Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

*****Matar khalees*****

✍️Alkalamin Nusaiba ibraheem rimi(Nusy bee)

بسم الله الرحمان الرحيم

Part 1

Matashiya ce wadda bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai ba, kyakykyawa ce wankan tarwada,tana sanye da golden lace riga da zani,ta yafa babban mayafi tun daga kanta,cikin takun ta na nutsuwa ta nufi bakin motar ta dake ma'ajiyar motoci ta kamfanin nasu

Muryar barrister Zee taji tanayi mata magana, Barrister Zee matar engineer Jabir wato mammallakin kamfanin,waigowa tayi fuskar ta cike da faraa ta qarasa kusa da zee suka tafa da raha irin ta qawaye, zee ta dube ta tace

"Su DEEJA manyan mata!sau hudu Ina shigowa kamfanin nan bana samun ki,yau ma Allah ya taimake ni"
Deeja tayi murmushi sannan tace"to zee me zan zauna nayi bayan na gama aiki na?dole na rinqa komawa da wuri,kin san ɗan rigimar nawa fa"

"Gaskiya kam deeja,ai rayuwar Sai haquri kawai"a cewar Zee

"Uhm!hakane,ni bari na wuce gida,Sai mun sake haɗuwa"a cewar deeja tana ƙoƙarin bude motar ta

"Okay!ki gaida gida"a cewar Zee,sannan ta juya ta nufi cikin kamfanin

Kamar yadda ta Saba yau ma bata tarar da KHALEES a gidan ba,hakan bei bata mamaki ba,Kai tsaye bandaki ta fada tayi wanka,bayan ta fito kaya kawai ta zura tayi sallah sannan ta zauna a gaban madubi ta fara kintsa kanta

Muryar engineer khalees taji,da alamu ya dawo,ta Dan saurara,ga dukkan alamu waya yakeyi,Don haka batayi gaggawar fitowa ba,ta cigaba da abinda takeyi,tana jinshi ya shige dakin shi

Bata fito ba Sai da ta kammala Shirin ta tsaf,cikin riga da skirt na lace orange colour,tayi kyau sosai,kanta Babu Dan kwali Sai mayalwacin gashin ta da ta tufke da ribbon kalar kayan jikin ta,Kai tsaye dakin khalees ɗin ta nufa

Da sallama ta shiga,yana zaune a bakin gadon yana latsa waya,ya amsa batare da ya kalle ta ba,bata damu ba ta zauna gami da fadin "sannu da dawowa"

Sai da ya bata lokaci sannan ya amsa da "yauwa"

Batayi zuciya ba,don idan da sabo ta saba,tace"na hada maka ruwan wanka fa"

"Naji"ya bata amsa har yanzu idanun shi Yana kan wayar shi

Ta ƙara da cewa "na Kai maka abincin dinning ko na kawo maka nan?"

Wannan karon ya dago ya dube ta,amma duban wulakanci yace"duk yadda kika gani,Kinga malama surutun ki ya ishe ni"

Batayi fushi ba,Don ta Saba da halin shi tace " I'm sorry"bata jira amsar shi batayi waje

Sai a lokacin khalees yabi hanyar da tabi da kallo na ƴan daƙiƙu Kamar wani Mai nazari,zuwa can yaja ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya nufi banɗaki

Tana zaune a falo tana danne danne a laptop ɗinta ya shigo falon,yadda yayi sallama batare da ya kalle ta ba haka itama ta amsa batare da ta kalle shi ba,bai damu ba yace

"Ina abincin nawa?"

"Gashi can na kammala shirya maka a dinning"ta bashi amsa,har yanzu kanta na ga laptop ɗinta,hakan bei dame shi ba ya nufi dinning set din ya zauna,ya zaro waya ya kama latse latse

Ta tabbatar bazei taba serving kanshi ba,hakan ne ya Sanya ta miƙewa ta nufi dinning ɗin tayi serving ɗin shi,yana ta danne dannen shi har ta kammala,tana kammalawa ta wuce ta cigaba da aikin ta

Deeja kenan,MATAR KHALEES!duk tarin ƙalubale da damuwowin da ta haɗu dasu a rayuwar ta hakan bai hana ta neman na kanta ba,Kuma tana matuƙar kama kanta a duk halin da ta riski kanta

A shirye take tsaf cikin doguwar riga light blue Mai adon duwatsu,ta naɗe mayafin rigar a kanta,cikin sauri take gudanar da Shirin ta don ta ɗauko hanyar makara,a main parlor ta riski khalees,batayi jinkirin gaishe shi ba Amma ko kallon banza bata Samu ba,Sai ma gyara agogon shi da ya cigaba dayi yana tafiya a cikin isa irin yadda ya saba,bata ƙara bi ta kanshi ba ta ɗauki hanyar waje abinta

"Ina zuwa?"taji muryar shi
Juyowa tayi cike da mamakin tambayar rainin hankalin da yayi mata,Ina zuwa kuma?bai san tana fita ba dama?Amma Sai ta daure tace

"Wajen aiki zan je"

Sai da ya bata lokaci sannan ya kalle ta

"Anyway!yau duk inda 1:00 pm tayi ki tabbatar kina gida,ki shirya Mana abinci don zanyi baƙi"yana Kai wa nan ya kewaye ta ya fice batare da yaji ta bakin ta ba

Itama rufa Masa baya tayi suka fito zuwa harabar gidan,shi ya nufi motar shi ƙirar BMW,ita Kuma ta nufi motar ta ƙirar anaconda

Tuƙi takeyi Amma tunani fal ranta,ƙwalla na neman zubo mata,amma tana ƙoƙarin dannewa,gaba ɗaya rayuwar ta tun tana ƴar ƙaramar ta take haɗuwa da wahalhalu dabam dabam,zata iya cewa bata taɓa jin daɗin rayuwar ta ba,a fili ta furta

"Gaskiya duk wanda ya rayu babu uwa to da sauran shi a farin ciki"

Ta tuna ummu,uwar riƙon ta, Imran masoyin ta,ga khalees mijin ta,hajiya uwar mijin ta,da su farida ƙannen shi,duk mutanen nan Babu wanda take jin daɗin shi

Jin ƙirjin ta ya fara motsawa ya Sanya tayi gaggawar kawar da wannan tunanin a ranta,domin ko da wasa bata ƙaunar ciwon zuciyar ta ya tashi

Ƙarfe takwas saura minti biyu ta shiga office ɗinta,an gyara shi tsaf, ta nemi waje ta zauna ta harɗe yatsun ta ta tokare haɓar ta gami da yin Shiru,tamkar Mai yin nazarin wani abu,ba komai take tunani ba illa mafita a rayuwar ta,ta kasa gane mei mutane suke nema da rayuwar ta,musamman mijin ta da ta kasa gane kanshi,duk hanyoyin da take tunanin masu bullewa ne tabi amma babu nasara,gaba ɗaya kanta ya kulle,gata ba ƙawaye ta cika ba Koda ace tana da ƙawayen surutu bai dame ta ba,balle har ta sanar wa wani taji sanyi

Abban ta ne ya faɗo mata a rai,a lokacin da yake raye shine abokin shawarar ta,bata manta wata rana a lokacin da tana gidan Imran, wani zuwa da tayi gida yaga yanda ta rame yace

"Khadija,ko da Baki gaya min halin da kike ciki ba nasan kina cikin matsananciyar damuwa,nasan cewa ke mai haƙuri ce,amma Ina so ki sani shi haƙuri baya yawa Sai dai yayi kaɗan,don haka ki cigaba da haƙuri Allah Yana tare dake"

Tace"babu komai abba in Sha Allah zaka same ni Mai biyayya,bazan baka kunya ba"

Allah yayi miki albarka"a cewar abban nata

Doguwar ajiyar zuciya ta ja bayan ta dawo daga tunanin daidai nan taji an ƙwanƙwasa ƙofar,ta bada izinin a shigo

Sa sallama sakatariyar tata ta shiga,ta amsa fuska a sake,a ladabce sakatariyar tata tace

"Madam oga na neman ki"

"Okay gani nan fitowa"ta bata amsa

Tana fita itama ta miƙe ta fice zuwa office din MD ɗin nasu

Batayi mamakin ganin khalees a office ɗin ba,sai dai yadda beiyi mata kallon sani ba itama haka,ta samu waje ta zauna,bayan sun gaisa ya dube ta yace"madam ya ake ciki game da aikin da na baki?"

"Ai na kammala tun jiya"

"Okay idan babu damuwa ɗauko mini su"

"Okay sir!"ta fada gami da miƙewa ta nufi hanyar fita daga office ɗin

Jim kaɗan ta dawo riƙe da takardu a hannun ta,ya amsa ya duba,ya kalle ta da murmushi yana fadin"very nice madam"

"Thank you sir!"inji ta

Wasu takardun ya miqo mata a files yana fadin "ga wani aikin nan da fatan Shima zai kammalu da wuri"

"In Sha Allah"ta fada gami da amsar takardun ta nufi waje

Sha biyu da rabi daidai ta miƙe ba don ta kammala aikin ba sai don umarnin khalees,Amma dai dai taci ƙarfin aikin,ta miƙe ta fito don rufe ƙofar office ɗin,sukayi sallama da sakatariyar ta ta nufi motar ta ta tayar ta ɗauki hanyar gida

#Nusy_bee
*****Matar khalees*****

✍️ Nusy bee

Page 2

Cikin sauri tayi wanka tayi sallah sannan ta shiga kitchen,farar shinkafa ta ɗora da miya sannan ta tayi papper chicken ɗin ta lafiyayye sannan tayi coconut juice,duk a cikin Abinda bei kai awa ɗaya da rabi ba ta kammala,ta jere su a dinning,cikin sauri sauri ta gyara ko'ina ta sanya turare gidan ya ɗauki ƙamshi,ta koma ɗakin ta tayi wanka ta shirya zuwa riga da skirt na atamfa ta ɗaura ɗankwali akanta ta zauna a bakin gadon tana mayar da nunfashi

Ta kai mintuna goma a zaune tana chatting taji sallamar su,sai da gaban ta ya faɗi saboda jin Muryar shi,tabbas shine ba amsa kuwwa bane,da sauri ta miƙe ta leƙa ,ga mamakin ta har da Yaya fauwaz,da sauri ta koma ta faɗa kan gado,gabanta yana dukan uku-uku,kanta ya fara sarawa,cikin rawar murya ta furta"wannan mummunar sakayyar taka ta ishe ni haka Imran"

Wayar ta ce ta katse ta,da sauri ta duba, khalees ne,ta san kiran me yake mata,da sauri ta janyo hijabin ta ta sanya ta miƙe ta nufi falon

Da sallama ta shiga,dukkan su suka ɗago suka amsa,a kallon da tayiwa Imran ta gano tsantsar mamakin da yake yi,wanda bata raba ɗayan biyu mamakin ganin ta a matsayin MATAR KHALEES yake yi,ita dai batayi ƙasa a gwiwa ba wajen gaishe su ba,su shida ne, banda yaya fauwaz da Imran,sai ragowar su huɗu da bata san su ba,suka amsa cikin fara'a, fauwaz ya dubi Khalees cikin tsokana yace

"Iyyeeee!ashe kaine kayi wuf da ƴar ƙanwar tamu shine ko mu sani?"ya dubi deeja yace"Dijangala ba'a sanar mana ba ko?ko da yake nasan fushi akeyi damu ko?"

Tayi ɗan murmushi tace"I'm sorry banyi gayyata bane,Kuma yazo a gaggauce shiyasa"

"Babu damuwa, Allah ya sanya alkhairi"inji shi

Ta wuce kitchen tana fadin"ameen,na gode"

Cikin ƴan mintuna ta gama halarto musu abincin,sannan ta juya ta shige ɗakin ta

Tana kwance tana jiyo hirar tasu sama sama, zuciyar ta na suya,tunani takeyi me ya haɗa Imran da Khalees?wace iriyar mu'amala ce ta haɗa su?ko dama can sun san juna?kai bei zama lallai ace sun san juna ba,don da ace sun san juna Imran zei taɓa bata labarin shi watarana,amma bata taɓa jin labarin shi a bakin Imran ɗin ba,to me haɗin su dashi yake nufi?

"Tabbas da wata ƙulalliya a ƙasa!"ta faɗa da raunin murya,idanun ta na kawo ƙwalla

Ta ɗaga hannun ta sama tace "ya Allah ga bayin ka nan,idan har da wani abu suke nufi na Allah ka tseratar dani,su kuma ka ganar dasu"

Tayi saurin goge hawayen da ya taru a kwarmin idanun ta suke ƙoƙarin zubowa,wayar ta ta janyo ta buɗe data suka cigaba da hira da aunty kiyya akan bikin Yasmin

Wayar ce ta soma ruri,sunan aunty Bintu ne taga yana yawo akan fuskar wayar,da sauri ta ɗaga da sallamar ta, cikin farin ciki take faɗin"aunty Bintu yau a gari?"

Daga ɓangaren aunty Bintu tace "kya tambaya mana,ke da bakya neman mutane"

Tayi ƴar dariya tace "ayya!am sorry aunty,yasu ilham da salim?"

Suna nan lafiya,wai da gaske ne kinyi aure?"a cewar aunty Bintu

"Deeja ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu kafin tace"haka ne aunty,anyi aure na watanni huɗu baya"

Aunty Bintu tace"Amma da mamaki Deeja,kinyi aure baki sanar dani ba,ko Mima ma baki sanar mata ba?"

"Uhm abinda Yaya fauwaz ya gama ce min kenan, wallahi aunty ba da shiri akayi auren ba,kawai lokaci yazo a haka"

"Haka ne kam!"inji aunty Bintu"shi aure lokaci idan yazo a lokacin shi sai anyi shi ko an shirya ko ba'a shirya ba,fatanmu dai Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitinar shaiɗan"

"Ameen"Deeja ta amsa cikin sanyin Muryar ta

"Kinsan da bikin Yasmin ko?"aunty bilki ta tambaye ta

"Eh na sani,Yasmin da hudan momy Aisha sun kawo min invitation card,Kuma tun kwanaki can ita Yasmeen din ta turo min hoton ankon ta WhatsApp"

"To shikenan,mu ma sun aiko mana da gayyata,don haka zamu zo,itama Mima next week zasu taso daga Malaysia

Cikin ɗoki Deeja tace"wayyo daɗi!da gaske don Allah aunty?"

"Wallahi kuwa,da jibi zasu taho,wasu uzururruka ne suka tsare su,amma in Sha Allah nan da five days zasu taho"

"To Allah ya kawo su lafiya"

"Ameen,me kika tanadar musu ne?wannan zumuɗi haka?"

Ƴar dariya tayi sannan tace"wallahi aunty nayi kewar Mima ba kadan ba,ga yaran ta masu shiga rai musamman ma mei suna na Khadija Mee'ad"

Dariya sosai aunty Bintu tayi tace"lallai,kiji ki da son kai"

"Ba son Kai bane aunty,Ina son yarinyar ne sosai"

"To da kyau,saura ke kema"

"Aunty Bintu lokaci ne,fatan mu Allah ya kawo masu albarka"

"Ameen ya Allah,sai anjuma,ki gaida mai gidan"

"Okay zaiji"daga haka suka ajiye wayar

Farin cikin zuwan su Mima ya danne damuwar da take ciki,don tasan Mima ko banza zata bata shawarwarin da zasu rage mata damuwa,don Mima wayayyiyar gaske ce sosai,kuma tafi Deeja shiga mutane sosai,hakan ya sanya ta karanci dabiun mutane da yawa

Tana jin sanda su Khalees suka fita,sun kwashi a ƙalla mintuna goma da fita,don taji tashin motocin su,sai a lokacin ta fita don kwashe kayan da suka kammala cin abincin,ta kimtsa wajen

Ko da Khalees ya dawo ma bei nuna mata komai ba,itama bata tambaye shi komai ba,don tasan bazai taɓa bata amsa ba

Da daddare tana zaune tana danne danne a laptop,lissafe-lissafe takeyi na kasuwancin ta,na wani babban shopping mall da ta buɗe, Khalees ne ya shigo da sallama,ya dube ta da fuska babu annuri yace"gobe su Hajiya zasu zo,don haka ki zama cikin shiri"yana gama magana bai saurari cewar ta ba ya wuce zuwa ɗakin shi,a ranta ta furta"oh!wata damuwar dai zan riska na sani"

Washe gari da safe babu aiki,don haka a nutse take gudanar da aikace aikace-aikacen ta,tabi ko'ina ta share tas har ɗakin Khalees,batayi tunanin ɗora girki ba,don ta san halin Khalees ba tun yau ba,baayi masa gwanin ta,don sai ta girka yace bazai ci ba,don haka water kettle kawai ta jona ta tafasa tea ta Sha da cake,ta koma kan computer ta cigaba da lissafin ta

**** **** ****

Cikin sauri take shiri don ta bar su salma jira,riga da skirt ta sanya waɗanda suka ji wani matsiyacin ɗinki,gaba daya jikin ta a waje,gaba ɗaya jikin ta a waje,ko budurwar mutunci bazata iya sanya Waɗannan kayan ba ballantana ita matar aure,ko ɗan kwali bata sanya ba sai wani yalolon mayafi da ta sanya kalar atamfar,sannan ta ɗauko purse dinta ta fito,tana rufe ƙofar kira ya shigo wayar ta,da sauri ta duba,kamar yadda tayi tsammani Yaya najeeb ne,tana ɗagawa tace "hello yaya najeeb"

"Haba sister!tun ɗazu nake jira,me ya hana ki zuwa ne?"

"I'm sorry bro! wallahi al'amuran bikin Yasmin ne ya sha kanmu shiyasa kaji ni shiru,amma in Sha Allah ko da yamma ne zan leƙo gidan,ba dai Ni nace zan zo ba?"

"So why not bazaki zo yanzu ba?"

"Saboda akwai abubuwan da zamu siyo yanzu mu da su salma,sai anjuma zamu dawo,kai tsaye gida zan wuto in Sha Allah"

"Okay to Allah ya kawo ki lafiya"

"Ameen,bye bye!"ta kashe wayar

A motar afra ta tarar dasu,afra na mazaunin driver sauran kuma suna baya,wato gaba wajen mai zaman banza ya tashi a matsayin mazaunin ta kenan,ta shiga tana fadin "oh sorry na bar ku jira ko?"

Zakiyya ta kalle ta sheƙeƙe gami da taɓe baki,afra kam murmushi tayi tana faɗin"sister kenan,kina wuta"

Tayi wani malalacin murmushi tana cigaba da danna waya,lubaisa kam kasa daure wa tayi,ta dube ta cikin ɗaurewar fuska tace
"Amma UMAIMA sai nake ganin kamar wannan shigar bata dace ba a matsayin ki na matar aure ko?"

A watse umaima ta kalle ta,sai dai tun kafin tace komai zakiyya tace "oh lubaisa ina ruwan ki?ita ƙaramar yarinya ce da za'a ce bata san me ya dace ba?"

"Ai kawai tsabar shegen shishishigi ne da hassada"a cewar afra,wadda dama tuntuni basa jituwa da lubaisa

Lubaisa na shirin sake magana nuwaira dake kusa da ita tayi mata nuni da tayi shiru,dole tayi shiru gami da zaro wayar ta ta kunna music ta dasa a kunne,don irin surutan da afra take cigaba da yi

Shopping mall suka nufa inda zasu yi siyayyar bikin,a bakin mall ɗin wayar afra ɗauki ƙara,ta ɗauko ta duba,ganin wadda take kiran nata ne tayi saurin ɗagawa,bayan sun gaisa take sanar da ita cewa ta shirya,sati mai zuwa zata zo don bikin Yasmin,cikin farin ciki afra tace"to ƙawa ta Allah ya kawo ku lafiya,muna waiting"

"Ameen, Sai nazo"sukayi sallama

Afra ta kalli umaima da murmushi a fuskar ta ta tace"umaima be ready,muna da babbar baƙuwa,wannan likitar da nake baki labari mun haɗu daita a ƙasar Lebanon,kin gane ta?"

Umaima tayi murmushi tace"eh na gane ta"

"Yawwa!itace zata zo bikin Yasmin,da alama bikin nan zai yi albarka"

#Nusy_bee

*****Matar Khalees*****

✍️ Nusy bee

Page 3

"Sosai ma kuwa afra,Ni kam zan so in ga wannan matar"a cewar umaima

"She is very nice umaima,ga yaran ta guda biyu masu tsananin kyau,mijin ta kuwa akwai class,ba irin abban haneef ba"

Umaima ta kwashe da dariya,daidai nan afra ta kammala parking suka fito, umaima ta kalle ta tace"a'a afra,ko dai kin ƙyasa ne na fara taya abban haneef kishi?"

Afra tayi ƴar dariya tace"a'a wallahi,shi abban haneef kamar shashasha yake,kowa kawai buɗe masa haƙora yake,ban samu kwanciyar hankali ba sai da na raba shi da Wannan matsiyaciyar yarinyar fa kina gani"

Umaima ta taɓe baki,suka jera suka nufi cikin mall ɗin suna cigaba da hira, afra na koɗa kyau da jan aji na mijin ƙawar ta likita

Sai wajen ƙarfe uku suka gama siyayyar suka ɗauki hanya,amma sai umaima tace a sauke ta a gidan su

Haka kuwa akayi,suka sauke ta sukuma suka wuce gida

Da sallama ta shiga cikin gidan,a falo ta iske su umma,har da najeeb ɗin,da sauri najeeb ya taso ya rungume ta yana faɗin"lovely sister oyoyo!"

Umma ta kalle su cikin rashin jin daɗi tace"haba najeeb!da auren ta fa!"

"No umma!ba ƴar uwata bace?"yayi saurin katse ta

Daga haka tayi shiru bata sake magana ba, najeeb ya dubi umaima yace"ki ci abinci zaki raka ni gidan wani aboki na"

"Okay!"ta bashi amsa,ta dubi umma tace"umma akwai abinci ne?"

"Eh akwai,bari in kawo miki"umma ta miƙe ita kuma umaima ta zube akan kujera don hutawa

**** **** ****

Tun azahar ta kammala komai,har abin taryar baƙin nata duk da cewa ba baƙin farin ciki bane,ta gyare gidan tsaf,tunda safe da taga Khalees bata sanya shi a idanun ta ba,hakan bei dame ta ba don ganin nashi babu abinda zai tsinana mata, wataqila ma ta samu ƙarin takaici

Ƙarfe uku da mintuna goma taji ƙarar gate,da alama su hajiyar ne suka iso mei gadi yake ɗage musu gate ɗin,dam!taji gaban ta ya buga,da sauri ta dafe ƙirjin ta tana fadin"allahumma laa sahla illaa maa ja'altuhu sahla wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahla"

Tana leƙen su ta window,har suka fito daga motar su,su huɗu ne, hajiyar,sai farida da jannat,sai direban su da ya tsaya a wajen malam Audu mei gadi

Da sallama suka shigo cikin gidan,a zaune suka same ta a falon tana jiran isowar su,da sauri ta miƙe tana ta faman fara'a,ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya,duk da cewa su jannat ƙannen Khalees ne,kuma ko itama ta girme su,amma hakan bei hana ta gaishe su ba,don ta san cewa su baza su taɓa gaishe ta ba

Hajiyance ta amsa, fuska babu yabo babu fallasa,sai jannat,amma ita Farida kallon ta tayi sheƙeƙe ta maida kai ga wayar hannun ta,da alama chatting takeyi

Bata kula ba,sai ma cima data jere musu a gaban su tana jansu da hira, hajiyance kawai mei amsa wa,sai jannat sama-sama,amma Farida ko uhum bata ce mata ba

Hajiyance ce ta dube ta tace"am dama ba wai zama nazo yi ba,nazo ne in sanar dake cewa jibi in Sha Allah su Farida da zasu dawo gidan nan da zama da zama,don haka sai ki shirya,na riga na sanar da yaron nan (tana nufin Khalees)tuni,don haka sai ki zauna da shiri" ta ƙarasa faɗa tana miƙewa tsaye

Wani irin jiri Deeja ta rinqa ji,amma da yake jarumar mace ce ta dake tace "to Hajiya, Allah ya kaimu jibin"

Hajiya ta amsa da "ameen"

Deeja tace"Hajiya baku ci abincin ba ma"

"A'a mun ƙoshi wallahi,zamu tafi"bata jira cewar Deejan ba tayi gaba,suma yaran suka biyo bayan ta, Deeja bata da zaɓin da ya wuce bin bayan su,ta rako su har bakin motar su

Bayan sun tafi komawa ɗakin ta tayi ta ɗaga waya ta kira zakiyya,a lokacin dawowarsu kenan daga shopping mall da suka fita, shigowar ta sashen ta kenan,ko zama batayi ba,sai ga wayar Deeja ta shigo

Da sauri ta ɗaga tana faɗin"Hello! Deeja manya"

Yanayin Muryar Deejan ya fahimtar daita cewa ba lafiya ba,tace"Allah yasa dai lafiya"

"Uhm! aunty kiyya bari kawai,ina cikin damuwa sosai"

"Kina bari na ɗan yi uzuri,zan kira daga baya"

"Okay I'm waiting"daga haka komawa tayi ta kwanta a rigingine,zuciyar ta nayi mata zafi,ta lumshe idon ta,ta kai mintuna goma sha biyar a haka kafin taji kuwwar wayar ta,ta buɗe idanun ta ta miƙa hannun ta a kasalance ta janyo wayar,ta ɗaga

"Hello ina jin ki"

Deeja tayi ajiyar zuciya sannan tace"bari kawai aunty kiyya,ina cikin tashin hankali da taraddadi"

"Me ya faru kuma?"kiyya ta tambaya tana gyara zama

A hankali ta warwarewa zakiyya komai, cikin mamaki da kaɗuwa zakiyya take gyaɗa kai,zuwa can tace

"Deeja,ki cigaba da haƙuri,haka Allah yaso dake,ki sani duk mutumin da kika ga Allah yana ta jarabtar mutum ta Allah yana son shi,don haka ki cigaba da haƙuri, akwai lokaci,ki saurari zuwan yaran kawai,ko me zasu yi kar ki kula su,ki kama kanki kawai,in Sha Allah zaki ga ribar abin, kuma ma Allah na tuba abin kwana nawa ne? 'yan mata ne fa,aure zasu yi"

Jikin Deeja yayi sanyi,taji sauƙi a zuciyar ta, cikin wata kasalalliyar murya tace"in Sha Allah aunty kiyya zan kiyaye"

"Well!yaushe zaki zo bikin ne?ko sai anzo dab?"

Murmushi mai sauti Deeja tayi,tace"Kai aunty!Sai kace wani gari dabam?"dariya aunty kiyya tayi tace"sai mun ganki dai"

"Okay na gode aunty kiyya"

"Nima na gode"sukayi sallama

Ai kuwa bayan kwana biyu ta dawo daga aiki ta samu motar su fareedan a harabar gidan,sai da gaban ta ya faɗi,amma da yake mace ce mei kamar maza sai ta dake,ta shiga falon da sallama

Dukan su suna zaune sun kunna TV suna kallo,suka ɗago suka kalle ta suka watsar,ta nuna kamar bata san sunyi ba,tace"sannun ku da zuwa"da ƙyar jannat ta amsa da cewa

"Yawwa kema sannun ki"bata damu ba ta kewaye su ta shige ɗakin ta,tana jin Farida na jan dogon tsaki,amma ko kallon sashen da take batayi ba,ta shige ɗakin ta

Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ta nufi kitchen,bisa mamakin ta sai ta tarar babu abincin sai warmers ɗin nata da akayi mata wancakali dasu,ta shiga bin ko'ina da kallo, girgiza kai tayi kawai, sannan ta fara kwashe kwanukan tana tattare su a water sink,ta wanke su tas ta maida su ma'ajiyar su sannan ta share kitchen ɗin sannan ta ɗora jollof ɗin Talia,don tasan Khalees yana hanya, gashi kuma babu abinda zasu ci ita da Khalees ɗin

Cikin azama ta dafa talia jollof da kifi taji kayan lambu, cikin ƴan mintuna gidan ya ɗauki ƙamshi,ta haɗa lemon mangwaro ta sanya a fridge,ta ɗibar wa su Farida itama ta ɗiba,ta zubawa Khalees nashi a warmer ɗin shi


#Nusy bee
*****Matar Khalees*****

✍️Nusy bee

Page 4

Babu komai a fuskar ta ta miƙa musu,ko kallon mutunci bata samu ba,itama bata damu ba,ta ɗauki nata ta shige ɗakin ta

Sanda Khalees ya dawo tana jin su,suna ta hira da ƙannen shi,bata kula su ba sai da taji ya shiga ɗakin shi,da alamu wanka zai yi,ta fito ta jere kayan abincin a dinning area,ta shiga ɗakin shi don yi masa sannu da zuwa

Har lokacin Khalees yana banɗaki bei fito ba,ta zaro masa kaya marasa nauyi na zaman gida ta ajiye masa a bakin gado,tana gamawa ta miƙe ta fice daga ɗakin

Tana cikin ɗakin ta taji Muryar shi,ta fito tayi masa sannu da zuwa,ta sha mamakin amsawar da yayi fuska a sake, amma bata bar hakan ya bayyana akan fuskar ta ba,kuma ta alaƙanta hakan da wanzuwar su Farida a falon,don ta juma da kula cewa basa iya kawo mata raini a gaban shi

"Idan ka shirya ga abincin ka nan a dinning"ta faɗa cikin kwantar da murya

"Dama shi na fito nema,bari in ci tukunna"ya nufi dinning ɗin,ita kuma ta koma cikin ɗakin ta

Da daddare suna zaune a cikin ɗakin nashi ta dube shi cikin kwantar da murya tace"am dama Ina son yin wata magana da kai"

Ya ɗan kalle ta sannan ya maida kanshi fuskar wayar shi yace"ina sauraron ki"

"It is better ka ajiye wayar nan,don kafi fahimta ta ko?"ta faɗa cikin kwantar da murya

Wani matsiyacin kallo ya watsa mata sannan yace"ashe?har kina da maganar da take da muhimmancin da zata sanya ni ajiye waya?"ya faɗa har yanzu idanun shi na kan fuskar wayar shi

Shiru tayi bata ƙara magana ba,shima shirun yayi, tsawon lokaci ganin bata da niyyar magana sai ya kashe data ɗin shi ya dube ta yace"ya ake ciki ne?"wacce magana ce take tafe dake?"

Shiru tamkar bata ji ba,sai da ya maimaita tambayar, cikin kasalalliyar murya batare da ta kalle shi ba tace

"Dama kan batun bikin ƙanwa ta ne"

"Ehen,me kike so nayi miki?"ya faɗa yana kallon ta

"Kasan tun ana igobe ko jibi za'a fara bikin nake so naje,to

Please Login or Register in order to submit comment