Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an kashe mata dauri mai step step, ga gold jewelry din da Aryan ya siya mata ta sanya yayi kyau, babies ma sunsha kwalliya cikin kaya iri daya white and gold colour na baby boys. Kowa na santin yaran amma ba'a bari ana daukansu ana jagwal gwala su, suna kwance cikin baby bed dinsu duk mai son ganinsu zai zo ya tsaya ya kallesu ya dan shafa su shikenan. Anty ounaisa ce ta shigo dakin hannunta dauke da wani golden tray an rufeshi da gold linen. Ajewa tayi gaban Noor, sannan ta dauko twins din ta daura mata saman cinyarta, bude tray din tayi ta fidda Ajwa(dabino ne da ake samu agarin Makkah da madina), sai ruwan zamzam, sai wani dan kwalban turare mai hegen kyau kana ganinsa kasan ba karamin kudi gareshi ba, sai kuma alkyabba uban ubansu white and golden colour da takalman jarirai guda biyu, suma golden colours sunsha ado.kamar na sarauta, cup ta dauko ta tsiyaya tabawa Noor ta shanye tas sannan tabata ajwan shima ta cinye shi, turaren ta dauko ta mikawa Noor tace ta fesawa yaranta, batayi musu ba ta fesa musu nan da nan dakin ya hade da kamshin turaren saiyabada wani irin kamilin kamshi mai sanyin shaka, takalman jariran aka sanya musu akafa saiya tafi da kayan dake jikinsu, alkyabban Anty ounaisa ta dauko sannan ta ratayawa Noor bayan ta kwashe yaran daga cinyarta. Masha Allah tabarakallah, saiga Noor tafito kamar wata matan sarkin saudiyya, tayi hadu sosai sosai. Mikawa Hanan da Hanifa yaran Anty ounaisa tayi sannan tace subi Noor abaya su sauko kasa wurin jama'a za'ayi hoto. Haka kuwa akayi, kowa na zaune a babban falon kasa ana hira ana dan motsa baki da kayan ciye ciye, tunda suka ji karan takalma ana saukowa ahankali, idanun kowa ya koma kansu, Masha Allah Masha Allah kawai kakeji afalon, wasu kuma suna kyasawa musamman yan matan dake falon yaran abokan Abba dasu uncle saif. Tafito kamar shining star tayi fice cikinsu, babu wadda ya kai kwatan kwacin haduwar datayi,yasmeen na bayanta tana gyara mata alkyabbar, su Hanan kuma suna bayan yasmeen suna rikeda babies. Har suka karasa saukowa babu wadda ya kyafta sai kallon su ake. Ammi dake zaune kujeran gefe ta kafe Noor da ido kawai taji hawaye nabin gefen fuskarta, yau Allah yacika mata burinta daya barta da ranta hartaga wannan rana. Yau gata ga jikokinta, Allah sarki suhail dinta inama yana raye, taso yaronnan kamar me saboda shi kadai Allah yabata namiji. Sai da tabi kowa dake zaune afalon manya ta gashshesu. Kafin aka mike aka take mata baya zuwa harabar gidan wadda yasha decorations da balloons masu kyau. Mazaje suna waje ana hira, can na hango baban jego tareda Ya Shareef suna hira. Tunda yaga sanyin idaniyarsa yarasa natsuwarsa, har wani rufewa Muhsin ido yake kar agane masa mata. Buge hannunsa muhsin yayi yana tabe baki,shi dakeda Nana mezaiyi da second hand din Aryan, bugu Aryan yakai masa shikuma ya kauce yana dariya. Itama kallonsa takeyi, ya hadu sosai shima sanye yake da alkyabbar irin nata, ga kuma shadda fari irin nata shima yasha aikin golden zare, takalmin kafarsa da hulan kansa kadai abun kallo ne. Sun shagala wurin kallon junansu, ahankali yake takowa har gabanta, bude mata hannunsa yayi alamar ta hugging dinshi, ba musu kuwa ta karaso jikinsa ta kwanta luff, tare suka sauke ajiyar zuciya, Aryan harda wani lumshe ido ya furta "ALHAMDULILLAH YA RABB". Kowa baki galala ake kallonsu, ko irin nauyin dumbin mutanen dake wurin basuji kunyarsu ba, daga sama sukaji muryar Dada tana cewa" ahap ai in wannan ne kar Ku wani ji mamaki, fiye da haka ma sai suyi, kunma gode rasa kunyar bai sumbaceta ba" ta karasa maganar tana jifan Aryan da harara, shi hankalinsa ma ba'a kanta yake ba. Anty ounaisa ce tayi magana" kai Aryan banason rashin kunya, kai ko nauyin mu baka ji dalla saketa mugani" turo baki yayi kamar karamin yaro da aka raba da bakin nono ya dan saketa amma still suna manne da juna, abinda yayi ba karamin burge yan matan dake wurin yayi ba, saisukaji inama inama sune. Allah sarki har na tausaya muku in wata acikinku tashiga hannun boss Noor😂😂

Inda aka tanada na zaman iyayen babies suka zauna sannan aka miko musu babies din, hoto aka shiga daukansu kit kit kit kamar ba gobe, kowa na zuwa adaukeshi hoto taredasu yadda kasan celebrities. Masu abinci kala kala aka gayyato,inda aka dafa both local and continental dishes kowa yaci yasha abun sai son barka. Matsowa Aryan yayi kusada kunnin Noor yayi mata kus kus aciki, saigani nayi tayi murmushi da alama wani abu yafada mata wadda yayi mata dadi sosai. Mc na cikin magana akan iyayen babies kawai mukaji dirowar motoci acan compound din gidan inda motoci suka parking. Yadda suke shigowa gidan saika dauka yan gudun hijira ne suka gudo daga hannun kidnappers. Ban sha mamaki ba dannan san su waye babu shakka yan gidan MIJIN TACE NE. Aikuwa ban gama rufe baki ba saiga su ANTY ASHANTY DA TAWAGARTA sun kuso kai, sunci anko ansha kwalliya kamar za'aje dinner party😜, can saiga MOM SANI ITAMA DA BATALIYARTA kowacce acikinsu tasha no red skirt(no respect/ google)😂😂, su AMMEY LAYLA su Anty yusrah ma da su Mrs Isa duk sun zo, sauran mutan gidan MIJIN TACE MA na hangosu ana dambe da security wai sai lallai anbarsu sun shigo da kulolin abincin dasukayiwa Noor niki niki kamar za'a shekara anaci😂. Dafe goshi Aryan yayi ya ce" kai Allah sun iso kenan, yanzu zasu hana mutane saqat" murmushi Noor tayi kawai tana kallonsu, can kaji DJ yasanya wakar BUGA na kiss Daniel, su Mom sani harda kwasan shoki ana shigowa fili, Anty Ayshu da Ammey layla sun kame kan high table( special guest of honour)😂.

Su Mrs Isa kuwa saida aka kwasa da Dada dan dama bawani shiri suke ba, matar tacika sa ido dan kawai taga Mrs Isa da dan atemaki wadanta( high heel) shikenan tahanata saqat wai tayi hankali kar ta gurde kafa😂. Kowa yaci yasha anyi rawa an gode Allah. Sai ana gab da ganawa baban jego ya amshi mike sannan ya yafara magana" NUWAIRA, NOORIE!!! SHE IS THE BEST THING THAT HAS EVER HAPPENED TO ME, SHE GAVE ME ETERNAL HAPPINESS, ITACE JIGON RAYUWATA, TABANI ABINDA KOWANI DA NAMIJI YAKE BURIN SAMU DAGA MATARSA WATO 'YA'YA, I DON'T KNOW HOW TO EXPREESS MY PROFOUND GRATITUSE TO RABBIS SAMAWATI FOR THE GIFT OF NUWAIRA, BUT SURELY DO I KNOW THAT BAZAN TABA BARINTA TA KASKANTA ARAYUWA BA, I PROMISE TO BE HER SOULMATE FROM NOW TILL THE HEREAFTER, THANK YOU SO MUCH UMMU MUBIN WA MUNEER" ko ina ya kaure da clapping di mutane, sunan yaran ya burge mafi yawan mutanen wurin, sannan kuma tsarinsa dayayi kafin ya fadi sunan yaran shiyakarawa abun armashi. Noor harda hawayenta, babu abinda zata cewa Allah face ta kara gode masa, ga iyayenta dukkansu biyu araye, ga kuma mijinta da 'ya'yanta, what other Ni'ma of her Lord is she to deny. Sai bayan sallan asr aka fara watsewa bayan an raba souvenirs nagani na fada babu wadda aka banbanta tsakanin mai kudi da kuma mai karamin hali. Aryan yayi kokari saidai mice Allah yabar dankom kauna tsakaninsada Noor dinsa.

Mutanena mutanin arziki FANS DIN MIJIN TACE,nagode sosai da zuwanku wannan taro, Noor da Aryan harda babies dinku duk suna godiya. Sai muce Allah ya raya mana MUBIN DA MUNEER.

Yau akayi sunan yaron Lubna, dan karamin taro akayi, mutanen gidan kadai sukayi shagalinsu, inda yaro yaci sunan Baffa aka sanya masa Muhammad amma Lubna tace saidai akirasa da little Aryan saboda ya dau halin mai sunan kar ya dau halinta(Allah sarki),daddynta yayi mata kaya daidai gwargwado. Duk yadda daddynta yayi kokarin gano inda sadiqboii yashiga ankasa ganosa, daga karshe ma labari ya iskesu ai baya kasar, bayan yayiwa wata yarinyar Governor din Niger ciki ya gudu. Sosai Lubna tayi kuka, lallai ya cuceta daga ita har dan data Haifa, shikenan rayuwarta ya zo karshe, ta rasa duk wani farin ciki da mace keji. Hattara yan mata, wlh karku taba bari wani saurayi ya yaudareku da dadin baki yace wani inbakeba sai rijiya, toh wlh gara ya fada rijiyar than ya gurbata rayuwarki, kece da asara bashiba. Kuma wlh muddin kika bari wani namiji wadda ba muharraminkiba ya dandani zumarki, toh kisawa ranki kin gama yawo kawai, amma babu namijin dazai aureki sannan kuma ya zauna dake cikin dadin rai,kullum zai rika zarginki ne musamman in ya gane ba budurwa ya aura ba koda kuwa kin daina aikata wannan mummunan zunubin. Maza da kuke ganinsu, babu wadda yakai namiji dadin baki, namiji zai iya kaskantar da kansa dan kawai yasamu abinda yakeso daga wurinki, amma wasunmu sai su dauka aishine namijin kwarai wadda zai iya sadaukar da komai akanki, hmmmm my sister day there dey play, yana samu guduwa zaiyi yabarki da abun kunya da dacin rai. Mu dage da addu'a sannan kuma mu kame kanmu da mutuncinmu. Matan yanzu, sai kaga mace tasa kaya zuwa wurin wani event, amma marabarta da tsirara kadan ne, toh Ku fadamin yaza'ayi wani katon banza bazai ganki yayi sha'awarki ba. Ku lullube jikinku wa mazajenku shine bayani. Allah yasa mu dace. Ameen


*************
Izuwa yanzu sofiyya taji saukin laulayinta, yanzu tana yin komai dakanta ba kamar da ba da Mahmud keyi mata komai, wasu lokutan har Satan hanya yakeyi daga gidan Moon zuwa wurinta dan kawai wani dawainiya nata. Koda moon tagane saita yi kokarin danne abun azuciyarta, yanzu ta fahimci haquri shine kawai zai zaunar da ita lafiya agidan mijinta. Babu wani abinda zatayi dazai hanashi zuwa wurin sofiyya ranan girkin ita Moon din. Fatanta yanzu kawai shine Allah itama ya bata nata cikin kuma mai albarka. Ta sawa kanta yin azumin ranan litinin da alhamis Indai Mahmud baya gidanta. Sosai takoma ga Allah tana rokonsa ya azurtata da ciki kodan fita daga wannan halin kuncin datake ciki. Shima Mahmud yana iya kokarinsa wurin ganin ya yi adalci tsakaninsu amma still hakan ya kasa saboda zumudin samun baby dayake, bawai ya daina son Moon bane, infact itace first love dinsa, kawai dai yana tsoron yakara rasa wannan na cikin sofiyya ne shiyasa yake haka.


************
Gyara na musamman Ammi takeyiwa Noor cikin da bai, yau sati daya kenan bayan suna, ga yara sai uban tsotso kuma Baby exclusive sukeyi dan doctors sun shawarceta akan tabasu nono na watanni shida cifcif kafin tafara basu wani abu daban. Daga ita har yaran sunyi jiki sunyi fresh kamar awanke hannu kafin atabasu, kammaninsu da babansu sai kara fitowa yake. Kowani ranan Allah Aryan agidan yake wuni yaita wasa da yaransa, ko da yamma yadawo daga office baya tafiya gida sai yazo wurin babynsa yaga lafiyarsu. Ba karamin jin jiki yake ba Allah ma yasani, har wani dan rama yayi amma ba sosai ba, kullum yana aikin shan lemun tsami just to calm him down, wasu lokutan ma Allah ya taimaka yana waya da Noor tana dan taimaka masa da daddare ya sauke nauyin mara kafin yasamu yayi bacci.

Acan gidan Ummi kuwa su Anty ounaisa basu tafi ba har saida aka tsaida ranan auren muhsin da Nana, ya addabi rayuwarsu wai saidai ayiwa uncle magana, saida iyayensa maza suka zo tun daga Saudi akayi magana sannan suka koma can tare. Ranan dazasu koma ba karamin kyauta muhsin yayiwa Nana ba, waya sabuwa dal ya siya mata kirar iPhone 15 pro max, ga kuma dinbin kudin daya girgiza account dinta dashi. Su mazan Saudi they believe in pampering matarsu, ba kamar wasu mazan mu na Nigeria ba, talatu bude kafanki kawai sukasani🙈🙈😂😂. Da kyar ya yarda ma yabisu aranan, dan wani maganan da Nana ta fada masa kadan ya rage ya zautar dashi, hegiyan kuwa rugawa tayi ta koma dakinta bata fito ba saida taji karar motocinsu ya bar gidan. Allah kadai yasan yadda suke son junansu.


Yau cib cib Noor ta cika kwana arba'in kuma yau take shirin komawa gidanta. Zumudi daga ita har Aryan. Ranan bai tafi aiki ba saida yasa aka gyara ko ina da ina na gidan, dama tun last week aka canza paint din gidan da kuma furnitures da kayan kitchen, new bed set aka sawa Noor adakinta kamar na sarauniya, shima ya canza nasa. Komai yayi kyau sosai, dakin twins dama tuni ashirye yake dan abubuwa kadan kawai aka canza. Bayan sallan isha'i ya ci wanka cikin kananan kaya, jeans da T-shirt sai pcap da snicker masu kyau, wankan black and white yayi. Motarsa Gwagon baka ya dauka straight sai gidan Ammi. Acan kuwa tuni Noor tagama shirya jariranta da ita kanta sai zuba kamshi sukeyi, yau wankan na abaya ne, wata pink colour abaya mai zip tun daga sama har kasa yasha aikin stones sai walwali yake, masha Allah. Ammi da sunaina duk jikinsunyayi sanyi kamar karta tafi amma ita Allah Allah ma take kamar ana yanka namanta agidan. Horn dinsa sukaji abakin gate, da sauri Noor ta dau mayafinta da jakarta tabarwa Ammi da sunaina yaran su sauko dasu. Murmushi kawai Ammi tayi ta girgiza kai, Noor case, wannan irin soyayya har ina.

A bakin kofa falo taci karo dashi shima yana shigowa, da sauri tafada jikinsa tana sakin ajiyar zuciya, hannunsa yadaura saman waist dinta ya matso ta cikin jikinsa, zuwansu Ammi ne yasa suka rabu da juna. Gaida Ammi yayi yana Sosa keyarsa, sunaina ma ta gaida shi, suna mutunci da yarinyar sosai da akwai ta da girmama na gaba da ita, gashi ta iya zuba surutu harma tafi Noor, tanada son wasa kuma tana sakewa da mutum da wuri kuma ba karamin damun Ammi yakeyi ba, from her experience. Basu bata lokaci agidan ba suka sallamesu sannan suka wuce da babies din su cikin mota. Baby seats ne masu kyau guda biyu abayn motar suka shimfida kowa anasa sannan ya zagaya ya bude mata kofar mota ta shiga yabasu zuwa gidansu. Tundaga bakin gate Noor ta sensing cewa anyi gyara agidan, aikuwa kamar tasani, suna shiga sai da ta bude baki, so goma wannan kayan sunfi wancan tsofaffin, yana tsaye abayanta yana jiran ganin reaction dinta,aiko da sauri ta juyo ta karbi mubin dake hannunsa ta hada da muneer dake hannunta ta wuce daki dasu, bai motsa ba yana tsaye awurin shidai baiga canjin ayanayin fuskar ta ba kenan kayan basuyi mata ba? Ai in hakane da sauri zaisa acanza mata wasu. Yana wannan tunanin yaganta agabansa kamar anjefota saboda gudu tayi zuwa inda yake, hayewa tayi saman jikinsa sosai ta manne masa, kiss tashiga basa ta ko ina ba kakkautawa, wannan lamari ba karamin dadi yayiwa Aryan ba,ashe hanyar nuna godiyarta kenan. Dayaga tsayuwa bazai fishesu ba kawai ya dauketa da kyau zuwa bedroom dinsa, kan gado ga shimfida ta shima ya haye. Hot kisses suka shiga bawa Juna kamar zasu cinye bakinsu, before you know it sun fita a hayyacinsu musamman Aryan wadda ya dade yana burin ganin wannan ranar. A zafafe ya rabata da kayan jikinta shima ya tube nasa aka fara gashi, wannan daren shi ake kira LA hot, sun yi kusan round uku kafin suka sarara wa junansu,tare sukayi wanka suka shirya cikin kayan bacci. Saida suka koma dakin Noor suka dauko yaran suka canza musu kaya zuwana bacci, kafin suka kwanta tare, sun manne da juna kamar karsu rabu, yara kuma na can kan gadonsu wadda ke dakin Aryan. Sun makara sallan asuba. Bayan sun idar suka kara komawa bacci gajiya.


Yau yakama Saturday week end, bayan tafiyan Noor da sati daya kenan. Daddy yadawo daga tafiyarsa dayayi zuwa turkey inda yake aiki, yana dawowa Ammi tasa masa pressure akan Mama. Dama wannan karon da karfinsa yadawo na kawo karshen wannan maganan shiyasa bai musa mata ba. Booking jirgi yayi wa Mama sannan yasa ta zo Abuja akwai babban taro karramawarsa, bata kawo komai ranta ba, ta shirya tana jin dadin wannan karramawarbda Daddy yayi mata. Har kiran danginta take tana fada musu cewa for the first time Daddy ya shirya tafiya da ita babban taron karramawa a Abuja. Da yamma jirginsu ya sauka agarin Abuja, driver dinsa yasa ya dauko ta zuwa gidan Ammi. Har wani zumudi take, yau gata awani babban gidan Daddy, aiko saita dauki hotuna tazuba a status kodan kawayenta na kano su gani,(kai Allah what you're about to see will shock you😂😂), ko sallama batayi ba ta shige falon, Ammi na zaune akan sofa ta juya bayanta, tana fuskantar TV, tunda Mama taga mace afalon Daddy tafara bombomi tun kafin ma taga fuskarta. Daddy ne yasauko hannunsa cikin an Sunaina, da Mama taga yarinyar taga fuskarta sak na Noor saidai Noor tadan fita haske kuma ta fita manyanta. Mikewa Ammi tayi tajuyo ahankali tana facing Mama. Dammmmmmmmm haka zuciyar mama ta buga, suuuu kawai kaji ta timmmmm ta fadi kasa sumammiya...

Gan gan gan😂😂😂 Mama Mama kashinki ya bushe dubunki ya cika.

COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/15/23, 8:36 PM - Reemah: 🌼 MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 65_ 66

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Second to the last page

Ruwa Ammi ta dauko daga fridge mai bala'in sanyi ta watsawa Mama a fuska. Firgigit ta mike zaune tana share ruwan daga fuskarta, kalle kalle ta shiga yi kamar mai neman abu, karaf idanunta ya sauka cikinna Ammi dake tsaye akanta ta harde hannayenta a kirji, zabura Mama tayi ta mike tsaye tayi hanyar fita daga falon, tana bude kofa taci karo dasu Noor wadda zuwansu kenan suma, Daddy ne ya kirasu wai akwai muhimmin taro, sunyi mamakin ganin mama a hargitse kamar wacce tayi gudun hijira,hannun Aryan ya nuna mata alamar takoma ciki, cikeda tsoronsa ta juya kamar kwai ya fashe mata aciki ta shiga falon. Still Ammi na tsaye Daddy kuma ya nemi wuri ya zauna dan ya ji lokacin dasu Noor suka shigo. Zama mama tayi kan carpet ta hade kanta wuri daya, Ammi ji take kamar ta mike ta rufe Mama da dan banzan duka, hakan ta kasance a wurin Aryan, Noor kuwa na rikeda muneer tana basa nono, sunaina kuma ta karbi mubeen ta wuce sama dashi zuwa dakin ta. Tsit kakeji a falon na wasu sakanni kafin Daddy yayi gyaran murya yafara magana, sunan Mama ya kira, bata amsa masa ba sai dagowa kawai tayi ta kalleshi, fuska a daure yace" Hamida, na dade da sanin cewa ke ba mace me kirki bace, kina yi min komai a duniyarnan na shanye amma kin taboni a wuri mai girma arayuwata, kin yi kokarin kashe min mata atunaninki babu wadda zai sani, kin sawa matata guba abincinta, kinyi kokarin datse duk wata farin ciki a rayuwar yata, saidai kuma inda bazan taba daina gode miki ba shine kula min da suhail da kikayi alokacin dayake buqatar uwa a tare dashi bayan mahaifiyarsa ta tafi" jin ya mabaci suhail yasa Aryan dagowa da sauri ya kalli Mama wadda itama shi din take kallo, wani kallo take mai wadda yake kama da roko,juyawa yayi ya fuskanci Ammi dake kallonsu su biyun kamar ta gaane wani abu. Sosai jikin kowa yaa sanyi afalon musamman Mama, ko ba komai tasan yau in har batayi kwanan gidan yari ba to zatayi kwanan zawarci dan tabbas yau aurenta da Nasir ya kare. Saida Daddy ya gama magana sannan Ammi ta amshe tace" Hamida, kin cuci rayuwata data yata, kin kyamacemu musamman yata wadda bataji ba batagani ba, kin wulakantata, wlh bazan taba yafe miki ba, dama ni kadai kika kyamata baki hada da yata ba, da zan iya yafe miki, amma ba komai yau Insha Allah abun yazo karshe, wlh mai rabani dake sai Allah" duk abubuwan da Ammi ke fada sam hankalin Mama baya wurin ita kawai hankalinta kan Aryan yake, tayi mamakin ganin baice komai ba, kenan bazaiyi magana ba, then it's her chance to use the opportunity wurin kare kanta, wani kukan munafirci ta fashe dashi tace" Rahma dan Allah ki yafe min, wlh nasan na tafka babban kuskure arayuwata kuma nayi nadama mara amfani, bayan mutuwarki nayi kuka nayi kuka karasa mai tausata, Dan Allah ko bazaki yafe min dan komai ba ki yafe min dan kula da suhail danayi..." Ran Aryan inyayi dubu to ya baci, bai taba ganin cunning woman kamar Mama ba wato ganin dai baiyi magana ba yasa take misusing chance din, zata kara magana ya daka mata tsawa tare da daga mata yarsa" enough!!enough is enough, ke yanzu wacce irin mutum ce, baki da ko digon imani azuciyarki,what do you take us for, fools?" Mamaki ne ya kama mutanin falon ganin yadda Aryan yake tada jijiyoyin wuya yana yiwa Mama magana kamar sa'arsa, Noor dake gefensa sai faman tausarsa take tana magana kasa kasa yayi shiru amma yaki, bata taba ganin tsantsar bciin rai a idanun Baby love dinta ba kamar yau, ko lokacin daya gano cewa itace matarsa bai bata rai kamar yanzu ba, lallai lamarin babba ne, Daddy abun ya daure masa kai, meke faruwa ne, dama Aryan ya taba sanin Mama ne abaya? Mikewa Aryan yayi tsaye ya tako tsakiyar falon yadda kowa zaina ganinsa yace" this woman is a murderer itace ta kashe danku suhail" dammmmmm haka sukaji gaba dayansu,harda Noor, ita ba sabon abu bane awurinta kawai tunani take yadda akayi yasan da wannan abun, dama ya taba sanin ta ne? Mama fa ta kame wuri daya tasha jinin jikinta, anan yacigaba da magana yace" years ago nida ammina mun tafi kano duba wani yaron aminiyar ammi wadda akayiwa aiki a ido, lokacinda mukazo, this woman arrived also da baby boy ahannunta yadda taketa kame kame kana kallonta kaga mara gsky, haka kawai naji inaso nabi diddigin ta, batare da saninta ba nabi bayanta zuwa office din doctor din dasuka hada baki dashi, I stood by the door,inda naji wannan babyn yana ta ihu alamar allura ake basa, ta handle din kifar na kalla, where I saw this woman telling the doctor " inaso kar ya kai har lokacinda ubansa zai dawo, inaso ya mutu abinneshi kafin yadawo karya zargi wani abu" shikuma kafirin likitan da babu imani azuciyarsa yace" ai wannan alluran baya daukan lokaci zai fara tasiri ajikinsa, sannan zan baki magunguna da zaki afka masa nan da kwana biyu na tabbarmiki zai mutu" bata dade ba tafito daga wurinsa, I'm not a coward so I stood there waiting for her, lokacinda ta fito muka hadu, she was shocked to see me dan bata ma lura dani ba, I threatened her cewa saina fadawa hukuma tanaso ta kashe dan cikinta not knowing ashe ma danta bane, a wurin tayi kokari tara min jama'a cewa I was harrasing her, looking at the nature of people dake wurin nasan sarai zasu yarda da maganarta shiyasa banyi jayayya ba na barta ta wuce but then nayi warning dinta haduwarmu bazai kaya da dadi ba" wani kuka ne ya kufcewa Noor da Ammi hatta Daddy hawaye ne ke bin gefen fuskarsa, wani irin kukan kura Ammi tayi tabi kan Mama sai duka kawai take kai mata left and right, babu wadda yayi gigin hanata sai ita maman dake kokarin kwatar kanta, sunyi kiciniya sosai kuma ba laifi Mama ta daku dan Ammi badai karfi ba. Allah ya isa kawai Noor ke furtawa ga Mama, ashe dai maganin datake ganin Mama tanabawa suhail bashi kadai bane, harda allura akayi masa, ashe one part of the story kawai tasani, anan Daddy ya kira police, Mama na jin haka ta rarrafo zuwa kafafunsa takama tana cewa" Dan Allah Nasiru kayi haquri,karka mun haka, da tsufana ace natafi gidan yari wlh bazan iya ba, wayyo ni hamidatu na mutu na lalace" hankadeta Daddy yayi da kafafunsa yamike rai abace yace "karki yarda ki kara rokata da sunan Allah, wlh Hamida marabarki da shedan kadanne inma akwai, me wannan yaron yayi miki arayuwa, yaronda baisan dama ba baisan hagu ba, amma Hamida kinji kunyar rayuwarki kuma kisani bazan taba yafe miki ba. Na tsaneki na tsani mai kama dake, kuma daga yau zamata dake ya kare har abada NA SAKEKI SAKI UKU, UKU, UKU" haka Mama taji a dodon kunninta, jitayi kamar ukun ma sau uku ya fada, bata gama

Please Login or Register in order to submit comment