Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskarta cike da damuwa.
Ayshacool
"Sayyid ka zo za ku gaisa da 'yan uwan Mamana, su ne suka kawo mana ziyara ka zo mu je ku gaisa. Amma idan da hali ka yi musu magana dan Allah"

Ya ce "To, amma idan ina kallon fuskarki a haka, ba zan iya magana ba"

Ta yi murmushi ta ce "Ba na son rigima, mu je to"

"Ina jin kunya, wuce gaba na biyo ki"

Ta yi murmushi, ta yi gaba ya bi bayan ta.

Ya yi sallama sannan ya shigo, ya tsugunna, ya sauke takunkumin fuskar sa ya ce "Barkanku da zuwa, ya hanya?"

Jin gaisuwar ta sa suka yi banbarakwai, amma Adda Saude ta ce "Lafiya ™alau, mun same ku lafiya? Ya iyalin?"

Ya ce "Alhamdilillah mun gode Allah"

"To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, bamu samu mun halarci taron biki ba, sai yanzu muka zo. Allah ya baku zaman lafiya. Sannan a yi ta ha™uri, shi aure Wan ha™uri ne, ba farkon auren ba, sai zama ya yi zama ake gane ha™urin. Ubangiji Allah ya yi muku albarka, dan Allah ka yi ha™uri da ita ka ri™e ta amana"

"In sha Allah"

Anty Fati ta ce "To ina fatan dai ba za ka yi mata kishiya ba, tun da ta ciri tuta ka aure ta, tun da dai an ce ba kwa auren wanda ba ™abilar ku ba? Dan ni 'ya ta daidai take da mata huWu, har da Woriya."

Mi™ewa ya yi yana murmushi, ya nufi hanyar fita. Nana cikin shagwaSa ta ce "Sayyid ba fa ka ba da amsa ba"

Yatsansa manuniya ya nuna mata, ya ce "Ke kaWai ce Ma vie"

"Anty Fati ki zama shaida"

Ya fice yana murmushi, Anty Fati ta ce "Ke babu ruwana, namiji na mata huWu ne, wasa nake yi kar ki saka a hakan a ranki"

Nana ta basar da maganar, dan wani irin zafi ta ji ya fara taso mata.

Adda Saude ta ce "Nana an baki 'yan abubuwa kuwa na gyara, ko kuwa haka kawai su ka ninko ki, su ka kawo ki?" Nana ta yi shiru, tare da sunkuyar da kai, wa ya tsaya bin ta kan ba ta wani abu, har gara Ummi ta kawo mata, ranar da su ka zo da su Jamila, ta rubuta mata yadda za ta yi amfani da shi, amma tun da ta jefa ledar a drower, ba ta sake bi ta kan su ba, saboda pressure gabanta ta ishe ta, ba ma ta taSa tsammanin wani abu zai shiga tsakaninsu ba.

Anty Fati ta yi wa Nana tambayoyi, a kan matsalar sanyi, Nana ta ce ita ba ta jin komai na alamar sanyi.

"To duk da ke kaWai ce a gurin mijinki, amma kar ki zauna ki mi™e ™afa Nana, kar ki ga ba shi da ™arfi, tsaf 'yan mata za su din ga kawo masa farmaki, ki na ganinsa tubarkallah da shi. Nana ki yi addu'a, ki yi gyara kuma ki yi biyayya, za ki zauna lafiya in sha Allah. Nana ki yi kissa, kar ki zauna haka sai abin da ya zo miki, ki zama mace mai tunani Allah ya baku zaman lafiya"

Suka yi ta yi mata nasiha, har aka yi sallar la'asar. Su na yin sallar la'asar, su ka ce za su tafi, saboda kar su yi dare a hanya.

Nana ta ce "Bari ya dawo daga masallaci, sai na raka ku" Duk s karSi lambobin wayar su, su ma suka karSi ta ta.

Suka shirya tsaf za su tafi, Nana ta fito ta tarar ya dawo daga masallacin.

Ta ce "Sayyid, za su tafi zan raka su ko bakin titi ne, su hau adaidaita sahu, su je tasha".

Ya ce "Bari mu je tare"

"Idan mutanen gidan su na neman ka fa?"

"Wata ta ™one a gidan, sun tafi kai ta Asibiti"

Nana ta waro ido, ta ce "Wace ta ™one?"

"Ban sani ba, kawai na buWe gate sun ce mini za su Asibiti, wata ta ™one da ruwan zafi"

Nana ta ce "Ikon Allah, Allah ya sauwwa™e."

Su Adda Saude, su ka fito, suka tafi raka su tare da Sayyid.

Su na tafe su na ci gaba da yi musu nasiha, a bakin titi, suka tarar musu adaidaita sahu. Nasiru dama tun da ya raka su, gida ya koma saboda zai je makarantar Islamiyya.

Nana ta tambayi mai Napep ta ce "Nawa za ka kai su tasha" hararta Buzu ya yi, ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu, ya bawa mai adaidaita sahun.

Ya sake Waukko ba™ar leda, ya ajiye wa Anty Fati a kan cinyar ta, ya ce "Mun gode sosai"

"A'a ba zamu karSa ba, Wawainiyar ta yi yawa"

Nana ta ce "A'a Anty Fati, ba zai ji daWi ba. A ce ina gaida Mama, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi magana idanunta na cika da hawaye.

"A'a Nana, kar fa ki je ki zauna ki yi ta koke-koken nan, idan haka ne, za mu daina zuwa"

Ta goge hawayen ta ce "Na daina, ku gaida gida"

Sai da su ka ja motar su ka tafi, sannan su ka dawo gida.
Ayshacool
Nana ta zuba masa Abinci, ya ce "A'a ba na jin yunwa yanzu"

"Sayyid ina jin daWin yadda ka ke mutunta 'yan uwana idan sun zo, kuma na ji daWin yadda yau ka yi magana da su, har ka yi raha, har cikin zuciyata na ji daWi sosai da sosai. Allah ya nuna mini 'yan uwanka haka, zan yi iya yi na, na kyautata musu nima, Allah ya sa su amince su karSe ni a matsayin Waya daga cikin ahalainsu".

"Na ji kin ce a gaida Mama, mamanki na nan ta bari, a ka aura miki ni?"

Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba ga Maman nawa nan ka gani ba, ranar da mu ka je duba Baba?"

"Ba maman ki ba ce, kuma ko mamanki ba ta so na, ba za ta din yi mana irin kallon da waccan matar ta yi mana ba. Amma wannan da su ka zo, na ga su na murna sosai da sosai da ganina, har suka yi mana addu'a, duk da ban san me yasa ki ka yi kuka ba da suka zo"

Nana ta haWiye abu mai Waci da ya tsaye mata a wuyanta, ta san yanzu ba ta da wani mutum mafi kusanci da ita, sama da shi, dan haka babu bu™atar Soye masa komai, dan haka ta numfasa ta ce "Tabbas ba Mamana ba ce wadda ka gani a gidanmu. Mamana sun rabu da Baba, tun ban fi shekaru tara ba. Ba komai nake iya tunawa ba, kawai dai na san Mama ba sa jituwa da dangin su Babanmu, su na yawan samun saSani. Har dai suka rabu. Ta ce Baba ya bata mu, ni da yayana amma ya hana ta. Ba ta daWe da rabuwa da shi ba, ta yi wani auren. Abin ya Sata wa Baba rai sosai da sosai, ya ce kamar ta sane ta kashe auren dan ta fita ta auri wani, wanda ta aura Win kuma an ce ya taSa son ta, ba ta aure shi ba.
Adda Saude ta zo ta Wauke ni ta ™arfin tsiya, ta tafi da ni, amma da ™yar na kwana a gidan da Mama take, mijinta ya ce sai an fita da ni. Abin dai duk babu daWi, aka sake mayar da ni gidan Baba. Na fi shekara bakwai ban ganta ba, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Ya rungume Nana a jikinsa yana shafa bayanta a hankali.

"Ki daina kuka, za mu je mu ganta in sha Allah, ke gara ke a kan ni ai. Ban sani ba ma ina da maman ko ba ni da ita, ni ke kaWai na sani"

Ya jima yana rarrashinta, sannan ta Wan tsagaita da kukan da take yi. Ta fara buWe kayan da suka kawo mata. Ba masu tsada ba ne ba, amma ta yi ™o™ari. Bedsheet kawai biyar ne, huWu na gida, Wan waje Waya. Ga kwanuka har da kayan sakawa.
Sai da ta bari an kira magariba ya fita, sannan ta sake fashewa da kuka, ta yi kuka sosai sai da kanta ya fara ciwo,  sannan ta ha™ura ta yi shiru.

*

Jikin Shukura ya yi kyau, ta warware, wannan kumburin duk ta sace, aka rubuta mata sallama.
Doctor Sharif ya sha jinin jikinsa, dan sai da ya tsorata ya fara wasi-wasin ko dai Shukura ta san abin da ya aikata mata, saboda yadda ta canza gaba Waya. Wasa da dariyar ma da suke yi, gaba Waya ta daina, da ya shigo sai ta tsuke fuska. Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya din ga ba shi, kawai yanayin da take ciki ne, na rasa Wan ta da ta yi, ya sanya duk ta canza ta daina walwala.

Hajiya Amina ta dube ta, ta ce "To Shukura yaya? Gidanki zan mayar da ke, ko gida za ki taho?"

"Mummy mu je gida na Wan huta tukuna"

Sagir ya harari Shukura ya ce "Mummy, a dawo da ita kawai, ke ma ki huta da Wawainiya tun da ta samu lafiya"

Su na cikin mujadalar, Alhaji Zailani ya kira waya, ya ce "An sallame ku ne ko kuwa? Ya ce mini yau za a sallame ku"

"Eh, an sallame mu, ta ce gidan zata taho, mijinta ya ce ta koma gida"

"Saboda me? Ta koma ta yi masa me? A dawo mini da 'ya ta gida ta huta, kafin ta koma, me za ta je ta yi masa da yanka a jikinta".

Hajiya Amina ya ce "A'a kar a yi haka, mijinta ne fa"

"Ni kuma ubanta ne, ki ce masa na ce a kai mini 'ya ta gida ta huta, idan ba za ki faWa ba, ni zan kira shi"

Sagir yana ji yana gani, haka ya ha™ura, aka mayar da Shukura gida, maimakon gidansa.

****

Nana ta kira su Adda Saude, suka tabattar mata da sun je Bauchi lafiya, ta yi musu bangajiya.

Yana ta shirin kwanciya, Nana kuma ta ™ura masa ido, zuciyarta ta yi mata nauyi, ba ta jin daWin komai.

Ya zo kusa da ita, hannunsa ri™e da kofi ya mi™a mata. Ta saka hannu ta karSa, tana kallon sa.

"Na ga ba ki ci abinci ba, madara ce na kuma karSo miki"
Ayshacool
Ta buWe kofin, ta kalli madarar, da wani ba™in abu a kai.

"Habattussauda ne a ciki, ko na fara sha ne?" Ya yi magana yana mi™a hannunsa zai karSi kofin.

Ta kafa kai, ta fara shan madarar, sai da ta shanye ta ajiye kofin.

Ta dube shi ta ce "Me yasa ka ke bani madarar nan?"

"Na ji wani likita ya faWa a radiona, yana ™ara wa mata lafiya sosai"

Ta Wan yi murmushi, sannan ta numfasa ta ce "Sayyid, da gaske ™abilarku, ba sa auren macen da ba ta su ba?"

Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce "Duk abin da zai fito daga bakina a yanzu, ™arya zan yi miki, saboda ba zan iya tuna komai a kan ™abilar tamu ba"

Cikin rawar murya ta ce "To yanzu idan Allah ya sa ka tuna waye kai, da asalin rayuwar ka, ni mece ce makomata? Za ka karSe ni a matsayin matarka kuwa?. Idan kuma aka samu akasi ka manta da ni baki Waya fa? Yaya zan yi? Mece ce makomata?"

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
41

Ya yi shiru yana nazarinta, hawaye ya wanke mata fuska, har cikin ranta maganganun da suke fitowa daga bakinta. Tabbas! Tambayoyin nata a kan hanya suke, kuma sun cancanci ta samu amsar su, amma ta yaya zai bayar da amsar abin da shi kansa bai sani ba?

Ya dake ya tattaro nutsuwar sa, ya Wago fuskarta, su ka haWa ido.

"Ba na so, ganin wannan na Waya daga cikin abin da yake tayar mini da hankali, na rasa nutsuwa, hawayen ki zafi yake haifar mini a zuciyata, kuma yau wuni ki ka yi kuka" ya yi maganar yana share mata hawayen da yake kan fuskarta.

"Sayyid ka bani amsa, zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, da kuma wasi-wasi"

Ya sassauta muryarsa ya ce "Ma vie. Idan har tunawa da rayuwata da waye ni, zai sanya na manta da ke a cikin rayuwata, ina fatan na dauwwama ba tare da na tuna waye ni ba. A jikina ina jin rayuwar da nake yi tare da ke, ita ce rayuwa mafi aminci da kwanciyar hankali. Ba ki yadda ba da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taSa barin ruhina cikin nutsuwa ba, saboda abokan rayuwa ne"

"Sayyid"

"Duniyata"

Wani kyakyawan murmushi ne ya suSucewa Nana, ta ce "Kalaman ka na ™ara mini ™warin gwiwa, har ba na son na ji muryar ka ta Wauke ko sau Waya"

"Da gaske?"
Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ™ayatarwa.

Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shau™i ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi.

Ya ce "FaWi mana, ki furta"

"Me zan furta?"

"Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faWa" ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?"

Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ™asaita yana kallon fuskarta.

Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta.

*

Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, "Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na rufe shi, wannan ai take ha™™in Wan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki".

"Wallahi haka Mama ma ta faWa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata ha™uri, nima na ce kar a kai shi, ta yi ha™uri"

"Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu"

Jamila ta ce "Kaii babban yayanmu ne fa Mummy"

"Shi Win fa, shi ba dukan ki ya yi ba?"

"A'a ai bai kamata ba, da kunya abun"

"Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ™ara wa banda koma baya da hassada da fitintinu"

Jamila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Dan haka duk wanda ya yi yin™urin taSa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daWewa zan yi ba amma"

"To a dawo lafiya" Jamila ta yi maganar tana kashingiWa a jikin kujerar 3 seater da ke Wakin.

Har bacci ya fara Waukar ta, ta ji ana sallama, ta buWe idonta ya ce "Yi ha™uri na tashe ki, Mummy ta fita ne?"

Ta jinjina masa kai tana ™o™arin mayar da kai ta kwanta.

"Ta daWe da fita ne?"

"A'a"

Ya ce "Ok thanks " ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya Wan ™ura mata ido, kan ya fice.

****
Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haWa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa. Ya Waga su ka gaisa. Ta ce "Zailani, matarka ta fi ™arfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun koma gida"

"Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ™arfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti"

"Ba ta da lafiya me ya same ta?"

Ya ce "We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita, so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba"

Hajiya Sa'a ta Wan yi jimm sanan ta ce "Yayi Allah ya raba lafiya"
Ayshacool
Uwargidan sa da ke ™o™arin haWa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila, kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne.

"Ya dai lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ajiye masa tea Win ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a kansa.

Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya.

Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daWi sosai. Sai dai ya ji tamkar an Wora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an Waure shi. Ya yi mi™a ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal.

Ya lallaSa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ™o™arin sa, bai bari ta fahimci wani abu ba, saboda kar ya ™ara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita.

****
Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ™o™ari meatpie ta tsiri yi da safen.

Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haWa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya Wauka ya kai bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa.

Ta ce "Da daWi?"

Ya Waga mata babban yatsansa, alamar jinjina.

"To ka ce Allah ya yi mini albarka"

Murmushin sa ya ™ara faWaWa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce "Allah ya yi albarka"

"Amin Shugabana" ta yi maganar tana dariya.

"Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya"

Ta tsuke fuska ta ce "Nonon ra™uma dai ba nawa ba" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa ™warewa, ta Waukko ruwa ta ba shi ya sha.

Ta ce "Ba ruwana, kar ka ™ware ka ce ni ce"

Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon ra™umin, amma ta fara jin daWin sa sosai da sosai a jikinta.

"Sayyid, bari na kaiwa ™awata ko za ta ci"

"Wa?"

"Yusra" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan.

Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ™one, a Sare mata ™unar.

"Sannu ina kwana?"

Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. Šakin Yusra ta shiga da sallama.

Yusra ta Wago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta saki murmushi.
Nana ma ta yi mata murmushi ta ™arasa ta zauna a kusa da ita ta ce "Yayata, kin tashi lafiya?"

Yusra ta ce "Lafiya ™alau"

"Abinci na kawo miki, ko kin karya?" Ta ce "A'a"

"To ga wannan" ta saka hannu biyu ta karSa ta ce "Na gode" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye meatpie Win.

Ta Wan numfasa ta ce "Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wu™a ki ji kamar ki cakawa kanki, ko ki faWo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daWi Win nan?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Sosai, na taSa yin™urin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina ro™on Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita"

"Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karSa, salla ma kamar ba daidai nake yi ba." Nana ta rufe mata baki ta ce "Ki daina faWar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karSar addu'armu, ba dan haka ba da wata™ila haukacewa zamu yi gaba Waya"

Yusra ta ce "Haka ne, wallahi na ji daWin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san abubuwan da nake ji ba ™arya nake yi ba"

"Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaWai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ™arya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki"

Ta girgiza kai ta ce "Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai jikina ya mutu, kuma damuwa ta ™ara yi mini yawa". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta ha™uri.

Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ™ofa.

Su na tafe ta ce "Kin ga Siyama ta ™one ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na she™e mata shi a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce "Saboda me?"
Ayshacool
"A'a kar ki yi kuka"

"To ni ka daina yi mini irin haka"

"To na daina" ya faWa yana kai hannunsa fuskarta.

"Kar ki yi kuka fa" jin yadda ya shiga damuwa nan da nan, ya sanya ta ci gaba da kunna shi, ta hanyar yin taSara iri-iri.

A ranta ta ce "Ohh, wai yau ni ce ba a son na yi kuka, da uban wa ya damu idan ma rijiya zan cika da hawaye?"

Ta ™arfin tsiya ta saka ya din ga rarrashinta, da Hausa da French.

Da Asuba kuwa sam bai tashi da alamar ma ya yi fushi ba, saboda kar ta yi kuka.

Bayan ya dawo daga salla, tana kwance a jikinsa ta ce "Dan Allah Sayyida ka bar ni na je a yi mini kitson nan, na je gurin 'yar uwata dan Allah"

"A'a"

"Dan Allah Sayyid."

"Idan kin tafi wa zai kula da ni?"

Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke bu™ata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba"

"A dawo lafiya" ta zabura ta ce "Ka yadda na je?"
Ya jinjina kai. "Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana"

Ya yi murmushi ya ce "Sayyid yanzu kuma Shugaba"

"To ai duk abu Waya ne" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki da ta shiga.

Da safe ta ya ™o™arin gama girki da wuri, ta Wora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da duk abin da take sanya ran zai nema.

Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huWu kenan, an yi wa Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta.

Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya na duba ta, sai na tafi gidan Ummi."

"A'a"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah, kar su ga kamar wula™anci ne, an gaya mini abu ban je ba"

Ya kalle ta ransa a haWe, ya ce "Kar ki je gidan nan" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana ta zuwa.

Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma.

Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matu™ar tausayinta.
Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi.

Habu ne ya buWe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce "Ina mutumin?"

Ta ce "Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo"

"A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?"

Nana ta ce "Lafiya ™alau, ba ka zuwar mana kwana biyu"

"Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa"

"Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa"

Ya yi murmushi ya ce "Sayyid kuma?"

Nana ta jinjina kai ta ce "To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka Waura mana aure da shi ne?"

"Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma ban san sunansa ba nima"

Ta jinjina kai ta ce "To da gaske kai ne ka ke ba shi kuWin da yake kashe mana? Na ga kuWin aikin gadin ba wani yawa ne

Please Login or Register in order to submit comment