Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kije kiyi cash nashi Dan dadin zai miki yawa and shukriya ya Allah da kikace walima zakiyi Dan bansan Inda zan boye kiba kar kijamin raini kalanma kishafawa mutane baqi mtsww nayi Murmushi nace Allah sarki ashedai baqi tsada yayi har ba a iya sayanshi fari kuwa gashi a shago ko ina i see da baqi nada daraja da bature ya dade da zama baqi nace darajarshi ce tasa ba za a iya samunshiba yace oh really nace yes yai dariya yace do you know tailor kena tuna nayi project din nan har naci na zaro ido yace maida wuqar I'm not saying i care kawai dai bayan naje can angayamana irin tsarin ginin da akeso akan kowa yayi modelling yakawo sun bamu a week nayi nayi in yi anything classic sainaga kamar bazai yi kyauba so ranar hajcy ta kirani wai nakiraki kuwa tun danaje nace mata wa dan harga Allah namanta ki Saida ta min fada tace maza na kiraki. So after. the call I think of you and how local you are so after that this idea come to me actually nayi modelling din very simple very natural and daga karshe mine was accepted. So nayi signing dasu na fara aiki so kinga how your thinking of your lowly life make me earns alot yayi shiru kafin yace in four days time we'll be married and it's a lifetime journey let me ask you zaki iya rayuwa dani bayan kinsan akwai wadda nakeso a zuciyata ya tsuramin ido nayi shiru kafin nace zan iya yace good for you ya ajiyemin check din a cinyata na dauka tare da shirin fita ya kamo hannuna nadawo nazauna jikina na karkarwa Dan yadda nakejin wani sanyi na ratsani har lokacin bai sake hannuna ba yace haba My tailor tafiya ba sallama murya na rawa nace to natafi dariya yayi yace haka ake sallama nace to ya zanyi yace ko dayake you are local bakisan komai ba a zuciyata nace adakenan ...ya sake min Hannu yace till Saturday My tailor bance komai ba na fita jikina asanyaye.....

Ina shiga daki na rungume hannuna tare da kissing dinshi ina tuna lallausan hannunshi daya rikeni .....sai bayan Maghreb nakaiwa baba check din naira dubu dari biyar aka rubuta baba yayita mita wai yayi yawa ....nima dai hakan nagani danasan haka ya rubuta ma danace ya rage .
Na kira baby ina mata mayar mata nace tace mai yayi yawa ya zo ya rage tace lallai angel kina raina mijinki aini a wurinama yayi kadan nace haba angel to nidai ki turomin nambarsa nagaya masa da kaina tace kiduba wayarki duk numban dakika ga an saving da baqon suna nashi ne ta kashe wayar. Na fara duba contacts dina har nakai "My Only" nace yaushe kenan baby tasamin nambarshi ban saniba lallai agaida baby .
Nafi minti goma ina niyyar kira in fasa daga baya na rubuta mai text kamar haka " Nagode da gudumawa amma yayi yawa Inda hali kazo ka rage" kafin na. tura ma ina ta Inda Inda kafin na tura minti biyu aka turo da reply "Do manage it My tailor" yafi sau hamsin ina karantawa ba abin daya tsayamin sai Kalmar MY duk da tailor ce a gaban amma naji dadin hakan....=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
[9/13, 2:11 PM]Maimunatu Telar Mata=ؙ

By

Azee cool=إ











Kashe gari talata gidan mu ya fara cika 'yan uwanmu na misau suka fara isowa wasu ko sai laraba su karaso dakin su khalil ya koma na baki sukuma suka koma shagonah suna kwana nikam zama ya gagareni saboda ranar ma sai yamma na dawo gida nida tasleemah da umaimah muka fita rabon katin walima dayake ni ba wasu qawayene dani ba yawancinsu ma 'yan islamiyyar mu ne sai wadda mukayi secondary da koyon dinki tare wasu ma sunyi aure ...

Nidai tunani na banga kayan daki kona kitchen ba hankalina ya Dan tashi saboda bana so ace gidansu mubeen zasu min komai amma dai na shanye damuwata dan nasan baba yana qoqari kuma bazai bari auren 'yarsa ta fari bai mata komai ba .......

A bangaren su mubeen kuwa Hajiyarsu ta tafi Hajji saisa daya dawo bai samu wata matsala ba shikan bai gaya wa abokanshi batun aurensa ba iyakaci 'yan uwa da suka sani shikenan sai abokinshi kuma PA nashi kamal saisa hankalinshi kwance ...

Gidan Hajcy kan ya cika dan yaranta biyu sun dawo sai Ahmad dashima ana jiran zuwansu gobe da iyalenshi ...

Tana sauko wa sai faman kiran haidar take haidarbad ,haidarbad , wai ina kake ne ta qaraso tana faman huci Anty Nusaiba matar yaya Yusuf tace haba baby wannan kira ko yaron hannu iyakaci haba Anty tin dazu nace mai zai rakani fah Kuma yanzu na duba dakinshi baya nan kema dai kinsan dole ya huta kwata kwata ba jiya yadawo ba to ni ina ruwa na ni nace kar yadawo da wurine tun yaushe hajcy tace Zasu dawo suka qi sai Kace garin ubansu ta fada tana zama kan kujera Anty nusaiba tace to ba ga Khalid ba saiya kaiki sai a sannan ta lura da akwai mutum a wurin tasan dai Haidar yace mata tare suka dawo amma bata ganshiba yana zaune kan kujera sanye yake da wata farar t-shirt da baqar jeans yana danna iPad dinshi da alama ma baisan me suke cewa ba tsaki tayi tace Dan girman kai kawai a zuciyarta yayin da tace Anty barin jira shi Tana faman kiran wayarshi amma bai dauka ba Anty Nusy tace kekika Sani ai taci gaba dashan fruit salad dake gaban ta
kaman minti biyar saiga haidar ya shigo yana Ganin baby a wurin ya riqe kunnenshi biyu yana sorry autan hajcy friend dina na raka wallahi ta wani kauda kai ya karaso daidai fiskanta ya lakuci hancinta yace I said sorry auta ta ja hancinshi da karfi tace to muje ya ce kai auta abinki harda mugunta inkika ciremin hanci fah tayi dariya saika sa na roba shima dariyar yayi yace saboda in rasa mata ko tace kaika sani yace oh hakama ko karki damu na angonki za'asa min ai tace yafi karfinka dariya kawai yayi tare da duban Inda Khalid ke zaune yace likita zo ka raka mu anguwa harara baby ta banka mai tace Haidarbad ni bana son gayya ehe yace ni da likitana zan fita khalid cikin wani sassanyar murya yace ku tafi kawai haidar yace dan kace ne amma dan wannan inna tsiwa din ne bazan yarda ba ya juya suka fita tana ta faman ma
sifa yace mata inna tsiwa shiko Khalid Murmushi yayi me cike da ma'anoni wanda yabarwa kansa sani anty nusy tace nikam khalid kodai akwai wata a kasa ne kaida baby yayi murmushin shi mai tsada yace Ba komai fah. tace intayi tsami maji ai ..


Yau laraba 'yan Maiduguri suka zo tare da gudummawarsu gaskiya sun nuna min gata akwati daya na kayan biki sukamin atamfa biyar shadda dinkakkiya daya,material biyu,sai takalma uku da gyele biyu da hijab biyu da jaka biyu, ga Kuma kayan kitchen irinsu microwave, blender, mixer, toaster, da fridge karami, da Hot plate banda coolers masu tsada da plates da sukayi ga abubuwan biki dasukazo dashi harda soyayyen nama inaji ma rago guda aka soya gashi dama baba ma ya daure rago biyu daza a yanka Saida nayi hawaye Dan murna dakuma tunowa danayi da mahaifiyata Nada rai da gatan yafi haka kayan gaba daya aka maida gidan Anty Fatima ...
Washe gari Alhamis Aka min lallae wata 'yar kawun nane da dama aikinta ne ta tsara minshi yayi kyau aka min kitso qanana Dan na zaunu kan gashi dama kaina irin mai cika din nan ne saidai yasha gyara sosai dayake dama tun tuni baby ta dage damin stretching dinshi duk bayan sati biyu yasashi ya yi tsayi ya rage cunkus dinshi danda bana iya kamashi waje daya tsabar cika .....



Ban gane har yanzu zancen auren na nan ba miki ke nufi Ramlah Hajiya khadija kenan data dawo daga hajji jiya da dare ta tadda gida ya cika da 'yan biki wallahi Hajiya nima haka nagani dad dakanshi ya kirani yake sanar Dani nima jiya naxo lallai da sakel bazai fa yiyu ba Hajiya kinsan ma abin haushi ne Sury kecemin wai harda baby akaje hada lefe Kuma wai tadinga saka hoton yarinyar Dana mubeen din a group tana zagin wadda basa son auren. Hajiya tace lallai ma yarinyar nan kira min sury kice ta kira banzar nan tace to tare da kiran layin sury bugu daya ta dauka hello sury wai inji Hajiya ki kira baby kuzo tare ina falonta tace to ...

Dayake taga baby a side din mom dazu data je yasata yi falon mom din tana zuwa taga hasken idaniyarta nagaida mom har qasa ta tsugunna ya Khalid ina wuni yace lafiya shikenan tinda ka dawo sai yau ake ganinku naje har gidan haj.babba jiya akace ka fita ko kallonta baiyi ba yace hakane. Ehm mom ina baby dazu naganta anan tace taje kitchen dauko abinci wai yunwa takeji kafinta rufe bakinta saiga baby tashigo da plate a hannunta indomie ne sai boil egg biyu tace kai Hajiya hidimar biki ba dadi kinga tun safe ba abinda naci sai ruwan tea tace kema za a miki ai tana ajiyewa center table din sury tace Hajiya na nemanki yanzu tana wani hararanta Dan wata doguwar riga ce sky blue da black stones agaban rigar da wajen hannun gyelen shi ta saqala a kafada ga gashinta data kama in a ponytail style yana taba tsakiyar bayanta tayi masifar kyau duk da daka ganta kasan agajiye take ita sury ba komai ne yasata tsani 'yar uwar tata ba fa ce dan ta fita kyau Dan kamar mubeen gareta .....baby tace to ina zuwa barin ci abinci tukunna ee lallai saima kinci abinci kenan Hajiya jiranki zatayi ta chuno baki mom indomin fa sanyi zaiyi mpm datasan masifar hajiyar tace jeki dear zankira asa miki a cooler kafin ki dawo ta tashi tana zumbura baki tabi bayan sury ......

Falon hajiya tashiga bayan ta yafa gyelen a kanta tasameta kame akan kujera daka ganta kasan tana tare da bacin rai Ramlah nacin ferfesu sury na zaune tana danna waya a hankali ta shiga Dan nesa dasu ta tsugunna tace gani Hajiya Ramlah tace lallai baby wuyanki yayi kwari wato ma bamu isheki gaisuwa bako bata ce komai ba Dan tasa aranta zata ja da duk wanda baya son auran nan koda kuwa hajiyarta ce ...
Hajiya tace a wani dalili kika je hado kayan lefe kanta a qasa tace a dalilin auren yaya na ne da qawata Hajiya ta fusata ta tashi tace kee banza ina .magana kinayi Dan rashin tarbiya ko baby tayi shiru taci gaba ke gaki uwar iskanci ko harda bin munafukar tsohuwar taki kuje hada lefe ko ran baby ya baci Dan baza ta juri azagi hajcyn ta ba tace hajiyata ba munafuka bace kee banza kiyi a hankali wato hajiya ce munafuka ko inji sury nibance ba ehe
Ramla tace. batta sury muga iya cin fiskarta
Hajiya tace to wallahi Zainab ki kiya yeni bake ba hidima a auren nan inaso ma ki shirya gobe ki wuce yola kafin insan yadda zan warware zan can nan Dan bazan juri wata sirika wai tailor ba sury tace saima kinganta Hajiya baqa kamar gawayi idon baby tace baqar ce naga haka Allah yayita Kuma ba Inda zanje yaushe nazama 'yarki daza ki wani turani wajen 'yan uwanki ni nan hajcy ce gata na Kuma aure duk muna funci mutum sai anyi Kuma ma da ake aibanta ta saboda ita tailor ce naga halaliyarta take nema sanin darajar Neman nakai yasata dinki Dan ta taimaka wa iyayenta take dinki Kuma wallahi Maimunatu ta auri mubeen an gama inba ma rashin sanin darajar Dan Adam ba miye aibi idan mutum yakasance tailor duk kankun nan ba abinda Kuka Sani sai kashe kudi bakusan darajar samunsa ba imba rashin imani ba Zuwanki Makkah a sanina ma yakai goma balle wanda ban sani ba amma Dan Neman suna mijinki na fama da ciwon kafa kin wani tafi wai hajji kona mene oho Dan nasan ba lada. Saukan wani lafiyayyen mari taji kafinta ankara aka sake qara mata wani har Saida ta fadi qasa yawwa Khalid qara mata inji Hajiya dake tsaye dama mamakin maganganun 'yarta ta yasa ta kasa aiwatar da komai ....
Jawota yayi yasa ke qara mata wani marin idonshi yayi ja saboda yatsani yaga ana wulaqanta iyaye gashi tunda kofa da yashigo Dan gaida hajiyar yakejin kalaman baby hakan yasa zuciyarshi tafarfasa ...
Ya daga hannunsa zai kaimata Marin na hudu ya lura da jinin dake fita daga hancinta da bakinta nan jikinshi yai sanyi ya saketa tace munafiki algungumi saika kasheni ai tunda baka da imani baice komai ba yaja baya dan ya tsorata da yadda fiskanta ya kumbura tashi daya a hankali ta tashi ta fara tafiya harta kai baqin kofa ta juyo tace saidai Ku kashe ni amma duk wanda ya nuna zai tozarta hajcy nah ko angel to wallahi zanja dashi koda kuwa wayeshi ta fita .....

A jiyar zuciya yayi yayinda Ramlah tace kamin daidai Khalid gara da Allah ya kawoka da wuri Dan rainin yarinyar nan yayi yawa shidai jinta kawai yake amma har zuciyarshi yayi Dana sanin abinda ya aikata musamman a yarinyar da kullum yake dakon sonta .... =ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
[9/15, 1:07 AM]Maimunatu Telar Mata=ؙ

By

Azee cool=إ













31













Tana fita falon mom ta wuce Dan ta raya aranta cewa wayarta kawai zata dauka ta wuce wurin hajcynta taga yadda khalid ya mata da fiska a zuciyarta wani tsanar shi takeji dama abaya ma bawai tana hulda dashi bane dan girman kai gareshi to gashi yanzu ya jawa kanshi baqin jini Kuma tadau alkawari da an qare biki zata dau mataki akansa

Tashiga falon ba kowa ta qarasa kujerar data ajiye wayan ta dauka tana tafiya zata fita jiri ya kwasheta ta fadi a wurin dayayi daidai da shigowar mom Innalillahi ta furta hankalinta a tashe ta qarasa ta dagota tana faman kiran sunanta amma ina ta suma kuka tafara dan batasan yazatayi ba alokacin Diyyah ce tashigo tana kiran mom mom ganin ta rungume da baby yasata fasa ihu ta fita da gudu tana kiran dad dinta Khalid dake shirin fita daga side dinsu Hajiya yaji kukanta ya nufi side din mom da gudu harda tuntube yana shiga falon yaga tana rungume da baby da waya a hannunta da alama dad take kira da sauri ya qarasa Inda take yajawo baby da fiskarta ya baci da jini ya Ciro handkerchief nashi yafara goge fiskanta yace mom ruwa Dan Allah ta tashi a kidime ta nufi fridge dindake falon ta dauko ruwan gora ta mika masa ya bude ya shafa a fiskanta a hankali hawaye na Zuba a idonshi motsi tayi da idonta a hankali ta bude ganin shi take dishi dishi ta qara rufewa mom barin shiga da ita daki ta kwanta tace to daukanta yayi cak mom nagaba har cikin dakinta yasaukar da ita kan gadon mom ya gyara kwanciyarta ya riqe hannunta daya ya tsugunna gefen gadon ya tsurama kyakykyawan fiskanta ido daya kumbura yai jaa abin ka da farar mace ......
Mom ta yi ajiyar zuciya Ganin bacci baby take yanzu bakaman daba da bata numfashi kiran sunanta dataji yasata fitowa falon dad ne ya shigo yana kan kekensa biye dashi diyyah daka ganshi hankalinsa a tashe yake yace Sakina meyasamu Zainab din? inatake ? Mardiyyah tace ta mutu? Ba gaskiya bane ko yajera mata tambayoyi. duk a firgice ta tsugunna kusa dashi tare da kamo hannunsa duka biyu ta ce Alhaji baby na nan daranta suma tayi dazu amma ta farka tana bacci yace suma Kuma me yasameta bata da lafiya ne mom tace Alhaji kashiga ka ganta tukunna ta tashi tana turashi yayinda diyya tayi waje Dan sanar dasu Hajiya ....

Dad na tura kofan yaga yanda Khalid ke tsugunne a gefen gadon idonsa taf da hawaye har yanzu yana riqe da hannunta daya yana cewa
" Zainab ba halina bane dukan mace amma naqi jinin naga ana walaqanta iyaye abin namin zafi I'm sorry Zainab ki yafe ni nayi sanadiyyar zubar da hawayenki da jininki I'm so sorry please karki tsane ni kinji please don't hate me "
yakai hannunta bakinshi yayi kissing nashi yace my heart barinje na sayo miki magani kinji ya sake hannun ta ya tashi ya mata peck a goshi ya juyo zai fita yaga dad da mom a bakin kofa suna kallonshi wani kunya ya kamashi Dan yasan tabbas sunji meya ce ya fara sosa kai kansa a sunkuye yace dad mom barin je na siyo mata magani dad Murmushi yayi yace alright ya fita batare da ya bari sun hada ido ba mom ta turashi har bakin gadon ya kura mata ido yace Sakina me yafaru ne waya taba ta mom tace Alhaji lafiya tabar falona daxun taje wurin Hajiya to ni naje na sauke wasu baqi dasukazo ina dawowa naganta tana shirin faduwa kafin na qarasa takai qasa ashe suma tayi ni tsabar firgicewa danayi ban iya komai ba shine na kiraka kafin kaxo Khalid ya shigo da alama Alhaji marinta akayi Dan daxu hancinta da bakinta duk jini dad yai salati yace ikon Allah badai Khadija tayi wa yarinyar nan haka ba saboda tsana
Mom tace bana zaton itane amma kayi bincike kafin yace wani abu baby ta bude ido Ganin dad ta fashe da Kuka ya kama hannunta yace tell me baby nah waye ya mareki ta tashi daga kwanciyar datake duk da yadda kanta ke sarawa ta rungume dad shikuma yana buga bayanta a hankali dakyar ta samu ta nutsu ta sanar dashi komai bata rage ko daya ba Dan tasan harga Allah itama nada laifi Dan koba komai Hajiya ita ta haifeta amma take gaya mata magana irin haka....

Dad yace kwantar da hankalin ki aure an daura shima angama inhar inada rai kinji baby ta nodding kanta tace thank you dad yanzu ba Inda ke miki ciwo tace kaina dad kamar zai fashe yace rest now kinji khalid yaje siyo miki magani jin ance khalid ta bata rai tace dad wurin hajcy zanje yace no princess inkikaje a haka hankalinta zai tashi ki kwana anan gobe sai ki koma xan kirata tace ok dad ta koma ta kwanta shikuwa ya danna kekensa yayi waje ranshi na quna mom tabi bayanshi ....

A hankali ya shigo falon diyyah da sury na kallo Ramlah na bawa danta sabir abinci suna ganinshi kowa yasha jinin jikinsa gashi dama diyyah ta gaya musu abinda ya faru amma Hajiya tace kar wanda yaje gurin, yana kan kekensa yace Ramlah Surayyah dake Mardiyya wato magana na ne baza kuji ba ko kunaso kumin tawaye to duk wanda tasan she's not happy da auran dazan yiwa Muhammad to tashirya barin min gida Ku Kuma biyun nan ku kiyayeni dan wallahi zan iya maida ku Jama'are na aurar daku a wanda naga dama gara Ku nitsu kusan me kukeyi maza Ku bace min da gani da gudu su ka fita Dan tsoron hukuncin dad din yayinda sabir ya cigaba dacin abincin shi Dan baisan me dad kecewa ba saboda bayajin Hausa ....

Dad dakin Hajiya ya wuce ya shiga tare da sallama ko amsawa batayiba balle ta kalleshi Dan taji duk me yace wa su sury saima gyara zamanta datayi akan gado .. ya ce wato khadija har yanzu baki bar wannan zancen ba ko har kina so ki sa yaran nan su ki bin umarnina to wallahi inkin ga auren nan bai yiwu ba to bana doron qasa Kuma kikayi yunqurin hana auren nan a bakin auranki zaro ido tayi tace lallai Aliyu ka shika Dan halak sai ka iya saki na saboda wata banza tailor Mara asali Mara gata ita waye dazata rabeni bata da matsayin dazata hada zuriya dani wallahi dad cike da mamakin yadda ta kira sunanshi karangatsau shekararsu talatin da uku da aure bata taba cemai Aliyu ba sai yau duk da kunyar filanin yau ta cireshi
Yace tukunna khadija in tambayeki Sana'ar tailor haramun ne ko me sannan ita tailor ba mutum bace sannan ke waye da bazata rabeki ba kisani ke mutumce kamarta yadda Allah ya halicceki haka ya halicceta Kuma duniya me gushewane khadija kullum ina tunatardake wannan nidai na gaya miki hukuncina Dan kuwa bazanyi kaffara ba Kuma ki gwada ki gani ya juyarda keken kujerarsa yai waje ita kuwa tayi tsaki tare da tafa hannu tace mu zuba dakai =ؙ=ؙ=ؙ=ؙ=ؙ
[9/15, 1:45 PM]Maimunatu Telar Mata=ؙ

By

Azee cool=إ










32







...lokacin da Khalid ya kawo magani har lokacin tana bacci Dan haka ya bawa mom tare da nuna mata yadda zata sha amma saita fara cin abinci mom tace ba komai....

Yaje falon dad Dan bashi hakuri akace ya fita masallaci sai lokacin ya tuna sallan maghrib yayi shima yai alwala ya fita masallacin dake gefen gidan Bayan sun idar ya matsa wajen dad dake lazimi ya zauna bayan dad ya gama Khalid ya sunkuyar da kanshi yace dad dan Allah kayi hakuri abinda nayiwa baby banida niyyar cutar da ita
Dad yai Murmushi ya shafa kanshi yace Allah yama albarka ka nuna
Halacci ne ai baka da wani laifi baby kanwarka ce kuma ta dace da duk hukunci daka mata saidai ka dauna saurin mari saboda fiska abace mai daraja Kuma ko manzon Allah bayason haka
Khalid yace Insha Allah haka bazai Kuma faru wa ba dad yace Allah ya maka albarka yaushe su Abbanku Zasu iso yace Munyi waya da Ammi tace gobe yace Allah ya kawosu lafiya Khalid yace amin dad....

A falo mubeen ya samu mom na fama da baby taqi shan magani yace batta dani mom zan maganinta ya karba maganin yace haa taki bude baki ya fara mata cakulkuli

Please Login or Register in order to submit comment