Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaban Lawan ya faɗi sai dai bai da zaɓi doli ya buɗa baki yace "gwara dai haukan amman ina son matata"
"Yayin gama recharge na Ƙarfin Iko direct nan za ka zo kayi tsaye ,wannan madubin zai yi scanning ɗin siffarka daga nan kuma sai ka fita" Lawan ya ƙura ido cikin mirror ɗin sai ya ga ashe Marlin ne ke magana.






Tsaye yayi mirror yayi scanning ɗin sa kafin ya fito,a zaune ya tarar da Sweety ta na soshe-soshe ta na wasar baki.Ya rumtse ido ya na jin wani irin raɗaɗi,Omar ya taɓe baki yace "tun yanzu kake da na sanin shiga ƙungiya?hum! Ka canza shawara "ya na gama faɗa yayi ficewar sa.
Ɓangaren BASHEER kuwa haka kawai yaji abokinsa ba daidai ya ke aikatawa ba,amman ya share ya shiga harakokin gabansa.



Bayan wasu watanni
Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Sheera da BASHEER,sai dai babu wanda ya sani iya su biyu ne ke yin kayarsu wacce har yanzu sun ƙi yarda kuma da soyayyar ce.Abu tamkar na mahaukata za su yi hira aure da masayar kalamai amman sai su ce kuma ba soyayya ba ce,duk da dai shi BASHEER wani sa'in ya kan ji zuciyarsa ta aminta da suna son junansu ne amman tsoron yadda iyayen Sheera za su ɗauki lamarin ya sa shi watsi da sha'anin sai yace kawai shaƙuwa ce.
Ɓangaren Mariya kam tun tuni suka rabu har ma ta bar gidan,ita kuwa Badiya sai rainon cikinta take wanda ya zo mata da muguwar sha'awa hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma BASHEER ba.



A shagwaɓe tace "to wai ya zan yi ?Allah wannan zafi na ke ji in ka na yi" Badiya ke faɗa kamar za ta yi kuka,ga ƙaton cikinta ɗan wata shidda ya turo.Basheer ya lumshe ido ya buɗe,sosai ya ke jin feeling bakinsa yayi nauyi bai ma iya yin magana.
"To bari na kwanta ki hau bisana"ya furta dakyar,ta waro ido kafin tace "to bari na gwada na gani,amman dan Allah kar ka zungure min Baby" duk da ya na a buƙace sosai bai hanasa darawa ba kafin ya taimaka mata ta zauna bisa erection ɗinsa.




"Washhh ! Allah har cikin hanjina ka ɗan fita kaɗan"Badiya ta kuma faɗa ta na mai ɗan yin zillo tayi sama, BASHEER ya riƙe cinyoyinta ya fara pompé daga ƙasa Badiya sai kukan da ta saba ta ke yi.






SHEERA POV.



Hawaye ne ke kwaranya a gefen idonta sai faman turo baki gaba take ta na jan ajiyar zuciya,hotunan BASHEER ta ke kallo wanda kusan rabin su duk ita tayi mashi su ba tare da ya sani ba.
Ta kuma goge ƙwalla ta ayyana a Zuciyarta "ya na can tare da matarsa ina jin haka a zuciyata, Allah ka tausaya min na rage kishi" zuwa can kuma ta ja tsuki tace "to wai miye ruwana ma tunda ba na son shi mtsw!In ya na so ma ya cire wutsiyar ya baiwa matar sa Ni ina ruwana"tayi maganar ta na hararen hotonsa.
"Miyasa ma na ke tunanin ka dube shi,ƙazami sai uwar suma a fuska kamar mahaukaci"tayi maganar ta na bugun screen ɗin wayarta ita a doli BASHEER ta daka.




Jummah da ke tsaye tun ɗazu a bayanta tayi gyaran murya,da sauri Sheera ta waigo tace "Jummahhh?ba kiyi barci ba har yanzu?"
Jummah tayi murmushi ta na mai zaunawa bakin bed tace "ta ya zan yi barci yarinyata ta faɗa tarkon soyayya?" Sheera tayi zaune ta na mai rungume pilow tace "Allah ban son shi kawai shaƙuwa ce haka shi ma ya ke damuna wai soyayya mu ke"
Kanta Jummah ta shafa nan Sheera taji wani abu tamkar shigar ruwa a cikin ƙarƙashin ƙasa,da sauri ta lumshe ido kafin ta buɗe su ta kalli Jummah.





"Na san da ina son shi amman ban iya auren shi kuma na san Daddy ma ba zai taɓa yarda na auri *ƊAN ACAƁA* ba"Sheera ta faɗi haka wanda zancen kuma har ƙasan zuciyarta ne.
Jummah tace "Daddyn ki zai shigo gobe,sai dai ina so kar ki saki ki nuna masa ki na son BASHEER.Ki aro jarumta ki rinƙa yi ma BASHEER wulaƙanci da kuma kallon ƙasƙantace a haka ne kawai Daddyn ki zai bar ki cikin kwanciyar hankali"
Shiru Sheera tayi ta na tunani haɗi da auna maganar Jummah sai dai sam ba ta fahimci komi ba,hakan kuma bai hanata cewa "to in shaa Allahu,amman dan Allah wai dagaske ina son Basheer ?" Jummah ta dungure mata kai tace "a'a sam ba ki son shi kin tsane shi mafarin ma kika saka hoton shi a gaba ki na kukan ya na can tare da matar shi" da sauri Sheera ta rufe ido saboda kunya.
Jummah na fita direct ɗakin Daddy ta shiga, system ɗin sa ta buɗe ta goge duk wata ɗauka da tayi washegari kuma ta ƙara komawa ɗakin Sheera ta cire Camera.


Yau ta kama Monday,tun safe ake gyaran gidan haɗi da yin girki kala-kala duk nau'in abincin da Daddy ya fi so.Mamy tuni an nemi excuse a wajen aiki, Sheera ta fito cikin shirin zuwa makaranta.Yau sanye ta ke da farar doguwar riga ta na ja har ƙasa,kanta kuma ɗan ƙaramin kallabi ne ɗaure wanda ya ɓoye sumar ta.
Lipton Jummah ta shiga haɗawa yayinda Sheera ke latsa wayarta ta na murmushi,saƙo ne ta tura ma Basheer wanda ya shaida mata tuni ya na ƙofar gida.
Ta na tsaka da shan shayi kiransa ya shigo "wai sai yaushe za ki bar raina Ni?ba ki ga text ɗina ba?"Basheer ke faɗa a zafafe, Sheera ta tuna huɗubar da Jummah tayi mata a daren jiya haka yasa ta ce bari ta gwada yi tun yanzu.
Cike da tsiwa tace "in ba dan ka na mahaukaci ba ta yaya zan maida saƙon da ban karanta ba?nace ka jira ni sakarai kawai mtws "ta kashe kiran kafin ta cigaba da shan tea Mamy ta dubeta tace "ke da waye?" "Wannan banzar abonné da kika ɗaukar min mana" Jummah kuwa farin ciki fal ranta.






Sai da SHEERA ta ɓata lokaci sosai sannan ta fita,zaune ta tarar da shi kan babu ya kife kansa kamar wani mai barci.
Ta taɓe baki ta ƙarasa ta haye babur ɗin,bai tashi ba balle ta sa ran zai tafi."Sheebar mu tafi mana"ta faɗa cikin sanyin murya a shagwaɓe kafin ta mitsili gefen cikinsa,sarai ya ji ta amman yayi banza da ita."Dan Allah dan Annabi mu tafi kar nayi lati"ta kuma faɗa,murya a dake yace "mashin ɗin mahaukaci za ki hau?"tayi shiru ta na tunanin abinda za tace kawai sai motar Daddy ta kunno kai a layin.



"Daddynaaaa"Sheera ta furta da ƙarfi wanda hakan yasa BASHEER ya ɗago kai,idonsa ya sauka cikin na Daddy wanda tuni ya fito daga mota.
Wani kallo mai cike da ma'anoni suke yiwa junansu ko ƙyaftawa babu ,yayinda Sheera ke zaune daram kan babur ta kasa sauka.
Daddy ya game fuska tayi baƙi ƙirin,kafin ya fara takawa inda suke.Wani gigitacen mari ya ɗauke Basheer da shi tare da nuna masa yatsa yace"kai waye da har za ka zo kusa da rayuwata?uban waye yace ka goya ta kan banzar mashin ɗin ka?"Daddy ya faɗa ya na cakumo wuyan Basheer.....
[09/08 à 11:15] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*




*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.





*W*



"Haba Daddy miye na ɓata min ranka akan wani banzar *ƊAN ACAƁA*? Please kayi haƙuri wuce mu shiga gida nayi missing naka,kar farin cikin da na ke ciki ya tafi" Sheera ta faɗa bayan ta sauka daga kan babur ɗin.
Ambatar kalmar banzan ɗan acaɓa ya fi komi yiwa Basheer ciwo fiye da yadda Daddy ya mare sa, Sheera ta harare sa tace "Miye kake wani kallon mutane sauka ka baiwa Daddy haƙuri" tamkar wani Ɗan ta haka Basheer yaji zuciyarsa ba za ta iya tsallake umarninta ba.
"Kayi haƙuri Alhaji Allah ƙara girma da ɗaukaka" shiru Daddy yayi ya na kallon Basheer sai ya hango zuciyarsa tsaf da ita ba ta da wani aibu ko kuma kwaɗayi hakan yasa ya murmusa yace "ok!"sai ya ja hannun Sheera zuwa ciki,ita kuwa waiwaye take baiwar Allah dan ganin wane hali Basheer ke ciki wata uwar harara ya banka mata ya na jan ƙyaci.






Mamy ta miƙe tsaye ta na kallon Daddy wanda yayi ƙiba abun sa ga wani irin haske da ya ƙara mai nuni da hankalin sa kwance.
"Wifer ko ba kiyi kewata ba ne na koma?"Daddy ya faɗa ya na ɗaga mata gira guda,shiru tayi kawai amman zuwan yanzu ta gama hasko waye Daddy zarginta ya ida tabbata.
"Daddy ka zama lukuti abun ka koko dai ba ka motsa jiki?" Sheera ta faɗa ta latsa ƙaton cikinsa.





Ya ja dogon hancinta yace "ke ma ga shi kin ƙara ƙiba miye sirrin?" Sheera tayi murmushi kawai, Jumma da ke fitowa daga kitchen tace "sirrin kwanciyar hankali ne kawai amman daga shi babu wani abu"
Cike da mamaki Daddy ya kalleta sai kuma gabansa ya faɗi hango wasu manyan-manyan Ƙarfin Iko a tattare da ita,a zuciya ya fara tunani "yaushe Jumma ta shiga ƙungiyar asiri ba tare da na sani ba?wace ƙungiya ce ta ke wacce ta bata ƙarfin iko har haka?" Muryar Jumma ta sake katse sa inda ta ke cewa "Alhaji an sha hanya amman alamu sun nuna kamar ba ka gaji ba kayi tsaye tun ɗazu"
"Jummah ki gabatar ma da Oga da abincinsa ni zan je na kwanta"cewar Mamy ta na mai nufar ɗakinta Daddy ya ƙara bin ta da kallon mamaki,wato ba ta ma damu da shi ba?



Sheera ce ta ja hannunsa zuwa tsakiyar salon ta fara yi masa surutu kamar kanya,shi kuwa saurarenta kawai ya ke amman hankalin sa bai tare da shi.
Jus kawai ya sha ya miƙe ya nufi ɗakinsa,wanka ya fara yi kafin ya buɗe drower sa ƙaton karensa mai suna RAM yayi ɓul ya fito ya na kaɗa bindi.Daddy ya saki wani murmushi "Barka da fitowa duniya a karo na biyu a rayuwar ka,yanzu kam za ka wataya cikin gari duk ina kake so.Za ka yi min maganin duk wani mugu da munafuki kar ka raga ma kowa duk wanda ya cuce ni ko da a ɓoye ne kai za ka ɗauki mataki ta hanyar cizonsa daga nan zan yi abinda ya kamata na janye masa sauran jinin jikinsa.Fatan za kayi haka domin ina son yin kuɗi fiye da kowa na duniya hhhh" Daddy ke faɗa ya na shafa kan baƙin 🐕 wanda tamkar ya na magana da mutum har gyaɗa kai ya ke ya na fiddo halshe alamun zai yi biyayya.
System ɗin sa ya kunna sai dai wayam babu komi,wani ƙululub baƙin ciki ya rufe sa so ya ke ya ga ta yaya aka yi Sheera ta samu lafiya tunda shugaba Marlin yace bai da hannu a ciki.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Jumma,ba ta wani jima ba ta shigo ɗakin fuskarta a murtuƙe.Kallonta yayi na wani ɗan lokaci kafin ya juya allon system ɗin gabanta yace "ya aka yi babu komi a ciki?" Cikin dakiya Jumma tace "ka tambayi system ɗin mana" Daddy ya waro ido sam bai yi tunanin abun Jumma ya kai haka ba na za ta iya gaya masa baƙar magana.




Dakewa yayi ya nuna kamar bai ji zafi ba ya ƙara tambayarta"kin taɓa ganin inda system tayi magana?" Ta fara wasa da yatsunta tace "mi zai hana in kuwa ta kasance ta matsafi ce?"tayi maganar ta na wurga masa idonta da suka rikiɗa suka yi wani irin ja tamkar garwashi.Sai da gaban Daddy ya faɗi amman da ya ke shi ma mugun gaske ne sai ya miƙe tsaye yace "zan ko tabbatar maki da Ni matsafi ne amman ki jira lokaci" "tabbarwa ta nawa kuma bayan ga baƙin kare nan ka aje a matsayin dodon tsafin ka?"
Gefen wuyansa ya shafa ya na wani juya kai kafin yace "fitar min daga ɗaki" ta taɓe baki tace "ko ba kace ba fita zan yi mtsw " zuciyar Daddy ta shiga bugawa da ƙarfi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito, RAM ya kalla wanda ke bin Jumma da ido, Daddy ya girgiza kai yace "a'a kar ka ɗauki matakin komi ta na da sauran amfani a gu na"ya na gama faɗa ya saka kaya ya nufi ɗakin Mamy.




A zaune ya tarar da ita kan sallaya ta na jan casbi,da mugun mamaki yace "sallar mi ce kike yi yanzu?"ba ta ko kalle sa ba balle yasa ran za ta amsa.Ya zauna kusa da ita ya ja ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta yace "kiyi haƙuri dan Allah ki bar wannan fushin"ta dubesa tace "fushi?fushi akan mi?saboda kai zan yi fushi?mutumen da ya tsallake Ƴar cikinsa ya tafi yawon shsƙatawa ba tare da ya tunanin wane halin iyalansa ke ciki?"kawai sai ta fashe da kuka ,Daddy ya rungumeta da sauri kuma ya janye jikinsa sakamakon wani abu girrr da ya ja sa tamkar lantarki.



Tashi yayi tsaye ya na kallonta,sai kuma ya fice ya na tafiya kamar wanda bai cikin nutsuwar sa.Ɗakinsa ya shiga ya ƙargame da key kafin yayi shigar jajayen kaya ya haɗe fuskarsa da farar hoda,sunayen manyan aljanu gami da wasu kalaman tsafi ya ke faman ambato.
Tamkar a Film haka shugaba Marlin ya bayyana a ɗakinsa tsaye a jikin madubi,fuska babu annuri Marlin yace "sanadin rungumar waccan banzar matar ta ka wacce ta mayar da ambaton Allah ruwan shan ta ga shi nan har hantar cikin ka na kaɗawa" Daddy ya dube sa yace "miye abun yi kenan?" Marlin yace "doli su nisanta da kai,haka na sake haramta masu dukiyar ka.Ka canza masu gida saboda zamanta a nan babban hatsari ne ,dan da zarar ka koma taɓa jikinta ƙila abun ya fi haka"



Daddy ya girgiza kai yace "a'a ba zan iya yin nisa da su ba saboda su ɗin rayuwata ne,amman zan kiyaye haɗa jiki da ita.Ya maganar Sheera ita wane lokaci ne kuka ƙa'ide min na karɓa budurcinta?"

Marlin yace "nan ba da jimawa ba dan na ga yarinya tamkar kanta ya fara rawa,in lokaci yayi zan faɗa ma" Daddy ya jinjina kai yace "akwai wani yaro da na gan su a tare Ƙarfin Ikona ya kasa tantance shi waye,kar yaje ya canza ma Sheera akala" Marlin yace "wai ka na nufin ta fara kula samari?ka na aikin mi?"yayi tambayar cikin ɗaga murya , Daddy yace "a'a ba saurayin ta ba ne juste abonné ɗin ta ne"
"Zan tafi na ga alamu ba ka da hankali ,ayi ma abu ka kasa ɗaukar mataki ita wannan Jumma sai yaushe za ka kawo min ita?" Daddy yace " sai nayi tunani" Marlin bai sake cewa komi ba ya ɓace ɓat.






A ɓangaren Sheera kuwa ɗakinta ta koma ta na ta jaraba kiran Basheer amman ya ƙi shiga ,da zarar ta fara ƙara sai a maido mata kiran.
Ta rasa mi ke yi mata daɗi,tashi tayi ta ɗauki ƴar ƙaramar bag ta fito.Babu kowa a falo hakan ya sa ta fita zuwa bakin titi, adaidaita ta tsayar tace a kaita bayan école Soura.Bayan ya kawota ta biya sa kuɗi,nan ta fara tambayar ina ne gidan Basheer *ƊAN ACAƁA* sai da ta sha wuya sosai kafin ta samu wani yaro ya kaita.



A tsakar gida ta ga babur ɗin BASHEER,tayi zaune a kansa kafin ta tura masa text.Kiransa ya shigo wayarta ta ɗaga ta na dariya "ka fito mana Allah gani a cikin gidanka bisa mashin ban san ina ne lungun ka ba" ya kashe kiran kafin ya fito.



Daga bakin ƙofa yayi tsaye ya na kallonta cike da mamakin yadda aka yi ta zo nan,ta miƙe tare da nufarsa ta na murmushi.Jikinsa ta faɗa ta na mai cewa "kayi haƙuri Sheebar"bugun zuciyarsa ne ya ƙaru yasa hannu zai cireta amman ta riƙe sa gam.A shagwaɓe ta kuma cewa "doli ce ta sa ni furta baƙaƙen lafuza a gare ka, amman dan Allah kayi haƙuri" ya kalli cikin idonta yace "to naji sake Ni"ta turo baki tace "dan kar matar ka ta gan mu?" "Ke da ba ki sona to miye na tambaya?"ta saki murmushi tace"ina sonka fa irin sosai ɗin nan" Badiya wacce barcin da ta fara bai gama game mata jiki ba,ta leƙo kenan taji wannan furuci da sauri tace "Innalillahi wa'inna iley raji'un"ta na mai kallon lalausan hannuwan Sheera wanda suka zagaye BASHEER ta baya.



Da sauri Basheer ya waigo ya na kallonta, Sheera ma sake sa tayi ta na ƙare ma Badiya kallo."Har kin tashi ne ?mi kike ji yanzu?"Basheer ya tambaya ya na nufar Badiya,ta ƙwace hannunta idonta na wani irin rufewa tsabar bala'i tace "Basheer har cikin gidan aurena?wannan karuwar fa?" "Uwar ki ce karuwa" Sheera ta faɗa daga can bakin ƙofa BASHEER ya harareta kafin ya rungume matar shi wacce ke ƙoƙarin tafiya ta shaƙo wuyan Sheera.




"Sake ni wlh sai na ci uwar ta ko ma ɗiyar uban wace ce,shegiya mai kama da kafirai" Badiya ta faɗa ta na son kubcewa daga riƙon da Basheer yayi mata.Sheera kuwa ido ta waro ta na kallon ƙaton cikin Badiya wani maƙoƙon baƙin ciki ne ya rufeta tuna wannan cikin fah na Basheer ne, wata zuciya ta ɗibi Sheera kawai sai ta kutso Basheer ya daka mata tsawa kawai sai ta fashe da kuka.
Ya sungumi Badiya ya kaita ɗaki "dan Allah ki zauna kar ki jajiɓo min aiki wannan yarinyar da kike gani ba daidai ta ke ba,dan Allah ki tsaya nan kar ki fita" Basheer yayi ta lalaɓa Badiya kafin ya dawo gun Sheera wacce sai gwanjin kuka ta ke.




"To sai ki wuce mu tafi tunda kin gama ni da matata"ya faɗa ya na hararenta kafin ya ja hannunta su fita,babur ɗin ya kunna Sheera ta hau za ta zagaye ƙugunsa yayi saurin dakatar da ita.
"Dallah Malama kar ki ƙanƙame ni nan ba ADS ba ce mu na fita yara za su iya bin mu da ihu" Sheera ta turo baki ta na mai gyara zama haɗi da goge hawayenta.



Basheer na tuƙi ya na satar kallonta har suka hau babban titin da zai sada ka da quartier ɗin su,ta kwanta bisa gadon bayan shi murya can ƙasa-ƙasa tace "Sheebar mu tafi Plaza akwai maganar da na ke son mu yi" yayi banza da ita ,ta zura hannunta na dama daidai cikinsa ta matsa tace "please kajiiii" Basheer ya ja wani uban burki ya tsaya kafin ya buge mata hannu yace "shine kuma sai kin min mugunta ko?"ta turo baki tace"to ba kai ne ka ƙi saurarena ba"ya banka mata harara yace "gayamin ina jin ki" ta saki baki "a nan kan titin za mu yi magana?" Basheer ya kunna babur ɗin shi ya na mai cewa "tunda ba za ki faɗa ba ke kika sani" da sauri kamar zubar ruwa tace "Daddyna na cikin ƙungiyar asiri"cak bugun zuciyarsa ya tsaya yayinda kwanyarsa ta shiga juyawa ta na son tuno masa tsohon mafarkinsa.






Ƙarƙashin wata bishiya ya nufa da su,ya na tsayawa Sheera ta sauka shi ma haka kafin ya tangale mashin.
"Zauna!"ya umarce ta ya na mai nuna mata moto,tayi zaune ta na kallonsa shi kuwa Basheer hannuwa ya harɗe ya na kallonta.
Sheera ta sunne kai tace "tun watannin baya da suka wuce na taɓa ganin Daddy a falo shi ɗaya zaune su na meeting da mutanen da idona suka kasa gani sai dai zantukansu kawai,Ni ba wannan ne ya ke bani tsoro ba yadda naji su na ambatar sunana"
"Miyasa ba ki gaya ma Mamyn ki ba?"
"Tunanina ne aka garwa da na wata lusarar dabba,sam na manta ko kaɗan wannan tunanin bai zuwar min sai yanzu.In na gaya ma Mamy za ta shiga damuwa kuma ban son matsala ta shiga tsakaninsu,ina son Daddyna sosai" Sheera ta faɗa ta na kuka, Basheer ya ja dogon numfashi kafin yace "babu abinda zai yi maki,yanzu ina son ki saka masa ido da farko ina son sanin plan ɗin sa game da ke kafin na san abun yi"
Sheera ta girgiza kai tace "ina jin tsoro sosai Sheebar,duk yadda kake tunanin Daddy to ya wuce nan har wani Mr ɗin mu ya kashe fa kawai dan yace ya na sona"


"Ke ya aka yi kika sani?"Basheer ya tambayeta,shiru tayi ta kasa yin magana dan kuwa ba ta sani ba kawai dai zancen taji a kwanyarta.Gashin kanta da ya rufe gefen fuskarta ya gyara ya na mai cewa "kalle ni cikin ido" Sheera ta zuba manyan idonta irin nasa cikin idonsa kafin ta fara motsi da baki "Sheebar Jumma...."sai kuma tayi shiru ,ya lumshe ido saboda abinda kwanyar sa tayi masa capté daga cikin memory Sheera.
"Tabbas Jumma ce take amfani da tunanin Sheera,wace ce ita?miye alaƙar su da ahalin?"duk a zuci yayi tambayoyin kafin ya buɗe idonsa.



Sheera kuwa zoben hannun Sheebar ta ƙura ma ido wanda ke fitar da wani haske,da sauri ta hannunta ta taɓa ta na cewa "Sheebar ina son wannan zoben" maganarta ce ta dawo da shi daga tunanin da ya ke.
Wani abun almara zoben hannun nasa ya rikiɗe ya koma na diamond sai ƙyalli ya ke, ƙoƙarin ciresa Sheera ta ke daga yatsansa shi kuwa sam hankalinsa ya fara fita daga gare sa har ta zare zoben ta saka sa a nata yatsan.
Tamkar yadda ruwa ke kashe wuta haka Sheera ta fara jin sauyi a jikinta wani tururi na fita daga ƙofofin hancinta,da sauri ta rungume BASHEER sakamakon wani irin sanyi da take ji.
Kasancewar unguwar ƴan bariki sam hakan bai wani damu mutane ba,hadari ne ya fara gangamuwa yayinda giza-gizai suka shiga gudu ruwan sama suka fara sauka.
Sheera ta fara sauke ajiyar zuciya ta na jin saukar ruwan tamkar ruwan zafi ne,sanyi da jikinta yayi a sannu ya fara fita.
Ruwa duk ya jiƙa su a haka Basheer ya goya ta ya kai ta gidan su, cike da nishaɗi ta shiga gida .
Wani uban ihu tayi ganin baƙin kare ya dirfafo ya nufo ta ya na habshi, Sheera ta ƙwala ƙara tare da faɗuwa ƙasa RAM ya rugo kenan zai cijeta wani haske ya fito daga zoben Sheera ya masa wani ƙulli cak ya tsaya daidai nan Daddy ya fito wanda dama bai jima da fiddo 🐕 ba a waje tsakar gida sai kuma ya ji kukansa.





Mamy da Jumma duk suma sun fito, Daddy ya ɗaga Sheera ya na tambayarta in ba taji ciwo ba.Da sauri ta shiga jikinsa ta na mai cigaba da kukanta,Mamy kuwa mafarkin da ta taɓa yi ya faɗo mata a rai.Da sauri ta ƙaraso ta na cewa "Daddyn Sheera ina kuma aka samu wannan baƙin Karen?gaskiya a fitar da shi" Daddy ya kalli RAM wanda ke fiddo halshe ya na son cizon Sheera wanda hakan ya tabbatarwa ma Daddy cewa lalle akwai laifin da Sheerar ta aikata.
Da sauri ya saki Sheera ya je ya Ram ya mayar da shi cikin kejin sa,kamar almara haka Ram ke yiwa Daddy magana a zahiri habshi ya ke amman abaɗini jawabi ya ke "Sheera ta sanar ma wani da sirrin ka amman ban san miye tace ba haka na kasa tantance ko waye" hankali tashe Daddy ya nufi cikin ɗaki ko kallon Sheera bai yi ba wacce Jumma da Mamy ke aikin rarrashinta.




"Ba ka da hankali AlGabid,har sai yaushe ne za ka gane cewa zaman iyalan ka cikin gidanka za su kawo ma matsala?ita wannan matar ta ka ina so ka koreta ta bar gidan ka duk wata matsa da kake ganin ta na tasowa daga ƙugunta ne.Budurcin Sheera kuma ina son ka karɓe min shi nan da sati mai zuwa,in mun je meeting zan gaya ma wajen da za ka kaita domin kwantawa da ita" shugaba Marlin ke magana ya juya ma Daddy baya.
Hankalin Daddy in yayi dubu to ya tashi "waye ta faɗa ma sirrina?" Daddy ya tambaya "ka nemo da kan ka wannan ba matsala ta ba ce!Sannan ka sani tuni kujerar muƙamin ka ta fara rawa hakan na nuni daf kake da rasata.Budurcin Sheera shine sacrifice na ƙarshe da za ka kawo,rashin kawo sa kuma ya na daidai da fitar numfashin ka" Marlin ke faɗa fuskarsa a murtuƙe.



Daddy yace "na sani shugaba,kawo budurcin Sheera shine abu ma fi sauƙi a rayuwata tunda da wannan burin na ke kwana na ke tashi.Zan nemawa ita mahaifiyarta ta wani gidan,amman ba zan iya nisanta Sheera daga gare ni ba za ta zauna nan ita da Jumma"
Marlin yace "in kayi hakan da ka taimaki kan ka"ya

Please Login or Register in order to submit comment