Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karasa cikin kitchen din, Mami na kallonsa tace "Ina jin ka Khaleel" Ya shafa kansa yana murmushi yace "A can aka haifeni na taso nayi karatu duk a can...." Mami tace "So ur parent are still there" Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya tace "Theye are late" Mami ta dinga kallonsa with pity kafin ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah ya gafarta masu" yana kallonta a hankali yace "Ameen" tace "But all ur relatives are in gombe still?" Ya sauke idonsa kasa ya gyada mata kai, Mami tace "What do you do for a living?" Shiru yyi na few seconds, can ya daga kai ya kalleta yace "Business nake yi" Mami tace "That's good, what are ur qualifications?" Ya shafa kansa a hankali yace "Diploma, Bsc, Msc.... I am an Architect" Mami tace "Maa sha Allah, kana da 'yan uwa a nan garin ne?" Ya girgixa mata kai, tace "To kanninka ko yayyinka fa?" Ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, deep down her she knows she isn't suppose to be asking him any of this, bai santa ba bata sansa ba, it's his private life, she isn't suppose to intrude but haka kawai taji she wants to know more about him, tana son saninsa sosai, may be because taji ya kwanta mata har ranta, kwata kwata bashi da hayaniya ga ladabi, ga kuma hankali, all in all his smile is just like that of her Junaid, Khaleel yace "I am an only son" Jin Mami bata ce komai ba ya daga kai ya kalleta, kallonsa kawai yaga take yi, tayi masa murmushin karfin hali tace "To Allah ya dafa maka, and u are still not married??" Ya gyada mata kai tace "Allah ya kawo ta gari" yyi kasa da kansa yace "Ameen" Tace "Amma a kawo maka abincin ko kadan ne ka ci" yace "Na ci abinci daxu Ummi" Mami tace "Alright, shkkn" Heedayah ta fito kitchen ta tafi dinning ta xauna da plate din abincin da ta debo, mikewa Mami tayi tace "Ina xuwa" daga haka ta wuce sama, Heedayah ta mike ta dawo parlon ta xauna kasa tana kallonsa tace "Yaushe ka xo?" Yace "Not less than 15 mins ago" Tace "Okay" yace "Daga ina kike?" Tace "Gidan Grandma dinmu, me yasa baxa ka ci abinci ba?" Yace "Na koshi" tayi shiru tana kallonsa, Yace "Waye kika ce ya ajiye ki?" Heedayah ta turo baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Yayanmu" Yace "But you look disturbed" shiru tayi tana kallonsa, can tace "Nothing, kawai nayi bacci ne na tashi sae aka maido ni gida" Khaleel bai ce komai ba, bayan wani lkci ya dago kai ya kalleta yace "To ki ci abincin" Ba musu ta ci gaba da cin shinkafar gabanta, ganin ynda yake kallonta ta wara masa ido tace "Ko xaka ci?" Yyi murmushi ya girgixa kai yace "Aa, lomar ki nake gani" tayi dariya tace "Toh baxan ci ba" ajiye abincin tayi gefe tayi tagumi, ya sakko kasa ya xauna a hankali yace "Aa yi hakuri" Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da sallama, Kallon Khaleel yake har ya karaso cikin parlon ya basa hannu suka gaisa da murmushi fuskarsa, Junaid yace "Ya jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Junaid yace "Allah ya kara lafiya" Heedayah na kallonsa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya lau, yaushe kika xo" tace "Yanxu na xo" Yace "Me yasa baki kwana wajen kakan ba" murmushi tayi tace "Aa ba komai" Sama Junaid ya nufa, Khaleel ya kalli Heedayah yace "What's his name?" Heedayah tace "Ya Junaid" Ta kalli Junaid da har ya wuce sama ta wara ido tace "Kasan fa kuna min kama da shi, just that you are a bit dark in complexion, and ur dimple... Not as deep as his" Khaleel yyi murmushi yace "He is nice, I like him" Heedayah tace "Sure, amma fa da yana neman tsokanata yanxu dai ya daina" Khaleel ya langwabar da kai yace "Ko dai son ki yake?" Ta turo baki tace "Aa, kawai dai ni kanwarsa ce" Yace "Toh shkkn, xan koma yanxu.... Kije kice ma Ummi na wuce" Heedayah tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "So early?" Yace "Ai na dade" Tace "Toh yaushe xaka dawo" yace "Duk sanda kika ce" ta mike tace "Bari in kira Mami" bata jira cewarsa ba ta wuce sama, a stairs ta hadu da Mami tare da Farida, Heedayah ta rungume Farida tace "I missed you sis" Farida tayi murmushi tace "Welcm back" Mami tace "Ya wuce ne?" Heedayah tace "Aa yace xai wuce" Mami na sakkowa kasa tace "Har xa ka wuce Khaleel" yace "Ehh xan wuce" Mami tace "Toh bari ka tafi da abincin tunda baxa ka ci a nan ba" Kitchen ta tafi, Farida na kallonsa tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, How are you" tace "Alhmdllh" A warmer Mami ta xuba masa abincin ta saka a leda ta kawo masa parlon ta ajiye kusa da shi tace "Here, anjima idan ka tafi gida sai ka ci" ya mike yace "Allah ya saka da alkhairi" Iya bakin kofa Heedayah ta rakasa sbda Mami dake parlor snn ta dawo ciki, ganin har Farida ta wuce sama ta bi bayanta da sauri, dakinsu ta sameta xaune gefen gado tana danna wayarta, Farida na kallonta tace "Me ya kawo sa?" Heedayah ta bude hannu alamar bata sani ba tace "Nima a nan na samesa" Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba, Heedayah ta xauna gefen gadon tana kallonta a hankali tace "You know what Farida?" Farida na kallonta tace "Aa me ya faru" hawaye ya kawo idonta, Farida ta kamo hannunta da sauri tace "What happened Heedayah talk to me plss" Ta fashe mata da kuka, Farida ta rude tace "Ki gaya min menene mana Didi" Heedayah ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "Ko ba ya Shureen bane" da mamaki Farida tace "What about him?" Heedayah na goge hawayen idonta murya can kasa tace "He kissed me..." Shiru Farida tayi tana kallonta ko kiftawa bbu, jin shirun yyi yawa Heedayah tace "Why don't you want to say anything?" Farida ta ta6e baki ta mike ta bar wajen tace "What did you want me to say" bin ta da kallo Heedayah tayi tace "Ohh haka ma xaki ce min" Farida ta juyo tace "Of course me xan ce maki, an ta6a kissing mutum baya so? Ai ke kika tsaya yayi maki, so why are you complaining?" Heedayah bata kuma cewa komai ba, Farida ta fice daga dakin. Mumy ce xaune ita da Hajiya Sadiya da Salima a dakinta, Hajiya Sadiya tace "Wllh damuwa ya isa ya maki illa Maryam, kina da saka ma ranki damuwa ba kadan ba, wnn abun fa duk mafita ake nema amma dubi ynda kika koma daga jiya xuwa yau...." Mumy ta matse hawayen idonta cikin rawar murya tace "Shkkn ni na tashi a tutar bbu kenan Sadiya, ashe da gasken dai ubanta ne ke neman takarar gwamna, ni yanxu meye ribata ga kishiya da a ko da yaushe xata iya dawo min tunda ba sakinta Barrister yyi ba" Sadiya tace "Toh dai uban yarinyar nan nema mukamin yake ba wai samu yyi ba, sai ki ga ma baxai samun ba in sha Allah" Salima dake taunar cingam tace "Tabb, da kyar kuwa wnn mutumi ace baxai samu gwamna ba, ku kun ga jama'arsa kuwa, mu dai shkkn kin mana bakin ciki, da kin rike yarinyar nan da yanxu government house sai dai mu shiga duk lkcn da muke so mu fito lkcn da muke so, amma yanxu ai sai dai kishiyarki ta shiga ta fito duk sanda ta ga dama, ni dama uban Heedayan xai ganni yace yana so duk da ba wai na hakura da Junaid bane amma wllh yarda xanyi ya aureni, kuma kar kiyi tunanin sbda ya aureni xa ki dinga xuwa government house, nima ba nuna xanyi na san ki ba gaskiya" Banda hararta bbu abinda Mumy ke yi da idanuwanta da suka yi jajir, Salima ta tabe baki tace "Duk da haka bai baci ba, da yanxu xa ki amince Shuraim ya aureta ai rass kema sai yanda kika yi da gidan gwamnati wllh" wani kallo Mumy ta dinga yi ma Salima tana huci, kafin tace komai Sadiya tace "To ai gaskiya ta fada wllh Maryam, kyansa kawai Shuraim ya aureta mu ga ta tsiya, kinga kuwa ikon Rahina daga ranan ya kare, Heedayah ta xama surkarki sai yanda kika yi da ita, idan ma rabata xa ki yi da Rahinar duk sai kiyi amma gaskiya wnn garabasar idan ta wuce mu kuma mun shiga uku, wllh shawara me kyau Salima ta kawo, d'an ki fa ke aurenta, waye kuma Rahinah ai sai yanda kika ce xa ayi"


*Thanks so much for ur prayers fans, Allah ya saka da alkhairi... Everything went smoothly, update din dai ba yawa coz Ina hanya yau*




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....










Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you.
Have u ever wondered how desserts are made?
Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from?
Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because
Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught:
*Profit analysis
*Ways to handle desserts
*Dessert marketing.
This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos.
Registration is on and the fee is just N3000 Naira.
Class starts on 27th august,2021.
And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕


WhatsApp 08135358038
Call 📞 08135358038
IG: najaatu Yakudima






Mumy ta ja wani tsaki tace "Ni an gaya maku ta mukamin ubanta nake, Ina ruwana da wani government house yarinya ta bi ta cuceni ta tarwatsa min rayuwa shekaru biyar kenan" Salima tace "Ke dai wllh Yaya kina da matsala, ga hanya dai mafi sauki da xaki musguna mata bbu me ce maki don me, wllh Aliyu na auren yarinyar nan shkkn sai yanda kika juyata kika takata, beside xa ma ki iya shiga ki fita idan ma yana da niyyar sonta watarana ki cire masa son nata a ransa gaba daya yaji ya tsaneta, you won't even give any space for him to begin having feelings for her, axabtar da ita kawai xai dinga yi wllh, Kai ko shimfida idan baki son su hada baxa su hada ba, dama fa sbda yanda kike tsangwamata ne ya sa ban kai ki gun wnn mutumi me min aiki ba, wllh yanxu haka d'an minister of finance nake hari, gashi har ya fara kulani a Instagram muna chatting yanxu har ya bukaci yaushe xa mu hadu, dubu 80 na kai ma mutumin yyi min wnn aikin duk da dai har yanxu ina son Junaid kuma shi nake burin aure, yanxu idan kin amince da shawarar nan da na baki kawai sai in kai ki gun Mutumin, kiyi ma Barrister karya kice xaki gidan Gwaggwo Rumaisa, wllh Yaya sai yanda kika yi da Heedayah da shi kansa Shuraim din, kuma sai dai ya ajiyeta a matsayin hoto bbu abinda xai faru tsakaninsu, snn ayi maki aikin da xata dinga tsoron ki tana maki biyayya kiyi ta juyata kamar masa, daga karshe ma idan kika so ki saka Aliyun ya saketa shkkn kinga ta xama bazawara, idan kuma aure kike son ya kara sai ya kara, daga gefe ke kuma kin samu connection da masu kudi, tunda duk da matan gwamnoni da manyan mutane iyayenta suke hulda" Mumy dai tayi shiru abun duniya ya dagule mata, Sadiya tace "Atoh dai, dadina da ke Salima akwai kwakwalwa" Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace "Ku kuna ganin hakan da xa ayi shine mafita?" Sadiya tace "Mafitan gaske kuwa, ke kina da wata mafitar ne banda wnn din" Mumy tayi tagumi tace "Toh ai tsoro nake kada wnn karan abun ya sake juye min, nifa wllh wllh ko mutuwata bana jin sa kamar yanda nake jin wnn yarinya, a dalilinta fa na shiga gararin rayuwa mijina ya juya min baya duk da biyayya da yake min" Salima tace "Bbu abinda xai juye kanki, wnn mutumi da nake gaya maki Gwaska ne wllh, gashi nan ya min na fara ganin aiki da cikawa kawai ke dai nemi karyar da xa ki gilla ma lauyan mijinki ki shirya mu je mu san tudun dafawa" a hankali Mumy tace "Toh bari ya dawo, amma fa...." Salima ta ja tsaki tace "Amma me, ke dai kin cika fitina wllh yaya, ga rashin bin shawara" Mumy tace "Toh goben sai mu je kawai" Sadiya tace "Ni connection din da xamu samu ma shi ya fi min dadi wllh, ko ba komai ai a fara damawa da mu a kasar" Da daddare Abba na parlonsa yana operating system Mumy ta shigo, xaunawa tayi gefensa tace "Sannu da aiki my Barrister" ba tare da ya kalleta ba yace "Sannu" tayi kasa da murya tace "Baka sha Watermelon din ba My Barrister" yace "When I am done..." shiru ne ya biyo baya, bayan wani lkci tace "Barrister dama akwai wata magana da nake son mu yi da kai" Abba yace "Ohk ina ji" tace "Ko in bari ka gama abinda kake" yace "No fire on, ina jin ki" Tana murmushi cikin tattausan murya tace "Barrister naga yanda kake ji da Heedayar nan, ga kuma yanxu Allah ya bayyana iyayenta cikin sauki bbu tashin hankali, nasan kuma shkkn yanxu idan ba wani ikon Allah ba tafiya xa su yi da ita idan xa su koma Abuja, toh sai nake ga don xumunci yyi karfi da iyayen nata me xai hana ka nema ma Shuraim aurenta gun Mahaifanta, nasan baxa su ce a'a ba, and I must confess my barrister duk da naki rike Heedayah, ita din yarinya ce me hankali nutsuwa da ladabi nagani, bata da hayaniya snn she will make a perfect daughter in law, ni gaskiya tsoron yan matan yanxu nake barin ma na nan kaduna, kada yaje ya kawo mana warce xata fi karfinsa ya fi karfinmu, kasan yanxu abinda ke faruwa kenan a duniya, shine tun da rana nayi wnn naxarin naga bashi da wani aibu, kuma xai kara karfafa xumuncinmu da iyayen Heedayah, hakan kadai xa suyi maka su kwatanta abinda ka masu na rike masu 'ya bisa amana, duk da matsalolin da ka fuskanta daga gareni wanda hakan ba komai bane facce sharrin shaidan, kuma wllh wllh nayi nadama, don d'a na kowa ne bawa sai mai shi" Abba dai sai danne dannensa yake yana murmushi bai ce mata komai ba, A sanyaye tace "Kayi shiru My Barrister" yace "Ehh ina jin ki" tace "Toh ai na gama" ya kalleta yace "Good, a xamaninmu an mana auren dole?" Tayi shiru tana kallonsa yace "Answer me" tace "Aa" yace "Toh baxa muyi ma yaranmu ba, Shuraim bai ce yana sonta ba, ita ma bata ce tana son Shuraim ba don haka ki ajiye wnn shawaran naki a gefe, it's shaky, with or without aure xa ayi xumunci da su sosai, don iyayenta yan Babban gida ne... Ba kananun mutane bane" Mumy ta bata rai amma ta rasa abun cewa, Barrister yace "That's just it" Mumy ta marairaice tace "Barrister auren kadai ne xai sa ayi xumunci wllh" Da mamaki Abba yace "Why are you bothered sai anyi xumunci da su? Saboda Mahaifinta na neman wani mukami a gwamnati and you have ur selfish interest da kike son achieving??" Ta mike tana masa wani kallo tace "Alhmdllh kasan dai ni ba kwadayayyiya bace, Ina ruwana da mukamin ubanta, su suna kano ni ina nan Kaduna, me ya kawo wnn magana, an basa mukamin ne ma balle kace min haka, shkkn daga kawo shawara sai a fassara ni, mummunan fassara kuma, daga nayi ma d'a na sha'awar aurenta sbda hankali da nutsuwarta sai ace ina kwadayi, me garesu da xa su bani wanda Allah bai bani ba" Abba dai bai ce mata komai ba yana ci gaba da abinda yake, ta juya a fusace ta fice daga parlon. Washegari Shuraim na dawowa gidan daga wajen aiki ya tafi parlon Abbansa da ya kirasa tun safe, gaida Abbansa da ya fito bedroom ya xauna saman kujera Shuraim yyi bayan ya xauna kasa kusa da shi, Abba yace "Ya aikin?" Ya shafa kansa yace "Alhmdllh..." Abba yace "Ya issue din Transfer da kace xa ayi maka" Shuraim yace "Still working on it, may be next year...." Abba yace "Good" shiru ne ya biyo baya, Abba yace "Are you listening?" Shuraim ya kallesa yace "Ina ji" Abba yace "What are ur plans on settling down with a wife" Shuraim yyi shiru yana kallonsa, can ya sauke kansa kasa, Abba yace "Xan fita office don haka you need to talk fast" Shuraim yyi kasa da murya yace "In sha Allah soon" Abba yace "Kana da warce kake so ne" nan ma yyi shiru kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Mun yi magana da Baffa, yace xa ku yi magana" Abba yace "Toh shkkn, you can go" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo har ya fita, Da sauri Mumy ta bar bakin kofar ta koma bangarenta, Shuraim dai ya bi ta da ido bai ce komai ba ya wuce dakinsa, yana shiga ya cire shirt din jikinsa sai ga kiranta, ya daga tace "Ka sameni parlona yanxu" Ya fita dakin nasa ya koma bangarenta, Tsaye ya ganta parlonta, tana ganinsa tace "Wanka xaka yi ne" yace "Nayi wanka, kwanciya xan yi" tayi kasa da murya tace "Me Abbanka yace maka?" Yace "Aa kawai yace xan ajiye sa anjima kadan" Mumy ta daure fuska tace "Karya kake wllh, ni xaka munafurta??" Ya buda manyan idanuwansa yace "That's it mum, abinda yace min kenan, nace masa Allah ya kai mu" Mumy tayi shiru tana kallonsa, can tace "Baxa dai ka gaya min ba" yace "I am serious mum" ta nuna masa kofa tace "Toh fita" ba musu ya juya ya fita ya kullo mata kofarta, ta cije yatsa, murya can kasa tace "Dole ma kawai abun nan ya tabbata, in sha Allahu sae auren nan ya tabbata kwanan nan ba da dadewa ba" tana fadin haka ta shige dakinta xata kira Salima. Kaka nata goge gogen windown dakinta sae da taga yyi fess ta juyo tana kallon Baffa dake xaune parlon tare da Abba tace "Idan na barsa ban karasa ba sae shaidan ya mantar da ni, kunga haka kuma bbu kyau, tunda bbu me taimakona sae Allah, 'ya yanku dama sae dai su shigo su xagi iyayena su fita" tana kai wa nan ta xauna tace "Wata kullalliyar kuma ku ka kulla xa a sanar min yanxu?" Baffa yyi dariya yace "Aa bbu, shawara muka xo nema..." Tace "To ina jin ku" Baffa yace "Ya kika ga idan aka ce xa a nema ma Shuraim auren Heedayah gun iyayenta?" Kaka tayi shiru tana kallonsu kamar ranan ta fara ganinsu, can tayi mitsi mitsi da ido tana kallon Ac dake dakin kamar me naxari tace "Waye kuma Shureen?" Duk suka yi shiru suna kallonta, tace "Aa ba batun wasa ba, don Allah ku sanar min waye Shureen din?" Nan ma bbu wanda yace komai, a fusace tace "To ni nasan wani Shureen ne? ba sai ayi min bayani ba duk kun wani min shiru, idan baxa a sanar min waye shi ba ku fita ku bani waje in ci gaba da tsaftace dakina ni dai" Baffa yace "Aliyu" kaka ta hade rai tace "Ban gane Shureen ba sai wani Aliyu, ko dai wiwi ku ka sha kafin ku shigo min, nifa kar a dinga damuna, ku min bayani filla filla yanda xan fahimta, idan kuwa kunbiya kunbiya za ku min ku fita" Baffa ya nuna Abba yace "Shuraim din Ahmad...." Kaka ta bude baki a hankali tace "Shureen din Ahmad kuma??? Ashe da gaske shi din ne ku ke nufi xuciyata taki amincewa..... To wiwi ku ka dirka halan ku ka ga hada Deedayah da Shureen ya dace" Abba dai TV kawai yake kallo, kaka ta mike tsam tace "Toh wllh bbu ruwana da wnn konanniyar shawarar taku duk kauri, a rasa wanda xa a ace xa a ba Deedayah sae Shureen, yaron da har yau uban da ya haifesa bai san xuciyarsa ba balle mu karere, to wai ma ina Deedayah xata kai gantsamemen Mutumin nan, anya kuna tsoron Allah kuwa Amadu, snn ko kakanninku ba a masu auren dole ba balle Deedayah.... To ba ruwana, Shureen kuma da tuntuni nayi masa mata yar gidan Rakiya ai maganar na nan bata mutu ba lkci kawai ake jira, ashe kuma dai kwadayayyu ne ban sani ba, daga ganin ubanta gwamna ne sai ku fara kokarin makala mata d'an ku da bashi da tarbiya bashi da kirki" A tare Abba da Baffa suka kalleta, Baffa yace "Subhanallah" Kaka ta zare masa ido tace "Ehh din, ba kwadayin bane ke dawainiya da ku xaka ce min Subhanallahi.... Mutumin da ko xo bai ta6a hadasa da Deedayah ba balle tafi xaku wani ce a aura masa ita, duk fa ina lura da komai ni ba Mahaukaciya bace, takama da ya dinga nuna mata cewar gidan ubansa take duk ina lura, to meye kuma daga ganin uban yarinya babban mutum ne sai a nemi makala mata sangamemen mutum, to ya xata yi da shi fisabilillahi jama'ah??" Mikewa Abba yyi yace "Sae da safe" tace "Allah ya tashe mu lfya" daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Baffa yace "Haba kaka...." Kaka ta tsuke fuska tace "Kai... Kai ma sae da safe na sallame ka" mikewa yyi ya nufi kofa tace "Ko kun mance ni yar gaskiya ce, Kai ni ko da ma suna son junansu baxan yarda wnn katon ya aureta ba, ya xata yi da shi mutum gantsameme haka gashi soja yaje ya hallaka yar mutane mu shiga uku, balle ma bashi da hali kwata kwata wllh, yaushe rabon ya xo yyi min gaisuwar mutunci har na manta, to ni nasan inda Amadu yaje ya samo sa ya xama d'an sa duk da shi ma Amadun haka yake ai" Ranan Monday Ammin Heedayah da Abbanta suka koma Abuja leaving Heedayah with Mami don Mami tace masu sun yi resuming boko, Ammi felt as if kara rabata xa ayi da Heedayah but ko kadan bata nuna haka ba ta danne xuciyarta sosai, amma har ranta ta so su tafi da Heedayah a sata a wani makarantar a can Abuja, she had no other alternative then to leave her behind suka wuce da Abbanta. Heedayah na hada abubuwan da xata koma makaranta da shi don gobe xa su koma da yamma, Farida ma na dakin amma tana kwance tana danna wayarta, Heedayah ta karasa kulle jakarta tana kallon Farida tace "In dafa Indomie din da ke?" Farida dake kallon screen din wayarta tace "Noo" Heedayah bata ce komai ba ta juya ta fita dakin, karfe sha daya saura ne na safe, su biyu kawai ne gidan don Mami ta fita office amma tace ba dadewa xata yi ba daga can ma xata yi masu shopping, Heedayah ta gama dafa Indomien tana xuba masu a different plate ita da Farida duk da tace baxata ci ba amma har ita ta dafa, taji kamshin turare ya cika hancinta, juyowa tayi da sauri suka yi ido hudu bata san lkcn da ta saki tukunyar hannunta ba a rikice, sauran Indomien ciki ya xube kan gas, ya karasa cikin kitchen din da sauri ya janyeta daga wajen yace "Are you okay" Jikinta ya dau rawa tace "Noo" gaba daya ta rude, kallonta kawai yake, can ya daure fuska

Please Login or Register in order to submit comment