Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don Yakumbo na daya daga mutanen da take son gani ido da ido, kafin ta karasa main parlor suka yi kicibis da Yakumbo, Yakumbo ta koma baya ta kare mata kallo daga sama har kasa sai kuma ta rushe da wani matsanancin kuka tace "Allah ya ga xuciyar mu, bama nufin kowa da sharri a duniya, bama nufin d'an kowa da sharri, yanxu Heedayah ce wnn nake gani Aisha? Heedayah ce wnn ta xama gandareriyar yan mata haka aure yau ko gobe?" Kuka take yi sosai ta koma parlor ta xauna tana cewa "Xuciyar mu daya laya, bama nufin kowa da sharri duniya da lahira.... Yau ba ga ranan hakuri ba amma da mata duk kin bi kin daga ma mutane hankali kin dami mutane, kowa na jin haushina ana ganin kamar hada baki muka yi da 'yan kinnafas din, toh ni dai duk a gaggauta neman gafarana don an xalunce ni da mummunan xato wanda har duniya ta tashi baxai gogu a raina ba, aka shiga tsakanina da d'an uwana da na rike tun yana karami duk sbda an sace Heedayah a gidana kamar ni na sace ta...." Heedayah dai sai kallonta take, can ta tafi ta rungumeta da murmushi fuskarta, Yakumbo dai sai kuka take, Ammi kuma ta xauna saman kujera tana karasa saka ma Ashnaah kayanta, knocking aka yi, Ammi ta kalli Heedayah dake ta kallon Yakumbo kamar ta samu TV, nan kuma Kaka kawai take gani wajen a xaune, mikewa Heedayah tayi ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel bakin kofar, ta koma baya tana kallonsa da mamaki, can tace "Anyi discharging din ka ne?" Ya gyada mata kai yace "Ur Dad... is he in?" Tace "Ehh yana sama" Juyawa tayi tana kallon Ammi tace "Ammi it's ya Khaleel" Ammi tace "Ohk, let him in" shigowa parlon yyi, Ammi na kallonsa tace "Sannu da xuwa" ya gaisheta ta amsa tace "Daxu Abbansu Islam ke ce min anyi discharging din ka.... Ya karfin jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh naji sauki, na xo yi masa godiya ne" Ammi tace "Ohh bbu komai ai, he is coming downstairs now, have a sit...." Xaunawa Khaleel yyi yana gaida Yakumbo dake ta kallonsa tayi mitsi mitsi da ido, can ta share hawayen idonta tana kallon Ammi tace "Shi kuma wnn din waye?" Ammi tace "Shine Honorable ke gaya maki ai" Yakumbo ta tabe baki tace "Toh ni dai ce masa nayi wa ya sani ko shi yayi kinnafin din nata da ya gaji ya ga ba sarki sai Allah ga yasin ana ta jifarsa da shi ya maido ta" Ammi ta d'an hade rai tace "Haba Yakumbo, wani magana ne wnn, Heedayah dake hannun mahaifiyar makociyar mu a kaduna, shi dai ta dalilin sa aka kawota nan gidan, ba wai wani abu ba" Yakumbo tace "Atoh ni babu ruwana wllh, ke baki ga kirarsa bane kamar ta mutan da, ai irin su ne ke kinnafin din yanxu, a ajiye batun wani kyansa, wllh duk haka suke ba muna gani a TV ana nuna mana su ba kullum" Ammi bata kuma cewa komai ba sai dai ranta ya baci sosai, Shi dai Khaleel kansa na kasa, Heedayah sai kallon Yakumbo take kamar xata yi kuka, Yakumbo ta kyabe baki ta bude yar jakarta ta fiddo tissue da aka nannade ta warware ta ciro goronta ta fara ci tace "Na nannade kayana kada kura ya fada kai in cutu...." Ammi dai ko kallonta bata yi ba ta kalli Heedayah tace "Ku je da shi gidan Dinar ya gaida Mamin ki a can kafin Abbanku ya sakko" A sanyaye Heedayah ta mike tana kallonsa, ya mike yyi ma Ammi godiya, amma shi ma gaba daya jikinsa yyi sanyi, ya bi bayan Heedayah da har ta kai kofa, Yakumbo tace "Toh Allah ya maka albarka, ai da ba don kai din ba da har yanxu ana ta xargina ana kullatata a xuciya, 6atan wnn yarinya bbu irin bakin jinin da bai ja min ba a duniya, duk inda na kutsa nuna ni ake da d'an yatsa har ya kai ya kawo na dena fita, ko kasuwa na shiga anyi ta leko ni kenan a shaguna" Heedayah ta kulle kofar bayan Khaleel ya fito, tana kallonsa cikin sanyin murya da damuwa tace "Kayi hakuri plss, Ammi na ta gaya min haka take, she's strange because she is old" Yyi mata murmushi bai ce komai ba, tace "Baka yi kama da kidnapper ba, kuma baxa ka ta6a kama da su ba" Kallonta yake without blinking, xata wuce a hankali yace "Why did you think so" Ta juyo da sauri tace "Dama me yasa xaka yi kama da kidnapper? My Yakumbo is just saying that out of frustration, Allah ya raba ka da kama da su, they are the deadliest set of beings on earth...." Sauke idonsa yyi bai ce komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta har suka isa gate, ta kallesa tace "Seems you are not still happy about what Yakumbo said..." Da sauri yace "Noo, it's nothing, nasan haka tsofaffi suke" A tare suka shiga gate din Dinar, ya tsaya bakin kofar parlon ta shiga sanar ma Mami xuwansa, a hankali ya xauna saman kujeran da ya gani a wajen, lkci daya hawaye ya kawo idonsa abinda tun da ya san kansa bai ta6a yi ba, sai dai ya ga ana kuka amma shi bai ta6a ko digon hawaye ba don ya taso xuciyarsa a kekyashe ne, Bai ta6a jin ya tsani rayuwarsa irin na wnn lkcn ba, he just hate everything about him immediately, a da ya kan ji hakan amma baya wani tasiri a xuciyarsa don in few minutes yake dawowa normal, yau kuma sai yaji hawaye na xuba idonsa sosai, fitowa Heedayah tayi tace "Ya Khaleel an ce ka shigo" Jin bai dago kansa ba ta isa gabansa tace "Ya Khaleel" durkushewa tayi gabansa ganin hawayen idonsa, lkci daya ta rikice ta kamo hannunsa tace "Are you okay? Me ne ya faru, ko kirjin naka ne ya fara, tell me plsss" ya girgixa mata kai trying hard to control the tears ya kamo hannunta amma ya kasa cewa komai ya xamo kasa, kuka take sosai tace "Plss ka gaya min what's wrong ya Khaleel, me ya same ka" cike da karfin hali cikin rawar murya yace "I... I want.... you to be a father... mother... and sibling... to me" Shiru tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ganin ya sauke kansa kasa hawaye na ci gaba da sakko masa ta rungumesa ita ma hawayen na xuba idonta tace "Did you lost them??" Gyada mata kai ya dinga yi amma ya ki cewa komai, tace "Talk to me plss, did u lost them" cikin sarkewar murya yace "I never had them" ta fashe masa da kuka sosai tace "I promise I will be, I promise you that..." Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta sake sa da sauri har lkcn tana kuka ta mike, Mami ce tsaye bakin kofar ta fito da mamaki tace "What happened???" Heedayah dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take, Mami ta daga kan Khaleel da ya sunkuyar da kansa ya ki dagowa, ganin idonsa tace "Subhanallah what happened, are you Okay" ya girgixa mata kai cike da karfin hali ya mike cikin sanyin murya yace "I... I came to thank you Ma, I appreciate ur care toward me...." Hawayen dake sauka idonsa yasa Mami ta ji lkci daya nata idon ya cicciko tace "But you don't need to dear, you don't need to..... Come in" kama hannunsa tayi xuwa parlon Dinar, Heedayah ta bi bayansu tana goge hawayen dake xubo mata, Xaunawa Khaleel yyi saman kujera lkci daya yaji ya samu nutsuwa, xuciyarsa ya daina masa xafin da yake masa with just Mami's word, daki Heedayah ta wuce ta ki tsayawa a parlon don gaba daya xuciyarta tayi rauni abinda yace mata, Mami ta sa mai aikin Dinar ta kawo abinci da ruwa ta ajiye masa, shiru yyi kawai yana kallon abincin, tun da ya san kansa sai dai ya shiga eatry ya ci abinci bai san dadin abincin da aka girka a gida ba, muryar Mami ya ji tace "Ka ci abincin" Ya kalleta snn ya xamo kasa a hankali ya xauna ya bude plate din abincin, shinkafa ne da miya with many meat sai coslow a wani d'an bowl a rufe, ya dau spoon ya fara cin abincin a hankali, Mami dai sai kallonsa take don exactly yanda Junaid ke xaman cin abinci ya xauna, Dinar na sakkowa xata dauko ma Fadil fresh yo a kitchen ta tabe baki tayi wucewarta kitchen din, kawai ita dai ta ji ranta bata yarda da Khaleel ba, ga shi da innocent face, very innocent, but ita dai bata yrda da shi ba. Abba ya dau makullin motarsa xai fita parlonsa Mumy dake ta kallonsa a tsaye tace "Yau naga ikon Allah, Ina kuma xaka daga dawowa barrister ko hutawa baka yi ba, ga abinci can nace maka na gama ka dau makullin mota xaka fita" Yace "Nace idan na dawo xan ci Maryam, xan je can gidan Dr ne Yanxu" Mumy ta kyabe baki tace "Toh aiki kaje yi Abujan ko har yanxu kan batun 6atan Heedayar ne, ni fa wllh da na ji shiru bbu wani labari kuma babu wanda ya sake cewa komai na xata an ganta ne" Abba ya juyo yana kallonta yace "Eh an ganta, a gidan mahaifanta a nan garin Abujan" Mumy ta saki wayar hannunta ba tare da ta shirya yin hakan ba tace "Ban gane gidan iyayenta ba?" Yace "Yes biological parent dinta, idan kina jin Honorable Ahmad Yusuf Ishaq, shine Mahaifinta" Mumy ta masa wani kallo tace "Ban gane ba, wacce Heedayar wai kake fadi barrister, Heedayah da ba lallai a sake ganinta ba kake nufi ko warce?" Abba yace "Toh ki tambayi d'an ki xai fi yi maki bayani in details a kan abubuwan da suka faru, tare aka yi komai da shi a Abuja, as for now sai na dawo...." Bai jira cewarta ba ya fita, ta cire dankwalin kanta jin wani xufa dake keto mata tun daga saman kanta har kasa duk da Ac dake kunne parlon, da dankwalin ta dinga fiffita ma kanta iska can ta dau wayarta da screen din ya tarwatse ta shiga kiran Shuraim, yana fara ring ya daga tace "Duk inda kake kuma duk me kake yi ka barsa ka dawo gida yanxun nan ina jiran ka" Jin yanayinta yace "Lafiya Mumy??" Kuka ta sakar masa tace "Ni dai nace ka dawo yanxun nan Aliyu" Daga haka ta katse wayar ta sake jefarwa kasa tana xagaye parlon, gaba daya xuciyarta ta ki yrda ko na second daya da xancen Abba sai kace wani film, wai wani Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq shi ne uban Heedayah, ta ina?? Bayan ko kama da shi ma bata yi ba, yarinyar da aka ce an tsinto a daji, to amma kuma ai barrister baya mata karya wasu hawayen da bata san dalilinsu bane suka shiga sakko mata tace "Aikin banxa, uban wa xa ayi ma wnn karyar, Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq ne ubanta shine da ta 6ata ba a ji a duniya ba...." Tsaki ya ja ta nemi waje ya xauna tana kara tabbatar ma kanta raina mata hankali kawai Abba yake, ya ma san wanda ya ambato mata a matsayin uban Heedayah kuwa, abinda ance mata Heedayah ta shiga duniya kenan ba dawowa, mikewa tayi ta sake daukar wayarta tana neman layin Sadiya.






Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....






Abba ne xaune parlon Kaka, ita kuma tana xaune daga kan darduman da tayi sllh hannunta rike da carbi, tun fara bayanin Abba kaka ke kallonsa kamar a lkcn ta fara ganinsa, har sai da ya kai aya kaka ta ki cewa komai sai xare ido take, Bude kofar parlon aka yi hade da sallama Baffa ya shigo, ya xauna saman kujera yana kallon Kaka ya gaisheta, jin tayi shiru bata amsa ba yace "Lafiya Baaba??" Kaka ta kunce ha6ar xaninta ta fara matsar kwalla tana shessheka tace "To dai tunda mu ke kallon banxa bai ta6a hadani da Heedayah ba Allah ya so ni, Umaru kaga shi yasa aka ce mutum ya ji tsoron Allah ko, yanxu da na biye ku nace baxa a rike wnn yarinya ba tun farkon kawota gidan nan da Amadu yayi da na shiga uku na lalace yau, amma da yake xuciyata fess ban biye xugar kowa ba, inji Amadu ya fada maka waye uban Heedayah, to wllh duk abinda mutum xai yi ya ji tsoron Allah ya ji tsoron gamuwarsa da Allah, ni dai duk xaman mu da yarinyar nan ko kallon banxa ban ta6a yi mata ba balle in hantare ta wllh, Allah ubangiji ya so ni, wa enda suka yi hakan ma Allah ya yafe masu, ni fa lkcn da ubanku ke da rai na sha tsinto yara a titi su girma wajena in aurar da su, kalar tawa baiwar kenan, shi sa Heedayah ma nayi mata rikon da ku kanku ban maki ba....." Tana kai wa nan ta mike ta nufi gun akwatinta tana share guntun hawayen idonta, daga akwatin tayi tace "Allah me yanda ya so...." Baffa yace "Me kuma xa ki yi da akwati Kaka" Kaka ta juyo da sauri tace "Ai Abujan xa ku kai ni in karanto ma uban duk abun arxikin da aka yi mata ba tare da mun dubi cewar a titi aka tsintota tana galantoyi ba, to wai ma waye silar riketa a gidan nan?? ba ni din bace dai, nan nan nan Amadu ya watsar da lamarinta ya bar mu daga ni sai Rakiya muna ta wahala da ita meye ba mu yi mata ba na gata wanda ko gaban uban nata take ba lallai yyi mata ba, har filina sai da na kusa siyarwa lkcn da xata makaranta, daga karshe ma Amadu koramu yyi ni da Rakiya daga gidansa ta dalilinta, shi dai kawai Allah ya basa baiwar tsinto mana ita ne ya kawo mana, amma asi bai mata ba, kashinta, fitsarinta, duk bbu wanda ni da Rakiya bamu ci ba, barin ni don Rakiyar ma gantalin aikinta take tafiya ta bar ni da ita" tana magana tana hawaye, daga Abba har Baffa kallonta suke baki bude, Ta sharbe majina tace "Kuma na daga jaka ace min ina xan je sbda rashin tsoron Allah, to Abuja xan tafi" Baffa yace "Haba kaka, ke ya kamata ki bi su, ko su ya kamata su xo su sameki a nan??? Da girman ki xaki ce xaki bi su Abuja, ba su ya kamata su xo nan su maki godiya su baki girman ki ba" Cikin daga murya Kaka tace "Aa wllh bbu ruwana da wani girman kai, rawanin tsiyar xa ku dinga laka6a min, shi yasa fa aka jefo shaidan daga aljanna aka ce, to meye kuma wani girma kamar wata gyambo, Allah ai shine abun girmamawa, bana son girman daga yau ma idan xaku ce min Patuu duk ku ce bbu ruwana da iskanci, meye wani da girmana kamar dai ni na halicce shi uban yarinyar, mu tafi kawai ku dora ni a mota inyi tafiyata, bance wani gantalalle ya kai ni ba dama" Abba dai bai ce komai ba sai kallonta yake, Baffa yace "Toh ki jira Allah ya kai mu gobe lafiya mana" Kaka tace "Ba a xuwa Abujan da daddare ne ko walakanta ni ku ke son ku yi?" Baffa yace "Yanxu idan ance ki bi hanyar nan da ba shi da kyau ai baxa ki bi ba kaka" Kaka ta jinginar da akwatin ta koma ta xauna tace "Matsiyatan yan kidinafin ma kadai ai sun isa hanani tafiya yau, shegu" Mikewa Baffa yyi yace "Na shigo in gaisheki ne dama, sai anjima" Bai jira cewarta ba kamar yanda Kaka bata ko kallesa ba har ya fita parlon, kaka ta rike ha6a baki bude tana naxarin Maganganun Abba, can ta daga hannu sama tace "Ni dai Allah ya rufa min asiri wllh, dama tun ranan da na fara ganin Deedayah na ji ta kwanta min sosai, ban bari tayi rashin uwa ba ko na sakwan daya, ban kyamace ta ba, abinda ma nake mata ban ma jikokina ba wllh" Washegari da ya kasance Friday, da safe karfe takwas Mami ta gama shirin komawa Kaduna tare da Farida, ta shiga bangaren Ammin Heedayah don yi mata sallama, Heedayah ta fito daki don a nan ta kwana tun bayan da ta dawo gidan nasu da Khaleel daren jiya gun Abbanta, ta xauna gefen Mami tana kallonta tace "Mami good morning" Mami tace "Morning dear, how was ur night" Heedayah tace "Alhmdllh, Ina xa ki Mami?" Mami tace "Xamu koma kaduna yau" cikin sanyi Heedayah tace "Mami tafiya xa ku yi ku bar ni nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Mami tayi murmushi tace "Abbanki xa su taho anjima sai ki biyosu" girgixa kai tayi ta mike tace "Noo Mami we are going together, ki jirani in hada kayana" tana fadin haka ta koma dakinta da sauri, Mami ta mike tace "Sae kun taho Amina" Ammi ta mike tace "Aa ki jirata ku tafi din Hajiya...." Mami tace "Aa, kamata yyi ku taho tare din xai fi" Ammi tayi shiru ganin Mami ta nufi kofa ta bi bayanta da sauri tace "Abban su Islam yace ya turo maki sako ta WhatsApp ki duba yanxu Hajiya" Mami tace "To in sha Allah" har bakin gate ta rakasu snn ta koma ciki, tsaye taga Heedayah a Veranda, ta juya da sauri ganin uwartata tana goge hawayen idonta, Ammi ta dinga kallonta snn tace "Don't worry dear, anjima xa mu wuce Kadunan gaba daya ai, flight sai nan da karfe biyar in sha Allah na yamma" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta wuce ciki. Mami na komawa ta bude WhatsApp din nata taga flight ticket guda biyu da Abban Heedayah ya turo mata, rasa ma abinda xata ce tayi, Dinar dake xaune tare da ita a parlon tace "Jirgin dai da baki son bi shi xa ki bi at last, ki kirasa kawai ki ce kin gani Allah ya saka, sai in kai ku airport din xuwa nan da karfe goma tunda flight din sha daya ne" Mami dai tayi shiru bata ce komai ba. Mumy ce xaune dakin Sadiya idonta yyi bulu bulu don kuka, Hajiya Sadiya tace "Ni fa wllh wllh idan ba ke kika yi ido hudu da shi wanda aka ce shine uban Heedayah ba kika xo nan kika fada min hakan da bakin ki to ni ba yarda xan yi ba, sai kace wasan kwaikwayo a taya wnn sanannen Mutumin xa ace shine ubanta, 'yar kamar wnn mutumin ta bace farat daya ace ba mu ji a gari ba" Mumy ta fyace majina da tissue din hannunta tace "Nima dai shi na gani Sadiya..." Sadiya tace "Toh wai da kika kira Shuraim din me ya ce maki?" Mumy tace "Uban me xai ce min dama, kawai ce min yyi eh haka ne, nayi nayi nayi ya fadadada min bayani amma yace bai san komai ba haka kawai Abbansa ya gaya masa shi ma, to ya xan masa?" Sadiya tace "Kaii karya ne wllh, wnn sanannen bawan Allah dai karya ne ace shi ya haifi Heedayah, ta ina suke kama? Shi baki ita fara, snn me kudi da fame kamarsa xai bar 'yar sa a makance??" Hajiya Baturiya dake dakin duk tana sauraronsa tace "Abinda ku ke mancewa a nan shine, shi wnn bawan Allah Honorable Ahmad Yusuf Ishaq da ake batu akai, duka duka yaushe ya fara siyasa da har yyi sunan?? Ina jin bai kai shekara uku ba, don ko da yana siyasar ma to gaskiya a shekaru uku xuwa hudu jama'ah suka san sa har ya xama famous haka, xai iya yiwuwa sai bayan batar 'yar tasa ya shiga siyasa gadan gadan har yyi kudi haka, kuma idan baku manta ba ni dai na sha fada maku wnn yarinya bata yi kama da yar kananun mutane ba, ku dubi jikinta ko a lkcn da Barrister ya kawota bbu wani alamar wahala kawai dai makauniya ce...." Mumy dake ta mata wani shegen kallo tace "Toh in sha Allahu ba ubanta bane shi din, idan Allah yayi duniya don manzon Allah, taya ma xa ayi ya xama ubanta, mutumin dake neman takarar gwamna a jihar kano, meye hadin biri da gada, yarinyar da mijina ya tsintota a makance a daji bbu galihu...." Hajiya Baturiya tace "To yanxu idan da gasken shine ubanta ya xa kiyi Maryam?" Mumy ta fashe da kuka tace "Wllh wllh ba shine ubanta ba in sha Allah, matsiyaciyar yarinyar da Mai gidana ya tsinto a bola xa ace attajirin nan ne ubanta, dubi fa uban plazozin da yake da shi a jihar nan da ma kano, in sha Allahu ni baxan ji kunya ba muna nan da ku xa ku ga karya ne, idan kuwa gaskiya ne toh sai dai fa ayi hakuri da abinda xai faru" Sadiya tace "Toh Allah ya sa karyan ne, amma idan haka ya kasance ai baki ci ribar komai ba wllh" Mumy tace "Ai sai dai idan ba ni Maryam ba, yanxu ma gidan Dakta xan tafi in ji abinda ake ciki nasan yanxu kaka tana da labari tare da ita" Sadiya tace "To mu je mana gaba daya" A tare su ukun suka tafi gidan Baffa a motar Mumy.... karfe shidda saura Abban Heedayah ya fito government house na Kaduna tare da few convoy, tun shigowarsu kaduna ya kira Shuraim da ya xo har government house din ya samesa don kai sa gidan Baffansa, sanye yake da khakinsa da yayi fitting dinsa sosai, Shuraim suka gaisa da gwamna dake tare da Abban Heedayah don da shi xa a taho gidan Baffa, tun da Heedayah ta yi ido hudu da Shuraim bata sake yarda ta kallesa ba, kuma ta ki gaishesa, shi ma din bai sake kallon direction dinta ba, mota daya ta shiga da Abbanta da Amminta, motoci biyar ne banda na sojoji da na governor da suka yi parking a kofar gidan Baffa, Shuraim ya sauka, Heedayah ta bude motar ta fito don Allah Allah take ta ga kaka ta nufi gate da sauri, parent dinta ma duk suka sauko motar, da ido Shuraim ya bi ta don sai da ta d'an bugesa ta shiga gate din gidan, Heedayah na shiga main parlor din gidan ta fara kwala ma kaka kira, Mumy ce xaune parlon da kawayenta da Mum din Sudais suna magana kasa kasa, bata ko kula da su ba ta ci gaba da kiran kaka.... Sai ga Kaka ta fito dakinta, da gudu Heedayah ta tafi ta rungumeta, Kaka tace "Ina gwamnan yake??" Kaka bata rufe baki ba Shuraim ya shigo, ganin Mumy a parlon ya ki karasawa, yana kallon Kaka yace "Xa a shigo..." Kaka ta tura Heedayah tace "Su shigo mana me suke jira a waje, ai tun daxu nake ta jiransu Umaru yace min suna hanya, mu dai ba mun rike yar su da amana ba, wanda ya ki Heedayah yau ne ranan jin kunyarsa, don ma Sudais da muka hada baki da shi aka rike Heedayar yana can kasar waje, da ba don shi ba, ba don ni ba da yanxu wani labarin ake ba wnn ba....." Mumy dai sai kikkifta ido take, haka Umman Sudais, Ammi ce ta fara shigowa parlon da wife din governor din garin da sallama, Kaka ta amsa da karfi ta karaso cikin parlon tana kallonsu Mumy cikin fada tace "Ku tashi ku basu waje su xauna mana, kun ja6e kamar masu neman aiki" Kallon kaka kawai Ammi take da murmushi, Kaka ta fashe da kuka sosai tana kallon Ammi tace "Wllh kamar kinyi kakin Heedayah, ni dai dama nasan Heedayah ba gantalalliya bace, dama kallon banxa bai ta6a hadani da ita ba, wa enda suka yi mata ma Allah ya yafe masu ita ma

Please Login or Register in order to submit comment