Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaban matarka, ku ji taimakon da nake buata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba"
Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya.
Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?"
Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini bauwa ce za ta yi salla"

Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faWi me take son mu yi mata".

Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?"

Nana ta ce "Ni bauwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a asar nan ba. E"

"Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana.

Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuWi a gurina, sai dai ban san kan kuWinku na asar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faWa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko Waki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah"

Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta Wan jinjina masa kai.
Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa.
Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini"

Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya arasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haWa mu da shi"

Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka"

Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani Waki, ta Waukar mata kayanta ta shiga da su.
Tana fita daga Wakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan Waukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba aramar wahala za ta sha ba.
Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi.
Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na buatar wani abu ne?"

Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka"

"To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba"

Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daWi ka Wora wa mutane Wawainiya sama ta ka"

Ta ce "Haka ne" ta haWa wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta Wauki soso da sabulu, da brush.
Ba aramin daWin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma Wakin da suka sauke ta, ta fito koma Wakin da aka sauke ta.
Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta Waukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu.
"In sha Allah za mu haWu Sayyid, ina fatan Allah ya addara haWuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye.
Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta.
"Ko ki na buatar wani abun ne?"
Nana ta girgiza kai fuskarta Wauke da murmushi ta ce "A'a ba na buatar komai, na gode sosai da sosai"

"Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa"

Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai"
Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na bauwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam"

"Ai kar Wawainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku"

"A'a babu wata Wawainiya" ta yi maganar tana fita waje.
Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata.
Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daWi, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai.
A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma"

"Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?"

"A'a zan daina in sha Allah"

Gaba Waya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki.

Nana ta ce "Ba ki taSa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai"

Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba".
Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka"
"To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa"
"Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka Wan din ga taSa hira.

Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na Waki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina bauwarmu?"

"Tana nan sai dai ba ta da lafiya"

"Me ya same ta?"

"Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi"

Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?"

"Tana dai ta yi"

Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta durusa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki.
Ta ce "Jiki Alhamdillah"

Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaWai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaWai babu Namiji babu tsaro ko kaWan.
Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku Wawainiya, Allah ya saka da alkhairi"

Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku"

Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma Waki"

Ya ce "A'a dama zan fitan"

Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faWo mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka.
Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da Wan taSa hira da Nana.
Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba"
"Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini"
Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?"
Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wataila, kina tunanin ina na samo ciki ne?"

Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi"

Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, Wabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni asar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida"

"Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema"

Nana ta amsa da "Amin na gode sosai"

*

Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su.

"Ya ya jikin Imam?"

Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun saui sosai da sosai"

"Ba yana samun saui muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?"

Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba Waya babu wani abu na cutarwa a tare da shi"

"Shi kuma matsalar zuciyar fa?"
"Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wataila ya daWe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala Waya"

Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?"

"wawalwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da wawalwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba, yana buatar kulawa ta musamman a bangaren wawalwa"

Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya Wago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake buata na kula da shi a Wakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can"

Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar"

Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya mie tsaye ya ce "Mu je na gan shi"

Su ka mie gaba Waya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya.
Cikin sauri suka arasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci.
Sultan ya arasa gaban gadon, fuskarsa Wauke da damuwa.
Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?"

"Babu ranka ya daWe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta wawalwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu...

"Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar"
Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke.

Sultan ya Wago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya Wago hannun damansa, ya ga babu azurfa Waya sai Waya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda Waya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya Wago wa Abdou hannun Imam.
A rikice Abduou ya kama hannunsa ya duba, ya kalli Sultan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abin da nake gaya maka ko? Kai ne ka ke oarin kare yaron can, ka ke cewa a bi shi a sannu ba ka tunanin zai iya cutar da shi, to ga shi nan ai ga irinta nan, tabbas ya san inda zoben nan yake, dole a matsa shi a fito da shi. Dalilin da ya sanya su ka sace shi kenan ma, su ka bar asar nan da shi, su ka kai Nigeria. Zoben suke so su sace"
Sultan ya dafe kansa, ya rasa abin da yake yi masa daWi.
"Sultan wannan ma wani sabon sirri ne, da yake buatar duk tsanani a rufa shi, a ci gaba da addu'a, amma dole a nemo zoben nan, idan ba haka ba zai fita daga sahun Imams"
Sultan ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya yana kallon yadda yake bacci a kan gadon.


Sai da Nana ta shafe kwanaki huWu a gidan Hajara, ba a samu inda za ta zauna ba. Nana ma abin daya dame ta, sai Wawaniya suke faman yi da ita, ga shi tana tsoron kar su osa da ita, dan babu mai jurewa yau da kullum sai Ubangijin da ya halicci bawa.
Ranar kwana na huWu da yamma mai gidan ya dawo, Hajara ta kira Nana.

Bayan sun sake gaisawa ya ce "Malama Nana, wallahi ba a samu gida ba, sai dai ina tafe a hanya wata shawara ta faWo mini. Akwai wata 'yar uwar Babana a can wata unguwa, itakaWai take zaune a gidanta, kuma akwai Wakuna a gida, kuma ba mazauniya ba ce, tana fita sana'iinta. Sai dai fa mace mafaWaciya, tana da yawan faWa, ba wuya ta hasala. Ban sani ba ko za ki iya zama da ita?"

Cikin farin ciki Nana ta ce "Zan iya zama da ita, in dai ta amince"

"A'a dai ki yi tunani, mafaWaciya ce sosai, idan kin amince zan tafi na je na same ta a daren nan, na yi mata bayani"

Nana ta ce "Wallahi kar ka damu, zan iya zama da ita"

Ya ce "To Allah ya sa, zan ne yi mata magana, idan ya so ko kuWin hayar ne ita sai a bata" Nana ta yi ta masa godiya tana murna.
Har Nana ta yi bacci bai dawo ba, sai washegari da safe, bayan ta karya, Hajara ta cewa Nana ta shirya, za su tafi can gidan matar.
Nana ta yi wanka ta shirya, suka fita suka hau abin hawa.
Hajara ta ce "Nana kamar kar ki tafi, kwana biyun nan har na saba da ke"

Nana ta yi murmushi ta ce "Nima haka, sai dai har Abada ba zan taSa daina yi muku godiya da fatan Alkhairi, ba dan ba aramin jihadi ku ka yi ba, ne ceton rayuwata"

"Ba komai, mu ma bamu san ta inda Allah zai taimake mu ba".

Sun yi tafiya mai Wan nisa, kafin su je unguwar da matar take.
Mijin Hajara ya sallami mai abin hawan, ya Wauki kayan Nana su ka shiga layin gidan.

A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake Wauri tana ta lissafin kuWi. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba.
Suka shiga Waya daga cikin Wakunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye.
Cikin girmamawa Nana ta gaida matar.

Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?"

Ya ce "Eh Nene"

"To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na Waukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaWai abina.
Sannan zan fara zama da ita na wata Waya, idan ba ta da ma      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  tsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuWinta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba".

Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda".

Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buWe Waya daga cikin Wakunan ta zaSa"

Mijin Hajara ya ce "akunan a rufe, ai na san sun sha ura yanzu, ki yi hauri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga Waya ki ba ta. Kin ga Wakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa Waki Waya, mai Wauke da labulaye da carfet.
Nana ta din ga godiya, ta ce "Saura kuWin hayar, nawa ne zan biya?"

"Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai"

Nana ta ce "Ai da kuWi a gurina"

Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu"

Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo.
Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaSa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki"

Nene ta ce "A'a ke da ki ke bauwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba.
Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki"
Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake.

"Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro asar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi hauri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai"

Nana ta ce "Haka ne. Mijina Wan asar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan"

"Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen asar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba.


Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa.
Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya Wago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa.
"Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faWa musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?"
Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faWa za su yarda da ni?"

"Iya abin da ka sani Win zaka faWa"

"A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani Win ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba"
"A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da Soye wasu abubuwan, ba fa za a yale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faWi abin da na sani"

Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba Waya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san Wayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu Waya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haWa mu a mota Waya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba"
Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun Satansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai Wan yanyasa a Soye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ara neman afuwarka a kan abin da ya faru"

"Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei"

"Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su"

"Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa.

*

Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi.
Ta buWe motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?"

Ya lumshe idanunsa, jin yadda amshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki Waya. Ya ce "Wa zan jira ban da anwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da bao, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki"

Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai bao, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani bai zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar.

Ya yi dariya ya ce "Laluba ki Wauki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na"

Ya ce "Ok" ya fara tua motar a hankali. Yana tui yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take arawa a idanunsa kullum. Kullum ara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "anwata"

"Na'am Yaya Abba"

"Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna"

Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya"

"Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa"

Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa"

Yayi dariya ya ce "Aya kawai?"

"Eh ita kawai"

"To an gama ranki ya daWe" ta fita daga motar tana Waga masa hannu"

Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom.
Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai.

"Jamila har na fitar da ran za ki zo ai"

"Ba na jin daWi ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa"

"Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu"

Jamila ta ce "Tom"
Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta Wan rio hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin i yarda ki shiga layi"

Jamila ta Wan Sata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"

Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda Waukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"
Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda Waukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba Waya gaskiya. Ba gara na bi maza ba"

Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita.

Umman Fadila ce take kallonta a

Please Login or Register in order to submit comment