Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu yaya zan yi da su Farida?"

Da sauri ya kalle ta cikin mamaki,yace "su Farida mana"

"Eh su Farida mana"ta bashi amsa tana kallon shi

Cike da mamaki ya gyaɗa kai sannan yace"to nono zaki basu kenan?"

Kallon shi tayi cikin mamaki tace"a'a ba batun haka bane,bei dace ace mun bar su a gida ba su kaɗai, Hajiya ma bazata ji daɗi ba,amma idan babu matsala sai in tafi ɗin"

"Babu"ya bata amsa a taƙaice,sannan ya juya ya kwanta,itama kwanciyar tayi,duk da ba bacci takeyi ba,kawai nazarin rayuwa takeyi

Washe gari basu tashi daga bacci ba sai da ta kammala girki,tana ji Khalees yana tayi musu faɗa,ita dai sauri takeyi don ta tsani makara a rayuwar ta,kunun gyaɗa ta dama da ƙosai sai plantain da miyar ƙwai,sai wainar ƙwai da chips,sai ruwan Lipton

Ko da Khalees baya yaba mata a fili,yana matuƙar jinjina baiwar iya girki, tsafta da hikima da Allah ya bata,gashi sam bata gajiya, kullum cikin hidima dashi take ko da ace zai kashe ta kuwa

Suna cikin cin abincin ya kalli Farida yace"yau ƙarfe nawa kuke da lecture?"ta amsa"nine zamu shiga lecture"

Ya kalli Jannat yace"ke kuma fa?"

Ta amsa "by 12:pm"

"Good!"ke Farida, kafin ki fita daga gidan nan ki tabbatar kin gyara wajen nan ki wanke kwanuka,ke kuma Jannat ki tabbatar kin yi girkin rana kafin ki bar gidan nan,okay?"

Hukuncin nashi yayi masifar bawa Deeja mamaki,amma sai tayi kamar bata sauraron su,sai cin abincin ta takeyi a nutse, lokaci lokaci tana kallon haɗaɗɗen agogon hannun ta gudun kada lokaci ya ƙure, Farida da Jannat suka dubu juna cikin tsananin kaɗuwa da al'ajabi,sannan suka kalle shi a tsorace,suna raya ya raina musu hankali ma,ya ɗebo su daga gaban Hajiya,don kawai ya basu wahala

Farida itace tayi magana cikin rawar murya"yaya ina da excuse"

"Wanne excuse kenan?"ya tambaya batare da ya kalle ta ba

"Zamuyi group meeting yau kafin mu shiga lecture,Kuma rashin halartar shi zai iya jawo min matsala"

Shiru yayi yana cin abincin shi a nutse,ita kuwa Farida addu'a takeyi a ranta Allah ya sanya ya bar ta ta fita amma ina! addu'ar ta bata karɓu ba,don cewa yayi

"A haƙura da group meeting ɗin,tunda anayi,kuma watarana ma za'a ƙara yi, shikenan ko?"

Shiru Farida tayi tana cika tana batsewa,dama ita Jannat ta daɗe da sanin halin yayan nasu,,kaifi ɗaya ne,idan ya faɗi abu,to abun yake nufi , shiyasa bata tanka ba

Deeja kam shiru tayi tamkar bata san me yake wakana ba,tana kammala cin abincin ta ta ɗauki jakar ta gami da yi musu sallama ta fice daga falon

Ranar bata dawo da wuri ba sai wajen la'asar, Saboda meeting da sukayi,a falo ta same su a zaune sun cika sun batse,falon kaca-kaca ta ko'ina,koda tayi sallama ma babu wadda ta amsa,sai Farida da ta kalle ta cikin fitsara tace"Malama har da zuwa a wani daɗe saboda kin bar bayi ko?to ga gidan ki nan,ki gyara abinci,girki kuma iya mu yamu muka yi,don haka ruwan ki ne kiyi abinda ya dace ruwan ki ne ki bari"

Ko kallon banza bata samu daga wajen Deeja ba,hakan ya ƙona ran Faridan, Deeja bata kula ba ta shige ɗakin ta

Wanka tayi ta ɗauro alwala don yin Sallah,tana shirin tada kabbarar Sallah kenan ta jiyo faɗan Khalees akan rashin gyara gida da basuyi ba,bata kula ba ta tayar da sallar ta,sai dai tana jin irin rashin mutuncin da yakeyi musu da dukan da yayi musu,cikin sauri ta idar,da gudu ta nufi falon tana faɗin"I'm sorry Khalees,nice nace su bari zan gyara fa"

Khalees ya kalle ta na wasu daƙiƙu,bei ce komai ba ya juya ya bar falon,itama Deeja haka ko badan komai ba,ta bar falon don watsatstsen kallon da suke jefa mata

Haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tsawon kwanaki shida, gaisuwar arziƙi bata haɗa su da su Farida,shi kuma Khalees ya kallafa musu yin aikace-aikacen gidan idan suna gidan

Ganin wahalar bazata ƙare ba ne ya tilasta musu guduwa, Hajiya na zaune sai kawai taga sun shigo,ta sha mamaki ƙwarai da gaske,don da kansu suka yanke shawarar komawa gidan ɗan'uwan nasu,da ta tambaye su dalilin dawowar tasu suka ce sun gaji da wahalar da yaya Khalees yake basu, Hajiya bata matsa musu ba,don dama su suka so komawar

Tafiyar su Farida ya faranta wa Deeja ba kaɗan ba,a ƙalla ko ba komai ta samu sakewa,kuma ɓacin ranta ya ragu,domin shi Khalees ta sani in dai ba harkar shi ta shiga ba ranta bazai ɓaci ba

**** **** ****

Ƙarfe biyar na yamma suka ji announcement na cewa jirgin su ya sauka,cikin nutsuwa suka sauko daga jirgin,ɗauke da kyawawan yaran su Mee'ad da muneeb,kai tsaye waje suka nema suka zauna, sannan ta kirawo aunty Bintu tare da shaida musu isowar su, aunty Bintu tace gata nan

#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 5

Cikin abinda bei wuce mintuna sha biyar ba aunty Bintu da babbar ƴar ta intisar mei kimanin shekaru goma sha bakwai suka iso, cikin murna mai yawa intisar ta rungume meema tana faɗin"wow! aunty meema you are highly welcome, gaskiya munyi missing ɗin ku da yawa"ta dubi hafeez fuskar ta ɗauke da murmushin farin ciki tana faɗin"uncle hafeez yau a gari?ai munyi tsammanin mutanen Malaysia sun riƙe mana kai"

Ɗan murmushi hafeez yayi sannan yace"ina!kuna raina intisar,kawai time ne baya samuwa,amma kuma ai auntyn ku tana zuwa ko?"

"Eh haka ne,to yanzu dai kuzo muje gida, Mamie na ta shirya muku delicious and wonderful dish"

Mima ta wuce gaba tana faɗin"kuzo muyi sauri,a gajiye nake ni"suka ɗunguma suka shiga motar,aunty Bintu taja suka tafi gida

Basu samu damar zama cin abincin ba sai da sukayi sallar maghriba,suna cin abinci suna hira,anan aunty Bintu ta sanar dasu batun auren Deeja

Cikin madaukakin mamaki Mima tace"kamar a mafarki?Deeja tayi aure kullum mukanyi waya ko chat amma ta kasa sanar dani?"

Aunty Bintu tace"kin santa da zurfin ciki,kuma ina zargin akwai matsala ne,duka duka fa kwananta arba'in da shida da yi mata aikin zuciya akayi mata auren fa"

Hafeez ya gyaɗa kai yace"lallai babu mamaki,to ina tsohon mijin nata?"

Aunty Bintu tace'yana nan"

Kuma suna haɗuwa dashi?"a cewar Mima tana tsare ta da ido

"Sai dai idan bataje gidan Mamie babba ba,kuma bikin a gidan mamien za'a yi"a cewar aunty Bintu

"Yayi aure ne?"hafeez ya tambaya

"Tun kafin su rabu da Deeja "a cewar Mima"wata fitsararriya mara kunya mara tarbiyya"ta ƙarashe maganar tana yatsina fuska

"Ke Mima!ina raba ki,a ina kika san bata da tarbiyya?"a cewar aunty Bintu

Murmushin takaici miman tayi tace"a bar maganar kawai aunty"daga nan suka sauya wata hirar

A ranar Mima ta kira Deeja ta sanar mata da saukar su,ihun murna ta rinƙa yi,tace"oh!leemo nayi missing ɗinki da yawa,ina my baby Mee'ad?"

"Tana wajen abban su ita da munib"

"Yayi kyau,to yaushe zaki ƙaraso?"

"Oho miki,mara mutunci kawai,kiyi aure amma ki kasa sanar dani?"

"Uhm!"da story sosai Mima,sai mun haɗu kawai,yaushe zaki zo?"

"It is better mu haɗu a gidan bikin, saboda abban Mee'ad ya matsa min gobe,jirgi zamu bi zuwa azare,don mu gaida ammin su"

"Okay,babu matsala, yaushe zaku dawo?"

"Jibi in Sha Allah,Kuma a gidan bikin zan sauka"

"Okay babu damuwa,Ni da gobe nace zan je,amma yanzu na fasa sai jibin"

"Haba ke kuwa,meyasa?"

"Mu haɗu a jibin kawai,da stories"

"Okay Allah ya nuna mana da alkhairi"

"Ameen"sukayi sallama

A ranar Deeja cikin farin ciki ta kwana,walwalar ta ta bawa Khalees mamaki ƙwarai, saboda irin tarin matsaloli da ta tsinci kanta a ciki basa bata damar yin walwala kamar kowanne mutum,amma sai sabgar ta takeyi cikin farin ciki,shi kuma Khalees jin kai irin nashi ya hana shi tambaya

Washe gari da safe daga office Kai tsaye wajen kitso da ƙunshi ta nufa,ai kuwa aka tsantsara mata kitso, dogon baƙin gashin ta ya amshi ƙananan kitson,lalle ja da baƙi ya amshi chaculate fatar ta,tayi kyau sosai ga wani haske da ta ƙara a ƴan kwanakin nan

A ranar bata koma gida ba sai shida saura ƴan mintuna,tun sanda mai gadi ya wangale gate ta hango khalees yana ta faman Safa da marwa, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,amma ganin shigowar motar ta sai ya tsaya cak yana kallon ta batare da yace uffan ba, fuskar shi har yanzu a ɗaure take

Kai tsaye parking space ɗin gidan ta nufa bayan ta daidaita parking ɗin motar ta fito tana ɗan satar kallon Khalees ɗin,ko uffan ba tace ba tayi nufin wucewa cikin gidan

"Daga ina kike?"

Batare da damuwa ba ta bashi amsa,"naje kitso da ƙunshi ne"

"Shine sai yanzu?"ya faɗa da ɗan ɗaga murya

Ganin hankalin mutanen da suke yiwa gidan hidima ya fara dawowa kansu ya sanya ta furta"I'm sorry"da sauri ta wuce cikin gidan

Ta fito wanka ta ganshi a bakin gado,har yanzu fuskar shi babu walwala,hakan bai dame shi ba,ta zauna a gaban madubi ta fara gyara kanta,sai yanzu Khalees ya ƙare mata kallo ganin tayi kyau sosai,amma duk da haka bai fasa faɗar abinda ya kawo shi ba

"Ban amince ki rinƙa zuwa ko'ina kina haura la'asar a waje ba,idan haka ta kuma faruwa rai zei ɓaci"bei jira amsar ta ba ya miƙe ya fice daga ɗakin

Wayar ta ta ɗauko daga jakar ta,miscall shida ta gani,shaf ta manta cewa ta sanya ta a silent,duk misscall shidan Khalees ne,a fili ta furta "oh!wato jin kai bazai bar shi yace"ya kira ni ban amsa ba ko?"

Washe gari ta kama juma'a,kuma a ranar zata tafi gidan bikin,sai zumuɗi take tayi,Khalees yana kwance yana kallon yadda take ta farin ciki, gaba ɗaya sai yaji ya shiga damuwa,wato farin ciki takeyi Saboda saboda zata nisance shi?"

Da yaga zumuɗin yaƙi ya ƙare sai yace"Malama haukan ya isa haka,idan kika matsa ma wallahi sai na hana ki"

Kallon shi tayi cike da mamaki,ganin ya ɗaure fuska ya sanya ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda takeyi, zuciyar ta cike da mamakin shi

Ƙarfe bakwai da mintuna arba'in ta kammala shirya komai,a lokacin tuni Khalees ya wuce wajen aikin shi,ta loda akwatunan ta a Boot taja motar ta ta nufi wajen aikin ta

Sha ɗaya da minti bakwai wayar ta ta fara ƙara,tana dubawa,sunan Mima ta gani,da sauri ta ɗaga tana faɗin"sister leemo ya?kun sauka lafiya?"

"Lafiya lau sister deejo,mun dawo fa"

"Da gaske don Allah?"a cewar ta cikin farin ciki

"Wallahi kuwa,yanzu haka ma gamu a airport,aunty Bintu zata ɗauke mu"

"To Allah ya iso daku lafiya,Ni ina wajen aiki"

"Okay to mu haɗu a can ɗin kawai"

#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 6

Sha biyu daidai Deeja ta tashi daga aiki,kai tsaye sardauna crescent ta nufa cikin unguwar Nassarawa GRA,in da gidan professor Ismail yake, kai tsaye gidan ta nufa,horn ɗaya daya tayi mai gadi ya leƙo yana ganin itace yayi mata sannu da zuwa,suka gaisa cikin mutunci,tayi masa alherin da ta saba yi masa sannan ta shiga cikin gidan

A makeken tempol ɗin gidan ta ajiye motar ta cikin jerin tarin motocin da ke cikin tempol ɗin,ciki har da motar Imran da Mima,da alamu dukkan su suna nan kenan

Bata damu ba ta nufi sashen Mamie don su gaisa,da sallama ta shiga,su huda da yusra da ke falon suka miƙe suka rungume ta suna murnar ganin ta,da ƙyar suka ƙyale ta,ta gaida da Mamie da kuma mummy Aysha,da fara'a suka amsa mata sannan ta yada zango suka cigaba da hira

** ** **

Ita kuwa Mima aunty Bintu ce ta ɗauko su ita da yaran ta,kai tsaye gidan professor Ismail ta kawo su,shi hafeez bai taho ba, Saboda yana da uzururruka a can,sai ranar ɗaurin aure zai zo

Bayan sun gaisa da Mamie sai ta kira afra take shaida mata isowar ta,cikin azama afra ta shigo ta rungume ta cikin murna taja su sashen ta,a can ta shirya musu abinci lafiyayye ,sosai Mee'ad da munib suka burge afra,cikin rawar jiki ta kira haneef tana fadin"haneef,zo ga aboki nayi maka"yaron ya shigo falon da sauri yaja munib suka nufi wajen wasan shi

Sun kwashi mintuna suna hira ,a ƴar hirar da sukayi Mima ta fahimci cewa afra mace ce mai surutu da rawar kai,don a hirar su ta fahimci cewa matar yaya fauwaz ce,kuma da alamu akwai aminci mai ƙarfi tsakanin ta da umaima,don haka gaba ɗaya taji batayi mata ba,don haka tace "bari naje mu gaisa da mutanen gidan ko?aunty kiyya tana nan kuwa?"

Sai walwalar Afra ta ɗauke,ta ɗan taɓe baki tace"suna main parlour Ina ga,muje can"Mima batayi musu ba suka wuce zuwa babban falon

A can suka haɗu da da su lubaisa,kiyya da nuwaira,sai aunty salma da aunty nafisa,sai minal da itama zuwan ta kenan,sai umaima

Sun gaisa da kowa, cikin mutunci,umaima da kuma suka fara kallon kallo, Afra tace "sisto ga ƙawa ta Dr halima azare"

Murmushi Mima tayi tace "nice to meet you umaima"ta miƙa mata hannu sukayi musabaha

"Na gode,ya gida?"ya mei gida da yara?"inji umaima cikin sanyin jiki

"Kowa lafiya,ya naki mai gidan?"

"Lafiya ƙalau,,a cewar umaima"Mima tace"good haka ake so"bata jira cewar umaima ba ta ja hannun kiyya suka bar falon suka nufi sashen kiyyan

A can Mima ta zube a kan kujera,ta dubi zakiyya tana fadin"aunty kiyya Ina yara na ne?ban gansu ba"

Zakiyya tace"Islam da Hisham suna makaranta,shi kuma Aisar babbar ƴar aunty rahama ta ɗauke shi"

"Yayi kyau"a cewar Mima,ta ɗan yi shiru,zuwa can ta kalle ta tace"aunty kinji sisto tayi aure?"

"Na sani wallahi,amma bamu samu halartar auren ba,wani irin aure ne kamar taron mutuwa"

"Akwai matsala kenan ko?"a cewar Mima

"Babu mamaki,amma sai tazo sai muji ta bakin ta"

"To Allah ya kawo ta lafiya"

"Ameen"

Haka suka cigaba da hira akan Deeja,sun ɗan juma kafin su miƙe su nufi main parlour

Mima na kula da kallon da umaima da lubaisa sukeyi mata lokaci lokaci amma tayi banza dasu, Afra kam sai zaƙewa takeyi akan miman,a ƙoƙarin ta na samun shiga fiye da zakiyya

Deeja ce tayi sallama ta shigo, hankalin su ya koma kanta, Mima tayi tsalle ta rungume ta suka fara ihun murna,zuwa can suka saki juna suna haki da dariya, Deeja ta kalli Mima tana dariyar murna tace"sister leemo! gaskiya Malaysia ta amshe ki,kinga yadda kikayi fresh kika ƙara kyau?ko dai munib ya samu ƙani ko ƙanwa ne?"

Dariya Mima tayi gami dukan kafadar ta tace"ai ke za'a yiwa wannan tambayar sister deejo,don Allah aunty kiyya taya Ni dubawa , yarinyar nan batayi ƙiba da haske ba?da alama engineer Abdul yayi ajiya"

Gaban Deeja ne ya bada dam!har sai da hakan ya so ya bayyana akan fuskar ta,don dama kwanan nan tana zargin hakan saboda rashin ganin al'adar ta,ga yawan kwaɗayi da ta koya,amma da yake jaruma ce ta dake tare da faɗin"ji sharri,ko don na rafko ki zaki wayance?"

"Aunty kiyya tace"wane sharri kuma?da gaske take wallahi,ko dai Khalees ya iya kiwo ko kuma yayi ajiya,cikin biyu ɗaya"

Dariya sukayi su duka, duk da cewa Deeja ta yaƙe tayi,ta nemi waje ta zauna tana faɗin"ke dai aunty kice ta Baki cin hanci ne kawai"

Su Afra kan mamaki ne ya ƙamar dasu,yaushe Deeja tayi aure?Nuwaira ce ta kasa jurewa ta kalli aunty kiyya tace"Aunty kiyya dama Deeja tayi aure ne?"

Mima da Deeja suka kalli juna a tare da sannan suka kalli nuwairan,Mima ce tayi caraf ta amsa da cewa "eh tayi aure,watanni huɗu baya ma,da mamaki ne a cikin ikon Allah? "

Cikin sanyin jiki nuwaira tace"babu kam, Allah ya sanya alkhairi"

"Ameen"in ji aunty kiyya,ita dai Deeja tana jin su,sai ma danne dannen waya da ta fara don ta nuna musu rashin muhimmancin nuwairan a wajen ta

Mima ce ta janye hannun ta tana fadin"zo muje sashen aunty kiyya muyi sallar la'asar, gashi can an fara kira"babu musu ta miƙe,itama Aunty kiyyan ta miƙe suka nufi sashen nata

A can bayan sun idar da sallah Mima da zakiyya suka sanya Deeja a tsakiya, Mima ta dube ta cikin damuwa tace"sisto me hakan ke nufi?"kaf family baki da kamar Ni da aunty kiyya Amma auren ki sai ji mukayi a gari,me hakan ke nufi?"

Shiru Deeja tayi zuciyar ta tana suya,da tana da saurin kuka da tayi ta samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar ta takeyi,amma ina! bata iya saurin kuka ba,ta dube su tace"aure na da kuke gani ban yi shi a mood na farin ciki ba,asalima har na auri engineer Abdul bansan shi bane,kuma wannan hasarar da kuka san shi da ita bai chanja ta ba,,ga mahaifiyar shi da ƴan'uwan shi da basa so na ko kaɗan,a haka mukayi auren duka duka ko kwana hamsin ban cika ba aka ɗaura mana aure dashi,har kwanan yau daurewa zaman gidanshi nakeyi kawai"

Shiru sukayi suna kallon yanayin ta ya sauya,alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta,Mima ta dafa kafadar ta cikin kwantar da murya tace

"Ki cigaba da haƙuri my Deeja,komai yayi farko zai yi ƙarshe,ki cire duk wata damuwa a ranki komai yayi tsanani yana tare da samu sauƙi in Sha Allah,shi kuma mijin ki ki cigaba da yi masa biyayya in Sha Allah zaki ga ribar abin"


#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 7

Zakiyya ma ta ƙara da faɗin"in har kika jure kika cigaba da kyautata masa babu dare babu rana ina mei tabbatar miki da cewa shi kanshi ba zei san lokacin da zai fara son ki ba,duk da cewa mijin ki mutum ne mai wani irin ra'ayi, ba'a tantance gaban shi da bayan shi,amma ai mutum ne shi,yana da zuciya,kuma namiji ne ko ba haka ba?

To kamar yadda na sanki baki da saurin fushi ina so ki daure ki cigaba da hakan,wannan shariya da ƙyaliyan ki ajiye su a gefe, Khalees mijin ki ne yayanki ne,ginshiƙin ki ne,kinga yanzu babu in da mama da Abba"

Kalaman kiyya na ƙarshe sunyi matuƙar tasiri wajen karya zuciyar Deeja,wato babu idanun mama da Abba,tunowa da shuɗewar gatan nata ya sanya ta fashewa da kuka cikin tausayawa,su Mima suka rinƙa tausar ta suna bata baki har ta daina kukan

Kasancewar ta tare da Mima da kiyya ya sanya damuwar ta ta kau,ga yusra da Huda ƙannen Imran da suke uwa ɗaya uba ɗaya,su kam suna matukar son ta,har ta kan ji dama ace suma ƴan uwan Khalees haka suke son ta.

Sun haɗu da su Imran ɗin a falon Mamie babba,bata nuna musu komai ba ta gaishe su cike da girmamawa a matsayin su na yayyen ta,Yaya fauwaz ya kalli Mamie yace"Mamie, Deeja fa wannan abokin Imran ɗin ne ya aure ta"

Gaban Deeja ya buga da ƙarfi,abokin Imran?tana jin momy na cewa "wanne abokin nashi?"

"Engineer abdurrashid mana, Khalees,wanda sukayi secondary tare kin gano shi?"

"Au!tooooo!!na gano shi, Allah ya sarki,yaron kirki kuwa,ashe shi ta aura"a cewar Mamie fuskar ta cike da fara'a

"Shi ta aura Mamie"Yaya fauwaz ya tabbatar mata

"To Allah ya sanya alkhairi"

Suka amsa da "ameen"

Miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita,cikin rashin sani idanun ta suka sauka akan imran,ai kuwa tayi amfani da wannan damar ta zabga Masa harara,ai kuwa ya sunkuyar da kanshi, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,hakan bai dame ta ba tayi saurin barin falon

Washegari ta kama asabar,a ranar ne aka fara biki, kiyya da Mima da Deeja sun ɗau wanka cikin lace Pink mai ratsin red flowers,wannan tsarabar Mima ce a wani zuwa Switzerland da tayi ta gano su ta siyo har da aunty Bintu da intisar,ai kuwa sunyi matuƙar haskawa a wajen party ɗin

Washe gari ta kama ranar ɗaurin aure,su Deeja ana ta hidima da baƙi,ga wankan da suke ɗauka tamkar amare ita da su Mima,kuma tunda Mee'ad ta ganta ta daina yarda da kowa,gata da farin jini amma ta dage ita sai Deeja kaɗai

Rashin son abincin da yawan kasalar da Deeja ke fama da dashi ne ya sanya zargin ta ƙaruwa,amma bata son tabbatar da hakan saboda bata san da wanne ido zata dubi Khalees da batun cikin ba,tun da a iya sanin ta baya son ta,to ta yaya zai so haɗa zuri'a daita?amma ta yanke shawarar tuntuɓar likitar ta Dr su'ad bayan biki don ta tabbatar cikin ne ko akasin hakan

Su Afra ne ita da umaima da wata ƙawar umaiman nadiya suka jero suka fito falon Mamie

Nadiya ce tayi saurin taɓo umaima tace"umaima!kinga wani handsome guy!da sauri umaima ta ɗago kai don ganin waye

Mutum biyu ta gani,wani guy da bata san waye ba sai mijin ta Imran,nan da nan kishi ya turnuƙe ta tace"to ƙwalelen kare da hantar kura,miji na ne"

Da sauri nadiya ta dafa kafadar ta tace"I'm sorry friend!ba shi ba fa,na kusa da shi"sai a sannan umaima ta ƙare wa na kusa dashi ɗin kallo

Wankan tarwaɗa ne,dogo mai ƙirar ƙarfi, kyakkyawa ne sosai,sai dai da alamu zai yi jin kai yana sanye da shadda,sky blue,ɗinkin yayi matuƙar kyau sosai,ɗan murmushi tayi tace"good,ina taya ki murnar wannan babban kamun,zan Miki hanya daga wajen mai gida na"cikin murna nadiya ke faɗin"na gode sister na"

An kammala biki lafiya,an kai amarya gidan mijin ta lafiya,washe gari ta kama Litinin daga wajen aiki kai tsaye Deeja gida ta wuce, zuciyar ta cike da tsoron wane sakamako zata gani game da zargin da takeyiwa kanta

Bata samu Khalees a gida ba,batayi mamaki ba don tasan bai ci ace ya taso daga wajen aiki ba,don haka wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa tayi kyau sosai,bata nemi abinci ba duk da yunwar da takeji,don ji tayi tana sha'awar alala,don haka tayi sauri taje inda zata je ta dawo akan kari

Asibitin Dr su'ad ta nufa, cikin Sa'a ta same ta da murmushi akan fuskar Dr su'ad ta dube ta tana faɗin"a'a!matan manyan injiniyoyi!kuma manyan akawuntoci,yau kune a asibitin namu?"

Murmushi Deeja tayi tace"mune wallahi,ya akaji da aiki da fama da jama'a?"

"Jiki alhamdulillah!ya ƙarin ƙarfin jikin?"

"Jiki alhamdulillah,mun samu afuwa"a cewar Deeja

"To Allah ya sa dai ba shine ya tashi ba ko?"

Deeja ta girgiza kai tace"ko ɗaya, dama suspecting nakeyi, Kamar ciki gare ni shine nazo kiyi mini test"

Cikin farin ciki Dr su'ad tace"Allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi,naga yaran Madam Deeja da angon ta abdurrashid"murmushin yaƙe kawai Deejan tayi

Dr su'ad tayi ƴan gwaje-gwajen ta inda ta tabbatar wa da Deeja zargin ta, Deejan tayi godiya ta ajiye mata kuɗin ta ta tafi

Tana shiga Mota ta kira safeena ƙawar ta, safeena na ɗagawa bata saurari komai ba tace"feena ya ma sunan maganin da kikayi amfani dashi kikayi abortion?"

Cike da mamaki feena tace"abortion kuma? abortion zakiyi ne?haba Deeja,ko nima a lokacin ƙuruciya ce ta ɗebe ni,kuma naga babyn da na haifa baiyi ƙwari ba,shiyasa"

"Wait malama!ba dogon bayani na tambaye ki ba just tell me idan zaki iya"

Cike da mamaki feena ta gaya mata,tana gama faɗa mata ta kashe wayar ta nufi chemist

Wani katafaren chemist ta shiga da sallama,mai chemist ɗin ya amsa sannan ta tambaye shi maganin,babu musu ya ɗauko mata,ta ajiye masa kuɗin shi ta ɗauki maganin ta juya ta bar chemist ɗin

Tana tuƙi kalaman kalaman Dr su'ad nata mata amsa kuwwa"congratulations Mrs Khalees!kina ɗauke da babyn mu na wata biyu da kwanaki shida, Allah ya raba ku da lafiya,sai a kular Mana da baby da kyau"

Dogon tsaki taja tana girgiza kai,a fili,ta furta"abinda bazan iya ba, Deeja bazata iya haifar yaran Khalees ba"

Gida ta koma,a harabar gidan ta iske Khalees yana karatun jarida,bata kula shi ba tayi shigewar ta shi kuma ya bita da kallon mamaki,a ran shi yana ayyana cewa lallai ba lafiya ba

A kan gado ta watsar da komai jakar ta,maganin da ta siyo wanda yazo a hannun ta,mayafin ta da ɗankwalin ta ta ɗauki towel ta shiga bayi don zafi takeji

Khalees ne ya shigo ɗakin,gefen gado yayiwa kanshi matsuguni yana jiran ta fito yaji ina taje har zuwa yanzu ƙarfe biyar saura,shi da yace huɗu tayi mata a gida,don masu gadi sun sanar masa dawowarta,kuma ga alamu ya gani,an gyara gidan tas.

Kwalin maganin da ya gani ne yaja hankalin shi kamar bazei duba ba sai dai ya ɗauka ya duba

Tashin hankali ne ƙarara a kan fuskar shi mei Deeja zatayi da wannan maganin?"ya tambayi kanshi

Ajiye maganin yayi ya miƙe ya fice daga ɗakin,baiyi cikakken minti guda da fita ba Deeja ta fito, doguwar riga ta sanya,ko mai bata shafa ba ta ɗauko gorar ruwa dake cikin ɗakin nata,ta ɓalli maganin ya zube a ƙasa

Da sauri ta ɗago kanta don ganin me wannan aikin, Khalees ne

#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 8

Yana tsaye sai huci yakeyi tamkar mayunwacin zaki, kyawawan idanun shi sun rine zuwa jajaye,alamun tashin hankali sun gama bayyana akan fuskar shi

Ita mamaki ya bata ma,amma sai ta ɓoye hakan akan fuskar ta,ta ɗauko maganin da nufin sake ɓalla sai ya fizge,sai taji ya fara bata haushi, cikin ɗaure fuska tace"bani!"

Bai bata ba kuma bai amsa ba,sai girgiza kai kai yakeyi,cikin tsawa tace"ka bani abu na mana!meye hakan?"

Juyawa yayi ya fita, Deeja ta raka shi da ido zuciyar ta nayi mata suya,a haukace ta miƙe ta ɗauki key ɗin motar ta tayo waje,a falo ta same shi ya rafka tagumi,ko kallon shi batayi ba ta ɗauki hanyar fita,sai jin Muryar shi tayi yana cewa

"Idan kika fita a bakin......."da sauri ta juyo tana murmushi tace"Please a bakin igiya nawa?uku?"

"Kar ki

Please Login or Register in order to submit comment