Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya raɗa mata a kunne,da sauri tayi baya Inna kuwa cewa tayi "ka tashi ka tafi gidan ka sha ɗayan dare har ya gota ni zan kula da ita"




Basheer ya miƙe ya na satar kallon Sheera kafin yayi masu sai da safe,har ya kai bakin ƙofa yaji Inna na cewa "ka kula da Azkhar kafin ka kwanta" "in shaa Allahu!"ya amsa mata.
Sai da Inna ta je ta rufo gidan kafin ta dawo inda ta bar Sheera,kuka ta tarar da ita ta na yi.Ba ta tambayeta dalili ba amman ta umarce ta da tayi wanka da ruwan addu'a bayan ta ajiye mata wata ƙatuwar roba da kuma zanen da za ta sa,Sheera tayi wankan ta wanke har gashin kanta kafin tayi ɗaurin ƙirji.


Ƙurya ɗaki suka shiga ta kwanta a gado yayinda Inna ta shimfiɗa sallaya ta shiga jero nafiloli haɗi da addu'o'in ta da ta saba yi.Sam Sheera ta kasa yin barci tsoron abinda Daddy yayi mata kawai ke ƙara shigarta,ta goge hawaye ta na ma Allah godiya da ya kuɓutar da ita kafin ya keta mata mutunci.Da tunanin Basheer ta samu barci yayi awon gaba da ita,bayan Inna ta gama sallar ta zo tayi zaune ta na kallon Sheera.Wani tausayinta taji ta na kuma yiwa Ɗanta fatan Allah sa iyayen Sheerar su bashi aurenta tunda ba sai ta ba kanta wahala wajen bincike ko suna son juna, bayyanar Abrar a tattare da Sheera kaɗai ya isa ya zame mata hujja.





BASHEER POV.


A zaune ya tarar da Badiya ta ci kuka har ta ƙoshi ido duk sun yi mata ja,ta na ganin sa ta tashi ta faɗa jikinsa.Ya rungumo abarsa ya na sunsunar gashinta,ta ɗan ja da baya ta kallesa tace "ina ka tafi har haka kuma ina ta kiran wayar ka ba ka ɗauka?" "Zan yi wanka dai yanzu,dan Allah ki nutsu lafiya ta lau ina son ki sama min nutsuwa a matse na ke"
Wani tsoro ne ya baibaye Badiya ta na jin kamar ta runtuma ihu saboda tunda cikinta ya shiga watan haihuwa ta tsani ya kusance ta.




Tuni Basheer ya cika bokiti da ruwa ya tafi banɗaki,ko da ya dawo ya tarar har ta cire kayan jikinsa.A mugun buƙace ya ƙarasa gare ta ya fara shafarta,murya na ɗan rawa tace "Ya Basheer nace ka fara cin abinci ko?"kai kawai ya girgiza mata dan ba zai iya yin magana ba.
Bakinsa ya ɗora kan nata ya fara kissing tare da matsa albarkatun ƙirjin ta uwanda suka ciko sosai saboda cikin jikinta.Idon Badiya sun raina fata ganin BASHEER na nuna alamar ya na son ya shigeta,ta na matsar ido haka ta barsa ya shigeta har wata ƴar ƙarar azaba ta ke yi.Bayan sun gama suka kwanta, Basheer kuwa sai murmushi ya ke ya na tuno yadda siffar Sheera ta ke.Yayi nisa a cikin tunanin sa ya ji Badiya na hucin wahala,da sauri ya tashi zaune ya na cewa "ya dai? "
"Ƙuguna Ya Basheer! Washhh marata" hankali tashe ya fara yin salati da hailala ga Ubangiji.Kuka Badiya ta fara yi masa dan kuwa ciwon sai gaba ya ke yi,rasa yadda zai yi yayi kawai ya tisa ta a gaba ya na kallo zuciyar sa na bugawa da ƙarfi.A tunanin sa ko ciwo ne ya ji mata sai da ya ga Badiya ta miƙe ruwan haihuwa sun fara yi mata zuba can kuma ya ga ta duƙa ta na nishi.





Da sauri ya buɗe ɗaki ya nufi na su SA'ADIYA,mijinta ne ya buɗe.A ɗan rikice Basheer yace"dan Allah Madam ce za ta haihuwa ko za ka kira matar ka ta taimaka mata"kasancewar mijin SA'ADIYA babu ruwan shi haka ya lamunce mata taje ta taimaka ma Badiya .
Ita ta shinfiɗa mata leda da wasu zannuwa,an fi awa ɗaya Badiya na cikin wannan halin kafin ta haifo Ɗanta namiji.
Kukan jariri shi ya saka Basheer shigowa da sauri,a wahalce Badiya ta yunƙura za ta tashi sai kuma ta jiri doli ta haƙura.




SA'ADIYA ta gyara bébé ta miƙa ma ubansa kafin ta taimaka ma Badiyar,tuni ɗakin ya ɗauki ƙamshi haihuwa Allah yayi Sa'a ma Badiya ba ta cikin mata masu zubda jini sosai.Turaren tsintsiya gami da na ɗaki ta yayafa kafin ta wuce ɗakinta,sosai Basheer yayi mata godiya sai kuma yaji kunya duk ta kamasa kasancewar ko gaisuwa ba ta haɗa sa da Sa'adiyya.






Washegari
Asibitin Ali Shaibu ya kai ta, likitoci sun yi faɗa sosai dan mi aka barta ta haihu a gida kafin su dubata.
Lokacin da Basheer ya zo ya gaya ma Inna sosai tayi murna,ita kuwa Sheera baki ta turo gaba ta na jin haushin ba ita ce mace ta farko da ta haifa masa Ɗa ba.



"Ita wannan baiwar Allah ya kamata ka kaita gidan su ko?"Inna ta faɗa, Basheer ya girgiza kai yace "a'a ta zauna nan wajen ki in ya so zan je gidan nasu na faɗa ma Mamy" Inna tayi shiru kafin tace"to in hakan shine daidai ai gwara ka tafi tun yanzu na san yanzu hankalinta na can a tashe"
Bai wani jima ba ya nufi ADS, lokacin duka-duka ƙarfe bakwai na safe.Ya na shiga da gawar baƙin karen Daddy ya fara cin karo amman yayi tafiyar shi zuwa ciki,a falo ya tarar da Mamy ta na kuka yayinda gefenta kuma Jumma ce kwance cikin mawuyacin hali.




Mamy ta miƙe da sauri ta na cewa "Ina Sheerar ta ke?Jumma tace min ta na gun ka?" Da alamun mamaki Basheer ya kalli Jumma wacce ke ƙoƙarin tashi zaune dakyar ta zauna ta na mai cewa "kar kayi mamakin haka domin tsawon shekaru masu yawa na ke zaune da wannan familyn ba tare da su sun san wace ce ni ba.Na kasance Ƴa ga Sarkin mahalbi,tun ina ƴar ƙanƙanuwata na mayar da wasa da aljannu ɗabi'a ta,domin kullum mu na cikin daji .Bayan rasuwar mahaifina ne na dawo cikin masarauta da zama a matsayin baiwa,sai kuma naci Sa'a sarki ya mayar da ni kwarkwarar sa.Ina da aljanata wacce duk dare ta na zuwa mu yi hira,sannan ta na gaya min duk abinda zai faru.Yanzu dai in taƙaice ma duk wani aikin assha da Alhaji ke yi duk na san da shi,wanda wajen bin didigi har na shiga ƙungiyar ban farga ba amman duk da haka ban faɗi a banza ba tunda na ceto Sheera da taimakon ka.Abinda na fi takaici shine yadda ya salwantar da rayuwa Ɗana Ahmad ya cire esprit ɗinsa ya saka shi a kwanyar karensa RAM yanzu haka kuma tuni ya mutu a wannan duniyar,sai dai zai cigaba da rayuwa ne a duniyar matsafa wacce ba'a gani." Jummah na kawowa nan ta fara yin tari kafin ta ɗora da "yanzu haka nima ina daf da mutuwa tun jiya suke son janye ni daga wannan duniyar kamar yadda suka tafi da Daddyn Sheera ya na can su na azabtar shi kuma ba zai taɓa dawowa wannan duniyar ba"



Da sauri Basheer yace "Mamy taimaka min mu fitar da Jummah daga wannan gidan kafin su ci galaba kanta,ba zan so ta mutu cikin shirka ba" ba ta tsaya wani tunani ba suka talalabeta zuwa mota,a baya suka sakata yayinda Basheer ya zauna wajen mai zaman banza Mamy kuma na driving.




Su na tsaka da gudu sai su ji tamkar ana son shigowa motar hakan yasa Basheer ya fara karatu cikin ɗaga murya,a haka har suka ƙaraso makarantar Malam Abba.Wacce makaranta ce mai yawan almajirai mahardatan alƙur'ani mai girma, Basheer ya sauka ya yiwa malamin bayani kafin su shigar da Jumma cikin wani zaro.
Manyan malamai gami da wasu almajirai da shi kansa Basheer suka shiga yi mata ruƙiya ta fiddar Aljannu sihiri da duk wani dattin shirka.





Tamkar wani robot haka Jummah ke kuka ta na ƙari ta na cewa su bar ta hakan amman ba su saurareta ba.An yi nisa sosai kafin muryarta ta canza zuwa ta namiji "banza *ƊAN ACAƁA* ka ruguza mana shirin da mu kayi shekaru da shekaru a kai,amman hakan duk sakacin AlGabid ne kuma wlh duk gare sa zan rama yadda ya sa nayi asarar clients ɗina uwanda suka shigo ta hanyar sa"Marlin shugaban ƙungiyar ASOMA gaba ɗaya ya faɗa kafin ya cire duk wasu makamansa daga jikin Jummah.



Bayan an yi libéré ɗin ta ne malam Abba dattijon arziki ya fara yi mata nasiha tare da shawartar ta tayi tuban gaske ta lazumci Istigfar in ba haka ba Marlin zai iya dawowa muddin babu ƙarfin imani.
"Mun gode sosai malam in shaa Allahu za mu sake dawowa"Basheer ya faɗa kafin su yi sallama.Asibiti suka kai Jumma domin a duba lafiyarta,a nan aka tabbatar masu doli sai an yi mata tiyata an cire dattin sperm ɗin da ke duburar ta.Tuni Mamy ta ɗauki charge ɗin komi kafin su nufo gidan Inna ,da murna suka rungume junan su Sheera sai kuka ta ke.




"Da har zan tafi asibiti sai Iya mai wake tace har an sako su tuni su na gida"cewar Inna ta na duban Basheer ,ya karyar da wuya yace "ban ma sani ba kasancewar wayata ta faɗi a jiya"


"Ƴar uwa na gode sosai da karamci,ina wuni ni shaf na manta ashe ba mu gaisa ba"Mamy ta faɗa ta na shafar ƙwalla,Inna tayi murmushi tace"na fahimce ki ai doli ki fita hayyaci ɓatan Ɗa ai ba wasa ba balle kuma ɗiya macce" nan suka ɗan fara tattaunawa har Mamy ta sanar da Inna Daddyn Sheera da kansa ne ya so wulaƙanta Ƴar sa.
"Innalillahi wa'inna iley raji'un !Duniya ina zaki je da mu garin son dauɗar duniya har idon mutum su rufe har haka?"Inna ta faɗa cikin kuka, Mamy tace "AlGabid babu abinda ba zai iya ba a duniyar nan sam bai da imani,ba zan taɓa yafe masa ba manyan zunuban da ya aikata min a duniya ba"

"Ina mai sunan AlGabid ya ga imani!na tsani sunan nan tunda shine silar zubar hawayen mijina tun ya na raye har ya bar duniya ya na da haushinsa" Inna ta faɗa cikin kuka.
"Duk abinda mai irin sunan Daddyn Sheera yayi maku na san ba zai kai irin nawa ba,ya rabo ni da gidan mu sannan ya sa na nisanta da Ɗan uwana mafi soyuwa a gare ni.Yanzu in na tafi AGADAS wa zai shaida Ni?ƙila ma sarki ya mutu har an ɗora wani kan karagar mulk...." Mamy ba ta kai ga dire maganarta ba Inna tayi saurin kamo hannunta ta na cewa "kar dai ace ke c...ce Hawas? Ƙanwar mijina Innalillahi ,dan Allah ke ma daga Masarautar Agadas kika fito ƴar asalin can ce?"



Zumbur Mamy tayi ta tashi tsaye ta na kallon Basheer wanda shi tun da suka fara hirar hankalin shi na kan Sheera suna magana da ido.
"Kamanin Ya Adams,sak Yayana Adams!wayyo Allah na!ya aka yi na zama shashasha har haka?ga photocopie Ya Adams amman na kasa ganewa?"sai kuma tayi ƙasa za ta faɗi da sauri Basheer ya tarota.



Zuciyarta ce ke bugawa da ƙarfi wanda kusan haka na faru da mutane da dama in sun ji abun farin ciki ko akasin sa.
Sheera ke yi mata fifita , Basheer na tallabe da kanta yayinda Inna ke ɗiga mata ruwan sanyi tare da yi mata addu'a.
An ɗauki lokaci kafin émotion ɗin ya saketa,ta ƙure Basheer da ido ta na cewa "mai sunan Sarki miyasa ba ka taɓa gaya min ba?ashe kai JININA NE KAI (MRS SADAUKI) zo na rungume ka Ɗana ashe ba banza na ke jin sonka ba tare da yarda da kai" Mamy ta rungumesa sosai a jikinta,Sheera kuwa kuka ta ke yi lokaci guda kuma ta na murmushi wanda ita kanta ta kasa tantance na miye.....
[15/08 à 13:20] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*




*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.




*The END*




Duk yadda suka so Jumma ta rayu amman Allah bai yi nufi ba tuni ta koma ga ubangijinta.Sai da malumai suka je suka yi saukar alƙur'ani sannan kawai Mamy ta shiga ta ɗauki duk abinda ta ke buƙata ita da Sheera kafin su dawo gidan Inna da zama.
Duk yadda Sheera ta so ɓoye kishin ta lokacin da suka tafi yiwa BADIYA barka abu ya cuttura,sai turo baki take ta na ɓata fuska.Ita kuwa Badiya baiwar Allah tuni ta sare tunda taji bayanin wai BASHEER da SHEERA ƴan uwan juna ne,tuni kuma ta san aurensu babu fashi sai kuma wani ikon Allah.
Kawu Laminu da iyalansa su ma sun zo musamman da Inna ta shaida masa abinda ke faruwa, Allah sarki aka ce so mugun ciwo tuni zuciyar Kawu Laminu ta motsa da ya ga Mamy sai dai ko kaɗan bai nuna ra'ayinsa a kanta ba sun dai yi kukan farin ciki tare da tambayar juna bayan rabuwa.





Sheera da BASHEER ne zaune a cikin Naturex wani filin shaƙatawa ne domin yara da dai sauransu.Yadda tayi saƙo ya saka shi jan ɗan yatsan ƙafarta,ta ɗago da sauri ta na zuba masa marayun idonta da suka yi wani yaushi kamar za tayi kuka."Mine ne kuma?kin san saboda ki rage damuwa na kawo ki nan shine kuma za ki wani zugum ki na tunani?" Ta ɗan kwaɓe fuska kafin ta matsa gunsa ta ɗora kanta bisa kafaɗarsa "ina kewar Daddy ne ,a kullum sai na yiwa kaina tambayar miyasa Daddy zai min haka?..."jin muryarta na rawa yasa ta ƙyale.Basheer ya zagaye bayanta da hannunsa yace "Babyna ki bar maganar nan please, Daddy ya cutar da mu sosai ba zan ce ki cire sa a rai ba saboda hakan abu ne mai wuya amman ki sani ba zai taɓa dawowa ba ya tafi duniyar matsafa kenan "
Hawayen idonta ne suka samu nasarar zubowa Basheer ya fara goge mata.



"Assalamu alaikum"wata murya tayi masu sallama da sauri BASHEER ya ɗago idonsu ya haɗu da na Baba tsoho,murmushi yayi ya na mai zama kusa da Basheer yace "na san ka gane ni,da farko ina baka haƙuri na wasa da rayuwar ka da nayi sai dai alhamdullah mun ci nasarar durƙusar da ƙungiyar ASOMA sannan ta dalilin ka na karɓi kalmar shahada na musulunta." Basheer kasa cewa yayi komi sai haɗiyar yawu, Baba tsoho ya cigaba da cewa "cire zoben nan na ga hannun yarinyar nan ka miƙo min shi" Basheer ya kalli Sheera wacce ita sam ba ta ganin Baba tsoho.





Hannunta ya kama tare da zaro zoben daga yatsanta,wata zabura tayi ta na jin tamkar an cire wani nauyi na jikinta.
Baba tsoho ya karɓi bague ɗin ya na mai cewa "Abrar daga yau ba za ki ƙara cutar da kowa ba zan je na ɗaure ki a kogo,Jikana na gode sosai Allah albarkaci rayuwar ku" ya na gama faɗa ya tashi yayi tafiyar sa, Basheer ya bi sa da ido sai yau ma kamar wancan karon bai yi nisa sosai ba ya ɓace ɓat.




Sheera ya kalla wacce tayi wani liƙis tamkar wacce ba ta da lakka a jiki,ya shafi kumatun ta yace "tashi mu tafi gida"ba tace komi ba ta fara ƙoƙarin miƙewa, Basheer ya taimaka mata ta tashi.
Kan babur ɗinsa suka hau kafin su ɗau titi,direct gidan Inna suka wuce.A zaune suka tarar da su suna cin dambun shinkafa da zogale,a gajiye Sheera ta nufi Mamy ta kwanta a jikinta.Basheer ya harareta yace "dallah tashi ƙatuwa da ke kin wani ɗale jikinta" Sheera ta turo baki ta na mai ƙara gyara kanta a kan cinyar Mamy.
"Tashi ki wanke hannunki ki zo mu ci abinci na san bai baki komi ba tunda kuka fita"Inna ta faɗa Sheera ta miƙe ta na cewa "wlh kuwa Inna kamar kin sani sai wani toyayen tsire da ya saya min "ta faɗi haka ta na mai shiga ɗaki Basheer ya take mata baya.





Ƙoƙarin turesa take amman ko gizau,ta turo baki gaba shi kuma yayi saurin duƙawa ya cabke dukkan laɓan nata ya fara tsotsa.
Zuciyarta ce ta fara halbawa ta na jin wani irin daɗi na ratsa ta,ya na ƙoƙarin saka hannunsa cikin rigarta yaji motsi bayan su da sauri ya sake ta.
Inna tace "mine ne kake yi mata?"bai ce komi ba ita kuwa Sheera sai zarar ido ta ke kamar tsohuwar mayya.Inna ta harareta tace "wuce maza mu je ki ci abinci in kika biye ta wannan zai kai ki ya baro ne"sumi-sumi Sheera ta fita tsakar gida ita kuma ta wani tsare Basheer da ido ta na kallo har sai da ya tsargu ya ɗago ya dubeta yace "Inna ...." Ta ɗaga masa hannu kafin tace "ya isa haka wuce ka tafi gidan ka"ya turo baki kamar wani ƙaramin yaro kafin ya fita.




"Kai ba za ka tsaya ka ci abincin ba ne?"Mamy ta tambaye shi,ya karye wuya yace "zan ci ina tafi gida" Sheera tayi saurin ɗagowa ta na kallonsa zuciyarta banda ƙuna babu abinda ta ke yi.

Har ya kai bakin ƙofa ya tsinkayo muryar Inna na cewa "Basiru na manta ban faɗa ma ashe abokin ka Lawan haka tashi mutuwar ta shi ta zo da hauka?" Da sauri ya juyo yace "wane Lawan ɗin"
"Abokin ka dai an ce ya na tsaka da tuƙin mota ya fito ya fara hauka kafin kuma wani lokaci wai ya mutu"
"Lawan ɗin ne ya haukace ?"
"Ni ma wannan ya fi tayar min da hankali ba irin yadda matarsa ta warke garas daga nata haukan sannan wai an zo wankan gawa aka tarar babu wasu sassa na jikinsa"
"Innalillahi wa'inna iley raji'un !" Shi kawai Basheer ke maimaitawa ya na jin kamar ma ace bai taɓa sanin Lawan ba amman ya zai yi sai dai haƙuri,jiki babu ƙwari ya nufi gidansa.






Duk yadda ya ke son hakice abun a ransa amman ya kasa doli yayi alwala ya fara karatun Alkur'ani a haka ya fara jin sassauci har ma ya ci abincin da Badiya ta kawo masa.
Ta zauna kusa da shi ta na kallonsa yayinda mai tsaronta ita ma ta kasa ta tsare ta na hankalce da su,jariri ta ke gasa ma cibiya amman rabin hankalinta na kansu.
"Miye wai ke damun ka?" BADIYA ta tambaya,kai ya girgiza mata yace "babu komi,je ki karɓo min Daddy ina son ganinsa duk yau ban ɗauke sa sosai ba"
"Yanzu aka yi masa wanka sai an shirya sa,tun ɗazu ya ke rigima wai zafi ya ke ji"
"In shaa Allah ya kusa shiga AC sati mai zuwa za mu tafi Agadas" BADIYA tace "na zata sai mun yi arba'in ai" ya waro ido yace "rufa min asiri ai na matsu na tafi na ga Kakanni na" Badiya ta haɗe rai tace "sai maganar auren ku ko?" Yi yayi kamar bai ji ta ba ya ɗauki ruwa ya fara sha.




BADIYA ta tashi daga inda ya ke ta na jin wani azababen kishi na taso mata,Bébé Adams ta karɓa ta fara basa nono yayinda idonta ke ɗigar da hawayen baƙin ciki.
Basheer ya girgiza kai a zuci ya na jinjina girman kishin mata wanda ya ke cike da zallar hauka.





A yau aka yi suna an yi biki sosai wanda Mamy ta ɗauki charge ɗin komi.Tunda ƴan bikin suka watse BADIYA ke kwance babu lafiya,jini sai zuba ya ke yi mata kamar yau ne ta haihu.
Doli suka tafi asibiti, Sheera ke riƙe da Bébé Adams ta na ririga shi,kamar an ce ta waiga ta tsinkayi Maryam.Mamy ta baiwa BB ɗin kafin ta nufi inda Maryam ke tsaye jikin wani iccen gwaba, "Maryam?" Da sauri ta waigo ta na ganin Sheera ta fashe da kuka tare da faɗawa jikinta.
"Minene ba ki lafiya ne na ga duk kin rame kin yi baƙi?"Sheera ta tambayeta,cikin kuka tace "Sheera ina cikin tashin hankali banda lafiya sosai duk exam ɗin da ake yi min result ɗin nunawa ya ke lafiya ta lau alhalin ina jin raɗaɗi musamman a ƙasana tamkar zai zazzago haka na ke ji.Tun da Farida ta ɓata kullum sai nayi mafarkinta wai ta na cikin wata duniyar mutanen ɓoye"
"Kamar ya ta ɓata?"Sheera ta tambaya , ta goge hawaye tace "kiyi haƙuri na ɓoye maki Farida da Daddyn ki suke holewa shi ya shigar da ita ƙungiyar asiri,nima Alhaji Tambari ke faɗa min ashe shi ma ya na ciki shine ya ke son nima na shiga in kuma ba zan yarda ba to ba zan taɓa warkewa ba"



Tunda Maryam ta furta da Daddy Farida ke holewa kwanyar Sheera ta tafi hutun wucen gadi,wata irin tsanar su ce taji hakan yasa ta bar Maryam nan tsaye ta koma ciki.
Da Basheer ta ci karo kawai sai ta shige ƙirjinsa ta fasa kuka, Mamy wacce ke can zaune ta taso ta fara tambayar lafiya Cikin kuka Sheera tayi masu bayani,da sauri Basheer ya fito ya samu Maryam ɗin.





"Kin ga illar zina da kwaɗayin abun duniya ko?yanzu da kike da gida da mota miye amfanin su tunda ba ki da lafiyar da za ki morar su?" Basheer ya faɗa tare da tsayawa ya nisa kafin ya cigaba da cewa "zan taimaka maki na kai ki gun malamina zai yi maki ruƙiya bi'izinin Allah za ki samu sauƙi" godiya Maryam ta yi masa,sai da ya koma ciki ya shaida ma Mamy kafin ya kai Maryam can gidan malam Abba.






Dakyar BADIYA ta samu tayi kokowa da zuciyarta har aka samu hawan jinin ya sauka,sosai Mamy taji daɗin ganin ta warware Sheera dai na tsaye daga bakin ƙofa ta na kallonsu har Basheer ya dawo.
Takardar sallama likita ya basu suka je gida bayan ya baiwa BADIYA shawarar ta cire damuwa,sannan ta rinƙa controling fushin ta.


40days later

Cikin motar gida suka so shiryar tafiyar sai dai motar ba za ta ɗauke su ba hakan yasa suka shiga Bus.
Tun ƙarfe biyar na asubah mota ke gudu da su amman ba su kai ba sai wuraren tara na dare .
Su na sauka Inna ta kira Kawu Laminu,ashe tun tuni su na cikin gidan motar shi da dogarai kasancewar shi tun jiya ya zo garin Agadas ɗin.
Motoci ne na alfarma suka zo tarben su,bayan an gama loda kayansu suka shiga zuwa Masarauta.Zuciyar Mamy banda buga babu abinda ta ke yi,su na shiga cikin masarautar aka fara yin busa irin ta ƴaƴan sarauta tuni duk jinin jikinsu ya fara gudu musamman Basheer da har wani cicira ya ke tamkar wanda ya hau mazari.



Duk ahalin gidan a falo suka tarar da su,Sarki Basheer wanda tuni tsufa ya kama shi sosai na zaune kan kujera ya miƙe ƙafafunsa gefensa na dama uwar gida sarautar mata ce uwa ga Adams da kuma Hawas yayinda gefen hagunsa kuma amaryarsa ce uwar ƴaƴansa Ƴan mata guda shidda.
Bisa gwiwoyinta ta zube ta na wani irin kuka tamkar ranta zai fita,yayinda su kuma iyayenta ke murmurshin farin ciki dan su tun da Kawu Laminu ya kawo masu labarin ta suka yi nasu kukan.



Sarki ya buɗe hannuwansa ya na cewa "ku zo nan jikokina" Sheera tamkar jira ta ke ta ruga ta faɗa jikinsa ta na kuka yayinda Basheer yaje gun Mamie wacce ta tsufa ita ma sosai.
Inna da Badiya suka samu gu suka zauna suma su na sharar ƙwalla.
Kawu Laminu ne mai juriyar gabatar da kowa, Sarki ya karɓi BB Adams ya rungume ya na jin tamkar Ɗansa ne marigayi duk da dai kammaninsa ba su gushe ba tunda ga Basheer nan.



Masauki aka basu suka yi wanka kafin a gabatar masu da abinci,sun kuwa ci kafin a buɗe babin hira wacce ta soma da neman gafara da kuma godiya ga Ubangiji.
Sai da dare yayi sosai kafin sarki ya umarci kowa ya je masaukinsa, Sheera kamar za ta mutu jin sarki ya ware ma Basheer da BADIYA part guda.Ta zuntar baki ta nufi ɗakin Mamie wacce ta kasance Kakarta, Mamy kuma da Inna a ɗaki guda suka kwana.





Wasu hawayen takaici suka zubo daga idonta,Mamie ta girgiza kai tace "ba'a san ƴaƴan Sarauta da zazzafan kishi ba,saboda duk tsiyar ki dama sai an yi maki kishiya.In ba abun ki ba ina kika taɓa ganin Sarki ya zauna da mata ɗaya?gwara ma ki aro juriya dan kuwa bayan ke akwai wata"
Sheera ta kalleta da alamun mamaki,Mamie tace "eh na san komi Kawun ku duk ya fayyace mana tun zuwansa,yanzu haka tuni an tanadi abubuwan da za'a yi shagalin bikin ku sati mai zuwa "ta faɗa ta na miƙo ma Sheera wani kindirmun nono cikin kofi fari ƙal da shi,ba tace komi ba ta karɓa ta fara sha sai taji ashe hadda niƙaƙen cikwi a ciki ga wani goût na daban wanda ba ta san ko miye

Please Login or Register in order to submit comment