Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai surutu a duniya wanda ya mayar da bakinsa tamkar rariya,da ace ka riƙe wannan zancen a zuciyar ka da ba ka jawo ma kan ka mutuwa ba"ya na gama faɗa ya yanki wuyan Kader tuni maƙogoran sa ya fara fitar da jini.
Kader ya riƙe maƙogoron sa ya fara magana dakyar "ka kashe ni amman ka sani mutuwata ita ce farkon rugujewar ƙungiyar ASOMA ta dalilin ka za'a shafeta a jerin ƙungiyoyin duniyar matsafa.Ka sa a ran ka Baba tsoho ba zai taɓa barin ka ba, ƙungiyar BOULE MAGIQUE ita ce ƙungiyar da duk ta gagari kowa amman yau kai ka ci nasarar kashe mumber ta hhhh ina tausayin ka" Daddy ya luma masa wuƙa a ciki yace " in kun haɗe lahira sai ka baiwa shi shugaban naku labarin wa ya kashe ka" Kader ya bushe da dariya yace "ba za ka taɓa ganewa ba sai ranar da na rusa plan ɗin ka,Baba tsoho Aljani ne ba bil'adama ba babu buƙatar sai na gaya masa waye ya kashe ni ( masu son jin taƙaitacen Baba tsoho gami da ƙungiyar BOULE MAGIQUE ta nemi littafin ABINCIN WANI GUBAR WANI🤧)

Daddy ya dawo gida ya na jin har yanzu takaicinsa bai kau ba,hakan yasa ya kira shugan su ya shaida masa komi dangane da abinda yayi.
Wasu dokokin aka ƙara shimfiɗa masa wanda suka kusan saka sa hauka,shi ba wai luwaɗin ne ya ke ma jimame ba a'a yadda Demon ya zaɓi Jumma a matsayin wacce zai rinƙa tarawa da ita.
Ganin bai da mafita ya sa shi yin amfani da maganin barci ya na zuba ma Jumma,in tayi barci sai ya lalaɓa ya biya buƙatar sa wannan shine ya basa kariya game da farmakin da Baba tsoho ke sawa a kai masa.
Ɓangaren Jumma kuwa sam ta ka sa gane kanta,macen da ke zo mata a mafarki ma ta bar zuwa sosai hakan ke damun ta. Ana haka har cikin Mamy ya tsufa,dukkan kulawarta ya dawo kanta.



_____

A ɓangaren su Basheer kuwa tuni ya girma yanzu Masha Allah ya na cikin 6years,duk wata kalma babu wacce ba zai furta da kyau ba.Sosai ya ke samun kulawa wajen iyayensa,kullum cikin karatun Alkur'ani ya ke wanda hakan shine burin Adams wanda ya ke kira da Abba.
Fatima na zaune ta na wanke kwanoni sai Basheer ya shigo da gudu hannunsa riƙe da wata ƴar ƙaramar ball ta leda,abun ka da yaro hannunsa ya kubce ta faɗa cikin ruwan da Innar sa ke wanke kwanoni.Dundu tayi masa a baya tace "ban hana ka wasa da wannan ball ɗin ba ?" Basheer ya fashe da kuka ganin Inna ta jefa ball ɗin saman rumfa.Wani dundun ta sake yi masa a baya wanda tayi da na sanin yinsa,wani raɗaɗi taji ga hannunta kafin ayi yarɓi da ita can gefe bisa kwanoni.Ball ɗin ta faɗo da kanta daga bisa rumfa Basheer ya ɗauki kayarsa ya na goge hawaye, Inna kuwa banda sunan Allah babu abinda ta ke ambata.
Abba ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, Basheer ya nufe sa sai kuma yayi tsaye ya na kallon mahaifin nasa.
Abba ya jawo sa jikinsa yace "Basiru na lafiya kayi tsaya?" Inna da ta tashi ta na kwashe kwanonin tace "yauwa tunda Allah ya kawo ka ai shikenan,yanzu nan wani lamari ya faru da ni"nan ta kwashe komi ta shaida masa shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yace " bari mu kai sa gun Baba Malam to ni wannan lamari na Basiru na rasa kansa haka fa jiya ya ke bani labarin wani abu da ya taɓa faruwa kawai shiru ne nayi.."bai ƙarasa zancen ba wayar sa ta ɗau ringing ya na ɗagawa aka ce "an kawo wata mata ne haihu jini ya ƙi tsayawa kamar irin cas ɗin da ka taɓa réglé ne shiyasa mu ka kira ka"


Abba ya nufi waje hankali tashe ,Basheer zai bin sa Inna ta riƙe sa.Kuka ya fashe da shi ya na cewa "Abba kar kaje zai k..a s.he kaaaa "kasancewar cikin kuka ya ke maganar sam Inna ba ta fahimci abinda ya ke cewa ba.Ganin rigimar Basheer ta ƙi ƙarewa ya saka Inna rufe ɗaki ta ja sa zuwa gidan Baba Malam.



Abba ko kuma Adams na zuwa asibiti ya aje babur ɗinsa,tun daga nesa Jumma ta gane sa.Zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi,sai ta samu kanta da ɓoyewa ta na kallonsa ya na yiwa wata nurse bayanin yadda ake yi a tsayar da jini tare da mata alama ta tafi ta fara aikin ya na zuwa.

Ya fito waje dan nemo wani abu pharmacie suka yi kiciɓus da AlGabid,ƴar kallon-kallon suka fara kafin AlGabid ya nuna sa da ɗan yatsan sa manuni kawai sai Adams ya dafe saitin zuciyar sa ya na jin wata azaba.
Jumma da ke can laɓe tace "Adamssss!"tare da nufo sa da sauri,kasancewar duk an tafi sallah asibitin tsit ta ke AlGabid da sauri ya bar gun ya shiga can cikin asibitin sai kuma ya kirawo Jumma ta na kallon Adams dafe da zuciya ta bar sa nan.
Dakyar Adams ya ɗauki babur ɗin sa ya nufi gidan Baba Malam,saboda sarai ya san da tsafi ne AlGabid ya riƙe masa zuciya.




A can ciki nurse tayi nasarar tsayar da jinin a ƙarshe kuma aka cire mahaifar Mamy gaba ɗaya,jaririya sai kuka ta ke carawa.
An kai Mamy ɗakin hutu, Jumma ido sun yi mata jawur saboda kukan da tayi, shi kuwa AlGabid duk bai cikin nutsuwar sa hakan yasa ya baiwa Mamy damar zaɓar suna.Murmushi kan fuskar ta tace "tunda Allah bai sa na samu namijin ba a saka mata Busheera" haka kuwa nurse ta rubuta a takardar jaririyar.


Kafin AlGabid ya tafi sai da ya ɗaure bakin Jumma ta yadda ba za ta gaya ma Hawas abinda ya faru ba,cike da so ta ke kallon Baby wacce ke kama da ita sak sai idon da ke kama da na Adams irin na mage.Tayi murmushi ta shafi sumar kanta kafin ta fara tofe ta da addu'a,ta na mai jin kewar Yayanta sai dai babu yadda za ta yi.
Ba su ɗauki lokaci ba aka sallame su suka tafi gida,nan ne kawai Daddy ya ɗauki Babyn nan yaji duk duniya in akwai wacce ya ke so to sai dai ta biyo bayan Ɗiyar sa.
"Yanzu sabida Allah duk sunayen ƴan gayu ga su nan dayawa amman ki rasa wanda za ki zaɓa sai Busheera?hum!to ni dai da SHEERA zan rinƙa kiranta"Daddy ke faɗa,ita kuwa Mamy dariya kawai ta ke yi sam ba ta gaya masa ba saboda Sarki Basheer wato mahaifinta ta saka sunan ba.
Ahmad kuwa na ta aikin shafar gashin Sheera wanda ya ke da yawa sosai ga sulɓi,Jumma dai na gefe ta na ƙara auna rashin imani na Daddy da farko mamaki ya ke bata amman yanzu tsoro ne ƙarara danƙare ga ranta.




Gidan Baba Malam Basheer bai jima da yin barci ba,aka kira wayar Inna aka shaida mata Abba yayi accident.Ko da suka isa asibiti tuni rai yayi halin sa,haka aka yi masa wanka tare da kai sa gidan gaskiya ita kuwa Inna tun daga ranar ta yi watsi da wayarta.Basheer kuwa tuni an tura sa Maiduguri wajen karatu,a nan gidan kakaninta ta cigaba da zama har ta gama ta kaba.Duk mijin da ya fito mata sai ta ƙiya, lokacin da ta zo ma Laminu da maganar ta na son zuwa AGADAS ko dan ta kai Basheer gun dangin sa kawai sai ya ɗauke ƙafar sa ma.
Sosai Basheer ya maida hankali gun karatun sa,sai da ya kai 10year sannan aka maido sa ya fara karatun boko sai dai bai yi nisa ba ya tsaya saboda rashin kuɗi,Bala malam ma da ke taimaka masu shi ma ya tarda wa'adi.
Kuɗin da Adams ya bari su ne aka tattara suka sayi gida,nan Inna ta fara yin ƙananan sana'o'i Basheer na yi mata talla.



A wani yammaci na juma'a, Basheer ya dawo daga talla kamar yadda ya saba.Shigowar sa kenan kawai ya yanke jiki ya faɗi,idonsa suka yi sama ya na juya su cikin kuka Inna ta fara jijiga sa sai dai shiru.Adaidaita ta tsayar dan su je asibiti,tun kafin su isa Basheer ya dawo daidai tamkar ba shi ne ya faɗi ba.
Ta goge hawaye tace "Basiru mi kake ji" ya kalleta da idonsa da har yanzu ba su ida dawowa daidai ba yace "ban jin komi Inna ,ina ne za mu je?"mai adaidaita ya mayar da akalar tuƙin ya maido su gida a bisa hanya ne ya ke cewa "ina ga fah yaron nan farfaɗiya ce gare sa ba ciwon asibiti ba" Inna tace "yau ne kawai ya taɓa yin haka fah" "to Allah kyauta ya basa lafiya" Inna ta amsa da "amen"kafin ta ja hannun Basheer su shiga gida.
Wunin ranar haka tayi shi babu daɗi,sai dai ganin kamar Basheer ɗin na cikin walwalar shi ya saka ta ɗan ji sanyi.




Kwanaki na tafiya a haka Basheer kullum sai ya faɗi in an ɗauki kamar minti goma sai ya dawo daidai, wannan dalilin ya sa Inna ta fara neman masa magani.Alhamdullah ya ɗan samu sassauci kafin a sannu ya bar faɗuwa,hakan yasa ya koma Maiduguri da karatu duk wata Inna na yi masa aiken kuɗi da wasu abubuwan buƙata.
Ya na ɗan 15years ya sauke alƙur'ani mai girma,zuwa wannan lokaci duk wata halitta ta cikar girman namiji ta bayyana gare shi.
Ranar da ya zo ganin gida a ranar ya ƙara faɗuwa,hankalin Inna in yayi dubu to ya tashi.
Da bincike har ta samu labarin wani mai bayar da magani a ƙauyen LUKA,tsaf ta shirya ita da Basheer suka tafi.



Gidan akwai mutane sosai sai ka kama layi,Basheer ya zauna bisa wani banci can nesa da inda Inna ta zauna cikin wasu mata.


Wata ƴar yarinya ce ba za ta wuce 9years ba,amman a ido sai kace ƴar shekara biyar komi na ta irin na yara.An yi mata kitso dunƙule uku an saka mata duwatsu,da gudu ta nufo inda Basheer ke zaune jikinsa ta faɗa ta na waiwayen bayanta ganin Jumma ta biyo ta.
Basheer ya riƙeta ya na cewa "tsaya mana kin ga kar ki wahalar da Mama" kuka ta fashe da shi ta na ƙanƙame Basheer,Jumma ta ce "ɗan samari dan Allah taimako min to ka kawota daga ɗakin da za'a duba ta ne ta tsera ke,ita ce mu ka kawo ba ta lafiya" Basheer ya miƙe saɓe da Sheera wacce ke ta kuka sam ba ta son a kaita ɗakin da malamin ke duba mutane.
Su na shiga ɗakin kan Basheer ya sara da sauri ya dire Sheera ya na dafe kansa,Mamy dai na duƙe ta na kuka tun bayan da malam ya fara bayanin abinda ke tattare da Sheera.
Faɗuwar sa kawai suka ji, Jumma ta riƙe Sheera da kyau yayinda ita kuma Mamy ta fita waje."Innalillahi shi ma bai da lafiya ashe"cewar Jumma ta na mai danne Sheera malamin ya saka wani abu cikin bakinta ya na tatso wasu ruwa tsanwa sharrr,malam ya dubi yaronsa yace "je kayi ma wanda ya kawo yaron nan magana,na ga alama abubuwan sa su na da yawa baya ga aljanar da ke jikinsa akwai wani babban al'amari na tambari ƙungiyar tsafi " ambaton ƙungiyar tsafi ya saka Jumma cewa "wannan ɗan yaron shi zai shiga ƙungiya oh duniya ta zo ƙarshe" malam yace "a'a shi ai wannan ƙarya matsafi akwai ƁOYAYYEN SIRRI (MRS SADAUKI) game da shi ne,ki na ga ta dalilin ɗaukar yarinyar nan da yayi duk wata gubar da ke cikin jikinta ta na fitowa za ta samu sauƙi nan ɗan lokaci" Jumma ta waro ido "kace ɗan baiwa ne"ta faɗa ta na kallon fuskar Basheer wacce ke ɗauke da wani ƙato tabon ja wajen kumcin sa na hagu.
"Kar ki fitar da wannan sirrin saboda yin haka tamkar wasa da rayuwar ki ne,duk wani mutumen da yaji wani zancen ƙauyen LUKA to a nan ya ke barin sa balle na wannan yaro" Jumma tayi gum da bakinta,kafin ta shiga goge ma Sheera baki.Lokacin da za ta fita suka yi karo ita da Inna wacce yaron malam ya nemo,haƙuri suka baiwa juna kafin kowa ya fice.




Mamy ta taso da sauri ta karɓi Sheera ta na cewa "ya kike Babyta?"nan kuwa ta fara zuba kamar kanya saɓanin da can da ba ta fiya yin magana ba ko ma tayi ba za ka gane ba. Cike da murna Mamy ta ke cewa Jumma "dan Allah ko Daddyn Sheera ya zo kar ki taɓa gaya masa kin dai ji yadda malam yace" "ai ba zan faɗa masa ba har abada" a zuciya kuma Jumma cewa tayi "ai tuni ya sani mutumen da banbancin da Aljani ɗan kaɗan ne" haka dai suka nufo gida Jumma na ta tunanin Basheer wanda ba ta ma san sunan shi ba ,ko da suka isa gida sun tarar da Daddy zaune a falo amman bai tambaye su daga ina suke ba.Jumma kawai ya kalla irin za ki san wa kika ɓata ma plan,Sheera ta ruga jikin Daddyn ta tace "Daddy ina cakuleti na ko yau ma ka manta?" Zuciyarsa ta sake yin ƙuna jin maganar Sheera raɗam.
Ahmad da ke gefenta yace "wa ya cire maki ak..."sai kuma yayi shiru bai ida ba,tuna gidan daga shi sai Daddy kawai suke ƴan ƙungiyar asiri kuma sun san duk wani sirrin gidan.




A can ɓangaren Basheer kuwa sai da malam ya sha daga kafin Abrar ta fara yin magana,da farko tayi gardama na ba za ta fita ba a ƙarshe kuma ta karɓi kalmar shada ta zama musulma.
"Madalla da Abrar tunda har kika karɓi kalmar shahada,na san sosai Sarki Nurein zai yi alfahari da ke kin musulunta kin zama tsarkaka dan haka ki nisanta da bawan Allahn nan"
"In shaa Allah malam nayi ma alƙawarin ba zan sake dawowa jikinsa ba"cewar ABARAR kafin ta fita ta hanci,Basheer yayi atishewa sau uku kafin ya dawo hayyacinsa.Ruwan magani aka basa yayi wanka,sannan aka baiwa Inna sauran magungunan da zai rinƙa sha."Ki ƙara zage dantse game da Ɗan ki domin ya na tare da wata baiwa duk da ta kasance da lamarin asiri ciki amman akwai alkhairi ba zai taɓa cutuwa ba,ki ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen riƙo da addini su sannan yayiwa zuciyar sa ado da Tauhidi"
Inna tayi godiya suka dawo gida,sosai ta cigaba da baiwa Basheer kulawa.Shine Ɗan farin kuma Auta a gare ta wannan yasa suke gane ma juna,zai iya zaunawa su yi hira da ita ba tare da yaji kunyarta ba suna son junan su irin soyayyar Ɗa da uwa.Abu guda ne yanzu ke damun Inna shine ganin tun ba'a je ko ina ba Basheer na fama da sha'awa wannan lamari sam bai yi mata daɗi.Azumin litanin da Alhamis suka fara yi ita da shi hakan kuwa ba ƙaramin taimaka masa yayi ba,tuni ya fara sanin yadda zai mayar da dala ta koma dala biyu.




Ɓangaren DADDY kuwa tsaye ya ke tsakiyar wani Teku ya na wanka da jini,bayan ya gama yayi nutso cikin ruwan an ɗauki lokaci kafin ya fito.
Sam ko kaɗan sharaɗin da aka gindiya masa bai yi masa ba,ta yaya ma zai kawo jinin budurcin Ƴar sa?da hannu zai fasa farjinta ya zubar da jinin ko yaya?wani namijin zai baiwa contrat ? "Kaiii ba zai yiyuwa ba!da dai na bar wani ƙaton banza ya taɓa min SHEERA har na gwammaci in fasa ta da kaina na kawar da budurcinta"......






😟😟😟na gaji
[28/07 à 12:50] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*




*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.



*L*


Da gudu Sheera ta rungume Daddy wanda ke shigowa,ya ɗagata sama yace "babyna yau kin ƙara tsayi ko idona ne?"tayi dariya tace "Daddy Ya Ahmad ya sayo min icce cream yau,kuma yace gobe ma tare da ni zai tafi" fara'ar fuskar Daddy ta ɗauke yace "a'a Sheera ko yace ku je kar ki tafi kin ga ke mace ce bai kamata ki na yawo ba" da to kawai ta amsa kafin ta ja sa zuwa dining,dama kusan kullum shi ke bata abinci a baki.
Ahmad ɗan shekaru goma sha shidda a duniya amman ya ƙware a harakar tsafi,shi ke kula da duk wasu lamurran Daddy en secret ba tare da kowa ya sani ba.
Abinci Daddy ke baiwa Sheera ita kuma sai surutu ta ke yi masa, Ahmad ya shigo ya zauna hannunsa riƙe da wani document.
"Daddy ga komi na haɗa,abu guda ne yayi mana cikas shine..."sai kuma yayi shiru ganin Sheera na kallon shi, Daddy yace "kai min ɗakina zan duba zuwa dare,sannan ka zo ina son yin magana da kai" Ahmad ya miƙe ya je ya kai document ɗin ɗakin Daddy kafin ya dawo falo.



"Sheera yarinya ce sannan kuma mace ban so ka na fita da ita waje balle kuma wuraren da ka san akwai cakuɗanyar jinsi,daga makaranta sai makaranta kawai za ta rinƙa zuwa ko Islamiyya kar ta je can mahaifiyarta ta koyar da ita.Daga yau na baka ragamar kula da ita,ban son ƙawaye mata balle maza ita ɗaya na ke son tayi rayuwarta" Daddy ya faɗa cikin bayar da umarni,Ahmad kuwa sai gyaɗa kai alamun ya ɗauka.




Sheera na gama cin abinci Jumma tayi mata wanka ta shirya ta tsaf cikin riga da sket na turawa.Gashin kanta kuma ta raba sa gida biyu ta tubke,Sheera ta fito ta na matsar hawaye kafin ta ɗale cinyar Daddy wanda shi ma yayi wanka ya canza kaya.
"Wa ya taɓa min ke kike kuka?" Ya tambayeta ita kuma cikin kuka tace "Jumma ta yi min kitso" Daddy yayi dariya yace "ta dai dunƙule maki gashi ,Sheera ki bari a rinƙa yi maki kwalliyar ƴan mata mana ina so in gani " ta shige cikin ƙirjinsa tamkar mage ta na ajiyar zuciya.



"Ko mu je Naturex kiyi wasa?"ya tambaye ta,da sauri Sheera ta tashi daga jikinsa ta na dariya tace "Daddy ina zuwa kuma ina son 🎈"ya laƙace hancinta kafin ya miƙe ya na zirar makullin motar shi.



Daidai za su fita ita kuma Mamy ta dawo daga aiki,ta sauke glass ɗin motar ta sannan ta fara magana "Sheera ina za ku je haka?" Sheera wacce ta buɗe marfin mota tace "gidan wasar yara Naturex,gaya min mi kike so na sayo maki?" Mamy tayi dariya tace "duk abinda kika ci shi na ke so" ta rufe motar da sauri ba tare da ta amsa ma Mamyn ba.





Yara ne da iyayensu wasu kuma Yannunsu ta ko ina, Sheera sosai take nishaɗi ganin yara kamar ita su na wasa.Daddy na riƙe da hannunta,duk wani kalar wasa sai da ya kaita ta hau sai selfie ya ke yi mata cike da nishaɗi.
Brochettes suka ci ita da Daddy ta ɗauki tsinke biyu ta mayar da su gefe tace "wannan na Mamy ne " "ki ci kawai in za mu tafiya sai na saya mata wani"
Ta ɗauko tsinken biyu ta mayar, DADDY shi ke bata a baki ta na ci kamar dai yadda suke in su na gida.Lemun kwalba suka sha kafin ta miƙe tace "DADDY zan hau shillo kafin ka gama ci" kai ya gyaɗa mata.


Ta je za ta hau shillon kenan wani yaro ya rugo ya haye,ita kuma da taji haushi ta ture sa ya faɗi.Yaron ya fashe da kuka,uwar shi ta zo ta ɗauke Sheera da wani irin mari wanda ya saka ta ƙwala ƙara.Hankali tashe Daddy ya nufo gun,bai tsaya ɓata lokaci ba shi ma ya yiwa matar mari biyu masu zafi.Ya jawo Sheera jikinsa ya nuna matar yace "ki shiga hankalin ki da ki taɓa wannan yarinyar har gwara ki rinƙa yankar jikin ki da reza ,zan iya ɓatar da ke daga wannan duniyar banza kawai" uwar yaron banda zanzana babu abinda ta ke dan ita kaɗai ta san raɗaɗin da ya ratsa kumatun ta.




Gida suka dawo Sheera ta ƙi yin shiru duk rarrashin duniya babu wanda bai yi mata ba,Mamy ta rungumeta kafin ta fara na ta rarrashin.A haka barci ya ɗauke ta suka samu kan su, DADDY kuwa ran sa in yayi dubu to ya gama ɓacewa dakyar yayi controling kansa bai son ya na yawan kashe mutane.




A sannu a tashi Sheera ta fara zama ƴan mata,wata irin shaƙuwa ta shiga tsakaninta da mutanen gidan su musamman Daddy wanda wani sa'in a jikinsa ta ke yin barci.Ɓangaren Jumma kuwa har yanzu ba ta san DADDY na amfani da ita ba tunda sai tayi barci ya ke zo mata duk tsawon shekarun da aka ɗauka sannan ya juyar mata da tunanin da za ta gane hakan.Ahmad kuwa yanzu har meeting ya ke zuwa a matsayin sa na magajin DADDY,tuni sun je sun sauke farali dukkan ahalin.



Cike da zumuɗi Sheera ta nufi step ɗin sabon gidan su wanda DADDY ya gina,yau ne suka tare babu abinda babu cikin gidan.
Ta rungume Daddy tace "yanzun nan part ɗina ne a sama waiiii am happy DADDY muaaah"tayi masa kiss a kumatu,yadda kawai ta ke farin ciki shi ya haifarwa Daddy jin sha'awata na bijiro masa wacce kusan kullum da ita ya ke kwana ya ke tashi.Sheera yanzu ta na cikin 18years duk wata kamala ta mace ta bayyana gare ta,sam ba su shiri da kayan atamfa kullum ta na cikin jeans ko kuma robe .Harakar boko tun daga nan har Faransa za ta iya zuwa sai dai karatun addini Fatiha ma dakyar ta ke kawota daidai.




Ahmad ya shagala sosai wajen kallon Sheera musamman ƙirjinta,wani raɗaɗi mai yaji ya farmaki idonsa na tsawon second biyar kafin su dawo daidai.A tsorace ya ke kallon DADDY kafin ya sunne kansa, Allah na gani wani irin MAHAUKACIN SO (MRS SADAUKI) ya ke yiwa Sheera sosai ya ke sonta da aure tun bayan da ya gane Jumma ce mahaifiyar sa ba Mamy ba.
"Ka cire wannan banzan tunanin a ranka ko innuwar Sheera ba za ka samu ba balle jikinta"Daddy ya faɗa ya na mai matsowa daf da Ahmad,da sauri ya ɗago ya na kallon Daddy zuciyar sa na bugawa da ƙarfi.Ta yaya ma zai iya haƙura da Sheera alhalin ya na yi mata son da bai yi ma kansa ma?



"Daddy ka saya min mota nima na gaji da sai Ya Ahmad ya kai ni makaranta"Sheera ta faɗa ta na mai riƙo hannun Daddy,ya sakar mata murmushi yace "ok babu damuwa zan sa a koya maki in kin iya sai a kawo maki ta ki motar,gayamin wace kala kike so?" Tayi shiru can tace "na fi son baƙa mai baƙin gilashi"ya mirza yatsunta yace "duk yadda kike so haka za'a yi princesse"tayi tsalle ta na ihu.Mamy ta girgiza kai tace "ke kam Allah kawo min lokacin da za kiyi aure na san za ki daina wannan shirmen da zarar kin fara yin Ƴaƴa" Sheera ta ɓata fuska tace "Ni kam ko nayi aure ba zan daina ba tunda a nan gidan za mu zauna kullum in rinƙa ganin Daddyna " Jumma tayi dariya tace "ai kuwa dai sai in Ahmad ne mijin...amm kuma babu aure tsakanin ku ashe"da sauri Mamy ta kalleta tace "Ni kam Jumma dan Allah ki ban labarin ki ke da baban Ahmad" Jumma ta tashi ta bar gun,Ɗanta ya take mata baya dan shi ma ya na son sanin waye mahaifin shi.





"Daddy ina za ka je?"Sheera ta tambaye sa ganin zai fita,ya shafi ƙasumbar sa yace "zan je a yi min aski ne na tara gashi dayawa" ta ɓata rai tace "Ni kam ka fi yi min kyau in ka na a haka please ka bar sa" Mamy da ke can gefe tace "Sheera wuce ki canza kaya ki zo mu yi karatu wannan shirmen na ki ba zai taɓa ƙarewa ba,bari in kin yi aure sai kice mijin ki ya bari" tayi dariya dimple ɗinta ya lotsa tace "mijina ɗan gaye ne,ya na da tsayi sosai da faɗin ƙirji kamar Singam sannan ya na da yawan surutu kamar Ni dai.Kullum a shagwaɓe ya ke ,fuskar sa ɗauke da murmushi sajen sa...." Tsawar da Daddy ya daka mata ne yasa ta yin shiru ta na turo baki kafin ta fashe da kuka.Da gudu ta nufi step, Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya na jin wani abu ya shaƙe masa wuya.Take mata baya yayi,a kan gado ya tarar da ita ta na kuka.Ya ƙarasa ya zauna ya na dadaɓa bayanta,tayi lamo ta bar kukan shi kuwa Daddy juyar da idonsa

Please Login or Register in order to submit comment