Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.

akin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar.
Ta daWe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin i.
Bayan ta idar, Waya daga cikin 'yan Wakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita.
Can Sangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waWanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.

*

angaren su Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta i yin awo a Asibitin su Doctor Sharif.
Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba.
Gaba Waya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shauwar da ya kuma yi da Yusra.
Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin anin mahaifinsa ya yi masa magana.
Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faWan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren.
Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i.
"Wato arata ka je ka kai wa anin ubanka saboda mace ko Sagir?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ararki na kai ba"
"Rufen baki ko na make ka, ba arata ka kai ba ya kira ni yana faWa? Tun da abin da ka zaSa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama"
Kalaman na Hajiya, tamkar Wsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba Waya ya rasa abin da yake yi masa daWi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.


Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar.
Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne.
Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan Wakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin.
Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuuru za a yi shi gurin.
Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba.
Su na nan tsaye shugabar Sangaren na ara yi wa Nana bayani, da gurSatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo.
Gaba Waya suka wani ruWe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Bauwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"

Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana"
Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"

Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci Waya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"

Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"

Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"

Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"

"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka Wan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba Waya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.

*
Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a Wan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaWinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba.
Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma.
Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto.
Kasancewar komai na su ba kamar na asarmu ba, cikin ananin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon.
Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai wawalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba Waya" wata irin ara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da arfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya wace.

Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"

Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.

Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle.
Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta Wauka tana bulayin neman haihuwa ba a taSa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?.
Gaba Waya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta.
Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta.
Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar Wimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar.
Gaba Waya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka arare da Likitan ba.
Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi Satan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.

*

Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin Worawa da saukewa.
Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata abilanci, saboda ita ba 'yar asar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana Wan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta Wan fara wanwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba Waya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba Waya ba ta ji ta aminta da ko mutum Waya daga cikin su ba.
Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya Wauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma.
Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara Wan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.

"'yar Nigeria ya alawarinmu ne?"

Nana ta Wan saki fuska ta ce "Wanne?"

"Au har kin manta?"

Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"

Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haWu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"

Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"

Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"

"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haWu ba, ban je Agadez ba"

"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"

Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"

"Alhamdillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taSa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta.
A hankali ta ce "Ka yi hauri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a oarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raWa.

"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"

Nana ta Waga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"

Matar ta ce "Kamar yaya?"

Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"

Gaba Waya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar Wakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.

Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"

Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa.
Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba.
Gaba Waya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam.
Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiWima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiWime, amma ta tarar da saon ya yi balaguro zuwa Abuja.

Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya Waga yana faWin "Hajjaju barka da yamma"

"Sharif abu zan tambaye ka dan Allah"

Gabansa ya faWi, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa.

"Hajiya lafiya dai?"

"Lafiya alau, tambaya zan yi maka dan Allah"

"To Allah ya sa na sani"

"Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?"

Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?"

"Ka bani amsa kawai"

Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani Soyayyen abin da bai kamata ba.
Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba.

"Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?"

"A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba.
"Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai Wauke da zuciya irin ta Wan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taSa zuciya. Duk da ta daWe tana yin sa a Soye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki Waya, sai ta sare.

*
Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita.
Ya kasance taronsu na ungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat.
Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi.

Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan"
Jamila ta Wan taSe baki kawai.
Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba"

Jamila ta ce "Mummy kenan"

"A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi"

"To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma arara ki ka nuna ba kya aunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haWe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki"

Hajiya Sa'a suka haWa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na i ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daWe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuWinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so."

"Amma Abba ma ai yana da kuWi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuWi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata asaita, kuWi da wadatar mace, inuwar aure ginshii ce kuma sutura ce ga 'ya mace.
Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son Wan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi oarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaWan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da arshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinura ta tashi, ta bar Wakin.

Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuWi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da arfin tsiya ta yi tawaye"

Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taSa rainon Wan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin aa, daga nan zan yi maganinta"

Safiyya ta jinjina kai.

Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ungiya.

Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call.
Ta Waga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?"
"Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba"

Cikin tashin hankalShukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?"

"Dan Allah idan da hali ki zo gida"

"Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya"

Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta Wauki mota ta tafi gida. Tana matuar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na anana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta rie ta da halin ta, sai da ta ara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta.
A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta arasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Yi hauri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daWi a raina."

Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?"

"Shukura wai ba ni da mahaifa"

Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?"

Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A arshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taSa gaya mini ba"

Shukura ta Wan yi shiru sannan ta ce "Anya kuwa? Kin san fa kin daWe da daina zuwa Asibiti a kan matsalar nan, Daddy ba ya so. Sannan ku ne ku ke yarda da maganar Sharif Win nan, ki rabu da shi mu je wani Asibitin daban, a sake duba ki a tabattar da abin da yake faruwa. Duk da ba na tunanin za a samu matsala a abin da can Egypt Win suka gaya miki."

Ta girgiza kai ta ce "A'a Shukura, babu inda zan sake zuwa, na yi maganar ne da ke dama na samu sanyi a raina, na kira babanki ba ta shiga"

Shukura ta yi shiru, kawai dai ta ji ita abin kamar akwai lauje cikin naWi.

*

Nana ta shafe sati na biyu, tana aiki a wannan gidan Abinci. Sai dai ita kanta tana mamakin irin yadda Al Hussain yake kyautata mata. Hakan ya sanya gaba Waya suka ara saka mata ido suka tsangwame ta, mussaman Adama da 'yar ta Raliya, da alamu suka nuna Al Hussain take so.
Idan aiki ya Wan yi saui, Nana kan fita ta shiga cikin gurin cin abincin, ta zagaya ko za ta ga ko mai da Sayyid ne, amma ba ta ga kowa ba. Sai dai gabanta ya kan faWi a duk lokacin da ta ga masu rawani sun zo gurin cin abinci, sai ta ga kamar za ta gan shi a cikin su.
Ta gama zagayenta, ta koma cikin gurin girkin, Adama ta kalle ta ta tsuke fuska ta ce "Daga ina ki ke, ana tsaka da aiki?"

"Na Wan je wani uzuri ne"

"Na me, kuma a ina?"

Nana ta ce "Uzuri dai na Wan Adam, na yau da gobe, ai rayuwa na buatar sirri ko?"

"Ni fa na fuskanci take-takenki na rashin kunya baki da kunya ko kaWan, saboda kin ga Al Hussain yana tsaya miki, wallahi idan ba ki yi wasa ba sai na kawo arshen aikinki a nan, sai na saka an kore ki daga gurin nan"
Kallonta kawai Nana ta yi ta kawar da kai, ta ci gaba da abin da take yi. Har ta gama bala'inta, 'yan korenta suka taya ta, Nana ba ta tanka mata ba.

Washegari da sassafe, Nana ta baro Wakinsu, ta tafi kitchen ta fara aikinta, duk da wasu lokutan suna yi mata mugunta, su din ga sakar mata aiki.

"Ina sauran ma'aikatan gurin nan?" Ta ji wata murya ta daki kunnenta, da ba ta san mai ita ba.
Ta Waga kai ta kalli matashiyar matar, doguwa fara jawur, mai kama da Al Hussain.
Kawai ta mayar da kanta ta ci gaba da aikin gabanta.

"Ke ba kya ji ina magana ne?"

Nana ta Wago kai ta ce "Su na zuwa"

Nana na rufe bakinta, sai ga Adama ta shigo, ita da sauran ma'aikatan.

Wata irin rikicewa suka yi, suka hau tsuma su na gaida matar.

"Wace ce wannan? Da ba ta da mutunci ba ta da Wa'a, nake magana tana bani amsa a wulaance" ta yi maganar tana nuna Nana.
Nana a ranta ta hau mamakin wane wulaancin ta yi mata, ita da ta zo guri babu sallama babu gabatar da kai, koma wace ce ba zai wuce ita ce mai gurin da ake faWa ba. Nana a ranta ta ce "Koma wace ce ke, Allah ya fi ki" sai dai ba ta sake Waga kai ta kalle su ba, ta ci gaba da yankan kabejin hannunta.

Ayshercool
08081012143.
Adama ta risunar da kai ta ce "Ki yi hauri ranki ya daWe, mu ma haka muke ta fama da ita mu ma, amma ki yi hauri bauwa ce"

"Bauwa kuma ba ta iya magana ba, bauwa daga ina?"

Raliya ta ce "'yar Nigeria ce"

" 'yar Nigeria, waye ya saka Al-Husssain Waukar wata 'yar Nigeria, dama haka 'yan Nigerian ku ke, ba ku da mutunci ba ku san me ku ke yi ba?" Maganganun matar sun soki zuciyar Nana, tamkar ta mayar mata da martani ta ce "Ku a Nijar ba ku san muhimmancin sallama, da girmama na asa da kai ba" Sai dai ta yi shiru ta ci gaba da aikin gabanta. Haka ya ara tunzura matar ta fita fuuuu tana bala'i tana sai Nana ta bar aiki a gurin.

Matar na barin gurin Raliya ta kalli Nana ta ce "Allah ya ara, idan kina cin asa ai ki kiyayi ta shuri, yau kin taSo abin da ya fi arfinki, kin yi a bakin aikinki"

Babban abin da ya Waure musu kai, bai wuce yadda Nana ta ara yin burus, ta ci gaba da aikin gabanta.

Adama ta ce "Anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?"

ayar ta ce "Ko ta mayar da mu mahaukata ba. Amma idan haukan take ji, ai Hasna babarta ce"

Wata matashiyar mata ce ta shigo, sanye da uniform a jikinta. Ta yi sallama suka amsa.
Ta ce "Ina Nana?"

Nana ta ce "Ga ni"

"Ki zo ana neman ki a ofishin Al Hussain"

Ta ce "To gani nan" ta yi maganar tana ajiye wuar hannunta, ta wanke hannunta ta bi bayan matar.

Sai dai har matar ta yi gaba ta bar Nana, da yar Nana take iya Waga afafuwanta, saboda matsanancin nauyin da ta ji sun yi mata, ga sanyi da ya fara ratsa ta ta ko ina.

"Ya hayyu ya ayyum. Allah ka taimake ni, aisar kar ka yi mini haka mana" Ta furta a hankali zuciyarta na bugawa.
Ta saka hannu ta tura ofar ofishin. A tsaye ta tarar da matar Wazu, tana zazzaga masifa, Al Hussain yana zaune yana kallon ta.
Sai dai Nana ta yi turus, ganin aisar a zaune a jikin na'urar sanyaya guri, da ke cikin Wakin.

"Nana araso mana" muryarsa ta dawo da Nana hayyacinta. A hankali ta arasa ya ce ta zauna a kan kujera.

"Al Hussain ka na da lafiya kuwa? Yarinyar ta yi mini rashin mutunci, ka ce ta zauna a kan kujera?"

Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na Wan lokaci, ba ta da matsala sam. Nana meyafaru ne?"

Nana ta buWe baki za ta yi magana, Hasna ta tari numfashinta ta ci gaba da masifa.
Al-Husssain ya daki tebur ya kalli Hasna, hakan ya sanya ta yin shiru tana harar Nana.
Nana ta ce "Ban san wace ce ba ne, ta yi hauri"

Hasna ta daki tebur ta ce

Please Login or Register in order to submit comment