Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba Waya.

Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta i sakar wa Jamila fuska gaba Waya.

Jamila kuwa ta din ga issimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaWan ba.

*
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa.
Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa.
Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara.
Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita.
Auwwalu ya Wauki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma Wan kyakykywan jariri, ka ga Wa kamar na larabawa"
Hajara ta amsa da "Amin dai"

Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?"

Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a a'ida fa Wan nan, sunana na ya kamata a saka masa"

Nene ta ce "Saboda kai Win waye?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laanin ne kawai ba Waya ba"

Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuWi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karSa ba, amma Nene ta amshe.
Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen mawabta, suka gaggaisa.
Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faWuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko aisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a asar da ba ta da kowa ba.
Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali.
Aka shimfiWa su tabarma, da yar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faWa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu.
Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi.
Ta daina ganin su Nene gaba Waya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta Wauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani bain warangwal da yake bin ta, hannun warangwal Win kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki.
Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da warangwal Win, tana son yin addu'a ta kasa.
"Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta.
Sai ta buWe ido ta kalli Nene.
"Tashi mu tafi yamma ta yi"
Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da warangwal ta nufo ta.
Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taSa ta, yi hauri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana.
Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben arf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta araso gare ta, ta illata ta.
Amma Nene ta dani hannun Nana, ta hana matar arasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga bauwa ba ce?"
Matar cikin wata irin harWaWiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan warangwal Win ya daina bina" gaba Waya suka kalli Nana. aya matar ta ce "Wani warangwal Win, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu"

Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa warangwal ya daina bin ta.
Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi.
Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba.
Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?"

"Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi"

"Ta zo ta yi mata me?"

Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako...
"Taimakon me?" Nene ta katse ta.

"Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo"
Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa.
Nene ta ajiyewa Nana nonon raumi, da abincin dare, amma ta i ci saboda sanyin da take ji.
Nana ta haWa kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji"

"Ke Nana" Nana ta Wago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?"

"Na oshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faWi wani abu a kaina ne?"

Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faWuwa.
"Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je"
Gaban Nana ya faWi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taSa gaya mata ba.

"Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karSe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke.
Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke.
Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da bain aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana oarin danne, amshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaa mai arfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara Wibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?"
Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni bain aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na i bayar da magani ya shanye mini afafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buWe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya Wauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu aautawa.
Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haura na ci gaba da bayar da magani.
Da yar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuWWa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuWWa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da yar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya i rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar Wa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can asarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taSa ni."
Nana tana Libraryn aisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene.
Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma bai irin da ya yi.
Ta daWe a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani.
Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a asa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da aisar ba ya cikin Wakin karatun nasa na wani lokaci.
Ta sanya hannu ta Wauki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa.
"Idan ka bari tsoro ya Warsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su Waya bayan Waya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya".
Ire-iren waWannan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daWa kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa.
Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na arashin asa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarWa.
Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin iyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaWayin Warewa gadon mulki.
Ga bautarwa ta fitar hankali ga na asa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba Waya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daWin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan.

A hankali ta buWe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana Waga kai ta ga wannan mahaukaciyar, rie da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan warangwal Win bai irin da shi kamar an gasa shi da wuta.
Ihu Nana ta saka a cike da matuar razana, ba wai dan ta ga warangwal Win ba, sai ganin Wan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke Wauke da zaren cibi.

Ayshercool
08081012143
Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga Wakin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana.
A matuar fusace ta arasa ta karSe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce "Uban me ya shigo da ke ki ka Wauke shi?"

Cikin tsoro ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Uban me ki ka yi masa?"

"Wallahi ban yi masa komai ba"

Nene ta shae ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa"

"To me yasa ki ka shigo?"

"Wallahi son shi kawai nake yi"

"an ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene"

Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan"

Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi hauri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa"

Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banWaki ke ki na bacci fa?"

Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida"

Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan"

Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani"

Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku arata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taSa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace"
Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan.

*
Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom Win ta.

"Magana nake yi maka, ka Wago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?"

Ya ce "Ba komai"

"To ka buWe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daWin abin da zai biyo baya"

Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye"

"Tashi ka bani guri" ya yinura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga Wakin, zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taSa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila.

Ko da ya tafi Wakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya Waga wayar ya ce "Hello Jamila"

"Jamila kuma, yau ba anwartaka?"

"Afuwan a yi mini afuwa"

Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Lafiya alau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba"

"Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba Waya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?"

Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaWan"

Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka"

Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?"

"Eh mana, ko na haura?"

"Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar aunar Abba"

"To abin aunar anwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya Wan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi.


Muhsin Win Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta i bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa.

Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama.

Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki yale shi yana kuka ki yi masa banza"

Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki"

"Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka Wauki yaron nan ki ka bata, sai na Sata muku rai daga ke har ita"

Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na bai"
Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga uruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ara wari, na nema miki ko gurin Winki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi wari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laSewa ai"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Nene ta ce "Amin yarinyar kirki"

Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faWo gidan.
Nana ta ba ta ce mata ta shigo Wakin, amma ta i.

Nana ta tashi ta fita ta shimfiWa mata tabarma, sannan ta Waukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi.
Ta karSe shi tana buWe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan"

Nana ta ce "Da gaske?"

Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi Waki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga warangwal Win nan.
Nana ta ce "Me ka ke buata ne?"

"Ki na ganina kenan?"

"Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da azanta ce"

Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta."

Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata".

Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda Waya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaSa ki ne"

Nana ta ce "Yaya aka yi ka san aisar, kuma ka san Sarkin baka?"

Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni warangwal, mun taSa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ona ni. Kuma na ga kin haWa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na Wauki fansar abin da aka yi mini a kan ki"
Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya.
Nana ta din ga jinjina azabar naci da rio irin na halittun nan.



BAYAN WANI LOKACI.

Girman Wan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene.
Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon Winki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haWuwa da Sayyid.
Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui.
Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan Wan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce Wan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga rauma, wai sai       

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  dai mu tsaya ya kalli raumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na Sata lokaci yana kallon rauma yana mia musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin i bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace."

Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faWanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni"

Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta Wauke shi.

Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene Wa"
Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan.
Nana ta din ga dariya daga Waki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri Waya, yana sha yana wasa da gashinsa.
Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji.

angare guda kuma, zuciyar Nana na saa mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haWa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take Soye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haWu da shi.

Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida.
Ta tashi ta fita kar ya yi wata Sarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen Win Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi.
"Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duununa kanta da hannu bibbiyu yana hira.
Ji ta yi tamkar an Waure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana.
Mesar ta mie sai ga aisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya Waga kai yana dariya yana kallon aisar.
aisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buWe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaSa ta jikinta.
Muhsin ya kama rigar aisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon aisar Win.
aisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya mie tsaye ya Sace. Sai da ya Sace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take.
Ta saka hannu da yar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya alau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?.
Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su aisar da kowane irin nau'i na shaiWani.

Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana.
Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya Sata rai, tamkar mahaifinsa.
Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa aisar da shi.
Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba.
Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi.
Ta shige Wakin ta udundune, ta bar su Nene.
Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu urar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaWai.
Ta taka sannu a hankali ta arasa inda yake, ya Wago ya kalle ta yana murmushi.
Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?"

"Da saui, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waWanda za su kashe ni"

Cikin damuwa ta ce "Ni fa?"

Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa

Please Login or Register in order to submit comment