Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka iso harabar makarantar. Ahalin yanzu Noor ta saba da irin kallon da ake binta dashi a duk lokacin data shigo makaranta, ba maza kadai ba har Mata. So dayawa mazaje nakawowa Noor tayin soyayyarsu amma kamar ma basu isheta kallo bane,batasan me ake nufi da soyayya ba dan agida Mama bata sake mata marar da har wani saurayi zaizo yace yanasonta ba. Lokacin datake gida maza dayawa suna zuwa gidan tambayar Noor amma Mama saita haqiqance akan babu wata budurwa agidan illa Moon.

Daidai wata mota mai azaban kyau ta danno kai cikin makarantar, gabadaya hankalin dalibai ya koma kan motan, so suke su gano wanene acikinta. Motace kirar Audi Q8 baka komai na motan baki ne harta glasses din, tayarsa ma baki ne,motarde ta hadu iya haduwa. Itama Noor hankalinta akan motan yake dan tunda take bata taba ganin mota mai azaban kyau haka ba, hala sabuwar fitowa ce, amma kuwa in haka ne toh duk mai motar ba karamin me kudi bane. Ahankali yabude murfin motar ya fito. Wow wow wow wow kawai dalibai ke fada kamar motar ambulance. Sanye yake cikin dark blue suit, yar cikinta kuma fara kal da tie dark blue. Takalmin kafarsa kirar Prada toms shima dark blue sosai yayi masa kyau. Bakin shades ne a idanunsa, fuskarnan as always murtuk babu wasa acikinta. Gashin kansa kwance yake luf akeyarsa se shining yake gwanin sha'awa, duk wacce ko wadda yazo wucewa ta gefensa wani irin kamshi mai sanyi yakeji. Tunda ya fito take kallonsa babu kiftawa, mamaki ne ya kama Noor lokacin da taga Nana tafito daga dayan side din mai zaman banza tana turo baki kamar yanzu aka gama mata fada. Yau kamanninsa yabace yakara wani irin kyau na musamman, azuciyar Noor tace"kodai saboda na dade ban gansa bane"? Dataga babu mai amsa mata kawai ta kawar da fuskarta zuwa wurin Nana dake takowa wurinsu. Shima Aryan tunda ya fito daga motarsa yake kallon Noor amma tunda bakin shade ne a idanunsa ba lallai mutum yasani ba. Take ma Nana baya yayi har inda su Noor suke tsaye itada yasmeen. Nana na karasowa suka rungumi juna itada Noor suna ihu irin yadda mata suka saba insuka hadu, shikuwa Ogan harararsu yayi ahankali ya furta" childishness", saida suka gama murnansu sannan Nana takalleshi tace" Ya Aryan bye" tama mance da fadar daya gama mata amota akan tana bata masa lokaci. Kallonsa Noor tayi ta gefen ido ta watsa masa wata uwar harara azatonta ba ita yake kallo ba harda murgude masa dan karamin bakinta. Shikuwa mamakin yarinyarnan yake, yarinya batako ganinsa da gashin ido, ko Nana bata isa ta kalli idonsa da zummar harara ba sai ga wata yar ficikar yarinya tana masa free if charge, lallai seyayi maganinta. Kwafa yayi ahankali yajuya ya shige motarsa yabasa wuta ya fice a makarantar.



Yau Abba ya canceling kowani schedule dinsa dan akwai wani abokinsa dazasu kai kudin sadakin dansa zuwa gidan yarinyar dazai aura. Bayan ya gama shiri yana zaune yana jiran call din abokinsa, ummi kuma tana hada masa coffee. Kirane ya shigo wayarsa ya daga ahankali yayi sallama Lamar me koyan magana(wannan mutumin shima A nefa kamar dansasai hegen miskilancin tsiya) adayan bangaren kuma Alhaji Saifullah yayi magana, bayan sun gama magana ya katse kiran. Ummi tace" dear wai ina zakune kaketa wannan uban saurin" murmushi Abba yayi yace" wlh sadakin dan saif ne Shareef zamu kai gidan yarinyar dazai aura" ummi tace "ikon Allah Shareef lokacin yayi, kai amma nayi murna, Allah nima yanuna min na Aryan dina" murmushi kawai Abba yayi yace ameen sannan yace mata tabar coffee din dan ana jiransa awaje. Har bakin kofar falo tarakasa sannan tajuyo tadawo ciki. Abba kuwa waje yafita dan bada motarsa zai tafi ba, motoci ne kusan biyar awaje, na tsakiyan Abba yashiga. Uncle saif yana ganinsa yasaki murmushi yabasa hannu sukayi musabaha sannan suka kama hanya zuwa gidan matar da shareef zai aura wadda itama a anan Abuja take da zama. Abakin gate din wani katon gida me kyau suka tsaya akayi horn sannan mai gadi ya wangale masu gate suka shiga. Sunsamu tarba mai kyau daga wurin iyayen yarinyar. Bayan an gama magana Uncle Saif yaciro rafar one thousand guda biyar yace " toh gashi nan dubu dari biyar ne, dubu Dari biyu na sadaki, sai kuma sauran kyauta ce nabawa 'yata" sosai sukaji dadin wannan kyautar dukda bawai basudashi bane amma dan tsantsar soyayyar da su iyayen shareef ke nunawa 'yartasu ne. Sunkai kusan awa biyu a gidan sannan suka fito. Ahanyar dawowansu Abba yakecewa Uncle saif" Saif wlh wata yarinya ce nida ummin yarannan muka gani kuma sosai muka yaba da halinta, shine dama nakeso ma nemawa 'dana Aryan aurenta" da mamaki uncle saif yace "toh babban magana wace yarinya kenan"? Abba ya sauke ajiyar yace " wata kawar Nana ce sunanta Noor" da sauri uncle saif yajuya ya kalli babban abokinnasa ya maimaita Kalmar Noor, Allah yasa abinda yake tunani ne yace" Noor? Tare suke karatu da Nana "? Uncle saif yakara jefowa Abba tambayar, Abba ma da mamaki yake kallon Uncle saif, gyada masa kai yayi alamar ehh. Murmushi ne ya subucewa Uncle saif yace" toh ai yata ce Noor din" mamaki da farinciki suka rufe Abba yace" kai haba, banason wasa yaranka ba biyu bane mata, Hanan da Hanifa" gyada kai uncle saif yayi yace"ehh, amma Noor itama amazaunin yace awurina tunda yarinyar yayar Jamila ce" hamdala Abba yayi sannan suka cigaba da tattaunawa da uncle saif akan yadda zasu nemi izini awurin Daddy. Haka kuwa suka shirya inda Uncle saif yace zeyiwa daddy magana duk ranan dayake free zasu tafi kano. Abakin gate din gidan Abba aka ajjesa sannan su uncle saif suka kama hangar gida, kowa na farinciki wannan hadin daza'ayi.



Shareef ne da Aryan zaune a office din Aryan din kowa na aiki a laptop dinsa. Can shareef yadago ya kalli Aryan yace" dude har yanzu bakayi maganin wannan mayaudarin cleaner din ba kardai yafe masa kayi" dago kansa yayi ya kalli shareef yace " jira nakeyi karshan watannan yazo za'abashi takardan sallamanshi tare da salary dinsa, harda yan control room dinnan gaba daya suma they're going, all of them" murmushi shareef yayi, akoda yaushe a Aryan na matuqar birgeshi, Sam baya tauye haqqin na kasa dashi, kome zaka masa insha Allahu bazakuyi rabuwar rashin mutunci dashi ba. Wayar Shareef ne ya fara kara, da murmushi afuskarsa yadau wayar, sunan my love ne ke yawo akan screen din wayar, daukawa yayi ya fice daga office din yana wani kashe murya, takaici ne ya kama Aryan yaja wani dogon tsaki yace" dan is kawai, meye amfanin wani kashe murya wa mace, salon ta raina ka kenan ko me" rufe system dinsa yayi yana ta jan tsaki. Can shareef ya shigo yana washe hakwara, kallonsa Aryan yayi ya kara Jan wani tsakin ya maida hankalinsa kan wayarsa yana latsawa. Shareef na zama yace" dude guess what" ko kallansa Aryan beyiba, murmushi shareef yayi yace" toh shikenan, bari na fada maka since you're bad in guessing, yau dinnan su Abba da daddyna suka kai kudin sadaki na gidan matata" ya kare maganan yana wani bude kafada irin shima ankusa zama miji dinnan. Da sauri Aryan ya dago kansa yace " wow congrats Allah yasa ayi damu" shareef yace"ameen Allah yasa a hada bikinmu rana daya" kamar ya sokawa Aryan mashi a kirjinsa ya wani watsa masa harara yaja dogon tsaki. Dariya kamar ya kashe shareef amma fa shi yanajin cewa nan bada jimawa za'awa Aryan aure dan kam su ummi sun gaji da ganinsa haka.


Normal time dinsu na tashi suka dawo gida. Kamar kullum yauma a gajiye suka dawo dan haka suna dawowa kowa ya wuce daki yayi wanka. Noor yanzu kam tasaba da kananan kaya, Anty Jamila tana siyowa dayawa taraba musu, yanzu ma haka data gama wanka bum short tasa da singlet ta kwanta akan gado tana maida gajiya. Su Hanan kuwa hirarsu sukeyi akan wani lecturer dinsu daya disgracing wata yarinya arniya data shigo masa aji da mini skirt. Ita karan kanta Noor saida ta dara saboda labarin abun dariya ne.

Acan falon uncle saif kuwa, duk yadda sukayi da Abba ya maida ma Anty Jamila, sosai taji dadin wannan hadin da ake sonyi dan Aryan namiji ne wadda ko wace mace ke burin samu a rayuwarta. Sun dade suna hira kafin su Noor suka shigo falon suka gaidasu suka fice zuwa dinning. Cornflakes kawai Noor tasha dan ba wani yunwa takeji ba.


Bari mu leka gefen su amarya Moon.

Moon yanzu anyi laushi, duk ta rame saboda jarabar Mahmud, dukya gama kwakwularta kullum ana abu daya, saukinta shine in ya fita aiki, haka zata kira Mama taita mata kuka ita wlh kasheta zeyi, haquri kawai Mama ke bata dan daddy ya riga yaja mata kunni karta sake tabawa Moon wani shawaran dazai affecting mijinta. Shiko ango Mahmud har wani fresh yakara yana shan romonshi iya son ranshi. Yau sati biyu kenan amma Moon ko tukunya bata taba daurawa akan gas wai zatayi abinci ba, to me zata girka in ba tafasa ruwa kawai zatayiba😂 Gida kam Mama tasamo mata me aiki tun bayan aurenta da sati daya. Kullum kwance take babu abinda takeyi sai In ango na nan shine batada hutu lols. Kullum ana aikin siyo mata abinci daga waje, wadda yanzu har Mahmud yafara zargin anya tama iya abincin kuwa(toh fa).


Lubna kam yanzu baki ya warke ankoma back to business dan wasu lokutan bama ta dawowa gida kuma mamannata bata nemanta danta san inda take. Sunma mance da batun wani Aryan yanzu, saima tsoron masa wani laifi dasuke. Anty Aisha yanzu ko ajikinta fushinda mahaifiyarta keyi da ita, wasu lokutan ma mancewa take da wata Dada aduniya(hmm lallai Anty Aisha Allah ya ganar dake).


Kamar yadda uncle saif yafadawa Abba haka kuwa ya kira Daddy yafada masa. Daddy bewani nuna damuwarsa akan hakan ba danyasan insha Allah yarsa bazata taba faduwa cikin mummunan hannu ba. Shiryawa sukayi akan ranan Saturday zasu tafi kano wurin daddyn. Bayan sun gama magana da Daddy uncle saif ya kira Abba ya sanar dashi yadda sukayi da Daddy, murna wurin Abba kamar me. Ummi kam ta kosa taji maganan me sukeyi dan tunda Abba yadawo dzu yaketa washe baki kamra ba shiba" dear dan Allah menene kafada mun" murmushi Abba yayi sannan yamaida mata duk yadda sukayi da uncle saif dakuma maganar zuwa kano wurin Daddy. Zakuso kuga murna awurin ummi, hamdala sosai tadinga yi tana godewa Allah.



Yau be dawo gida da wuri ba saida yayi sallan isha sannan ya shigo. Su ummi yasamu a dinning suna dinner. Gaidasu yayi yawuce dakinsa ya watsa ruwa. Kayan bacci me kyau yasa fari kal with touch of blue aciki silk, irin dogon wando me rigan nanne, rigan nada dogon hannu dakuma buttons Jere a gabansa. Kamshi kawai yake bazawa mai sanyi, kai Aryan yayi 100% komai nasa cikin salo yake yinsa Masha Allah. Falonsa yafito yasamu anriga ankawo masa abincinsa, fruit kawai yasha beko kalli abincin ba. TV ya kunna ya fara kallon labarai har kusan karfe goma sannan ya tashi ya kashe komai afalon ya wuce daki.


Wanka tayi ta fito da towel babba yawuce guiwarta tana tsane ruwan kanta. Bayan ta gama shiri cikin kayan baccinta doguwar riga medan kauri ta zauna abakin gado tana latsa wayarta. Hanan tace" kai bakusan menene ba yau naji Daddy yana gayawa Mommy sun kai kudin sadakin ya shareef yau da safe" murna sosai sukayi har hanifa tafitar da hotunan wasu atamfofi waisu fara zaban anko dazasuyi harda shagalin dazasuyi, itakuwa Noor kallonsu kawai take dan ita bawata fan din irin shagalgalunnan bane, kodan Mama bata zuwa da itane yasa oho.


Agurguje


Yadda su Abba suka tsara, yau Saturday suka kama hanyan kano. Agidan Abba suka sauka, bawani tarba sosai Mama tamusu ba, Uncle saif beyi mamakin hakan ba amma Abba kam yayi danshi yadauka itacema mahaifiyar Noor sai bayan u e saif yafada masa cewa ba ita bace mahaifiyarta ta dade da rasuwa. Bayan sun gama gaisawa da Daddy da yanuwansa Alhaji sani da kuma Kawu Mansur sannan aka fara magana. Daddy beyi wani ja dasu ba kuma ya amince da wannan hadin da akayi. Sosai sukayi farinciki da yadda Daddy ya amshi kokon baransu, a wurin Daddy yace asa rana kawai basai an bata lokacin ba, haka kuwa akayi inda aka tsayar da ranan bikin lokacin daya dana Shareef( toh fa jama'a karfa maganan shareef yazo gsky). Alhaji jibril kanin Abba wadda tare suka zo shiya rufe musu taron da addu'a. Sai karfe biyu suka kamo hanyan dawowa Abuja.


Yau tunda Noor ta tashi takejin faduwar gaba kamar wani abu na shirin faruwa da ita. Sam ta wuni batada walwala ko kadan. Anty Jamila ce kawai ta lura da hakan harta bata tausayi dan kamar kuwa Noor din tasan wani abunne ke shirin faruwa gagarumi. Anty Jamila bata fada mata akan maganan ba dan sun shirya da uncle saif sai ana sati daya da bikin zasu sanar da ita dansunga alaman Noor bazata yarda da wannan auran ba duba da yadda take bala'in son karatu.


Da daddare Abba yasa Nana ta kira masa Aryan. A kofar falonsa tayi sallama amma babu kowa, abakin kofar dakinsa ta tsaya sannan tayi knocking, zaune yake akan study chair dinsa yana karanta wani littafin daya danganci engineering. Ahankali ya tako har bakin kofan sannan ya bude, Nana yagani a tsaye, bayan ta fada masa sakon Abba tafice, shikuma ya koma ya sa jallabiya dan dama 3qtr ne da singlet ajikinsa ya fice zuwa falon Abba. Ya na zuwa yasamu daga Abba sai ummi Afalon suna hira kadan kadan. Zama yayi akan one seater din dake facing na Abba yace" Abba gani" gyaran murya Abba yayi sannan yafara magana" Aryan mune muka haifeka, kuma muna da kowani right din zaba maka abinda mukaga ya dace dakai, kaiba yaro bane shekarunka gaba sukeyi ba baya ba, kana neman 31 kenan amma gashi shareef da yake bayanka har ya fidda mata zeyi auransa kaikuma shiru, toh dan haka inaso na sanar dakai cewa munmaka mata kuma insha Allah za'a daura auranku rana daya dana Shareef dan har mun kai sadakinka" tunda Abba yafara magana kan Aryan ke kasa amma jin an ambaci cewa anmasa mata nan da nan idanunsa suka rikide suka zama ja jazur. Wani irin juyi yaji kansa na masa, babu damar yayi fushi da iyayensa amma tabbas daba subane suka yanke masa wannan hukuncin da wadda yayi hakan yaga kololuwar bacin ransa. Abba ne yace" kai nake jira kamin magana" da kyar ya dago kansa ahankali kamar bayaso yace" shikenan, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" murmushin manya Abba yayi dan ya gano tsananin firgici a fuskar Aryan. Ahaka yamike yafara tafiya har yana hada hanya saboda wani irin juyi da kansa kemasa. Ummi takalli Abba tace" kaga abinda nagani akwayar idanunsa kuwa"? Babu abinda Abba yace kawai mikewa yayi ya shige dakinsa, ummi tasauke ajiyar zuciya tace"Allah yasa mu dace".


Aryan na shiga dakinsa ya fada kan gado yana sauke wani irin ajiyar zuciya. Inama zai iya kuka da ba makawa kuka me rai da lfy zeyi harda majina. Meyasane su Abba da ummi sukeson matsa masa akan abinda bayaso, Shifa be taba fadamusu cewa yana buqatar wata arayuwarsa ba. Yanzu kenan responsibility din wata zai dawo kansa? Kansa ya rinka jujjuyawa akan gadon kamar zai cireta. Tabbas wannan yarinyar da tayi kuskuren amincewa zata aureshi tayi babban kuskure, batasan wanene Aryan ba sunansa kawai takeji, amma tabbas seya shayar da ita ruwan mamaki. Kwafa yayi ya mike yana tangal tangal ya shige bayi. Alwala yayi ya fito ya tada sallah. Addu'a sosai yayi kan Allah yakawo masa sauki a wannan al'amarin. Yana idarwa ya koma gadonsa ya kwanta yanata tunani, yanzu ya zeyi ya fara zama da mace under the same roof a matsayin ma'aurata. Haka ya dade yana tunani har bacci barawo yayi awon gaba dashi.



COMMENT AND SHARE




REEMAH✍️
10/12/23, 6:21 AM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼



REEMAH



PG 25_ 26



Yau Sunday, su Noor basu farka ba sai karfe tara na safe bayan sun gama hada breakfast tunda yau sune da girki, lokacin su Anty Jamila harsunma gama breakfast suma sun koma dakunansu. Wanka tayi ta shirya cikin wata atamfa riga da skirt blue and white ya zauna das das ajikinta kamar ajikinnata aka dinka shi. Daurin ture kaga tsiya tayi sannan jelar gashinta kuma yana reto agadon bayanta. Bayan suma sun kammala breakfast dinsu suka zauna afalo suna hira, hiran dai har yanzu akan shagalin bikin daza'ayine. Itadai Noor kallonsu kawai takeyi amma ko uffam bataceba, tama rasa meke damunta, tun jiya takejin kirjinta na dukan uku uku gabanta na yawan faduwa. Tayi kwana biyu batayi magana da daddynta ba, dan tun dawowarsu daga kano batakara kiransa ba shima kuma be kirata ba saboda gudun karta fashe masa da kukanta na fama. Wayarta ta dauka tayi dialling numbersa, bugu uku ya dauka kamar dama jiran kirannata yakeyi, ajiyar zuciya ta sauke tace" Daddy " murmushi yayi mai sanyi yace" shalele, yakike, shine kika share daddynki har na wannan tsawon lokacin ko"? Murmushin yake kawai Noor tayi tace" Daddy kaine kadai ke gane damuta ako wani lokaci so bazan iya boye maka komai ba, Daddy wlh tun jiya nakejin faduwar gaba kuma na rasa dalilin haka" tafada kamar zatayi kuka. Da damuwa a fuskar Daddy yace"shalele kina shan magungunan ki kuwa"? Inba yanzu da Daddy yatunatar da ita ba tama mance akwai wani maganin daya kamata tana sha. Kamar Daddy ya harbo jirginta yace"Noor dan Allah kikula min da kanki , bazan iya losing wani acikin 'ya'yana kuma ba, kibarni da zafin mutuwar suhail da Amminki plss" Noor batasan lokacin da ta fashe da kuka ba jin daddy ya ambaci suna suhail da Amminki, Allah sarki bawan Allah bemasan cewa matarsa ta gida itace sanadiyyar rashin matarsa da kuma dansa ba. Kuka take rerawa sosai wadda yayi sanadiyyar shigowarsu Anty Jamila falo daga bedroom dinsu itada Uncle saif. Daddy jin haka ya katse wayar dan kukannata bame tsayawa bane. Su Hanan ma suka matso kusa da ita dansuna falone atare lokacin data kira daddyn. Rarrashinta sukeyi amma kamar kara ingizata sukeyi, wani irin sharp pain ne taji a zuciyarta me wuyan fassarawa har ya kaiga tana shidewa kamar zata suma, da sauri uncle saif ya dauke ta yayi hanyar mota da ita su Hanan suka take masa baya, Anty Jamila sai kuka takeyi Ya Shareef na aikin rarrashi. Babu bata lokaci Uncle saif yakaita National hospital dan asibitin dayafi kusa dasu kenan. Suna zuwa aka turata a gado me taya sai emergency, da kyar suka iya shawo kan al'amarin dan harda oxygen suka Samata. Uncle saif ne ya kira Daddy ya sanar dashi halin da Noor keciki, sosai hankalinsa yatashi amma bazai iya zuwa ba, baze iya jure ganin Noor dinsa a wannan halin ba. Su hanifa suna waje sai ruskan kuka sukeyi suna rungume da juna. Doctor Awwal ne ya fito ya ce uncle saif yabishi office dinsa. Suna shiga suka zauna uncle saif najiran yaji me Doctor zaifada. Gyaran murya doctor Awwal yayi sannan yace " a gaskiya wannan yarinyar tana cikin mawuyacin hali, domin kuwa damuwa ne yamata yawa wadda yakaiga zuciyarta barazanar bugawa, amma don't worry she's out of danger, saidai kuma ina tunanin wannan ciwon ba yau ya fara ba, halan wasa takeyi da maganinta" wani irin zufa ne ya keto wa uncle saif yace" hakane doctor kuma muma munada laifi, da mahaifiyarta ce ke bata maganin, saita bukaci abata maganin kawai zatana shaa awurinta, damaa mun sani bamu bata ba" ajiyar zuciya kawai doctor yayi yace" karka damu zan kara rubuta mata wani maganin, insha Allah inhar tayi kokari tasha to zata samu sauki" godiya uncle saif yayi sannan ya karbi takardan prescription din magungunan ya fice daga office din. Har I zuwa lokacin Noor bata farka ba, wani daki aka kaita daga Anty jamila saisu Hanan adakin kowa ya zauna jigum jigum sunyi tagumi suna tausayawa Noor da halin datake ciki. Wayar Noor dake hannunsa Hanifa ne ya dau haske alamar kira, daukawa tayi amma batace komai ba, Nana daga dayan bangaren tace" haba Noor where did you keep your phone, inata kiranki amma baki daukaba" hanifa tace" Nana nice, muna hospital da Noor an admitting dinta" arazane Nana ta mike tace "what? Meyasameta,"? Duk abunda yafaru hanifa ta fadawa Nana. Ummi jin Noor na asibiti dukta rude dan dama suna zaune tare da Nana ne adakinta. " Nana menene, meyasami Noor" ummi tafada cikin tsantsan tashin hankali, duk yadda hanifa ta fada mata ta maidawa ummi, cikin hanzari ummi tace su shirya sutafi asibitin. Babu bata lokaci harda Dada aka shirya zuwa duba kawallinta. Driver Nana ta kira da sauri ya karaso sannan yajasu suka tafi.


*******
Aryan kuwa tunda yadawo daga gym din gidan yake bacci be tashi farkawa ba sai karfe sha biyun rana. Wanka yayi yasanya wani pencil jeans da white t shirt sannan yadau snicker fari kal yasanya. Sosai yayi kyau, turarensa masu sanyin kamshi ya fesa sannan ya dau p cap dinsa yasanya akai. Wayoyinsa da makullin motarsa ya kwashe yafice daga dakin cikin takunsa metafiya da imanin mata. Part din ummi ya nufa amma ga mamakinsa basunan dukkansu, wani ma'aikacin gidan ya tambaya yace masa yaji suna cewa zasu tafi asibiti. Mamaki ne ya kamashi to wanene ba lafiya. Ahankali ya taka ya fice daga falon ya shige motarsa yafice daga gidan.


*******
Moon ne zaune a falo karfe sha biyu da kwata na rana tana latsa wayarta sai faman dariya takeyi kamar tababbiya. Mahmud ne ya shigo falon yasameta a wannan halin. Zama yayi yace" baby, yau abokai na zasuzo pls inaso kimusu wani hadaddiyar girki, kinji" hararan takaici ta watsa masa kayi tsaki tacigaba da danna wayarta, mamaki ne ya kama Mahmud, me yarinyarnan take nufi dashi, kodai saboda ya daga mata kafa ne Yau satinta kusan uku agidannan amma kulllum yana hanyar siyan abinci? Tsawa ya dakamata yace"what nonsense Moon, me kike nufi da tsakin da kika min, nifa mijinki ne, kodan na daga miki kafa kina duk abinda kikaga dama shine zai baki right din wulakanta ni"? Mikewa Moon tayi ta daga masa hannu alaman ya dakata tace" kaga malam, ba baiwa aka kawo makaba, ni ko a gidanmu mamana bata bari na dau tsinke bare har kai kazo kanacewa inyiwa abokanka girki, ni ban girka abinda zanci ba shine zan girkawa wasu kattin mazan? Mamaki,takaici duk sune suka mamaye Mahmud. Lallai akwai sauran aiki agabansa, anya soyayyar daya kewa Moon, is it really worth all the insult? Girgiza kai kawai yayi ya fice daga gidan. Tsaki Moon tayi ta gyara zamanta tana surutai marasa kan gado.


******
Tunda su ummi sukaje asibitin Noor bata farka ba sai kusan maghrib kafin ta farka. Kuka sosai takeyi tana kiran Amminta, ta matukar bawa mutanin dakin tausayi, ummi tayi tagumi sai kallon Noor takeyi ba kiftawa azuciyarta tana cewa" tabbas bayan aurensu Noor da Aryan yakamata tabata kulawa sosai a matsayin wacce ta rasa soyayyar mahaifiyarta tun tana yar shekara goma. Da kyar su Hanan suka rarrasheta tayi shiru, tea me kauri Anty Jamila tahada mata tabata, bayan tasha kuma aka bata magani shima tasha ammafa da kyar. Bayan isha doctor Awwal yabata sallama tunda jikinnata yasamu sauki sosai. Tare suka fita daga asibitin tare da su ummi kafin kowa yadau hanyarsa zuwa gidansu.


*******
Aryan bedawo gida ba sai 9pm. Afalo yasamu su ummi suna dan taba hira. Zama yayi ya gaidasu, Dada tace" dannan tunda safe rabona da saka ka a ido, gashi kawalli na ba lafiya shine mukaje asibiti sai dazu muka dawo" shi Aryan bemasan wacece kawallin Dada ba dan haka gyada kai kawai yayi ya mike yabar falon dan damuwarsa ma tafi takowa haka yake gani. Yana shiga daki yazauna abakin gado yadafe kansa, zuciyarsa wani irin kuna yakeyi masa, bakin ciki duk ya mamayesa. Shifa haryanzu

Please Login or Register in order to submit comment