Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sati bai ganta tazo gidan ba,hakan ya sanya shi yarda da batun Najeeb, zuciyar shi ta cika da haushin Deeja

Rana tsaka Deeja tazo da farin cikin ta wajen Imran tana shaida masa abban ta ya amince tayi aiki a asibitin mijin zee,Amma yadda yayi mata ya sanyaya mata jiki, ko da ta gaya masa baiyi wani appreciating ba sosai, don haka bata wuce minti goma ba ta tafi gida

Daga lokacin ya zamana ba sosai suke haɗuwa ba ma, musamman da ya zamana kowa cikin su aikin shi ya ɗauki zafi,a waya kam sukanyi wata babu wanda ya taɓa wani,tun abin na bawa Deeja mamaki har ta watsar

Shekarar shi guda da zuwa mahaifiyar shi ta bukaci yayi aure a wata ziyara da ya kai mata Abuja,babu ɓata lokaci ya gabatar mata da umaima wadda zuwa yanzu sunyi nisa a soyayya, Deeja kam yanzu sun zama baƙin juna

Ya ɗauka momy Aysha zatayi farin ciki amma sai yaga ta ɗaure fuska ta fara faɗa

"Wacece wata umaima?to ban amince ba, ba da yawu na ba,ga yarinya ƴar mutunci wadda tayi maka halacci amma saboda tsabar butulci ka guje mata,to wallahi dole ka aure ta,zan shigo kanon ma next week, wallahi bazaka mayar dani ƙaramar mutum ba,a cewar momyn cikin faɗa

Shiru yayi cikin ɓacin rai,shi kam duk kusan mutanen da yake tare dasu haushin shi suke ji akan Deeja,a ƙarshe ga mahaifiyar shi ma,take yaji wata tsanar ta ta dirar masa,haka dai yayiwa momyn nashi sallama ya tafi

Kwana biyar da faruwar haka Deeja tazo gidan,a lokacin ma bata san abinda yake faruwa ba,dama wajen su Yasmeen tazo,bayan sun gama hirar su ta fito,har ta nufi parking space ta tuna sun kwana biyu basu gaisa da Imran ba,don haka ta wuce lambun gidan kai tsaye da hope ɗin zata same shi

Ilai kuwa yana zaune,sai dai maimakon karatu yadda ya saba yau waya yakeyi yana lumshe idanu yana murmushi da alamu yana jin daɗin wayar da yakeyi

Ta nufe shi kai tsaye,a dai-dai lokacin da ya kammala wayar tayi masa sallama,ya amsa fuska a ɗaure, bata damu ba ta gaishe shi,nan ma ya amsa ciki-ciki sannan yace "lafiya dai ko?"

Ɗan murmushin da bai kai zuci ba tayi ta zauna tana faɗin"lafiya ƙalau,dama zuwa nayi wajen Yasmin shine sai na biyo wajen ka mu gaisa"

"To yayi kyau,kina iya tafiya"ya faɗa idanun shi a kan wayar shi

Tabbas ranta ya ɓaci amma bata nuna ba,sai tace"wai yaushe momy zata dawo daga China?naji su Yasmin sun ce taje China shekaranjiya"

"Ki tambaye ta,kun fi kusa ai"ya bata amsa idanun shi na kan wayar shi

Ta buɗe baki da zummar yin magana ya ɗaga mata hannu yace"kinga!tashi kije kawai,kin fiye shishshige min,Ni kuma na tsani mace mai shishshige wa namiji!!"

Tunda take ba'a taɓa furta mata kalmar da tayi mata ciwo ba irin wannan,don haka ta miƙe batare da tace uffan ba ta bar wajen

Kwana goma da faruwar hakan taji Labarin auren ta da Imran a bakin mamie,sai da gaban ta ya faɗi don a lokacin ko sannu bata haɗa su da Imran,sai dai bata ce komai ba

Kwance tashi har bikin yazo,komai proffesor Isma'il ne yayi mata,ya hana Dr Mahmud komai,an shirya biki na garari an kai amarya gidan mijinta

Kusan lokaci guda akayi bikin su da Mima,sati biyu ne tsakanin su,don haka Mima ta samu halartar auren Deeja,itama Mima ɗin ɗan ƙanin baban ta zata aura,shima ɗan azare ne amma baki ɗaya zaman su da iyayen shi a Malaysia suke,sai dai su auren soyayya zasuyi ba kamar su Deeja ba

To fa!tunda aka kawo Deeja gidan Imran ta gane ainihin kalar shi,babu irin izayar da baya mata da shawarar babban abokin shi Najeeb,wanda ya nuna idan har baiyi yadda zai yi ya kori Deeja ba bazai bashi ƙanwar shi ba,hakan ya tayar da hankalin shi ya dage cikin rufewar idanu ya cigaba da ƙuntatawa Deejan,bata taɓa faɗawa kowa ba duk zuwan da akeyi gidan,sai dai ramar da takeyi tana bawa Kowa mamaki,amma idan an tambaye ta dalili sai dai tace babu komai

Watannin su biyar da aure Imran ya bijiro da maganar umaima bayan ya shawo kan Najeeb da ƙyar,amma momyn shi sam bata bashi goyon baya ba,sai ya tuntuɓi proffesor,shi kam ya wuce gaba,nan da nan akayi komai aka gama aka sanya lokacin aure

Lokacin da momy Aysha taji Labarin tayi baƙin ciki sosai,amma yadda bai same ta da zancen ba itama bata tuntuɓe shi ba

Professor da kanshi ya kira Deeja ya sanar mata maganar auren,ya lallashe ta da kalaman kwantar da hankali,bata nuna masa damuwa ba don ta san hakan zai faru watarana, amma duk da haka hankalin ta ya ɗan tashi,sai dai ta fauwalawa Allah komai don ya san shine mai iko a bisa komai

Anyi biki lafiya,anyi sharholiya sosai, amarya ta tare a gidanta

Tunda umaima ta tare Deeja ta fara ganin yadda ake soyayya,sam basa jin kunyar ta,wani abin ma basayi sai sun ga idanun ta a wajen,gashi ta zama tamkar baiwa,duk wasu aikace-aikace na gidan ita takeyi,sai dai bata taɓa nuna damuwa ba duk da abin yana cin ta a zuciya

Makirci kala-kala babu wanda umaima bata taɓa yiwa Deeja,da taimakon Najeeb,Imran kam ya ƙara tsanar ta har ta kai yana dukan ta,ga horon yunwa da yake mata,ta sake lalacewa,da yawan mutane zargi sukeyi kishi ke damun ta

Lokaci ɗaya ta fara wani irin ciwon ƙirji,wani lokacin numfashin ta har ƙoƙarin ɗaukewa yakeyi,ita kaɗai ta san me takeji idan ciwon ya tasar mata,sai dai ta sani bata da Muhimmanci a wajen Imran da zai tsaya ya saurare ta

Zuwan Mima daga Malaysia ya faranta mata rai sosai,a lokacin miman har da ƙaramin ciki,kuma anyi Sa'a lokacin su Imran sunje Abuja gidan momyn shi,don haka suka baje a falo suna hirar yaushe gamo

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️ Nusy bee

Page 24

Mima ta ƙare wa Deeja kallo,tace sister deejo,me ya same ki ne naga kin rame haka?ko baki da lafiya ne?"

Deeja ta ɗan yi shiru, Mima abokiyar sirrin ta ce,ba don haka ba da baza ta iya sanar da Mima abinda yake damun ta ba,amma saboda muhimmancin Mima sai ta bata labarin irin wahalar da take sha a gidan

Tabbas lamarin ya bawa Mima mamaki da tsoro,kuma ta tausayawa Deeja sosai,tayi shiru cikin alhini tana kallon Deeja,zuwa can tace"amma Imran ya cika butulu,yanzu duk irin soyayyar da kukayi ta zama tarihi saboda ya samu wata?"

Deeja ta girgiza kai tace"ba soyayya mukayi da Imran kamar yadda kukayi tsammani ba,abota ce kawai,kuma shigowar maganar aure ciki ita ta watsa abotar"

Shiru Mima tayi tana jinjina abin,zuwa can tace"gaskiya lamarin da mamaki sister,Imran ya bani mamaki sosai"

Deeja tace"Ni kam sam,don ya gwada min tun Kafin auren"

Mima tace"to Allah ya kyauta,ki cigaba da haƙuri watarana sai labari"Mima dai tayi ta kwantar mata da hankali,duk da cewar abin ya dame ta,kuma abin da ta sani shine da ace itace Imran bazei fara abinda yayi wa Deeja ba

A ranar Mima a gidan ta kwana, Deeja taji daɗi sosai, saboda Mima ta ɗebe mata kewa,dama kuma gwanar surutu ce da barkwanci

Washegari Mima ta tafi,Deeja sai taji dama kar ta tafi saboda taji daɗin zuwan ta,kuma a ɗan zaman da sukayi taji sauƙin ciwon kirjin ta

Kwanan Mima biyu da tafiya su Imran suka dawo,ta fuskanci ya ƙaro wulaƙanci, saboda momyn shi tayi masa faɗa sosai akan rashin zuwa da Deeja,sannan batayi wani marari akan umaiman ba,don haka ya ƙudurce a ranshi Deeja sai ta gane kuren ta

Tunda tayi masa sannu da zuwa ya daka mata tsawa ta shige ɗaki bata sake yarda sun haɗu ba,da sassafe zata fice aikin ta,sai ta kai biyar na yamma bata dawo ba,da zarar ta dawo sai ta rufe kanta a ɗaki,haka tayi ta gudanar da rayuwar ta tsawon sati guda

Baƙar rana a gare ta,ranar da baza ta taɓa gogewa a cikin ranta ba,itace wata ranar talata takwas ga watan biyu

Dawowar ta kenan daga aiki,ta jefar da jakar ta akan tiles abinda bata taɓa yi ba,yau tun safe jinta takeyi wani iri kamar ba ita ba,ta rasa me yake damun ta, wanka ta shiga,tana fitowa tayi sallar la'asar da taji ana kira,tana idarwa ta ɗan kwanta don ta huce gajiya,sai bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita

Bata farka ba sai bayan maghriba,tayi matuƙar mamakin baccin da tayi,ta miƙe tayi sallah,haka kawai yaji gaban ta na faɗuwa,ƙirjin ta ya tsananta ciwo,abu ya dame ta,ta ɗan yi shiru,zuwa can ta janyo jakar ta dake yashe akan tiles don ta ɗebe kewa sai taji ta a kashe,abin ya bata mamaki sosai,don ta san wayar ta akwai ragowar chaji,amma hakan bai wani dame ta ba ta sanya ta a chaji,sai bayan ƙarfe tara na dare ta kunna ta

Saƙonni da miscalls ta gani barkatai,da sauri ta fara duba miscalls ɗin,yaya Ma'aruf ta gani

Mamaki ya kamata,indai Ma'aruf da ta sani ne baya kira sama da biyu,amma yau shine mai kira har sha ɗaya,to lafiya?sai taji gaban ta ya faɗi,da sauri ta buɗe saƙonnin don ganin abinda suka ƙunsa

Tashin hankalin da ta gani ne ya sanya ta ƙwala ƙara tana faɗin"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"jikin ta na matsanancin rawa

"Aslm auta,Abba Met with an accident on his way back from Abuja today,and sadly we lost him,I called you several times but you are not picking"

Tashin hankalin hankalin da Deeja ta shiga baya faɗuwa,daga tsaye ta saki wayar tana jan numfashi,amma saboda tsabar ƙarfin hali da tashin hankali haka ta nufi parlourn tana haki,still ta kasa yarda abban ta abin ƙaunar ta ya tafi ya bar ta,kuka take so tayi amma ta gagara,ko a mafarki bata taɓa kawo abban ta zai tafi ya bar ta a wannan halin ba

A parlour ta iske Imran da umaima suna shan soyayyar su hankali kwance, umaima ce ta fara ganin ta,cikin masifa tace"Malama Lafiya,uban me kika zo yi mana?"

"Abba na!yaya Ma'aruf ne yace wai ya tafi ya barni,yaya Ma'aruf yace na rasa Abba na garkuwa na"ta faɗa cikin fitar hayyaci lokaci guda kuma tana ficewa daga cikin parlourn

Imran ya bi ta da kallo,karo na farko kenan bayan auren su da yaji tausayin ta,ganin har ta fice daga parlourn cikin sauri ya miƙe ya bi ta,amma kafin ya riske ta a waje ta hau napep ta tafi,bai bi ta ba sai ya dawo gida,duk da ya tausaya mata

Ita kam kai tsaye gidan su ga nufa,tana zuwa ta samu yaya Ma'aruf a harabar gidan da shi da aminin shi na amana Khalees, dukkan su sai sharar ƙwalla sukeyi,ta jefa musu tambaya cikin tashin hankali

"Ina Abba na?"

Bin ta sukayi da kallo,don sun sani sai tafi kowa jin mutuwar,don itace favourite ɗin shi kuma shi kaɗai gare ta a yanzu,gaba ɗaya tausayi take basu,ta ƙanƙame Ma'aruf tana faɗin"yaya Ma'aruf abbana!Abba na kar ya tafi ya bar ni,wallahi ina son shi,idan ta tafi ya zanyi?"

Yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali amma ina!kafin ya ankara sai gani yayi ta sulale ƙasa sumammiya

Cikin kuma mai motsa rai Ma'aruf ya durƙusa ya ɗago ta,cikin sauri Khalees ya miƙo masa ruwa ya amsa ya yayyafa mata,ta ja ajiyar zuciya

Zumbur ta miƙe tana zare idanu,sai ta fashe da kuka mai ban tausayi, Ma'aruf ya kama hannun ta suka shiga gidan tana ta sambatu

A ranar babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali da suka shiga, Deeja ta gigice sai suma takeyi,tilas aka ɗauke ta sai asibitin da suke zuwa wajen likitar ta Dr su'ad

Cikin lokaci ƙanƙani likitoci suka rufu akanta,sun ɗau kimanin awa uku kafin su fito, hankalin Dr su'ad a tashe

Office ta ja Ma'aruf ta sanar dashi cewar zuciyar Deeja ta kamu da ciwo

Hankalin Ma'aruf yayi matuƙar tashi,yace"ciwon zuciya kuma doctor? innalillahi wa Inna ilayhi rajiun! Deejan har nawa take da zata kamu da irin wannan ciwon?"

"Ko kwanan ta ɗaya da haihuwa idan Allah ya ƙaddara sai kaga ta kamu da ciwon, ballantana ma ana haifar jarirai dashi,amma ita nata ta same shi ne due to depression and anxiety,tana cikin tsananin damuwa,why baka san abinda ya janyo ciwon ba a matsayin ka na yayan ta?"

"Dr Ni dai nasan na sanar mata rasuwar mahaifin mu,and I know she is his favorite,and they love each other,but Bana tunanin wannan dalilin can lead Deeja to this stage,ko babu komai itama musulma ce ta yarda da ƙaddara"

Dr su'ad ta girgiza kai tace"ba wannan bane,don da alamu ciwon ya kwana biyu a tare da ita, and it's better a kula da ita yadda ya kamata,gudun samun wata matsalar again"bai sake magana ba ya juya ya fice daga office ɗin cikin mutuwar jiki,Dr ta biyo bayan shi

Waje ya samu ya zauna yayi tagumi,ya kai mintuna sha biyar a zaune kafin abokin shi Khalees ya shigo reception ɗin

Ya kai mintuna biyar a tsaye a kan shi amma bai san yazo ba,sai da ya taɓa shi sannan yayi firgigit kamar wanda ya tashi daga bacci

Khalees ya samu waje ya zauna kusa da abokin nashi,ya zaro wayar shi daga aljihu ya miƙa masa,ya amshi wayar, cikin nutsuwa Khalees ya kalle shi yace

"Ana ta kiran ka don ayi maka ta'aziyya amma baka tare da wayar ballantana ka ɗaga,sai yanzu naje gidan naku Abida ta shaida min abinda yake faruwa ta bani wayar na kawo maka,ya mai jikin?"

"Da sauƙi"ya bashi amsa cikin matsananciyar damuwa

Shiru sukayi su duka, Ma'aruf damuwar da yake ciki ta hana shi magana,shima Khalees duk da cewa akwai damuwar dama can shi ba mai yawan magana bane

Sun kwashi kusan rabin awa kafin Imran ya shigo reception din,yayi musu sallama suka amsa,cikin mamaki Khalees yace"isn't you Imran alƙasim?"

"Yeah abdurrashid Abubakar!dama zan sake ganin ka?many years ahead!"Ma'aruf yana kallon su da mamaki akan fuskar shi, Khalees ya kalli Ma'aruf cikin murmushi yace"he is friend of mine lokacin da nayi boarding school a Bauchi,a good friend of mine"

"Wow!very nice!Ashe kun san juna?"a cewar Ma'aruf da ɗan murmushin yaƙe a fuskar shi,don ya fara zargin kamar Imran ne silar ciwon Deeja

Imran ya gyaɗa kai yana murmushi,sannan ya ɗan kalli Ma'aruf yace"ya ƙarin haƙuri kuma?"Ma'aruf yace"haƙuri mun godewa Allah"

Imran yace"to Allah yaji qan shi yayi masa rahama, Allah ya albarkaci bayan shi ya sada shi da annabin rahama, Allah ya bada haƙurin rashin shi"Khalees da Ma'aruf suka amsa da ameen,Imran ya ƙara cewa "ya mai jikin? fauwaz ya sanar dani tayi collapse tun jiya?"

Ma'aruf ya ja ajiyar zuciya yace"yeah,Amma for now da sauƙi,don ta dawo hayyacinta yanzu ma bacci takeyi".

Imran fa ka tara maƙiya,ya kamata ka kama kan ka,don kowa yace baya yin ka😁

#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 25

"Okay to bari na shiga na ganta"a cewar Imran,bai jira cewar su ba ya shiga don ganin Deeja

Kwanan Deeja shida a asibitin aka sallame ta,,ta rame tayi zuru-zuru,ta sake zama so silent,Wai a haka kullum Ma'aruf,matar shi fareeda da su Aunty Bintu suna kusa da ita suna tausar ta,baba Prof ma sau uku yana zuwa duba ta, mamie kam ita da yaran ta kullum suna hanya,yanzun ma da aka sallame ta kai tsaye Mamie ta wuce da ita can gidan

Ta kai kwana goma kafin ta dawo hayyacinta,su mamie da yaran ta suna tarairayar ta da mantar da ita damuwar ta,hakan ya sa ta fauwalawa Allah komai ta kwantar da hankalin ta

Ta kai kimanin sati uku a gidan bana Prof kafin mamie ta mayar da ita gidan ta,tun a ranar da ta koma umaima ta tare ta da wulaƙanci iri-iri,sam bata gaban ta don yanzu abinda ya dame ta ma dabam, tuni ta kama harkar gaban ta

Cikin lokaci ƙanƙani shima Imran ya dawo da ainihin siffar shi,suka ƙara santa Deeja a gaba da cin mutunci iri-iri

Sai ya zamana idan ta fita aiki bata son dawowa, Saboda Imran ya ƙuntata mata sai ya hana ta zuwa aikin,haka tana ji tana gani ta ajiye aikin ta da take matuƙar so

Yau watan ta biyu da dawowa gidan Imran,da kaɗan kaɗan sai da ciwon ta ya kai ta ga kwanciya,yau kam ta wayi gari da tsanantar ciwon don yadda numfashi yake wahalar daita kamar mai athma,don haka ta yanke shawarar zata je asibiti don gwada lafiyar ta,don haka Imran yana shirin fita ta same shi shi da umaima a bakin motar shi tana zuba masa shagwaɓa

Tayi musu sallama,Imran ya amsa amma fuska a ɗaure,ita kuwa umaima wani kallon banza ta bi ta dashi kafin ta taɓe baki ta ɗauke kai

Cikin sanyin murya ta gaishe shi,ya amsa a daƙile sannan yace"me ya kawo ki?"

"Bana jin daɗi ne,ina son zuwa asibiti"ta bashi amsa cikin yanayin ciwo

Ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa,eh tabbas ga alamu nan ya gani,amma sai yace"sai ki jira,ƙarfe tara zan zo na kai ki asibitin"

Cikin Muryar ciwo ta amsa da cewa to "to na gode, Allah ya dawo da kai lafiya"ta juya ta koma cikin gida,tana jin umaima na jan dogon tsaki,ko kallo bata ishi Deeja ba

Kafin ƙarfe tara fa gama shirya wa duk da bata da lafiya,amma Imran shiru,har goma shiru,da taga sha ɗaya tayi sai ta fara neman shi a waya,amma sai ya rinƙa danna mata busy,ganin hakan bai wani bawa Deeja mamaki sosai ba, instead ma sai ya kira ya'yan ta Ma'aruf ta shaida masa

Shiru yayi cikin mamaki da haushi,can yace"shi Imran ɗin ne yace ki jira shi kuma yake katse miki kira?"

Deeja tace "eh"

"Gaskiya Imran ya bani mamaki,ban zaci zai yi haka ba,kar kiyi wasa da lafiyar ki,maza ki shirya kije ki ga doctor su'ad,don kema kin san ciwon ki bana wasa bane"

Ta amsa da"to"sannan ta kashe wayar

Shiryawa tayi cikin ƙarfin hali ta fice zuwa asibitin Dr su'ad, Dr tayi mata gwaje-gwaje ta tabbatar mata dole sai anyi admitting ɗin ta,don babu wani improvement da aka samu yanzu

Deeja Imran ta fara turawa text message ta sanar masa sannan ta turawa Ma'aruf

Ko awa ɗaya baayi ba Ma'aruf da Farida suka bayyana, Farida ce ta zauna a wajen Deeja,shi kuma Ma'aruf da ya ga babu matsala ya wuce wajen aikin shi

Wajen ƙarfe uku fareeda na zaune a kujerar da ke gefen gadon da Deeja take kwance,sai kallon ta takeyi tana mamakin yadda ta ƙara ramewa ta lalace,Imran yayi sallama ya shigo

Cikin nutsuwa ta amsa,ya shigo cikin ɗakin,suka gaisa a mutunce ya tambayi ya mai jikin?ta amsa da sauƙi sannan ya dire mata dubunnan kuɗaɗe a matsayin kuɗin magani,sannan ya ɗora wata envelop akai yace

"Kuɗin nan na magani ne,wannan envelop ɗin saƙo ne idan ta tashi ki bata"

Ta amsa da"to shikenan"ya miƙe ya nufi hanyar fita yana faɗin"Allah ya bada lafiya"

Farida ta amsa da"ameen"

Wajejen ƙarfe huɗu da rabi Deeja ta farka,Farida tayi mata sannu,ta haɗa mata ruwan wanka,tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallah,sannan ta gabatar mata da abinci, kaɗan taci saboda gaba ɗaya hankalin ta yana gida

Bayan ta dawo nutsuwar ta fareeda ta bata saƙon mijin ta, kuɗi ne kimanin 500k,sai envelop,ta ajiye kuɗin sannan ta buɗe envelop ɗin

Sai da taji gaban ta ya yanke ya faɗi,don haka sai ta fasa warware takardar tayi shiru tana fargabar abinda zata riska

A lokacin Farida bata ward ɗin,ta fita zuwa office ɗin Dr su'ad

Cikin dakiya ta ɗaga takardar ta warware ta a hankali,gaban ta yana dukan uku-uku ta soma karantawa

Assalamu alaikum

Nasan ba za kiyi mamakin ganin saƙo na ba saboda kema kin san me kikayi kuma tun da can ma kin san zaman haƙuri nakeyi da ke, saboda ba son ki nakeyi ba,kullum cikin saɓani da mahaifiya ta nake a dalilin ki,wato yanzu har ta kai zan ce kar kiyi abu,kuma kiyi, gaskiya bazan iya da halayen ki ba

A don haka na yanke duka igiyoyin aure na da ke,inayi miki fatan alkhairi, Allah ya baki wanda ya fi ni"
Imran alƙasim

Bayyana irin tashin hankalin da ta shiga ma ɓata baki ne,ta miƙe a gigice tana furta"innalillahi wa inna ilayhi rajiun"dai-dai nan Farisa da Dr su'ad suka shigo

Da sauri suka ƙaraso suna faɗin"lafiya dai Deeja?me yake faruwa?"bata ƙarasa faɗa ba sai gani sukayi Deeja ta sulale ƙasa,ko alamar motsi babu a tare da ita

A gigice tayi ƙasa ta fara girgiza ta tana ambaton"Deeja! Deeja!!"amma ina babu alamun rai a tare da ita,ita ma dai Dr su'ad a gigicen take, sai dai tayi ƙoƙarin saita kanta ta bata taimakon gaggawa

Hakan yayi matuƙar gigita su ganin still babu wani improvement,Farida tayi waje a matuƙar kiɗime,karo sukayi da Ma'aruf.....

Gaskiya fa ko ni na fara jin tsoron Imran 🥺

#Nusy_bee

****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 26

Zubewa tayi a ƙasa tana haki cikin tashin hankali,da sauri Ma'aruf yaja baya yana faɗin"subhanallahi!me ya faru ne?"

"Deeja!Deejan mu ta mutu"a cewar ta cikin tashin hankali

Cikin sauri ya faɗa ɗakin,daidai lokacin wasu nurses suka shigo alamun Dr su'ad ta sanar dasu,da sauri aka ɗauke ta aka nufi emergency room da ita

An kai kimanin awa biyu kafin a shawo kan matsalar,abin ya ɗagawa kowa hankali, musamman Farida da take ta gursheƙen kuka, saboda ta sani tuntuni kaf ƙannen Ma'aruf da Deeja kaɗai suke shiri saboda su faiza basu da mutunci sam,haka ya janyo musu shaƙuwa,ta sani in dai ta mutu to tabbas zata shiga wani hali

Su kansu likitocin sunyi mamakin abinda ya taɓa ciwon nata lokaci guda,sukayi musu warning akan cewa su kula da duk abinda zai ɓata mata rai

Abin ya bawa Farida mamaki, saboda ta san dai har ta fita babu alamun damuwa a tare da Deeja

A sanyaye ta koma ɗakin da aka kwantar da Deeja,ta fara tattare kwanukan da Deejan ta kammala cin abinci,har ta gama sai ta kula da takardar saƙon Deeja a yashe a ƙasa,kamar kar ta ɗauka sai kuma taga gwara ta ɗauka,ta ɗauka ta buɗe ta karanta

"Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!!!"ta furta cikin ƙaraji

Sai ta zubar da kayan ta ruga wajen da Ma'aruf yake tsaye,cikin kuka ta miƙa masa takardar

Ma'aruf ya girgiza sosai ya gyaɗa kai tare da faɗin"lallai babu shakka Imran ya cika butulu"

Farida cikin kuka tace"ai wallahi bazai gama da duniya lafiya ba, Allah ya sai ya bi mata haƙƙin ta"

Baƙin ciki da takaici ya hana Ma'aruf sake magana,ita kuwa Farida kuka take tana la'antar Imran

Da Deeja ta dawo hayyacinta Farida ce mai tausar ta tare da bata shawarar ta manta da wani Imran ta cigaba da rayuwar ta,Hajiya mamie tazo,jin abinda Imran yayi ya girgiza ta matuƙa,abin yayi mata ciwo,amma ganin momy Aysha ta fita shiga tashin hankali har da kuka sai ta saukar da nata fushin

Gashi kuma Imran yana sakin Deeja ya ɗauki umaiman shi suka wuce US in da fauwaz ya tafi honeymoon da amaryar shi

Satin Deeja uku ta samu sauƙi sosai,mamie da kanta ta ɗauko ta a asibiti,ta dawo da ita gidan baba Prof,cikin ɗan lokacin aka sake mayar mata da matsayin ta na auta, saboda gata da sakalcin da ake mata, tarairaya sai abinda aka manta, yaya abdallah ƙanin fauwaz kullum sai ya fara zuwa wajen ta a falon Mamie yayi ya tsokanar ta sannan yake fita aiki,idan ya dawo kuma ya taho mata da favourite ɗin ta,nan ma su sha hira,hakan yana damun matar shi lubaisa wadda itama ba wani sakewa Deejan take sosai ba,itama Deejan ba shiga sabgar ta takeyi ba

Cikin ɗan lokaci Deeja ta mayar da jikin ta tayi kyau,fatar ta tayi fresh asalin chaculate skin ɗin ta ta fito,ta cigaba da rayuwar ta cikin farin ciki

Watannin ta uku a gidan su fauwaz suka dawo,shima Imran gidan ya wuto instead of gidan shi da ya saka Deejan da umaima a ciki. Shi kanshi fauwaz bai ji daɗin abinda Imran yayi ba amma ƙarairayin da suka yi ta zuba masa ya sanya shima ya fara ganin laifin Deeja

An tarbe su cikin mutunci,babu wanda ya nuna musu komai,don dai baba Prof yayi warning kan kar a sake tayar da zancen,don haka ko a fuska babu wanda ya nuna musu komai,umaima sai yatsina takeyi

Lokacin da suka dawo ko ƙeyar Deeja basu gani ba,don bata nan ma ta je yiwa yaya Ma'aruf da Aunty Farida sallama da zasu wuce turkey gobe,bata dawo gidan ba sai bayan maghriba,a lokacin dukan su suna zaune a main parlour ana hira cikin raha da farin ciki,tayi sallama da yawan su suka juyo,ciki har da su fauwaz da umaima,shi kam Imran all of a sudden yaji wani guilty conscience ya shige shi,ya kasa ɗaga kai ya kalle ta

Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai ta gaishe su babu yabo babu fallasa,wasu sun amsa,wasu basu amsa ba,ta tsallake su ta wuce part ɗin Mamie in da ɗakin ta da aka kashe wa kuɗi kamar na amarya yake

To fa!ganin Deeja a gidan,gashi Imran da alamu ya dawo gidan shima,sai umaima taji hankalin ta ya tashi,ta samu aminiyar ta afra ta karanta mata komai sannan ta nemi shawarar ta

Itama afra tana tsoron fauwaz zai iya auren Deeja,don tun ba yanzu ba yana yawan ba ta labarin

Please Login or Register in order to submit comment