Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wani azafi da cin mutunci da ki ke yi mini, har azafin maita kin yi mini duk abi dame ni ba, kuskure ma fi girma da za ki yi shi ne, yi mini azafin zina, babu wanda ya kama ni ra'ayil aini, ina yi kar ki ara danganta ni da zina"

Jamila ta zaburo ta ce "Nana, Maman ki ke gaya wa haka? Ki ke kiran sunanta gatsal haka?"

"Ba ita kaWai ba, kafataninku nake yi wa kashedi, kar wanda ya sake gangancin danganta ni da zina, amma idan kun i ji ba za ku i gani ba"

Ta nufi banWaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza, ta shiga ta yi alwala ta koma Waki ta tayar da sallar azahar. Tana zaune a bigiren da ta yi salla, ta kasa addu'a ko lazumin ta kasa, haka zalika ta kasa kukan ma, ta rasa me ma za ta ce. Kawai ta haWa kanta da gwiwarta ta yi shiru. Har yanzu ji take tamkar kawai barazana ake yi mata, amma ba da gaske ne wai an yi mata aure ba.
Ga yunwa tana ji, ga jikinta a mace babu wari, ga damuwa gaba Waya ji take kamar ma ba ita ba ce ba.

Can Sangaren Hajiya Amina kasa zaune ta yi ta kasa tsaye, ta din ga mita tana faWa, har da cewa sai ta kai Baban Nana Human rights.

Shukura ta ce "Mummy ki na da Worawa kai, mutumin ya yi wa 'yar sa aure, kuma ki ce za ki kai shi human rights?"
Ayshacool
"To Shukura na rasa abun da zan yi zuciyata ta yi mini sanyi ne, gaba Waya tausayin yarinyar nake ji. Ba na tunanin an tsaya an ji ta bakin ta. Ke ba kya gurin lokacin da aka kira ni, aka ce an ganta a Wakin masu gadi. Gaba Waya ba ta hayyacinta, ba ki ga a yadda aka fito da ita ba. Kuma shi ma a buzayen wannan wanda ba ya maganar ne fa, har aka yi ta balahirar nan aka gama bai yi magana ba. Ke wait kamar fa yarinyar nan ita ma tana da mental issues"

Shukura ta ce "Au ke sai yanzu ki ka gane? Ni na daWe da fuskantar hakan, shi yasa wasu lokutan ba na sakewa da ita, ko na ganta da Haidar"

Cike da damuwa ta sake cewa kuma babanta ya san mutumin da ya aura matan, yana da mental issues?"

"Mummy ina zan sani ina nan?"

"Oh my God" Mummy ta faWa tana zama.

Ta ci gaba da cewa "Wannan mutanen da ba sa iya zama guri Waya, yanzu suna nan anjima su na can, yanzu haka za su yi ta yawo da ita, ko kuma can asar ta su zai kaita oho. Dan Allah Shukura, ki Wan haWo Wan abin da ya sauwwaa mu haWa a kai mata, ko ma mene ne ya same ta, duk a dalilin mu ne"

Shukura ta ce "A'a ba a dalilinmu ba ne, ki daina Wora mana laifi Mummy, zan haWa abin da ya samu, ni yadda za mu yi da Haidar kawai nake ji wallahi, dan yadda yake aunar ta ba ya aunata haka. Inda Allah zai taimake ni babansa cikin satin nan zai dawo, da ban san yadda zan yi ba"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Ina jin sa fa tun safe yake bin Jummai, yana ce mata ina Anty. Tana tsokanarsa tana cewa antynta ce ba ta sa ba, har da kukansa ya zo yana gaya mini, in cewa Jummai Anty Nanansa ce ba ta ta ba"

"Ai sun shau sosai ne, zan ga abin da zan yi a kai". Shukura ta yi maganar tana Waukar remote.

****
Cikin ananin lokaci labarin aure Nana, ya karaWe dangi da unguwa baki Waya, Mama na ta nanata ai cikin dare aka Waura auren a gidan mai unguwa, jin hakan ya sanya sai mutane su tambayi ba'asin dalilin yin hakan, saboda ba abu ne da aka saba da shi ba, mussaman auren budurwa, a ce an Waura shi cikin dare kamar yai.

Sai Mama ta ce "Hmm ku dai a yi sha'ani, labarin ne babu daWin ji"

Yaya Atine ce ta bi Nana da kwanon abinci har Waki ta tsaya a kanta ta ce "Ki tashi ki saka wani abu a cikin ki, kina ta kwanciya kin wuni ba ki ci komai ba" Nana ta yi mata banza ko wawwaran motsi ba ta yi ba.

A hasale Yaya Atine ta ce "Shikkenan kin yi wa kanki" Nasiru kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan ya fita ya zagaya sai ya dawo ya lea Nana, har aka yi sallar magariba salla ce kawai take fito da Nana, babu wanda ta tankawa a gidan.

Saura iris Alhaji Zailani ya furzo abincin da yake ci, bayan da Hajiya Amina ta kammala yi masa bayanin abin da ya faru. Ji ya yi tamkar ta zuba masa wuta a zuciyarsa. Wannan shi ake cewa ga oshi ga kwanan yunwa. A zuciyarsa ya ce amma wannan an yi la'anannen tsoho, mu gama yarjejeniyar zai ba ni aurenta burina na daf da cika, kawai sai ya aurawa wani, saboda hauka. A fili kuwa cikin warewa da iya duniyanci, ya nuna halin ko in kula ya ce Allah ya kyauta. Bayan ya kammala cin abinci ya cewa Hajiya Amina ta zauna a sashenta kawai, zai Wan fita.

"Amma na ga yaushe ka dawo, da har zaka sake fita koma mene ne ka bari sai da safe mana?"

"Yaushe ki ka fara kafa mini dokoki a gidana?" Yayi maganar yana tsare ga ido, babu shiri ta ce "Allah ya baka hauri"

Kamar zai haukace, haka ya Wauki mota ya fita, yana tafe yana ta Wure-Wuren ashariya a cikin mota, yana zage-zage.
Gidan malam Gambo ya nufa, gurin sha Waya na dare, haka ya kira shi a waya ya fito.

"Alhajin Allah, lafiya kuwa ka zo a daren nan, ba yau ka dawo daga tafiya ba?"

Cikin damuwa ya ce "Babu lafiya, dan kuwa an yanka ta tashi"

"Too ikon Allah, me ya faru?"

"Yarinyar nan, da za a Waura mana aure, babanta ya yarda zai bani aurenta, ina murna muradina zai cika, kawai yau na dawo na tarar wai ya aurawa Waya daga masu gadin gidana, saboda an ganta a Wakinsu, wai ko yana zarginta ne oho masa, ni ko inda yake ban je ba, dan Allah meye abin yi? Ni fa ina iya saka a kashe ko ma uban wa aka aura mata, muddin muradina zai cika"

Ayshacool
"Idan ma kin kashe kanki, addara ta riga fata, dole ki tashi ki warara jikinki, ki ci abinci ki ware. Ko dai mu yi gaba da gaba da alubalen da yake tunkaro mu, ko kuma ki amince na Wauke ki baki Waya, idan ba haka ba ba zan iya cewa ga abin da zai faru ba"

Nana ta Waga ido ta kalli inda yake zaune, ta yi masa shiru ba ta ce masa komai ba.

Ya mie tsam ya rufe littafin, ya mia hannunsa can saman wani guri, ya Waukko wata kwalba, ya zo gabanta ya zauna, ya ura mata ido, take ta ji tamkar an zare mata kuzarinta.

Ya watsa mata wani koren abu a fuska, babu shiri Nana ta yinura ta tashi zaune tana tari.

Ummi ta gani a Wakin da take a asibiti.

"Zan sha ruwa" Nana furta a wahale. Aka kawo mata ruwa, ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta. Sai da Nana ta kwana a asibiti sannan aka sallame ta, wata irin azababbiyar yunwa da ta sako ta gaba, haka ta din ga cin abinci.

Sun koma gida babu daWewa sai ga Hajiya Amina, tare da Haidar. Yana ganin Nana ya je ya maalale mata yana murna. Ita kanta Nana ta yi murnar ganin Hajiya Amina da Haidar.

"Nana, duk da ni ba na zargin ki, kuma ba zan takura miki da tambayar jin abin da ya faru ba, amma ki yi hauri da abin da ya faru, amma idan ba kya son auren nan ki yi mini magana, a shigar da ara a hukumance a raba auren, kalli duk yadda ki ka rame"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Na gode sosai da sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi ina fatan Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi, ni ba auren ne damuwata ba, zargin da ake yi mini.. ta kasa ci gaba saboda yadda kuka ya wace mata.

Ta dafa bayan Nana ta din ga rarrashinta. Kaya ta kawowa Nana, har da bedsheets sabo da tsofaffi amma masu kyau, ga 'yan kayan kitchen da ta kawo mata, da Shukura ta bayar a kawo mata. Ta yi ta godiya, ta tashi za ta tafi, Nana ta ce za ta raka ta, ta ce "A'a ai ke yanzu matar aure ce, ki yi zaman ki Allah ya sanya alkhairi" ta arasa maganar tana danawa Nana kuWi a hannu.

Mawabta na ta zuwa Allah ya sanya alkhairi, da biyu domin su ga halin da Nana take ciki, har da 'yan islamiyyar su, da tun da ta bar makarantar babu wanda ya bibiye ta, balle a ji dalilin daina zuwan ta.

Baba sai kaiwa yake yi, yana komowa yana nanatawa Nana ta haWa kayanta cif, ta fara shiri. Yanayin yadda take ganin duniya ta juya mata baya, ta ji ina ma ba a haife ta ba, kuma duk wannan abin babu wanda ya kira mahaifiyarta ya gaya mata halin da ake ciki. To me ye ma amfanin gaya mata, tun da ba wani abin za ta amfana miki ba, kuma kin san ba zuwa za ta yi ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.

Da daddare gari ya yi tsit, Nana tana ta juyayi da tunanin wa ma aka aura mata a cikin buzayen, tun da su na da yawa.
Babu tsammanni bacci ya yi awon gaba da ita, sai dai ta din ga jin ta tamkar a zahiri ba mafarki ba. Da wata irin murya mara daWin ji, cikin maWaukakin sauti mai matuar razani da kiWima zuciya ake yi mata magana.

"Ko kin san wa ki ka aura? Mutumin da shi kansa bai tantance waye shi ba, bai san mene ne jinsa ba, mutum ne shi ko aljan. Rayuwa da shi na iya sadar da ke da ajalin ki. Lokaci ya yi da za ki biya abin da kakannin ki suka aikata, da kuma abin da ya faru a silar ki ke ce tabbas ke za ki biya wannan bashin. Ki tsira da ranki ki bar gida, ki yi nesa da gida, ko kuma ki fuskanci rayuwa mafi muni da hatsari" A gigice Nana ta tashi, ta fita tsakar gida da gudu tana haki, jan burki ta yi duk da zuciyarta na raya mata ta zare sakata ta ruga da gudu. Wani irin zafi take ji da matsanancin tashin hankali, ji take kawai ta buWe ofa ta fita shi ne za ta samu nutsuwa.

Juyawa ta yi da nufin ta fice ta bar gidan, amma ta ji kamar ta na wawaran motsi, zuciyarta za ta yi bindiga saboda bugun da take yi.

"Ki na ara Waga afarki, zuciyar ki za ta tsaya da aiki. Sai da na gaya miki, babu irin kashedin da ban yi miki ba, ki ka yi kunnen uwar shegu da ni, wallahi da kin sake kin buWe ofa kin fita, haukacewa za ki yi. Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya" A wannan karon ta gane muryar aisar ce, amma ta farkon ba ta san muryar waye ba.
Ayshacool
Zumbur ta tashi zaune, tana kallon Wakinsu, a iya saninta dare ne ta kwanta tana bacci, amma yanzu ta ga azahar ce.

Yaya Atine ta shigo Wakin tana faWin "Kin gama shure-shuren da ihun, kin ga dama kin tashi kenan? Wallahi tun wuri ki ajiye wannan haukan aljanun naki, ki kama kanki, ba kowa ne zai zauna kina masa wannan shirmen banzar ba, idan kin ga dama ki tashi ki wuce ki yi wanka ki zo ki ci abinci" Nana ba ta motsa ba, tana tunanin ko ta yi sallar asuba?.

Ummi ta shigo Wakin da jaka fuskarta Wauke da mamaki ta ce "Nana" Nana ta Waga kai ta kalle ta.

"Kin ga yanzu daga fita ta, na haWu da wasu buzaye, wai 'yan uwan mijin ki ne, suka ba ni wannan kayan wai a ba ki, sun ce , a ce ki yi hauri abin ya zo babu shiri, kuma ba su da isassun kuWi. Kin ga dubu hamsin, wai a baki ki yi wani abin ga kuma kaya"

Yaya Atine ta waro ido ta ce "Buzayen?"

"Wallahi kuwa"

"Kirawo Rabi maza a yi a gabanta" aka kirawo Mama, aka buWe zip Win jakar.

Danareriyar shadda bazin ce a farko, fara al an yi mata aiki irin na buzaye, har da awarwaraye da Wan kunne, da sara.
Kaya dai Atamfa set biyar, sai takalma guda biyu da turare har da na wuta.

Ummi ta ce "To ke Nana ki na ta wani buntsire-buntsire da alama wannan za su kula da ke. Kalli a yadda aka yi auren fa, amma har suka yi miki wannan kayan haka." Ita kanta Mama abin ya ba ta mamaki ya tsaye mata a rai ta za ta Nana za ta tozarta fiye da haka.

Ummi ta ce sai An yi wa Nana gyaran jiki an yi mata lalle da gyaran gashi, tun da har sun oarta sun kawo wannan kayan.
Da aka gaya wa Baba nuna wa ya yi ko a jikinsa, duk da cikin ransa ya ji daWin kayan da suka kawo mata, damuwarsa kar ma a fara yi masa zancen kayan Waki. Dan sadakin ma naira dubu hamsin ya ware zai ba ta.

****
A tsanake yake are masa kallo, tun daga kansa, har zuwa kan yatsunsa da suke Wauke da manyan zobunan azurfa. Duk da fuskarsa a rufe take, sai idanunsa kawai ake iya gani, yatsun hannunsa su ka fallasa asirin kalar farar fatarsa.

"Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?" A hankali ya juya wayar idonsa, yana kallonsa amma bai yi magana ba.

"Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi magana" still bai sauke ba, kuma bai yi magana ba, sai ma yinurawa da ya yi, ya juya zai fita" cikin azama ya tashi ya sha gabansa ya ce "Ya mu na magana za ka tashi ka tafi?"

"Me yasa ka kira ni?" Ya yi maganar yana tsare shi da ido.

"Buata ce"

"Ta me?"

"Ina so ka gaya mini ko nawa ka ke buata, ka saki yarinyar nan Nana da babanta ya aura maka"

Ya gyara tsayuwarsa sosai yana kallon cikin idanun Alhaji Zailani, ya ce "Je devrais divorcer?" Alhaji Zailani ya yi uri da ido yana kallonsa, dan bai gane me ya ce ba.

Ya taka a hankali ya je gaban Alhaji Zailani ya tsaya, sannan ya ce "Me yasa ka ke so na sake ta?"

"Saboda na fi ka buatar ta"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ka ce ka fi ni buatar ta?" Kafin Alhaji Zailani ya ba shi amsa, kawai ya gansu a tsakiyar dokar daji.

Ya saka hannu, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakyawar fuskarsa ta bayyana ya ce "Ka ce ka fini butarta? Har ka manta da abin da na yi maka a wancan lokacin?, shi ne ka sake biyo ni da wannan maganar?"

Ya saka hannunsa a wuyan Alhaji Zailani, wasu irin dogwayen farata suka tsiro a yatsunsa, a hankali kamaninsa suka gushe, fuskar wani tsoho tukuf ta bayyana.

Ya ara tsananta shae Alhaji Zailani ya ce "Ni na fika buatar ta, fansa ta zan Wauka a kanta. Mallakina ce, fansa zan Wauka, dan haka na fika buatar ta!!

Jin numfashin sa ya yi, ya dawo iya irjinsa, jini ya fara zubowa daga gurin da ya huda shi da faratansa.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
****
Gidan su Nana kuwa, ranar ta kasance ranar da za a kaita, sai dai babu wanda ya san ina za a kai ta, kuma ko katifa Baba bai saya ba. Da Ummi ta yi masa magana sai cewa ya yi ba shi da kuWi, ita ta yi mata. Abin ya Sata mata rai, babu wanda ya san wani irin guri za a kaita, idan babu labule da katifa a asa za ta zauna? Ga kuWin sadakin Nanan har dubu Wari biyu a hannunsa.

Nana kuwa kawai dai ga ta nan ne, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tana tunanin maganganun da ta ji da wannan muryar, ga kuma abin da aisar ya gaya mata. Duk da wani Sangaren na zuciyarta na gargaWinta da yadda da maganganun Aljanu, wataila kawai wasa suke yi mata da hankali. Tana jiyo Mama tana SaSSaka dariya tana cewa yanzu idan buzayen su ka i zuwa, su nuna in da za a kai Nana, ko kuma suka gudu shikenan Nana ta zama bazawara.
Maganar ta sosawa Nana rai nesa ba kusa ba, wato duk bayan abubuwan da ta yi mata a baya, har ma tunani take yi, ta yi zawarci. A take Nana ta yi wa kanta alwashin ko bangon duniya wanda aka aura mata, zai Wauke ta ya kai ta, za ta bi shi ko da kuwa zai din ga azabtar da ita ne, ta gwammace hakan da ta sake dawowa gidan nan da sunan zawarci tun da dai ibada take yi.
Abubuwan da suke damunta kuwa, ta fauwwalawa Allah, ta dake ta je ta yi wanka. Ta yi kwalliya da wannan shaddar, da kayan da aka kawo mata.
Kasancewar Nana tana da fata mai kyau, 'yan kayan da Ummi ta haWo ta yi mata gyaran jiki na kwana biyu, ta yi kyau fatar ta ara haske. Ga zanen lalle an yi mata. Gashin kanta ma ya yi kyau, komai kyau ne da shi idan ya sha gyara.

Sai da Mama ta yi saroro, da Nana ta fito cikin kayan nan, tamkar matar wani hamshain mai kuWi. Duk da ta rame sosai, amma kayan sun zauna a jikinta, tamkar tela ya gwada ta. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta fito tana gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.

Nan gida ya Wauki guWa, aka din ga yi mata fatan alkhairi. Duk da ga a yadda auren ya zo mata, kuma har a lokacin ba ta tantance waye ma mijin nata ba. Amma ganin mutanen da suke ta shiga su na fita, ana cin abinci, a dalilinta. Kawai ta durusa ta yi sujudu shukur, ko ba komai wannan wata rana ce da kowace mace da ta san ciwon kanta, take fatan gani a rayuwarta.

"Allah ga Nana, Allah ga baiwar ka. Ina godiya da tarin ni'imomin ka a gare ta" ta Wago fuskarta duk hawaye. Suwaiba ta ce "Ji wata gulma, har da sujjada kamar auren gaske, wai a dole sai an raina wa mutane hankali. Mu dai a hanzarta a yi a bar mana Waki"

Nana ta kalle ta ta ce "Suby kenan, ai duk ci gaba ci gaba ne, ba Waki ba gidan zan bar muku baki Waya ku sake, ina fatan aniyar kowa ta bi shi"

Suwaiba ta ce "Aniyar kowa ta bi shi kamar yaya, me ki ke nufi?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zan biye miki ba, ni yau ina cikin farin ciki ne a gare ni, ba zan biye miki ki lalata mini ita ba" Suwaiba ta ci gaba da faWar maganganu. Nana kuma ta fice ta bar mata Wakin.
A hakan an sassamu wanda suka bayar da gudummawa sosai da sosai, domin kowa yana yabon Nana da halaye na gari, dan duk 'ya'yan malam Isa babu mai haurinta da biyayya, duk da wasu lokutan ita ma tana da faWa, amma akwai ladabi. Ummi ta kasa ta tsare tana karSar kaya da kuWin gudunmawar da kanta,
Ta kuma din ga oarin, duk wani yinurin kawo hargitsi da Mama take oarin yi a gurin taron ta hana.
Nana ta samu kayan kitchen, da kuWaWe daga hannun jama'a da dangi.

Da yamma sai ga Yusuf da mota, tare da Sule, Hajiya Amina ta ce a Wauki Nana a ciki.

Yaya Atine ta ce a fara zuwa su ga gurin, su san abin da za su saya, amma Yusuf ya ce babu buatar hakan, amarya za su Wauka.

Gaba Waya jikin Nana a sanyaye yake, su Yaya Atine suka saka ta sake wanka, Ummi ta bata wata lafaya da ta saya mata, ta saka ta feshe ta da turare.

Ana ta rangaWa guWa, aka kai Nana gurin Mama wai ta yi mata nasiha.

Mama ta ce "A'a ni me zan ce, ai ta san komai ba abin da ba ta sani ba, a sauka lafiya"

Nana a ranta ta ce "Ko ba ki faWa ba lafiya zan sauka, kuma sai Allah ya kunya ta ki".

Baba yana ofar gida, aka kai masa Nana ya yi mata nasiha.
Ayshacool
Ya are mata kallo ya ce "Yanzu kin ga abin da ki ka janyo wa kan ki ko Asma'u? To ki buWe kunne ki saurare ni, babu zawarci a gidana, duk Wan da zan aurar kin san ina jaddada wannan, ba zawarci babu yaji a gidana. Allah ya rufa miki asiri da miji na gari, amma fafur ki ka i. Je ki Allah ya ba da sa'a ya baku zaman lafiya" Nana ta daskare a gurin ta kasa motsi balle ta tashi.

"Na ce ki je Allah ya sanya alkhairi" ya maimaita mata.

Ta Wago idanunta a hankali ta ce "Baba... Sai kuma maganar ta maale ta i arasa fitowa, saboda kuka da wani abu mai nauyi da ya danne mata maoshinta.
Ta yinura ta tashi, har sun kai bakin motar, ta waiwaya, kawai ta ga Baban ya zubo mata ido, idanunsa cike da hawaye.
Kawai ta yi bismillah ta shiga motar.

Ba Nana ce yarinya ta farko da Baba ya aurar ba, amma har cikin zuciyarsa ya ji rabuwa da ita, duk da tarin haushinta da yake ji. Wani sashen na zuciyarsa kuma ya fara tunatar da shi, da jin kamar bai kyauta ba abin da ya aikata.

Kasancewar mota Waya tak aka kawo, daga Yaya Atine, Anty Sa'a sai Ummi suka tafi raka Nana.

Su na tafe a hanya su na ta hirar su, Nana kuwa zubar da hawaye kawai take yi.
Sosai Yusuf ya ji tausayin Nana, shi kansa ya jinjina girman wauta da rashin sanin ciwon kai da mahaifin Nana ya yi.

"Kai wannan wace irin unguwa ce duk babu mutane, wannan ai sai a yanka mutum a binne ba a sani ba"

Ai kuwa babu shiri Nana ta Wago, tabbas haka ne, unguwar manyan gidaje ne sosai awon gwamanti, sai dai babu alamar akwai jama'a da yawa a unguwar.

Gaban wani gida suka yi parking, mai Wauke da doguwar katanga.

Ko da suka fito, Yaya Atine ta ce "Aka ce mai gadi ne, ya na ga katafaren gida haka?"

Sule ya ce "Eh gidan da zai yi aikin gadin ne, a Wakin masu gadi za su zauna"

Ta ce "To ikon Allah" ya buWe gate Win suka shiga.

Akwai atuwar haraba a gidan, ta ko ina shuke-shuke ne, main gidan kuma yana can nesa da gate Win gidan. Daga nan kusa da gate Win kuma wani wani aramin gini ne.
Sule ya buWe Wakin ya ce su shiga. aki ne babba falle Waya, sai banWaki sai amshin sabon fenti da kuma turaren wuta yake tashi.
Sabuwar katifa ce gal babba a Wakin, ga labulaye da wardrobe mai guda biyu da mudubi arami, ga kuma carfet a tsakiyar Wakin.

Yaya Atine ta ce "Yanzu a sati Wayan ku ka yi wannan shirin?"

Sule ya ce "Eh, wani mu muka yi, wani kuma Hajiyar da muke yi wa aiki ce, ita ta sai labulaye da abin shimfiWar nan, da kayan Wakin ma, abubuwa kaWan mu ka arasa"

"Lallai tana da kirki sosai, bayan kayan da ta je ta kai mata gida. Amma Ummi babanku ya tafasa makaronin asara ko cokali fa bai saya wa Nanan ba"

Ummi ta tsuke fuska ta ce "Babu kitchen kenan? A ina za mu ajiye mata kayan kitchen Win"

Sule ya ce "Ai abu ne na maleji, sai dai a ajie mata a nan Win, tun da yana da girma sosai"

Anty Saude ta ce "Bawan Allah kuma cikin gidan da mutane?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh akwai, sai dai ba ma zauna bane ba"

Ya Atine ta shiga banWaki, ta kunna famfo ta ga ruwa na zuwa, ga shi har da wearing Win nepa da sola na gidan a Wakin.

"To yanzu ina angon, mu fa ko sau Waya ba mu gan shi ba"

Sule ya ce "Yana nan tafe, sai an jima za a rako shi, idan kuma za ku jira ne to shikenan"

Yaya Atine ta waro ido ta ce "A ina Win? Wannan unguwar duk kangwaye, ku wuce mu tafi ke Nana Allah ya baku zaman lafiya"

Ummi ta rie

Please Login or Register in order to submit comment