Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da maganar jiya?a sanyaye nace masa na amince,sai naga fuskar shi ta faɗaɗa da murmushi,yaja hanci na yana min godiya

A taƙaice dai,a ranar Dr Najeeb ya fara sani na ƴa mace,ya gama wulaƙanta rayuwa ta,amma ya kula dani sosai,ya tarairaye ni kamar sabuwar amarya,daga hotel ɗin da ya kai ni ya wuce dani ƙaton store ya siya min sababbin kaya da kayan kwalliya da kayan ƙwalam,ya sake min Sabuwar waya,ya kai ni tsadadden eatry yayi min order na favorite ɗi na, sannan ya mayar dani gida. Ni da ya kamata ace tun biyu da rabi ina gida ban koma ba sai biyar,amma umma ko uffan ba tace min ba, gani na cikin yanayin damuwa ma bai saka ta tambaye ni komai ba"Umaima ta kuma yin shiru tana share hawayen ta

Bayan ƴan sakwanni ta cigaba"duk lokacin da ya kwanta dani yana bani wata ƙwaya, ashe ta hana ɗaukar ciki ce,tun ina jin tsoro ina ɗari-ɗari har na saki jiki,wani lokacin ma nice nake kai kaina gare shi, a haka muke kasance har tsawon shekaru biyu

A lokacin ina da shekaru goma sha tara da haihuwa,a shekarar ne na gama secondary School ɗi na,kuma still a shekarar ne Najeeb ya jefa Ni a rayuwar Imran

Da farko bai gaya min shirin shi akan Imran ba,nasan dai yana yawan kira na ko yace nayo girki kala kaza na kawo masa,sai da ya samo kan Imran yake shaida min so yake na aure shi

Da farko ban so ba,amma Najeeb ya nuna min wannan itace mafita dole,da haka ya samu na sauko na fara kula Imran,kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Allah ya jarabce ni da son shi

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 35

Komai zanyi sai nayi shawara da Najeeb,da farko naso na auri Imran lokacin da ya aure ki na zauna lafiya da ke,ko babu komai zan samu sauƙi daga Najeeb,don har a lokacin bana ƙaunar yadda yake kwanciya dani,wani lokacin ma a ɗaki na musamman idan mahaifiyar shi bata nan

Amma sai Najeeb yayi ya zuga Ni har naji nima na tsane ki,naji bana buƙatar zama da koma wacece wadda akace Imran ya aura

Ban tashi sanin Najeeb shaiɗani bane sai da aka tashi auren mu da Imran,don zama na musamman yayi dani ya shaida min adadin kuɗaɗen da zan rinƙa tatso masa a hannun Imran,da kuma cewa har gobe duk sanda ya buƙace ni zan zo,na tsorata sosai, kuma na shawarci Nadiya, Nadiya ta nuna min ba wata matsala,kuma hakan ta kasance,duk sanda Najeeb ya neme Ni zan san dabarar da zanyi naje gare shi,gashi kuma har lokacin bai daina bani maganin hana ɗaukar ciki ba

Deeja,abinda baki sani ba shine,bani ce naso Imran ya rabu dake ba,shima Imran bai so rabuwa da ke irin haka ba,duk shirin Najeeb ne,mafi girman laifin Imran shine bakin shi baya shiru, kullum a asibiti bashi da magana sai taki da irin ƙauna da sadaukarwar da kikayi masa,wannan shine dalilin da ya jefa tsanar ki a zuciyar Najeeb, Nadiya ma sai daga baya na gane ƙawar Najeeb ce, saboda tsanar da yayi miki ya tura ta rayuwar ki ta san yadda zatayi ta auri mijin ki Khalees don ta ƙuntata miki

Da farko bansan hanyar wajen boka ba, Amma a sanadin Nadiya na sani,ba don kaina ba sai don buƙatun ta,a tsawon zama na da Imran ban taɓa kai shi wajen boka ba,amma Nadiya ta saka Ni na kai ki, na kai Khalees, na kai mahaifiyar shi da ƴan uwan shi

Bayan Khalees ya sake ki kinyi ɓatan dabo Imran yazo ya tuhume ni,na nuna masa bansan zancen ba,duk da ina zargi biyu a lokacin, ko dai ke kika ɓoye kanki ko kuma Nadiya ta ɓatar dake,don na santa,hatsabibiya ce ta gaske

A saboda haka naje gidan Nadiya,Amma sai ta nuna min babu ruwan ta da maganar,ƙarshe ma bamuyi rabuwar daɗi da ita ba,don a lokacin Imran yayi min abinda bai taɓa yi min ba saboda ke,wato mari

Ina cikin wannan tashin hankalin ne Najeeb ya turawa Imran evidence ɗin abinda muke aikatawa, saboda ya neme ni naƙi bashi haɗin kai, daga nan kawai na saddaƙar aure na ya gama mutuwa,gashi Imran sai nanata min yake na nemo ki duk inda na kai ki

Ina cikin wannan mugun halin tsawon kwana huɗu Imran ya zo da ƴan sanda suka kamani ina kukan tashin hankali,sai da suka kaini station naga Ashe har da Nadiya,wadda na firgita sosai da ganin ta yadda ta fice daga hayyacin ta,ƴan sandan nan babu tausayawa suka rinƙa gallaza mana don mu fito dake,amma amsa ɗaya muke nanata musu itace bamu san in da kike ba,kwanan mu shida a hannun su muna shan azaba iri-iri,ƴan uwan Nadiya sukayi bailing ɗin ta da ƙyar,a lokacin na ƙara kukan rashin dangi,don Ni dai nasan babu mai bailing ɗi na

Ilai kuwa babu wanda yazo min,amma bayan kwana uku suka sake ni,kai tsaye gidan su Najeeb naje amma yayi min korar kare,dole na koma gidan Imran,amma tun a compound ya bani takarda ta yace na fice masa daga gida,nayi ta kuka ina roƙon shi kan bani da in da zan je,yace wannan bai dame shi ba,na fice masa daga gida,da yaga naƙi fita ya janyo Ni kamar bola ya jefar dani sannan ya gargaɗi mai gadin kar ya kuma bari na na shiga

Ban daddara ba naje gidan fauwaz,amma abinda Imran yayi min nafila ne,don shi sakawa yayi mai gadin nashi kore ni da bulala,na koma bakin gate ɗin gidan Imran na raɓe,ga dare,ga yanayin sanyi,ga sauro,haka na kwana har asuba,da ya fito zashi sallar asuba ya ganni ranshi ya ɓaci,Ni kuma na fashe da kuka don a lokacin bansan yadda zanyi ba,ya tsallake Ni yayi tafiyar shi masallaci,to bayan ya dawo ne da ya shiga gida ya fito da kuɗi a envelope ya bani yace yayi min iya abinda zai iya,na fita daga rayuwar shi ko ya wulaƙanta ni,nayi ta roƙon shi ya yafe min,amma magana ɗaya yake nanata min,baya son sake gani na a rayuwar shi

Da kuɗin da ya bani nayi kuɗin mota na dawo garin mu taura,yadda na tafi ba'a sani ba hakanan babu wanda ya damuwa da dawowa ta,na buɗe ɗakin mahaifiya ta na gyara na shiga,nayi ga jinyar kaina tsawon sati ɗaya

Bayan na dawo dai-dai nayi amfani da kuɗin wajen Imran na saro kayan miya da omo da sabulu na fara siyarwa,amma saboda rashin kasuwa yasa na fara fita bakin kasuwa na kasa kayan na siyar,idan nayi ciniki na sayi abinda zan ci,idan banyi ba ciniki ba na zauna da yunwa,don na gwammaci yunwa akan baƙar rayuwar da Najeeb ya jefa Ni a baya,don nayi alƙawarin bazan sake ba

Bayan watanni biyu na fara yawaitar ciwon kai,da kai amai,alamomin ciki masu yawa suka bayyana a tare dani,har a lokacin ban wani gane ba, kasancewar bani da wannan wayewar

Sam ban fahimci ciki gare Ni ba sai da naga ƴan gidan mu suna nuna ni,daga karshe dai wata matar ƙanin baba na tazo ta zage Ni da gori,wai naje nayi karuwanci nazo zan haifa musu shege

Tabbas na tsorata da jin ina da ciki,ba don komai ba sai don bani da ƙarfin gwiwar tunkarar Imran,don dai nasan ba na Najeeb bane,don na kai watanni biyar inayi masa hanya-hanya idan ya neme ni, saboda all of a sudden kawai naji na gaji da rayuwar dabbobin da mukeyi

Nayi laulayi sosai,don sai da ta kai bana iya fita sana'a ta,amma ƴan gidan mu babu mai zuwa inda nake

Sai da ciki na ya shiga wata na biyar sannan na samu sauƙin laulayi,na cigaba da sana'a ta,haka zan ɗauki kaya,ga nauyin ciki,kuma ko sau ɗaya ban taɓa tunanin zuwa awo ba

Sai da ciki na yayi wata takwas sannan wata dattijuwa maƙwabciyar mu,tace na daina fita zata ɗauki abinci na,nayi ta mata godiya

Ai kuwa ta cika alƙawari,don safe, rana,dare sai ta aiko min da abinci,in da na godewa Allah cikinnawa ba mai tsirfa bane,komai na samu ci nakeyi. Ciki na yana cika lokacin haihuwa na fara yawan ciwon mara akai akai,sai nayi zaton haihuwa ce sai kuma abu ya lafa,sai da nayi kwana tara a haka sannan na fara naƙudar gasken

Na sha wahala sosai,don sai da na fara tunanin ko mutuwa zanyi,amma saboda taurin kai yadda ƴan gidan basu nemi taimaka min ba nima ban nemi taimakon su ba,da dai naga ciwo ya ƙi ci yaƙi cinyewa sai na faki idanun su na kira wani yaro nace ya kira min dattijuwar da ke aiko min abinci Inna laraba,ai kuwa bata juma da zuwa ba na haihu

Tsawon kwanaki bakwai inna itace ke shigowa tayi min wanka ta wanke jaririya,ɗan ta ta sanya yayiwa yarinyar huɗuba,da aka tambaye Ni suna ke kika zo min rai,don haka nace a sanya mata Khadijah

Inna laraba ta kula dani har nayi kwana talatin da biyar,a lokacin na cigaba da fita sana'a ta Saboda kula da little Deeja

Yanzu watannin Deeja ƙarama huɗu da haihuwa, Allah ya rufa min asiri da ƴar sana'a ta bana rasa ci ko sha,sannan bana fashin yi miki addu'ar Allah ya bayyana ki ya tsare ki a duk inda kike

Rabo na da karatun addini tun bayan rasuwar mahaifi na babu jumawa,don haka lokacin da aka buɗe wata makarantar matan aure banji ƙyashin shiga ba,a lokacin Deeja watannin ta biyu da haihuwa

A haka nake rayuwa har zuwa yau,ko da bana farin ciki amma bana cikin baƙin ciki,kuma ina zaune lafiya da Ni da ƴar jaririya ta

Wannan shine labari na Deeja,haƙiƙa ni ɗin mai kuskure ce,amma kuma na kasa gane wanene silar hakan,mahaifi na da ya kasa mayar da raino na wajen dangin mahaifiya ta,ko dangin mahaifiya ta da suka kasa nema na tsawon shekaru,gashi ni bazan iya kai kaina gare su ba,ko dangin mahaifi na da basu mayar dani dangin uwa ta ba bayan sun san ba riƙe Ni zasuyi ba,ko ma dai menene, alhamdulillahi,na godewa Allah da ya nufe ni da shiriya tun kafin lokaci ya ƙure min"

Menene ra'ayin ku game da labarin Deeja da na Umaima?wannene yafi ban tausayi kuma yafi Zama matsala a cikin al'ummar mu?sai naga ra'ayoyin ku a comment section, Allah ya barmu tare MATAR KHALEES fans 🥰

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 36

Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu ƴan mintuna bayan gama labarin Umaima,bakajin komai sai shashsheƙar kukan Afra da Umaima,da ajiyar zuciyar Deeja,kiran sallar la'asar ne da akayi ne ya sanya Umaima miƙewa tana goge kumburarrun idanun ta,a lokacin ruwan yayi sauƙi,ta ɗauki ƴar butar ta guda ɗaya ta zuba ruwa a ciki tace"gashi ku fara yin alwala,akwai makewayi idan kuna buƙatar shiga"Afra ta miƙe ta ɗauki butar batare da tace uffan ba,don har yanzu kuka takeyi

Ita kam Deeja har yanzu idanun ta suna kan little Deeja da ke kwance a jikin ta tana shan baccin ta cikin kwanciyar hankali,ko alamun hawaye babu a idanun ta,amma a zuciyar ta ji takeyi da zata samu tayi hawayen da taji sauƙin raɗaɗi da ciwon da takeji,ta juma bata ji tashin hankali irin wannan ba,shiyasa bahausheyace kai dai kaga mutum,amma bakasan yaya yake gudanar da rayuwar shi ba,baka san kalubalen da yake fuskanta ba, lallai rashin uzuri a rayuwa babbar masifa ce

Afra ce tayi sallama ta shigo tana duban Deeja tace"kije kiyi alwalar Deeja,nayi"sai a sannan Deeja ta kwantar da little Deeja ta miƙe cikin mutuwar jiki ta fice daga ɗakin

Umaima ma ficewa tayi Afra kuma ta tayar da sallah

Bayan sun idar da sallah ma zama sukayi jugum jugum kowa da tunanin da takeyi,don ma ita Umaima ta ji sauƙin nauyin da ke zuciyar ta,a ƙalla tayi magana da waɗanda ta san sun fahimci halin da take ciki,basu daɗe da idar.da sallah ba ruwa ya dawo kamar da bakin ƙwarya,cikin sanyin murya Deeja ta kalli Afra tace"Afra anya kuwa zai yiwu mu koma yau?"kafin Afra tayi magana Umaima tace"mai zai hana ku kwana anan?kunga yadda akayi ruwa hanyar ba lallai tayi daɗin tafiya ba"Afra ta kalli Deeja don jin me zata ce,cikin sanyin murya tace"to Allah ya kaimu goben"

Sosai fara'a ta bayyana a fuskar Umaima,taji daɗi sosai,ko babu komai dai yau ɗaya zata sake da wasu mutane da ta sani a rayuwar ta,cikin murna tace ameen ya Allah"su dai su Deeja sai kallon ta sukeyi cike da tausayawa

Deeja ta kalli Umaima da ke chanjawa little Deeja kaya tace"yanzu Umaima idan Allah ya fito miki da miji zakiyi aure?"

Umaima tace"ƙwarai kuwa,bayan haihuwa ta wani abokin ƙanin baba na ya nemi aure na,da farko har na amince masa,har Wajen sana'a ta ƴaƴan shi sukaje sukayi min rotse suka watsa min kaya na suna faɗin uban su bazai auri karuwa mai ƴar shege ba, dalilin haka na tsorata na sallame shi"

Daga Afra har Deeja sakin baki sukayi suna kallon ta da mamaki, Deeja tace"saki nawa Imran yayi miki?"

"Saki ɗaya ne,takardar ma tana nan har yanzu"

"To shine kike tunanin auren wani bayan Imran?"a cewar Deeja tana kallon ta

Daga Umaima har Afra a firgice suka kalli Deeja, Umaima cikin in Ina tace"I....I... Imran kuma?...yace baya son gani na fa,yace ba fita a rayuwar shi, kuma kema ba sai na gaya miki ba kin san Imran yafi karfi na yanzu"Deeja bata sake magana ba ta amshi little Deeja da take ta kallon ta,don ruwan da akayi da sakin asabarin da Umaima tayi yasa ɗakin yayi duhu,sai Deeja ta kunna torch da ke jikin power bank ɗin ta,ta haske ɗakin tarwai

Murmushi tayi tana kallon ta, itama yarinyar kamar ta sani ta fara ɓangale baki tana dariya, Deeja ta shagala tana mata wasa,dama ita fa tun ganin ta da babyn a farko ta shiga ranta

Umaima ce ta miƙe tsaye tana ɗaukan hijabin da tayi Sallah bayan ruwan ya tsaya,tace"bari naje nayo cefanen girkin dare,biyar ta gota yanzu"itama Deeja ta miƙe tana faɗin"nima dama ina son zaga garin,mu je, Afra ke kam nasan bakya jure wahala zauna ki jira mu"

Afra ta kalli Deeja tana ƴar dariya tace"ai kuwa sai naje,idan na gagara ai kuna da ƙarfin goyo ni"sukayi dariya su duka,Afra ta miƙe ta ɗauki mayafin ta, Deeja ta goya little Deeja, ta kalli Umaima tace"da me za'a lulluɓe ta saboda sanyi?"Umaima ta ɗauko ɗankwalin atamfar ta ta miƙawa Deeja, Deeja tace"wannan ai bazai yi ba,akwai showel ɗin Affan a mota,bari nayi amfanin dashi"

"Ni kam zan ce yayi yawa ma ban tambaye shi ba,banga kinzo dashi ba"a cewar Umaima

"Yana wajen ubanshi,da yake na yaye shi"ta ƙarasa faɗa tana ficewa daga ɗakin,su Umaima suka biyo bayan ta

A bakin motar ta suka same ta tana ƙulle showel ɗin da ta ɗauko,sosai take tausayin yaran saboda bata da wasu kaya masu yawa,hulunan ta guda biyu ne kacal,kuma su ma ba masu kauri ba,rigar sanyin ta guda ɗaya ce,ta dubi umaima tace"muje kasuwa kawai,akwai abinda nake son siya"babu musu suka wuce kasuwar a ƙafa,don babu nisa

Suna shiga kuwa sukayi Sa'ar ganin shagon kayan sakawa na manya da na yara,kai tsaye Deeja ta nufi can ta siyo kayan jarirai da diapers masu yawan gaske,sannan ta siyo dogayen riguna da undies sannan suka fito,cefane sukayi mai kyau,duk yadda Umaima ta so biyan kuɗin Deeja bata saurare ta ba ta biya,suka ɗebo kaya niƙi-niƙi sukayo gida

Shinkafa jollof da kifi Umaima ta dafa musu, sai haɗiyar yawu takeyi don zata iya cewa rabon ta da kifi ta manta,bayan ta gama ta ɗora ruwan wankan little Deeja a ɗan murhun

Bayan Isha'i bayan sun gama cin abinci Deeja tayiwa little Deeja wanka ta sanya mata ɗaya daga cikin sababbin kayan sanyin da ta siyo mata ɗazu har da hula da safa,ɗan ƙaramin baby net ɗin da ta siyo ta buɗe ta sanya ta a ciki,don dama ƴar ƙarama ce sosai,watan ta huɗu amma ko wata ƴar wata biyun ta fita girma, Deeja ta lulluɓe ta tana tapping bayan ta a hankali har bacci ya ɗauke ta,tayi mata addu'a ta tofe tada ita ta mayar da net ɗin ta rufe ta ɗago tana kallon su Afra da Umaima da suka zuba mata idanu suna kallon ta

Murmushi tayi tace"ina matuƙar son ƴa mace,amma na godewa Allah da ya bani namijin ma,yanzu gashi na kuma samun macen"Umaima tana murmushi tace"idan zaku tafi ki tafi da ita na bar miki,nasan zatafi samun ingantacciyar rayuwa a hannun ki fiye da hannu na"Deeja tayi murmushi kawai

"Bayan wasu mintuna Deeja ta kalli Umaima ta fara magana cikin kwantar da murya"Umaima,da ace Imran baya buƙatar ki a rayuwar shi da saki uku zai yi Miki kamar yadda yayi min,ranshi ya ɓaci ne,amma har yanzu yana sob ki,irin soyayyar da Imran yayi miki I don't think it can be vanish a dare ɗaya,sannan ki goge dukkan abinda ya faru,ki ɗauka irin taki kaddarar kenan,baki san abinda Allah ya rubuta miki ba,don haka gobe tare dake zamu koma,akwai sabuwar rayuwar da take jiran ki a Kano,da ke da takwara ta"

Umaima ta girgiza kai tace"Deeja ki barni kawai na cigaba da rayuwa ta anan,bani da inda yafi nan"

"Wannan ba mai yiyuwa bane Umaima,ko kinji daɗin rayuwar da kikayi har haka da kike fatan ta wa ƴarki?ko kinsan abinda zai faru gobe?so kike itama ta tashi tana jin haushin ki kamar yadda kike jin haushin magabatan ki?"

A sanyaye umaima ta girgiza kai tace"a'a, idan zaku tafi ku tafi da ita,ku tambayi baban ta idan yana so sai ku bashi,idan baya so kuma na bar miki"

Duk da cewa jikin su a sanyaye yake sai da suka kama dariya, Deeja tace"umaima akan takwara ta nake magana fa,ba jaka ko ɗan kunnen ki ba"Umaima ta wara idanu tace"na sani mana,nima akanta nake magana"suka ƙara fashewa da dariya, Afra har da riƙe ciki, Deeja tace"lallai na yarda da abinda ake cewa akan ɗan fari,amma a hakan kuke cewa kun fi mu wayo"itama Umaima dariya tayi tace"kema kinsan ƴan fari sun fi auta wayo"Deeja tace"ga evidence na gani"daga nan suka shiga tsokanar juna suna dariya,soon ta manta da damuwar da take ciki

Washegari da safe Deeja ta kalli Umaima fuskar ta babu wasa tace"Umaima ki haɗa dukkan ababen ki masu muhimmanci,zamu wuce Kano in less than one hour"

Kallon ta Umaima tayi,zatayi abinda ta saba wato musu,amma ganin yadda Deeja ta ɗaure fuska alamar ba wasa sai tayi shiru,a sanyaye ta janyo jakar Ghana must go ɗin ta ta fara jera kayayyakin ta, wadanda duk yawanci na little Deeja ne,Afra ta taimaka mata, Deeja kuma ta shirya little Deeja ta goya ta

Bayan sunyi wanka Deeja ta fito da dogayen rigunan da ta siyo,ta ɗauki ɗaya ta basu ɗaiɗaya,ta Deeja light blue,tayi mata kyau sosai,ta hau sosai da chaculate skin ɗin ta,ta Afra blue Black ce, kasancewar tafi Deeja haske itama Tata tayi mata kyau,ta Umaima maroon colour,Wai don ma yau da taɓa ta fatar tayi ɗan duhu,amma da yake kyan na nan da ta shirya sai gata ta fito a umaiman Imran ɗin ta, Afra tace"awwwn!naga manyan mata anan", Deeja tayi murmushi tace"dama kyan akwai wanda aka adanawa na Musamman,sai yanzu zai bayyana"Umaima tayi murmushi tana girgiza kai tana ƙoƙarin ɗaure dogon gashin ta

Yau da shagali🤗 Deejan Khalees da umaiman Imran sun haɗe kai sun bar mu🥺oho dai mu ma biye muku zamuyi mu haɗe kai🙈

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 37

Wajen ƙarfe goma na safe suka fito don tafiya gida,babu yadda Deeja batayi da Umaima ba tayiwa mutanen gidan sallama ba amma taƙi,da ta matsa mata ma kuka ta fashe mata dashi,sai kawai ta ƙyale ta,ta saɓa little Deeja a kafaɗa,wadda tayiwa kwalliya da overral ta ɗora mata doguwar riga mai kyau da hula har da Safa,ta lulluɓe ta da sabon showel,fari tas sai ɗaukan idanu yake

Tafiyar awanni uku da rabi ya kawo su kano,kai tsaye ƙaton shopping mall suka nufa,anan su Afra suka ga yadda ake haukar siyayya,ashe ba komai Deeja tayi a taura ba,don sai ta ta cika Boot taf da kayan little Deeja masu tsada,da kayan wasa,na Umaima da ta siya a backseat ta zuba su,ta fara biyawa gidan fauwaz ta sauke Afra sannan ta ɗauki hanyar gidan ta na Na'ibawa

A falo suka zube suna hutawa, Umaima sai kallon gidan takeyi don ya burge ta sosai,Deeja ta miƙe ta shiga kitchen ta samo musu drink ta zubo akan ɗan plate da glass cup ta kawo ta zuzzuba musu a cup

Suna sipping a hankali Deeja ta kalli Umaima tace

"Nan gida na ne,zaki zauna anan,duk abinda kike buƙata zan saka a kawo,ranar asabar idan Allah ya nuna mana zan kawo miki wadda zata taya ki zama da aikace-aikace,that same day kuma zan kai ki islamiyya ki cigaba da karatun kina addini,ranar Monday kuma in Sha Allah zan kai ki don kiyi registration na JAMB"

Umaima ta buɗe baki da zummar yin magana kuka ya kubce mata,cikin kuka ta fara magana

"Deeja ban san da me zan biya ki ba,haƙiƙa a dukkan rayuwa ta babu wanda yayi min rana ya sanya na ji Ni a mutum kamar ki,na gode Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Ta sauko daga kan kujerar da take zauneta durƙusa ta kama ƙafafun Deeja,wadda tayi shiru kawai tana kallon ta,tace

"Don girman Allah Deeja ina roƙon ki ki yafe min abinda nayi miki,don Allah ki roƙar min yafiyar Imran da duk wanda na cutar,na...."Deeja ta toshe mata baki tana girgiza kai cikin ɗaure fuska tace"indai kin san idan nazo kuka zaki rinƙa yi min gwara ki gaya min kar na sake wahalar da kaina na dawo"da sauri ta share hawayen ta tace"na daina in Sha Allah"Deeja ta ɗan yi murmushi ta dafa kafaɗar ta tace"don Allah ina so ki manta da duk abinda ya faru a baya kiyi facing new life ɗinki,ki ɗauke ni a matsayin yayar ki da kuka fito ciki ɗaya,wadda a kowane hali sai dai ta ƙaurace miki na ɗan lokaci,amma bazata guje ki ba,don haka ki kwantar da hankalin ki ki manta da baya,ki goge shi a ranki,you are starting a new life,wadda a cikin ta babu Najeeb,babu Nadiya,babu talla,babu ƙuncin rayuwa,babu kaɗaici da kewa,in Sha Allah very soon komai zai wuce"tana gama magana tayi mata side hug ta miƙe ta ta ƙarasa kan two sitter da ta kwantar da little Deeja, yarinyar sai kallon juyawar fanka takeyi tana ƴan wasannin ta,babban ɗan yatsan hannun ta ta zurmuƙa shi a baki, Deeja ya durƙusa tana shafa fuskar ta tana murmushi tace"to Angel,zan tafi,i will miss you so much, much luv sweetheart"tayi kissing ɗin ta a goshi da kumatu,sai wulla ƙafa takeyi tana dariya, Deeja ta waiga ta kalli Umaima tana murmushi tace"to maman takwara,sai Saturday"bata jira amsar ta ba tayi sauri ta fice ganin umaiman tayi wani irin sanyi

Ai kuwa ranar asabar ɗin Deeja ta dawo da wata mace dattijuwa,zata kai 47-48 years, sannan ta ɗauki umaima suka je wata makarantar matan aure,ta gama mata komai suka dawo gida

A ranar ta sa aka ƙaro kayan abinci masu yawa,sannan ta bawa Umaima tsadaddiyar waya da makullin tsadaddiyar mota, Umaima bata taɓa tsammanin zata sake tuƙa mota a rayuwar ta ba,duk yadda taso kar tayi kuka ta kasa sai da ta fashe da kuka tana rungume Deeja ta kasa magana, Deeja na goge mata hawayen tace"ki shirya jibi zakiyi registration ɗin JAMB"

Umaima ta ƙara goge hawayen ta tace"amma lokaci bai ƙure min ba kuwa?ina nufin a karatun"

Deeja tace"shekarun ki nawa?"Umaima tace"I'm turning 25 next month"wani kallo Deeja tayi mata tace"dudud nawa kike,har ƴan 60 years ma karatu sukeyi ballantana ke haihuwar kwanan nan,c'mon malama ki koma makaranta,don wannan karatun shine best pride ɗin ki,kar ki kuskura kiyi wasa da opportunity ɗinki na karatu"Umaima ta gyaɗa kai cikin sanyin jiki ta kama hannun Deeja tace"na gode sosai, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"Deeja bata daɗe sosai ba tayiwa umaima sallama ta tafi bayan ta gama wasa da takwarar ta,amma ta dawo ranar Litinin,a motar umaiman suka je sukayi registration na JAMB

Satin Umaima uku a Kano aka mayar da auren Deeja da Khalees, Deeja ta zama MATAR KHALEES a karo na biyu,ita da Khalees cike suke da farin ciki don wannan shine auren su na farin ciki a iya tsawon rayuwarsu,an sha shagali sosai,su Mima suka miƙa ta sabon gidan mijin ta da ya siya a state road

Satin su biyu da aure suna shan soyayyar su Aunty nusaiba ta dawo musu da Affan,mijin ta da yazo ya saka su gaba ita da yaran ta suka koma US, Deeja tayi kewar su sosai

Watan ta uku da aure tana zaune a parlourn ta tana duba wasu files da zatayi submitting gobe a Company ɗin su,don tuni ta koma companyn su ta cigaba da aiki

Ji tayi an rungume ta ta baya,ta san Khalees ne,ta ɗan yi murmushi tana faɗin"sannu dai

Please Login or Register in order to submit comment