Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita!"ya faɗa cikin wata raunananniyar murya da Deeja bata san yana da ita ba

Jin hakan ya sanya Deejan dawowa tana faɗin"to bani magani na"

Shiru yayi zuciyar shi cike da damuwa,ita kuwa ganin bashi da niyyar magana taja ƙafafuwan ta ta shige ɗaki ta faɗa kan gadon ta,ko second talatin batayi ba ya shigo da sallama,ta amsa idanun ta a lumshe,har yanzu yunwa na ƙwarzabar ta,amma damuwa ta hana ta bawa cikin ta haƙƙin shi

Zama yayi a bakin gadon,cikin sanyin murya ya furta"Khadija!"

Zata iya cewa wannan shine karo na farko da ta taɓa jin sunan ta a bakin shi,amma hakan bei hana ta amsawa

"Na'am abdurrashid!"itama ta kira cikakken sunan shi

"Ki tashi zamuyi magana"ya faɗa cikin marairaicewa

"Yunwa nakeji Ni kam,bazan iya fahimtar zancen ka ba"

"Don Allah ki taimaka min,zan samo ko me kike so ki ci, maganar ba mai tsawo bace"

Zaune ta tashi tana cike da mamakin sauyawar Khalees lokaci ɗaya amma har yanzu ta hana hakan bayyana akan fuskar ta

"Khadija me ya sauya ki ne?"me ya sauya min ke ne?me ya same ki ne?"

"Me nayi?"ta faɗa cikin ɗaure fuska

"Menayi miki da zafi haka kika tsane ni?kike son yi min asarar ɗa na?"ƙwalla ta cika idanun shi

Sai jikin Deeja ya fara rawa, Khalees ya cigaba da cewa"ko da ace wani laifi nayi miki bei kamata ki hukunta Ni ta wannan hanyar ba,balle ma me nayi miki?"

Deeja ta dake tace"haba Khalees!ai girman ƙiyayyar da kakeyi min ta fi ƙarfin wani gama garin laifi,to baka san saniya me zaka yi da ƙahon ta?baka so na me zaka yi da ɗa na?"

Da sauri ya katse ta yana faɗin"Khadija wa yace Miki bana son ki?me yasa kika ce haka?kin san yadda nakejin ki a raina kuwa?kwana biyu da kikayi bakya nan kin san a halin kewar da na kasance kuwa?idan kika ce haka bakiyi min adalci ba"

Daga inda take tana iya jin sautin bugun zuciyar shi,hakan ya sanar da ita irin tashin hankalin da yake ciki, cikin sanyin murya tace

"To meyasa baka nuna min so kamar yadda kowaɗanne ma'aurata suke gudanar da rayuwar su?ban taɓa yin abu ka yaba ba,sai dai idan nayi kuskure ka janyo min ɓacin rai, tsakani na da kai kallon banza,tsawa,baƙar magana sai kace baiwa,kayi min adalci saboda Allah?"hawaye suka ciko idanun ta

Ba ƙaramin abu ne yake sanya Deeja kuka ba,ya daɗe da sanin hakan,da sauri ya goge mata hawayen sannan yace

"Khadija, wallahi tallahi ba da nufi nayi miki abinda nayi miki ba,nayi hakane don na nisanta kaina dake kar ki illata ni kamar yadda sauran mata na sukayi min

Khadija! mahaifi na bai taɓa bani damar auren zaɓi na ba, karon farko ya aura min fadila,fadila ta kasance malalaciya,babu abinda ta iya sai rashin wda nuna ita wata ce,gashi a ƙarshe tace bazata haihu yanzu ba don kar ta tsufa,wannan ne yayi sanadin rabuwar mu

Banyi cikakken wata uku ba daddy ya kuma zaɓa min suhaima,ita kam lamarin ta yafi na fadila muni,don kwata kwata bata zaman gida,ga sace sace kamar ɓera,ban isa nayi ajiya a gida ba sai ta ɗauke,na sanar da Daddy Amma sai yake ganin kamar ƙarya nayi,haka nake ta haƙuri daita

Rana tsaka ta tayar da ballin sai na sake ta,na sanarwa Daddy abinda ke faruwa,ya kira mu sa niyyar yayi mana sulhu,amma sai ta baɗawa idanun ta toka ta ci masa mutunci,ganin haka Daddy ya bar Ni na sake ta

Bai daddara ba,naje Egypt na dawo bayan naje gaishe shi yake shaida min cewa yayi min aure, hankali na ya tashi,amma hakan na daure na amshi maganar da girmamawa, musamman ma da aka ce min ƙanwa ta ce aka aura min

Labiba,itace ƴar ƙanwar Daddy da aka aura min,itama sam bata da lokaci na,ta sha fita ƙasashen waje batare da sani na ba,da sunan tana zuwa kasuwanci,tun abin na damu na har na cire shi a raina

Baƙar ranar da bazan iya mantawa daita ba itace ranar da na kama labiba da wasu mata suna sheƙe ayar su,abin nan ya gigita Ni sosai,kafin nasan abinyi labiba ta buga min wani abu a kai na da ƙarfi,na daɗi sumamme, ita kuwa ta tattare duk wani abu mai muhimmanci da tasan inayin amfani dashi ta gudu

Sai da nayi kwana biyu a asibiti sannan na samu kaina, mahaifiya ta da sauran ƴan uwana sun shiga matsanancin tashin hankali suka yi ta roƙon mahaifi na akan yayi haƙuri ya bar ni na samu zaɓin raina ko Allah zai sa a dace,amma sai yace har yanzu Ban mallaki hankalin kaina ba,kuma a lokacin ina da shekaru talatin da biyar zuwa da shida

Ganin irin kafiyar shi ya fusata mu,muka ɗauki aniyar duk macen da ya ƙara aura min sai mun matsa mata mun takura mata har ta gudu ta bar mu,cikin ikon Allah sai kika zama mace ta gaba

Wannan shine dalilin da yasa bakya samun afuwa a wajen mu ko, ko ni ko hajiya ko qanne na

Wallahi ba don Bama son ki ba,don uzzurawar daddy,Amma kiyi haquri ki yafe mana,haƙiƙa mun aikata kuskure

Kuka sosai Deeja ta fashe dashi na tausayin mijin nata,ya janyo ta ya rungume ta yana sauke numfashi,da ƙyar ya lallashe ta tayi shiru,sannan ya miƙe ya nufi kitchen don samar mata abinda zata ci

***** ***** *****

Tana kwance jikin kafaɗar shi ta ɗago idanun ta ta kalle shi tace

"Honey!"

Kallon ta yayi batare da ya amsa ba,ta tashi zaune sosai tana fuskantar shi tace"honey tambayar ka nake son yi"

"Okay Ina jin ki, Allah yasa na sani"

"Ranar bikin Yasmeen na ganka tare da wani,wanene shi don Allah?"

"Wa kenan?"ya sake tambayar ta

"Wani kyakkyawa kamar kai,amma da alamu zeiyi jin kai"


#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 9

Wani mugun kallo ya watsa mata,tayi dariya tace"haba my king, wallahi ka fi dukkan maza a waje na,so nake nasan waye shi?"

"Ban gane shi ba"ya faɗa yana sassauta fuska"

"Haba!wani mei shadda sky blue!naga kun fito daga falon Mamie tare"

"Ooooooo! Na gane, engineer abdurrashid kike nufi"

"Yauwa,ƙawa ta Nadiya ce ta ganshi,kuma yayi mata"

Wani watsatstsen kallo ya jefa mata yace"to yana da aure idan baki sani ba"

"And so what?ba namiji bane?ai shi namiji mijin mace huɗu ne"

"Eh lallai umaima!to mijin Khadija ne"

Ta ɗan bi shi da kallo kafin tace"wacece khadija?"

Ya amsa da cewa"tsohuwar mata ta"

Taɓe baki tayi tace"to wacece ita? sai me?"

"Kinyi silar barin ta gida na,bazan taɓa bari kiyi silar barin kiyi silar barin ta gidan Khalees ba, saboda ta bani farin ciki ta bani walwala a lokacin da na rasa walwala,ta zamar min bango a lokacin da na rasa masafa,ni kuma na kasa yi mata halacci,na baɗa mata ƙasa a ido,na guje ta a lokacin da take buƙatar kulawa,don haka kawai ki bawa ƙawar ki haƙuri"

"Abinda bazei yiwu ba kenan!"a cewar umaima

"Okay!sai kiyi duk abinda kike ganin zaki iya"

"Zanyi kuwa"tana faɗa ta fice daga ɗakin,ya bi ta da kallo

***** ***** *****

Rayuwar auren Deeja ta sauya,kullum cikin tarairayar ta yake,haka suma dangin shi sun chanja mata sosai,duk wani abin kwaɗayi da take so sukan shirya su kawo mata,nan da nan ta murje tayi kyau,ciwon zuciyar ta ya lafa sosai da sosai,ta kasance cikin farin ciki sosai, yanzu abu ɗaya ne yake damun ta in da zata samu yayyen ta guda biyu,nusaiba da Yusuf da ko ɗuriyar su bata ji,amma Mima ta kan kwantar da mata da hankali da cewa in Sha Allah suna cikin kwanciyar hankali,kuma zasu waiwaye ta duk daren daɗewa

Hakan ya sanya ta cire damuwar wannan a ranta,ta rungumi mijinta ta cigaba da rainon cikin ta da a yanzu zai kai watanni biyar

***** ***** *****

Nadiya ce zaune ita da umaima a haɗaɗɗen ɗakin umaiman, Nadiya ta kalli umaima tana faɗin"ƙawa ta ya ake ciki ne?Ni fa na damu da batun wannan sweet guy ɗin"

"Sunan shi abdurrashid,kuma tsohon mijin wannan kucakar ne, tsohuwar matar husby"umaima ta faɗa zuciyar ta cike da hassada,don dai ta san Deeja tafi gaban a kira ta kucaka,ban da wannan ma,ko a faifai aka ajiye mai kama da ita da mai kama da Deeja sai an riga ɗaukar Deejan

"Da kyau,kice zamu gwara kan shegiya mu ga mei tsaya mata,kaf garin nan waye ya isa ya ja damu?"

"Babu kam,yanzu dai mu shirya mu je wajen boka mai gaba ɗaya"babu musu suka miƙe suka ɗau hanya

***** ***** *****

A ƴan kwanakin nan Deeja ta fara ganin sauyi a wajen Khalees,ya rage zaman gida,ya rage tarairayar ta da kulawa da ita,hakan na damun ta sosai,da ta sanarwa fareeda sai tace suma ya chanja musu,sun kasa gane kanshi, Deeja ce tace zata tambaye shi

Da ya dawo ta same shi a ɗakin shi,da ta tambaye shi sai yace ayyuka ne suka sha kanshi,bata yarda ba amma sai ga bar shi a hakan

Har ma'aikatar su Nadiya taje da zummar tana neman wani,anan ta haɗu da Khalees,ai kuwa ya rikice mata sosai,ta rinqa ja masa aji,da ƙyar ta yarda ta bashi number wayar ta

A ranar ta kira umaima ta shaida mata,ihun murna umaima ta rinƙa yi tana godewa bokansu

Allah Sarki!Nana khadija baiwar Allah!!zuwa yanzu Khalees baya samun lokacin ta,sai dai su Farida sukan zo ɗebe mata kewa, hakan yana kawo mata sauƙi


Yau asabar ce,yana gida,akan gado ta riske shi yana waya,ga dukkan alamu da mace yake waya,sai fara'a yakeyi yana kashe murya, gefen gadon ta samu ta zauna,lura da zuwan ta ya sanya shi saurin katse kiran yana kallon ta tare da faɗin

"Ya dai?maman twins?"

"Ta zuba masa idanu,tana lura da yanda ya daburce tace"da wa kuke waya haka ne?ko sanin da shigowa ta ma bakayi ba da alamu"ta ƙarashe da ɗan murmushin da za'a iya kiran shi da na yaƙe

Al'adar Khalees bei iya ƙarya ba, balle yaudara,don haka ya gyara zama ya dube ta yana faɗin

"Luvly Deeja,nasan cewa zaki fahimce ni,nasan cewa zaki iya haƙuri dani

Deeja kiyi haƙuri,nan da three days za'a ɗaura aure na"

"Aure fa kace!"ta faɗa cikin ɗaga murya, hankalin ta a tsananin tashe

"Be calm please! wallahi nima bansan yadda akayi hakan ta faru ba,ban san me ke damu na ba, Please kiyi min uzuri"hawaye suka ciko idanun shi

Babu abinda Deeja keyi sai nanata"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"har taji relief a zuciyar ta,ga kalaman kwantar da hankali da yake mata

Sun kwashi mintuna a haka kafin tace"to naji Khalees,nasan haka zata faru daman, wacece zaka aura ɗin?a ina take?"

"Ƙawar matar abokina ce"

Gaban Deeja ya buga tace"wa kenan?"

"Aboki na Imran!"

"What!a cewar Deeja cikin ƙaraji,tayi wani kukan kura ta ci kwalar shi...

#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 10

Duk yadda yayi ya kwace kanshi yaci tura,ta damƙe shi cikin fitar hayyaci tana faɗin"macuta! azzalumai!!mugaye!!!me nayi muku?dama nasan bazaku ƙyale ni ba,dama nasan sai kunyi min haka, Allah ya fi ku!"haka tayi ta sambatu cikin fitar hayyaci wanda Khalees ba fahimta yakeyi ba, ƙoƙarin shima ya ƙwaci rigar shi da ta cukwikwiye

Allah ya bashi Sa'a,yana ƙwace rigar tashi kuwa yayi harabar gidan a a guje, Deeja kam yaraf ta faɗi ƙasan tiles tana mayar da numfashi,amma har yanzu idanun ta babu hawaye,amma sun tsumu da tashin hankali

Shi kam Khalees cikin azama ya nufi motar shi,yana shiga ya fara yiwa mai gadi horn,cikin azama ya ɗaga gate ɗin,har yayi gaba ya dawo ya cewa mai gadin

"Ko da yaya kar ka bari matar gidan nan ta fita,idan kayi wannan kuskuren to a bakin aikin ka"yana gama faɗar haka ya ja motar shi ya bar wajen zuciyar shi cike da tashin hankali

Cikin tsananin gigita Deeja ta yunƙura ta miƙe zata fice daga ɗakin,wayar Khalees tayi ƙara,babu dogon tunani ta ɗauki wayar ganin sunan my heartbeat da emoji na heart ❤️,tayi gaggawar ɗagawa amma bakin ta ɗauke da sallama

Daga can ɓangaren taji anyi shewa gami da faɗin"MATAR KHALEES a yanzu"

"Wacece?"Deeja tayi ƙarfin halin tambaya

"Upcoming MATAR KHALEES,don ki sani Khalees nawa ne Ni kaɗai,muddin na shigo gidan nan babu wata mace da ta Isa ta ko da kalle shi ne,amma a yanzu dai na baki aron shi kafin in shigo......"jin bazata iya jurar abinda matar ke faɗi ba ya sanya ta saurin datse kiran,ta miƙe a gigice ta janyo mayafin ta ta yafa,ta nufi harabar gidan ko ganin gaban ta batayi

Sai dai duk yadda taso malam Audu ya bar ta ta fita hakan ya ci tura,nan da nan ta fara wani irin haki wanda sai da ya kai ta ƙasa

Ma'aikatan gidan ne suka nemo Khalees a waya,dama ba nisa yayi ba,ai kuwa sai gashi yazo,cikin sauri ya sanya ta a mota ya umarci driver ɗin shi da ya kai su asibitin Dr su'ad

A can asibiti Dr su'ad da wasu manyan likitoci suka rufu akan ta,sun kai awa guda suna abu ɗaya, Khalees sai kai wa da kawowa yakeyi cikin tashin hankali da damuwa,ya san zancen auren shi ne ya tayar wa da Deeja hankali har haka, amma bayajin zai iya janye maganar auren,da zai iya da ya janye

Yana tsaye Dr su'ad ta fito fuskar ta babu walwala,yana ganinta sai da yaji gaban shi ya faɗi,ta kalle shi tace"engineer Abdul biyo ni"babu musu ya bi ta,amma zuciyar shi cike da taraddadin abinda zata ce,yasan ko menene ba mei daɗi bane

Suna shiga ta nemi waje ta zauna, shima ta nuna masa wajen zama,ya zauna yana sauraron abinda zata ce

Ta zare glass ɗin idanun ta tana kallon shi tace

"Wato da farko munyi tsammanin ciwon Deeja ya tafi tun bayan dawowar ta daga Spain,duba da cewa zaka kula da lafiyar ta,sai dai kuma abu ya chanja ba kamar yadda muka zata ba,ciwon Deeja yana nema ya dawo sabo,ga cikin ta da yake barazanar fita, gaskiya Khalees idan baka kula ba zaka iya rasa Deeja da abinda yake cikin ta baki ɗaya,don haka ka kula"tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga office ɗin

Faɗar irin tashin hankali da Khalees ya tsinci kanshi a ciki ma ɓata baki ne,ji yake a ranshi dai da yanda zai yi da yayi ya fasa auren,amma ina!ji yake idan bai auri Nadiya ba zai iya mutuwa,yayi tagumi da hannu bibbiyu yana tunanin mafita

Ganin bai samu komai ba ya tilasta masa miƙewa,jikin shi babu ƙwari ya fito daga office ɗin,yana fitowa wayar shi ta soma ƙara

Da yayi niyyar share ta,amma sai ya ɗauko ya duba,fareeda ce

Cikin sanyin jiki ya ɗaga, Farida ce ta soma magana"bros meke faruwa ne?ina ta kiran ka amma kaƙi picking"

Cikin Muryar tashin hankali yace"Farida ina cikin damuwa, luvly Deeja tana kwance a nan asibiti bata san in da kanta yake ba"

"Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!me ya same ta?"a cewar Farida cikin ruɗewa

"Ciwon ta ne ya tashi"a cewar Khalees cikin rawar murya

A gigice Farida tace"wane irin ciwo ne da ita?"

"Heart attack ne"ya bata amsa

"Subhanallahi!gamu nan zuwa"ta kashe wayar

Yana zaune a reception abin duniya ya dame shi suka ƙaraso,har da Hajiya da ƙanwar shi mai bin shi Aunty sameera,suka ƙaraso fuskokinsu babu annuri kowacce ta nemi waje ta zauna

Sun ɗan yi shiru na ƴan sakwanni kafin hajiya ta dubi Khalees cikin ɗaurewar fuska tace

"Me nakeji haka ne?wane irin baƙin labari Farida ke sanar dani ne?"

Shiru Khalees yayi,kafin ya fara maganar cikin rawar murya

"Hajiya ciwon ta ne ya tashi"

"Me ya tayar mata da ciwo?"ta faɗa tana tsare shi da idanu

"Eh.......to........dama.......dama....zancen a...auren nawa ne"yayi shiru cikin damuwa

"Wai auren dole ne yin shi?"ta faɗa cikin ɗaga murya

Khalees ya kwantar da murya yace"amma hajiya ya kamata kiyi min uzuri,dukkan ku kun so ace na auri zaɓin raina,amma hakan bei yiwu ba sai yanzu"

Hajiya ta girgiza kai tace"tabbas a da naso ka auri zaɓin ran ka,amma banda yanzu,ko a lokacin da naso ka auri zaɓin ran naka naso hakan ne saboda rashin dacen zaɓa maka mata da abban ku keyi maka,amma yanzu alhamdulillahi,an samu dace,to meye na ƙara auren kuma?"

"Don Allah Hajiya ku taimake ni ku bari nayi auren nan, wallahi idan har banyi ba zan iya mutuwa,ina matuƙar son Nadiya"

Har hajiya ta buɗe baki da zummar yin magana sameera ta kaɗa mata ido tayi shiru

Sun samu ganin Deeja, hankalin ya tashi ganin yadda ta rame lokaci ɗaya,sai ɗan cikin ta da shima ya rame,cikin sanyin jiki suka fito suka nufi gida

Suna tafiya akan titi,sameera ce mai tuƙi,sai hajiya a gefen ta,sai Farida da Jannat a baya,sameera ta kalli hajiya tace"hajiya dole fa ki ƙara ƙaimi da addu'a, alamu sun nuna akwai hannu cikin lamarin yaya Khalees"

Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace"Ni kaina zargin da nakeyi kenan surayya,kuma babban abin takaicin da mahaifin shi yaƙi mara masa baya ya nemo matar aure amma yanzu don Allah ji ya amince da wannan auren,kuma wallahi tausayin yarinyar nan nakeyi,don bansan me amaryar nan tazo dashi ba,amma kuma ai akwai Allah"

"Hakane,inji Aunty sameera"Allah ya shige mana gaba"suka amsa da "ameen"

Sai da Deeja ta samu awa shida sannan ta dawo hayyacinta,a firgice ta farka tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin da aka kwantar da ita, Dr su'ad da ta shigo yanzu tayi saurin kwantar da ita tana fadin"Ina zakije ne?"

Ta kalli Dr su'ad da rinannun idanun ta tace"Dr rabu da ni kawai"ta ƙarasa tana ƙoƙarin zame hannayen ta daga na Dr ɗin,kuma a lokaci guda tana ƙoƙarin miƙewa tsaye

"Cool down madam,me yayi zafi haka?don Allah ki bi komai a sannu,komai zei warware in Sha Allah,Amma wannan zafin ran da kike nunawa ai bashi da wani amfani ko?"

Cikin Muryar ɓacin rai tace"Dr duk bayanin da zanyi miki baza ki gane bane,kawai ki bar ni naje in da zanje"

"No bari na sanarwa engineer,don bazan kwana a ciki ba"

#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****

✍️ Nusy bee

Page 11

Kafin Deeja ta kuma cewa wani abu ta zaro waya ta fara kiran Khalees,ganin kiran doctor su'ad ya Sanya shi azamar ɗaga kiran,yana ɗagawa tace"kazo ɗakin da aka kwantar da Madam ɗin ka"bata jira amsar shi ba ta kashe kiran

Minti biyu tsakani sai gashi ya shigo cikin sauri,ganin ta a zaune yayi saurin nufar ta,amma ta dakatar dashi cikin ƙaraji

"Kar ka ƙaraso in da nake Khalees,kar ka soma, Wallahi na tsane ka macuci, mayaudari, azzalumi,wanda bei san darajar mace ba,wallahi abinda kukayi min sai Allah ya saka min,don bazan taɓa yafe muku ba, munafukai annamimai,kuma na gama auren ka,dole ka sake ni,maƙaryaci kawai"idanun ta sun kaɗa sunyi jawur,amma ko ɗigon hawaye babu,don dama can ita ba mai saurin kuka bace

Ba Khalees ba,itama Dr su'ad abin ya ɗaure mata kai,suka shiga bin ta da kallo, Dr su'ad ta matsa kusa da ita tana faɗin"haba malam!mijin ki ne fa,a ƙalla ya samu wannan alfarmar ko?"ita kanta Dr jikin ta rawa yakeyi, ballantana Khalees da ya shiga mummunan tashin hankali

Deeja ta ƙarasa zare hannun ta gami da faɗin"a da yake amsa sunan miji a waje na,amma a yanzu"ta girgiza kai gami da miƙewa tsaye

Duk yanda suka so Deeja ta saurare su hakan yaci tura,a ranar Khalees yaga ainihin kalar matar shi,dole suna ji suna gani ta fice daga asibitin

Bin ta sukayi da kallo,tana fita Khalees ya lallaɓa ya bi bayan ta,napep ta tsare,ta shiga, shima ya shiga motar shi ya bi su

Kai tsaye gidan Aunty Bintu ta nufa,mai adaidaita sahun yayi parking, wajen mai gadin ta ranci kuɗi ta sallami mai adaidaitan,sannan ta shiga cikin gidan

Khalees ne ya fito daga motar shi ya baiwa mai gadin maƙudan kuɗaɗe,mai gadin ya fara godiya,yayi saurin dakatar dashi yace"kuɗin da Deeja ta karɓa a Wajen ka ne,ragowar kuma ka riƙe"yana gama faɗar hakan ya koma cikin motar shi ya tayar ya tafi

Deeja kuwa a hargitse ta shiga cikin gidan,intisar tana zaune a falo tana buga game a wata Deeja ta shigo

Cikin tsoro da mamaki intisar ta tare ta tana faɗin"sannu da zuwa,lafiya Aunty Deeja?"don ta san Deeja da nutsuwa

Deeja ta kalle ta da rinannun idanun ta tace"ina Aunty Bintu?"

"Ta tafi dubiya,ɗan wata ƙawar ta aka kwantar a asibiti"

Deeja ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,ita dai intisar kallon ta kawai takeyi a ɗimauce,zuwa can Deeja ta kalli intisar tace

"Kina da ɗari biyar?"

"Eh,amma dubu ɗaya ce"

"Babu laifi,kai wa baba mai gadi ki ce ya ɗauki kuɗin shi"babu musu intisar ta miƙe ta nufi harabar gidan,jim kaɗan ta dawo ta shaidawa Deeja cewa baba mai gadi yace wani ya biya kuɗin

Sai da gaban Deeja ya faɗi,don bata raba ɗayan biyu Khalees ne, saboda tayi zargin ya biyo ta,amma sai bata nuna ba,sai ma kwanciya da tayi tana tunanin mafita

Intisar bata sakeyi mata Magana ba,ta koma kan computer ta cigaba da danne-dannen ta

A haka suka kasance har sanda aunty Bintu ta dawo,da sallama ta shigo falon

Dukan su suka amsa mata,tayi mamakin ganin Deeja,amma sai ta ɓoye,sukayi mata sannu da zuwa,ta amsa da sakin fuska,ta dubi Deeja da sigar tsokana tace

"A'a!mai jegon gobe,yau wacce rana mai girma Khalees ya bamu aron ki?"

Dukan su sukayi ƴar dariya, amma Aunty Bintu ta gane dariyar dole Deeja takeyi, saboda alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta

Amma a lokacin Aunty Bintu bata nuna mata komai ba,ko ba komai bai kamata ta sanya ta tona cikin ta a gaban intisar ba

Wajen ƙarfe tara na dare Aunty Bintu suna tare da Deeja a ɗakin Auntyn,in da suka bar intisar da salim da mei bi wa salim sumayya suna kallo a parlour,su Kuma suka zame suka nufi cikin ɗaki

Cikin kulawa Aunty Bintu ta kalli Deeja tace"Deeja,ko baki gaya min ba akwai alamun damuwa a tare da ke,damuwar da ce ta dawo ko wata sabuwa ce?"

Duk abinda ke faruwa zuciyar Deeja a dake take,sai yanzu ta fashe da kuka mei cin rai,sai da tayi mai isar ta,aunty Bintu batayi ƙoƙarin dakatar daita ba,ta kalli aunty Bintu tace

"Aunty Ina cikin wani hali,aunty ina cikin tsaka mai wuyar fita,Aunty Ni dai tawa ta ƙare,Aunty Ni kam......."

"Wait!wait!!yaya kikeyi min wasu zantuka kamar wata jahila?me kike nufi da hakan?ki fito kiyi min bayani sai nafi fahimtar ki,ko sakin ki Khalees ɗin yayi?"

Cikin kuka tace"ƙanin saki yayi min aunty,Wai.....Wai kishiya zeiyi min"

Cikin takaici Aunty Bintu ta ja dogon tsaki tace "to sai me?kishiya kan ki aka fara?ko akan ki za'a ƙare?ko a kanki zata zauna?"duk da cewar maganar ta doki ran ta

"Aunty ƙawar matar Imran fa zai aura,,tace wai sai ta raba Ni dashi fa"

"Ƙawar matar Imran kamar yaya?"Aunty Bintu ta tambaya a ɗan firgice

"Wallahi ƙawar matar Imran zai aura,saura kwana uku ɗaurin auren"

Aunty Bintu ta danne damuwar tava matsayin ta na babba tace"to sai me?ya auro ko waye ma?me zai tsorata ki?ke fa jinin ISHAQ ce,kuma kin san mu Bama sanya da addini,don haka kar kiyi wasa da addu'a,idan da nufi akayi auren kina zaune gayyar zata watse,idan ba da nufi bane ma zaki gani,na sanki da dauriya,to ki ƙara daurewa,kiji ki nuna baki ji ba,ki gani ki kauda kai,kar ki kuskura ki nuna musu ɓacin ranki,don zasuyi miki dariya, Allah shine gatan mu baki ɗaya,duk abinda ya samu bawa dama can tun kafin halittar shi Allah ya ƙaddara haka,don haka ki maida dukkan lamuran ki ga Allah"

Kalaman Aunty Bintu sun sanyaya mata jiki,tayi shiru tana nazari, cikin kwantar da murya Aunty Bintu ta ƙara da cewa

"Ki daina saka damuwa irin wannan a ranki, tabbas nasan akwai ciwo amma idan baki ɗauke shi da zafi ba zai zo miki a sauƙaƙe,kinga dai baki da wadatacciyar lafiya,kuma bake kaɗai bace,idan kika yi ganganci da Rayuwar ki har kika mutu mu kikayiwa asara,mijin ki wata zai auro,burin kishiyar taki kenan,to ina ranar wannan abu?"

Likers sa commentors wannan naku ne👍👍👍🥰

#Nusy_bee


*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 12

"Nayi Miki alƙawari in Sha Allah zan bi maganar aunty,bazan Sanya damuwa a raina ba"Deeja ta faɗa tana mai son bawa kanta ƙwarin gwiwa

"Yawwa little sis, Allah ya Miki Albarka, kwanta maza ki huta"Deeja ta kwanta batare da ta sake magana ba

Wajen ƙarfe ɗaya na dare Deeja ta farka tayi ta sallolin nafila tana roƙon Allah ya kawo mata sassauci

Washe gari Aunty Bintu da kanta ta kai ta akayi mata gyaran jiki,sannan aka mata lalle ja da baƙi,ga gyaran gashi,ba don cikin da ke jikin ta ba babu mai cewa tana da aure,ai kuwa Aunty Bintu ta rinƙa koɗa ta har ta saki ranta

Kai tsaye daga nan gidan ta suka wuce,duk dakiyar Deeja sai da tsoro ya ɗarsu a ranta,amma dai haka ta cije ko don ganin idon aunty Bintu

A harabar gidan suka samu Khalees,yana ganin ta ya taho da sauri,suka gaisa da Aunty Bintu a Mutunce, fuskar ta babu yabo babu fallasa ta dube shi tace"ga auta nan na dawo maka daita,ni zan wuce, Allah ya sanya alkhairi"tana gama faɗar hakan ta faɗa mota

Khalees yazo daidai windon kusa da ita yana faɗin"Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi"ta kalle shi tace "a'a babu komai wallahi"

Kuɗi ya zaro masu ɗan yawa ya miƙo mata yana murmushi,amma tace bazata karɓa ba ta gode,ta ja motar ta bar shi nan tsaye

Ya mayar da

Please Login or Register in order to submit comment