Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƴan'uwan damar ganawa da junan su sosai

Intercom Amra ta matsa,within some seconds Aunty nusaiba ta bayyana

Fara ce tas kamar abban ta,babu in da tabar shi sai yanayin idanun ta irin na maman su(zainab)doguwa ce mai madaidaicin jiki,ta saki baƙin gashin ta irin na Deeja sak da suka gado daga zainab har gadon bayan ta,alamun hutu da gyara sun gama bayyana a tare da ita,wani idan ya ganta zai ɗauka bata wuce sa'ar Deeja ba

Ba sai ance wa Deeja ga yayar ta ba,babu ɓata lokaci ta faɗa jikin ta ta ƙanƙame ta ta fashe da kuka,ita dai nusaiba murmushi takeyi tana shafa bayan ta,wata nutsuwa ce ta shigi Deeja,don sai ta ji tamkar jikin mahaifiyar ta ne,lallai Bature yayi gaskiya da yace(blood is thicker than water

Sai da Aunty nusaiba ta ja ta zuwa parlourn sannan ta sake rungume ta tana goge mata hawayen tana faɗin"is okay! shikenan,ai kuma kuka ya ƙare,ko nima taɓarar zaki yi min?don ance min dama baba da Abba sun sakalta ki ko?"ta ƙarasa da sigar tsokana tana murmushi

Tura baki Deeja tayi tana faɗin"Ni Allah bani da taɓara"

"Naji,ina su yaya Ma'aruf?"da sauri ta kalle ta ta ɗaure fuska tace "bai san nazo ba,bana son ya sani for now please"

Nusaiba ta buɗe ido ta kalle ta tace"to ta yaya zai sani?"

Deeja ta juya hannu tana faɗin"na sani ko kuna communicating?"

Ƴar dariya nusaiba tayi tana dungure mata kai tana fadin"lallai dai naga autar mamma,babu inda kika bar halin ta Allah yaji ƙan ta,bari nayiwa su Amra magana su kawo babyn nan ku samu ku yi wanka ku ci abinci ku huta"daga nan ta wuce zuwa ɗakin su Amra

***** ***** *****

Cikin shagwaɓa ta kalle shi tana faɗin"haba honey!kana kallo na maƙaryaciya ne?ka duba da kan ka ma ka gani,wallahi abubuwa da yawa sun ƙare,idan baka siya ba wa zei siya min? Please mana my gentle"ta ƙarashe tana kwanciya kan kafaɗar shi

Ya kalle ta cikin ƙosawa da halayen ta yace"umaima!wallahi na gaji,daga Ni sai ke kawai a gida amma ko waɗanda suke rayuwa su goma basu kai mu cin kuɗi ba,yau kwana tara kawai da yin monthly shopping Amma har abubuwa sun ƙare,zubarwa kikeyi ne ko me?naga dai ba ƙananan kuɗi nake kashewa ba amma a banza,to wallahi nan da next one week Kar ki saka ran zan sake siyo ko tsinke"

"Haba my heart,ka daure mana,Ni a gani na duk abinda kayi min ai baka faɗi ba ko?"cikin shagwaɓa da kissa take maganar

Ko kallon ta bai sakeyi baya miƙe yana ƙarasa sanya rigar suit ɗin shi, yana gama shirya wa ya ɗauki briefcase ɗin shi bayan ya saka sau cikin shi ya fice daga ɗakin,ta biyo shi har harabar gidan kamar yadda suka saba

Yana ƙoƙarin buɗe motar shi yaga mai gadin yana ɗage gate ɗin gidan,daga shi har umaima suka bi motar da ta shigo da kallo,wata farar mota ƙirar GMC ce ta shigo cikin gidan,suka bi motar da kallo don ganin waye wannan ya kawo musu ziyara da wannan farar safiyar

Sai da hantar cikin su ta kaɗa ganin mamallakiyar motar, umaima har wani jiri ne ya fara ɗibar ta ta dafa motar Imran tana kallon ta tana nufo su, fuskar nan kamar koyaushe a ɗaure

Ba kowa bace baƙuwar ta su sai likitar zuciyar nan uwar khadija Mee'ad,wato Dr halima Kabir azare,wadda dai muka sani da MIMA

Sanye take da doguwar rigar abaya da mayafin ta,ta rufe idanun ta da baƙin spec,tana ƙarasowa gaban su ta sanya hannu ta cire glass ɗin tana watsa musu mugun kallo,kafin ta mayar da kallon ta ga Imran tana kallon shi a ƙasƙance tace

"Da kyau malam Imran!jarumin jarumai,mai iya sakayya,ka kyauta!!

Wato ka muzgunawa sister na,sannan kayi mata wulaƙanci,ka auro wannan ƙazamar kun haɗu kun ƙuntata mata,a sanadin ku ta kamu da ciwon zuciya,sannan kayi mata sakin wulaƙanci,duk wannan bai ishe ka ba sai da kukayi abinda kukayi kuka kashe mata auren ta da ya fara samar mata peace of mind,sannan ka ɓatar da ita, da kyau mr cinnaka,ko nace ɗan kunama!!"

"Ke Malama!dalla dakata!! ba'a haifi wadda ta isa tazo har gidan miji na taci masa........"bata ƙarasa ba taji saukar wasu mahaukatan maruka kamar ba hannun mace ba,aikin Mima ne,a fusace tace"kika sake interrupting ɗina idan ina magana sai kin raina kanki,ba da ke nake ba,da wannan sokon mijin naki nake,na sake jin kinyi tari anan!"

Tsit umaima tayi ganin cewa Imran ɗin da taso ya kare ta idan tayi kurin ko motsawa baiyi ba,ko niyyar tari ma bashi da ita,idan ba idanun ta ke mata gizo ba ma kamar shima jikin shi ɓari yakeyi

Mima ta sake kallon Imran da ya kiɗime,kafin tayi magana ya riga ta

"Deeja ya ɓata? yaushe?ina ta je?"

Wani watsatstsen kallo ta jefa masa tace "ban sani ba munafuki, na ba ka nan da 24 hours,ko dai sister na ta dawo ko na ɗaure ka"tana gama magana ta juya cikin kwanciyar hankali ta koma motar ta,ta fizge ta ta bar gidan

Sai da ta hau titi sannan ta kira Deeja tayi mata Barka da sauka, a lokacin Deeja tana ɗakin da aka kai ta tana hutawa,bayan sun gama gaisawa cikin kwanciyar hankali Mima ta kora mata bayanin abinda ta aikata,salati Deeja ta rafka tace" leemo kanki ɗaya, Allah ya shirye ki"

"Ameen!wallahi sai na hana su zaman lafiya baki ɗayan su musamman wannan tainannen Imran ɗin,i hate him wallahi"dariya Deeja tayi ta kashe wayar ta tana girgiza kai

Imran kam Mima tana fita shima ya fice daga gidan,kai tsaye ya nufi gidan Khalees da mugun speed,hankalin shi idan ya kai dubu ya tashi

Yana isowa ya danna wa Khalees kira,sai da yayi masa kira na huɗu a na biyar ya ɗaga

A lokacin Khalees yana dining yana juya abincin gaban shi, zuciyar shi cunkushe da damuwa amma ya rasa takamaimai abinda yake damun shi,can ƙasar zuciyar shi yana jin wani abu mai kama da gurbin da bai cika ba,yana jin wani abu mai kama da kewa amma ya kasa gane menene

Wayar shi ce ta ɗauki ringing, Nadiya da ke zaune tana chatting ta kalli wayar ta cigaba da chatting ɗin ta,shi kam yayi zurfi a tunani bai ma ji ba,sai da wayar ta damu Nadiya ta ɗauko,ganin Imran ta dungura masa tana faɗin"Dr ke kiran ka"

A kasalance ya ɗaga wayar,kafin yace komai yaji Imran yana cewa"Abdul ka fito ina ƙofar gida"ya kashe wayar

Miƙewa yayi batare da yace uffan ba ya nufi ƙofar fita,! Nadiya ta bishi da kallo kafin ta taɓe baki

A bakin gate yaga Imran sai safa da marwa yakeyi,Imran ya riga shi magana da tambayar

"Khalees ina Deeja?da gaske ne Deeja ta ɓata?wai me ya faru ne?me kayi mata ne? Please Khalees kar kayi mata abinda nayi mata har yanzu ina regretting nima"

Shiru Khalees yayi yana kallon Imran kamar wani sabuwar halitta,Imran ya kama kafaɗar shi yana jijjiga shi yana faɗin"Khalees Are You okay? are you with me?"

"Imran me yake faruwa dani ne me ya same ni?"a cewar Khalees cikin wani irin firgice

"I don't get you Khalees,what do you mean?"

"I'm serious Imran,I don't know what came over me,me nayi ne?ne na aikata?ina Deeja na?me nayi mata?why Imran why?"babu ɓata lokaci hawaye suka fara wanke masa fuska,ya dafe kai cikin karayar zuciya

Imran ya zuba masa idanu cikin mamaki ya kasa magana, Khalees ya kamo hannayen shi cikin karayar zuciya yana faɗin"Please Imran kaga kai aboki na ne,help me to find my life,idan na rasa Deeja ban san ya zanyi ba, Please friend,she is my everything,my happiness"

Cikin tausayi Imran ya dube shi yace cikin sanyin murya"in Sha Allah zamu nemo ta,zamu ganta,zata dawo gare ka da ikon Allah,mu bi komai a sannu Please friend,in Sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya"da haka ya samu ya kwantar masa da hankali har ya koma cikin gidan,shima Imran ya shiga motar shi ya tayar ya tafi cikin tsananin tashin hankali da ruɗani

Ɗakin umaima ya dosa,amma sai yaji tana waya,don haka ya tsaya yana kallon ta ganin bata ma kula da ya shigo ba

"Kayi haƙuri don Allah,wallahi Ni kai na ƙoƙarin da nakeyi kenan,a yanzu ya chanja min bana samun yadda nake so sosai"

"Don Allah kayi haƙuri,nayi maka alƙawarin nan da kwana uku zanyi maka ƙoƙari"

"To shikenan"

Tana ɗaga kai taga Imran,sai da gaban ta yayi mummunar faɗuwa,alamun rashin gaskiya suka bayyana a tare da ita

"Da wa kike waya?"

Kai!anya kuwa? Mima ina jin fa kamar baki kyauta ba,ki je gidan mutane ki tayar musu da hankali ki mari matar gida ki yiwa miji rashin kirki?? a'a ba dani ba!kai kam malam Audu ihu bayan hari kakeyi don dai Deeja ta haure boarder😅ke kam umaima anya kuwa? gaskiya ban gane ba🥺

Yau dai nayi zuciya na sakeyin post biyu a rana ɗaya,ba don kowa ba sai don ku likers da commentors, Allah ya sani ina matuƙar jin daɗin hakan, Allah ya bar mu tare🥰

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 30

Cikin in Ina tace"eh.....um....uh ......wawwallhi.....da...da... qawa ta nake waya"duk ta firgice

Kwata-kwata bai yarda ba,amma da yake ba ta wannan yake ba ya kalle ta fuskar shi babu rahama yace

"Ina kuka kai Deeja ke da ƙawar ki?

Me kukayi mata?

Me yasa kuka raba ta da mijin ta?"

Miƙewa tsaye tayi,tana so tayi tsiwa amma babu fuska ba,a tsorace tace"ni ban san inda take ba,ni ban ma san auren ta ya mutu ba"

Imran yayi ƴar dariyar takaici yace "Are You for real?

Baki San auren ta ya mutu ba,ashe ban san wacece ke ba!"

Kuka ta fara tace"Ni wallahi ban san me yake faruwa ba,kawai dai......."

"Hold it please!"ya daka mata tsawa"wallahi sai na wulaƙanta ki if I find out da sa hannun ki a ɓatan Deeja, wallahi sai kinyi nadamar sani na"

Ranta ya fara ɓaci,a zafafe ta fara magana tana kuka"shikenan babu dama tayi tafiyar ta wani wajen sai a zarge ni?ita ƙaramar yarinya ce da......."bata ƙarasa ba taji shuuuuu a kunnen ta,sai daga baya ta fahimci marin ta Imran yayi,irin marin da rabon da ayi mata irin shi ta manta lokacin,zuruu tayi tana kallon shi kukan ma ya ɗauke batare da ta sani ba

"Don't let me repeat my self,ki nemo Deeja,ko zama na dake ya ƙare"yana kai wa nan ya juya ya fice daga ɗakin

Zamewa Umaima tayi ta zauna akan tiles tana jan numfashi,tashin hankali ba'a saka maka rana!take kanta ya fara juyawa saboda shiga tashin hankali,a wannan yanayin ta ɗauki mayafi da key ɗin motar ta tayiwa gidan Nadiya tsinke

Nadiya tana zaune a parlour tana cin cup cake tana danna waya umaima ta faɗo kamar daga sama

A firgice Nadiya ta kalle ta tace "lafiyar ki kuwa?"

Umaima ta zama yaraf akan kujera tana faɗin"ba lafiya ba Umaima, Umaima ina cikin wani hali,a kowanne lokaci aure na zai iya mutuwa,kinga kunci na Nadiya"ta juya mata side ɗin da Imran ya mare ta tace"Dr ne ya mare ni kinga"

"To fa!me kika masa haka?"Nadiya ta faɗa tana gutsirar cake ɗin hannun ta

Umaima ta share hawayen ta tana faɗin"wai cewa yayi in nemo Deeja?yanzu ina zan fara neman Deeja fisabilillahi?"

"Deeja kuma?wacece haka?"a cewar Nadiya tana kwanciya a kan three sitter da take zaune

Umaima ta kalle ta da mamaki tace"Deejan ce baki sani ba?matar mijin ki fa da suka rabu"

Nadiya ta yamutse fuska tana taɓe baki tace"ɓata tayi ashe?shine ake tuhumar ki?lallai ma an gaishe su"

Umaima ta marairaice tace"don Allah ki taimaka min mu nemo ta kar aure na ya mutu Please"

"Toooo!Ni kuma da nemo Deeja?au Allah?gaskiya ya kamata a daƙile siyar da wiwi a ƙasar nan"duk wadannan maganganun da takeyi ko kallon banza umaiman bata ishe ta ba

Umaima da ta fuskanci raina mata hankali Nadiya takeyi sai ta fusata tace"Nadiya naga kamar maganar nan ma Baki ɗauke ta a matsala ba ko?"

"Matsala? Allah ya kaɗa ta can ya bar ku da kayar ku hajiya"

Hawaye ya zubowa Umaima tace "kenan baki ɗauki matsala ta a taki ba?"

"Me ya shafe Ni da matsalar ki har da zan cusa kaina a cikin ta?"

Umaima ta miƙe a fusace tace"eh zaki faɗa hakan bayan nayi miki komai,to wallahi ko ki fito da Deeja ko na tona miki asiri idan yaso aurenki ya mutu kafin nawa,don nasan halin ki nasan abinda zaki aikatawa"

Wata dariyar rainin hankali Nadiya tayi sannan ta gintse kamar ba ita ba tace"yaro yaro ne!kar nake kallon ki Umaima,wai ma kin manta ni malamar ki ce kuma uwar ki a makirci da tuggu?to kar ki fara abinda bazaki iya ba,kar ma ki jefa kanki a uku"

Zama dirshan Umaima tayi ta fashe da kuka cikin karayar zuciya tace"don Allah Nadiya Kar kiyi min haka,ya zanyi,kin juya min baya,yaya Najeeb ya juya min baya,ga Dr ma,ku kaɗai ne hope ɗina,ya kuke so nayi ne?"

"Kije ki tambayi ragowar biyun don wataƙila su suna da Lokacin ki,amma ni kam bani da lokacin sauraren haukan ki"tana kai aya ta nufi uwar ɗakin ta,har ta kai ƙofa ta juyo tana kallon umaima da har yanzu take kukan tashin hankali tace "idan kin fita ki ja ƙofar parlourn"ta sa kai ta shige ɗakin ta

Cikin tashin hankali Umaima ta miƙe ta fice daga gidan,kai tsaye gidan fauwaz ta nufa, Afra na zaune tana yanke wa haneef farce sai ganin Umaima tayi a kanta,a ɗan tsorace tace"Malama Lafiya?"daga yanayin fuskar ta za'a iya gane haushin da taji na abinda umaiman tayi mata

Amma da yake umaima tana cikin tashin hankali bata kula ba,ta zauna gefen Afra tana faɗin"ina fa lafiya Afra, Imran zei iya rabuwa dani,ina cikin tashin hankali"

Afra ta ɗan buɗa ido da mamaki tace"ikon Allah!to me kikayi masa?"

Umaima ta warware mata labarin kaf tun daga lokacin da nadiya taga Khalees har auren su da sakin Deeja da abinda ya faru yau bata ɓoye mata komai ba

Shiru Afra tayi cike da ɗimbin mamaki,zuwa can tace"ya kuke da wannan nadiyar ne?"

"Nima ban sani ba,amma yaya na Najeeb yace cousin ɗin mu ce"wani kallo Afra tayiwa Umaima tace"shine dalilin da yasa kikayi mata hanyar da ta auri engineer ko dai da wata a ƙasa?"Umaima ta sunkuyar da kai ta kasa bata amsa

Afra tayi murmushin takaici tace"uhm!umaima kenan!Ni kishin miji na nakeyi da Deeja, saboda ina da yaƙinin babu wani mai hankalin da zai samu Deeja a matsayin mata yayi wasa da damar shi,tunda na samu labarin auren ta da mijin da yafi nawa komai na zubar da makaman yaƙi na,lubaisa ma haka,amma ke saboda ƙiyayya da hassada ce a ranki sai da kika shigar da wata ƙawar ki kika tarwatsa mata farin ciki da ta ɗauki lokaci mai tsawo tana nema

Mu kanmu son zuciya ne ya rufe mana idanu saboda Imran ɗin nan a wulaƙance ta samo shi ta mayar dashi mutum,amma yau an wayi gari akan wata can da bai san asalin ta ba yayi mata cin mutunci,to Ni dai babu abinda zan iya,kuma wannan haliman da kike magana duk wani rashin mutunci da wata fitsara da kike taƙama da ita ta zarce ki,don haka Ni kar kija min magana,miji na yana nan,tun wuri ki koma gidan ki,nima kar kija yaji aure na ya fara rawa"

"Allah sarki Deeja baiwar Allah!"Muryar fauwaz sukaji,a firgice suka waiga suka kalle shi,yana sanye da jallabiya milk colour yana tsaye fuskar nan babu Rahama

Sai da hantar cikin su ta kaɗa,afra ta firgita don tasan itama nata auren zai iya fara rawa

A nutse ya ƙaraso ya samu waje ya zauna sannan ya dube su yace"kun bani mamaki,wannan abu yayi min ciwo sosai, Afra,wallahi ba don kinyi nadamar abinda kukayi ba da yau babu abinda zai hana Ni sakin ki

Ku in banda rashin iymani bakwa ganin cewa Deeja marainiya ce?kuma ita mutum ce da ko magana bata dame ta ba ballantana shiga shirgin wani?to don Allah meyasa zaku matsawa rayuwar ta?

Shi kanshi Dr auren ki da yayi shine sakayyar abinda yayi wa Deeja,don ke dai wallahi ba matar zama bace

Duk halin da kuke ciki da najeeb ina sane"

A tsananin kiɗime umaima ta ɗago ta kalle shi idanun ta a waje, fauwaz yayi murmushi yace"well!you think kuna yin dabara kuna ɓatar da hankalin mutane ke da Najeeb babu wanda ya sani ko?to tun barowar ki garin ku taura,da Abinda yayi silar zuwan ki garin nan na sani,kuma saura ƙiris mijin ki ya sani"

Faɗuwa tayi a gaban shi tana faɗin"don girman Allah ka taimake ni ka rufa min asiri,na roƙe ka"

"Zan rufa miki asiri but in one condition"gyaɗa Kai takeyi tun ma kafin taji sharaɗin,bai damu ba ya cigaba"sai kin datse kowacce alaƙa dashi wanda ya mayar da rayuwar ku kamar waina a tanda daga ke har Imran,idan nace alaƙa ina nufin kowace iriyar alaƙa"da sauri tana share hawayen ta tace"Ni dama don babu yadda zanyi ne,amma na kai watanni biyar ma yanzu ko haɗawa bamuyi ba,nima dama bana son alaƙar"

"Wannan ya rage naki kuma,na biyu kuma wanda shine ma yafi Zama wajibi,ki nemo min ƴar'uwa ta"

Umaima kukan ta ya ƙaru,tashin hankali ya mamaye ta,ita ina zata ga Deeja? meyasa ake ɗora mata alhakin ɓatan ta,ko kallon ta fauwaz bai sakeyi ba ya kalli Afra yace

"Ke kuma,duk abinda kikeyi kinayi ne don kinga alamun ina son Deeja ko?to Kar kiji da wai,ina son ta fiye da yadda kike tunani ina son ki,kuma duk ranar da na ganta ki shirya zama daita a matsayin kishiya ko ki bar mata gidan"

"Wallahi abban haneef na amince,na yarda zan zauna daita a matsayin kishiya nayi alƙawari"Afra ta amsa har yanzu zuciyar ta bata daina bugawa ba

Ɗaga kafaɗa yayi gami da taɓe baki alamar bai damu ba,ya fice daga parlourn

Umaima babu shiri ta koma gida,zama tayi tana tunanin mafita,zuwa yanzu kukan ma ya ɗauke mata,sai kanta da yake sarawa, abubuwa sun taru sun cunkushe mata

Wayar ta ce ta ɗauki ruri,a ɗan firgice ta kalli wayar,ta janyo tana duba mai kiran

Ganin Najeeb sai da gaban ta ya faɗi,ta daure ta ɗaga ta kai kunne,kafin tace komai taji yana faɗin

"Malama kina raina min hankali!na buƙaci kuɗi daga gare ki naji shiru,na buƙace ki kina ta min yawo da hankali,to na baki nan da awa uku,ina son ganin ki"

Cikin kuka tace"haba yaya Najeeb!wai me yake damun ka ne?na gaya maka ina cikin damuwa amma maimakon ka tausaya min sai ƙara min wata damuwar kakeyi,ya kake so nayi ne wai?"ta ƙarashe cikin ɗaga murya

"Ke ballagaza!kama kanki!!kar ki sake ɗaga min murya,or else na ɗauki mummunan mataki akanki,ina ruwa na da wata damuwar ki ta banza? Abinda nace idan bazakiyi ba ki gaya min!"

Cikin kuka tace "bazan yi ba wallahi,na gaji da halin ka,haba!"

Wata dariyar rainin hankali yayi yace"I see,to ko me kika gani kar ki zarge ni,ki zargi kanki"yana kai wa nan ya kashe wayar shi

Takurewa tayi tana zubar da hawaye, rayuwar ta ce ta baya take rotating akan ta,wani irin kuka mai ciwo ya ƙwace mata,amma duk da haka gwara waccan rayuwar akan ƙazamar rayuwar da Najeeb ya jefa ta, mahaifin ta ya faɗo mata a rai, ta sake fashewa da kuka mai ciwo,zuwa yanzu kaso saba'in da biyar cikin ɗari na hope da take dashi a komai ya tafi

To pa 🥺 umaima ya dai??
#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 31

Zama tayi dirshan a ƙasa tana tunanin mafita,ji takeyi dama tun farko mutuwa,amma tabbas tayi wauta,tayi tsalle ɗaya mai jefa mutum rijiya yayi dubu bai fito ba,duniya ta ruɗe ta da yawa,ta sake fashewa da kuka tana faɗin

"Ni umaima na cuci kaina,naga ta kaina,nasan abinda nayi ne yake bibiya ta,kaicon rayuwa ta!"

"Ai baki fara kaico ba umaima!munafuka,matsiyaciya, tsinanniya,amma dai bakin uwa ne a kanki ko?dama ke mutuniyar banza ce? dama ke ɗin karuwar Najeeb ce?na godewa Allah da bai bani haihuwa da ke ba annamimiya!"Imran ne mai faɗar wadannan maganganu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, fuskar shi a matuƙar ɗaure da ɓacin rai da tashin hankali

Wayar shi ya jefa mata a fusace yana faɗin"Umaima!a yau na fahimci kuskure na na auren ki,nayi nadama mara amfani ta auren ki,ashe ragowar wani ƙato ce ko ma nace ƙatti?kuma da auren ki kike fornication?the worst part ma da aboki na?wato da ke dashi dukkan ku mutanen banza ne,Ni zaku cuta Ku ci amana,shine kuka shiga tsakani na da khadija ya cuso ki don ku cuce ni"yayi murmushi mai ciwo yana kallon umaima da ke daskare tana kallon wayar shi da hotunan ta da najeeb suna sheƙe ayar su yake,ya cigaba da cewa

"Nayi miki alƙawarin sai na ganar da ke kuskuren ki daga ke har babban matsiyacin,sannan magana ta ƙarshe,ki nemo min ƴar uwa ta,idan ba haka nima na ɓatar dake"yana kaiwa nan ya ɗauki wayar shi ya take ta ya fice daga ɗakin

Sai a yanzu ta ji wani kukan ya kubce mata,nadama mara amfani ta cika zuciyar ta,a fili ta furta "ya Allah ka taimake ni,Deeja ina kika shiga ne? Allah ka bayyana ta"

*** *** ***

Ita kuwa Nadiya ta kunna ta ƙure volume tana bin waƙar tana rausaya, Khalees ne ya shigo ɗakin kamar an jefo shi,a raine ta kalle shi tace

"Tun ɗazu ka fice,ina kaje?"

Wani watsatstsen kallo ya bi ta dashi,sai da taji hantar cikin ta ya kaɗa,bai ce mata uffan ba ya wuce closet ɗin shi ya fara loda kaya a cikin trolley,yana gamawa ya janyo ya fito,da mamaki ta dube shi tace"ina zaka?"

"Kar ki kuskura ki biyo NI,zakiyi danasani"abinda yace mata kenan ya fice

Mamaki ne ya ƙamar daita,lallai ba shakka aikin ta yayi sanyi,don ita dai a iya sanin ta ko kara ta ajiye Khalees baya iya tsallakewa ballantana har ta kai su ga haka,da sauri ta ɗauki figigin mayafi ta ɗora akan English wears ɗin ta tayi waje,tun kafin ta baro parking lot take zuba mahaukacin horn,bawan Allah jiki na rawa ya buɗe,kafin ta fita sai da ta tsaya ta auna masa zagi da cin mutumci sannan ta fice,tana fita yace"da izinin Ubangijn ka'aba yadda asalin matar gidan nan mutuniyar kirki ta bar gidan nan kema sai kin barshi ita ta dawo,ai Allah nace"ya koma kan benchin shi yana tuna nagarta da halin ƙwarai irin na Deeja

Ita kuwa Nadiya Kai tsaye gidan bokan ta ta nufa,bayan ya gama ƴan dube-duben shi ya kalle ta rai a ɓace yace"kinyi sake mahaifiyar shi ta ɓata mana aiki,yanzu ko da wasa bata sakewa da addu'a,har ƙannen shi ta shi ya sanya sunayi,sannan bata tsaya anan ba,akwai wani abokin aikin shi mijin naki, mahaifiyar shi ta haɗa kai da wannan mutumi tana bashi ruwan addu'a yana bawa mijin ki,aikin mu ya lalace sosai"

"Na shiga uku!"ta faɗi cikin ƙaraji tana dafe kai,"yanzu ya zanyi?"

"Mafita ɗaya ce,ga wannan maganin"ya miƙa mata wani ƙulli yace"ki zuba masa a abinci,ki tabbatar yaci,yana ci shikenan zaki samu kanshi kamar baya ko ma fiye,amma idan bai ci ba za'a iya samun matsala"da rawar jiki ta amshi maganin tana faɗin"zai ci ma,zan tabbatar da yaci"ta ajiye masa kuɗin shi ta fice daga ɗakin nashi

Tana komawa gida babu ɓata lokaci ta ɗora girki,white rice ta dafa da miya taji kifi,ta san shine favourite ɗin Khalees,ta tsala wanka ta sanya sexy English wears ta zubo da kitson attachment da tayi bayan ta,tayi wa fuskar ta light make up ta zauna tana danna waya tana taunar chewing gum,a lokacin ana ta sallar Isha'i amma ba ta ita take ba

Tun lokacin take jiran dawowar shi shiru,har tara shiru,goma shiru,sai hankalin ta ya fara tashi,ta ɗauki waya ta fara kiran shi,amma switch off,hankalin ta ya fara tashi,don sai lokacin ta tuna cewa ya ɗauki jakar kaya,ai bata san lokacin da ta ɗora hannu aka ba ta kama gunjin kuka,faɗi take "na shiga uku na lalace,asiri na ya tonu"

Kafin washegari da safe wasu ƙuraje masu ruwa da mugun wari suka feso mata a dukkan ilahirin jikin ta,ga ƙaiƙayi da raɗaɗi da suke mata,da ta kalli kanta a madubi ita kanta sai da taji ƙyanƙyami, bata taɓa shiga matsanancin tashin hankali da masifa irin wannan ba,ta koma bata da aiki sai kuka da tunanin mafita

***** ***** *****

Ta nutsu sosai a gidan Auntyn ta Nusaiba tana jin daɗin rayuwar ta,yau kwanan ta shida kenan a US, Rayuwar su sukeyi ciki ita da Aunty nusaiba da yaran ta Amra da Ajmal,sai auta Adnan,gaba ɗaya ta manta da wani abu wai shi ɓacin rai ko damuwa

Affan kuwa koyaushe yana hannun ƙanin mijin ta Safwan da Allah ya ɗora masa ƙaunar yaron,shi kanshi Affan yanayin san Francisco ya karɓe shi yayi fresh abin shi

Suna zaune a parlour suna kallon wani American film,yaran duk basa nan sun tafi makaranta,hatta Safwan ya fita aiki, Deeja ta ɗago ga kalli auntyn tata tace cikin shagwaɓa"Aunty"

Cikin kulawa Aunty nusaiba tace"ya dai auta?"

Deeja ta zauna daga kishingiɗar da tayi tana kallon ta tace"Aunty na ganki Amma banga Yaya Yusuf ba"

Murmushi aunty Nusaiba tayi tace"inna bata gaya miki

Please Login or Register in order to submit comment