Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalin shi kan Deeja,a lokacin ma tuni ta shige cikin gidan,don haka shima ya rufa mata baya

A ɗakin ta ya riske ta,tana ƙoƙarin shiga banɗaki,amma shigowar shi bai hana ta shigewar ta ba,don haka bashi da zaɓin da ya wuce ya nemi waje ya zauna

Bata wuce mintuna biyar ba ta fito, yana kallon ta ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa da suka amshi jikin ta,cikin ta ya fito ɗas gwanin sha'awa

Ganin tana shirin ficewa ya sanya shi faɗin"Deeja zauna muyi magana"

Babu musu ta nemi waje ta zauna, fuskar ta babu alamun damuwa,ta zuba masa idanu jin me zai ce

Cikin taushin murya ya kalle ta yace"Khadija,kin san dai ina son ki ko?"

"Me ya kawo wannan maganar kuma?"ta faɗa tana kallon shi

Hannayen ta ya riƙo yace"ga dukkan alamu kina kallo na a macuci, mayaudari,kuma wallahi ba haka bane, maganar aure na dabam matsayin ki a cikin zuciya ta dabam,inayi miki son da ban taɓa jin irin shi akan wata ƴa mace ba,don haka kar kiyi tsammanin na daina son ki,aure na da Nadiya wata ƙaddara ce da bazan iya kauce mata ba,kiyi ta min addu'a kin ji?"ya ƙarashe maganar cikin Muryar tausayi

Shiru ta ɗan yi,kafin tace"shikenan Khalees,komai ya wuce, Allah ya sanya alkhairi"

Yayi ɗan murmushi yana faɗin"ameen na gode my dear wife"

Mima ma babu shiri ta tattaro ta dawo daga Malaysia,Ana igobe ɗaurin aure ta iso,gidan Deeja ta wuni tana ƙara wayar mata da kai tare da jaddada mata ta riƙi addu'a, don itace makami,kuma makari ga mumini

Anyi biki sosai,an sha shagali, Khalees sai faman rawar kai yakeyi,su Mima ne suke nunawa Deeja cewa kar ta damu,idan namiji yayi sabon aure haka yakeyi

Ta ɗau wanka kala-kala da kwalliya,mai kwalliya ta musamman Aunty Bintu ta ɗauko,sai ta zamo tamkar itace amaryar

Da daddare aka kawo amaryar,a lokacin Aunty Bintu bata ɗakin,sai Mima,kiyya da barrister zee da suke tare da Deejan

Jin guɗa da iface-iface ya tayar da hankalin Deejan,ta miƙe tsaye a firgice,zee tayi saurin kamo ta ta zaunar da ita, Mima tace"cool down my sister,ki kwantar da hankalin ki,wannan damuwar ba mafita bace,kuma idan suka gano cewa kin sani sun fara samun lagon ki,don haka ki daure, Allah yana tare dake, Please my sis"da waɗannan kalamai zuciyar Deeja tayi sanyi,ta samu waje ta zauna

Kai tsaye babban falon aka nufo da amarya,suma su Deejan duk a babban falo suka zauna, Deeja tayi kwalliya har ta gaji da kyau

Umaima tana sawun farko a masu shigo da amarya, sukayi wa juna kallon-kallo ita da Deeja,daga bisani tayi mata murmushi mai nuni da zamu ganar da ke kuren ki, Deejan ma murmushin nuna ƙwarin gwiwa tayi sannan ta kawar da kanta

Suka shigo gaba ɗaya,har da Afra,su Deeja kam basuyi mamaki ba, Saboda sun san Afra da Deeja jirgi ɗaya ya kwaso su suka sauka a tasha ɗaya,nan dai aka gabatar da al'ada sannan masu kawo amarya suka juya suna ta habaice-habaice,babu wanda ya tasamma kula su

Umaima da wata ƙawar su mai suna siyama ne suka zauna da amarya,a cewar su suna ɗebe mata kewa,babu wanda ya damu da su,Aunty Bintu, kiyya da zee suka wuce gidajen su,ya zamana saura Mima kaɗai

A zaton su umaima sun ɗauka duk sun tafi saura Deeja kaɗai,don haka kai tsaye ta shiga ɗakin Deejan a gadarance,ko sallama babu,gashi kuma tayi babbar Sa'a Mima ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin

A lokacin Deeja ta chanja kayan ta zuwa na bacci,baby Pink,sai wata ƴar hula da ta ɗora akan ta, Alqur'ani ne a hannun ta tana karantawa a zuci,sai ganin mutum tayi a gaban ta

Duk da ta ɗan tazama hakan bei hana ta ɗagowa cikin nutsuwa ba,tana ganin umaima ce ta maida kanta ga abinda takeyi

Umaima ta saki shewa tare da faɗin"da kyau MATAR KHALEES ta wucin gadi,ko da yake nayi miki uzuri,da alama giyar soyayya da miji ce take ɗiban ki,amma nan gaba idan zaman gidan Khalees ya gagare ki,ko mukayi miki adalci muka maida ki baiwa a nan gidan,nasan dole za'a girmama mu ko?"

"Ke jahila daƙikiya!ke har kin isa ki maida ta baiwa?ke dai ki lallaɓa auren ki da aka samu aka liƙawa saunan mijin ki,amma Deeja tafi gaban bauta ko a gidan ubanki ne,banza mei toshashshiyar ƙwaƙwalwa,kije ki nemo ilmi ko Allah zai sa a rage asara, Deeja tafi gaban bokan ku ko malamin tsibbun ku"Mima dake fitowa daga banɗaki ce ke faɗin haka

A tsorace umaima ta kalle ta,har ga Allah tana tsoron Mima,don da ganin ta bata da mutunci,Mima ta ƙaraso inda umaima take ta nuna mata ƙofa tana faɗin"maza ɓace min da gani tun kafin wannan koɗaɗɗiyar fuskar taki ta yayyage yanzun nan"sum sum sum umaima ta fice daga ɗakin,cikin sanyin jiki

Tana jin Mima na jan dogon tsaki,amma bata da damar magana don duk masifarta mimab ta sha gaban ta

Mima ta dubi Deeja tace"sister sai haquri fa,kar ki tsaya zub da ajin ki akan Waɗannan karnukan"

Deeja ta mere baki tace"ai tuntuni na bawa banza ajiyar su,don da alama basu san ƙimar kansu ba"


Ina gaishe ku likers da commentors,kune ƙwarin gwiwa na😁🥰😍

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 13

A hargitse umaima ta shiga ɗakin Nadiya tana faɗin"ƙawa!ashe wannan shegiyar likitar tana nan?tsinanniya masifaffiya"

Nadiya tace"rabu da ita,ai dole ta tafi tunda dai ba gidan ubanta bane"

Mima bata juma ba ta wuce gida,tana fita Deeja tayi saurin datse ɗakin ta da makulli,kamar ta sani kuwa,motar Mima na barin gidan su umaima suka zo suka fara buga mata ƙofa,cikin sauri ta ɗauko airpiece ta kunna Suratu Yusuf a wayar ta ta toshe kunnen ta, a haka bacci yayi awon gaba da ita

Washe gari a kitchen ta Samu amarya da ango,cikin shauƙin soyayya suke sarrafa abinda zasu ci,ta sha mamakin ganin Khalees ko kallon ta baiyi ba,amma ta dake tace

"Yallaɓai ina kwana"

Ya waigo yana kallon ta kamar mai yin mamaki,sannan yace"lafiya,bazaki gaida amarya ba?"

Wani watsatstsen kallo tabi amaryar dashi kafin tace"amarya ina gajiya?"

Cikin salon kissa Nadiya tace"gajiya kam babu ita bata da muhalli, saboda na mallaki gwarzon namiji Ni kaɗai,ya zama nawa"

Wani malalacin murmushi Deeja tayi,sannan ta ɗaga babban ɗan yatsan hannun ta alamar jinjina tace

"Ina taya ki murna,kuma na sara miki babbar mace"tana gama faɗin hakan ta ɗauki abin da ya kawo ta tayi hanzarin barin kitchen ɗin

Abin yazowa nadiya a bazata,don tayi tsammanin zata ƙuntata ran Deejan amma sai taga akasin haka,don haka ta bi ta da ido zuciyar ta cike da ƙunci

Duk da hakan ya ɓata wa Deeja rai amma sai tayi ƙoƙarin dannewa,ta shirya ta karya sannan ta fice zuwa office

Daga office gidan barrister zee ta wuce,zee ta rinƙa tausar ta,tare da ƙara jaddada mata ta riƙi addu'a,kuma sam kada ta daina bawa mijin ta kulawa,anan ta yini har bayan la'asar sannan ta koma gida

A falo ta iske su, Nadiya ta kwanta a jikin shi tana ta zuba masa shagwaɓa,shi kuwa duk yabi ya ruɗe,ta shigo da sallama,amma babu wanda ya amsa,itama sai ta ɗauke kanta da nufin faɗa wa ɗakin ta

"Ke dakata!"a cewar Khalees

Cak ta tsaya batare da ta juyo ba,bai damu ba yace"daga ina kike?"

"Daga office,da na taso sai naga ya kamata na bawa amarya da ango waje su sake,don haka nima nayi nawa wuri"ta bashi amsa

"Tabbas kinyi tunani mai kyau"a cewar Nadiya

Deeja ta kalle ta sannan tace"ai ni koyaushe tunani na mai kyau ne,bana abu mara kyau,ba kamar sauran gama garin mutane nake ba,ina fatan kin gane"bata jira amsar ta ba ta shige ɗakin ta

Nadiya tana mamakin Deeja,amma idan ta san wata ai bata san wata ba,dole a haɗa da asiri da tuggu don ganin bayan ta,don haka ta ɗaga kai ta kalli Khalees cikin kissa tana faɗin

"Love da alama gidan ka yafi ƙarfin ka ko?"ya kalle ta cikin kulawa tare da faɗin"me kika gani?"

"Ace kamar ka da kuɗin ka da martabar ka amma ace matar ka tana fita aiki?me za'ayi tunani kenan?baka bata abinci kenan fa,wannan ai sai ya zubar maka da mutunci"ta tsare shi da idanu don ganin yanayin shi

Shiru yayi kafin daga bisani ya gyaɗa kai yana faɗin"zancen ki gaskiya ne love,dole nayiwa tufkar hanci"

Wani sanyin daɗi ya ratsa Nadiya,ta sake gyara kwanciyar ta tana faɗin"Weldone my love,lallai ka cika jarumin maza"yayi wani murmushin nuna jin daɗi yana kallon ta

A ɗaki ya samu Deeja tana danne-danne a laptop ɗin ta,ganin yadda ya shigo mata fuska babu rahama ya sanya itama ta dake ta sha mur, tun daga amsa sallamar shi bata sake duban inda yake ba,shima bai damu ba ya dube ta yana faɗin

"Ban amince miki ki qara fita aiki a gidan nan ba, saboda ba zaman kanki kikeyi ba,da fatan kin gane"yana gama faɗin"hakan ya juya ya fice daga ɗakin

Ta ɗan bi shi da kallo,kafin tayi ɗan murmushi,ta sani sarai aikin Nadiya ne,ai kuwa zata basu mamaki

Washegari ta fito cikin shirin riga da zani na lace,ta ɗora ƙaton mayafin ta a kanta, hannun ta rataye da jakar ta

Yau ma kamar kullum a falo ta tarar dasu suna ciyar da junan su abinci,ko kallon banza basu ishe ta ba tayi hanyar fita

"Ke dakata!"taji Muryar Khalees a fusace

Ta juyo fuskar ta babu alamar damuwa,ta zuba masa ido tana jiran mei zai ce

"Ina zakije?"ya tambaye ta

"Idon ta fes cikin nashi ta amsa"in da na saba zuwa,wato wajen aiki"

"To ban bada izini ba"

Ai dama ba kai ka bani izini na fara aikin ba


"To sai ki zaɓi ɗaya,auren ki ko aikin ki?

Maganar ta dake ta sannan ta qara jinjina wa kaidin Nadiya,Amma da yake jaruma ce idanun ta fes cikin nashi kanta tsaye ta amsa"na zaɓi aiki na"

Ba Khalees ba,hatta Nadiya ta tsorata da jin furucin Deeja, Deeja bata kula ba ta juya ta fice daga falon

Da shirin ta ta dawo daga wajen aiki,a nufin ta duk abinda Khalees zai yi mata ta tanadi abinda zata mayar masa,sai dai ko da ya dawo ko kallon sashen ɗakin Deejan bai yi ba

A haka rayuwa ta kasance musu har zuwa tsawon sati biyu, Nadiya da umaima babu irin asiri da tuggu da basuyiwa Deeja ba amma a banza,duk da anyi nasarar raba ta da mijin ta, tsakanin ta dashi sai kallo daga nesa,amma Allah ya cire mata damuwar hakan

Da farko su Farida suna kawo mata ziyara suna ɗebe mata kewa,amma sai da Nadiya tayi tuggun da Khalees ya hana su zuwa,hakan bai dame ta ba don sau tari ta kan je gidan hajiyan suyi hira,hajiyar tayi ta mata nasihohi da ƙarfafa mata gwiwa

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 14

A haka har lokacin haihuwar ta yayi,tun safe takejin ciwo,amma hakan bei hana ta fita aiki ba,don ciwon ba sosai yake damun ta ba,sai dai ta sanarwa Aunty Bintu da Aunty kiyya cewa EDD din ta ya cika, kuma ga dukkan alamu zata iya haihuwa yau

Daga wajen aikin ta kai tsaye gidan Aunty Bintu ta wuce,ai kuwa ko mintuna ashirin batayi da zuwa ba ciwo ya buɗe mata,aka gaggauta nufar asibiti daita

Sun kai kimanin awa biyar kafin ta haifi sankacecen yaron ta mai tsananin kama da mahaifin shi,sai a sannan hankalin su ya kwanta,Aunty Bintu ta kira kiyya ta sanar da ita,nan da nan tace gasu nan zuwa

Aunty Bintu ta kira Khalees ta sanar masa,amma sai yace bazei samu ɓullo wa ba sai anjuma,yana gama faɗin haka ya kashe wayar

Hakan ya bawa Aunty Bintu mamaki ƙwarai da gaske,sai dai bata sake saurarar shi ba ta zauna jiran su kiyya

Kafin su kiyyan su iso har an shirya baby,ita Kuma Deeja an kai ta ɗakin hutu,su Aunty Bintu suna zaune riƙe da yaron su kiyya suka shigo

Nasir mijin kiyya ne ya kai su,momy Aysha,Mamie babba, nuwaira,lubaisa,sai aunty salma babbar yayar su fauwaz

Nan suka zauna suna kallon baby mai tsananin kama da mahaifin shi,da murmushi a fuskar kiyya tace

"Babyn nan kyakkyawa ne,ya kwaso abban shi da yawa"lubaisa ta leƙa fuskar shi tace"ƙwarai kuwa, Allah ya raya

Basu dauki lokaci ba suka tafi,sai dai sun kawo duk wani abu da suka san mai jego da jariri zasu buƙata

Deeja kam ta sha gata kala-kala,bayan ta nutsu Aunty Bintu ta haɗa mata tea ta bata,haka tayi ta kulawa da ita sosai

Sai dai rashin zuwan mijin nata ya ɓata mata rai duk da cewa batayi mamaki ba,amma sai ta bar abin a ranta

Daga asibiti gidan Aunty Bintu suka wuce kai tsaye,har lokacin Khalees bai zo ba,amma hajiyar shi da ƙannen shi sun zo,don a tare suka fito daga asibitin,hajiyance take tausar Deejan,ita kuma Deeja tana nuna mata babu komai

Khalees ko kiran ta a waya baiyi ba sai da ta kwana shida sannan yaje shi da Nadiya,an karɓe su babu yabo babu fallasa ba'a nuna musu wata damuwa ba, Nadiya ta Sha kwalliya amma sai da ta raina kanta da taga su Bintu da su Mima, don itama a lokacin tazo

Mima ce ta kawo musu jaririn,ya ƙura masa idanu yana kallon shi,wata ƙaunar shi tana ratsa shi,a hankali moments da sukayi da Deeja ya fara dawo masa,ya shagala yana ta kallon shi ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a kwarmin idanun shi, nadiya tana kallon shi tana ganin ikon Allah,ganin kallon yayi yawa sai nadiya tayi saurin amshe shi tana kallon shi,tace"babyn kyakkyawa kamar baban shi"

Bai fi second goma a hannun ta ba ta miƙawa Mima shi,dama dabarar shi ta raba shi da hannun Khalees


Ya kalli aunty Bintu yace"yanzu sai ayi min list na abubuwan da ake buƙata sai na bayar da kudin ko?"

"Ai ko nawa ka bayar ma yayi"a cewar ta

Sai ya zaro bandir na 50k ya dire mata yana faɗin"to ga dubu hamsin"

Abin ya basu mamaki da haushi, amma suka dake,Mima tace"yayi,an gode,sai ka zaɓar wa yaron suna"

Ya miƙe tsaye yana faɗin"ace na bar mata zaɓi,Ni zan wuce, Allah ya raya"

"Ameen,sai anjuma"a cewar Mima suka ɗauki kuɗin suka fito, suma su Khalees suka biyo bayan su, zuciyar Nadiya kamar ta fashe don baqin ciki,ta so tsiya ta tashi, dama ita ta yanke nawa Khalees ɗin zai bayar,amma kuma idan sun san wata basu san wata ba

A cikin mota nadiya ta kalli Khalees tace"honey, gaskiya wadannan mutanen basu da mutunci da alama"

Ya kalle ta yana faɗin"me kika gani?"tace "don Allah kalli abinda sukayi mana,suna magana sai wani ciccin magani sukeyi,ga ƴar wulaqancin ko ƙeyar ta bamu gani ba,kuma ka bayar da kuɗi amma an kasa yi maka godiyar da ta dace, maganar gaskiya bakayi dacen mata ba"

Yayi ɗan shiru yana nazari,ganin ya ɗauki lokaci baiyi magana ba ya sanya ta faɗin"bakace komai ba"

Ya amsa mata da cewa"ai na riga na tanadi hukuncin da zan yanke tuntuni,don ta gama fitar min a rai,gashi ko ke shaida ce bata jin magana ta,kuma kalli irin wulaqancin da tayi mana,ta nunawa duniya Ni ba komai bane a wajen ta,don haka dole nayiwa tufkar hanci"

Wani sanyi ya ratsa Nadiya,amma sai tace"No Kar kayi saurin yanke hukunci,ina da shawara"

Ya kalle ta yana faɗin"menene shawarar ki?"

"Why not bazaka saka wa yaron sunan dad ɗi na ba?"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu

Batayi mamakin ɗan murmushin da yayi ba,yace"good idea,haka za'a yi"

Shiru tayi tana kallon shi fuskar ta ɗauke da murmushi,a ranta kuwa yabawa takeyi da aikin bokan ta mai faɗa da cikawa

Waya ya ciro ya danna number din Deeja,wadda rabon da ya kira ta har ya manta,a da yayi saving number din da luvly Deeja,amma Nadiya ta mayar da sunan Khadija

Bugu ɗaya ta shiga,a lokacin tana zaune tana kallon su Mima da suke ta surutun wulaqancin Khalees ita da intisar da Farida matar yaya Ma'aruf,ta san za'a rina,shiyasa batayi mamaki ba

Wayar ta ce ta soma ruri,ta kai hannu ta ɗauka,ganin sunan Khalees ta tsaya tana kallon wayar da mamaki,amma dai sai ta ɗaga

"Assalamu alaikum"tayi masa sallama

"Wa'alaykis salam,sannu uwar isassu"

Tayi shiru zuwa can tace"ina wuni!"

"A'a riƙe gaisuwar ki,na gode da wulaqanci,sannan da na bar miki zaɓi,amma yanzu na fasa"

"To ba laifi,wanne suna ka zaɓa masa?"ta tambaye shi babu alamun damuwa a tare da ita

"Sa'eed nake so a saka masa"

"Kamar sunan mahaifin Nadiya"ta faɗa da mamaki da ɓacin rai

"Eh,haka nake buƙata"

"To bazan sanya ba,idan tayi zuciyata haifi nata ta sanya"tana gama faɗin hakan ta kashe wayar baki daya tana masifa

Su Mima suka mai da kallon su kanta,ta kalle su tana faɗin"kunji wai sunan mahaifin Nadiya zaa saka?"

"Kamar yaya sunan mahaifin Nadiya?ba cewa su Aunty Bintu yayi ki sanya sunan wa yaron ba?"cewar Aunty Farida cikin mamaki

"Ya chanja shawara,wai na saka sunan baban matar shi, saboda ni daga sama na faɗo bani da uba"ta ƙarashe tana watsa hannayen ta a iska

"Kan bala'i!lallai ma wannan mutumin ya cika ɗan rainin hankali,to me ya mayar da ke?sokuwa ko me?"a cewar Mima cikin fushi,dama a cikin family ɗin su Mima tana daya daga cikin masifaffu

Murmushin takaici kawai Deeja tayi,don tafi zargin akwai abinda Nadiya tayi masa yakeyi mata haka

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 15

Ranar suna an sha shagali,yaro ya amsa sunan Mahmud,sunan mahaifin Deeja, amma Mima ta ɓoye sunan da Affan,anyi hidima sosai,mai jego ta sha ado cikin manyan kaya kala-kala ita da jaririn ta, wasu ita ta siya,da yawan su kuma siya mata akayi,don daga gidan professor Ismail an kawo mata sama da kala ashirin kayan fitar suna,banda na jaririn ta ma,ga su Aunty Bintu,hidima dai sai son barka

Har da umaima akazo suna,sarai sun gane cewa leƙen asiri tazo yiwa Nadiya,don haka Deeja ta zage gayu da facaka iri iri,mai make-up din da tayi mata lokacin bikin mijin ta da nadiya ita Aunty Bintu ta sake ɗauko mata,ga sutura masu asalin tsada da ɗinki mai kyau,ga adon gold abin sai son barka,ga cima kala-kala sai wanda Mutum ya zaba,ba umaima ba kaɗai,hatta da lubaisa sai da ta raina kanta

Umaima bata wani dade a gidan sunan ba ta tafi gida,tana komawa ta kirawo Nadiya ta shaida mata abinda ya faru a gidan sunan, Nadiya taji takaici sosai don so tayi ace Deeja ta wulaƙanta,amma wai umaima ke sanar mata yadda Deeja ya haska kuma ake tarairayar ta a wajen sunan,don haka tace

"Ƙyale ta umaima, alƙawari fa na ɗauka,sai na rusa mata farin ciki,zata san cewa da ni Nadiya gagari kowa takeyi,sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane,sai na sanya ya ɗora hannu aka na rasa mafita,don wallahi sai na sauke mata wannan ji da kan nata,sai tayi data sanin zuwa duniya"ta ƙarasa cikin ɗaukar alwashi da ɓacin rai

"Wallahi ina bayan ki,ke dai kawai ki shirya,dole mu komawa boka"a cewar umaima

"Ai haka za'ayi kawai,don naga alama tana ɓata min aiki,kuma idan nayi mata baya kama ta"

Umaima ta jinjina kai tana fadin"wannan ai mei sauƙi ne,tunda kin gama da wanda take taƙamar ai shikenan"

"Ke dai bari kawai umaima,duk da na raba su harkar gaban ta kawai takeyi,ko kaɗan bata da damuwa,kuma ya kasa kataɓus akanta"

"Keep on trying, watarana zakiyi nasara"a cewar umaima,tana mai ƙarfafa mata gwiwa"

"Har sai kin faɗa?ai na riga na gama yanke abinda zanyi mata na samu ta fita daga rayuwa ta"

"Okay!to Sai na jiki"suka kashe wayar

Taro ya tashi lafiya, hankalin Deeja ya kwanta sosai,don yadda aka tarairaye ta aka nuna musu kulawa ita da jaririn ta ya sanya ta kuma sakin ranta,rashin damuwa da al'amarin ta da Khalees yakeyi kwata-kwata baya danun ta,don ta sani ba yin kanshi bane,kuma bata taɓa fashin saka shi a adduoin ta ba

Gyara sosai aunty Bintu tayi mata,ga ƙara wayar mata da kai da takeyi, kullum cikin tofe ɗan ta da adduoi kala-kala take,kuma dare da rana bata gajiya da yiwa mijin ta addu'a,tare da addu'ar Allah ya bayyana mata yayyen ta,tana son zuwa Yola amma fargaba ta hana ta

Watan ta guda amma har lokacin bata koma gidan auren ta ba,sai dai ta koma bakin aikin ta,Affan kuwa yayi kyau yayi ɓulɓul abin shi,kamannin shi da Khalees sun ƙara fitowa sosai

Zaman Deeja a gidan Aunty Bintu ya taimaka ƙwarai wajen tafiyar da kaso mai yawa na damuwar ta,ta nutsu sosai tana aikin ta,tana son komawa makaranta don ƙaro karatu amma tana tsoron tunkarar Khalees da batun,don haka taga gwara ta haƙura kawai,har sanda al'amura zasu daidaita

Don haka ta cire damuwar komai a ranta,ta riƙi aikin ta da yaron ta sosai

Watanni biyu suka shuɗe,Deeja tayi kyau tayi haske sosai,a lokacin sati biyu ya rage su Aunty Bintu su tafi kasar Syria,don haka Deeja ta fara shirin komawa gida

Ranar da zata koma Aunty Bintu ta aika aka gyara mata ɗakin ta,nadiya na zaune tana jin kiɗa sai ga su intisar sun shigo da sallama

Su shida ne,intisar,ilham ƙawar intisar sai masu aikin Aunty Bintu su huɗu

Sheƙeƙe ta kalle su sannan ta zare airpiece ɗin kunnen ta tana kallon su a wulaƙance,cikin isa da gadara tace "ku kuma fa?daga ina?"

Intisar ta kalle ta sama da ƙasa tace"yi haƙuri,ba wajen ki muka zo ba,kin gane?"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta ciki,suma sauran suka biyo bayan ta

Nadiya ce ta biyo bayan su tana faɗin"maza maza kuzo ku fice min daga gida,matsiyatan yara kawai"ko kallon ta basuyi ba suka wuce suka kama aikin su

Basu juma sosai ba suka koma gida,suka zayyane wa Auntyn Abinda Nadiya tayi musu amma suka mayar da ita mahaukaciya,sukayi ta dariya

Da yamma su Aunty Bintu suka raka Deeja gidan ta tamkar masu kai amarya, nadiya ta tsorata sosai ganin dawowar Deeja,ganin Deejan babu alamun damuwa a tare da ita ya firgita Nadiyan,amma sai tayi tsammanin ko ta san da tafiyar da Khalees yayi ne, kasancewar Khalees yaje wata seminar a Abuja jiya,Kuma bazai dawo ba sai bayan sati uku

Su Aunty Bintu suka gama abinda ya kawo su suka tafi, Nadiya na ganin sun tafi sai tayi azamar shigowa

Deeja na zaune tana shayar da Affan Nadiya ta shigo,kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kanta,don ta san ko ma menene ya kawo ta ba na arziki bane,don ko sallama batayi ba. Nadiya ta dube ta a wulakance tace

"Ai dole ki ɗauke kanki,don ni na baki damar shigo min gida har zan shigo in da kike ki ɗauke kai,wato kinji labarin miji na baya nan ko?hakan yayi kyau,amma ki shirya karɓar tanade tanade da nayi miki......."

Karatun Alkur'ani Deeja ta sanya,ta janyo airpiece ta saka a jikin wayar ta toshe kunnuwan ta dashi hakan ne ya tilasta wa nadiya ficewa daga ɗakin tana jan tsaki,a ranta tana ayyana ko me zatayi sai tayi don ganin ta kuntatawa Deeja

Daga lokacin ya zamana kowa harkar shi yakeyi,sai dai Nadiya ta tsani ta buɗe idanu taga Affan,ta tsani yaron tsana mafi munin,don haka ta sha alwashin sai taga bayan shi,har da uwar tashi ma

Har da zan ɗauki hutun ma'aikata na yau nima,kawai sai nayi tunani na fasa😁😉

Ayi min afuwa biki mukeyi shiyasa akaji ni shiru

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Kwanan nan fa sai ana min uzuri 😅 saboda ciwo na da yake yawan tashi yana buƙatar hutu,still ayyuka sunyi yawa,gashi nan dai gashi nan dai,duk da haka ina godiya kuma at the same time Ina neman afuwa 🙏

Page 16

Sai dai bata samun damar,hakan, saboda Deeja bata taɓa barin Kofar dakin ta a buɗe matuƙar ba fitowa zatayi ba,kuma indai zata fita goya shi takeyi ko ta datse ɗakin

Kwanan ta tara da dawowa da yamma bayan tayi sallar la'asar tana zaune tana gyara kayan Affan a taji ƙaurin miyar da ta ɗora,da sauri ta miƙe ta fito ta gyara miyar sannan ta koma ɗakin ta

Tun kafin ta ƙarasa ɗakin taji Affan ya canyare da kuka,da gudu ta ƙarasa don ta san bacci ta fita ta bar shi yanayi

Abinda ta gani ne yayi matuƙar gigita ta, Nadiya ce take shafawa Affan niƙaƙƙen barkono a fuska,wani ihu Deejan ta saki sannan tayi kan Nadiya, Nadiya ta firgita da zuwan ta amma tayi saurin watso mata ragowar yajin, Deeja ta goce sannan ta hankaɗe Nadiyan ta ɗauke ɗan ta

Kai tsaye banɗaki ta nufa da yaron tayi masa wanka sosai,amma har lokacin bai daina kuka ba,ta fito duk jikin ta rawa yakeyi,a lokacin Nadiya bata ɗakin,ta cire zanin gadon ta sanya wani ta kwantar da yaron tana kallon yadda fuskar shi tayi ja yana ta tsanyara ihu,kamar wadda aka tsikara tayi maza ta ɗauke shi da nufin shayar dashi amma yaƙi kamawa,sai kawai ta fashe da kuka mai motsa rai, hankalin ta ya kai ƙololuwa wajen tashi,tana tunanin mafita amma ta rasa dabara

Wayar ta ta soma ruri,a firgice ta ɗauka ko ganin sunan batayi ba ta ɗaga

Muryar ƙawa ta safeena taji tana faɗin"Hello! Deeja bakya ji na ne?"

Sabon kuka Deeja ta saki, safeena tace"subhanallahi!ina hanya gani nan zuwa"

A harabar gidan ta samu Deeja tsaye tana jiran ta,ko daidaita parking batayi ba ta fito tana faɗin"lafiya dai?"

Deeja bata iya magana ba illa nuno mata Affan da zuwa yanzu ya fara rage kuka,da sauri safina ta amshe shi suka faɗa mota suka nufi asibitin doctor su'ad

Tayi masa abinda ya dace,ya samu bacci,sai a lokacin

Please Login or Register in order to submit comment