Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma"

Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar afa da suka sha.

Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba Waya tsoron taSa kuWin take yi. Gani take yi kamar arewa za su yi.

Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan.

Nana ta shiga Wakin da Sallama, tana faWin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi hauri Uwani ce ta din ga ja na, afafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba.
Ga shi a tsakiyar Wakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba.
Ayshacool
Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi.
Aikuwa tana juya shi ta Wan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi.

Wayarta ta gani a arashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baar wayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta.
Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta Webo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah.
Ta je ta rufe ofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raWaWin da take ji a fatarta.
Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana mia jikinsa yana ara sandarewa.
A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta Wan Waga idonta, ta ga aisar tsaye a jikin ofar Wakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raWaWin da yake ji.
"Ko dai ki bi a hankali, ko wannan Wan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta Waga kai ta kalli inda aisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa Wan yatsanta.

"Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaWai abin da nake yi.
Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar aisar.

****

Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba Waya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe".

Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin oshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haWa ki da ita."

"To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaWa na raya, Baban su Walida ya i ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi".

"A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaSa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata"

Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba Waya ba ta cikin nutsuwarta.

****

Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa anin wanka a Waki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya.
Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu wari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taSa yarda ta kwanta.
Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman afafuwansa.
Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faWo mata. Sai da ta Wan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?.
"Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa.

"To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?"

"Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaWe ta.
Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faWi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yainin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu arara ayyukansu da abubuwan da suke faWa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya.
Ayshacool
"Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba.
Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba"

Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid"

"Ma vie"

Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaWo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune.

Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuWi a hannun ta.
A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haWawa masu hawan jini, da wanda Sarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya.

Ba ta jira ya idar       

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haWa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba.

Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ofa ya zauna yana kallon hanya.

Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo Sawon kwakwa da sassaen zogale, sai kuma farin zoSo.
Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo Wan kanumfari ta zuba a ciki.
Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi hauri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla"

"To na gode"

"Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba"

"Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki mawabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi ta gigice gaba Waya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karSi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na mawabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roa mini"

Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata"

"Sayyid, anya an taSa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daWi wallahi"
Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta.

Maganinta ya daWe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa.

"Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana Sata rai.

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu Waci ko bauri fa"

"Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"

"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"

Da yar ya yarda ya karSa, ya WanWana ya ji babu Waci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji Wumin maganin ya yi masa daWi.
Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya Wora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haura da shan shayi.

Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karSe shi.
Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a asa ta sha.
Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banWaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.

Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"
Ayshacool
Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya Wan yi shiru yana kallon ta.

"Ranar da aka kai ni, kai ma an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daWe muna haWuwa da kai."

Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"

Ta Sata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".

Ya Wan sake zua shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"

"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"

Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin lie mini, har cikin Wakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"

"Ni ba ina sane na shiga Wakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin Wakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"

"A'a faWi gaskiya dai, ni ki ka leo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.

"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse walla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faWa da wanda Mama ta din ga yamaWiWi da ita, abin ne kawai ya dawo mata.
Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa Wauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" KwaSe baki ta yi cikin shagwaSa, wasu hawayen na ziraro mata.

"Na ce na daina fa, ki bari irjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta.

"Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke"

Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faWuwa.

"Amm na san kina hauri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan Sangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san...

Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na Wora wakena"

"A'a ki tsaya mu yi magana"

"A'a ba sai mun yi ba"

"To kar na sake jin kin bi dare ki na taSa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta Sace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba Waya. Cikin azama ta mie ta Wauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiWa yana dariya.

Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita.
Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaWai.
Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan Wawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai.
Tana Wagowa suka haWa ido, ta murguWa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta.
Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna.

"Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa"

"Kawo na yanka miki salak Win"

"A'a kar ka yanke hannu"

Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda saui ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?"

Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta Waga ido, sai su yi ido huWu da shi, sai ya yi mata murmushi.

Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?"

"Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba.

"Idan na ara jin saui, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya"

Ta ce "Alhamdillah, lallai saui ya samu."

Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na Wan tattaka na ga gari"

Nana ta faWaWa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi"

Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan"

Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi hauri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya arfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ure masa."

Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa.

Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, irjinta na bugawa da sauri da sauri.

Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take Wauke da wasu irin murWaWWun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda asa suka mamaye gurin. Ga wani irin aton kogo a jikinta, hakan ya nuna daWewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin.

"Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye.
"Ji nake yi kamar na san gurin nan"
Ayshacool
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taSa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin waliyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, rie da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya Wau kyarma, ta ara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su aisar ne su na bayyana a bayansa.
Tsohon ya kalle ta, ya buWe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki."

Yana rufe bakinsa, Waya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan.
Tana zuwa matar, ta hankaWa Nana asa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini.

"Ya hayyu ya ayyum ya Allah. Allah ka kawo mini Wauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi" Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci.

Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?"

"Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni"

Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?"

"Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa.

Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko Waya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta.

Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni"

Ya ce "To mu je ki yi"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube"

Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta mie ya kama hannunta, ya haska fitila har banWaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta mie jikinta yana rawa.

Ya rungume ta ya ce "Ki yi hauri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi Sari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"

"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"

Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaSa ta da yar, ta gyara jikinta, ta Wauraye jikinta, da banWakin su ka koma Waki.

Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.

Suka kwanta yana Wan shafa ta, cikin sigar rarrashi.

A hankali ta ce "Sayyid"

"Na'am"

"Da gaske mun fita Wazu ko?"

"Eh mun fita"

"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"

"Eh haka aka yi, mun je"

Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"

"FaWuwa ki ka yi, na rie ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"

Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa.
Wannan bafulatanar matar ce, ta ara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ara rintse idanunta tare da aname Sayyid.

Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da yar ta samu ya yi alwala ya yi salla.

Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta Wauke.
Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko Waga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaWa a gona.

Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.
Ayshacool
Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta dama masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ame am. Ta sake oarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.

Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.

Gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma oarin ganin ta miar da hannun nasa, amma hannun yana maale, kamar an tsotse shi.

Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa Wauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta Webo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buWe bakinsa ba.

"BuWe baninka na baka" Ta yi maganar tana oarin danne hawayen da ke oarin wace mata.

A hankali ya buWe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na oarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta.
Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa.
Ta fara oarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haWiye wani kuma ya zubo.
Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido.
Ganin yana gyangyaWi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.

Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"

Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"

"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"

"TaS gaskiya da nisa gurin nan ba kaWan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"

"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"

Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"

Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist Win ya bi Nana.

Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne,

Please Login or Register in order to submit comment