Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi ya matso kusa da ita ya kura mata ido yace I'm sorry to hurt your innocence tailor but you accepted me despite knowing that I love someone else ....=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
[9/25, 1:27 AM]Maimunatu Telar Mata=ؙ

By

Azee cool=إ











37








......kunnenta ya ja da qarfi tayi firgigit ta tashi Dan bata San sadda bacci yayi gaba da ita ba ganinsa yana mata dariyar mugunta yasa ta hade rai tace dazafi fah Kuma kake min dariya
Ya tsagaita dariyan yace see your ugly morning face kawai kina bacci akan sallaya local girl kawai..
Duk da taji haushin me yace amma ta daure tace ina kwana yayi Murmushi yace ki tashi ki shirya ankawo break fast daga gidan Hajiya and I want to talk to you baijira mizata ce ba ya fita

Ta sauke ajiyar zuciya tace zan bika duk yadda kake so har insamu soyayya daga wajen ka koda kadan ne ta tashi ta nade sallayar ta cire doguwar Riga da hijabin datayi sallah dashi ta nadesu ta ajiye

Cikin akwatin kayanta na gida ta saka wata doguwar riga coffee colour ta yafa gyalensa ta fesa turare ta fito falon
Yana kan dining yana danna waya ta karaso taja kujera ta zauna tace good morning bhayya bai kalleta ba yace the morning was not good for me bata qara cewa komai ba dukkansu sukayi shiru bayan kamar minti biyar ya ajiye wayar ya dago ya kalleta suka hada ido ta sauke nata yace my tailor nasan jiya kin kalle ni cikin wani hali but I want you to zip your mouth about it nasan you are very close with baby but duk ranar dakika kuskura kika gaya mata you won't like what I'll do to you yayi shiru kafin ya cigaba kafin a daura auranmu na tambayeki shin zaki iya zama dani knowing inason wata sannan bazaki samu soyayyata ba kika ce kin amince naga kin juyar da hoton simran a dakina tun yanzu kin fara jealous toh ki Sani ba ruwanki da hotonta zansa a falona da dakina so it won't disturb you duk ranar da kikayi gigin cireshi a Inda nasa you will face my wrath and you won't like it
Gidan dakike gani ba nawa bane Hajiya babba ta bamu mu zauna for the mean time according to her saikin yi kaman wata daya ko biyu kafin natafi dake Abuja so ki kula mata da gida and don't worry nima ina Gina nawa gidan so kafin a karasa ginin we'll stay here
Nayi deciding zan dinga baki allowance duk wata amma sai nayi tunanin you may need the money kafin wata ya qare so yanzu namai dashi duk sati zan dinga baki fifty thousand naira and idan ya kasa miki just kiyimin text zan turo miki tunda kwadayi yasaki aurena bazan hanaki jin dadi ba you will get everything you want but not love
Nayiwa dad alkawarin bazan sake kiba saidai ke da kanki kika nemi haka so welcome to being Mrs Mubeen
Tunda ya ce min kwadayi ya sa ni auranshi nakejin quna araina gaba daya na rasa nitsuwata amma na dake sai daya karasa maganarsa nace nagode Allah ya qara arziki na tashi nawuce daki inaji yana bazaki ci abincin ba na share shi
Ina shiga daki na fashe da Kuka wato ma tunaninsa kudinshi nake so nacewa kaina anya mubeen zai soni kuwa anya banyi wautan auranshi ba wani zuciya yace haba Maimunatu tun yanzu zaki sare tun day one dinku ai yanzu yakamata ki kara shiri Dan yaqi da soyayyar simran daya rufe mai ido haka tayi ta tunani karshe Ganin hakan bazai fishsheta ba yasa ta dauko wayar ta ta kira baba bai dauka ba ta kira Khalil ma bai dauka ba sai ta kira baby
Hello amarya ya kike fatan bhayya ya gasa ki da kyau karya barki danya
Baki da lafiya baby wani gashi Kuma tayi dariya angel ba haka ake cewa ba a first night wai da safe ango ya gasa amarya
Ke kikasan wannan niban Sani ba naga missed call naki ina baccine
Iye amaryar babban yaya sai a hankali nazo kawo miki abinci ma ango ya hana ni shigo wa kar naga kina tafiya a karkace kai angel Neman magana gareki nidai ba abinda ya faru kwantar da hankalin ki tace really angel dina nothing happened last night nace nothing nothing
Tayi dariya tace to saidai Mun hadu Dan ina hanya zan kawo abincin rana so we'll talk nace ok sai kinzo na kashe wayar

Tana isa gida ta tadda sury,ihsan,khalid,da haidar a falo suna hira ta qaraso tace lallai abin yayi karfi matar kebin mijin
Haidar yace autis kin fara hausan kin nanko bawani Hausa gaskiyar Dana gani na fada ta haye sama sury ta ja tsaki dama saboda khalid ne bata tanka mata ba Dan tasan sarai baby da ita take
Haidar yace ban gane ba surayya kuna fada da baby ne naga ko gaisawa bakuyi ba
Sury tace ba wani fada kasan qanwarta ka sai ahankali raini gareta ihsan tace da munafirci ba khalid ya daka mata tsawa kee bana son rashin kunya
Sorry yaya haushi ta bani


Dakin hajcy ta shiga ta samu tana karatun Qur'ani tace hajcy love kinga bhayya ya hanani Ganin angel dina tayi Murmushi bayan takai aya tace barsu su huta mana autana ta shagwabe fiska hajcy toh nayi missing dinta nefa Hajcy tace daga jiya kedai kice gulma zakiyi
Haba hajcy ni bana gulma fah tace inkince haka ba tasa dariya barin je gidan dad mom ta ce inxo tace ba komai ki gaidata

Data zo fita ma suna wurin ko kulasu batayi ba ta fita

Sai da naji fitar mota a gidan lokacin karfe sha daya kafin na fita dining din na samu abincin ma kadan yaci na Debi wadda xai isheni naci kafin na sa katon hijabina har qasa na kaiwa maigadi sauran bayan na juye a wani flask din daban maigadin wani tsohone atleast zaikai 55 years har kasa nagaida shi nace mai yayi hakuri ban kawo mai abin kari da wuri ba yace ba komai dama harda kudin abinci ake bashi nace duk da haka yayi hakuri yaji dadin yadda na girmama shi yamin adduan samun zaman lafiya tsakanina da mijina

Dana koma daki na sake kiran babana wannan karan ya dauka nayi mishi godiyar kayan daya min yace nayi hakuri yaso na samu fiye da haka amma bikin yazo a lokacin da ya kure sosai yamin nasiha wadda saida nayi Kuka daga baya mukayi sallama na kashe nakira umma da Anty suma duk na musu godiya

Karfe biyu da Rabi baby ta kawo abincin rana har lokacin mubeen baya gidan ..sai dana kaiwa baba maigadi kafin na dawo muka fara hira duk yawanci na biki ne daga karshe ta fara bani tips yadda zan jawo ra'ayin mubeen gareni duk da ba yau muka fara irin hiran ba amma sai naji na yau yafi shigana sai karfe hudu ta tafi tace suna da picnic a maisanda green garden karfe hudu da Rabi

Tun a hanyar komawa gida Sagir yakirata kan yana kofar gidansu tace gatanan zuwa tana gama wayar kamal ya kirata in law kina ina ne haka tace ina hanyar koma wa gida ya akai yace zan koma Abuja gobe shine nakeso inzai yiwu muyi magana da mutuniyar tawa tace gaskiya bansan yazata kasance ba Dan muna da picnic da aka hada na family yanzu amma why not ka kirata kaji ko she's free da dare Dan yanzu ta dawo gidan hajcy itama yace ok barin gwada kiranta

Tausayinsa takeji wai sury yakeso wadda tasan da dadewa sury Khalid takeso Kuma inhar khalid ya amince da haka bashida chance a wajenta poor kamal !!!

Tana isa ta tadda gwaninta yana jiranta akan mashin din abokinsa ta qarasa wajensa fiskarta dauke da Murmushi tace love Kuma kana tsaye a waje yace na tambaya akace Hajiya ta fita saisa ban shiga cikiba tace to yanzu tafiya zakayi bazaku sallama da hajcy naba yayi dariya love kenan da badan rashin lafiya kawuna ba da sati zanyi but I have to go tace barin shiga na canza kaya sai kara kani wurin picnic din nan nayi ko minti biyar ne kafin sai na raka ka park ko yakace
Kai princess mu tafi haka mana you look beautiful haka saidai in kinaso wani ya kwacemin ke acan tayi dariya haba ai ba wadda ya isa ni taka ce har abada Insha Allah
Ta hau mashin din dama tasaka wani leggings baqi ne da T-shirt jaa tasa after dress akai

Tunda aka hadu a wurin yake jiran zuwanta kamar yadda haidar yace mai ya apologising kan marinta da yayi a gaban kowa haka zaisa ta rage tsanarshi da takeyi
To him taron nan without her is meaningless duk da gashi 'yan uwa an hadu yara da manya anata hira da barkwanci

Tunda ya sauketa sury ta hangosu ta taba ihsan sukayi Murmushi
Gaskiya love kije ke kadai bazan biki ba Dan Allah love muje tare inhar naje ni daya bazasu bari na tashi a wurin nan ba sai angama amma inmukaje tare Zasu karbi uzurina please dear yace ok muje tare suka jero suna hira har suka iso gurin a zaune suke akan wani carpet me kyau suna zagaye sunkai su ishirin tsakiyarsu kuwa cike yake da snacks da fruits
Saitin haidar taje ta rufe mai ido dayake ya basu bayane baiga zuwansu ba
Kai tsaye yace autis tayi dariya ya akayi ka gane ni yace seriously tun kina 2years nake rike hannunki I know the softness of your hand ta zauna gefenshi tace love zauna mana tadan matsa caraf sury tace baby waye wannan Kuma Dan Allah ance family only kin kawo mana Dan going (dan achaba) ai sai ya matsa can gefe inma jiranki zaiyi
Sagir daya kulu amma ya daure yace kuyi hakuri bansani bane ihsan tace kodai ka manta da matsayimka ba Dan ba kaga any body anan daya ke irin class naka ba ko kaga mai taxi balle Kace daya kuke
Aminah ........baby ta daka mata tsawa tace haba Zainab so kike mu zauna da bare bayan ance family only what did you mean
Khalid da tsawar baby yasa shi katse wayar dayakeyi ya qaraso wurin dan yaga meke faruwa

Sagir yace kuyi hakuri barin tafi zai juya baby ta rike hannunshi daya tace jirani mu tafi tare amma kafin nan ta kalli ihsan tace barin sanar dake wani abu walau Dan achaba,walau mai taxi, ki kirashi komai shi nakeso dama gaisuwa zaiyi mu wuce amma naga non of you deserve it ta miqe suka hada ido hudu da khalid wadda duk yanayinsa ya canza Ganin yadda ta riqe hannun Sagir gashi har tana jaddada soyayyar sa garesu tace congratulations your plan is successful ta juya suka tafi
Wurin ya kaure da cecekuce suna isa wurin da suka faka mashin din yace kinga irinta nan ko saisa nace bazan jeba batace mai komai ba Dan ranta yakai qololuwar baci zata hau mashin din taji an riqeta ta juya taga haidar ne yace Sagir ka tafi abinka zankaita ba musu ya kada mashin dinsa yayi gaba Dan dama zuciyarshi na quna Dan sun walaqantashi wai Dan achaba !!!

Shi dakanshi ya kaita mota ya bude ta shiga yazagayo ya shiga ya fara tuqi har suka isa gida bawadda yace kala
Saida suka isa falo yace I'm sorry baby about what happened earlier tace ba laifinka bane duk plan din khalid ne dashida kanwarsa da budurwarsa suka humiliating dina bakomai I know what to do ta haura sama yasan koyamata magana yanzu bazata saurareshi ba cause she's still upset amma bari zuwa dare ya mata maganan kan balaifin khalid bane she's just misunderstanding him.....

Sai biyar da rabi mubeen ya dawo nikan ina daki naji karan motanshi na yi ajiyar zuciya dan nasa wata riga marar hannu jaa da wani bum short na denim jeans ash saina daura kaina da plain dankwali jaa ni kaina kunyar kaina nake dakyar na gathering courage na fita yana zaune kan dining yana cin abinci na karaso dining din nace sannu da dawowa ya daga kai ya kalleni sama da kasa irin kallon rainin nan yace tailor what's this are you trying to seduce me ya kwashe da dariya wonders shall never ends gaskiya you look pathetic kinganki kuwa so horrible it doesn't fit you ko kadan
Hawaye ne suka gangaro kumatuna ina jin zuciyata kamar zata fashe na koma daki na zauna ina Kuka inajin dariyarshi da kalamansa na yawo akaina .......=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
[9/25, 6:42 PM] Maimunatu Telar Mata=ؙ

By

Azee cool=إ











38












.......nasha kuka har na gode Allah daga baya na tashi nashiga bayi nayi wanka nasaka doguwar rigar atamfa na daura dan kwali na tsaya agaban mirror ina kallon kaina ni nasan cewa bawani kyau nake dashi amma alhamdulillahi ina da kyan jiki lokacin ina da ina zuwa tailoring school ogan mu na cewa ina kama da Ghanian actress din nan Jacky appieh har hoton ta ya nuna min bawai Isma'il kadai bane saurayina inada manema dayawa kawai dai da Isma'il kadai na taba soyayya
Na goge hawayen dake gangaro mani nace Insha Allahu zan nuna maka badan kudinka na aureka ba Kuma tunda Kace I look pathetic bazan qara saka kaya Dan na burgeka ba

Yana gama cin abinci ya shige daki yana kwance amma shi tunaninsa yadda zaiyi ya jure rayuwa da wannan baqar yarinyar romantic moments nashi da simran ya tuno ya kawar da duk wani tunani sai nata

Tunda haidar ya tafi da baby shima ya dawo Dan yasan babu amfanin zaman sa a wurin picnic din ya samu haidar adaki yana duba wani magazine ya dafa shi yace Dan uwana ya akayi ne ka bata hakuri kuwa ta daina Ganin leifina ya dube shi khalid I try to talk to her amma she won't listen mubarta zuwa gobe by then ta huce
Haidar baka Ganin yayi nisa I really want to be close to her bana so ta ciga ba da tsanatah it hurts
Ya ce saidai mu gayawa hajcy no gaskiya bana so tasani
Ok apart from hajcy saidai mubeen Kuma he's newly married bazamu disturbing nashi ba
Ok na tuna junior zamu kira kasan shima they are close
Inaga haka za ayi
Dakinta haidar ya nufa yasamu tana hada kayanta a jaka yace auta inazakije kike hada kaya ko kallonshi bata yi ba tace Hutu zanje
Haba baby nah bayan gani na dawo wani Hutu Kuma ai muna nan dake a bauchi
Bata kulashiba yace by the way zokiga wani surprise ta ce I'm not in the mood yahada hannayenshi biyu yace please little sis kizo kigani I promise you will like it tace ok muje
Falon sama suka shiga Ganin Khalid yasata tsayawa tace yaya haidar indan wannan ka kirani barin koma yace a'a baby mu karasa dai
Yana riqe da laptop a cinyar shi yana magana yasa earpiece a kunne suna karasowa taji yace little bro gata nan ya cire earpiece din ya mika mata taqi karba haidar ya karba ya ce sister kisa Imran junior ne ya saka laptop din a cinyarsa ya juyo mata yadda zata gani ta karba earpiece din tasa
Sallama yayi ta amsa tace junior ya kake ya Mumbai
Yace didi I'm fine here saidai ke kamar you are disturbed
Tace no bro I'm normal nan suka fara tadi harda dariya Dan qanin nata ya kawar mata da baqin ciki
Yace naga video na bikin bhayya harda kikayi rawa ko ina hardar taki taje kike rawa
Tayi dariya tace ayi hakuri Dr. Imran naik baza akuma ba yace seriously you look adorable there I missed you didi tace I missed you more junior fatan dai kana karatu yace sosai ma
Sunkai 20minutes suna hira kafin ta ending video call din tace wa haidar na gode yaya tace I don't like this formality call me haidarabad like you used tace bazan Kuma ba ta fita
Haidar yayi ajiyan zuciya yace likita na miyasa baka gaya masa ba yace nayi tunanin sanar dashi will make her more mad at me
Kaika Sani Dan na gaya maka Mafita kaki bi ni nasan gobe zamu shirya but kaifa I'm worried idan tacigaba da tsanarka bazaka samu chance a wurinta ba
Yace don't worry bro I'll handle her ...

Sai bayan Maghreb hajcy ta dawo lokacin baby ta gama hada
Kayanta taje ta mata sannu da dawowa tace hajcy na zan tafi hutu Jama'are gobe daga nan zan wuce kano
Hajiya ta kalleta tace baby are you alright bawai Dan surayya ta dawo gidan nan zaki tafi ba
Ta rungume hajcy tace no sweet mom kawai zanje ne kinsan rabona dacan tin azumi

Hajcy tayi dariya nasan wannan bashine dalili ba you are just covering up amma bakomai Allah ya kaimu gobe din tace that's my hajcy!!!

Baby ta kirani take sanar dani tafiyan ta nima nayi mamaki Dan baby bata son nisa da hajcynta Dana tambayeta hutun gaggawa haka tace angel zamu yi chatting idan na isa zan sanar dake komai muka taba hira ta tambayeni mubeen nace baya gida
Bayan munyi sallama ta kira sagir ta bashi hakuri kan rashin mutuncin da su sury suka masa abin ka da masoya tuni suka shirya ...

Washe gari da sassafe baby ta wuce Jama'are Hajiya ce ta raka ta park bayan ta dawo ne haidar ke tambayan Inda taje da sassafe haka tace autana na raka park bata gaya maka zata tafi Jama'are ba cike da mamaki yace ta gaya min na dauka ba da wuri zata je ba hajcy tace 'yar tawa nasan fishi take akan wani abu amma kafin ta dawo nasan she'll be over it
Yace hakane takwarar taki Hajiya sai a hankali kin sakalta tah daya wa Hajiya tace to ba dole ba tunda ita daya gareni mace yayi dariya intayi aure naga yadda zakiyi da rashinta ai hajcy tace ai mijin mu biyu zai aura suka sa dariya gaba daya

Yana shiga daki yadau wayar shi da niyyar kiranta yaga message nata kamar haka

"Dear lovely bro sorry bamuyi sallama ba na tafi i was just excited ne naga na bar gidan cause bazan iya zama gida daya da Sury da khalid ba please take care of hajcy for me kafin na dawo kafin nan stay blessed yayanah @missing you already"

Yayi ajiyar zuciya kai baby akwaita da saurin fishi yanzu har abin jiya ne yakai ta dauki decision din nan lallai ma ....



Nikan a nawa bangaren tun daga ranar da mubeen ya gwaleni na fara wasan buya dashi bana bari mu hadu yanzu saude ke kawo mana abinci inta kawo nakan deba nawa Dana mai gadi na bar masa nasa a dining idan naji ya fita na zo na tattare na gyara wurin
Duk bayan kwana biyu sai na kira Hajiya na mata godiyar hidima da take damu iyayena kan kullum sai Munyi waya

Yau ta kama Friday daya zamo kwanana shida a gidan mubeen bayan saude ta kawo mana breakfast nake cemata Dan Allah tace wa Hajiya dawainiyar yayi yawa Inda hali ta bari in fara girki saude tace dama daga gobe tace zata bari ki fara amma tunda kinyi magana zan gaya mata nace na gode

Ina cin abinci a daki Dan dama kullum a nan nake ci naji an turo kofa na daga ido na na kalleshi kafin na sunkuyadda kai nacigaba da cin abincina ya karaso har inda nake zaune yace My tailor zan tafi Abuja yau sai next Friday kafin na dawo ya ajiye min kudi yace if you need anything else kimin text ko kallonshi banyi ba ya tashi ya fita
Yana fita na fashe da Kuka wato shi tunaninsa kudi kenan na dau kudin na ajiye a cikin drawer nace kozan mutu da babu bazanyi amfani da kudin ka ba

Ranar asabar kannena suka zo su biyar muka wuni har yamma lis kafin Alfarouq yazo ya tafi dasu wai baba ya hana su kwana banso ba amma haka suka tafi suka barni ni kadai a gidan sai maigadi

Kullum muna chatting da baby amma ban taba sanar da ita halin da nake ciki ba kullum ina nuna mata akwai improvement tsakanin mu da mubeen amma Sam ba haka bane Dan tunda ya tafi bai taba kirana ba

Ganin bana komai a gidan daga kallo sai chatting yasa na kira Tasleemah daya ke tazo sau daya gidana nace mata Dan Allah tasanar da costumers dina kan ina dinki har yanzu tace min insha Allah
Wadda nake da contact dinsu haka nayita kira ina musu kwatancen gidana idan Zasu kawo dinki dayake tarayya ta da baby yasa na kara samun customers daya wa
Na dau aniyar da zaman banza gara na ci gaba da sana'ata tunda keke na nanan


Haka rayuwa ta cigaba duk sadda mubeen ya zo weekend zai bani kudi nikuwa in ajiye a drawer na ban taba gigin yimai tayin abinci ba na lura ma bai damu ba Dan ko kitchen din baya leqawa

Baby ta dawo daga Hutu kamar yadda ta ke so bata tarar da khalid ba dama tun tafiyar ta da kwana biyu ya koma Abuja sury ma ta bishi Dan dama shine sanadin zamanta a gidan

Bata cika zuwa min ba kamar yadda ta saba lokacin ina gidan mu saboda school da Kuma Hajiya da take taka mata birki kan tabarni ina sakewa ni daya

Randa ta sameni ina dinki tayi mamaki dama cikin daya dakin da ke kusa da nawa nakeyi nace mata ai saboda zaman kadaici idan mubeen baya nan yasa nake yi tace gaskiya zata mawa hajcy magana domin inkoma Abuja tare da shi nace mata a'a nafison zaman bauchi tace ba wani ni bana son kina wahala Kuma ma you need to be with him always to win his love.....=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
Maimunatu Telar Mata=ؙ


By

Azee cool=إ













39













Jollof din shinkafar manja na mana da yaji bushashshan kifi,da tarugu, bayan Mun ci abinci baby tace angel watan ki daya da sati daya a gidan nan baki taba fita ba ko gaisuwan bayan biki bakiyi ba meyasa? Na fara kame kame dan bansan me zance ba nikaina ina so inje inga iyayena na Kuma gaida iyayen mijina amma saboda na daina shiga harkan mubeen yasa

Please Login or Register in order to submit comment