Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke.




"To sai ki wuce mu tafi tunda kin gama ni da matata"ya faɗa ya na hararenta kafin ya ja hannunta su fita,babur ɗin ya kunna Sheera ta hau za ta zagaye ƙugunsa yayi saurin dakatar da ita.
"Dallah Malama kar ki ƙanƙame ni nan ba ADS ba ce mu na fita yara za su iya bin mu da ihu" Sheera ta turo baki ta na mai gyara zama haɗi da goge hawayenta.



Basheer na tuƙi ya na satar kallonta har suka hau babban titin da zai sada ka da quartier ɗin su,ta kwanta bisa gadon bayan shi murya can ƙasa-ƙasa tace "Sheebar mu tafi Plaza akwai maganar da na ke son mu yi" yayi banza da ita ,ta zura hannunta na dama daidai cikinsa ta matsa tace "please kajiiii" Basheer ya ja wani uban burki ya tsaya kafin ya buge mata hannu yace "shine kuma sai kin min mugunta ko?"ta turo baki tace"to ba kai ne ka ƙi saurarena ba"ya banka mata harara yace "gayamin ina jin ki" ta saki baki "a nan kan titin za mu yi magana?" Basheer ya kunna babur ɗin shi ya na mai cewa "tunda ba za ki faɗa ba ke kika sani" da sauri kamar zubar ruwa tace "Daddyna na cikin ƙungiyar asiri"cak bugun zuciyarsa ya tsaya yayinda kwanyarsa ta shiga juyawa ta na son tuno masa tsohon mafarkinsa.






Ƙarƙashin wata bishiya ya nufa da su,ya na tsayawa Sheera ta sauka shi ma haka kafin ya tangale mashin.
"Zauna!"ya umarce ta ya na mai nuna mata moto,tayi zaune ta na kallonsa shi kuwa Basheer hannuwa ya harɗe ya na kallonta.
Sheera ta sunne kai tace "tun watannin baya da suka wuce na taɓa ganin Daddy a falo shi ɗaya zaune su na meeting da mutanen da idona suka kasa gani sai dai zantukansu kawai,Ni ba wannan ne ya ke bani tsoro ba yadda naji su na ambatar sunana"
"Miyasa ba ki gaya ma Mamyn ki ba?"
"Tunanina ne aka garwa da na wata lusarar dabba,sam na manta ko kaɗan wannan tunanin bai zuwar min sai yanzu.In na gaya ma Mamy za ta shiga damuwa kuma ban son matsala ta shiga tsakaninsu,ina son Daddyna sosai" Sheera ta faɗa ta na kuka, Basheer ya ja dogon numfashi kafin yace "babu abinda zai yi maki,yanzu ina son ki saka masa ido da farko ina son sanin plan ɗin sa game da ke kafin na san abun yi"
Sheera ta girgiza kai tace "ina jin tsoro sosai Sheebar,duk yadda kake tunanin Daddy to ya wuce nan har wani Mr ɗin mu ya kashe fa kawai dan yace ya na sona"


"Ke ya aka yi kika sani?"Basheer ya tambayeta,shiru tayi ta kasa yin magana dan kuwa ba ta sani ba kawai dai zancen taji a kwanyarta.Gashin kanta da ya rufe gefen fuskarta ya gyara ya na mai cewa "kalle ni cikin ido" Sheera ta zuba manyan idonta irin nasa cikin idonsa kafin ta fara motsi da baki "Sheebar Jumma...."sai kuma tayi shiru ,ya lumshe ido saboda abinda kwanyar sa tayi masa capté daga cikin memory Sheera.
"Tabbas Jumma ce take amfani da tunanin Sheera,wace ce ita?miye alaƙar su da ahalin?"duk a zuci yayi tambayoyin kafin ya buɗe idonsa.



Sheera kuwa zoben hannun Sheebar ta ƙura ma ido wanda ke fitar da wani haske,da sauri ta hannunta ta taɓa ta na cewa "Sheebar ina son wannan zoben" maganarta ce ta dawo da shi daga tunanin da ya ke.
Wani abun almara zoben hannun nasa ya rikiɗe ya koma na diamond sai ƙyalli ya ke, ƙoƙarin ciresa Sheera ta ke daga yatsansa shi kuwa sam hankalinsa ya fara fita daga gare sa har ta zare zoben ta saka sa a nata yatsan.
Tamkar yadda ruwa ke kashe wuta haka Sheera ta fara jin sauyi a jikinta wani tururi na fita daga ƙofofin hancinta,da sauri ta rungume BASHEER sakamakon wani irin sanyi da take ji.
Kasancewar unguwar ƴan bariki sam hakan bai wani damu mutane ba,hadari ne ya fara gangamuwa yayinda giza-gizai suka shiga gudu ruwan sama suka fara sauka.
Sheera ta fara sauke ajiyar zuciya ta na jin saukar ruwan tamkar ruwan zafi ne,sanyi da jikinta yayi a sannu ya fara fita.
Ruwa duk ya jiƙa su a haka Basheer ya goya ta ya kai ta gidan su, cike da nishaɗi ta shiga gida .
Wani uban ihu tayi ganin baƙin kare ya dirfafo ya nufo ta ya na habshi, Sheera ta ƙwala ƙara tare da faɗuwa ƙasa RAM ya rugo kenan zai cijeta wani haske ya fito daga zoben Sheera ya masa wani ƙulli cak ya tsaya daidai nan Daddy ya fito wanda dama bai jima da fiddo 🐕 ba a waje tsakar gida sai kuma ya ji kukansa.





Mamy da Jumma duk suma sun fito, Daddy ya ɗaga Sheera ya na tambayarta in ba taji ciwo ba.Da sauri ta shiga jikinsa ta na mai cigaba da kukanta,Mamy kuwa mafarkin da ta taɓa yi ya faɗo mata a rai.Da sauri ta ƙaraso ta na cewa "Daddyn Sheera ina kuma aka samu wannan baƙin Karen?gaskiya a fitar da shi" Daddy ya kalli RAM wanda ke fiddo halshe ya na son cizon Sheera wanda hakan ya tabbatarwa ma Daddy cewa lalle akwai laifin da Sheerar ta aikata.
Da sauri ya saki Sheera ya je ya Ram ya mayar da shi cikin kejin sa,kamar almara haka Ram ke yiwa Daddy magana a zahiri habshi ya ke amman abaɗini jawabi ya ke "Sheera ta sanar ma wani da sirrin ka amman ban san miye tace ba haka na kasa tantance ko waye" hankali tashe Daddy ya nufi cikin ɗaki ko kallon Sheera bai yi ba wacce Jumma da Mamy ke aikin rarrashinta.




"Ba ka da hankali AlGabid,har sai yaushe ne za ka gane cewa zaman iyalan ka cikin gidanka za su kawo ma matsala?ita wannan matar ta ka ina so ka koreta ta bar gidan ka duk wata matsa da kake ganin ta na tasowa daga ƙugunta ne.Budurcin Sheera kuma ina son ka karɓe min shi nan da sati mai zuwa,in mun je meeting zan gaya ma wajen da za ka kaita domin kwantawa da ita" shugaba Marlin ke magana ya juya ma Daddy baya.
Hankalin Daddy in yayi dubu to ya tashi "waye ta faɗa ma sirrina?" Daddy ya tambaya "ka nemo da kan ka wannan ba matsala ta ba ce!Sannan ka sani tuni kujerar muƙamin ka ta fara rawa hakan na nuni daf kake da rasata.Budurcin Sheera shine sacrifice na ƙarshe da za ka kawo,rashin kawo sa kuma ya na daidai da fitar numfashin ka" Marlin ke faɗa fuskarsa a murtuƙe.



Daddy yace "na sani shugaba,kawo budurcin Sheera shine abu ma fi sauƙi a rayuwata tunda da wannan burin na ke kwana na ke tashi.Zan nemawa ita mahaifiyarta ta wani gidan,amman ba zan iya nisanta Sheera daga gare ni ba za ta zauna nan ita da Jumma"
Marlin yace "in kayi hakan da ka taimaki kan ka"ya ɓacewa ganin Daddy tamkar wani hayaƙi.








FARIDA POV.


Sosai ta zo da maƙudan kuɗi wanda ita kanta ba ta san iyakar su ba,déjà ta buɗe compte bancaire can ta zuba dukkan kuɗin da Daddy ya bata.
Ranar da ta dawo dakyar Maryam ta gane ta,ihun murna suka fara kafin su zauna su fara hirar yaushe gamo.
"Yanzu nan dagaske ke ce Farida?kin ga yadda kika koma fatar jikin ki sai wani sheƙi? Gaya min wace irin rayuwa kuka yi ke da alhajin ki?" Maryam ta faɗa ta na gyara zama,Farida tayi dariya tace "dan Allah ƙawata ki bari har gobe duk zan gaya maki komi yanzu dai wanka zan shiga in na ci abinci ki raka ni na sayo mota" Maryam ta waro ido tace"har da mota za ki saya waiiii! Kice dai za mu zaga gari sannan mu ci mai kyau ?"


"Eh duk abinda mu ke so za mu yi a yanzu tunda ina da isassun kuɗi,ke dai bari nayi wanka"Farida ta faɗa ta na shiga toilet.Bayan ta gama wanka ne ta fito "wai Ni kama ya Ameee Ɗan gouverneur har yanzu ya na nan da ɗaukar kai?"
Maryam tace"hum!ai ki bari wulaƙanci sai ma abun da yayi gaba"
"Wlh ƙawata ina mugun son gayen nan,ban san ya zan yi ba" Maryam ta marairaice fuska tace "nima bayan tafiyar ki na faɗa son Yayan Sheera Allah kamar nayi hauka"
"Dama Sheera ta na da wani magaji ne?shine kuma AlGabid bai taɓa yi min hirar shi ba?"
"Waye kuma AlGabid?"Maryam ta tambaya
"Baban Sheera mana"Farida ta ba ta amsa , Maryam tace "kar dai ki ce min shine ya ja ki zuwa Dubai" Farida ta ɗaga gira tace"eh ko da matsala ne?" Maryam ta girgiza tace "sam hakan bai dace ba!Kuma in Sheera sani ba za taji daɗi ba"
"Sai in ke za ki faɗa mata kuwa"daga nan ba su ce komi ba har Farida ta gama shiryawa suka fita cikin motar Maryam.




Macijin cikinta ne ya fara yi mata yawo ya na yi mata tuni akan lalle yunwa ya ke ji,Farida ta ja tsuki tace "dan Allah ki canza akala mu fara zuwa gidan cin abinci kafin mu tafi sayen motar" Maryam tayi dariya ta canza alakalar kamar yadda ta buƙata ta na mai cewa "ke wannan duk ranar da kika samu ciki an shiga uku,lokacin da kika shigo fa da ledar abinci a hannunki ki na ci kuma yanzu har kin ji yunwa" Farida kasa cewa tayi komi saboda cikinta ke faman ƙugi.
Ko da suka isa gidan cin abinci da sauri ta masu oder abincin mutum biyar,Maryam da ɗaya ita kuma huɗu.
Maryam sai kallonta ta ke cike da mamaki yadda har ta canye plat biyu ta fasa ta uku,su na nan zaune Alhaji Tambari ya zo a bazata ya ja kujera ya zauna ya na shirin magana idonsa ya sauka kan macijin Farida....
[10/08 à 14:39] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*




*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.





*X*



Bai ce komi ba sai ɗan satar kallonta da ya ke yi ya na mamakin yaushe kuma ta shiga ƙungiyar asiri?
"Ka tuna ta kuwa?ƙawata wannan wacce ka tarar da ita a hotel?"Maryam ta tambayi Alhaji Tambari ganin kamar ya na yiwa Farida kallon ƙasa-ƙasa ita a tunanin ko bai gane Faridar ba ne.
Ya murmusa yace "na shaida ta!" "Yauwa! Ta na son sayen mota ne shine za mu je in mun gama cin abinci" cewar Maryam, Alhaji Tambari yace "ta gayi irin wacce ta ke so sai ta bani congilar kawo mata ita"


Farida wacce ke ta fafutukar cin abinci ta dube sa ,karon farko da ta sa baki cikin hirar "irin ƙatuwar nan na ke so mai taya baya,fara mai baƙaƙen madubai"
"An gama ba ki da matsala in kin shirya saya sai ki min magana sati mai zuwa ana kawo maki ita"
Farida ta siɗe yatsunta tace "ko a yau in zai yiyu a shirye na ke" Alhaji Tambari ya ciro wayar sa daga aljihu ya nuna mata hotunan motoci kala-kala,nan Farida ta ruɗe ta rasa wacce za ta ɗauka duk da can farko ta na da chooce .
"Ina ma ace duk a bani su wlh duk sun yi min"ta faɗa cikin dariya, Maryam ta karɓi wayar tace "RAV4 ɗin nan dai duk ta fi su kyau kawai ki ɗauketa,in kuma ki na da ra'ayin ƙari sai ki sayi ƴar ƙarama kamar tawa"



Sai da Farida ta sha kwalbar exotic guda biyu manya-manyan sannan tayi gyatsa tace "wai Allah!Yanzu kam garas na ke za mu iya yin cinakin cikin nutsuwa" Maryam ta kece da dariya tace "ai kuwa ke wannan zuwan ki Dubai bai ƙara maki komi ba sai uban cin abinci tamkar wata mai ciki"
Alhaji Tambari kuwa macijin da ke cikin Farida ya kuma kallo wanda ke faman lumshe ido alamun ya ƙoshi.
"Ai ba sai mun yi cinaki ba kawai ƙarshen prix ɗin su zan gaya maki"ya faɗa ya na mai tashi tsaye,suma duk suka miƙe bayan Farida ta wanke hannunta kasancewar ba ta ci da cokali ba.



Alhaji ya shiga motar shi yayinda su kuma suka shiga ta Maryam,makarantar suka tafi.
Tun a bakin ƙofa ta hango Ameer sanyi idonta,wani farin ciki ne ya luluɓe ta da sauri ta buɗe portière ta nufi gun sa.
"Ameerrrr!ta faɗa tare da rungumesa alamun gaisuwa,ƙamshin dadaɗan turarenta ya kaiwa hancinsa farmaki kafin ya ida tantance wace ce ta kuma cewa "ya karatu ana tayi ko?Ni kam sai nayi rattraper dan yau na sauka daga Vol" kallon tsaf yayi mata kafin ya shaidata sosai ta canza tayi kyau ta zama sexy lady.



Dogon gashin dokin kanta ya ja kafin ya shafi gefen kumatunta yace "oh Baby kin kyau sosai fah!kenan voyage kika yi?" Cikin yanga tace "Dubai na je wlh! Ya ne ina Fuddal?"
"Sun tafi Buzu City shi da wata budurwar sa amman na san ba za su jima ba "ya bata amsa ya na kallon sauran abokansa huɗu wanda suke tsaye tare da shi.
Yadda yayi masu alama da ido yasa suka sulale suka bar su,Maryam ta ƙaraso murmushi kan fuskarta.Cike da girmamawa suka gaisa da Ameer kafin yace "Ni kam yau Sheera ba za ta zo ba ne ko miye?" Maryam tace "to ban sani ba dai!Amman kusan haka ne tunda yau Daddyn ta ya dawo daga voyage"



Farida tayi kicin-kicin da rai idonta ya ɗauki wani launi suna haɗa ido da Ameer haske ya fito daga idonta suka shiga nashi,ba ta san ya aka yi tayi haka ba amman tabbas taji lokacin da cikinta ke juyawa yayinda wani abu ya fara yi mata yawo a maƙoshi.



"Nace ko za mu je shan cream ?"Ameer ya faɗa cike da kulawa, Farida ta lumshe ido Maryam tayi mata dundu a baya tace "ke wai miye?ya na tambayar ki amman ki na wani lumshe ido dan iskanci?to ni kin ga tafiyata in kun dawo ki isko ni classe"


Sosai Ameer ya ji daɗin tafiyar Maryam ɗin,iskan bakinsa ya busa ma Farida a ido ta saki murmushi ta na mai buɗe su."Mu je motata na can parking spécial"ya faɗa ya na jan hannunta, wata aniyar mota ce ɓaka wuluk Ameer ya fitar cikin jerin motocin.
Wani ƙayatacen gidan shaƙatawa suka nufa,tamkar wasu tsofin masoya haka suke hira cike da burgewa.Kayan shiga piscine ya saya masu,Farida ta girgiza kai tace "ban taɓa shiga piscine ba ina jin tsoro" Ameer ya waro ido yace "kin je Dubai shine ba ki shiga piscine ba?" Ta turo baki tace "bai burge ni ne shiyasa,amman in baignoire ne zan shiga" Ameer yayi dariya yace "mu je na koya maki shiga ɗin dan ba zan auri baƙauya ba" kalmar aure da Farida taji ya ambata ya sakata ruɗewa,da sauri tace "mi kace?aure ko mi?"
Cikin jaddadawa Ameer yace "Yes!Rida wani son ki naji ya shige ni kai tsaye ba tare da na shirya ba,ke ban masa ya haka ta faru da ni ba.Please kar ki kuje ni kin ji?"yayi maganar ya na matsowa daf da ita har suna jin bugun zuciyoyin juna musamman ta fari wacce ke dakan tara-tara.



Ganin ba za tayi magana ba yasa Ameer jan hannunta zuwa ɗan ƙaramin ɗakin da ake sauya kaya,même pas 5mn suka fito cikin shigar ƙananun kaya tamkar wasu turawa.
A tsorace ta shiga ruwan duk da Ameer na riƙe da ita,daga bayanta ya tsaya ya rungumota hannuwansa zagaye da ƙugunta yayinda ita kuma ta kwanto da kanta a ƙirjinsa.



A sannu ya ɗan nutsa da su cikin ruwan kafin ya jata zuwa inda babu zurfi sosai,cike da nishaɗi ta juyo suna fuskantar juna.Leɓanta na ƙasa ya kamo a hankali ya tura halshensa cikin bakinta kafin ta fara shan yawunta,Farida ta riƙe sa da kyau ta na jin wani daɗi wanda ba ta taɓa jin kwatankwacin sa ba a duk tsawon lokacin da suka kwashe ita da AlGabid wato Daddyn Sheera.
Fiye da 10mn su na embrassements kafin ya ja rigarta ƙasa hakan ya baiwa breast ɗinta uwanda suka sha wuya a hannun Daddy damar fitowa,bai wani damu da yaushin su ba ya fara matsa su gami da tsotsar nipple ɗinta.
Cikin ƙanƙanen lokaci suka fita hayyacin su, string ɗinta ya ja gefe kafin ya fiddo Dick ɗinsa ya fara neman hanya.
Ta ja dogon numfashi sa'ilin kayan aikinsa suka ratsa ɓargon ƙasanta,daga tsaye ya fara aikin azafafe duk da su na cikin ruwa hakan bai hana su fitar da gumi ba.Wata irin nutsuwa ta musamman suka samu kafin su fito,kayansu suka mayar.
A cikin mota ne Ameer yace "Ni kam Rida a wane gari iyayen ki suke a zaune?" Ta na kallon titi tace "su na Zinder ne" "shiyasa kike kwana a makaranta ashe?"
"Eh to kusan haka ne!A nan Maradi mu na da ƴan uwa hasali ma da farko gidansu na fara zama,to kasan zumuncin yanzu bai cika ƙarko ba musanman in guda ya kasance mai arziki ɗaya kuma talaka"
"Haka ne kam yanzu in ina son auren ki ya za'a yi?"wani mamakin ne ya kuma luluɓe Farida jin ya ƙara zancen aure amman sai ta dake tace "Zinder za ka je mana!"nan suka ci-gaba da tattaunawa har suka isa makaranta.




Farida ta ɗan tsaya tare da kiran wayar Daddy,shi kuwa kamar mai jira haka ya ɗaga a bugun farko.Ba ta kai ga yi mashi tambayar da ta ke so ba ya fara masifa "na san da kin ci amanata kin baiwa wani ƙato kan ki.Sai dai abinda ba ki sani ba babban kuskure kika tabka,maganar aure kuma da kike duk a banza ne tunda ƙungiya ta shimfiɗa maki sharaɗin aure a rayuwar ki.Ke da yin aure sai kuma a lahira in ana yi,nan gidan duniya kuma sai dai ki kalli ƙawayen ki nayi banza shashasha!"


Murya na ɗan rawa tace "ƙungiya?wace irin ƙungiya kuma?" Daddy ya gagaɓe da dariya yace "yaro man kaza!Wato maƙudan kuɗin da kika zuba a Bank tunanin ki kawai dan na tafi da ke Dubai ne na baki su?to ki buɗe kunnuwan ki da kyau macijin da ke cikin cikinki shine masarrafar kuɗin ki daga yanzu duk namijin da kika kwanta da shi zai tatsi jinin shi ne sai a mayar maki da shi kuɗi"
Wasu hawayen takaici ne suka zubowa Farida ta tambayi Daddy"yanzu AlGabid ƙungiyar asiri ka saka ni ?" Ya bata amsa da "kika dai saka kan ki!burin ki shine kiyi kuɗi fiye da Sheera hhhh fiye ma da uban Sheera hhh! ƘUNGIYAR ASOMA ta na amfani ne da burin mutum,da wannan nayi capté ruhin ki har na kai ki ga shugaba Marlin" ambaton sunan ya saka Farida tunowa da abubuwan tashin hankalin da ruhinta ya tsintar mata a ranar da Daddy ya kai ta wajen meeting lokacin su na Dubai,wayar hannunta ta saki kafin ta faɗi nan take a some....
[11/08 à 11:07] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*




*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.




*Y*



"Na amince da dukkan sharuɗan ƙungiya muddin zan yi mahaukatan kuɗi na fita hankali,zan kiyaye komi kamar yadda aka tsara"

"Tunda ta amince ku bata naman mutum ta fara ci"
Wani dafafen nama aka miƙo ma Farida cikin wata ƴar tasa,naman ba'a ko dafasa ba haka ta rinƙa cinsa jini na bin hannunta,ta na gamawa mutanen ƙungiyar suka shiga yi mata barka.

Dr da ke kanta ne yace "kin farka?" Farida wacce duk abinda ya faru da ita a Dubai ya gama zuwar mata a kwanya ta ƙara fashewa da kuka ta na mai buɗe ido.Bisa gadon asibiti ta gan ta wanda ko shakka babu ta san kawota aka yi,abu guda ke yi mata yawo a kwanya shine shin wai dama ba mafarki ne tayi ba ta ci naman ɗan Adam?ta yaya aka yi tayi wannan babban kuskuren?
Wani irin gishiri-gishiri ta ke ji a bakinta tamkar yanzu ne ta ci naman ga wani wari da bakinta ke fitarwa,Dr ya taimaka mata tayi zaune kan gado.
"Mi ke maki ciwo yanzu?" Ta goge hawayenta tare da girgiza masa alamun babu,cikinta ne ke juyawa wanda kuwa ya tabbatar mata macijinta ne ke son ta bashi abinci.
Wani maƙoƙon baƙin ciki ne ya rufeta,da gangan ta ƙi cewa a bata ko da ruwan tea ne .
A zuci tace "sai dai ka mutu amman babu abincin da zan ci"ta ƙara komawa ta kwanta,ta na shirin rufe ido taji murya Daddy.Ido cikin ido suke kallon juna shi kuwa munafukin sai wani murmushin mugunta ya ke yi mata.Ledar hannunsa ya miƙo mata yace "tashi ki ci abinci "ta hararesa murya cike da ƙunci tace "na ƙi na tashi ɗin,ban ci ka shafa min lafiya"
"Ko na shafa maki lafiya shi wannan na cikin ki ba zai bar ki ba har sai kin basa abinci"cewar Daddy ya na sake miƙo mata,hawaye suna zuba a idonta tace "wlh sai dai ya kashe ni amman ba zan ci ba mugu kawai a duk laifin ka ne" Daddy ya kece da dariya yace "au !Haka za ki ce daga taimako?...." Shigowar Maryam ya saka shi ya ƙyale,ta ƙaraso ta na mai gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska.
"Ya jikin naki ƙawata?"
"Da sauƙi ban jin komi muna iya tafiya gida"
"A'a likita yace sai zuwa yamma jinin ki ne ya ɗan hau sakamakon wani firgici" Maryam ta faɗa,ita kuwa Farida hawayenta ta goge ta na cije baki saboda halbin da ake mata cikin ciki "mu je gida Maryam ban iya zaunawa nan har yamma akwai abinda zan yi"
"Mine ne za kiyi?kar ma ki soma Farida wannan hanyar ba mai ɓulle maki ba ce" Daddy ya faɗa bayan ya karanci tunanin zucinta,ta banka masa harara ta na mai tsayuwa kan ƙafafunta.Maryam ta ja ajiyar zuciya kafin tace "jira to na shaidawa likita"ta fita yayinda Daddy ya jawo Farida jikinsa har suna jin bugun zuciyoyin juna.
"Banzan tunanin ki na ce ki watsar da shi!Ko kin je Zinder babu abinda za suyi maki sai dai su ƙara saka ki cikin wata matsalar wacce kuma hatta su sai ta shafe su"da dukkan ƙarfin ta ta ke bugun ƙirjinsa ta na kuka tare da cewa "babu ruwan ka sai na je ai iyayena ne"





Saurin sakinta yayi saboda shigowar Maryam "likita yace ki jira ya sake duba ki kafin mu tafi"
Babu wanda ya sake magana har Likitan ya zo ya dubata "da dai kin ƙara haƙuri jinin ki har yanzu bai sauka yadda ake so ba"
Cike da masifa ta nufi ƙofa ta na mai cewa "ba zai taɓa sauka ba dan haka gwara na tafi" Maryam ta take mata baya ta na cewa "Farida ki tsaya dan Allah duba ƙafafun ki ko takalmi babu"ba ta saurareta ba har sai da ta kai inda Maryam ta ajiye motar ta.




A haka suka shiga zuwa gida,banda kuka babu abinda Farida ta ke yi har suka isa.
Akwatin kayanta ta shiga zuba ma kayan da za ta tafi sai dai da mamakinta duk kayan da ta zuba sai su rikiɗe su koma macizai, ta tsoron da taji ne ya saka ta komawa gefe ta cigaba da kuka kafin ta nemi maganin barci ta sha ko taji sanyi a ranta.
Wani wahaltacen barci ya ɗauketa,sosai ake gana mata azaba macijin cikinta duk ya galabaita saboda yunwa wannan ya saka yayi ta cizonta,a cikin barcin kuwa shugaba Marlin yayi mata kashedi akan kar ta saki ta fallasa sirrin ƙungiyar sa.






Wuraren ƙarfe shidda na marice Farida ta farka,jikinta duk yayi birdi tsabar yadda macijin ya cijeta sai wani ja da fatar ta tayi.Wanka ta so shiga sai dai azababiyar yunwar da ta ke ji ta hanata doli ta nufi kitchen,sauran abincin da ta gani ta canye tass kafin ta buɗe frigo ta fara shan madara da jus ɗin ciki har sai da taji ba ta iya sheɗawa.
Tayi gyatsa ta na jin ta sakai maciji an samu abinda ake so, Farida ta nufi toilet ta fara wanka sai taji kamar ana kallonta.
Waigawa tayi, Daddy ta gani cikin ɗan ƙaramin mirror ɗin da ke manne ga bangon toilet ɗin .Wani irin tashin hankali ne ya dirar mata ta ƙwala ihu tare da ƙoƙarin fita sai kuma ta ga ya ɓace ɓat,a tsorace tayi wankan ta fito.






A ɓangaren Sheera kuwa sam ta kasa sukuni tunda ta ga gidan Basheer ya shiga uku,kusan kullum sai ta je muddin ta buƙaci ganinsa bai zo ba.
Ƙarfe tara na dare

Please Login or Register in order to submit comment