidan yake, snn a tafi a dauko mana mahaifiyar ita yarinyar yau din nan" Wani kara Zayyad yyi ya buga tsalle ya dawo da hannunsa dake daure ta baya gaba, ya haure Oga Arne dake kan kujera da kafarsa snn yyi hanyar bedroom da gudu ya bude wani daki ya shiga ya sa makulli yana huci, da sauri ya tafi gaban mirror ya fiddo karamar wayarsa ya shiga dialing number din Khaleel, yana jin suna kokarin balle kofar gaba dayansu, har wayar ya katse Khaleel bai dauka ba, gaba daya Zayyad ya hada xufa, ya sake kira praying hard Allah ya sa Khaleel ya dauka sai gashi ya dauka, da sauri Zayyad yace "Brainiac ka dauke Barrister din nan a gidanta with every other person, su Oga Arne xa su je gidan yanxun nan, I am giving them the address nowwww....." yana fadin haka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar ta bayan mirror ya durkusa a dakin ya sunkuyar da kansa kasa, suna 6alla kofar Zayyad ya dago da sauri nan ya zayyano masu full address din gidan Mami ya kara da cewa "Xan iya kai ku gidan ynxu ma...."








Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Heedayah dai taki yarda ta dago kanta, Mami tace "Wai baxa ki bani amsa ba?" Ta dago a hankali tace "Mami nace ba komai, kaina ne ke min ciwo" Mami ta hade rai tace "Ciwon kan yasa kika yi kuka har idonki ya kumbura?" Heedayah ta marairaice tace "Yayi min sauki ynxu Mami, ask Farida" Farida dai na xaune can karshen gado tana danna wayarta bata ce masu komai ba, Mami tace "Toh yayi kyau, keep on lying, and why did you change your mind about going to kano with them?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami sati daya xan yi in dawo in sha Allah, kawai dai ina son in je" Mami dai bata kuma ce mata komai ba ta fita dakin, Heedayah ta goge guntun hawayen idonta, Farida ta mike ta dawo kusa da ita tace "Heedayah me yasa baki son gaya ma Mami, why are you hiding this serious issue from her" Heedayah ta kalleta bata ce komai ba, Farida tace "It's better ki gaya mata, kinga she likes the guy, gwara ta sani tun wuri wllh, damuwata daya yanxu ya san gidanmu, I don't think we are safe anymore" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Heedayah na ci gaba da share idonta tace "Tun da ya san na sani ynxu baxai sake xuwa nan ba, and just watch and see" Farida tayi mata wani kallo tace "Wa yace maki?? Mutumin dake son ki, snn sbda son da yake maki har ya tona ma kansa asiri ya gaya maki shi wanene, ae wlh baxai ta6a daina bibbiyar ki ba, tafiyar ki kano shine kadae mafita gare ki" Heedayah tace "Wait Farida, is he even crazy to come back bayan ya riga yasan na san komai a kan sa ynxu??" Farida tace "Ke baki san so ba ko?? Wllh ko xaki tona masa asiri in dai yana son ki da gaske baxai daina bibiyar ki ba" Heedayah ta hade rai tace "Then he will be playing with fire, I will have to expose him to everyone" Farida tace "Exactly Heedayah, yanxu ki tashi mu je ki sanar ma Mami first..." Heedayah tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta mike ta kamo hannunta, xame hannunta tayi cikin sanyi tace "Baxan iya ba Farida, kawai let just leave him, I don't want anything to happen to him ta dalilina, ni nasan baxai ma sake dawowa ba" Farida tayi shiru tana kallonta. Mami ce tsaye dakin da Yakumbo ke ciki tana xuge handbag dinta tace "Toh ni yanxu wa xai kai ni can gidan lauyan??" Mami tace "Driver xai ajiye ku yanxu" Yakumbo tace "Ya san gidan ne?" Mami tace "Aa tare da Heedayah xa ku je" Yakumbo tace "Toh ni dai Allah ya rufa mana asiri kada tafiyar nan ya sha ruwa yau, ita Aisha na can tana xaga Kaduna da sojoji bata da niyyar dawowa, komai dai sai an bata ma mutum rai, amma ba laifin kowa bane laifin Amadi ne" Mami dai bata ce komai ba ta fita su Ashfah da suka makale mata na biye da ita, bbu abinda suka mance na Heedayah yaran kawai dai ta fi su haske, dakinsu farida Mami ta shiga, Mami na kallon Heedayah tace "Idan kin ga dama kin gama kukan iskancin naki sai ki shirya ki raka Yakumbo gidan Abban ki...." Da sauri Heedayah ta juyo tana kallonta tace "Gidan Abba kuma, Ba yanxu xa mu tafi ba Mami?" Mami tace "Wannan kuma ban sani ba" Heedayah tayi shiru, Mami ta juya ta fita dakin, Bata fuska Heedayah tayi ta rungume hannu, Farida dai na tsaye jikin window tana kallonta, bayan minti kusan goma Yakumbo ta leko dakin tace "Toh ni dai idan baxa ki je ba ai sai yar uwarki ta xo ta rakani, bbu ruwana da wahala..." Heedayah ta kalli Farida tace "Farida ki rakata ni kaina ciwo yake min wllh" Yakumbo ta rike ha6a tace "Ga dukkan alama Rahinah ta sangarta ki, kuma wnn wlh ba halin xaman gidan miji bane, kaji min fitsararriyar yarinya kawai" Heedayah bata ce mata komai ba, Yakumbo na kallon Farida tace "Kinga shirya ki rakani kin ji yar nan" Farida tace "Toh" Yakumbo ta fice daga dakin ta koma gun Mami, Mami tace "Baxa ki ci abincin ba kafin ki tafi?" Yakumbo tace "Kyaleni da abincin nan ke dai, amma a gaskiya wnn Heedayar taki bata da hali ko kadan, ga rashin kunya fal cikinta, wai yarinyar ta dubi tsabagen idona tace ita baxata ba sai dai Farida ta kai ni, irin tarbiyar da kika mata kenan??" Mami tace "Kiyi hakuri bata jin dadi ne, amma dole ma xata bi ki" Yakumbo tace "Aa ba ruwana, ta sha xamanta ni Faridar ma ta fi min sau dubu" Mami ta fita dakin ta koma dakinsu Farida, fuska daure tana kallon Heedayah tace "Tashi ki shirya ki fito ku wuce" Heedayah ta mike bata ce komai ba ta tafi press dinsu ta bude ta fiddo hijab dinta har kasa, Farida ta bi bayan Mami bayan ta fita, parlor ta sameta tace "Mami can I go with them?" Mami tace "Kince kina da lectures by 2, but if you want to go, you can" Farida tace "Toh Mami" daga haka ta fita, Nikab Heedayah ta saka ta fito parlor tare da Farida, Yakumbo tace "Allah ya kiyaye, uban wa xa ki bi a haka?" Mami dake parlon ita ma a xaune tace "Da shi take fita Yakumbo" Yakumbo tace "Toh ai ba da shi na ganta jiya a gun taron ba, Kai ni fa idan ma xata ce ba nice yar ubanta ba bbu abinda ya sha min kai" da turanci Mami tace ma Heedayah ta tafi ta cire Nikab din, ba musu Heedayah ta koma ta cire snn ta dawo, gaba daya bata da walwala, motar sojoji guda ne a layin tun xuwan su Amminta gidan Mami jiya, Heedayah dai na xaune bayan mota tare da Yakumbo, Farida kuma ta shiga gaba suka bar layin. Suna isa gidan Abba mai gadi ya bude masu gate, driver ya shigar da motar yyi parking, Heedayah ta sauka snn Farida, Yakumbo ma ta sauka tayi hanyar cikin gidan suna biye da ita... Mumy ta fito daga kitchen kenan suka shigo parlon, ganinsu ta baje fara'a a fuskarta tace "Sannun ku da xuwa" kallo daya Yakumbo tayi mata ta nufi kujera tana cewa "Ina patun take?" Mumy na ta murmushi ta karaso cikin parlon tace "Ta je gida, Amma yanxu xata dawo" Yakumbo tace "Ya mai jikin?" Mumy tace "Da sauki Alhmdllh, yana cikin daki, Heedayah rakata dakinsa" sosai Heedayah tayi mamakin abinda Mumy tace, ta dai gaisheta tare da Farida, Mumy ta amsa tana washe baki tace "Ki kai ta dakin Shuraim" mikewa Heedayah tayi ta nufi dakin Shuraim Yakumbo na biye da ita a baya, ta bude kofar dakin ta tsaya nan bakin kofa ta ki shiga, Yakumbo ta shige dakin tana kallon Shuraim dake kwance yyi rub da ciki yana bacci, he looks so sick and tired, Yakumbo tace "Toh kai kuma ya da kwanciyar 'yan wuta, cuta ai ba mutuwa bace" Shuraim ya bude ido a hankali, ganinta tsaye dakin ya mike xaune da kyar, Yakumbo tace "Sannu, ya jikin?" Ya gyada mata kai yace "Da sauki, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, me ke damun ka haka?" Murya can kasa yace "Na ji sauki" Ta xaro ido tace "A haka?? Toh Allah ya sauwake, amma wnn kam ai kana jin jiki...." Ya daga kai ya kalli Heedayah da ta ki shigowa har sannan, suna hada ido ta sauke kanta tace "Ya jiki" Bai amsa ba ya cire Duvet din jikinsa ya saukar da kafafuwansa kasa, Yakumbo tace "Tana maka ya jiki" ya daga kai ya kara kallonta yace "Fine" Yakumbo ta kyabe baki ta nufi kofa tana cewa "Ita ma ai bakin halin gareta" da sauri Heedayah ta bi bayanta bayan ta fita ta kullo masa kofarsa suka koma parlor, Mumy tuni ta ajiye ruwa da lemo har da abinci a kasa kusa da kujeran da Yakumbo ta fara xama, Yakumbo na kallon abincin tace "Aa mu mun ci abinci kafin mu fito, kamar dai ana yunwa" Tana fadin haka ta matsar da abincin gefe ta xauna tace "Me ke damun shi Aliyun haka?" Mumy tayi kasa da murya tace "Wllh bamu sani ba, ya ki fadi...." Yakumbo tace "Toh ba a je asibiti bane?" Mumy tace "Yayan Abbansa ya xo daxu yyi masa allura ma, toh shine yake ta bacci tun daxun, yana dai complain din ciwon kirji" Yakumbo tace "Toh Allah ya sauwake, ita patun yanxu xata dawo kuwa?" Mumy tace "Ehh taje yi masa girki ne kafin ya tashi wai, na ma ce ta barsa gashi nayi amma ta ki saurarata" Yakumbo tace "Toh ai da kince mana yana bacci da bamu tashe sa ba yyi baccinsa isasshe" Mumy dai sai murmushi take bata ce komai ba, Farida dai idonta na kan TV da gaba daya bata san abinda ake ba, Mumy ta mike ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da cup din shayi ta nufi Heedayah dake xaune ta mika mata tace "Tunda ya tashi gashi ki kai masa, tun safe bai ci komai ba, Allah ya sa ya sha wnn din ma" Heedayah ta d'an buda ido tana kallonta, ganin mika mata dai Mumy ke yi ta amsa ta kalli Farida dake kallonsu, Yakumbo tace "Toh ko baxa ki kai masa din bane tunda kunya bai isheki ba, sai Farida ta amsa kawai ta kai ita" Heedayah ta d'an hade rai ta mike ta nufi dakin, Farida ta bi ta da ido, a hankali ta bude kofar dakin tana kallon ciki, xaune ta gansa yanda suka barsa ya rike kansa da duk hannunsa biyu, jin an bude kofa ya dago sai dai bai kalli kofar ba, ta shigo dakin ta ki kulle kofar, kamar warce aka tilasta tafiyar ta isa inda yake xaune tace "Mumy tace in kawo maka" Jin yyi shiru ta durkusa ta ajiye masa cup din tea din, ta mike xata fita taji yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba gabanta na faduwa, bayan few seconds ta juyo a hankali tana kallonsa.... Bayan tafiyarsu Heedayah kafin azahar Ammi ta dawo gidan, Mami na kallonta tace "Amma dai bbu tafiyar ta ku yau ko?" Ammi tace "Ehh wai Aliyu bashi da lafiya daxu Abbansu Islam ke gaya min, kuma Yakumbo ma taje can gidan ko?" Mami tace "Ehh tana can da su Heedayah" Ammi tace "Dole sai gobe kenan xa mu tafi, anjima daddare xan je dubasa idan Allah ya nufa" Mami tace "Allah ya kai mu, xan d'an fita in dawo yanxu Maman biyu" Ammi tace "Toh shhkn Allah ya tsare hanya" Hijab Mami ta sa har kasa ta dau wasu files Ashnaah ta fara kuka xata bi ta, Mami ta kama hannunta suka fita, Abba take son kai ma files office kamar yanda ya bukata, bayan tayi warming motarta ta fita gidan tare da Ashnaah dake xaune front seat.... Mami na fitowa daga layin, aka sauke glass din wata farar mota dake parke nesa da layin, Oga Manga ya kalli Zayyad dake gefensa cikin motar yace "Ita ce wancan?" Zayyad yace "Aa...." Wani naushi Manga ya kai masa yace "Ba matar nan muka tarar asibiti a Abuja ba??" Zayyad yyi shiru a ransa yana mamakin me yasa Khaleel yyi ignoring din message din da yyi passing masa ta waya da safe, Wani naushin Manga ya kai masa, Zayyad yace "Ita ce" tada motar Salim yyi suka bi hanyar da Mami ta bi a guje kafin Wani barrier ya shiga tsakaninsu, Mami na isa office din Abba tayi parking waje ta dau wayarta ta kirasa don ya fito ya amshi envelope din hannunta don baxata shiga ciki ba, Ashnaah dake xaune tace "I want to ease my self..." Mami ta kalleta tace "Ohk" daga haka ta bude motar ta sauka ta rufe ta xagayo ta inda take ta bude motar ta sakko da ita, A bayan motarta su Manga suka tsaya da tasu motar, duk da ta ga motar bata kawo komai ba ta xata client din Abba ne, Manga na kallon Fago yace "Kayi attacking yarinyar karama first...." Fago ya dira motar ya nufi Mami da ke daga kayan Ashnaah, lkci daya ya fiddo bindigarsa ya daura mata a kai yana kallonta da masked face dinsa, Xaro ido Mami tayi tana kallonsa kafin tace komai ya fixge Ashnaah daga hannunta xai koma motarsu ta bisa a rikice yana ganin haka ya bude motar ya jefa ma Manga Ashnaah, Manga na kallonta yace "Ki shigo idan kina son yar ki da rai...." Ai Mami bata san lkcn da ta shiga motar ba, ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, a rikice take cewa "Ku fadi abinda ku ke so daga gareni amma ku rufa min asiri kar ku tafi da 'yar mutane..." tuni Fago ya rufe motar ya shige gaba Salim ya tada motar suka bar wajen a guje, Zayyad dai ya sunkuyar da kansa ya kasa dagowa, Ashnaah ta haye jikin Mami a tsorace tana kuka sosai don gaba daya fuskarsu a rufe yake, Mami ta rungumeta har ranta taji farin cikin ba Ashnaah kadai xa su tafi da ba har ita....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....








Khaleel na kwance saman 3 seater a parlonsa, yyi nisa tunanin da yake idonsa na kan pop din parlon, a hankali ya juya yana kallon wayarsa da yyi vibrate a gefensa, ganin me kiran nasa ya ki dauka har ya katse, sake kira aka yi, ya mike xaune da kyar ya daga kiran yace "You called bana jin ka daxu kuma ka kashe waya gaba daya, What's up?" Muryar Oga Arne ya ji yana dariyar bosawa, Khaleel yyi shiru ya sake kallon screen din wayar yaga number Zayyad ne ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar nan gefensa ya koma ya kwanta ya lumshe ido xuciyarsa na bugawa.... Mami na kallon katti ukun dake kanta a tsaye cikin wani daki ko wannensu rike da bindiga, tana son magana amma ta kasa cewa komai sai hawaye, Ashnaah ma sai kuka take tana shigewa jikin Mami, fuskarsu dake boye cikin face mask shi ke kara tsorata yarinyar, cike da karfin hali Mami tace "Ku fada min me ku ke so daga gareni?" Bbu wanda ya tanka ta cikinsu da alama gadinta kawai aka ajiye su suyi, Ta rungume Ashnaah tana lallashinta tana karanto addu'o'i a xuciyarta na neman tsari da sharrinsu. Shuraim bai yarda ya hada ido da Heedayah dake tsaye tana kallonsa ba yace "Close the door" ta kalli kofar sannan ta kallesa, kin xuwa ta kulle kofar tayi kuma bata ce komai ba, ya kalleta suka hada ido yace "Baki ji me nace bane?" Tace "Toh saboda me?" Mikewa yyi ta koma gefe da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka, ya isa gun kofar ya kulleya juyo yana tsaye wajen yace "I want to ask you 2 to 3 questions" Ta d'an yi shiru, sai kuma ta gyara tsayuwarta tace "Ina ji" Ya jingina da kofar bai yrda sun sake hada ido ba yace "And promise to say the truth... Nothing but the truth" ita dai tayi shiru tana jin sa, yace "Kin tuna lkcn da Abba ya kawo ki gidanmu ko?" Ta gyada masa kai, yace "Good, daga lkcn xuwa ynxu shekara nawa kenan?" Still not looking at him tace "Shidda" Yace "Alright, a cikin shekara shiddan nan can you plss remind me ko na ta6a cutar ki?" Kura ma carpet din dakin ido tayi trying to digest what he just said, bata san lkcn da tayi murmushi ba don ba karamin dariya tambayar ya bata ba, yana kallonta ce "Ina sauraron ki" tace "Wani irin cuta kenan?" yace "Duk abinda a tunanin ki cuta ne" tace "Ni na manta" Yace "Baki manta ba, bani amsata" Tace "Toh idan ma conscience dinka na judging dinka ne sbda abubuwan da yasan kayi, duk da ni dai manta pass dina balle in tuna abinda aka min, to I've forgiven you" Yace "My conscience can never judge me don nasan ban maki komai ba duk Shekarun nan...." Tace "Toh me ya kawo maganan nan yanxu idan kai kasan baka ta6a min komai ba?" Yace "Like, kina min kallon kamar wanda ya cuceki a rayuwar da kika yi gidanmu, always frowning when ever u see me, and many of that" Da mamaki take kallonsa tace "To dama mun saba magana ne da kai balle kace Ina frowning? I've known you to be someone that don't bother about others, baka shiga harkan kowa, kowa ma baya shiga naka harkanka, to me yasa xaka yi tunanin xan dinga shiga harkan ka yanxu?" Shiru yyi yana kallonta, can yace "Kin fahimci haka nake yi ma kowa kenan" A takaice tace "Ba kowa ba, ai kana sake ma cousins dinka, ur sisters idan sun gaisheka kana amsawa, kana siya masu abubuwan da ya kamata...." Yace "Ke kuma fa?" Ta d'an kallesa tace "Do I need to tell you that" Yace "Bana maki abubuwan duk da kika lissafa kenan" ta buda hannu yace "You've said it" komawa yyi gefen gadon ya xauna yyi shiru, bayan minti uku tana kallonsa tace "Can I go" ya dago ya kalleta, a hankali

Please Login or Register in order to submit comment