Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki Waya. Ta Waga kanta ta ga ba ta iya gano arshen Wakin.
Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga aisar a zaune lulluSe da wani abu mai haske sosai.

"aisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.

Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba Waya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"

"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."

"Kuma ka sha? Wai meye alaar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"

"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"

"Fushi da Sacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library Wi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama.
Duk ba wannan ba, duba can."
Ta Waga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library Win aisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya WaWWaure shi da wata irin igiyar arfe. asan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a asa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne"
"warai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu Waya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"

Nana ta buWe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaWin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.

Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi uri da ido ta ce "Kamar na san wannan"

"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da anwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ungiyar asiri. ayar kuma wannan bararojin da ta taSa baki magani, ta aura mata Wanta, wanda yake bain aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba Waya.
Ayshacool
Shikenan bissalam"

"aisar" sai kuma 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ ta yi ido huWu da Sayyid.

"Kin tashi?" Ta yinura ta tashi zaune, tana kallon Wakin.

Sayyid ya ce "aisar Win ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.

"Wane aisar Win?"

"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a asa, sai kuma abin da ya faru ya faWo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe Win, tana zazzage kayan tana kuka.

"KuWin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.

Ya yi mata shiru ya i kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faWa za su yi. Cikin ananin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.

Barira na kwance a Wakinta, ta yi WaiWai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a afafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo eyarsa a can arshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya.
Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banWakin, kanta ko Wan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.

Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiWe ta zama wata irin atuwar mage, baa irin, girman ta ya yi na tunkiya osashiya da ita, ta yo kanta tana buWe haora.
Da gudu Barira ta shiga Wakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.

"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"

Ba ta ce masa uffan ba, ta duunune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da yar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.

Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haWa kai da gwiwa.
Ya yinura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya Wauke ta.
Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.

Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaSi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.

Kwanki biyu da sace kuWin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuWin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. KuWin Nijar Win kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin Win nan, ba tare da ta rushe gaba Waya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata Waya dubu goma sha biyu take sayen su.
Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi hauri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.

Kwana biyar da kwashe kuWin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haWo mata da su, take ta cancana musu.
Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daWi, yana ta numfarfashi.

Abin Duniya ya ara damunta, ya kuma i cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.

"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da arfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi arfin mutum".

Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"

Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"
Ayshacool
"Ni fa ba na son kurman bai, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"

"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"

Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayai, mai azabar yaji, ya turnue gidan.
Nana da take lafiya alau ma, ta fara tari.
Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai Wauke, ta Waukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake onawa yake wannan uban hayain haka. Amma ya rie hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayai.

"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"

"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"

Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu.
Washegari ma, azabar hayain nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai Wauke saboda azaba.
Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayain nan.

A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.

Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a Waki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"

Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"

Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"

"Kamar yadda ki ka ji"

"Ni dai koma mene ne, ki yi hauri idan ba ki yadda ba, zo mu je Wakin ki ga halin da yake ciki"

"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi arfin duk wani maye wallahi"

Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faWa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauWa?"

"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zain kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"

"Mu ne mayun Barira?"

"Eh ku ne, ko na ce ke"

Nana ta arasa daf da Barira ta dami tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faWi asa.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
"Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?"

"Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba"

A sukwane Baba ya mie ya ce "arya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya Waukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?"

"Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan"

"Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri.

Ummi ta tsaya a bakin ofar, tana ta ba su hauri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga Wakin.

"To ban da wulaanci ma, ta shige Waki tai fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da hauri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya"

Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi hauri" Sai dai abin ya fi arfin Ummi, oarin hankaWe ta kawai suke yi, su cimma Nana.
Ana haka sai ga mawabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani.

Ana haka Baba ya araso, cikin tashin hankali.

Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?"

"Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?"

"Ai gama 'yan sanda sun zo, saSani suka samu da wanda suke zaune gida Waya, shi ne suka ce mayya ce"

Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?"

Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance"

"Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi arya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti.

Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba Waya zancen ya zagaya unguwa.
Har sha Wayan dare case bai are ba, Nana ta farfaWo ta ga Ummi a Wakin su, ga duhun dare ya fara yi.

"Ummi lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya Nana, meya haWa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".

"Mayya kuma?"

"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faWi sakamakon binciken su."

Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta.
Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi.
Sajida ta haWa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.

Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken wawaf da suka yi, suka gano ta yi Sari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaSi na typhoid amma suka alaanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faWuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon arya ne kawai aka gaya musu.
Ga Barira ta farfaWo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.

Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba Waya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.

Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuWin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ara rikicewa.

Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun i dawowa gidan wai tsoro suke ji.
Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga Wakin. Hannunta rie kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"

"Wallahi Ummi, gaba Waya hankalina a tashe yake"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"

Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?"
Ayshacool
Cike da karaya, da matsanancin tausayin anwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuWin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuWinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya i wai wannan Win ma da yar ya samo su ya kawo."

Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

"Nana mene ne abin yi yanzu?"

Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"

"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roi alfarmarsa?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"

"Bari na kira Baba na ji me zai ce"

Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya Saci"

"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana Waga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case Win a gurin 'yan sanda ba?"

Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"

"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"

"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce arama pressure ta yi mata yawa."

"To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su Wauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani"

Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba"

Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba."

Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faWin "Sannu Sayyid"

"Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta Waukko ruwan leda, ta buWe masa ya tashi zaune ta fara bashi.

"Sannu Sayyid" Ummi ta faWa cikin tausayawa, kallo Waya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buWe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta.

arar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta Waga wayar tare da yin sallama.

"Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka i Wagawa?"

Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?"

"Lafiya alau, ya na ji muryar ki asa-asa, laulayi ko rashin lafiya"

Ummi ta yi yae ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa"

"Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, anwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa Waya uba Waya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta Soye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da iyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa rie su kuma shi yana yi musu rion sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?"






AREWABOOKS
"Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.."
Ayshacool
"Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta.
Na san babu lallai ta iya zaman auye, amma mu nan akwai Wakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi.
Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faWa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi hauri. Ta gama faWan ta, Ummi ta kashe wayar.

Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaSa shi take, da alamu abincin ma ba ya so.

"Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a.

"Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta arawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?"

"Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka mia masa, ai karSa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan Win. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba auye ba"

"Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau Waya Baba ya taSa bari, muka je muka kwana biyu"

Nana ta ce "Ba komai, zan zauna"

Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya dame na Nana.
Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?"

Idanunsa sun kaWa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta Waga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. LaSSansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka.

Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye.

"Ummi ki gaya wa Uwani na amince"

Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?"

"Ina ga a sayar da kayan Wakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar Waki, sai kayan sawarmu"

"Nana, kina amarya amma a ce Wakin ki babu kayan Waki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen auye ba sa raina abin surutu dai"

"Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. KuWin kayan ma rie saboda Wawainiyar abinci da kuma magani"

Ummi ta Wan yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya"

Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi"

"To shikenan, bari na fita na gani"

*

Yana zaune a cikin office Win sa, ya Wora afafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a Wauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta Wauka, sai dai ta yi shiru.

Da sauri ya sauke afafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Hello ki na ji na?"

"Eh" ta amsa a raunane.

"To ba za ki yi mini magana ba?"

"Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya Wan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi hauri, sai daga baya na Wauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?"

"Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa"
"A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na haura. Ya jikin ki?"

"Da saui, amma ni ba mahaukaciya ba ce"

Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba"

"Lokacin da muna tare ai

Please Login or Register in order to submit comment