Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya US ba?"

"Ta gaya min,amma kuma ai bazaki rasa sanin inda yake ba ko?"

"Eh!yana tokyo,a can yayi karatu kuma ya fara aiki,yau kwanan mu sha shida da dawowa matar shi ta haihu,yaushe kike zuwa?"

Da mugun zumuɗi Deeja tace"ko yau a shirye nake wallahi"

"Lallai kam,to be ready next week in Sha Allah zamu tafi,amma muna dawowa zan nema miki admission ki yi masters ɗin ki idan kin yarda"

"Yeah Aunty!na yarda, wallahi dama na so ɗorawa kawai ban samu dama bane"

"Okay,in Sha Allah idan muka dawo sai ki ɗora karatun"

Murna Deeja ta rinƙa yi har da tsalle,Aunty nusaiba sai kallon ta takeyi tana murmushi

Satin ta biyu a ƙasar suka cale zuwa ƙasar Japan,tun a airport taga yayanta Yusuf,sai da gaban ta ya faɗi da ta ganshi,don babu in da ya baro mahaifin su sai hasken fata,da gudu taje ta rungume shi tana hawaye,ya rungume ta yana shafa kanta,kafin ya ɗago ta yana kallon ta da murmushi,yace"Are little sister?

Kin girma fa! lokacin da muka bar ki You was just a little girl"

Murmushi Deeja tayi tana nuna masa Affan da ke hannun Aunty nusaiba tace"yanzu nima gashi na dire little baby"dariya sukayi daga shi har matar shi hanan da ke rungume da ƴar babyn su safna

Farin ciki iya farin ciki kam Deeja ta shige shi,taga soyayya ta ga kulawa daga kowanne angle, Yusuf ma daina fita aiki yayi,kullum yana tare da ƴan uwan nashi ana ta shan raha da hira,ga matar shi mai kirki da barkwanci

Satin su ɗaya a Japan suka tattara suka koma US,Deeja taji tamkar su kar su rabu,amma hakan bai hana ta farin ciki ba

Satin su uku da komawa Deeja ta fara ɗaukar lecture a Cambridge University cikin farin ciki da nasara,karatun nata yana gara mata yadda take so,don taji sauƙi ma Aunty nusaiba ta samar mata Nanny da zata rinƙa kular mata da Affan,ƴar ƙasar Uganda, dattijuwa mai tsafta

***** ***** *****

Babu irin cigiya da neman da Khalees da Imran basu yiwa Deeja ba,gidajen rediyo da na tv babu in da basu kai cigiya ba, Khalees har wani ɗan ƙaramin hauka yayi,ya zabge ya rame ya fita hayyacin shi,ko abinci baya iya ci sai Imran ya lallaɓa shi yake shan yoghurt ko tea,yanzu haka ma ya janye shi zuwa Lagos don abin nashi ya fara yawa

Suna zaune a ɗakin hotel ɗin da suka sauka,waya ce a hannun Khalees ɗin ya ƙurawa hoton su shi da Deeja idanu,sunyi kyau a hoton dukkan su sunyi murmushi,sunyi hoton ne a wani lokaci da suka shirya zasu je gaida Hajiya yace mata"ƴan matan Abdul kinyi kyau fa"

Tayi murmushi tana masa hararar wasa tace"don kar nace ka chanja kar ƴan mata suyi min shigar sauri shine kayi riga malam masallaci?ko baka san ka fi Ni kyau ba?"shine yayi dariya ya janyo ta yayi musu hoton suna dariya,suka hau musu akan wanda yafi kyau,ƙarshe sai da suka ɓata lokaci suka fita, dukkan hotunan Deeja da ke wayar Nadiya ta goge su,wannan ne kaɗai saboda son hoton da yakeyi ya ɓoye shi Nadiya bata ganshi ba

Imran da ya shigo yanzu ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke zubo masa yana kallon wayar shi,yasan abinda yake kallo don wannan hoton shine abokin hirar shi,abincin shi, walwalar da duk wani farin cikin da ya rage masa, tabbas ya jinjina irin son da Khalees yakeyiwa Deeja,ya ƙarasa inda yake yayi tapping kafaɗar shi,ya ɗago a sanyaye yana kallon shi,ya samu waje a gefen shi ya zauna

Cikin kwantar da murya yace"Ni kam Khalees why not mu koma gida mu tuhumi matan mu kan batun Deeja,nasan Umaima bazata iya ɓatar da Deeja ba,amma nasan idan Nadiya ta aikata wata ɓarnar musamman wadda ta shafi umaiman zata gaya mata,so definitely indai sune suka ɓatar da ita idan muka tuhume su zamu samu hint"

"Kana ganin hakan mafita ce?"a cewar Khalees yana kallon shi

"In Sha Allah,mu jarraba hakan"

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 32

"To shikenan,muje"

A ranar Imran ya yankar musu ticket suka dawo Kano,a gidan Imran suka sauka,ko mintuna talatin da sauka basuyi ba Imran ɗin ya ɗebo ƴan sanda suka shiga suka fito da umaima da ke ta gunjin kuka,dama already ya tura wasu gidan Khalees, sai da aka tafi dasu sannan suka shiga cikin parlourn gidan suka zauna jugum,an rasa mai yin magana a cikin su

Turo ƙofar akayi da karfi,da sauri suka kalli ƙofar, Ma'aruf ne,yana zuwa ya shaƙe wuyan rigar Imran ya hau zazzaga masa masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,babu abinda bai kira shi ba,matsiyaci,butulu,maci amana,wanda bai san ciwon kanshi ba,a ƙarshe ya kaɗa masa warning cewa ya nemo masa ƴar uwar shi ko ya ɗauki duk matakin da ya ga dama akanshi,sannan ya juya kan Khalees da shima ya zuba masa idanu kamar yadda Imran ɗin yayi yace

"Ka bani mamaki Abdul,ban taɓa tunanin za'a haɗa kai da kai a cutar da wani wanda yake da alaƙa dani ba,zuwa yanzu nasan waye kai,na gode"yana gama bayani ta take ƙafar Imran ya juya ya fice daga parlourn

Shiru ya ratsa parlourn,Imran ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Khalees kam ya rasa mai ya kamata yayi ma,duniyar baki daya tayi masa wani irin ƙunci,da wanne zai ji?da ɓatan Deeja da yaron shi ko da laifin da wasu suke ɗora masa,a sanyaye ya miƙe yana goge ƙwallar da ta cika idanun shi,da sauri Imran yace"ina zakaje?"bai amsa ba ya nufi ƙofa,da sauri Imran ya riƙo hannun shi yana faɗin"I'm sorry gaskiya bazaka fita a wannan halin ba"

Cikin sanyin murya yace"gidan mu zan koma,wajen Hajiya ta"

"Okay bari nazo na mayar da kai,don bazan bar ka kayi driving a wannan halin ba,bai sake magana ba ya samu waje ya zauna, Imran ya shiga don ɗauko makullin mota

** ** **

Babu irin wuyar da su Umaima basu sha ba don su faɗi in da Deeja take,amma basu faɗa ba saboda basu sani ba,ga Nadiya da take fama da jinya,cikin wannan halin Khalees ya aikowa da nadiya takardar saki,da ƙyar dai ƴan uwan ta suka samu suka karɓe ta, Umaima tayi kuka sosai,ta ji inama ace tana da wani a kusa da ita nata,dama Najeeb ne ya ɗauko ta daga ƙauyen su, kasancewar bata da iyaye sai ya mayar da ita gidan su,amma ya mayar da ita tamkar matar shi

Yanzu kuwa ta sani bata da gata,bata san yadda rayuwa zatayi da ita ba

***** ***** *****

Lokaci guda Deeja tayi kyau tayi ƙiba,ta zama abin burgewa, hankalin ta ya kwanta sosai,amma dai tana matuƙar kewar mijin ta Khalees,ko ya yake zuwa yanzu bata sani ba

Tsawon shekara guda ta ɗauka tana karatun ta kafin ta kammala, result ya fito tayi murna sosai ganin sakamakon yadda yayi kyau,a lokacin ne hankalin ta ya koma gida,sai taji sam bata kyauta ba abinda tayi,don haka ta shawarci auntyn ta kan cewa tana son komawa Nigeria

Aunty nusaiba ta kalle ta tace"tuntuni ya kamata ace kin je ko da da ziyara ne,amma bazan matsa miki ba, shiyasa na ƙyale ki,yanzu dai ki bari sai nan da three weeks sai mu tafi gaba ɗaya,nima Ina son naje na ga ƴan uwa na"

"Su Aunty masu ƴan uwa,to Allah ya nuna mana dai"cewar Deeja tana dariya

Itama dariyar tayi tace"ameen,ko kin ɗauka ke kaɗai ake so?"

Kafin lokacin yazo Deeja ga ƙasa,sai ƙirga kwanaki takeyi,ranar tafiya Deeja sai zumuɗi takeyi,su Aunty suna ta tsokanar ta suna dariya

A gidan baba Prof suka sauka,basu sanar da zuwan su ba,amma anyi Sa'a yawancin jama'ar gidan suna nan,ganin Deeja ya haifar da sowar murna da farin ciki,don kowa ya cire rai daita,duk da har zuwa lokacin ana saka ta a adduoi,Aunty Bintu ma satin su biyu kenan daga dawowa daga Syria,bata samu shigowa gidan ba sai yau,ashe dai ta taki Sa'a

Fauwaz ne ya kira Ma'aruf, Khalees da Imran da basa nan,bai gaya musu abinda yake faruwa ba,sai da suka zo kusan a tare,Imran ya riga su shigowa,yana zuwa Ma'aruf ya shigo,bai kai ga fitowa daga mota ba ma Khalees ya shigo,sai dai har kwanan yau Ma'aruf baya yi musu magana,don haka ko da sukayi masa sallama ma tsallake su yayi ko kallon su baiyi ba,suma suka bi bayan shi zuwa cikin gidan

Sunyi matsanancin mamaki da farin cikin ganin Deeja,da alamu ma hankalin ta a kwance yake,ɗan jaririn yaron ta Affan yanzu yawon shi da gudu babu inda baya zuwa,babu abinda baya ci maganar ce dai ba sosai ba,kallo ɗaya Deeja tayi wa Khalees ta fashe da kuka,don yadda ya rame ya lalace abin tsoro,shi kam da sauri ya ƙaraso inda take ya riƙe hannun ta gam yana faɗin"Deeja ina kika shiga? hankalin mu ya tashi sosai,komai ya ƙare min Deeja,komai yayi min duhu saboda babu ke,nayi missing ɗin ki sosai Deeja"

Deeja ta girgiza kai tace"ka yafe min Khalees,na aikata kuskure,nayi abinda bai dace ba,na daga muku hankali,amma komai ya wuce,ga yaron ka nan"ta miƙa masa Affan"shima yayi kewar ka"

Ya ƙanƙame shi yana kallon shi yana murmushi,idanun shi cike da ƙwalla,kusan kowa a parlourn sai da ya jinjina irin soyayyar da sukeyiwa juna, Ma'aruf yace"Weldone auta,mu ba'a ganmu ba ko?"da murmushi ta tashi ta ƙarasa kusa dashi ta rungume shi tace"kaima nayi missing ɗin ka yaya,ina Aunty Farida?"

"Tana gida,ashe all this while gidan nusaiba kika je kika tare kika barmu da tashin hankali?"

Nusaiba tace"yaya Ma'aruf ita tace bata son kowa yasan tazo,shiyasa nima nayi shiru"

"Yanzu fisabilillahi idan tana shirme sai ki biye mata?"

"To yaya Ma'aruf nasan abinda aka mata?"Ma'aruf yayi ƴar dariya kawai,ya kama hannun Adnan suka fice daga parlourn

Ɗaya bayan ɗaya Deeja ta gaisa da yayyen nata,suka rungume junan ita da kiyya, Afra ma tazo ta rungume ta cike da farin ciki,daga nan suka ja ta sashen kiyyan,don yanzu ita da lubaisa ne kawai a gidan, fauwaz da Imran kowa ya koma gidanshi

A can taji labarai iri-iri,har da na Umaima,sai taji tausayin ta sosai,har ma tayi alƙawarin zata nemo ta ta taimaka mata jin wacece ita,abin ya bawa su Afra mamaki, Afra ta kasa haƙuri tace

"Gaskiya ke ta dabam ce Deeja,yanzu duk wahalar da Umaima ta baki har zata baki tausayi bayan ta fita daga rayuwar ki ki sake dawo da ita?"

Murmushi Deeja tayi tace"kika sani ko hakan ya zama silar shiryuwar ta,ke ce fa yanzu kika ce min bata da iyaye,Najeeb ya kawo ta kuma yanzu basa tare,kika san a wanne halin rayuwar take?kuma ma Ni sam banga hikima don mutum ya aikata maka sharri ka rama masa da sharri ba"

"Hakane kam, Allah ya sa hakan ya zamo silar shiryuwar ta ta"

"Ameen ya Allah"inji Deeja

Khalees ya nemi izinin tafiya da Affan,don dama Deeja ta yaye shi,babu musu ta haɗa masa ƴan kayayyakin shi,yana ta ɗaga mata ɗan hannun shi ta rako su har bakin mota,sai da suka tashi sannan ta koma gida

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 33

Kwanan Deeja da dawowa ta ja Afra suka nufi gidan su Umaima ko nace gidan su Najeeb,sun sha mamakin a halin da suka same shi,yayi haɗari ya faɗo daga mashin ya gamu da matsalar spinal cord,ko iya tashi bayayi, mahaifiyar shi mai jinyar shi

Da sallama suka shiga parlourn da Afra ta rinƙa bin shi da kallon mamaki ganin yadda ya sauya,suka gaida mahaifiyar tashi,da ke bin su da idanu,ta amsa da fara'a, Deeja ta gaishe da najeeb da ke kwance yana jin jiki,don bayan wannan matsalar har da brain cancer da ta kama shi,ya amsa cikin rawar murya, Afra kam ko kallon banza bai samu daga gare ta ba, Deeja ta kalle shi tace

"Am dama gidansu umaima muke son zuwa,to bamu san address ɗin ba,shine nazo idan Allah ya sa ka sani ka sanar mana"

Shiru Najeeb yayi na ƴan sakwanni kamar bazai ce komai ba,ƙwalla ta tarar masa a idanu,cikin karayar zuciya ya fara bayani

"Umaima ƴar garin taura ce,tana zaune a wani family house mai suna gidan cheɗiya,kaf garin su ansan gidan,sai dai umaima bata ji dadin gidan ba,don haka ko Ni bani da tabbacin zaku same ta ko bazaku same ta ba"

Deeja ta miƙe tana faɗin"zamu jarraba zuwa mu gani,in Sha Allah zamu same ta"daga nan tayi wa mahaifiyar shi sallama ta dire mata kuɗi 20k, mahaifiyar shi sai godiya take kamar zatayi wa Deejan sujjada, shima Najeeb cikin karayar zuciya yace

"Deeja,ki yafe min,kinga yadda rayuwa tayi dani,idan kika haɗu da umaima itama kice ta yafe min,don na cutar da rayuwar ta da yawa"

Deeja ta goge ƙwallar idanun ta tace"na yafe maka"sannan ta fice daga parlourn, Afra ta biyo bayan ta

Kai tsaye Deeja ta nufi taura jihar Jigawa,daga ita har Afra suna fatan Allah yasa su ga umaima

Basu wani sha wahalar gano gidan ba,amma da suka tambayi wata mata da ke tatar gasarar koko ina Umaima?sai ta yatsina fuska tace"bata dawo daga kasuwa wajen sana'ar ta ba,sai dai ko ku jira ta ko ku bi ta"Deeja da Afra suka kalli juna suka sake kallon matar,Deeja tace"babu matsala zamu jira ta,inane ɗakin nata?matar ta nuna musu tsohon ɗaki mai tsohon ƙyaure batare da ta sake magana ba

Allah yaso da bishiya a kofar ɗakin umaiman, Deeja ta koma mota ta ɗauko musu babbar dadduma suna hira suna shan iska,babu wanda yayi musu tayin ko ruwan sha,in da Allah ya taimake su suna da ruwan gora a mota,shi suka sha sukayi,Deeja ta ɗauko musu ƙatuwar dadduma sukayi alwalar azahar sukayi sallah. Zaman awa biyu da mintuna sukayi umaima ta dawo, Deeja tana bawa afra labarin Cambridge University ta hango Umaima tana shigowa gidan,shiru tayi tana kallon yadda ta fice a hayyacin ta tayi duhu sosai,tana sanye da atamfa da hijabi da suka ji jiki,amma fes take,fuskar ta ma babu alamun damuwa sam a tare da ita, Afra ma kallon ta takeyi,har taje wajen wata igiya ta kwaso kayan shanya sannan ta nufo ƙofar ɗakin nata

Sam bata kula da wasu a zaune ba sai da ta ƙara matsowa, Deeja ta fara gani,don tafi saitin inda take tahowa,ƙamewa tayi tana kallon Deeja da tunanin ko mafarki takeyi, Deeja tayi murmushi ganin irin shock ɗin da Umaima ta shiga ta miƙe tana murmushi ta rungume ta, Umaima ta ƙanƙame Deeja tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya,afra ma ta miƙe tazo ta rungume ta, Umaima ta haɗa su duka ta rungume tana kuka,sai da ƙyar ta ɗago tana kallon Deeja tana faɗin"Allah Sarki Deeja!ina kika shiga ne?yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke Ni ba,na shiga tashin hankalin ɓatan ki,ki yafe min Laifuka na Deeja......"maganar Tata ta katse saboda kukan da jaririyar bayan ta ta fara tana mutsu mutsu,wadda Allah bai sa Deeja da Afra sun kula da ita ba

Sakin Deeja tayi ta ɗanyi baya tana sauko da babyn,kallo ɗaya Deeja tayi wa jaririyar ta waro idanu tana faɗin"umaima haihuwa kikayi?"

Murmushi umaima tayi,Deeja ta amshi yarinyar tana ƙara kallon ta,bata da maraba da mahaifin ta Imran, Umaima ta ɗauke daddumar da suka shimfiɗa da suka shimfiɗa ta buɗe ƙofar ɗakin ta suka shiga cikin ɗakin

Siminti ne malale a ɗakin,amma duk ya faffashe,daga gefe kuma yaloluwar katifa ce da aka shimfiɗa mata zanin gadotsoho,sai dai ɗakin ƙal yake,dama umaima ba daga nan ba wajen tsafta

Cikin rawar jiki ta dauko murhun ta na gawayi tana ƙoƙarin hura wuta, Deeja ta dakatar da ita, Umaima tayi murmushi tana kallon Deeja tace"ko dai bazaki iya cin cimar mu ta ƙauye bane?"

Da sauri Afra ta kalle ta,nan da nan hawaye suka ciko idanun ta,tace "Umaima yau ke kike kiran kanki ƴar ƙauye?"

Umaima ta waro idanu tana murmushi tace"to da Ni ɗin ƴar ina ce?nan ce mahaifata,nan ce mahaifar baba na,kinga kuwa bani da inda yafi nan"bata ƙara sauraren su ba ta cigaba da ƙoƙarin hura wutar ta, Deeja tace"mu fa ba yunwa mukeji ba,ki zo mu zauna, magana zamuyi tukunna"Umaima tace"duk da haka dai sai mun ci abinci tukunna"tilas Deeja ta ƙyale ta, Umaima ta ɗora musu faten tsaki da yaji yakuwa da gyaɗa

Bayan ta gama a kwano ɗaya ta zuba musu,ta ɗebo musu ruwa a ƴar randar ta,suka ci a tare suna hira,bayan sun gama ta kwashe kwanukan don wankewa, Deeja kuma ta gyara wajen, Umaima tana shigowa tace"kai!daga zuwa kawai sai ki fara aiki?"

"Ke dai zauna kawai Umaima"a cewar Deeja,babu musu ta zauna tana fuskantar Deeja

Deeja tace"umaima me ya faru bayan tafiya ta?kuma dama kina da ciki kika taho baki gayawa Imran ba?ya na ganki haka?me yake faruwa ne?"

Murmushi mai ciwo umaima tayi,ta karɓi jaririyar ta daga hannun Afra,ta fara shayar da ita,ta jingina kanta da jikin bango ta fara magana cikin sanyin murya

"Iyaye na dukka biyun na rasa su ina ƙarama, mahaifiya ta ta rasu ina da shekaru biyar, lokacin da ƴan uwan ta suka zo gaisuwa bayan an share makoki sun so tafiya dani,amma mahaifi na yace a'a, tabbas ran ƴan uwan mahaifiya ta ya ɓaci,ƙarshe dai baayi rabuwar daɗi ba,don baba na jadaddawa ya rinka yi ƴa tashi ce babu mai raba su,dangin shi suka shiga maganar suka ƙara dagula lamarin

Haka dangin mahaifiya ta suka koma garin su suka barni a hannun mahaifi na,babu irin gatan da baiyi min ba, makaranta boko da islamiyya da kanshi yake kai ni,ya zauna yayi hira dani,yayi wasa dani,don sam bana iya shiga cikin yara kamar kowa nayi wasa,don haka idan mahaifi na bayan na dawo daga makaranta ɗakin mu nake shigewa nayi ta wasanni na da kayan wasan da baya gajiya da siya min

Haka rayuwa ta kasance har tsawon shekaru uku,a lokacin ina da shekaru takwas,a wannan lokacin ne nasan ma'anar rashi duk da ƙarancin shekaru na,don a shekarar ne na rasa mahaifi na bayan rashin lafiya da yayi ta kwana ɗaya"umaima ta kasa cigaba saboda kukan da yafi ƙarfin ta,da alamu har yanzu tana jin zafin mutuwar,su kansu Deeja da Afra kuka sukeyi,Deeja ma mutuwar mahaifin ta ce ke dawo mata

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 34

Umaima ta cigaba"lokacin da mahaifi na ya rasu na samu tausayawar al'umma da dama, musamman ƴan gidan mu,amma abin mamaki wannan karon ko mutum daya daga dangin mahaifiya ta bai zo ba, ina jin ƴan gidan mu suna zunɗen wai dangin mahaifiya ta basu san mutuwa ba,kuma soyayyar ƙarya sukeyi min don babu yadda za'ayi ace basuji mutuwar mahaifi na ba,tun maganar bata wani dame ni ba,amma da aka ɗauki lokaci da mutuwar mahaifi na sai ta dame ni

A lokacin duk masu nuna min soyayya da tausayawa sun janye daga gare ni, ba'a maganar dangin mahaifi na da muke rayuwa gida ɗaya amma duk da haka abinda zan ci sai sun ga yunwa tana neman kwantar dani suke san min, ba'a yi shekara guda da mutuwar baba ba na daina zuwa kowacce makaranta, don sharaɗi ƴan gidan mu suka saka min, sharaɗin cewa sai na ɗauki talla tukunna za'a bani abinci,babu musu na amince don bani da wata mafitar bayan wannan

Kusan kowa a gidan nan yana ɗora min talla,masu iymani a cikin su ne ke bani abinci,amma wasu cikin su yadda na siyar na kawo musu kuɗin su haka zasu cafke batare da sun yi min ko godiya ba, ballantana na saka rai da abincin,idan kuwa ƙwandala ta ɓata a kuɗin ina cin mugun duka irin na rashin gata,wasu ma sai suyi ta rantsuwar sai na biya su

Sutura kam idan aka ganni da ita to wasu bayin Allahn ne sukaji tausayi na suka bani kunce,tunda mahaifi na ya rasu ba'a sake yi min sabon ɗinki ba,nayi ƙanƙanta da yawa ballantana nayi tunanin ko da sana'a,Ni ba ƙawaye ko abokan wasa gareni ba,tallar da aka ƙaƙaba min shine aboki na,an sha kawo min farmakin lalata rayuwa ta amma Allah yana tsare Ni

Shekaru na goma sha uku,a lokacin rayuwa tayi min ƙunci sosai, kullum aikin ɗaya ne na ɗauki talla na fita,a lokacin na fara dabarar idan yunwa ta ishe ni na sauke kwanonin abincin na rarrage a leda na samu wanda zanci,har na fara rarrage abincin ina siyarwa ina samun ɗan kuɗin kashewa batare da sanin masu ɗora min talla ba

Ina da shekaru sha biyar muka haɗu da Najeeb,a lokacin sun zo garin nan aiki a wani asibiti, ciwon mara na al'ada ya riƙe Ni a hanyar dawowa ta daga siyar da dambun da nayi

A yashe suka ganni a gefen hanya na dafe ciki ina murƙususu,gefe kuma kwanukan abincin da na siyar ne, Najeeb ne da kanshi ya ɗauke Ni ya saka Ni a Mota muka nufi asibitin da suka kawowa ziyara

Da kanshi ya duba ni ya bani magunguna,da na dawo hayyacina sai na kasa zaman asibitin,nayi ta kuka sai da ya mayar dani gida

Sai dai kafin muje gida ya biya ta shago ya siya min kayan ƙwalam da maƙulashe,da kayan shayi sannan ya bani kuɗin da ban taɓa ganin irin su ba yace na kashe matsalar gaba na

Da farko na tsorata,har na ƙi amsa,amma da ya nuna min shi kawai taimako na yayi sai nayi ta masa godiya,na kwashi kayana na kai ɗaki sannan na mayarwa mai dambu kwanukan ta da kuɗin dambun ta

Daga lokacin na daina talla,dama don abinda zanci ne nakeyi,yanzu kam wannan ya kau,amma ban koma makaranta ba,sai dai na kasa cire wannan saurayin da ya taimake ni a raina

Kusan watanni biyu Najeeb ya dawo,nayi farin ciki sosai,amma sai ya tambaye Ni dalilin talla bana zuwa makaranta ban ɓoye masa komai ba na bashi labarin kaina,ya tausaya min sosai,yace to mai zai hana na bishi ya kaiwa umman shi ni?don bata da ƴa mace,kuma nima ina buƙatar kulawar uwa a shekaru na,sannan zai mayar dani makaranta

Faɗar hakan da yayi yasa ko musu banyi ba na amince,washe gari babu wanda nayiwa sallama na biyo Najeeb muka nufi kano

Babu laifi maman shi ta tarbe ni da kulawa,aka bani ɗakin da na ganni tamkar amarya, saboda kyan shi da tsaruwar shi

A gidan su Najeeb na samu ƴanci sosai,abinda naso shi nake ci,sutura sai wadda na so zan saka,gashi kuma ya sanya Ni a tsadaddiyar makaranta,ya ɗaukar min lesson teacher

Ban ɗauki lokaci ba nayi wani irin haske,nayi kyau sosai,sau tari haka Najeeb zai yi ta kallo na kamar wani wawa,wani sa'in har kunya yake bani

Shekaru biyu da dawowa ta kano,babu wanda zai ganni yace na taɓa yin rayuwar ƙauye, amma kuma a kullum umarnin Najeeb nake bi,ya hana ni kula ƙawaye,sai Nadiya da aƙalla zata bani shekaru biyar zuwa sama, Nadiyan ce take haɗa ni da ƙawayen ta,ƴan gayu ne sosai, rayuwar su tana matukar burge ni

Rana tsaka Najeeb yace nazo na raka shi unguwa,sai dai maimakon unguwa hotel ya nufa dani,anan yake gaya min manufar shi ta shekara da shekaru,na tsorata sosai,sai dai ya nuna min zaɓi biyu gare ni,ko dai na amince da buƙatar shi ya nuna hidimar da yake min,ko kuma naƙi amincewa ya mayar dani in da ya ɗauko Ni, hankali na ya tashi sosai,ba tsorata matuƙa da makircin Najeeb,yace ya bani nan da gobe na yanke shawara,ko na yarda dashi ko na koma gidanmu,daga nan bai jira komai ba ya ɗauko Ni ya dawo dani gida

Nadiya na kira ina kuka nace don Allah tazo ina son ganin ta, Kasancewar duk wannan abin da akeyi Najeeb ya saka min doka mai tsanani,bana fita sai ya san in da zanje,don haka idan naso ganin Nadiya sai dai na kira ta,ita kuma babu ɓata lokaci tazo,yanzun ma haka akayi,cikin ƴan mintuna tazo

Ɗaki na na ja ta cikin kuka na sanar mata yadda mukayi da Najeeb,ga mamaki na sai naga ta kwashe da dariya,tace"Ni wallahi har kin bani tsoro,yanzu akan wannan minor problem ɗin zaki wani tattago ni?to shikenan kar ki amince,sai ya mayar dake can ƙauyen,a banza za'a yi miki fyaɗe a yasar dake a titi a wulaƙance,kowa yana kallon ki a yatsine,amma idan kika amincewa Najeeb ko babu komai zaki ga tarairaya da kulawa, kuma cikin farin ciki zaki rayu"

Cikin kuka nace"to me zai hana ya aure ni?idan yaso ko ma menene sai yayi dani"wani kallon rainin wayo Nadiya tayi min tace"lallai na yarda yarinta ke damun ki,Malama idan zaki saki jiki ki saki jiki,wanne aure kuma ana zaune ƙalau?ki bar wani batun aure har ki kammala makaranta,amma yanzu kiyi rayuwar ki"haka tayi ta min zuga tana kawo misalai har na yarda na amince"umaiman ta rufe fuskar da tafin hannun ta tana kuka mai soya rai, Afra ma kuka take har da shashsheƙa, Deeja ce dai kukan ya ɗauke sai ajiyar zuciya take saukewa,daidai nan aka tsuge da ruwan sama,da sauri Umaima ta miƙe ta saki asabarin ɗakin da windon ɗakin sannan ta koma ta zauna,sai da ta daidaita nutsuwar ta sannan ta cigaba

"Washegari Najeeb yaje ɗauko ni daga makaranta,a hanya yake tambaya ta,me na yanke game

Please Login or Register in order to submit comment