Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Deeja ta samu nutsuwa,tayi musu cikakken bayanin abinda ya faru

Salati suka sanya suna tafa hannaye, doctor su'ad tace"lallai matar nan bata da ko ɗigon iymani, jariri yaron da bazai iya aikatawa kanshi komai ba ballantana ya aikatawa wani me yayi zafi haka za'a yanke masa ɗanyen hukuncin da ko babba bazai jura ba?"

"Wanne laifi kuwa?bakin hali ne fa kawai,ke dai Deeja ki ƙara kula da yaron ki kawai"a cewar safeena cikin ɓacin rai

"Ina kula dashi sosai, duk da cewa Allah ne mai tsarewa,yanzun ma Allah ne kaɗai yasan abinda zai faru ya taƙaita mana wahala"a cewar Deeja

Doctor su'ad tace"hakane kam,yanzu dai gashi nan an magance matsalar,a shawarce Kar ki nuna mata damuwa,ki rabu da ita,ki bar ta da halin ta kawai"

Deeja ta girgiza kai tace"Ni dama ko kallo bata ishe ni ba,ko me zatayi bata gaba na,idan tayi min na rabu daita ai idan tayiwa wani bazai ƙyale ta ba ko?"

"Hakane kam, to Allah yasa mu dace"a cewar safeena

Doctor su'ad ta amsa da"ameen

Sun daɗe suna hira har maghriba,sukayi sallah sannan safeena ta mayar da Deeja gida

Har parlour suka shigo suna hira da dariya, Nadiya ta fito da sauri,ganin su Deeja a haka ya tabbatar mata da babu matsala,nan da nan ranta ya ƙara ɓaci,Deeja na kula da ita,amma sai ta nuna tamkar bata ganta ba

Deeja ta cigaba da gudanar da rayuwar ta yanda ya kamata,har zuwa sanda su Aunty Bintu zasu tafi ƙasar Syria,tafiyar ta kama ranar Lahadi,don haka ranar ta kama babu aiki,don haka Deeja taje yi musu sallama

A can ta yini,itace ta kai su airport,a gaban ta akayi komai ƙarfe biyar na yamma jirgin su ya tashi,itama ta juya zuwa gida

A falo ta samu Nadiya da umaima da ƙawar su siyama zaune suna hira,da farko ƙin shiga tayi ta tsaya daga bakin ƙofa don jin mei zasu ce

Umaima taji tana faɗin"ai tunda kin ce aikin baya cin ta na samu wani boka ya bani wani magani tace ayi haƙa a ƙofar ɗakin ta a binne,to tabbas zata gamu da hauka idan ta tsallaka,kinga tana can tana hauka,ga miji ya dawo naki ke kaɗai,yaron kuma zai dawo ƙarƙashin ki,kin ga sai kiyi abin da kika ga dama ko?"

"Kuma nima akwai wani hatsabibin boka da na samo,ya bani siddabaru yace na binne a maƙabarta,hakan zai sanya ya tsane ta har yaji baya ƙaunar ko ganin ta a kusa dashi,kinga dole ta bar gidan ko na uban ta ne"

Nadiya ta amsa"good job! Allah ya bar mu tare,da alama kuna damuwa da al'amura na,idan na gama da ita sai na koma kan waɗannan matsiyatan ƴan uwan nashi,nan gaba ko kallon shi zasu yi sai dai daga nesa

Umaima ta buɗe baki da niyyar yin magana Deeja ta faɗa falon fuskar ta babu alamun damuwa,duk da cewar ta tsorata da lamarin su,ganin ta sai suka sha jinin jikin su,ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya a raine,sannan ta ɗauke kanta ta shige ɗakin ta

Sun firgita sosai,don sun ga alamun hirar su,don haka suka chanja hira

Tun daga lokacin ta sake zage dantse ga kulawa da take bawa kanta da yaron ta,a haka har tsawon sati guda

A lokacin ne Khalees ya dawo,a lokacin Deeja bata nan tana wurin aiki,don haka Nadiya ta samu cikakkiyar damar ƙulle ƙullen ta na kissa da kisisina da sharri,shi kuwa Khalees ya bi ya haye kai

Da ta dawo tun a parking space taga motar shi,hakan ya tabbatar mata da dawowar shi,hakan bai dame ta ba,kanta tsaye ta shigo cikin gidan

Bata same su a parlour ba,hakan bai dame ta ba ta shige ɗakin ta

Bayan Isha'i tana jin su a parlour suna ta shewar su,ta so ta fito amma sai ta tuna da cewa zai iya yi mata wulaƙanci a gaban Nadiya,don haka tayi zaman ta a cikin ɗakin ta

Washegari sun haɗu dasu a kitchen,batare da damuwa ba ta gaishe su,amma ko kallon banza bata samu ba,bata damu ba ta cigaba da harkar gaban ta, Nadiya sai kwarkwasa da kisisina takeyi masa,shi kuwa sai faman tarairayar ta yakeyi,ko kallon su Deeja bata sake yi ba,tayi aikace-aikacen ta ta kammala ta fice daga kitchen ɗin

Tsawon kwanaki uku kenan,da dawowar Khalees,amma ko sannu bata haɗa su da Khalees ba,idan tayi masa magana ma baya amsawa, don haka ta haƙura da yi masa magana

Dawowar ta kenan daga Wajen aiki,tana shigowa parlourn taji an bangaje ta,da sauri ta ɗago don ganin waye, Nadiya ce

Ganin Nadiya ce ta san magana take nema,don haka ta mayar da kallon ta kan fuskar wayar ta

Dawowa tayi da baya ta kalli Deejan a ƙasƙance tana faɗin"oh sorry fa!na ɗauka akuya na bangaje shiyasa kika ga ban damu ba"

Wani banzan kallo Deeja ta watsa mata sannan tace"kar ki damu,nima dama sai naji kamar bangazar batayi min kama da da ta mutum ba,nayi tsammanin tinkiya ce ta bangaje ni shiyasa ban kula ba"

A zafafe Nadiya tazo wajen tana yi mata kallon wulaƙanci tace"ke!ki shiga taitayin ki ko kuma jikin ki yayi tsami"

Wani watsatstsen kallo Deeja ta watsa mata na sama da ƙasa sannan tayi wani murmushin rainin hankali tace"haba yarinya!ko wanda ya dire ki bai isa ba ballantana ke!!"

Cikin ɗaga murya ta shiga faɗin"wanda ya kawo ni fa kika ce, luvly kana jin abinda kike cewa"

Faɗar hakan ya tabbatar wa Deeja cewa Khalees ne ya shigo parlourn,sai ji tayi yace

"Ai tuntuni dama ta nuna tafi ƙarfi na,don haka dole ta bar min gida na"ya ƙaraso inda Deeja take ya zaro takarda a envelope ya miƙa mata yana duban ta a wulaƙance yace"kije na sake ki saki ɗaya,ki tattara ki bar min gida,dama ban ɗora miki idda ba"

Gaban ta ne yayi mummunan faɗuwa a ranta ta furta"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"tare da amsar takardar,bata kuma magana ba ta wuce ɗaki

Tana jiyo shewa da habaice-habaicen nadiya,tayi mata banza,ta kwashi abubuwan ta masu muhimmanci ta zuba su a mota ta fice daga gidan

Sai da tayi ƴar doguwar tafiya sannan tayi parking tana nazarin wajen zuwa,daga bisani ta yanke shawarar wucewa gidan ta da ta gina, saboda dama tuni ta zuba komai

Ƙerarren gida ne dake unguwar Na'ibawa,duk da ƙarami ne amma ya tsaru sosai,ta shigo da motar ta ta rufe gidan ta shiga ciki

Kwanan ta biyu babu wanda ta sanarwa mutuwar auren ta,sai dai akwai abinda ta shirya,don a ganin ta lokaci yayi da ya kamata ta samu farin cikin da ta rasa shekaru masu yawa,don haka ta ɗauki hutu a wajen aikin ta,ta soma shirye shiryen barin garin

Satin ta biyu ta gama shirya komai,motar haya ta hau airport,daga nan ta haye jirgin su zuwa in da take fata...

Ayi min afuwa Please

"Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 17

Ƙarfe uku na yamma ta sauka a garin jimeta da ke Adamawa,ta sha wahala sosai kafin ta gano address ɗin gidan da Dr Mahmud ya taɓa bata kafin rasuwar shi saboda bata san garin ba,bata samu kanta a ƙofar gidan ba sai bayan huɗu na yamma

A bakin gidan ta samu wani dattijo,tayi masa sallama ya amsa,ta durƙusa cikin ladabi ta gaishe shi cike da girmamawa,ya amsa yana ƙare mata kallo,bayan sun gaisa ya dube ta yana faɗin

"Yarinya idan na gane ki zan iya cewa autar wajen ZAINABA ce ko?"

Murmushin Deeja ya faɗaɗa,tace "eh baba,nice autar ta"

"Allah sarki zainab! Allah yayi mata rahama ya kyauta makwanci,ita da mai gidan na ta"

Deeja ta amsa da"ameen cikin sanyin murya"

Yace "ki tashi ki shiga ciki,mariyan tana ciki"Deeja ta miƙe zata shiga,yace "kawo yaron,ko bacci yakeyi?"

Deeja ta amsa da"bacci yakeyi"

"Allah sarki!yaya sunan shi?"

"Sunan mahaifi na ne amma ina kiran shi da Affan"

"Allah sarki! Allah ya raya shi"

Ita dai Deeja tayi shigewar ta gidan

Da sallama ta shiga tana rarraba idanu,wata dattijuwa na zaune tare da samari da ƴan mata a tangamemen tsakar gidan, ƙarƙashin wata ƙatuwar bishiyar mangwaro,sai hira sukeyi,da alamu dai jikokin ta ne,duka suka dawo da hankalin su kanta

Ta ɗan daburce kafin daga bisani ta daidaita nutsuwar ta,ta gaishe su sannan ta fara bayani cikin dakiya

"Ni ƴar gidan zainab ce,ƙanwar su nusaiba da Yusuf"

"Ai na ga alamu, Allah yaji ƙan zainaba, Hadiza ce ko?"a cewar dattijuwar

"Eh nice"ta bata amsa kanta a ƙasa

"Masha Allah!ke suwaiba maza kai ta ɗaki tayi sallah ta huce gajiya,ki kai mata abinci maza"kafin ta rufe baki ɗaya daga cikin ƴan matan ta miƙe ta karɓi akwatin Deeja ta jagorance ta zuwa wani ɗaki

Bayan Isha'i Deeja ta kammala komai da komai,ta nufi ɗakin Hajiya Mariya,tayi sallama

Hajiya Mariya ta amsa tare da yi mata yi mata izinin shigowa,ta shigowa,ta shiga gami da neman waje ta zauna,Hajiya Mariya ta dube ta cikin kulawa tana faɗin"ina mahmudun?"

"Yayi bacci"ta amsa mata

"Da kyau,kinyi masa adduoi kuwa?"

"Ai bana sanya,inayi masa sosai"

"To Allah yayi muku albarka gaba ɗaya"

"Ameen Inna"

Hajiya Mariya ta kalle ta sosai tace"da alamu akwai magana a bakin ki ko?"

Deeja ta gyara zama tace"eh Inna,dama Abba ya sanar dani cewa kece kika raini yayye na Nusaiba da Yusuf,shine nazo na gansu, saboda tsawon lokaci ban gansu ba"

Hajiya Mariya tayi murmushi tace"hakane,tabbas Ni na karɓi Yusuf da nusaiba,a gaba na suka tashi,amma daga baya sun koma hannun babban ɗa na dake can ƙasar America dazama,a can sukayi karatu,a can nusaiba tayi aure,shi kuma Yusufu ya matsa sai dai yanzu ban san a in da yake da zama takamaimai ba, kasancewar ba ma a American ya zauna ba"

"Amma ina meyasa aka raba mu?gashi ban shaƙu dasu ba"a cewar Deeja cikin damuwa

"Labari ne mai tsawo Hadiza,idan zaki yi jumuri sai na gaya miki,har da labarin mahaifiyar ki ma"

"Ki bani Inna,dama an ce mahaifiya ta ma tayi haƙuri sosai,zan so na san labarin ta"

Hajiya Mariya tayi murmushi tana kallon Deejan

WAIWAYE............

Malam Ishaq cikakken malami ne mai cikar kamala da sanin ya kamata,yana daga cikin manyan malamai masu karatu da akeji da su a wancan zamanin

Yana da mata ɗaya da yara biyu,matar shi ruƙayya mace ce mai sanyin hali da sanin ya kamata,gata da kirki da mutunci,babu wani wanda zai ce ga abinda tayi masa na ƙuntatawa

Sai dai dangin malam Ishaq sun matsa mata ƙwarai da gaske,a cewar su ta hana shi ya ƙara aure,shi kuma yace aure lokaci ne,idan lokacin ƙarawar yayi ba sai an gaya masa ba

Ismail da sakina yaran su sun taso cikin gata da tarbiyya,sai dai basa iya kaiwa dangin su ziyara saboda tsangwamar da suke sha daga wajen su

Daga baya kuma sai suka dami malam Ishaq da batun ruƙayya bata haihuwa sosai,tun daga kan sakina bata ƙara haihuwa ba,kuma sakinan shekarunta goma sha shida

Rana tsaka malam Ishaq yazo da batun abokin shi ya bashi yarinya,zai ƙara aure,hakan ya tashin hankalin ruƙayya sosai,don tsoro take ji kar ya zamana dangin mijin ta zasuyi amfani da amarya su fitar daita daga gidan,amma sai ta fawwalawa Allah

Anyi auren malam Ishaq da Amina, yarinya ce da bazata wuce sa'ar Isma'il ba,sai dai ga dukkan alamu yarinyar ta samu ingantacciyar tarbiyya,don duk zugar da dangin mijin ta suke mata sai dai ta ji su da kunne,wanda hakan ya dawwamar da zaman lafiya tsakanin ta da ruƙayya,kuma babu wanda ya kai ruƙayyar jin daɗin dacen da tayi na abokiyar zama

Zama yayi daɗi tsakanin ruƙayya da Amina, Amina na girmama ruƙayya, itama ruƙayya taba mutunta ta, hakan ne ya wanzar da zaman lafiya a gidan

Watan ta shida a gidan ta fara laulayi,duk yadda su dangin Ishaq suka so shiga tsakanin ruƙayya da Amina hakan bai samu ba,tilas suka sanya musu idanu

Sakina ta zamto babbar aminiyar Amina, kullum suna tare,hakan ya sanya suka saba,tun kafin zuwan Amina dama sakina ce nauyin komai a gidan,yanzun ma ita ɗin ce maiyin komai a gidan,da kafin Amina ta fara laulayi tare sukeyi,amma yanzu Aminan bata iya yin komai

A haka har lokacin haihuwar Amina yayi,kai tsaye tace a bar ta ta haihu a gida,hakan kuwa akayi,don babu kulawar da bata samu a wajen su sakina,hatta da Isma'il ya kan siyo duk wani abu da yaji tace tana so har ya ishe ta,wannan hadin kan nasu yana matuƙar sanya malam Ishaq cikin farin ciki

A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo ƴar ta mace, ruƙayya ce ta karɓi haihuwar ta gyara mai jego da jaririya,nan da nan gida ya cika da mutane,ana ta murnar wannan ƙaruwa

Sai dai Inna Mariya ta katse musu hanzari,don kuwa cewa tayi da ita zata tafi can Adamawa in da take aure,sam hakan baiyi musu daɗi ba,amma tunda malam Ishaq ya amince haka dole suma suka haƙura,don dai ita Amina marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu tun tana ƙarama,sannan uwar riƙon ta ko da wasa bata ji daɗin ta ba,dole Inna Mariya ƙanwar mahaifiyar tata itace zata maye gurbin yayar tata

Ranar suna malam Ishaq ya raɗawa jaririya suna zainab,an sha shagali sosai, sannan suka shirya suka tafi Adamawa

Mutanen gidan sunyi kewar Amina da zainab ba kaɗan ba,su kenan kullum a lissafin kwana nawa ya rage su dawo

Ranar da zasu dawo Mutanen gidan sai ɗokin dawowar su sukeyi,aka gyara ko'ina akayi ta dafa abinci kala-kala,duk don dawowar Amina da zainab

Sai dai mummunan labarin da suka ji yayi tsananin tayar musu da hankali, Amina sunyi hatsari ita da waɗanda zasu dawo da ita,cikin tsananin tashin hankali gaba dayansu suka nufi asibitin da aka kwantar dasu

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 18

Sai dai a halin da suka same su ya ƙara firgita su,kuka suka rinƙa yi sosai,zainab ta samu karaya shida a hannaye da ƙafafuwan ta,banda manyan raunuka,sauran mata uku da suka rako ta biyu daga cikin su ma rai yayi halin shi,har an kai su mutuary,sai dai wani ikon Allah zainab ko ƙwarzane batayi ba,asalima a lokacin baccin ta takeyi hankali kwance

Amina ta dube su cikin zafin ciwo take faɗin"ga zainab nan,ku kular min daita,Ni bazan rayu ba,na bar amanar ta a hannun ku,don....don....don....."yadda maganar take sarƙewa ya ƙara ba su tsoro,a gigice sakina ta fice da gudu zuwa office ɗin babban likitan

Amma ko da suka dawo gani tayi mahaifiyar su ruƙayya riƙe da hannun Aminan, Isma'il dama bai shigo ba yana daga bakin ward din, ruƙayya sai kuka takeyi,likitan ya duba pulse dinta ya tabbatar musu da Amina tayi tafiya mai nisa,jiri ne ya ɗebi sakina,sai da likitan ya taimaka ya riƙe ta

Basu juma sosai ba aka yi cike ciken da ya dace aka basu gawar Amina,aka sanya ta a ambulance aka tafi daita zuwa ainihin gidan iyayen ta

Tabbas anji mutuwar Amina,don Amina yarinya ce ta gari bata da abokin faɗa,gata da girmama na gaba da ita

Baba talatu itace uwar goyon Amina,sai a yau tayi nadamar abubuwan da ta aikatawa Amina ita da yaran ta, domin ko babu komai Amina ta kular mata da yara,amma ita kullum talatu bata da burin da ya wuce ta ci zarafin Amina,yau dai ga Amina ta bar mata duniyar

An yiwa Amina sutura an kai ta gidan ta na gaskiya,su kuma su ruƙayya suka dauko zainab suka dawo gida

Sun daɗe sosai kafin mutuwar Amina ta sake su,suka mayar da hankali wajen rainon zainab baiwar Allah

Shekarar zainab ɗaya akayi auren sakina da Kabiru,Kabiru da kowa nashi ƴan garin azare ne,don haka can aka kai su,wannan dalili ya janyo shaƙuwar zainab da sakina tayi rauni

Sai Isma'il ya zamana makaranta ce kawai take raba su da zainab,kuma shima sai anyi mata dabara yake samu ya tafi,idan tayi kukan bai dawo ba sai ta haƙura taje wajen ruƙayya,amma da zarar ya dawo to ta bar wajen ruƙayyan

Sun saba sosai,hakan ya faranta ran malam Ishaq,sakina ma ta kawo musu ziyara sau biyu a tsayin shekaru uku da tayi aure,a lokacin zainab na da shekaru huɗu

A lokacin ne ruƙayya ta kama wata iriyar cuta da aka kasa gane kanta,wadda taso tsaidawa da Isma'il karatun shi,amma tawakkali irin nata ya sanya take matsa masa akan yaje makarantar kawai,babu abinda zai same ta

Tun tana kwanciya yau gobe da sauƙi har ciwon ya kwantar da ita gaba ɗaya,sunyi zaryar zuwa asibiti amma an kasa gano kan abin,har ruƙya anyi mata amma duk babu cigaba

Sai da ta shafe shekara biyu tana fama,a lokacin ne Isma'il ya ƙare karatun shi ya dawo don jinyar mahaifiyar shi

Dangin malam Ishaq ganin har lokacin yaƙi aure sai suka rinƙa zuga mahaifiyar shi,ai kuwa tace ko dai ya ƙara aure ko ta tsine masa

Haka dai ba don ya so ba aka aura masa lubabatu, auren luba uku amma bata zama, saboda fitinanniya ce ta gaske,gashi kuma sam sam bata da tarbiyya

Zuwan luba gidan ya haifar da fitina, saboda irin cin zalin da takeyiwa zainab,abinda sam Isma'il da ruƙayya basa jura, shiyasa kullum suke rigima da Isma'il,ƴan uwan mahaifin shi kuwa dama tuntuni sun daɗe da yi masa tambarin rashin tarbiyya,don sam baya ɗaukar shirmen su

Watan luba uku a gidan Allah yayiwa ruƙayya rasuwa,mutuwar ga jijjiga malam Ishaq da Isma'il ƙwarai,ita kanta zainab da bata gama wayo ba amma ta fuskanci anyi musu rashi itama ta sha kuka, hakanan itama sakina da aka sanarwa mutuwar

Sakina ta so tafiya da zainab,don dama ita har yanzu Allah bai bata haihuwa ba, Isma'il yace tayi haƙuri don bazei iya jurar rashin zainab ba

Basu juma sosai ba jarabawar su ta fito,inda tayi kyau sosai,don haka aka bashi scholarship inda zai tafi san Francisco University donyin degree ɗin shi na biyu a can

Yayi murna sosai,amma sai ya fara tunanin yadda zai yi rayuwa ba tare da zainab ba, mahaifin shi ya nuna masa kar ya damu,ko shi zai iya kula da ita

To fa!tunda ya bar ƙasar zainab ta fara rayuwar wahala,duka,zagi,cin mutunci,horon yunwa,babu abinda luba bata yiwa zainab,amma ta kaɗa mata warning cewa kar ta sanar da mahaifin ta,idan ta sanar masa sai ta yanka ta,zainab akwai tsoro gashi bata da wayo don haka ko da wasa bata taɓa gigin sanar da malam Ishaq ba

Ɓangaren abinci kuwa,idan luba ta bata abinci tun safe bazata sake bata ba sai dare,kuma shima ba wanda zata ƙoshi ba,ga aikin da take sanya ta wanda yafi ƙarfin shekarunta,idan tayi ba dai-dai ba tayi mata mugun duka,da malam Ishaq ya taɓa kama ta ta tula mata wanki ya tambayi ba'asi sai cewa tayi

"Haba malam!idan ban koyawa zainaba aiki yanzu ba sai yaushe?idan ta girma fa ba yi zatayi ba,kuma bazata iya ba,kuma ai abin kunya ne a ce an kai zainaba gidan miji bata iya komai ba,kaga sai a zage mu a duniya a ce don uwar ta bata raye yasa muka kasa koya mata ƴan aikace-aikacen gida"

Jin hakan ya tilastawa malam Ishaq zuba musu idanu,ƴan'uwan shi suna sane da abin da takeyi mata amma ko a jikin su,sai ma ƙara zuga ta da sukeyi

A haka zainab ta cigaba da rayuwa har Allah ya nufi Isma'il da kammala karatun shi,kuma ya samu nasarori da yawa,juna a can san Francisco Allah ya haɗa shi da faɗima, faɗima dai balarabiyar ƙasar Yemen ce

Sun shaƙu sosai da faɗima,daga mutunci lamarin nasu ya juye zuwa soyayya,amma yawanci hirar su akan zainab ne,take taji tana son yarinyar duk da bata san ta ba,amma kullum sai ta ga hotunan ta,a ƙarshe dai da kanta ta nemi idan Allah yayi sunyi aure ya dawo da ita gaban su su rike ta,yaji daɗin hakan sosai

Zainab na durƙushe tana faman yin wani uban wanki,duk da cewa zazzaɓi ne a jikin ta, sakamakon mahaukacin dukan da luba tayi mata, saboda ta aike ta da kuɗi sun faɗi, dai-dai nan Isma'il yayi sallama ya shigo

Da sauri ta ɗaga kai gami da amsawa,ganin Isma'il sai ta nemi zazzaɓin da takeji ta rasa,da gudu ta nufe shi ta ƙanƙame shi,sai ta fashe da kuka,shima hawaye ya fara cikin tsananin baƙin ciki da mamakin halin da yazo ya same ta a ciki,ya ɗago kanta cikin raunin murya yace

"Zainaba kinyi jinya ne?"

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 19

A hankali ta girgiza masa kai,yace"amma kuma jikin ki da zazzaɓi"ita dai shiru tayi bata ce komai ba

Gefe ya ja ta ya zaunar da ita,sannan ya kalli uban tulin kayan wankin,ya maida kallon shi kanta gami da tambaya

"Waye ya baki wannan wankin?"

Cikin yanayi na ciwo ta amsa"gwaggo ce"

"Ita ta baki wannan uban wankin?"ya tambaya a fusace

A hankali ta ɗaga kai

Ya girgiza kai zuciyar shi cike da damuwa, lokaci guda kuma ya miƙe gami da kama hannun ta,suka shiga cikin gidan,ko ta kan kayan da ya shigo dasu bai bi ba

Kai tsaye ɗakin ta ya nufa daita ya kwantar da ita,yana fitowa suka yi kiciɓus da luba,ta firgita ƙwarai da gaske,don tasan waye Isma'il musamman akan ƴar gudaliyar nan zainaba,amma sai ta basar,cike da yaƙe da inda-inda take faɗin

"Ah!mutanen Amurika ne yau a gidan namu?Barka da sauka"

A daƙile batare da ya kalle ta ba yace"Barka"

Bai fi mintuna goma ba suka suka shigo da likita,ya dudduba zainab ya rubuta mata magunguna sannan yace a tabbatar taci abinci kafin ta sha,bayan likitan ya fita Isma'il ya tambaye ta ko ta ci abinci,ya sha mamakin jin cewa bata ci ba,cikin ɓacin rai ya fice daga gidan

Abinci ya samo mata mei rai da lafiya da kanshi ya bata sannan ya bata magani,da yaga ta ɗan dawo hayyacinta sai ya miƙe ya ɗebo kayan da ya shigo da su,ya juye mata tsarabar da yayi mata a gaban ta

Kayan sawa ne,sai takalma da kayan ciye-ciye iri-iri, sai ta hau murna da tsalle-tsalle,ta manta da ciwon da ke jikin ta,shima Isma'il sai ya damu kanshi da farin ciki,ya tattare mata kayan sannan ya fita zuwa ɗakin luba

Da sallama ya shiga ta amsa da rawar jiki,ya gaishe ta fuska babu yabo babu fallasa,ta amsa tana ta faman wage baki haɗe da faɗin"Masha Allah ismaila!Yaya karatun?"

"Karatu mun gama alhamdulillahi"

"To Masha Allah!yanzu sai aiki ko?"

Ya ɗan kalle ta a kaikaice ya ƙara ɗauke kanshi yana faɗin"shima an samu"

"To lamari yayi kyau,sai aure ko?"

Kamar yace shima an samu sai yaga kamar tambayoyin nata da rainin wayo a ciki,don haka sai yace"gwaggo bari na leƙa cikin gari"bai jira cewar ta ba ya fice daga ɗakin

Yana fita Luba ta leƙo ɗakin zainaba,a lokacin zainaban ɗin bacci takeyi,a fili ta furta"eh lallai,wato an samu sake har da bacci!to dole ki tashi ki ƙarasa aikin nan,ke zainaba! zainaba!!"ta shiga ƙwalla mata kira

A firgice zainab ta farka, Luba ta tsaya a kanta tana yi mata kallon banza,gaban ta ya faɗi,ta miƙe zaune tana kallon luban,cikin gadara Luba tace"wato don isa da ƙwarewa har da bacci don kinga wancan saƙagon ya dawo ko?to maza ki tashi ki ƙarasa yi min wanki na"

Shiru zainab tayi gami da zuba mata idanu, Luba ta daka mata tsawa har sai da ta firgita,ta miƙe jiki na rawa ta nufi tsakar gidan domin ƙarasa wankin

Tana cikin yin wankin malam Ishaq ya dawo tayi masa sannu da zuwa ya amsa cikin kulawa, cikin farin ciki take shaida masa dawowar Isma'il

Shima ya cika da farin ciki,ya tambaye ta

"Yana ciki?"ta bashi amsa

"A'a ya fita,amma inaga ya kusa dawowa,ka zauna ka jira shi"babu musu malam Ishaq ya shige cikin gidan,ita kuma ta cigaba da aikin ta

Tana cikin yin wankin Isma'il ya dawo,da sallama ya shigo,ta amsa cikin farin ciki,ganin ta tana wankin ya sanya ranshi yayi mummunan ɓaci,cikin fushi yace

"Zainab ba na hana ki wannan wankin ba?"

Tsoro ya kama zainab,ganin shi cikin fushi tace"gwaggo ce tace nayi wallahi"

"To ajiye,wuce mu je"babu musu ta ajiye ya kama hannun ta suka wuce cikin gidan

Jin Muryar malam Ishaq ya wuce ɗakin mahaifinsa,da sallama ya shiga,malam Ishaq na zaune yana cin abinci,yayi matuƙar farin cikin dawowar ɗan nashi,suka zauna suka kama hira,basu ɗau lokaci ba ya sako masa batun zainab

Cikin rashin walwala yace"gaskiya baba ya kamata a tausayawa zainab,don a ƙananun shekarun ta bai kamata ace ana bata ayyuka fiye da ƙima ba,gashi bata da lafiya"

Malam Ishaq ya numfasa yace"wallahi Ni kaina abin yana damu na Isma'il,don dai bani da yadda zanyi ne,amma na bar komai a hannun ka,ka ɗauki matakin da ya dace"

Isma'il ya gyara zama yace"na gode baba,yauwa,dama ina so na shaida maka wani Company ya bani ya bani aiki a can san Fransisco ɗin,kuma nan da next month zanje na fara yi musu aiki"

"Masha Allah alhamdulillahi! gaskiya nayi farin ciki, Allah ya taimaka"

"Ameen baba, godiya nake"

"To batun aure kuma fa?"ismaila?"a cewar malam Ishaq

Ismail ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin jin nauyi yayiwa malam Ishaq bayanin faɗima balarabiyar ƙasar Yemen

Har malam Ishaq ya fara murna sai ya ɗan yi shiru kafin yace"anya ismaila?baka ɗauko fin ƙarfin ka ba kuwa?"

Ɗan murmushi Isma'il yayi sannan yace"ai tuntuni mun fahimci juna har iyayen ta sun sanni,kuma sunyi na'am da ni"

Murmushin malam Ishaq ya faɗaɗa yace"to Allah ya sanya albarka, Allah ya kaɗe fitina". Isma'il ya amsa da"ameen baba"

Cikin sati biyu zainab tayi kyau ta murje ta maida jikin ta,bata kowane aiki sai wanda baza'a rasa ba,sai wanda Isma'il ya bar

Please Login or Register in order to submit comment