Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tayi,abin yana damun Luba sai dai babu yadda zatayi

Ana isaura kwana Shida ya koma san Fransisco ya shawarci malam Ishaq akan cewa yana so ya mayar da zainab gidan sakina,malam Ishaq ya nuna musu babu damuwa,don haka ya sanar da zainab cewa ta shirya kayan ta

Ba ƙaramin murna tayi ba, washegari ya ɗauke ta zuwa azare,sakina tayi matuƙar murnar ganin ƴar'uwar ta, Isma'il ya damƙa ta a hannun sakina tare da yi masa fatan alkhairi

Watannin shi uku da fara aiki a ƙasar America akayi auren shi da faɗima,bayan auren ne ya ɗauki zainab ya tafi da ita,a lokacin ma sakina tana laulayi,yayi matuƙar taya ta murnar samun ƙaruwa,domin zuwa yanzu babu wulaƙanci da gore-goren da bata sha daga wajen dangin miji duk sai akan haihuwa,to yanzu dai ta samu ciki bayan shekaru goma sha biyu da tayi da yin aure

Rayuwar zainab ta chanja a ƙasar US,yanda faɗima take son ta da nuna mata kulawa yana faranta mata,haka shima Isma'il,kuma ya sanya ta a makaranta mai matuƙar tsada, cikin lokaci ƙanƙani ta sauya baki ɗaya

Isma'il bai manta da mahaifin shi da kuma ƴar'uwar shi ba,don haka yana kula dasu sosai,da sakina ta haihu faɗima da zainab sun zo suna,sun taho mata da kaya tuli guda, yarinyar ta ci sunan surukar ta hajiya Fatima amma suke kiran yarinyar BINTU

Yau dai na karya record nayi post biyu a rana ɗaya 🤣🙃😅

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️ Nusy bee

Page 20

Wannan shafin naku ne matar Khalees fans, readers,more especially likers da commentors, Deeja da Khalees sun ce a gaishe ku🥰

Itama faɗima bata rufa shekara ba ta haifo ƴar ta salma,itama sakina tazo suna,itama sakina tazo suna,kuma ta ga Garba ta mutunci a wajen faɗima da ƴan'uwan ta,babban abin farin cikin ma shine,yanayin da suke zaune da ƙaramar ƙanwar su zainab,hakan ya faranta mata rai sosai

A haka suka cigaba da rayuwa,har zainab ta kammala karatun ta na secondary,kuma ta fara karatun babbar makaranta cike da nasara,a lokacin faɗima na da yara biyar,sakina kuma uku gare ta,akwai shaƙuwa mai tsanani tsakanin zainab da yaran faɗima,salma,nasir,fauwaz,abdallah da Minal,tana kula dasu sosai,Kuma basa rabuwa dare da rana,sai dai makaranta ko bacci

A shekarar ne auren ƙanwar faɗima mai suna AYSHA ya mutu,ta zo ta samu yayar ta ta cikin kuka take shaida mata wulaƙancin da mijin ta yayi mata

"Aure ya ƙara shikenan ya juya min baya,da Ni da IMRAN yanzu bamu da maraba da bola,wani lokacin abinda zamu ci ma gagarar mu yakeyi,duk a tunani na komai zai wuce,kawai shekaranjiya sai gashi ya kawo min takarda,wai ya sake ni saki uku"ta ƙarashe cikin rushewa da kuka

Shiru faɗima tayi tana jin babu daɗi na abinda mijin ƙanwar ta yayi mata,ta san wacece ƙanwar ta Aysha,duk da cewa ɗan adam na iya chanjawa,amma tana yiwa one and only qanwar tata kyakkyawan zato

"Nayi nadamar auren ɗan Nigeria wallahi,sun cika son kansu"Aysha ta cigaba

Murmushi faɗima tayi tace"kayya Aysha!Kar ɓacin rai ya sanya ki yanke hukunci cikin fushi,idan mutum yayi miki laifi sai ki yanke hukunci gwargwadon laifin da yayi miki,shine adalci. Amma hukunta wani da laifin wani rashin adalci ne, Aysha Nima ɗan Nigeria nake aure,kuma ina zaune da ƙanwar shi,amma koda yaushe da shi da family ɗin shi ƙoƙarin su su faranta min,rashin dace ne kawai da jarabta daga Allah ya same ki,ki roki Allah ya baki ikon hayewa,sai kiga yayi miki sakayya mai girma"

"Hakane ukhty!da har nace zan zubar da cikin nan nan jiki na amma na fasa,sai dai ina tausayin Imran,don yana da haƙuri da zurfin ciki,ina tsoron kar a cutar min dashi,don matar nan bata da iymani"

"Ki bishi da addu'a,a duk inda kike a faɗin duniya addu'ar ki zata riske shi,kuma addu'ar uwa a kowanne lokaci tana tasiri akan ɗan ta"haka faɗima tayi ta kwantar mata da hankali har ta samu sauƙin damuwa

Akwai wani abokin Isma'il mai suna MAHMUD,likita ne babba,yana aiki a wani asibiti dake cikin san Francisco University inda zainab take karatu,kuma abokin Isma'il ne sosai,yana da mata ɗaya hajiya bara'atu,da yara uku,Ma'aruf,Abida da faiza, kwata-kwata bara'atu bata daraja mai gidan nata,yaran duk sun raina shi, Ma'aruf ne kawai ya fita Zakka,domin shi ɗabiun mahaifinshi gare shi kuma dama sun fi sabawa dashi,amma matan duka mahaifiyar su suka biyo

Lokacin da yaga zainab ya yaba sosai da nutsuwar ta,don haka ya miƙa tayin shi a wajen Isma'il, Isma'il yaso yi masa musu don yasan halin matar shi,amma haka ya danne,ya bawa Mahmud auren zainab

Ana i saura wata uku biki suka dawo Nigeria gaba ɗaya,suka sauka a tangamemen gidan Isma'il da ke sardauna crescent Nassarawa G.R.A,gida ne ba garari,babu abinda babu a ciki,sannan ya gina parts a ƙalla goma a gidan saboda yace so yake ya haɗe kan yaran shi ko da bayan sunyi aure,ya so malam Ishaq ya dawo gidan amma ya nuna masa a'a,a cewar shi shi da tsufa ya cim masa ma jiran lokaci yakeyi,anan suka cigaba da zama har lokacin biki yayi

Anyi biki lafiya, Isma'il ya nunawa zainab gata sosai,an kai amarya gidan mijinta wanda ke badawa layout, kasancewar shi dama iyalan shi a Nigeria suke zaune ba kasafai suke zuwa US ba

Sai dai tunda ta tare take fuskantar matsaloli daga wajen abokiyar zaman ta,ga yaran ta basu da kunya ko kaɗan, Ma'aruf ne kawai mai tausayin ta da girmama ta

Duk abinda akeyi doctor Mahmoud bai sani ba,kuma zainab bata taɓa shaida masa ba,ba shi ba ma,ko ƴan uwan ta bata shaidawa,idan abin ya dame ta sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka

A haka ta kasance har tsawon shekara guda,a lokacin ne ta haifi ƴar ta ta farko wato NUSAIBA,a lokacin bayan an kammala suna gida aka maida ita gaban faɗima har ta murmure

Ranar da zata koma tun safe take zullumi,har faɗima ta fahimci halin da take ciki,amma da ta tambaye ta sai tace ba komai,tilas ta ƙyale ta,amma ta rinƙa yi mata nasiha cikin hikima da kara ƙarfafa mata gwiwa

Shekaru biyu tsakani ta kuma haifar ɗan ta YUSUF,a lokacin doctor Mahmoud ya fara gane makircin da bara'atu,ta sha haɗa su faɗa,zainab ta san aikin ta ne amma bata taɓa gaya masa ba sai da ya gane da kanshi,wannan shine dalilin da yasa ya raba musu gida,sai a sannan zainab ta samu kwanciyar hankalin gidan auren ta

Sai da Yusuf ya shekara bakwai sannan zainab ta sake haihuwar ƴar ta mace,a lokacin bara'atu ƴaƴan ta bakwai,bayan faiza akwai sadiya,fadila,Mubarak da shukra sadiya sa'ar nusaiba ce,Yusuf ya bawa fadila wata bakwai,Mubarak shekarar shi huɗu,ita kuma shukra watan ta tara

Nusaiba da Yusuf kamannin doctor Mahmud suka ɗebo,har gwara Yusuf ya dauko chaculate skin ɗin zainab,amma nusaiba har farar fatar doctor Mahmud babu abinda ta bari,amma ga wannan sabuwar jaririyar abin ba haka yake ba,don babu abinda bata dauko irin na zainab ba,hatta da farce, Mahmud bai taɓa ɗorawa wani ɗan shi so irin yadda ya ɗorawa wannan jaririyar ba,ya zaɓa mata sunan uwargidan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wato NANA KHADIJA

sai a wannan karon sakina ta samu halartar sunan ƴar uwar tata,itama a lokacin tana goyon yarinyar ta halima wadda suke kira da MIMA,a lokacin tana da watanni tara

Soyayyar da Mahmud yakeyiwa Deeja har tayi yawa,ya zamana sunyi tsananin sabo tun tana ƴar ƙarama,hakan sam bayayiwa zainab daɗi don tana tsoron abinda zai je ya dawo, musamman ma da ya kasance ba ita kaɗai bace,amma shi Dr Mahmud ko a jikin shi,duk wasu abokan shi sun san Deeja

Muna miki maraba da zuwa duniya Deejan mu🥰kuma mu ma fa muna son ki kamar yadda doctor yake son ki🤗

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 21

Shekarar Deeja ɗaya da haihuwa Allah ya amshi ran malam Ishaq bayan ya ɗan yi fama da jinya, mutuwar ta girgiza ƴaƴan shi sosai,don ita zainab tun daga nan ma lafiya ta ƙwace mata

Bayan shekaru biyu kuma ta sake haihuwa,sai dai wannan haihuwar tazo da matsala,don itace silar rasuwar zainab da abinda ta haifa, Mahmud da Isma'il hauka ne kawai basuyi ba,babu wanda bai tausaya musu ba,hatta da sakina ma ta jijjiga iya jijjiga,amma suka fauwalawa Allah suka bita da addu'ar neman rahamar Allah

Inna Mariya da tazo gaisuwa itace ta nemi alfarmar tafiya dasu Nusaiba,kallo ɗaya zakayiwa yaran su baka tausayi ƙwarai, Dr Mahmud yace ta tafi dasu amma ta bar masa Deeja don ta rinƙa ɗebe masa kewar zainab,ba haka ta so ba amma ta ɗebe su,a lokacin idanun ta taf da hawayen kiran "ammi na!"da Deeja takeyi

Daga baya dai Deeja hannun Bara'atu ta koma, Bara'atu kam dama ta samu, don babu kunya take gallazawa baiwar Allah da batayi mata komai ba, Ma'aruf ne yayi masa hannun ka mai sanda,wanda a silar hakanne ya samar mata masu aikin da zasu kula da ita ta bar hannun Bara'atu,amma duk da haka sai dai idan ƙannen Ma'aruf basu ga ta fito ba,uwar tayi musu huɗuba,haka zasu doddoke ta ta koma wajen mariƙiyar ta tana kuka

Yau ma Ma'aruf suna zaune da babban abokin shi kuma ɗan aminin mahaifinsa abdurrashid wanda suke kira da KHALEES,suna hirar makaranta yadda suka saba,sai ga shukra ta biyo Deeja da gudu, Ma'aruf ya daka mata tsawa,a tsorace ta koma,ya kama hannun Deeja ya mayar da ita wajen mai rainon ta sannan ya dawo wajen abokin shi suka cigaba da hira

Lokacin da Dr Mahmud zai sanya Deeja a makaranta ma bai saka ta makarantar da ƴan uwan ta sukayi ba,wadda tafi ta komai da komai ya saka ta,ya ware driver mai Kai ta yana dawo da ita

Shekarar ta goma sha shida ta kammala secondary,babu ɓata lokaci ya nemar mata admission a university of Sydney Australia inda ta karanci accounting,duk da soyayyar da yake gwada mata haka ya tsaya tsayin daka ganin bata lalace ba har ta kammala karatun ta cike da nasara,ta haɗe kan kwalin ta cike da farin ciki ta roƙi abban ta ya samar mata aiki

Sai dai karo na farko yace a'a ga uzurin Deeja,duk kuka da taɓarar da tayi ya kafe akan ra'ayin shi hakan ya bawa Deejan mamaki sosai,amma saboda bata iya musu ba haka ta haƙura

"Babu Abinda kika nema kika rasa auta na(da yake haka yake kiran ta)ba sai kinyi stressing kanki da aiki ba,duk abinda kike bukata duk girman shi I'm there for you"tayi murmushin yaƙe bata ƙara cewa komai ba

Ranar birthday dinta da ya zagayo Dr Mahmud ya bata mamaki inda ya gwangwaje ta da dalleliyar mota sabuwa fili,kuma mai ainihin tsada,a ranar tayi farin cikin da ta dade rabon ta da irin shi,kuma batare da ɓata lokaci ba driver ɗin ta ya fara koya mata motar,bata wani daɗe ba ta iya

Ma'aruf da Khalees lokaci ɗaya sukayi karatu a ƙasar England, Ma'aruf ya karanci banking and finance,shi kuma Khalees ya karanta mechanical engineering,sai da suka haɗa master's degree din su da PhD sannan suka dawo gida,batare da ɓata lokaci ba sukayi aure,sai dai Khalees ya riga Ma'aruf aure kasancewar mahaifinsa mutum mai tsari da tsanani,da shi da sauran ƴan uwan shi mata shi yake zaɓar musu abokan rayuwa

Anyi shagali sosai a bikin Ma'aruf,duk wulaqancin da ƙannen Ma'aruf sukeyi mata bai dame ta ba,don dai ita ta hannun daman ango ce,sannan bayan amarya tazo sai suka fi shiri da Deejan, saboda a bayyane yake ƙannen Ma'aruf basu da kunya

***** ***** *****

Dawowar ta kenan daga gidan su ƙawar ta zee da suka haɗu a Australia, abokiyar karatun ta ce,sai dai zee ita law ta karanta,ita kuma accounting,tasu tazo ɗaya da zee sosai saboda kirkin yarinyar,gashi mahaifiyar zee tana janta a jiki tamkar ƴar ta,hakan ne ya sanya Deeja take jin shauƙin zuwa gidan don a bayyane yake Deeja ta rasa soyayyar uwa,yanzu dai shirye-shiryen bikin ta sukeyi da CEO din kamfanin da Deejan take so tayi aiki,dama zee din ce mai zuga ta ta nemi aiki a can,amma da mahaifin ta ya nuna baya so tilas aka haƙura

Tuƙi takeyi tana bin waƙar da ta kunna Justin Bieber mai taken love me, batayi aune ba sai ganin mutum tayi a gaban ta,kafin ta kauce tayi sama dashi,ta shiga tashin hankali da gigita irin wadda bata taɓa shiga,tayi parking jikin ta na rawa ta nufi wajen da mutumin yake kwance har mutane sun fara zagaye shi

Sai da gaban ta ya faɗi ganin mutumin, tsananin kamar shi da su Mamie babba ts ɓaci,yana kwance zuwa lokacin baya hayyacin shi,sawa tayi a sanya mata shi a mota,ba'a Musa mata ba suka sanya mata shi a mota suka miƙo mata ƴar jakar kayan shi kai tsaye ta ja mota zuwa asibitin mahaifin ta da ya gina a kano,kafin ta ƙarasa ta kira shi tana kuka ta shaida masa abinda ya faru,shima nashi hankalin ya ɗan tashi

Tana zuwa aka karɓe shi aka fara treating din shi,tana rungume da jakar kayan shi tayi tagumi,zuwa can ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya,tasan babu likitan da zai tuntuɓe ta ko da da akwai matsala sai dai mahaifinta,don haka ta ɗauki jakar jiki babu ƙwari ta wuce parking space don mayar daita mota

Sai dai har ta kusa wajen jakar ta zame ta faɗi,ta durƙusa don ɗauka sai ta ci karo da wani hoto ya leƙo,har zata mayar sai ta fasa,ta zaro,gaban ta ya faɗi ganin momy Aysha maman su Aunty Ramlah,qanwar Mamie babba,da wani yaro a hoton, wannan hoton idan bata manta ba momy Aysha na da irin shi,kuma tace shine only son din ta IMRAN,Wanda ta bari a gidan mahaifin shi a Bauchi

Jikin ta yayi sanyi,sai yanzu ta gane ɗan momy Aysha ne kenan,to me ya kawo shi Kano shi da yake Bauchi?ko momy Aysha da ta ƙara aure yanzu ai tana Abuja ne,amma maybe wajen Mamie babba yazo,da wannan tunanin ta mayar da jakar sannan ta koma asibitin

Few hours ya dawo hayyacin shi,sannu take ta jera masa amma sai bin yake da idanu kamar bai taɓa ganin ta ba,itama ta gaji don kanta tayi shiru

Kwanan shi biyu a asibitin aka sallame shi,zuwa lokacin ya saba da Deeja,har ta bata labarin irin wahalar da yasha a hannun matar uba,a ƙarshe dai ta sanya mahaifin shi ya kore shi da ƙazafin wai yana leƙa mata yara mata

Tausayin shi ya rufe Deeja ƙwarai,tace "in Sha Allah daga yanzu ka fita a sharrin ta,ita kuma taje rayuwa ce"

Har gida ta samu baba Prof (professor Ismail)ta bashi labarin komai da kuma tabbacin da ta samu na cewar Imran ɗan momy Aysha ne, baba Prof yaji dadi kwarai,da kanshi ma yaje asibiti ya dauko Imran ya ware masa part a gidan ya bashi,amma lokacin baiyi wa yaran shi bayanin komai ba,gashi mamie da ita kanta momy Aysha sunje Yemen ganin gida

Ko sati baiyi da zuwa ba Deeja tayi insisting abban ta ya bawa Imran aiki a asibitin shi, kasancewar shima likita ya karanta,shi kam yayi farin ciki da haɗuwa da Deeja matuƙa,ya fara aiki cikin kwanciyar hankali, saboda zirga-zirga ta sauƙaƙa baba Prof ya bawa Imran kyautar motar hawa,Deeja ta taya shi murna ƙwarai da gaske

Kusan kullum Deeja sai ta kawowa Imran ziyara,wani sain ma ta kanyi girki ta kawo masa,shaƙuwa mai tsanani ta shiga tsakanin su,duk gidan Professor sun san da haka,kuma suma su fauwaz tun suna ɗari-ɗari da Imran ɗin har suka gane cewa mutumin kirki ne

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 22

A Asibitin da yake aiki ne suka haɗu da NAJEEB,shima likita ne,kuma matsayin su ɗaya da Imran ɗin,sai kuma tasu tazo ɗaya

Abokan aikin su basa son mu'amalar Imran da najeeb, saboda sun san Najeeb ba mutumin kirki bane,shi kuma Imran da alamu mutumin kirki ne,ga iya mu'amala da mutane da girmama na gaba dashi,ga tausayi

Shi kuwa Najeeb Imran ya burge shi ganin shi kyakkyawa mai ilmi da nutsuwa,ga tsafta da iya gayu,gashi bashi da hayaniya da kwaramniya,sai yaji sha'awar haɗa shi da ƙanwar shi UMAIMA

kwanan Imran tara da fara aiki Mamie babba da momy Aysha suka dawo, Deeja ta cika da murna,ta je har garden da Imran kan zauna yana dudduba manyan litattafan su na likitanci ta kira shi su gaisa da Mamie,baiyi mata musu ba ya bita,amma me?

Tun kafin ya kai ga gaisuwar idanun shi suka sauka akan momyn shi da tayi stiff tana kallon shi,a wajen ya zube idanun shi suka tara hawaye,Muryar shi tana rawa ya furta "momy na!"

Tabbas tun kallon farko faɗima ta gane cewa ko waye wannan daga ahalin su ya fito, saboda tsananin kamanni,dama babu abinda bana prof yace musu har yanzu,su kansu su fauwaz basu san komai ba

"Ukhty Imran ne! Imran ɗi na ne ukhty!!"a cewar momy Aysha cikin gigita,sai ta fashe da kuka,Imran ya ƙarasa ya rungume mahaifiyar shi yana ƙara fashewa da kuka

Bayan an nutsu Imran ya bayar da labarin yadda rayuwa tayi dashi a gidan su

"Momy bayan kin tafi kin barni ban sake farin ciki ba,ban sake jin daɗin rayuwa ba,bani da abokin hira,Bani da abokin kuka, Hajiya zulfa'u da agololin ta sune kawai suke rayuwar farin ciki a gidan, abinci wannan da zan ci gagara ta yakeyi,ta sanya daddy ya sauya min makaranta mara kyau kuma mai nisa,ta sanya aka sallami driver na,da ƙafa nake zuwa nake dawowa,da na dawo kuma zata fara sanya Ni aikace-aikace,kamar su wanki,wankin mota,share-share da sauran su,sai na gama sannan idan an ga dama a bani abinci,don ma Allah ya sa mama ladi mai aiki tana fakar idanun su ta ɗibar min abincin

Haka na gudanar da rayuwa ta har na kammala primary,sai tace a tura Ni boarding Kar na dame su,haka Daddy ya kaini boarding,tun daga js 1 har ss3,daga nan kuma na samu da ƙyar ta yarda ya biya min kuɗi na karanci medicine a ATBU,shima rayuwar cikin makaranta nayi,don tafi min kwanciyar hankali da zaman lafiya,a wani zuwa weekend da nayi na farka cikin dare naji tana kiran suna na,da na leƙa ta window dai naga tana zuba wani ruwa akanta tana kiran suna na, hankali na ya tashi na tabbatar tsafi takeyi,don haka ko da wasa ban taɓa wasa adduoi ba dare da rana,a ɓangare ɗaya kuma na dage da karatu na wanda nakejin cewa shine gata na,ko ta dalilin shi wataran zan iya haɗuwa da ke

A wannan halin na ƙarasa karatu na na medicine mai wahala a yanayi mai matuƙar wahala,amma alhmdllh takardu na sukayi kyau,a satin da na karɓo takardu na ne ina kwance a ɗaki na sai ga ƙaramar ƴar ta tazo tace na zo na duba yayar ta ameera numfashin ta ne yake ƙoƙarin ɗaukewa,sam banyi tunanin mutanen basa kyautata min ba,iyakar abinda na sani shine profession ɗina,naje Ina ƙoƙarin duba matsalar sai ji nayi uwar ta rafka salati, wai ina ƙoƙarin haiƙewa ƴar ta,sai ga yarinyar ta miƙe tana mitstsika idanu wai bacci takeyi taji kamar an danne ta,abin ya bani mamaki nace ai salma ce tazo kira na tace ameera ba lafiya,salma ta zabga wani ihu tana faɗin"ita wallahi bata fito daga ɗakin ta ba tunda garin Allah ya waye sai yanzu,abin ya bani mamaki na kasa magana,sai ji nayi Daddy yana sauke min maruka hagu da dama,yana faɗin na gado uwa ta na zama mutumin banza,a nan ne naji bazan jure ba nace Ni uwa ta ba mutuniyar banza ce sai dai matar shi da gayyar agololin ta,nan ya hau Ni da duka tamkar ya samu ɓarawo,Ni kam ko ƙoƙarin kare kaina banyi ba sai da ya illata ni,ameera ta miƙe tana hawaye wai sai ta bar gidan tunda na kira ta da agola,buɗar bakin Daddy sai cewa yayi sai dai Ni na bar gidan ba ita ba,don ta fini Amfani,haka inaji ina gani na kama tattara dukkan kaya na zan bar gidan,sai ga Hajiya zulfa'u tazo tana murmushi tana faɗin"nayi ƙoƙarin jefe ka amma hakan bai ci tura ba,to da sauƙi dai tunda na jefe ubanka,kaima gashi ko sisi na batayi ciwon kai ba na kaɗa ka kamar yadda na kaɗa uwar ka, Allah raka taki gona"ban kalle ta ba itama bata damu ba tana gama bayanan ta ta juya ta bar wajen

Shine dalilin da ya sanya ni barin Bauchi na shigo Kano,ranar da nazo Kano a ranar Deeja ta buge Ni a mota, saboda tunanin yadda zanyi da kaina bai bani damar kallon gaba na ba,amma a ƙarshe hakan ya zame min alkhairi tunda gashi na dawo gare ki momy"ya ƙarashe hawaye na zubo masa

Kusan kowa a parlourn hawaye yakeyi, Deeja kamar zata shiɗe duk da kasancewar ta mara saurin kuka da dakiyar zuciya, a hankali momy Aysha ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"babu komai, ƙaddara ce, alhamdulillahi alaa kulli haalin,nayi farin ciki da rayuwar ka bata lalace ba, Allah yayi maka albarka"shi dai murmushi kawai yakeyi yana goge hawaye

Bayan ta nutsu tace"Imran lokacin da na bar gidan mahaifin ka na bar shi da ciki wata uku,ga abinda na haifa nan"ta nuna masa Ramlah wadda a lokacin zata kai 27-28 years

Murmushi yayi yana kallon Ramlah, Ramlah ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"yaya momy tana yawan bamu labarin ka,tana nuna mana hotunan ka,munyi missing dinka sosai,yana murmushi yace "nayi missing ɗin ku,amma yanzu alhamdulillahi"

Babu wanda ya kula da sanda Deeja ta zame ta fice daga falon,sai daga baya Imran ya kula,babu ɓata lokaci ya miƙe ya nufi garden din gidan inda suka saba zama suna hirar su,a can ya hango ta ta jingina kanta da kujerar da ta zauna ta lumshe idanu tana ajiyar zuciya,a hankali ya ƙarasa inda take zaune,ƙamshin turaren shi yasa ta buɗe idanu tana kallon shi, yayi murmushi yana faɗin"da tsoro zan baki ai,kuma na manta ashe sister ɗin tawa jaruma ce"

Itama murmushin tayi,ya samu waje ya zauna,ya ɗan yi shiru sannan ya fara magana

"Khadijah, I have no enough words da zanyi miki godiya,kinyi min abinda har abada banajin zan manta,kin cika min farin cikin da na rasa tun ina ɗan ƙaramin yaro,bani da bakin yi miki godiya,bani da abinda zan iya biyan ki,fata na Allah ya buɗa miki dukkan alkharin shi duniya da lahira,na gode sosai Deeja"

Deeja ta girgiza kai tace"wannan duk ya wuce ya Imran,yanzu tare zaku koma da momy?"

"A'a,a nan zan zauna,ko don aiki na,amma zan rinƙa kai mata ziyara"tayi murmushi tana faɗin"nima dai Allah yasa Abba ya barni nayi aikin nan,kowa yana aiki ban dani,Mima ma tace ta samu aiki,ga zainab,amma Ni daga ci sai kwanciya kamar wata saniya"ta ƙarasa tana yamutsa fuska

Imran ya fashe da dariya yana faɗin"kaji min mata,don kin samu kin zama ƴar hutu shine zaki yi mana iyayi?zan zuga Abba ya janye miki tallafi tunda daɗin yayi miki yawa"

Ta tura baki gaba tace"Ni da ya daina tura min tallafin ya bar ni nayi aiki nafi son haka,yanzu fa duk na zama malalaciya"ta ƙarashe kamar zatayi kuka

"Common ba wani malalaciya,ke fa jaruma ce,ko baki sani ba?"

"To amma ai rashin aiki zai saka experience ɗina na aiki na aiki ya gudu fa!"

"A haba!babu inda zashi,ki kwantar da hankalin ki, wataran ma Abba da kanshi zai yarda kiyi aiki ki daina saka damuwa a ranki,gata fa Abba yayi miki, common cheer up please!wannan fuskar ko kyau batayi miki ba"da haka ya sanya ta koma yadda take da

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 23

Momy Aysha ta so tafiya da Imran amma sai yayi mata bayanin aikin shi,kuma ma still baya son rabuwa da Deeja, saboda halaccin ta a gare shi,don haka momy Aysha ta bar shi a gidan tayi tafiyar ta Abuja da yaran ta

Shi kam Najeeb shirye-shiryen haɗa Imran da umaima sunyi nisa,don haka ya fara kiran umaiman ta rinƙa kawo musu ziyara,ya rinƙa gabatar da ita a wajen Imran,tun Imran baya damuwa har ya fara ba da kai,umaima fara ce ƙal, kyakkyawa sosai mai gashi har gadon baya,bata da ƙiba kwata-kwata amma ba ramammiya bace,tana da yawan fara'a da iya hira,ga ta da son gayu da kwalliya,ga iyayi,da wannan ta samu ta fara janye shi daga wajen Deeja,wadda shi mu'amalar su a abota ya ɗauke ta da ƴan'uwan taka,da babu soyayya a tsarin shi a yanzu,amma umaima ta tarwatsa komai

Najeeb ne ya rinƙa sukar Deeja a wajen Imran da dabara da wayo,don tuni ya fahimci Imran cewa bashi da wani wayo sosai,a hankali a hankali ya fara cin nasara,dama Najeeb ya kwaɓe shi kar ya kuskura ya bawa Deeja labarin umaima don zata iya raba su,ya nuna masa tun farko ba don Allah ta cece shi ba,ta cece shi ne don taga zai yi mata amfani,har ya ƙara da cewar mata irin su Deeja basa ɓata lokacin su wajen abinda bai shafe su ba,har da misalai,tabbas he is on point,don Deeja bata shiga shirgin da bai shafe ta ba,ko wajen al'ummar gidan bata cika zuwa ba sai wajen shi,yanzun ma takanyi

Please Login or Register in order to submit comment