Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta,don haka suka fara ƙulle-ƙullen yadda Deeja zata bar gidan,tunda dai ba gidan ubanta bane (a cewar su umaima fa 😁)

Kwanan su biyu da dawowa Imran na zaune a lambun gidan inda ya saba zama yana duba wani littafin su na likitoci anatomy sai sallamar Deeja ya ji,yayi saurin ɗago kanshi yana amsawa,duk da cewar yayi mamakin zuwan nata amma ko a fuska bai nuna ba,don shi dai tun ranar da suka dawo sai dai ya gano ta daga nesa,don ko ya shiga parlourn mamie gaishe ta baya ganin Deejan

Sam bai ji daɗin yadda ya ga ta koma so lean ba alamun dai har yanzu ba wani daɗin jikin ta takeji ba,ko kuma tana cikin damuwa

"Sannu da hutawa!"ta furta fuskar ta babu yabo babu fallasa

"Sannu Khadijah,mun same ku lafiya?"ya furta da ƴar fara'a a fuskar shi

Maimakon ta amsa sai gani yayi ta dire masa kuɗi a kan ɗan table ɗin da ke gaban shi,har yanzu fuskar ta babu yabo babu fallasa ta kalle shi cikin idanu tace

"Wannan kuɗin ka ne,kasan a musulunce idan aure ya rabu batare da ma'auratan sunyi wata mu'amalar aure ba namijin yana da rabin sadaki,dama 300k ka bayar ko?to ga 150k ɗin ka

Sannan wannan kuma"ta faɗa tana nuna wanda yafi yawa ta cigaba"kuɗin da ka kai asibiti ne,tunda a lokacin da ka bayar auren ya ƙare responsibility na zuwa lafiya ta ya koma kan iyaye na,so shine na dawo maka da kuɗin da ka bayar na asibiti,na gode"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana yunƙurin ɗaga kiran da akayi mata a waya

Imran da mamaki ya ƙamar dashi ya taso da sauri ya biyo ta da kuɗin duka yana faɗin"haba Deeja!yanzu waɗannan kuɗin zaki dawo min dasu bayan kema kin san ninkin su ma kin fi ƙarfin su a waje na? Please Deeja menene na dawo dashi kuma?"

Fasa ɗagawa wayar tayi ta kalle shi cikin idanu tace"bana buƙata ne,zai fi ka samu waɗanda suke buƙata ka basu zaka fi samun lada,ko ka ganni a buƙace ne?"

"Kin raina kyautar da na miki ko me?"ya faɗa zuciyar shi na sake karyewa

Yatsina fuska Deeja tayi tace"bakaji abinda nace bane?bana buƙata,idan ma kace na fi ƙarfin su ne to babu laifi,kyauta kuma bana so,na gode, Allah ya sa ka gane"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana ɗaga sabon kiran Mima da tayi mata a lokacin

Tabbas idan yace baiyi nadamar sakin Deeja ba yayi ƙarya,bai yarda shi wawa ba ne sai yanzu da har aboki zai shiga rayuwar shi ya tarwatsa masa farin ciki,ya tabbatar yana son umaima Amma Sam baya mata kallon mutum mai ƙima,yasan bayan momyn shi babu wata mace da ta bawa rayuwar shi gudunmawa,ta magance masa damuwa kamar Deeja,amma shi kanshi baya son ma tuna irin abubuwan da yayi mata waɗanda ya san har abada bazata taɓa mantawa ba

Jiki a saɓule ya koma ya zauna yana kallon kuɗin da kawo masa,ba sai an gaya masa ba ya san definitely Deeja ta fi shi kusan komai na rayuwa, musamman gata,duk da cewa a yaran professor ta girmi Yasmin Amma ita yake kira autar shi, ballantana sauran mutane,tana samun gata da kulawa fiye da tunani,kowa son ta yake, saboda tsabar gata da soyayyar da ake mata ma lokacin da ta kammala karatun ta ta dawo Nigeria abba ya hana ta aiki,baba Prof ma ya goyi bayan shi,su a ganin su zata je ta sha wahala,don haka suka yanka mata kuɗi mai kauri a matsayin albashi,kuma ko da ta samu suka bar ta ta fara aikin ma basu daina bata albashin ba,amma duk da haka ya kan tuna duk ƙanƙantar abinda ya bata a lokacin ko ya siyo mata tana karɓa da farin ciki tayi masa godiya,karo na farko da Deeja ta dawo masa da wani abu da ya bata,wanda ba sai an gaya masa dalilin ba

Duk wannan tattaunawa da Deeja da Imran sukayi akan idanun umaima,amma bata jin mei suka ce,ai kuwa ta cika tayi fam tana ta huci,a ranta ayyanawa takeyi dole ma ta ci uban Deeja don ta fara kai ta bango,ta kama ƙugu ta tsaya tana huci,ita kuwa Deeja ko lura ma da ita batayi bata tana magana da miman ta a waya suna dariya,sai kawai ji tayi an damƙar mata wuya

Da sauri ta juya tana kallon umaima,tare da faɗin "zan kira ki leemo"ta kashe wayar

Cikin mamaki tace"baiwar Allah lafiya?"

"Oho ban sani ba,meye alaƙar da ta haɗa ki da miji na?wai ma ba an rabu ba?"

Abin ya bawa Deeja haushi,ta kalli umaima da ke girgiza jiki tana ɗaure fuska,tana kuma sake riƙe mata wuyan hijabi

Ta san dai ko dambe zatayi da umaima sai ta karya ta ma umaiman bata mata ko mintsini ɗaya ba,ture ta tayi tana faɗin"dalla sake ni,har wani miji ke gare ki?me ya shafe Ni dashi?"

"Oho naji,to me ya kai ki wajen shi?"

Deeja ta ja tsaki ta kalle ta cikin idanu tace"shi da kika isa dashi kije ki tambaye shi"daidai nan afra da zakiyya suka iso wajen,zakiyya itace matar Nasir Wanda yake bin salma

Kwata-kwata ba ta shiga shirgin su Afra sai ta kama, saboda ta fuskanci basu da tarbiyya kwata-kwata, musamman afra da umaima,har gwara gwara lubaisa ma,don haka Deeja itace mutuniyar ta

Fuska ɗaure ta kalli su Deeja tace"lafiya kuwa?"

Umaima ta kalle ta a yatsine tace"wannan ƙaruwar gidan ta daina bibiyar min miji"

Zakiyya ta kalle ta cikin ɓacin rai tace"karuwa?"

"Eh karuwa!"a cewar afra cikin tsiwa, zakiyya zata sake magana afra tayi mata nuni da tayi shiru,sannan ta ja hannun ta suka bar wajen,tana jin umaima na jan dogon tsaki

Ɗaki suka shiga, zakiyya ta rinƙa tausar ta amma sai Deeja ta nuna mata abin bai dame ta ba, dama kuma bata saka su umaima a layin masu hankali ballantana suyi abu ya dame ta

Umaima da Afra kuwa sashen afra suka wuce suna shawarar yadda zasu ɓullowa Deeja,a ƙarshe dai suka samo hanyar da zasu fara musguna mata,sukayi shewa suka tafa

Kwana biyu tsakani Mamie ta wuce Abuja,wanda daga nan zasu Yemen ita da momy Aysha

Deeja ta shigo main parlour tana tafiya tana chatting da Aunty Bintu,labari take bata cewa yaya Ma'aruf da Aunty Farida zasu dawo next week,dama tafiyar ta yaron su ce Ayman da yake fama da matsalar ciwon ƙoda,amma yanzu da sauƙi sosai,tana cikin karanta amsar Aunty Bintu da take sanar da ita sun yi waya da Aunty Farida ɗin sai kayi taji santsi ya kwashe ta ta tafi luuu ta bugu da ƙasa,sai ji tayi an kwashe da dariya ta rainin hankali,ta kalli ƙasa don ganin abinda ta taka,ɗanyar kuɓewa ce kuma ga dukkan alamu zuba ta akayi,ta kalli masu dariyar, umaima,afra ce da lubaisa

Afra ce ta ƙaraso wajen tana kallon ta a wulaƙance tace"kaɗan kika gani, indai kin nacewa zaman gidan nan,tunda baki da zuciyar da zaki zauna a gidan naki uban

Deeja batayi jinkirin mayar da amsa ba"gaskiyar ki,tunda ko babu komai a gidan naki uban nake da zama"tayi ƴar dariya tace"shashashu"ta miƙe a zafafe ta tsallake kubewar ta bar wajen

Umaima ta ɗura wani ashar ta nufe ta tana huci, lubaisa ta riƙe ta, umaima tana huci tace"sake ni,wannan karyar har ta isa ta zage ni?"

Afra tace"easy sister,rabu daita,kema kin san bazamu ƙyale ta ba"

Kai amma umaima kina da ƙarfin hali😥ko da yake banga laifin ki ba, saboda kinga Imran a mutum,baki ganshi lokacin da yake wulaƙantaccen shi ba

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 27

Tun daga ranar su umaima suka matsa wa Deeja lamba,duk abinda zasuyi don su ɓata mata rai yi sukeyi,kuma ta hanyar da ba kowa ne zai gane ba ballantana a tsawatar musu,bugu da ƙari ma Mamie bata nan, ballantana ta saka idanu

Sai dai Deeja bata taɓa ɗaga kai ta kalle su duk da cewa suna ɓata mata rai,ta cigaba da harkar gaban ta kamar bata san sunayi ba

A lokacin ba ƙaramin kewar aikin ta takeyi ba,da akwai shi yanzu ta san ganin ta ma sai yayi musu wahala ballantana su sanyo ta a gaba,amma yanzu babu aikin,sai dai ranar da ta gaji da zaman gidan ta tafi gidan Aunty Bintu ko gidan zee ƙawar ta,ko safeena,itama ƙawar ta ce tun ta secondary School,dama ita bata tarin ƙawaye

Ganin irin takurawar da sukayi mata ya fara yunƙurin tayar mata da ciwo ya sanya ta ƙuduri aniyar ɗaukar mataki akan su

Tana tsaye daga gefen ƙofar main parlour tana danna waya sai ji tayi an bangaje ta har wayar hannun ta ta faɗi,sai da ta firgita,ta ɗago da sauri tana kallon mai wannan aikin,sai taga Afra

Tsaki ta ja ta sunkuya ta ɗauki wayar ta da har ta ɗan tsage,a zafafe ta furta"ki rinƙa kallon gaban ki idan kina tafiya,idan kuma makancewa kikayi sai kiyi magana a samo miki ɗan jagora"

Kamar jira Afra take tayo baya da sauri tana nuna Deeja da yatsa tana faɗin"ke kama kanki,don dai kin san nafi ƙarfin wata trash ke,kar kiyi min abinda zai ɓata min rai na wulaƙanta ki a gidan nan wallahi"

Deeja na kallon cikin idanun ta har ta kai aya sannan ta amsa mata"mijin naki bai karanta miki cewa ba'a nuna ni da yatsa bane?fara sauke yatsan idan yaso sai nafi fahimtar magana kikeyi"

"An nuna ki da yatsan,kiyi abinda zakiyi,mijina kuma yafi ƙarfin yin magana akan wata kucaka ke"

Deeja tayi wata dariyar rainin wayo sannan ta kewaye afra zata wuce, Afra ta finciko ta baya tana huci,Deeja ta kalle ta a nutse tana ƙoƙarin danne ɓacin ran da ke yunƙuro mata,kamar zatayi magana sai ta fasa tayi gaba

Batayi aune ba sai ji tayi Afra ta ɗauke ta da mari, Deeja tayi stiff a wajen cikin tsananin mamaki da ɓacin rai,don samun waje Afra ta fara zazzaga mata masifa tana nuna ta da yatsa da tayi mata magana

Batayi aune ba sai ji tayi anyi sama da ita an buga da ƙasa,aikin Deeja ne,a cikin tsananin fushi ta rinƙa wanke fuskar ta da maruka hagu da dama,tsabar gigita ma ko kukan afra ta gaza yi,umaima ce ta shigo parlourn ganin halin da Afra take ciki ya sa ta taho da gudu don ƙwatar ta,amma cilli ɗaya tayi daita umaima ta gane wannan ba kalar su bace,wato cika baki ba ƙarfi,da gudu ta kwasa zuwa part din afran,nan ta samu fauwaz ta shaida musu yayi hanzari yazo kar Deeja ta kashe Afra,a bala'in sauri ya ƙaraso wajen,kafin ya ƙaraso ma Deeja ta gama abinda zatayi ta watsar da umaiman can gefe ta ɗauke wayar ta da ta faɗi tana ƙoƙarin barin wajen

Fauwaz ya kalli afra da umaima take taimaka mata ta tashi,ya kalli Deeja da ta sha mur tana ƙoƙarin shigewa ɗakin ta,a fusace yace"Deeja mahaukaciyar ina ce ke da zaki kama mata ta kiyi mata irin wannan dukan sai kace kin samu banza?"

Wani kallon rainin wayo ta watsa masa fuska a ɗaure tace"shafa kaji!

Ba fauwaz ba,hatta umaima da afran da ke fama da kanta sai da suka kalli Deeja da sauri saboda tsananin mamakin amsar da ta bawa fauwaz, fauwaz Sarkin zuciya ya kai mata mari,tayi saurin gocewa sannan ta kalle shi cikin idanu tana kaɗa babban yatsan ta da dan tsakiya a fuskar shi tana faɗin"mafi girman kuskuren da zakayi a rayuwar ka shine marin DEEJA! don't attempt it again!"tana kaiwa nan ta samu waje akan two sitter ta zauna don zuwa yanzu ita kaɗai ta san me takeji a ƙirjin ta

"Okay! that's right!tattaro kayan ki ki koma gidan ubanki,wato mugun halin da kikayiwa Imran shi zakiyi mana ko?"

"Imran!"ta maimaita da wani yanayi a fuskar ta,sam korar da fauwaz yayi mata ma bata gaban ta,amma ambatar Imran da fauwaz yayi ya daki ranta,wato sharri ma Imran yayi mata,hawaye Masu zafi suka silalo a fuskar ta, bata sake magana ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta ta ɗauko ɗan ƙaramin trolley ɗin ta ta zo ta wuce ta gaban shi,don lokacin afra da umaima basa parlourn,ko kallon tsiya batayi masa ba ta fice daga parlourn

Sai fauwaz yaji babu daɗi abinda yayi mata,cikin sanyi jiki ya biyo ta,har ta kai main entrance na gidan yace "Deeja dawo,kar ki fita"

Banza tayi masa ta cigaba da tafiya,ya sake cewa"Deeja bakya jin ina miki magana,i said don't move an inch daga in da kike"

Juyowa tayi ta kalle shi sama da ƙasa tace"kwantar da hankalin ka yaya fauwaz,bari kawai na bar muku gida kuyi sakewar ku yadda kuke so da matan ku,dama Ni na matsa muku"tana kaiwa nan ta sa kai ta cigaba da tafiya

"Deeja nace......"

"Hold it Yaya fauwaz!"ta faɗa a ɗan tsawace sannan ta juya ta cigaba da tafiya

Kai tsaye gate ta nufa, fauwaz ya ƙwalawa driver din su kira yana bashi umarnin ya ajiye ta a duk inda zataje,ko kallon fauwaz batayi ba cikin ɗan sakin fuska ta kalli driver din tana faɗin"yi zaman ka kawai baba,na gode"ta fice daga gidan

Fauwaz yayi mamaki,ya tsorata sosai da zuciyar Deeja,ko da yake yasan Deeja tana da ɗauke kai akan abubuwa da yawa, kuma sau tari ko da anyi mata abu bata rama ba lokaci take jira,amma tana da uzuri,kuma tana da haƙuri,sai dai yau ga dukkan alamu an ƙure haƙurin ta

A sanyaye ya juyo yana nadamar abinda yayi mata,ya san shi da ya sake samun fuska a wajen ta kamar da sai wani ikon Allah

Ita kuwa Deeja gidan Aunty Bintu ta wuce,ta so tafiya gidan yaya Ma'aruf amma har yanzu basu dawo ƙasar ba,don haka ta wuce gidan Aunty Bintu

Wujiga-wujiga ta shiga parlourn Aunty Bintu,sallama kawai tayi ta shiga, Aunty Bintu ta ɗago da sauri tana kallon ta,bata sake kallon ta ba ta nemi waje ta zauna,Aunty Bintu tayi mata kallon tsaf sannan tace

"Auta lafiya dai?"

Bata tanka ba kuma babu alamun zata tanka ɗin,ganin hakan sai ta ƙyale ta,don kowa ya ga Deeja kallo ɗaya zaiyi mata ya gane da matsala

Ta kai mintuna biyar kafin ta miƙe don yin alwalar sallar la'asar da taji ana kira,sai kawai ta yanke jiki ta faɗi, Aunty Bintu ta rafka salati da ihu, intisar da ke ɗakin ta bata ma san da zuwan da Deeja ba ta rugo a guje, ganin Deeja a kwance a ƙasa ta tafi tana girgiza ta tana kiran sunan ta,ganin ba tashi zatayi ba ta fita compound ɗin gidan tana ihun neman taimako, within few minutes ma'aikatan suka hallara a parlourn

Kai tsaye asibitin Dr su'ad aka wuce da Deeja,sai dai wannan karon abin yafi ƙarfin asibitin,dole Aunty Bintu ta sanar da Ma'aruf da ko cikakken awa uku da sauka a ƙasar basuyi ba,haka ya sake shirya tashin su zuwa ƙasar Spain,don dama ya daɗe yana nema mata damar ganin wani babban likitan zuciya Dr Nicolas Alfred,babu ɓata lokaci kuwa suka wuce zuwa can ƙasar Spain

A ranar ya gayawa Mima,ai kuwa nan da nan ta shirya ta wuce garin Barcelona da ke can ƙasar in da a can Dr Nicolas yake

Awanni biyu da saukar jirgin su Ma'aruf da Farida sai intisar a Barcelona Mima ta sauka a ƙasar,dukan su babu walwala a fuskokin su,a lokacin da Mima taje har an shiga da Deeja observation room

Dama kafin su tafi Ma'aruf ya shaidawa Alhaji Abubakar mahaifin Khalees da baba Prof,dukan su sunyi mata fatan samun lafiya tare da bada kuɗi mai yawa na gudunmawa

Binciken Farko likitocin suka gano zuciyar Deeja ta kumbura,tana buƙatar aiki,wanda babu ɓata lokaci Ma'aruf ya saka hannu aka shiga daita theater room

Aikin ya ɗauki tsawon awanni shida,su Ma'aruf suna ta addu'ar Allah yasa ayi aikin a Sa'a

Bayan sun fito an tura ta ɗakin hutu ba tsawon awanni ashirin da huɗu,su ma su Ma'aruf suka koma masaukin su suna jimami

Anan Farida take bawa Mima labarin mutuwar auren Deeja,Deeja ta sha mamaki matuƙa,take tsanar Imran ta sake ninkuwa a ranta, ranar dai Imran ya sha tsinuwa da la'anta da alkaba'i daga wajen Farida da Mima har ma da intisar da bata saka musu baki ba,amma tana aika Tata tsinuwar a ranta

Sai da Deeja ta kwashe watanni biyu aka sallame ta,ta samu kulawa sosai,sau wajen biyar baba Prof yana zuwa duba ta,haka masu mamie da su yaran ta su fauwaz,duk da cewa ko sau ɗaya fauwaz ɗin bai ga haƙorin ta a waje ba kuma ya san dalili

Sosai Deeja ta mayar da jikin ta ta koma walwalar ta,daga Spain Kai tsaye Umrah suka wuce Saudiyya,daga nan suka wuce Malaysia,kwanan su goma suka dawo Nigeria,amma a can suka bar Mima

Kwanan su uku da dawowa Alhaji Abubakar yazo har gidan marigayi Dr Mahmud, kasancewar yanzu Deeja ta koma gidan su da zama,a babban parlourn Dr Mahmud ɗin Ma'aruf ɗin ya sauke shi da girmamawa,bayan ya gaishe shi ya umarce shi ya kira masa Deeja

Jidda Ahmed,Deeja tace a gaishe ki yadda kike supporting ɗin ta da taya ta yaƙar Imran 😁

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 28

Da sallama ta shigo parlourn,ta durƙusa cikin girmamawa ta gaida shi,ya amsa cikin kulawa yana tambayar ta jiki,ta amsa da alhamdulillah, fuskantar ta yayi sosai sannan yace

"Khadija naji duk abinda ya faru,kar ki sanya hakan a ranki ya dame ki,ki ƙaddara cewa jarrabawar ki kenan,amma in Sha Allah komai yazo ƙarshe yanzu,yau juma'a ko?to in Sha Allah zuwa juma'a mai zuwa da kaina zan aura miki mutumin da ya dace,in Sha Allah hakan zai kawo ƙarshen dukkan matsala"

Kan Deeja a ƙasa tana sauraron aminin mahaifin nata da maganar shi tayi mata gingirin aka,shi kanshi Ma'aruf maganar ta zo masa a bazata,amma duk a cikin su babu mai iya cewa komai,sun daɗe da sanin aminin abban nasu baya magana biyu,kuma ba'a chanja masa magana, Ma'aruf ne yayi ƙarfin halin yin fatan alkhairi,ya miƙe yayi musu sallama, suma sallama sukayi masa suka biyo bayan shi suka nufi cikin gidan suna tunanin wanda za'a bawa Deeja

Babu wanda Deeja ta sanar wa sai Mamie da Aunty kiyya,don ko Aunty Bintu bata sani ba ballantana kuma Mima,a lokacin ma mamien bata nan tana Abuja,momy Aysha bata da lafiya taje dubiyar ta

Ɗaurin aure kawai akayi,don ko walima ba'a yi ba,Deeja sai tarar rabin wanda ta aura takeyi,Aunty kiyya da Aunty Farida ne suke kula da ita,sai zainab ƙawar ta wadda zuwa yanzu ta gama yi mata komai don komawa bakin aiki

Da daddare bayan Isha'i aka kai Deeja gidan ta,sai rarraba idanu take na fargaba,don bata san me zata tarar a wannan auren ba,to Imran ma da ta san shi ta saba dashi ya aka ƙare ballantana wanda ko ganin shi bata taɓa yi ba?

Da wuri suka tafi ya rage saura ita kaɗai, ban da sunan Allah babu abinda bakin ta yake ambato

Sai wajen sha ɗaya taji shigowar motar shi,takure kanta tayi a cikin kujerar da take zaune,gaban ta sai dukan uku-uku yakeyi

Da sallama ya shigo,ji tayi kamar ta san muryar,har bata san sanda ta ɗaga kanta da sauri don tabbatar da zargin ta ba

Ai kuwa mamaki mai tsanani ya mamaye fuskar ta ta kasa amsa masa sallamar,ba kowa bane face engineer abdurrashid Abubakar Yusuf wanda muka fi sani da KHALEES.

Shima wani kallo ya bi ta dashi alamar mamaki,kafin ya wuce zuwa ɗakin shi

Itama a saɓule ta tashi ta wuce ɗakin ta,a ranar dai bata runtsa ba saboda tsananin mamaki da takaicin wannan haɗin,to ya ta ƙare da Imran ma da suke shiri ballantana wannan dimkin ɗin da ta daɗe da daina gaishe shi saboda tsabar rashin amsawa?

"Oh Ni Khadija!"ta faɗa a fili"nan kuma rayuwa ta jefo ni?wancan dai ga irin rayuwar da nayi a gidan shi,saura wannan mai fuskar mala'ikan tsaron wutar, kullum fuska a ɗaure yana cin magani, ko Ni da na rasa iyaye na duka biyun ai bana daure fuska sai wannan da duka iyayen shi suke raye, Allah ya sani na tsani a ɗaure min fuska wallahi idan naga ya cigaba da wannan mugun halin wallahi sai in........."

Maganar ta maƙale tare da hannun ta da take ƙoƙarin cire rantsatstsiyar rigar lace da ke jikin ta,jikin ta ya kama rawa sosai,ta sake murza idanu tana kallon Khalees da ya biyo ta zuwa ɗakin nata,shima dai kallon nata yake cikin idanu, fuskar tashi a ɗaure amma bazata iya cewa ga expression ɗin da yake kai ba

Dama biyo ta yayi ya kawo mata kazar da ya kawo ta al'ada daga nan ya gani ko bata lacking komai,sai yazo ya samu tana kwashe masa albarka

Sunkuyar da kanta tayi ƙirjin ta na dukan uku uku,shi kam ya taɓe baki ya ɗauke kai ya ajiye mata kazar ya fice daga ɗakin

Deeja bata sake tabbatar da baƙin miskilancin Khalees ba sai da zaman su ya miƙa,yayi mamakin samun ta a matsayin cikakkiyar budurwa duk da cewa ta taɓa aure,amma bai nuna ko a fuska ba ballantana har ya tambaye ta

Zaman nasu dai babu yabo babu fallasa,baya zama daita suyi hira,idan tayi kuskure yayi ta faɗa da tsawa,baya yaba mata,tun tana tsoron shi har ya zama jiki ta daina

Sai dai yana sauke haƙƙin auratayya da ya rataya akan shi,sannan bata rasa ci ko sha, kazalika yana matuƙar kulawa da ita idan ciwon ta ya so tashi ko wata rashin lafiyar,sannan kuma ya bata dama ta koma aikin ta,don ana i gobe zata koma yayi mata kyautar sabuwar mota

Ƴan uwan shi ma ba wani zuwa sukeyi ba,idan taje kuma bata samun fuska shiyasa take janye jikin ta,kuma tana shakkar shiga cikin su

Wannan shine tarihin Deeja da gwarazan ta Imran da Khalees 🥰

CIGABAN LABARIN.......

Ƙarfe biyar da mintuna biyar haka agogon ƙasar US ya nuna,a hankali take saukowa daga matattakalar jirgin janye da trolley ɗinta,tana rungume da yaron ta Affan, zuciyar ta cike da tunane-tunane,a wani ɓangaren kuma cike da farin cikin haɗuwa da ƴar uwar ta

Sai da ta samu waje ta zauna sannan ta ciro wayar ta tayi activating international mode ta fara kiran number din da Inna Mariya ta bata,bugu biyu aka ɗaga

Sai a sannan fargaba ta shige ta,cikin rawar murya tayi sallama,wata murya mai cike da nutsuwa ta amsa,cikin rawar murya take faɗin

"Good evening ma!I am Khadija Mahmud,am talking to Dr nusaiba mahmud please?"

Matar tayi dan murmushi tace cikin harshen Hausa"eh nice auta,Inna Mariya ta sanar dani zuwan ki,kin sauka ko?"

Haba!ai Deeja ji tayi kamar an tsunduma ta a aljanna,ta washe baki tana faɗin"yeah na sauka few minutes ago"

"Okay!just wait for few minutes, you will be home very soon in Sha Allah"daga nan aka kashe wayar

Cikin farin ciki ta cigaba da kallon masu kaiwa da kawowa a reception na airport ɗin, lokaci ɗaya kuma zumuɗin ta ya ɗan ragu tuno Khalees da tayi,ta san duk lokacin da ya dawo hayyacin shi akwai daru,to mutumin da in dai tafiyar kwana ta kama ta ko kwana ɗaya ne sai tayi da gaske ballantana wadda ita kanta bata san ranar komawa ba?

Ta sauya layi, kuma babu wanda ta sanarwa tahowar ta sai Mima,wadda ta korawa warning ko da wasa kar ta sanarwa ko Aunty Bintu, ballantana yaya Ma'aruf

Ta kalli ɗan ta wanda babu inda ya baro Mahaifin shi, Allah sarki!a yadda ta san soyayyar yara irin ta Khalees da yanzu tare suke rainon abin su,amma shigowar Nadiya cikin rayuwar su ya tarwatsa musu farin ciki,ta goge ƙwallar idanun ta da sauri tana bin danƙareriyar G-wagon ɗin da ta gani tayi parking ɗan nesa da ita

Wani kyakkyawan matashi da zai iya yin Sa'an ta ne ya fito daga motar,sai sai wasu yara mace da namiji da suka biyo bayan shi

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 29

Macen zata Kai shekaru goma,namijin bai wuce shida ba,kallo ɗaya tayiwa macen gaban ta ya faɗi,don ko ina yarinyar nan ta fito bata da maraba da abban ta,tayi musu kuri har suka ƙaraso in da take zaune da murmushi a fuskar su

Sallama sukayi mata,ta amsa itama fuskar ta a sake,cikin murmushi matashin yace"Deeja, right?"

Gyaɗa Masa kai tayi tana murmushi tace"yeah"yace"wow!very nice!!you are highly welcome, let's go, Aunty nusaiba is waiting for you"ta miƙe tsaye,yarinyar tayi saurin amsar Affan suka wuce suka nufi motar

A motar ƴar ta macen ta kalli Deeja tana murmushi tace"Aunty Deeja what's his name?"tana nuno mata Affan

"Mahmud,known as Affan,what about You and your brother?"

"I am ZAINAB known as amra,my brother is Ismail known as ajmal,and this is Uncle safwan"ta ƙarashe tana pointing matashin, murmushin fuskar ta yana nan

Wata ajiyar zuciyar farin ciki tayi tana sake rungume yaran tana jin ƙaunar su a ranta, Safwan da ke gaba yana driving yana kallon su ta madubi yana murmushi

Suna isa bakin tangamemen gate ɗin gidan Dr nusaiba Safwan yayi horn, guard ɗin ƙofar ya ɗage, zumuɗin Deeja ya ƙaru, Allah Allah kawai take ta ganta a gaban sister ɗin ta

A balcony ɗin suka tsaya,shi dai Safwan bai ma shigo ba,daga nan fita yayi uzurin gaban shi don ya bawa

Please Login or Register in order to submit comment