Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana dariya tana Allah zansha ka tsaya yace in baki shaba kinsan sauran ta karba watsa a baki ya mika mata ruwa ta kora dashi tace bhai nasha ai karka Kuma min cakul kuli yace inkinci abinci ba tace naci fah yace bangani ba tace Katambayi mom mom dake zaune gefe tace ba abinda taci tea kawai tasha yace you see tace haba mom ta turo baki yace barin yanka bakin naga ta tsiya gashi dama ya koma ugly lips ta daki kafadanshi yana dariya ya fara bata abincin abaki tanaci a hankali ...
Khalid da tun dazu yake bakin kofa yana Ganin su cike da shauqi. Mom ta hango shi tace khalid karaso mana kana tsaye daga kofa Kuma ya karaso yana Murmushi yace mubeen bhai ina wuni mubeen ya juwo yace a'a. Babban likita ya kake yace lafiya MB yace gaskiya US ya karbe ka kaga yadda ka koma kuwa yayi dariya yace kaima Nigeria ya karbeka fa bhai yace koh ni miye field naka ne Khalid yace pediatric doctor (likitan yara) MB yace wow nice choice dama ana lacking consultant a field din gaskiya Allah ya taimaka yace amin
Tunda suke magana baby ta hade rai kamar taga mutuwa tana faman hararanshi ...khalid ya ce baby ya jiki tsaki tayi tace munafiki baiji dadi ba inma ka biyo nine kaga yadda fiskata ya koma to aniyarka ta bika dan yana nan da kyaunsa dan bakin ciki sai ya mutu tana gama fada ta shige daki

MB yace naughty girl kawai khalid kar ka damu zanyi maganin tsiwarta kaji shidai murmushi yayi yace bakomai ni zan wuce gidan Hajiya babba anan na sauka mom tace ka gaidata yace zataji ....

Mubeen ya tambayi mom abinda ya faru da baby ta sanar dashi komai yayi ajiyar zuciya lallai da sauransa wato hajiya bata hakura da zancenta ba ... Ganin ya shiga wani hali mom ta nutsar dashi ta hanyar mai nasiha sosai yaji dadi tare da cewa ya gode har zuciyar shi yana ina ma mom ce ta haife shi yasan tunda ya tashi Haka halin hajiyar sa take da kin talaka tun acan india ma bata harka da talakawa ...shikan harga Allah bawai yana kyamar maimunatu bane saboda tana talaka shidai rashin son wata mace bayan simran yasa yake jin bazai iya zama da kowace mace ba sai ita. ....
Dakin mom ya shiga yasama baby na waya da hajcy ya jira ta gama kafin ya mata fadan ta daina raina nagaba da ita kuma tayi hakuri da abinda khalid ya mata tace never bazan taba yafe mishi ba yace kinaso muyi fada kenan tace haba bhayya nah nida kai sai mutuwa. yace toh forgive him tace ba yanzu ba yace when tace sai an daura auranka ya ce tum pagal hai tace just like you ba yaja kunnenta tana dariya ....


Yau jumma'ah daya zamto ranar walimar saukatah da na aurena gidan mu yacika sosai Ko ina haya niyar jama'ah kake ji baba fenti yasa akayii a gidan jiya gidan ya qara fasali ..... Da karfe goma su Anty Sana suka wuce gidan Anty Fatima za aje min jere inaji ana cewa gidan nawa a new GRA yake nidai ban tanka ba ....tare muke dasu tasleemah suna tayani shirya wa Dan tare ma muka kwana .....karfe biyu da rabi baby ta shigo gidan mu ina ganinta na rungumeta ina haba angel kin gujeni fah tace wallahi ina son zuwa amma aiki ya riqeni. Sai dana saketa na lura da yadda lip dinta nasama ya tashi nace baby faduwa kikayi tace barshi kawai ill jist you later haka dai muka shige daki ....
Karfe uku da rabi motoci biyar sukazo daukar mutane zuwa wurin walima daga wurin Hajiya gashi baba ma ya nemi mota uku haka aka fara fita da kaya da masu tafiya dan dama baba yace baya son ayi african time sai alokacin na lura anyi anko 'yan maiduguri nasu daban na nan bauchi ma haka hatta inna tah ta saka kawayena nasu daban na ji dadi da baby tayi irin na 'yan gidan mu dik da ba wai atamfar mai tsada bace dubu hudu da dari biyar suka saya ......


An shiryani cikin wani gown mai kyau baby pink da da golden design a jiki aka tsantsara min kwalliya nasaka alkyabba nayi kyau sosai kowa sai masha Allah yake cewa daka ganni kaga amarya ga qanshi danake sosai ....
Hudu da kwata muka isa harabar makarantarmu acikin mota nida baby da tasleemah ina zuwa suka kama hannuna har kujerar da aka tanadar mani idona a rufe da anja hular alkyabbar ta rufe min fiska amma ana ganin bakina iyi kasa ....
Hudu da rabi aka fara jawabi anyi magana akan mahimmancin karatun alqur'ani kafin nan aka kira ni nazo na yi karatu baby da tasleemah suka riqeni har wurin da akayi shimfida na alfarma na zauna aka miqa min microphone na fara karanta karshen suratul baqara cikin karatu mai dadi danazo karshe dakyar nagama ina Kuka Dan sai lokacin nake ganin girman kyautar da Allah ya bani ina gamawa aka sa kabbara nanfa aka fara zuwa ana ajiye min kyaytuttuka dayake an hana kari a islamiyyarmu saisa kowa yazo ya ajiye a gabana nakai minti sha biyu ina wurin ana ajiyemin kyauta daga maza har matan mata insunzo sai sun rungumeni ko su sunbaci hannuna

Daga baya akace na tashi nan ma su baby suka mayar dani wurin zamana har lokacin ban bar Kuka ba ....a haka aka kira baba nah yazo yayi jawabi baba yazo yasha malummalum ash color data sha aiki baba addu'a ha dinga min dakyar ya qarasa dan kuka ya fara kowa abin ya birgeshi ...daga nan aka kira wani babban malami ya fara wa'azi akan aure wanda ya ta bo fannoni da dama daga karshe aka kira ayi addu'a kafin taro ya fara watsewa karfe shida da minti ishirin ....
Ba wadda yazo wurin walimar nan bai samu abin riqewa ba domin daga bangarenmu Munyi kokari anmin souvenirs mafifici,plate na roba da Kofi,da sponge case da leda sunana kawai aka rubuta na taya murnar Sauka da walimar aure
Bangaren su mubeen gaskiya sun nuna halacci Dan masu rabon abinci da souvenir ma takanas hayar su akayi na maza daban na bangaren mata daban sun raba bags manya da kanana,jugs,dustbin,parker,cups,plates,tray, manyan robobi,buckets, books,biro,towel,handkerchiefs,joters,kitchen towel,t-shirts abin gwanin sha'awa kowa sai san barka kafin mu tafi naje na gaida hajcy da mom sunsamin albarka sosai dama nayi mamakin ganin jama'ah dayawa haka ashe 'yan uwan mubeen ne suka cika wurin baby kecemin har. Dad yazo amma ya koma ba a gama walimar dashi ba
Sai karfe bakwai saura muka dawo gida ana kiran sallan maghrib ana isha baby ta wuce gida dan tace akwai abu buwan daza tayi da daren ....
'Yan uwana sai yaba halin dangin mijina suke dan basuyi zaton zasu xo walimarba balle har suyi halacci irin haka kuma ma manyan baqin dake waren duk nasu ne gaskiya sunyi hidima ....
Da karfe goma baba ya aika akirani nasa meshi adaki sosai yamin wa'azi da addu'o'in samun alkhairi a rayuwata yace gobe idan an daura aurena bani da uban dayafi mubeen dan haka na bishi sau da kafa yace min gimbiya yaushe kika dau hoto dashi ban sani ba na dago idona da sun yi jaa Dan Kuka nace baba ban taba daukan joto dashiba ya miko min books da joters din da gidansu mubeen sukayi naga daya ina xaune akan kujera nasa wata arabian gown light blue nayi rolling da gyalenshi mubeen na dauremin igiyar sandal heel dina shima wata light blue shalwar da farin jeans duk kanmu muna murmushi amma ba aga fiskanmu sosai ba saboda fiskarshi nakallon kasa ni ina kallon shi, daya kuma ina zaune yana tsaye hannunsa ya taba kafada nah na daga kai ina kallonsa ina Murmushi shima yanayi ,dukkanmu cikin indian wedding dress mai kyau gashi dama yana kama dash, haka na kare kallon hotunan dake jikin cover din duk Kansu hoton Dana dauka da baby ne amma yanzu ansauyata da mubeen nayi mamaki sosai nace baba da baby nadau hotunan nan bansan ya akayi yazama ansa hotonsa a madadin taba yace ba komai kinsan bature da hikima an ma naso ace koma miye sunanku ya wadatar basai an hada da hoto ba anma bakomai yace min nasama kyautar kudi dubu Dari hudu da ishirin da sauran Kyaututtuka daba a bude ba nace baba kari qesu kawai yace baza ayi hakaba nasamai Kuka dole ya amsa yana kara samin albarka....

Ina zuwa daki na kira baby nace nagode abin da kikamin ai wato hikimar daukan styles din hoton nan kenan tace relax sweetheart nasan in na gaya miki niyyata bazaki yarda ba nace shine kika shanmaceni ko tukunna ma yakikayi kika hada tace kin manta computer nake karantawa wannan duk mai saukine Kuma surprise dinki saima gobe Dan haka yanzu ki kwanta ki huta cox tomorrow is your day nace kema naki zaizo ai tace sosaima muka danyi tadi tacemin harsu sury suje walima nah saidai sun tafi da wuri nace ayyya Allah baiyi zangansuba tace karki damu gobe war haka zaki gansu na kashe wayar ina dariya...





Ranar aure

Karfe sha daya na ranar asabat aka daura auran Architect Muhammad Mubeen Aliyu Abdullahi da Maimunatu Ibrahim Misau

Daurin auran daya samu halattar manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan sarkin misau,Jama'are, da manyan 'yansiyasa da 'yan kasuwa,muqarraben sarkin bauchi da manyan 'yan boko suka halatta ......=Ø™Ü=Ø™Ü=Ø™Ü=Ø™Ü
[9/16, 11:12 AM]™ÜMaimunatu Telar Mata=Ø™Ü

By

Azee cool=Ø¥Ü















33





.



.....Mubeen sai a wurin daurin aure yaga friends dinsa dasuka yi makaranta a India da south korea sosai yayi mamaki saboda shi. Yasan bai gayyaci kowa ba amma yaji dadi bayan daurin aure akayi reception na maza zallah a zaranda hotel....

Tunda aka daura aurena hankalina ta tashi dan gani nake kamar nayi wauta da amincewa da auren mubeen bacin ya gaya mani bazan taba samun soyayyarsa ba haka dai na daure idan na yi tunanin haka sai inta karanta Innalillahi har na sama nutsuwa

Karfe bakwai da arba'in an gama shiryani cikin wani indian bridal dress ja mai kyau aka min kwalliya gaskiya kayan sun min kyau sosai tunda na fito kowa ke yaba yadda nayi kyau acikin kayan aka nufi dakin umma dani bata iya min wani nasiha ba sai addu'a data min tuni na fara hawaye aka wuce dani falon baba yana zaune akan kujera na tsugunna kusa dashi ina Kuka tashi yayi ya rungumeni yace gimbiya ba abin dazan ce miki sai Allah ya miki albarka duk wani abu daya kamata na gaya miki nayishi tun jiya ya mikar dani muje ana juranki haka ina rungume dashi har muka fita Ya zaunar dani acikin o
Mota na kamkameshi ina Kuka shima lokacin dauriyarshi ta kare ya fara hawaye yace gimbiya aure ba mutuwa bane Allah ya sada mu da alkhairi ya sun baci goshi na ya fita na sukuyadda kaina ina Kuka naji an dago ni Khalil nagani yana hawaye yace U'una tafiya ba sallama na rungume shi yace sake ni kar ki samin baqi na daki bayanshi ya rada min a kunne kinyi kyau sosai fatana mubeen ya kula dake inba haka ba har gida zan bishi na sare mai kai nayi Murmushi nace Khalil zaka na zuwa min ko yace sosaima ya sakeni tare da kissing kumatu na I'll forever miss you maimunatu nace me too.....
Anty sana da anty fatima ne suka zauna tare dani aka wuce dani gidansu mubeen kafin mu qarasa sun gyara min kwalliya na saboda Kuka da nayi.. Motoci goma ne suka zo daukana motar mu na tsayawa Aka fito dani dayake anja min dupatta din ya rufe fiskana gaba daya a hankali muke takawa har bakin kofar shiga tun daga kofa aka fara guda Ga wakokin India da ke tashi ga hayaniyar jama'a MC ya ce amarya bazata shigo ba sai an biya kudin takunta nan wani ya bada dubu dari aka sa tafi a hankali muke tafiya nidai bana Ganin komai har muka iso inda MC yace yanzu ango zaizo ya karba amaryarshi duk da turanci yake magana nidai kirjina sai bugawa yake nan su Anty sana suka sake hannuna nan fa naji kaman zan fadi Dan jikina duk na tsargu da yadda kowa ke kallona
A hankali mubeen ya karasa cikin takun alfarma yasha wani majestic sherwani very light brown da touches din jaa a jiki sai Nehru(turban) da wani dupatta da jaa da ya saka a wuya jelan guda biyu ta gaba ji nayi an kama hannuna bazan taba mantawa da taushin hannunsa ba a hankali yana Jana har muka fara hawa step dayake bana kallon gaba na Kuma bansan da step dinba ga takalmi mai tsini nan na harde kaman zan fadi kafin na kai kasa ya sa hannunshi ya tallafoni na fada kirjin shi ya rada min a kunne hey local girl kinga akwai manyan mutane anan don't make any foolish scene dayake ba wadda yasan me yace abin sai ya bada kala akasa tafi nan ya sakeni muka karasa hawa steps din

MC yace yanzu ango zai bude fiskan amarya amma sai an biya kudin fiska nan aka bada dubu dari da hamsin nidai ji kawai nake ina Ganin ikon Allah bansan za ayi wani shagali a gidansu mubeen ba da bazan yadda ba . .

A hankali ya daga dupatta din da aka rufe min fiska ya maidashi daidai goshina nikan idona a kasa shi Kuma ya tsuramin ido Dan yau yaga nayi daban anya ma itace abin da yake fada kenan akasa tafi kafin akace mu zauna shi ya zaunar dani kafin ya zauna shima nikan kunya nakeji na kasa daga ido na kalli jama'an wajen ...
Baby ce ta dafani na juyo na kalleta takashe min ido tana dariya tasha wani lehenga dark blue da touches na fari a jiki sun mata kyau

Hajcy ta mika min Varmala(garland) ni ban ma San sanda sukazo ba tace in sawa mubeen a wuya nidai kunya nakeji na karba hannuna na rawa idona a kasa nakai zansamai amma Ashe hannuna bai kaiba Ganin nakasa yasashi kama hannuna mukasa tare abin sai ya birge mutane aka fara tafi nan mom ta mika mai shikan ko tsayawa baiyiba yasamin nan ma aka sa tafi

Abu na gaba aka ce yasa min sindoor(red vermilion) Nan ya Dan gwala da yatsar sa ya samin a tsakiyar goshina daidai farkon gashina daga nan aka fara kiran abokin ango kamal yayi bayani akan mubeen sai baby ta fito tayi bayani a kaina

Next sai naga an kashe wuta aka kunna Kuma nan kidan Aaja nachle ya fara exactly irin rawan da maduri dixit tayi a wurin shi baby da tawagarta mutum takwas suka yi abin ya burge kowa harni ma Dan zagewa nayi ina kallonta data gama aka sa tafi sosai

Ko kishi ne ko dama sun plan ne haka sury da diyyah suka zo suma sukayi rawan dola re dola re na film din devdas sury tayi acting as Aishwariya diyyah kuma as madhuri abin gwanin sha'awa sai lokacin naga yadda hall din ya kayatu dan bakaramin gyarashi akayiba ko ina ga flowers jama'a kuma wasu a zaune wasu a tsaye gashi kowa ja ganshi cikin shigar indiyawa yake harta su anty sana dana hango su sunsha sari mai kyau friends dina da 'yan uwana dasuka kawoni sunyi ankon salwar kameez wasu pink wando da gyale pink sai rigar fara da flowers pink wasu kuma blue ne nasu kowa yayi kyau

Manyan matan dake wurin ma wasu sari suka sa wasu salwar kameez,wasu lehenga, hajcy ma sari tasha. 'Yan matan wurin wasu sun rufe kansu wasu ko kansu bude da gashin su ko kuma gashin aro(wig,attachment, Brazilian hair ko wool)

Daga nan aka fara bada gift aboka nan mubeen suka fara zuwa kowa yazo ya congratulating dinmu suyi shaking da mubeen ni kuwa hada hannu nake kamar yadda India ke namaste nasu yadda mutane suka futo bada gift nikan sai dana tsorata dan ma abin anyi wrapping ne bana ganin miye aciki amma inada yaki nin abubuwane masu tsada

Ana gama bada gift akace ango da amarya su fito su taka nikan ki nayi shima yamin rada a kunne dont embarass me please ki tashi haka na tashi muka isa wurin nidai tsaya wa nayi Dan wallahi bazan iya rawa a gaban mutane ba harda Sara ka naina haka akazo akayita mana kari ina tsaye ko gizau banyi ba yadda suke zuba kudi kamar basa so nace Allah ya bawa talaka hakuri

Ana gamawa aka bada fili kowa yayi rawa MC yace this is an indian night so every bodu should just nachle ve ...haka 'yan mata da samari suka dinga rawa duk Indian songs ake playing baby ba abarta a baya ba tama je ta chanja kaya zuwa wani anarkali gown mai kyau orange sosai aka chase daga nan aka dinga daukan hotona. Bana so amma ya na iya masu selfies masu hoto duk an sha hoto sai goma da rabi aka kare nan su anty sana suka kaini falon mom tamin addu'a daga nan sai falon Hajiya muna shiga 'yan uwanta suka fara mana habaici amma su anty suka daure basu tanka musu ba raina ba karamin baci yayi ba hajiya da ko kallo ban isheta ba tace jibeta dallah ina mubeen ina wannan baqar toh koda asiri kikayi kika shigo gidannan ni zan fidda ki na tsorata da maganganunta haka su anty ma bangaren mubeen aka daukemu akan gobe za a wuce dani gidana

Anty sana tayi ta bani hakuri kan kar insa damuwa araina Insha Allah ba abinda hajiyar mubeen zata min baby ce ta kawo mana abinci mukaci namata fada kan party data sa akayi tace haba angel a gida ne fah Kuma dad ne ya amince dan da bai amince ba baza ayi ba tunda mubeen ma baisan da Indian night dinba sai yau haka muka sha hira tana tsokana na sai one muka kwanta
Nida baby da tasleemah,ummita,Aisha,da umaimah a dakin mubeen muka kwana,su Kuma su anty sana, Fatima,da antynmu Dan ba azo da umma ba suka kwana a daya dakin dayake part din falo ne da daki biyu .....


Asuba ta gari amarya Maimunatu=Ø™Ü=Ø™Ü=Ø™Ü=Ø™Ü=Ø™Ü
[9/18, 3:01 PM]™ÜMaimunatu Telar Mata=Ø™Ü

By

Azee cool=Ø¥Ü












34









Da safe lafiyayyar breakfast aka kawo mana wasu abin ma ban San sunansu ba ko jiya da akayi Indian night ma duk abin da aka serving a wurin Indian cuisine ne tun daga chicken biryani,aloo tikki,aloo paratha,chapati,golgappas,kebabs, idli,dosa,dal bati,dal roti,kachori,upma,uttapam,etc gaskiya Arziki na inda yake

Bayan munyi breakfast aka shiryani cikin wani atamfa riga da siket duk yadda suka so nasa gyale haka naki nasaka hijab dina daya matching kayan Mai hannu daya rufe gwiwa na mukaje gaida mutanen gidan dayake baby tace dad yana da baqi sai muka wuce falon Hajiya kamar dai jiya ko kallo bamu isheta ba dan ko da su Anty sana suka gaishe ta tsaki tayi ta juyadda kai wata acikin matan dake zaune a wurin tace Dan Allah kun cika mana wuri bama bukatar gaisuwanku ayi gaba can karku shafa mana tsiya Dan naga shi Kuka gada baby tace Alhamdulillah Umma Habiba tunda yanzu tsiyar ta zama naku ba Kuma mutu ka raba wallahi na harari baby ta juyadda kai gefe tace mu tafinku har muka fita muna jin mitar matar da alama kanwar hajiyar ce

Baby ta cewa su anty sana suyi hakuri suka ce ba komai amma ni nasan kawai sun danne ne saboda anty sana ma mace mai zafi nikaina bawai najin dadin abinda ya faru bane saboda nida 'yan uwana aka walaqanta saidai maganan baba na yasa na daure nayi kamar abin bai dameni ba (baba yacemin maimunatu Gidan mijin ki gida ne na masu arziki dole sai kinyi hakuri Dan bakowa zai soki ba Kuma ba kowa zai kalle ki da daraja ba sai dai ki sani wanda ya nuna yana sonki a yadda kike ki girmama shi wanda ya nuna yana qinki ki nuna kowa naki ne karkiyi gaba da kowa )

Falon mom mukaje tana zaune da Ammi,Anty Zahra ,anty nusaiba,da mama matar uncle muhammad cikin farin ciki suka tarbe mu kowa yana fadin tubar kalla amarya ta dace da mubeen hira sosai sukayi dasu nidai ina gefe kaina a kasa dayake baby ta fita munfi awa kafin baby tazo tace mu tafi baqin dad sun tafi Nida baby da su tasleemah ne muka shiga falonshi su anty suna tare dasu mom Dan ko kadan basu kyamace su ba sun nuna musu anzama daya .....

Da muka shiga ciki jinayi duk kunya ta kamani danko jan hijabina nayi ya rufe min goshi na zuwa hanci shi kadai ne yana zaune akan kujera gefe kuwa keken kujerarshi ce hannunsa da carbi yana ja. Baby ta fada jikinsa tana dad ga amarya na kawo maka kyauta ya sunbaci goshinta cikin so da kaunar diyar tasa dan ita kadai take murna da wannan aure Dan duk wata hidima da akayi jiya da gayyatar friends din mubeen ita tayi

Yace princess nida nake gurgu ina ni ina amarya tayi dariya tace kana dai tsoron su mom da hajiya karsu kara saka yace gaskiyanki kar tsohin nan su illata mini amarya Gaba daya aka sa dariya dad ya tambayi sunayen su gaba daya cikin kulawa da barkwanci daga baya yace zai yi magana da surukuwarsa nidai jikina sai rawa yake baby tace dad kar abata duka fa a rage mana muma yayi dariya yace karki damu kadan zan bata

suka fita saura ni da dad Har lokacin kaina a kasa
Yace Maimunatu barka da shigo wa wannan Gida Kuma ina tayaki murnar auren Babban Dana Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da hakuri da juna yakuma baku zuriya dayyiba

Da farko ina so ki daukeni tamkar mahaifinki bana so kimin kallon uban miji domin ke yanzu 'yata ce duk abinda zan yiwa baby kema zan miki
Nasan kinada masaniya kan Muhammad yataba soyayya da wata kuma bayanta be taba son wata ba amma inada tabbacin Muhammad zai soki wata rana koda ba nan kusa ba amma ke zaki sanya yasoki ke zaki koya mai soyayyar ki ta inda zaiji bazai iya rabuwa

Please Login or Register in order to submit comment