Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa gun Safiyya da dai daya dayar jakarta na gado da xa a iya xura jariri a ciki, takalmin kafarta ma me d'an tudu ne, Heedayah na hango kaka duk da tashin hankalin da take ciki sai da ta nemi kujera ta xauna ta dinga kyalkyala dariya Zainab da Nafisa na taya ta, kaka ta nufi gun Umma dake ba frnds dinta pass tace "Dama kada a kuskura a raba ma tsofaffi fass din nan, kar su je su cika mana waje a shiga uku, kuma wani motar xa mu hau da Ta salla? Ta kirani tace kila tana hanya" Umma ta kalleta daga sama har kasa snn ta kauda kai tace "To ai motocin ake jira, kowa ma motar yake jira" Kaka tace "Toh a ajiye mana daya da Heedayah da Zainab da Farida" tana fadin haka ta koma canxa jaka ganin kowa da sabon jaka yake yawo ita kadai ce me tsohon jaka, Sudais ne ya bita dakin bayan Ummarsa taje ta samesa a dakinsa ta lallabasa yaje yyi mata magana duk da baya son fitowa sbda mata da suka cika gidan, ganinsa Kaka tace "Kai baxa ka bane Sudess, gashi kowa na ta shiryawa, shi dama Shureen bakin hali baxai bari yaje ba, barin yanxu kuma da yake tunanin ya xama soja" yace "To me xan je inyi" tace "Oho" yana kallonta daga sama har kasa yace "Duk kwalliyar xaman gida ne kika yi hka Hajjaju" Kaka na nemo sabon jakarta a kwallayenta na daki tace "Wani xaman gida, ga can an je kawo motoci xa mu dinner, Ta salla ma kila a can xa mu hadu" Sudais yace "Ynxu ke fisabilillahi godai godai idan ance ki tafi dinner sai ki tafi?" Ta mike tana kallonsa baki bude.... yana kallonta da kyau yace "Idan ma xaki tube kayan nan ki tube ki saka na xaman gida, don bbu wanda xai kai ki wani dinner, Abba da Baffa sunce bbu inda xa ki yanxun nan suka kirani, idan kuma basu isa da ke bane sai mu ji, meye kuma dinner tsofe tsofe da ke xa ki ce sai kin je cikin jikokin ki" yana fadin hka ya fita dakin ba tare da ya jira cewarta ba, yana fita su Umma da kawayenta na shigowa da manyan kuloli dakin. Bayan Magrib duk aka watse gidan xuwa wajen dinner, Ko kadan kaka bata wani tada hankali ba ganin duk namomin bikin gobe da kaji su Umma suka kawo dakinta a manyan kuloli har ma da cartoons din malt da lemu iri iri, ga ganda da aka soya da naman saniya, sae cewa take kuyi maxa kada ku makara bbu ddi. Har suka isa gun dinner Heedayah bata da walwala, bayan sun sauka motar su Farida da Nafisa sun shiga cikin event center din Zainab tayi kasa da murya tana kallon Heedayah tace "Kin samu kin basa gate pass din?" Hawaye ya kawo idon Heedayah a hankali tace "Ya Sudais ya amshi wayar" Da mamaki Zainab ke kallonta, can tace "Ya aka yi ya gani?" Heedayah tace "He caught me at the backyard" Zainab tace "To yanxu ya xa ayi? And baki da number tasa ko?" Heedayah ta gyada mata kai a hankali, Zainab tayi shiru don ita ma bata ji dadi ba, can ta d'an yi tsaki tace "Ya Sudais din nan na da matsala wllh, duk ya bi ya takura mutum, mu ma fa haka yake mana har duka ya ta6a yi ma Nafisa wai sai mun gama waec, amma ga su Rabi'ah su yi ta waya da samari kala kala Ya Shuraim baya ce masu komai wllh, a gabansa ma suna iya daukan phone call he won't even look at them" Dallaro su aka yi da fitilar mota lkci daya kuma aka kashe, duk suka kalli motar dake parke daga opposite dinsu....






Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....






*Masu bukatar cream that is tested and trusted ga dama ta xo maku....*


*Whitening lotion 4500*
*Shower gel 3500*
*Tone lotion 3500*


You can contact 08038103096....




Kallon Zainab Heedayah tayi, Zainab tace "Ko shi ne?" Heedayah ta dinga kallon motar, can tace "Aa ba da motar nan nake ganinsa ba" Zainab tace "To ki je ki duba" Karasawa Heedayah tayi gun motar, taga an sauke Windshield din motar, sosai gabanta ya fadi bayan sun yi ido hudu da shi, sanye yake da wandon sojoji da polon su, ya dauke kai daga kallonta ya kara haska ma Zainab fitila, Kamar ana tilasta Heedayah tayi kasa da murya tace "Ina yini" bata jira ya amsa ba ta bar wajen tana turo baki, Zainab sai kallonta take har ta iso, Heedayah tace "Ke ake kira" Zainab ta xaro ido tace "Ni kuma? Waye ke kirana?" Heedayah tace "Oho ki je ki gani" karasawa Zainab tayi tana d'ari d'ari, Shuraim ya sakar mata murmushi, ta buda ido sosai ganinsa tace "Lahh ashe ya Shuraim ne, kai ma dinner din ka xo?" Ya hade rai yace "Dinner kuma? No, not at all" tace "To me kaxo yi nan?" Yace "Yanxu xan wuce wajen aiki, na ajiye wasu ne" Zainab tace "Ohk Ina yini Ya Shuraim" yace "Lafiya lau, me yasa ita kadai ta xo gun motar sbda taga anyi flash din fitila maimakon ku biyu?" Zainab tace "Ohh ni ce nace taje ta ga wa ke haska mu" Yace "Wato ita ce fitsararriya, da wani ne haka xata xo ta tsaya masa a mota tana kallonsa ko?" Zainab tace "Aa fa Yaya, ni nayi insisting taje ta ga waye da gaske" kallonta ya tsaya yi, can yace "Then... Don't do that again, Ina Farida?" Zainab tace "Sun shiga ciki" yace "Ke ina pass din naku?" Zainab tace "Gashi a jaka, nata na wajenta" yace "Ohk, till after the dinner kar ku fito waje" Zainab tace "Dama ai baxa mu fito ba Yaya" Yace "Good" tace "Yanxu xaka wuce?" Yace "Ehh" tace "Toh Allah ya kiyaye" Heedayah dai na can tsaye nesa da su sai turo baki tayi, can kuma sai ta tabe bakin, wani abu kamar kwandala taga ya gangaro inda take, ta dinga kallon d'an abun me shige da ring da ya kwanta a gabanta bayan ya gama bouncing, Daga kai tayi ta kalli direction din da abun ya taho, suka yi ido hudu da Khaleel jikin wata farar mota me ubansun kyau, tuni ya dauke kai yana danna wayarsa ya kasance side view dinsa kawai take iya gani, parking space din event center din ne, ya d'an saci kallonta bayan sun hada ido ya bar wajen ya koma can bayan wani mota ya tsaya, don motoci ne iri iri a wajen, Zainab taga Shuraim ya bude mota xai sauka ta matsa da mamaki tana kallonsa, karasawa gun Heedayah ta ga yyi, ita ma Heedayah kawai ganinsa tayi kamar daga sama a gabanta, ya duka ya dau ring din, sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya a tsorace, ya mike yana bin wajen da kallo, Tuni Khaleel ya canxa wani motar ynda ko ganin alamarsa Shuraim baxai yi ba, Heedayah dai sai kallon Shuraim take a tsorace, Zainab ta karaso kusa da su tace "Me ya faru Yaya? What's that" Shuraim ya amshi jakar Heedayah, ba musu ta sakar masa jakar, ya bude, pass din dake ciki guda biyu ya ciro ya yayyaga a wajen ya jefar sannan ya nuna mata motarsa, fashewa da kuka tayi sosai, Zainab da ta xaro ido tace "Yaya why did u do that, there is no other pass fa??? Me ya sa kayi haka yaya" Shuraim ya nuna mata hanyar shiga wajen fuska daure yace "Yi wucewar ki ciki" ganin kallon da yake mata dama kuma sun taso suna tsoronsa fiye da yayansu Sudais kawai ta kama hanyar shiga event center din wanda policemen ke tsaye suna amsan pass, tana yi tana waigosu, Heedayah sai kuka take tana yarfe hannu, yayi mata wani tsawa yace "Wuce mu tafi nace" Bata masa musu ba ta nufi motar da sauri, ta bude back seat ta shiga, ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya fita parking space din driving with speed, Khaleel dake jingine jikin wata mota daga nisa ya bi motar da kallo, bayan few seconds yyi wani murmushi yana juya wristwatch din hannunsa almost whispering to himself yace "Waow... A soldier, then... either I or him" daga haka ya koma gun motarsa ya shiga. A hankali Heedayah ke kuka a motar tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Driving dinsa kawai yake yi yana yi yana duba motocin dake bin sa a baya, bayan wani lkci wayarsa ya fara ring, dauka yyi yana duba me kiran nasa ya ga Mumy ce, ya daga wayar ya sa a handsfree, Mumy tace "Aliyu nasan sai takwas xa ka tafi aiki don Allah ka rufa min asiri ka xo ka daukeni da su Hajiya Sadiya da Hajiya Amina ka kai mu wajen dinner din nan, duk motocin sun tafi, tawa motar ma an tafi da ita haka na Hajiya Amina" Shuraim dake ta sauraronta har ta kai aya yace "Ina wajen aiki ynxu" Mumy tace "Haba Shuraim, karfe takwas fa kake tafiya gashi ynxu bakwai yyi" Yace "Ehh colleague dina dake dutyn rana xuwa yamma ya tafi gida before his time elapsed, his wife is sick shi yasa ya nemi alfarman in xo da wuri don inyi takeover from his time" Mumy tace "Ae shkkn sae mu nemi adaidaita amma abu bai yi ba manya kamar mu a ganmu a tricycle, shi Sudais yace baya kusa kai kuma yanxu kana ce min ka tafi asibiti" bata jira cewarsa ba ta katse wayar ya ajiye yana ci gaba da driving dinsa, Heedayah sae shessheka take tana ji kmr ta rusa ihu tayi kuka sosai ko xata ji dadi. Parking ta ga yyi a wani waje da akwai haske sosai, nan da nan ta dakatar da kukan da take yi ta goge idonta da sauri, ya bude motar ya sauka snn ya bude side dinta, kallonsa take a tsorace, ya hade girar sama da ta kasa yace "Sakko" Ba musu ta sakko da sauri, yace "Jiya waye na gani kofar gida kika min karya xa ki je ki siyi ruwa" Ta xaro ido tace "Ya Shureen ni ban san sa ba, na fito ne yana wucewa a mota sai naga ya tsaya yana kallona, I am telling you the truth ban san sa ba, believe me plsss...." Ta fashe da kuka amma hawaye ya ki sakkowa tana kallonsa a tsorace, yace "Ohk da ya tsaya kallon ki sai ke ma kika tsaya kallonsa a gate din ko?" Tace "Aa tsoro na ji shine ban fita ba na tsaya bakin gate din in ga ko xai wuce naga bai wuce ba" Shuraim yace "Toh yau kuma meye wnn aka jefo gaban ki ya fadi?" Ta daga hannu sama da sauri tace "Ya Shureen nima kawai gani nayi kila daga sama abun ya fado, ban san meye shi ba wllh, wllh I don't know what is that, believe me plsss" Kamar xata yi kuka ta kare maganan tana kallonsa da manyan idanuwanta, yace "Good, maxa su tsaya suna kallonki kema sai ki tsaya kina kallonsu ko?? to daga yau anytime you are going out you just have to wear a nikab, a must" Ta xaro ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, strictly yace "Kin ji abinda nace?" A hankali tace "Ni ai bani da Nikab ya Shureen" yace "Yess xan siyo maki, and if you should dare tell anyone that ni nace ki fara sa Nikab sai na baki mamaki..." Kamar xata yi kuka tace "Ban iya sa wa ba ai" yace "Ehh idan na kawo maki sai ki koya" Bata kuma ce masa komai ba, ya bude mata motar, ta marairaice ta shiga ya kulle, murguda baki tayi a ranta tace ai baxan sa ba sai dai kai ka saka, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, ganin hanyar gidan Mami ya nufa da ita taji kamar tayi ta ihu tana birgima a motar, nan da nan hawaye me shegen xafi ya dinga sakko mata taji kamar ta shakosa, Wayarsa yayi dialing snn ya kai kunne, ba a dau lkci ba yyi sallama yace "Ina yini Mami" Daga daya bangaren Mami ta amsa masa, yace "Kina gida ne?" Mami tace "Ehh ina gida Shuraim, ya aka yi?" Yace "Ohk Ina shigowa yanxu" Tace "Toh sai ka xo" daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gida yyi parking ya sauka motar, Heedayah ta share hawayen da ya ki tsaya mata ya fito daga cikin motar, bin bayansa tayi don har ya shiga gate bayan sun gaisa da Mai gadi, Da sallama Shuraim ya shiga parlon Mami, Mami ta sakko downstairs ganinsa tace "Aa, daga ina haka Shuraim, welcome, baka je dinner din ba kenan" kafin yace komai Heedayah ta shigo, da mamaki Mami ke kallonta tace "Wancan fa? Daga ina kike" Shuraim yace "Tace cikinta na ciwo shine na dawo da ita gida" Mami tace "Ikon Allah, tun yaushe" Shuraim yace "Da rana" Heedayah dake goge hawayen da ya ki tsaya mata ta gaida Mami a hankali snn ta wuce sama, Mami ta mike ta bi bayanta, kwance ta sameta saman gado tana rusa kuka kamar yar yarinya, har downstairs Shuraim ke jin kukan nata, Mami ta shiga dakin da mamaki sosai tace "Meye haka kamar 'yar yarinya, bana son iskanci, period din ne ya dawo??" Cikin kuka ta girgixa kai tace "Aa ba shi bane" Mami tace "Toh ya cikin yake maki?" Tace "Ya daina ynxu" Mami tace "Ya baki magani ne?" Gyada kai kawai Heedayah tayi bata ce komai ba amma taki daina kukan, Mami tace "To ki kiyayeni da kukan nan, tunda ke ba jaririya bace, idan bacci xa kiyi kiyi bacci" daga haka Mami ta fita dakin, Heedayah ta tura fuskarta cikin pillow tana rera kukanta. Mami na dawowa downstairs tace "Tace ka bata magani" Yace "Ehh na bata" Mami tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake" Mikewa Shuraim yyi yace "Xan wuce aiki, I am almost late" Mami tace "Toh abinci fa?" Yace "Aa am full" tace "You are always full dama, Toh Allah ya tsare" ya amsa da Ameen yana murmushi, ya mata sallama ya fita parlon, Mami ta koma sama xuwa dakinsu Heedayah, Heedayah na jin an bude kofa ta hadiye kukan ta rufe ido da sauri, Mami tayi xaton ta fara bacci ne ta juya ta fita. Karfe sha biyu saura Heedayah ta koshi da kukan da take ta mike xaune, sai turo baki take ita kadai, bandaki ta shiga tayi alwala ta fito tayi Isha, tana idarwa ta cire kayan jikinta ta dau kayan baccinta ta saka snn ta sa Hijab ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar ta fita, downstairs ta sauka xata tafi kitchen ta hada shayi, kwance ta ga Junaid 3 seater yana kallon wrestling, ya mike xaune yana kallonta da mamaki yace "Heedayah" sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace "Yaushe kika dawo?" A hankali tace "Tun daxu" yana kallon idonta with surprise yace "What's wrong, kukan me kika yi?" Kafin tace komai taji muryar Mami a sama, ta juya da sauri tana kallonta, Mami tace "What are you doing downstairs?" Cikin sanyin murya tace "Ina jin yunwa xanyi making tea" Mami tace "Go and make it ki xo ki wuce" Kitchen din ta nufa, Mami na ta tsaye har ta fito da cup din shayi, Junaid dai bai ce ma Mamin tasa komai ba, Heedayah ta wuce sama, Mami ta jira ta ga shigarta daki sannan ta bi ta cikin dakin, tana kallonta tace "Ya jikin?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Na ji sauki" Mami tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka tayi mata sai da safe ta fita ta koma dakinta, kasa ci gaba da kallon wrestling din Junaid yyi duk son sa da wrestling kuwa, ba karamin kuka idonta ya nuna tayi ba, lkci lkci yake kallon agogo har karfe daya yyi, ya mike xaune daga kwancen da yake saman kujera, yana ta xaunen har daya da rabi snn ya mike ya wuce sama, ya fi minti uku tsaye corridor din dakunan, can ya nufi kofar dakinsu ya bude very careful kar yayi kara, shiga dakin yyi da yyi sanyi sbda Ac dake kunne wutan dakin a kashe, ya rufe kofar, Heedayah na jin an bude kofa dama ba bacci take ba abun duniya ya isheta, gaba daya ji take kaf duniya dai a ynxu bata tsani kowa ba kamar Shuraim, ta mike xaune da sauri tana kallonsa ta duhun kamar me rada tace "Yaya" ya karasa gefen gadon ya xauna ya haska mata fitilar wayarsa mara haske yace "Kukan me kika yi Heedayah" Ta dau pillow ta daura jikinta kamar xata yi kuka tace "Yaya Mami fa xata yi fada" Hade rai yyi yace "Tell me what's wrong with you" Ta hadiye abu da kyar tace "Ciwon kai nake yi shine na dawo gida" Yace "Ciwon kai? To kin sha magani?" Ta gyada kai tace "Na sha" yace "Wa ya baki?" Tace "Mami" cikin sanyin murya yace "Allah ya sauwake dear, but ya daina ciwon ynxu ko?" Ta gyada masa kai, yace "Shayin ya ishe ki?" Nan ma ta gyada masa kai, gaba daya a tsorace take, yace "Why are you scared??" Ta marairaice tace "Mami... wllh xata iya dukana" Shiru yyi yana kallonta, snn ya kamo hannunta yace "Toh xan tafi yanxu, but watarana baxa ki ce kina tsoron Mami ba idan muna tare ai ko?" Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idonta kasa, mikewa yyi yace "Ki kwanta kiyi bacci, idan kuma baki jin baccin ki tashi kiyi sllh, good night" ta gyada masa kai kawai ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle mata kofar, downstairs ya koma ya kwanta coz he prefer lying down there, sai a snn kuma bacci ya daukesa. Washegari Saturday Mami bata ce Heedayah taje wani yinin biki ba, ita ma a gida ta yini abunta sai kusan yamma ta tafi gidan bikin bayan ta tabbatar Junaid ya fita gidan, gidan ya rage daga Heedayah sai Zainab me aikin Mami, tun da gari ya waye sai wani nukurci da miskilanci Heedayah take, Mami na ganin mood dinta dama ta kyaleta tayi ta xama a daki ita kadai, Da Heedayah ta tuna abinda Shuraim yyi mata sai ta fashe da kuka ita kadai tace "I hate you" da ta tuna wayar da Sudais ya amshe a hannunta shi ma sai ta fashe da kuka kamar 'yar yarinya. Karfe shidda saura ta sakko downstairs da dubu daya a hannunta, Zainab ce xaune parlor tana kallo, Zainab tace "Ga abincin ki can a kitchen ba ki ci ba Heedayah" a hankali Heedayah tace "Baxan ci ba" daga haka ta fita, ko gaida Mai gadi bata yi ba ta fita xuwa kanti ta siya chocolate. Zaune yake 4 houses away tare da mai gadi suna hira, malt ne a hannunsa yake sha, shi ma Mai gadin malt din yake sha yana lullumshe ido kana gani dai kasan siya masa aka yi, Mai gadin ya kara kurban malt din hannunsa, ya d'an yi gyatsa snn yace "Ai tsiyar basa fitowa ne yan matan gidan, duk safiya dai xaka ga uwar tasu a katon motarta ta fita, Ina jin wata babban ma'aikaciyar gwamnati ce, tana kuma da d'a wani matashi yana nan kamar balarabe, ya ma fi ka haske, to shi gaskiya Ina jin ba kullum yake dawowa gida ba don sai in kwana biyu ban ga motarsa ba a layin nan, su kuma Yan matan sai dai ka gansu an fita da su a mota daga cikin gidan, ban san ko su nawa bane balle in san ko warcece a ciki ma" Shiru yyi kansa a kasa yana rike da can malt dinsa yana sauraron Mai gadin, can ya dago kai yace "Mahaifinsu fa?" Mai gadin yace "Anya, Ina jin gaskiya ya rasu ban ta6a ganin dattijjo ya fito gidan ba duk xamana a layin nan inda gadin gidan nan" Ya gyada kai cike da gamsuwa sannan yace "Akwai Soja a gidan?" Mai gadin yace "Aa babu wani soja a gidan, basu fi su hudu ko biyar ba a gidan, matashi kuma daya ne a gidan" Khaleel ya gyada kai yana naxarin maganan mai gadin, d'aga kai yyi ya hangota tana tahowa da Hijab har kasa.






Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....






Mikewa Khaleel yyi carefully surveying the street and he saw nobody apart from her, Mai gadin ya hango Heedayah shi ma da sauri yace "Au to ai ga daya daga yan matan gidan can ranka shi dade" Juyawa Khaleel yyi yana facing dinsa amma bai ce komai ba, nan kuma bai son ta gansa ne, ita kuma ta riga ta gansa, sai da ta wuce su snn ya juyo ya bi bayanta, tsayawa tayi da ta gane yana bin ta, ya karasa gefenta ya tsaya, murya can kasa yace "How are you?" Ta wani hade rai tana kallonsa da kyau tace "I'm not fine, and I am begging you ka daina bi na, kana ja min matsala a gida...." Shiru yyi yana kallonta, ganin ya ki cewa komai ta ci gaba da tafiyarta walking faster, bin ta yyi suka kara jerawa, ta juya kamar xata yi kuka tace "Don Allah ka kyaleni ka daina bi na tunda dama kawai sbda in kulaka ya sa kake min karya kace ka san ni" ya girgixa mata kai a hankali yace "Ki daina cewa babba yana karya..." Ta yi facing dinsa da kyau fuska daure tace "But you lied to me" yace "No I didn't...." Tace "To a ina ka san ni??? Tell me now" Ya kalli motarsa da yyi parking can farkon shigowa layin snn ya kalleta yace "But we can't talk here" tace "Sai a ina?" Yace "Toh wai da mu shiga gidanku...." Ta wani xaro manyan idanuwanta a tsorace tana kallonsa, ya dage girarsa yace "Yess akwai matsala ne idan na shiga gidanku, daga nan ma ba sae in gaida mutanen ciki ba...." Kamar xata yi kuka tace "Ni dai don girman Allah ka daina bi na, you are a joker.... Plss let ur joke end here now and forever" yace "Billah na san ki Heedayah, what's my gain lying to you cewar na san ki bayan ban san ki ba" Kallonsa kawai take, yace "Nasan ba tare da iyayenki da suka haife ki kike ba, nasan cewar probably few years ago or even recently kika fara gani coz you were unsighted as at the time I knew you, a lkcn da na sanki kina 'yar karama" cikin sanyin murya tace "Toh a ina ka san ni plss? And did you know my real parent?" ya nufi inda motarsa yake walking slowly yace "Mu je mota, I can't talk here" Bin bayansa tayi a sanyaye maganganunsa na mata yawo a kai, ya bude mata front seat yana kallonta ba musu ta shiga ya rufe sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya kulle. Juyawa tayi tana kallonsa bayan ya shiga motar tace "Tell me plss, ka gaya min inda ka san ni" yace "I will, but waye wnn sojan na jiya?" Tace "Ya Shureen" Khaleel ya dinga kallonta kafin yace "Did you mean Shuraim?" Ta bude hannu tace "Ni dai Shureen naji kaka ke kiransa" yace "Who is he, I mean the Shuraim, and waye kaka?" Tace "First son din Abba ne shi Ya shureen, kaka kuma Grandma dinmu ce...." Yace "Grandma dinsu dai, and Waye Abba?" A hankali tace "I call him my father...." Yace "Nan ne gidan Abban?" Ta girgixa kai tace "Aa, gidan Mami ne nan" yace "Waye Mami" a hankali tace "I call her my mother" shiru yyi yana kallonta snn yace "Shuraim din ne yyi picking call dina jiya da na kira?" Ta girgixa kai tace "Aa that's Ya Sudais" da

Please Login or Register in order to submit comment