Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan. Sosai jama'ah suka cika gidan biki ana ta shagalulluka a katon tsakar gidan, lallai taron ya amsa sunansa na Mother's day, don iyaye ne mata sun yi shiga ta kece raini, can Heedayah ta hango kaka cikin jama'ah yanda ta kankance ido ya isa kasan cewar ba maganar arxiki take masu ba a can don wasu sai tabe baki suke, Heedayah ta bi bayan Mami da Farida da suka shiga parlon, Hajiya Hauwa na welcoming dinsu, kiris ya rage ta ci karo da Mumy da ta mike xata bar parlon cike da isa don bai ma Mami access din ganin kwalliyarta da gwalagwalanta da kyau, Heedayah ta koma baya tayi kasa da kai ta bata hanya tace "Ina yini" Ko kallonta Mumy bata yi ba ta wani daure fuska ta fita parlon Heedayah ta shiga a sanyaye, da fara'a Step mum din Sudais ta amsa gaisuwan Farida da Heedayah sannan tace "Ga can Sudais xai ajiye su Zainab saloon ku bi su ku ma kuyi gyaran gashi" da sauri Heedayah tace "Aa gashin mu a gyara yake ai" Mami ta juya tana kallonta, Farida tace "Toh bari mu je Mama" Hajiya Hauwa tace "Su Zainab din na daki ku tafi ku samesu sai ku wuce tare" Farida ta tafi inda Hajiya Hauwa ke nuna mata, Heedayah ta turo baki ta bi bayanta ranta bai so ba, Zainab 'yar Hajiya Hauwa ce, sai Jamila daya daga amaren, Daya Amaryar Safiyya dakinsu daya da Sudais sai Nafisa da Aisha, Zainab da Rabi'ah da Khadijah kadai xa su tafi saloon din don sauran sun je jiya tare da amaren, sae ynxu da Heedayah da Farida xa su bi su, Zainab na ganin su Heedayah tayi welcoming dinsu da fara'a tana masa sannu da xuwa, Aisha ma dai tayi masu sannu da xuwa sama sama, amma Nafisa tayi kamar bata gansu ba ballantana Rabi'ah da Khadijah, a haka dai har Sudais ya kira Zainab yace yana jiransu a waje, Zainab ta mike tana kallonsu Farida tace "Mu je yana jiranmu a waje" har ta fita ganin Rabi'ah da Khadijah basu fito ba ta dawo tace "Yana fa jiran mu a waje" Khadijah ta wani yatsine fuska tace "Ku je ku, anjima xa mu je wani saloon din" Zainab bata ce komai ba ta fita, a parlor Hajiya Hauwa tace "Ina sauran fa" Zainab tace "Wai baxa su ba" Mumy da shigowarta parlon kenan ta xo debar ma bakinta lemo tace "A kan me baxa su je ba??" Zainab tace "nima ban sani ba" da haka ta fita Farida da Heedayah na biye da ita, Mumy ta wuce sama fuskarta a tamke tana cewa "Bari in kira driver na ya xo ya kai su saloon din, ai ba dole dama su bi ku ba, ko wani saloon din ne sai ya kai su yanxu" Hajiya Hauwa dai bata ce komai ba balle Mami dake parlon. Zainab ta shiga front seat Heedayah da Farida suka shiga baya, Sudais ya amsa gaisuwarsu gaba daya yana kallonsu ta madubi yace "Yaushe ku ka xo?" Farida tace "Ba dadewa" yace "I see, ku ma xa ku yi gayun kenan" dariya kawai Farida tayi, ya kalli Heedayah da tayi shiru yace "Cutie kema gyaran gashin?" Murmushi tayi ta sauke idonta kasa tace "Uhn" yace "Toh idan kun dawo anjima sae a nuna min gashin in gani" Nan ma bata ce komai ba sai murmushi, sai da suka yi nisa Sudais ya d'an kalli Zainab yace "Wai su Rabi'ah sun fasa xuwa ne" Zainab tace "Ehh wai anjima xa su taho" yace "Ohk then" yana ajiye su saloon din ya ba Zainab kudin gyaran gashin nasu da kudin adaidaita da xai maida su gida sannan ya wuce. Sai kusan Magrib su Heedayah suka dawo gida, basu tadda Mami a gidan ba, Heedayah na kallon Farida da ta amshi gugan tiles din da kaka ke yi a dakinta tace "Toh mu wa xai kai mu gida?" Kaka ta juya da sauri tana kallonta tace "Wa xai kai ku gida kuma? Ba lafiya, Nan ba gida bane? To nice nan nace Rakiya tayi wucewarta kuna nan har bayan biki tunda ita baxa ta tsaya ba, idan ma ita faridar taga baxata xauna ba to ke kina nan, nan ne dolenki" Heedayah ta xauna saman kujera kaman xa ta yi kuka, Farida dai bata ce komai ba. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh taji vibration din wayarta dake kusa da ita, bin dakin tayi da kallo, Farida da Zainab ne xaune dakin suna hira, sai wata yar uwar Umma dake dakin tana waya. Heedayah ta saka jakar cikin hijab dinta cikin dubara ta mike ta ta shiga toilet, ciro wayar tayi ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata ta amsa yace "Kince anjima xa mu yi magana kuma nake ta kiranki baki dauka ba" ta wani turo baki tace "Toh ni ai bana nan mun fita, kuma the phone isn't ringing" Yace "Ina kika je?" Tace "Saloon" yace "Why didn't you tell me?" Tace "How will I tell you?" yace "Call me" tace "A rufe wayar yake, you didn't tell me the password" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "I remember, so where are you now?" Tace "Gidan yayan Abbanmu" yace "A ina?" Tace "Unguwar rimi" yace "Wani layi?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Toh ki tambaya" a hankali tace "Toh" yace "I will call back in few minutes" tace "Tell me the password" yace "Sai na xo...." daga haka ya katse wayar, fita tayi bandakin ta xauna gefen gado, Farida dai ta kalleta bata ce komai ba suna ci gaba da labarinsu da Zainab, Bayan kusan minti biyar Heedaya ta kwanta tana kallon Zainab tace "Ya ma sunan layin nan sis" Zainab ta kalleta tace "Wai anguwar nan?" Heedayah tace "Ehh" Zainab ta gaya mata sunan anguwar, Heedayah tace "Ohk" bata kuma cewa komai ba tana ta kwance, sai taji wayar na vibrate, mikewa tayi tace "Bari in je in amso abinci am hungry" daga haka ta fita, can bayan gidan ta xaga bayan ta fita, ta daga kiran having making sure that bbu kowa wajen, nan ta gaya masa sunan layin yace "Ohk I am on my way" komawa tayi cikin gidan bayan ta mayar da wayar jaka, ta ki komawa bangaren kaka ta xauna parlor duk da akwai mutane, wasu na yanke yanken kayan ganye, kowa dai da abinda yake yi, bayan kusan minti sha biyar sai ga kiransa, da sauri ta fita ta daga kiran, yace "I am outside" sosai ta ji gabanta ya fadi, a hankali tace "Toh amma idan aka gan ni fa?" Yace "Babu wanda xai gan ki, ki fito" A hankali ta katse wayar ta mayar cikin jakar dake cikin hijab din jikinta sannan ta nufi gate tana yi tana waige waige har ta isa gate din xata fita, tana dube duben inda xata gansa, karo suka kusa ci da Shuraim da xuwansa gidan kenan, Suna hada ido ta koma baya a tsorace tana xare ido, juyawa yyi yana bin layin da kallo as if wanting to figure out something, suka hada ido da Khaleel da yyi parking daga daya side din kafin a iso dai dai gate din gidan, Khaleel ya fiddo wayarsa ya fara danne danne ya kai kunne, magana ya fara yi a wayar yana driving a hankali, har ya iso dai dai saitin Shuraim sannan yace "Ohhh ba nan bane? But I am seeing no. 28 here, ohk sorry 38, but wait.... can you plss come out ka daina bani wahala??" Sai kuma ya ja tsaki yace "kasan ba karamin aiki na bane in koma gida ko" yana magana yana tuki slowly har ya wuce Shuraim, Heedayah dake xare ido cikin rawar murya tace "Inn... Innaa yini" ya hade rai sosai yace "Ina xa ki?" Bakinta na rawa tace "Ruwa xan siya...." Yana mata wani kallo yace "Bbu ruwa a duk gidan sai kin fito siya?" Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai kamar kadangariya, yace "Go back inside now" juyawa tayi da sauri ta wuce ciki tana hade hanya, ya juya ya sake kallon motar ya gansa can tsaye 4 houses away, can wanda ke cikin motar ya sauka ya nufi me gadi dake xaune bakin gate din, sai kuma mai gadi ya bude masa gate ya shiga cikin gidan, Shuraim ya dauke kai ya shiga gida shi ma snn ya rufe gate din. Farida na balcony tana danne dannen wayar hannunta Heedayah ta wuceta sai a sannan ta bi ta da kallo, Shuraim ma ya wuce bata ce masa ba bai ce mata ba, mikewa tayi ta bi bayansu, Dakin kaka Heedayah ta shiga ta rakube can karshen gado har lkcn gabanta bai daina faduwa ba, kaka tace "Ga abinci ki diba ki ci, ni na rasa gane ko Rakiya bata baki abincin kirki ne, wnn sirancin haka ai yyi yawa kamar bafillatanar da shanu ya kare ma" Heedayah ta turo baki bata ce komai ba, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo, kaka ta dauke kai kamar bata gansa ba, dubu ashirin ya ciro aljihunsa ya mika mata yace "Abba yace a kawo maki" Kaka ta amsa ta kirga gaba daya sannan ta yashe kudin gefen gado tace "Ni dai na shiga uku, meye dubu ashirin kuma Allah na tuba, wnn ai baxai isa liki ba wllh, snn duk a ciki in ba bakina da suka xo kudin mota me yasa Amadu ke min haka ne ni" Shuraim dai sai kallon Heedayah ta gefen ido yake yi, don kai kana ganinta kasan bata da gaskiya sai wani kokarin boye jaka take a cikin Hijab nan kuwa vibrating wayar yake, Suna hada ido da shi ta daburce, can ta mike ta nufi kofa ta fita da sauri, kaka tace "Ni kawai a kira min Junaidu bani da kowa sai shi, shi daya xai fitar da ni kunyar likin nan da xan ma yara, da tsofaffin nan da suka xo min" Heedayah na fita dakin su Zainab ta wuce da sauri ta shige bandaki ta kulle, tunanin inda xata boye wayar jakarta take, ta fiddo wayar tana kalle kallen bandakin, window ta bude ta jefa wayar ta waje sannan ta fito bandakin.




_I want to alert those that didn't patronize the book Heedayah, pls and plss don girman Allah su rike sharhinsu su bar wa enda suka siya littafi su yi, baki siya littafi ba baxa ki xo kina gaya min abinda ya kamata inyi da abinda bae kamata inyi ba, littafin nan dai ba kyauta bane amma wasu a kyauta suke karanta shi comfortable hankali kwance, to su ji da wannan kawai ma mana_










Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....








Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....


Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍






Zainab ta mike jin ana knocking din kofarsu ta bude, ganin Shuraim tsaye bakin kofar tace "Ina yini Ya Shuraim" Aisha da Nafisa duk suka kame kansu a dakin kuma bbu wanda ya kallesa cikinsu, cikin few seconds ya gama bin dakin da kallo snn ya amsa gaisuwar Zainab yace "Lafiya" Heedayah dai na kwance saman gado tayi backing din kofar gabanta sai faduwa yake, karasawa cikin dakin yyi cike da kasaita ya nufeta yace "Bani jakar ki" kamar jira take ta mike xaune da sauri ta dau jakar ta mika masa, ya amsa ya bude ciki, bbu komai sai kudi da awarwaro with different chocolate, tunda ta mika masa jakar bata yrda ta kallesa ba, xuciyarta kamar xai fito don tsoro, ya jefar da jakar saman gado ya juya ya fita, Zainab ta xauna gefen Heedayah tace "What is he looking for?" Heedayah tayi tagumi tace "Ohon masa" Zainab ta tabe baki bata ce komai ba ta fita dakin. Har karfe dayan dare Heedayah bata yi bacci ba, amma bbu wanda xai ce ba bacci take ba, ita da Farida da Zainab sai Aisha ne a dakin, Mumy ta kwashi su Rabi'ah sun wuce gida tun karfe goma saura wai baxa su kwana gidan ba, a kashe wutan dakin yake almost an hour ynxu, kowa na dakin taji alamar yyi bacci, Heedayah ta sauka saman gadon a hankali ta nufi kofa ta bude very careful not to make any sound that will wake anyone sannan ta fita, bbu kowa parlon ta karasa tsakar gida taga har sannan murhu na ta ci ga manyan tukwane ana dafa kayan miya, sai da ta tsaya tayi naxarin inda xata bi snn ta xaga ta nemo dai dai windown bandakin su Zainab a bayan gidan, wayar na nan inda ta jefar amma screen din yyi raga raga ba na wasa ba, shi kansa wayar ya gurgurje, a hankali ta duka kamar xata yi kuka ta dau wayar tana jujjuyawa, har ranta taji ta tsani Shuraim din nan, meye xai wani sa mata ido, Ina ruwansa da ita wai ma, dudduba wayar tayi taga yana yi, ta turo baki ta xagayo gaban gidan ta shiga ciki ta koma can dakin da suke, a hankali ta bude press din su Zainab ta durkusa ta saka wayar a can kasan kaya sannan ta hau gado ta kwanta. Washegari juma'ah xa ayi dinner, Da rana duk 'yan matan suka shirya cikin daya daga ankon bikin, ana ta shagali a gidan, abinci iri iri aka girka ranan sae kace ranan ne yinin bikin, Duk Heedayah ta xo wucewa sai Mumy ta bi ta da kallo kmr idanuwanta xa su yi magana, duk inda ta bi idonta na kanta haka ma kawarta Sadiya, nan ko ita ta kagu a kare biki ta san na yi, ko kiris bata kaunar duk abinda xae sa Heedayah farin ciki, barin gashi ta ganta fes fes alamar hankalinta a kwance yake, ba komai ya kara tsaya mata a rai ba sai irin kyan da Heedayah ke da shi, wnn idan ta jera da su Rabi'ah sae a dauketa sau goma ba a daukesu sau daya ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya tana ci gaba da rabon abincin da take. Heedayah ta shiga daki dauko mayafinta xa su je dauko bak'i a bakin titi ita da Aisha kamar yanda Hajiya Hauwa ta umarcesu, Zainab ce kadai dakin duk kowa ya fita har ynxu tana make up, Zainab ta juya ganin Heedayah tace "Ke kika ajiye waya kasan kaya, yana ta vibrating??" Heedayah ta xaro ido a tsorace ta nufeta ta duka kusa da ita tace "Da gaske? How did you hear it?" Zainab tace "Kawai Ina son daukan takalmina kasan press din yanxun nan na ji vibration din sai na duba naga waya, and nasan Farida na tare da wayarta ynxun nn ta fita" Heedayah ta fara kalle kallen dakin, a hankali tace "Ke da wa ku ka ji vibration din plss?" Zainab tace "Just me, yanxu ma fa aka kira" Heedayah ta marairaice tace "Toh don Allah don't tell anybody about this Zainab, not even Farida" Zainab ta gyada mata kai tace "I am giving you my words" Fiddo wayar Heedayah tayi tana dubawa, Zainab tace "But saurayin ki ne ya baki waya kike boyewa" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba saurayina bane" Zainab tayi murmushi tace "Toh sai ki kira" Heedayah xata yi magana wayar ya fara vibrate kuma... Kallon Zainab tayi da sauri, Zainab tayi tagumi tana murmushi tace "Pick..." Tana fadin haka ta tashi ta kulle kofar dakin ta sa makulli, Heedayah ta daga kiran ta kai kunne, she could hear him suspire but still bai ce komai ba, a hnkli tace "Hello..." Cikin cool voice dinsa yace "Who was he Heedayah?" Heedayah tace "Yayanmu ne" Yace "Really?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Hope he didn't suspect you" a hankali tace "He did" yace "And how did it went?" Tace "Ni ba mu hadu da shi ba har ynxu" yace "Yaushe xa ki bar gidan??" tace "Kilan anjima da daddare" yace "Wa xai maida ki?" Tace "Daga wajen dinner xamu wuce gida" yace "Ke da wa?" Tace "Farida" ya d'an yi shiru snn yace "Ohk, where is the venue for the dinner?" Tace "Ban sani ba sai na tambaya" Yace "Do ask plss, Kar ki katse kiran kawai ki ajiye idan kin tambaya ki dawo" ta kalli Zainab da ke ta kallonta don tana jin komai da suke cewa, Heedayah ta cire wayar a kunne tace "Ina ne venue din dinner din?" Zainab ta gaya mata, Heedayah ta maida wayar kunne ta gaya masa, yace "Who did u ask?" Tace "My sis" yace "Ur sis??? Kuna tare ne?" Tace "Yess" yyi kasa da murya yace "Why?? You shouldn't have..." Sai kuma yyi shiru, can yace "Will call back later keep the phone close to you" daga hka ya katse kiran, Heedayah ta kalli screen din sannan ta kalli Zainab, Zainab tace "Waye shi? And why is he bothered because you are talking in front of me" Heedayah ta kirkiri murmushi tace "Sbda ya ga ina tsoro..." Zainab tayi shiru, sae kuma ta kalli Heedayah tace "But he shouldn't be bothered, idan yana son ki ya xo gidanku mana, why is he making it confidential??" da sauri Heedayah tace "Noo he isn't, and wllh ba saurayina bane, beside Mami will punish me if she gets to find out, kawai dai...." Zainab tace "Uhn kawai dai me?" A hankali Heedayah tace "Ba saurayina bane wllh" Farida ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, kamo hannunta Heedayah tayi tace "But promise me that you are saying nothing to anybody Zainab" Zainab tace "Trust me" Heedayah ta jira har Zainab ta gama kwalliyar sannan suka fita dakin. Da yamma ana ta shirye shiryen tafi wajen dinner da xa a fara bayan Magrib, Su Heedayah suka sa ankon lace dinsu tare da su Zainab duk suka yi kyau sosai, Su Rabi'ah dama wanda ya fi wnn tsada Mumy ta siya masu ga jaka da takalmi duk sababbi, Har sannan Farida ta ki yrda ta shiga harkan Heedayah a gidan, hakan ya d'an fara damun Heedayah don basu ta6a haka ba tunda suke amma dae bata ce mata komai ba, kuma bata da intention din ce mata dama. Ana ta kwalliyan tafiya dinner wajajen karfe shidda, mai make up aka kawo gidan tayi ma yan matan make up, Heedayah dai tace baxata yi ba, ana gamawa Zainab kwalliya aka hau yi ma Aisha, Heedayah ta bi Zainab gun madubi a hankali tace "I want to talk to you Zainab" Zainab tace "Ohk" Fita Heedayah tayi Farida ta bi ta da kallo, Zainab ta bi bayan Heedayah, Heedayah ta kamo hannunta a hankali tace "Plss can I get spare gate pass?" Zainab tace "For who?" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, Zainab ta d'an yi murmushi tace "Ohk I get, but aiki ne babba fa, kinsan gate pass din ba shi da yawa, but let me try...." Daga haka ta wuce dakin da amaren suke ana shirya su cikin hadaddun kayan dinner dinsu, cikin dubara Zainab ta jawo jakar Aunty Safiyya dake gefenta ta bude, gate pass biyu ya rage da xata ba wasu schl frnds dinta, Zainab ta xare daya ta mayar mata da jakar ta fita da sauri, ta mika ma Heedayah dake tsaye tana jiranta tace "It was easy but not funny" Heedayah tayi murmushinta me kyau tace "Thanks Zainab" daga haka ta sa gate pass din a jakarta, tana jin wayarta ya fara vibrate ta fita parlor da sauri ta xaga ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata tace "How will you collect it?" Yace "Ohk kin samu?" Tace "Ehh" yace "We will meet there, but ki ajiye wayar kusa dake plss" tace "Toh, ana jirana" daga haka ta katse wayar ta mayar cikin jaka, har ta fara tafiya ta ji ance "Heedayah" gabanta ya wani irin faduwa ta juya da sauri ganin ba kowa sai ta kalli sama, Sudais ta gani bakin windon dakinsa tsaye yana kallonta, Kasa cewa komai tayi xuciyarta sai bugawa yake ta marairaice xata yi kuka, da sauri xata bar wajen yace "Jiran ni a nan, kar ki je ko ina" bata iya ta ce komai ba ta tsaya hawaye na sakko mata, bayan kusan minti uku sai ga shi, har ya iso inda take bata yadda ta kallesa ba xuciyarta sai bugawa yake, yana facing dinta ce "Ke da wa kike waya?" Kamar jira take ta fashe masa da kuka ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Ni ban ce ki min kuka ba answer my question now" Cikin rawar murya tace "A frnd" yace "Frnd?" Where did you know him from" hawaye kawai take ta ki cewa komai, yace "I asked where did you know him from" Ta kuma fashe masa da kuka tana kallonsa, yace "Schl??" ta gyada masa kai, yyi shiru yana kallonta, can yace "Ur classmate?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh waye?" Ta ki cewa komai, strictly yace "Answer me now Heedayah" Cikin rawar murya tace "A hanya na san sa" yace "Mami ce ta baki waya?" Murya can kasa tace "Shi ya bani" yace "Amma Mami ta sani?" Ta girgixa masa kai, da mamaki yake kallonta, can yace "Farida fa?" Nan ma ta girgixa masa kai, ya fi second talatin yana kallonta with surprise, can yace "Bani wayar to" ba musu ta bude jakar ta fiddo wayar ta mika masa, yana kallonta yace "Why Heedayah, Don't you know u are too young for this, idan kika gama secondary school babu wanda xai hanaki waya da wani, seriously bana son in sake ganin haka, face ur studies, in a year time after ur secondary schl you can speak to anyone... provided Mami ta sani kuma ta amince da hakan" cikin sanyin murya tace "To Yaya" Yace "Shi a ina yake?" Ta girgixa masa kai tace "Nima ban sani ba" Yyi shiru yana kallonta, can ya kara duba wayar yana kallon hotonsa duk da wayar ta fashe sosai, but he still can see him a little, mika mata wayar yyi yace "Bude min" tace "Ban san password din ba" Da mamaki yace "Baki sani ba? Haka ya baki wayar?" Ta gyada masa kai, yace "Me yasa bai bude maki ba" tace "Nima ban sani ba" yace "Baki ce masa ya bude maki ba?" Tace "Nace masa amma bai bude ba" yace "Toh xai kira kuma xan yi warning dinsa, bbu ke bbu shi, idan kuwa kika sake kulasa sai na hada ki da Mami and even Abba" Hawaye ya kawo idonta tana girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "Don Allah kar ka gaya mata wllh dukana xata yi, don Allah Yaya kayi hkuru" yace "Toh naji, but karki sake kulasa anywhere, and hope bai san gidanku ba" Ta d'an kallesa sai kuma da sauri tace "Aa bai sani ba" Yace "Good, I will warn him if he should call, I don't think mutumin kirki ne da baxai ki baki password ba, and plss bbu ruwanki da maxa sai kin gama secondary schl Cutie, is that clear?" a hankali tace "Toh Yaya" yace "You can go" a hankali ta fara tafiya har ta d'an yi nisa sai kuma ta juyo da sauri tace "Yaya don Allah har Yaya Shureen kar ka gaya ma" Murmushi yayi yace "Baxan gaya masa ba" ta marairaice tace "Plsss" yace "I promise" juyawa tayi ta ci gaba da tafiya ta koma cikin gida. kaka ta gama shirinta tsaf ita ma cikin wani lace dake ta walkiya ta kima uban dankwali a kai ga katon mayafinta da ta

Please Login or Register in order to submit comment