Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zauna saman gadonta ta dafe kanta,wannan wani irin mutum ne wai, muguntarsa is on another level, ahaka akeso suyi zaman aure anya zaiyu kuwa? Gabadaya sai tafiya makarantar ma ya fice akanta.

Bayan ya gama shiri cikin suit dinsa white colour yasanya agogonsa kirar Rolex da takalminsa kirar company Versace black colour shima, sosai yayi kyau kansa tasha gyara, abinda yafaru tsakaninmu dazu ya dameshi, kuma inza'a duba ai laifinsa ne tunda shiyace mata he doesn't give a damn. Amma still shi mijinta ne baikamata ace tana bijirewa umurninsa ba, karasa shirinsa yayi yadau jakar system dinsa da key ya fito. Still yanajin sheshshekar kukanta amma babu yadda zaiyi haka yajuya ya fice. Koda yafito har ya shige motarsa saikuma yayi tunani Kodai yakoma yabata haquri ne ganin jiya shiya hanata zuwa school, yau ma kuma ace same thing ai bai dace ba. Girman kan Aryan yawuce duk inda mutum ke tunani, haka yashare shawarar da zuciyarsa ta basa ya figi motarsa yabar gidan. Noor tanajin lokacin daya fita takara fashewa da kuka.

******
"Daddy dan girman Allah ka roke shi karya min haka, wlh bazan jure zama da kishiya ba, kataimaka kabashi haquri wlh na tuba nabi Allah nabar Mama bazan sake ba na yarda zan haifa masa 'ya'ya bama d'a ba" Daddy dake zaune akan cushion yana kallonta da wani irin ido, kallon bakin ciki kallon takaici yake binta dashi bai taba tsammanin rashin imanin su har ya kai wannan stage dinba, yanzu badan labarin auren Mahmud yataso ba da haka wannan maganan zai yi shuru kenan, Mahmud kuwa duk tausayinta yakamashi, dama agidan Daddy ake wannan shari'ar, "Moon I am so disappointed in you wlh, dama ance in daya ya bakanta ma daya zai farantama, Allah yasa ba ke Kadai na Haifa ba kuma bake Kadai na aurar ba dan haka in Allah ya yarda nan nada jimawa ba Noor zata haifo min santalallun jikokina tunda ke kinmin buqulun samunsu daga wurinki, kuma ki sani ba zan taba rokon Mahmud yafasa wannan auren ba saboda ke San.." Mama ce ta katse masa maganar sa ta hanyar fadin" amma nasiru anji kunya wlh, yanzu meya kawo maganar wannan shegiyar bayan ana kokarin kashe wani wutan , toh bari kaji, ko wannan yaron yayiwa 'yata kishiya bazata taba kamo kafafun Moon ba kuma bari kagani sai Moon dina tafara aihuwa kafin ita yarinyar taka, aikin banza aikin wofi" murmushin takaici Daddy yayi, yanzu agaban surukinsa take fada masa wannan maganar bako kunya harda kiran yarsa shegiya hmm tayi nisa. Itako Moon sai sambatu takeyi tace" Mahmud dan girman Allah kayi min rai karka yanka min wannan hukuncin ka canza wani wlh na amince zan maka biyayya" sosai Mahmud yaji dadin maganarta amma awaje saiya nuna har yanzu fushi yakeyi da ita " Moon kinfi kowa sanin inason yara amma haka kika rufe idanunki kika biyewa son zuciya kika aikata babban laifi, toh idan na yafe miki shi Allah kuma fa" mama dan tsaban takaicin abinda Moon keyi saikace mara gata sai wani rarrafawa take daga kafar wannan zuwa kafar wannan tana rokonsu, mikewa tayi tabar wurin, Daddy ne ya kamo hannunta ya matso da ita kusa dashi yace" Moon" amsa masa tayi da na'am," kiyi haquri kinji, kibari mijinki yayi abinda yaga dama, kinga anriga ansa ranar auren sa, bazaiyi kyau yaje yace ya fasa ba saboda ke, dan haka kawai ki rungumi kaddara kibarwa Allah komai kinji"? Yayi maganar yana shafa kanta, ahankali ta gyada Kanta alamar ta yarda amma tace" Daddy kace masa dan Allah kada ya hadamu gida daya da ita, abinda ban gani ba banjiba bazai dameni ba balle haryakai ga sabani tsakaninmu" murmushi Mahmud yayi yace yayi alkawari bazai hadasu gida daya ba. Haka Daddy yayi musu sulhu sannan ya musu fada da nasiha. A daren ranar Moon tahada kayanta tabi mijinta. Mama kamar tayi hauka tsabar bakin ciki. Jawa Moon kunni tayi akan karta kara takowa zuwa gidanta ko kuma takirata awaya, ko ajikin Moon din, Daddy ba karamin dadi yaji ba yadda Moon tadawo kan hanya.

******
Ummi ce ke waya da Abba,suna magana ne akan Aryan da matarsa, " gsky hakan yayi, karki maida mata da motar yanzu, inta kiraki ta tambaye ki akan motar kice driver yayi tafiya kuma Nana bata iya tuki ba,shi Aryan din yarika kaita makarantar, da haka inasa ran Insha Allah zasu samu kusanci da juna " sunjima suna magana kafin Abba ya katse kiran, hankalinta bai kwanta ba har yanzu, dazu da rana tayi magana da Noor kuma taji muryarta ashake hakan ya nuna cewa kuka tayi amma bataso ta fada mata. Ita yanzu tama rasa yadda zatayi, a idon Aryan dai kamar tafara hango soyayyar Noor amma ita Noor Sam ba haka bane, saima wani tsoronsa da takeji kamar wani mala'ika. Still dai bazata yi kasa aguiwa ba, kuma alwawari ta daukar wa kanta cewa cikin wata guda zata daidaita tsakaninsu( ummi anya? bakisan cakwakiyan da akeyi agidan can bane hala).

*****
Hutu Ya Shareef ya daukar wa kansa saboda Na'ima dake fama da laulayi sosai, komai na gidan shike mata kuma ba komai take iya ci ba sai yan wasu abubuwan. Saukinsa shine da weekend Hanan da hanifa suna zuwa su taimaka mata. Sam baya gajiya da dawainiya da ita,saima wani soyayya dake kara habbaka a tsakaninsu. Allah ya raba lfy amaryar yayanmu.


Wannan hutun da shareef ya dauka ba karamin batawa Aryan rai yayi ba, awurinsa kawai yake sa ran samun shawara, gashi ko ya kirashi badagawa zaiyi ba, shikuma harga Allah bazaije gidansa ba karyaje yaganowa kansa abin takaici yahanashi bacci tunda shi ba samu zaiyi daga wurin matarsa ba. Halindaya barta aciki yake tunani, Allah Kadai yasani ma ko taci abinci. Gaba daya ranan ya kasa tabuka komai a office.

******
Karfe 5:30 ta farka daga bacci ko sallan asr batayiba. Sharp sharp ta mike ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta fito da alwalarta takabbara sallah. Cikin sallan taji shigowar motarsa. Bayan ta idar ta zauna rufka tagumi, ita tama gama yanke shawaran bazata tafi makaranta wannan satin ba, tasan ko ma dai menene weekend za'a dawo mata da motarta shikenan ta huta da wulakanci. Yunwa sosai takeji rabonta da cin abinci tun safe kuma tea da bread ne. Mikewa tayi ta nufi wardrobe dinta, wani dogon rigar roba ta dauka ta zura ajikinta sannan ta dau hularsa tasanya. Flat shoe ta Sanya tafito,data iso kitchen din tama rasa mezata dafa, deciding tayi ta girka jallof din taliya, cikin mintuna kadan ta gama hadaddiyar taliyarta wadda yaji kayan ciki da kayan lambu sai tashin kamshi yake, milkshake ta hada sannan ta fito zuwa dinning. Zamanta keda wuya taji anja kujerar dake kusa da ita anzauna, da farko harta razana amma ganin wanene yasata sakin jikinta tawani matse fuskarta babu alaman wasa. Tana tsoma fork zatafara ci taga shima ya zura nashi, dama gashi tana kule dashi tunda safe ai batasan lokacin data bare baki tafara kuka ba, da abinci abakinsa yama kasa hadewa kawai sakin bakin yayi galala yana kallon ta, yanzu saboda yaci mata abinci yasa take kuka? Noor fa ta dage sai kuka takeyi kamar zare ranta akeyi, gaba daya kukanta ya hargitsa masa tunani, wannan wani irin mutum ce, yanzu tsaban yaranta saboda anciwa mutum abinci sai yafara kuka saikace wani last born. Ahankali ya zare fork dinsa daga plate din ya dau ruwa ya shaa sannan ya mike dan yama rasa mezaice mata, gashi abincin yamasa dadi kamar karya daina ci amma gashi tamasa buqulu. Tana ganin ya mike yabar wurin ta dau plate dinta da milkshake tashige kitchen ta kulle kofa. Saida tagama ci tas ta wanke plate sannan ta fito lokacin har an fara kiran sallah maghrib, haurawa sama tayi ta shige dakinta dan gabatar da sallah.

Sai wuraren karfe goma yadawo hannunsa rike da ledoji guda biyu,kitchen ya shiga ya dau plate sannan ya bude ledan daya siyo burger da chicken wings ya juye acikin plate din, dayan ledan kuma chips ne da banana smoothies, yunwa yakeji sosai bana wasa ba dukda cin abincin dare bawani damunsa yayiba amma yunwar yau na daban ne Kodai kila saboda one spoon din daya ci daga plate din Noor ne ya kara masa yunwan tunda ba koshi yayi ba. Burger din ya dauka yakai bakinsa yadan gatsara kadan, da kyar ya iya cinye na bakinsa saiyaji komai ma ya fita aransa, fridge ya bude ya sa abincin sannan ya dau bottle wata kawai yasha ya fice daga kitchen din. Yanzu haka zasu cigaba da zama da ita, shida gidansa amma ace saidai ta girka abinda takeso kuma taci ita kadai, dayasa cokali zaici saita fashe masa da kuka, gsky da sake shi yanzu bazai iya da wannan horon ba tunda ya riga ya dandana dadin abincinta. Yazama dole yasan yadda zai gyara zamansu tunda yanzu yariga ya fada babu hanyar fitowa. Wanka yayi ya shirya cikin kayan baccinsa, system dinsa yadauka yahaye saman gadonsa, tunani yafara yi mema zai fara searching, google ya shiga ya rubuta" how to make a girl fall for you" ahankali yafara karanta bayanan da aka fitar, daya ance" take her on a date" na biyu" buy her Flowers " na uku " be nice to her" na hudu" say romantic words to her" duk wannan abubuwan daya karanta abu biyu kawai ya iya dauka zai jarraba, na daya shine taking her on a date na biyu kuma be kind to her. (Toh fa mutumin Ku ya fada dumu dumu😂😂). Ahaka yaita searching different ways to win a woman's heart, wasu ya dauka wasu yayi watsi dasu. Sai kusan karfe goma shaa biyu sannan bacci ya saceshi yabar laptop din akunne kan cinyarsa.

******
Yau Friday, su Anty Aisha keta shirye shirye mijinta wato baban lubna zai dawo daga port Harcourt. Su Lubna anyi karatun ta natsu dan babanta baisan duk wani shirme datakeyi ba, hasalima tsoronsa takeji danshi mutum ne mai zuciya da kuma addini bazai taba bari wani daga cikin 'ya'yansa su zama lalatattu ba amma kash Lubna tawuce tunaninsa saboda goyon bayan data samu daga wurin mahaifiyarta. Itama Anty Aisha ta natsu sai gyare gyare takeyi harda kunshi da gyaran jiki. Masu aiki kam suna kai da komowa wurin gyaran gidan dakuma girke girke. In mutum yaga Lubna zai rantse ma bata taba soyayya ba balle har takaida sanin da namiji tazama wani kamila tunma kafin babannata ya iso( shegiyan miya😒)

Yau aka daura auren Mahmud Ja'afar da amaryarsa Sofiyya Ahmad. Koda labarin ya iso kunnin Moon ba karamin kuka ta shaa ba, amma tayiwa kanta alqawari bazata taba nuna gazawarta ba. Ba karamin tausayi tabawa mutane ba dukda yawancinsu basusan dalilin karin auren ba, amma aganinsu ai yayi wuri saboda kwata kwata aurensu wata bakwai kenan, wasu kuma zagin Mahmud sukeyi wai ya cika ruwan ido shiyasa haryayi mata kishiya kafinta cika shekara daya agidansa. Set din akwati guda akayiwa Moon amatsayin danna kirji. Bayan sallan isha'i aka kai wa Mahmud amaryarsa gidansa dake angwansu Mama wato hotoro. Sai muce Allah ya basu zaman lfy.

******
Washe gari

Wasu zafafan restaurant ne masu kyau da tsari yake dubawa awaya, wani daga cikin su wadda shiyafi sauran kyau da kuma tsada ya zaba inda ya kira masu kula da wurin ya making reservation na couple table. Bayan ya gama duk wani abinda yakamata ya mike ya dau key din motarsa ya sauko babban falo. Shara takeyi tana yan kabe kabe hadi da bin karatun dake tashi cikin sipikun gidan. Tsayawa yayi yana kallonta kamar ya zo ta bayanta ya rungumeta saboda wani irin kaunarta dake yawo cikin zuciyarsa, komai nata tanayinshi ne cikin natsuwa da kamala, awani bangaren kuma za'a kirata da childish saboda abinda tayi masa jiya, yara kawai aka sani da rowa amma gashi itama ta nayi masa( to ba kai kace itadin tatsitsiyar yarinya bace, ta ai halinsu take nuna ma). Girgiza kai yayi ya saki murmushi sannan ya fice daga falon. Tanajin ya fita ta sauke ajiyar zuciya tacigaba da aikinta. Shiko yana fita ya wuce wani boutique, yana ciki zagayawa idanunsa suka sauka akan wani kyakkyawar lafaya black colour yasha adon black stones, sosai lafayar ta dau hankalinsa. Wata sales girl yasa ta packaging masa kayar sannan ya dau wani half cover shoe shima baki mai kyau sai walwali yake gwanin ban sha'awa, set din Jewelry ya siya silver colour masu tsadan gaske. Komai aka hada masa sannan yabiya bayan shima ya dau abubuwan dayake buqata.

Toh fa Aryan dinku yafara siyayyar women attire nan gaba kuma zaifara siyan wannan abinda yake jin kunyarsa wato pad.😂😂


Mu hadu gobe muji yadda date dinsu zai kaya, shin Noor ma zata yarda ta tafi? Allah ya kai mu gobe rai da lfy. Inawa kowa fatan alkhairi. Love y'all my fans❤️❤️❤️


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 41_ 42

Tundaga gate yakejin hayaniya acikin gidan. Da alama baki sukayi, su Hanan ne dasu yasmeen da Nana sai Anty jamila. Ledojin siyayyarsa ya kwaso daga bayan mota sannan yashigo ciki, Nana ce tafara gaida shi sai sauran shikuma ya gaida Anty jamila. Lokacin dayashigo Noor bata falon hala kitchen ta shiga. Haurawa yayi zuwa dakinsa itakuma daidai ta fito daga kitchen hannunta dauke da tray dinsu kayan motsa baki. Kusan ten minutes amma Anty jamila ta lura Noor ko motsawa batayi ba irin ko zataje tawa mijinta barka da zuwa dinnan, mikewa Anty jamila tayi ta shigo kitchen sannan ta kira Noor din, "habibty gani" Noor tafada, kallon tsaf anty jamila tayiwa Noor wato dai haryanzu ba canji azamansu kenan, gsky da sake," baki ji mijinki yadawo ba"? Anty jamila ta tambayeta, sarai Noor tasan ya dawo amma dayake zaman ko in kula akeyi shiyasa ma bata damu ba. Anty jamila tace" yanzu fisabilillahi Noor irin tarbiyyar da muka baki kenan, koda bakwa zaman lfy da mijinki kamata yayi ace kin nuna agaban kanwarsa? Idan wannan labarin yakai kunnin mahaifiyarsa kinsan ba dadi zataji bako, toh yanzu maza ki shirya abin sha a tray kikai masa dakinsa" turo baki gaba Noor tayi tace" habibty nifa ko kofar dakinsa bantaba knocking bafa" ha'ba Anty jamila ta rike tana kallon ikon Allah," wa ke gyara masa daki ya wanke masa bathroom"? Kafada ta daga alaman batasani ba, duka Anty jamila takaimata amma ta kauce, haushi kamar ya kashe Anty jamila " yanzu duk wannan wayon naki abanza ya tashi kenan, duk ilimin dakike dashi abanza yatashi, kinfasan hakkin mijinki akanki, koda baku son juna sai kirika masa wulakanci? Wlh kin bani kunya ban taba expecting haka daga gareki ba"? Tunda Anty jamila tafara magana jikinta yayi sanyi dan fada sosai tayimata ta inda take shiga batanan take fita ba. Sunkai kusan minti ashirin a kitchen din kafin tasa Noor tahado masa drink da ruwa a tray ta fito. Su Hanan suna ganinta sunsan ba lfy ba saboda yadda take ta turo bakinta gaba, dariya suka tuntsire dashi dukkansu suka hada baki wurin fadin" matan yayanmu" Noor ji tayi kamar ta fasa ihu haka ta wuce sama zuwa dakinsa. Ko da ta iso abakin kofa ta tsaya,knocking tayi amma ba'a amsa ba,saida ta kara sannan taji yace" who's there" ahankali tace" nice", Aryan ko mamaki yakamashi mai kuma tazoyi yau adakinsa, dagashi sai gajeren wando da singlet, zuwa yayi ya bude kofar, atsaye ya ganta rike da tray din juice,tundaga sama har kasa yakalleta azuciyarsa yace" tohh sabon salo" matsawa yayi ya bata hanya ta shiga sannan yarufe kofar. A bedside drawer ta aje masa sannan tajuyo zata fita, kawai ganin mutum tayi atsaye abayanta, rabawa tayi ta gefensa zata wuce yakamo hannunta,bazato ba tsammani kawai taji ya rungumota ta baya, zuciyarta ne yafara bugu da sauri sauri, hannunsa yasa yazagayo zuwa cikinta yafara goga mata sajensa afatar wuyanta, wani irin kasala ne ya saukowa Noor, ahankali yake numfashi a wuyarta ba karamin kashe mata jiki yayi ba, cikin sigar rada ya whispering mata a kunni yace" I'm sorry, I'm sorry for what I did yesterday, bazan karaba kinji"? Wani irin ajiyar zuciya Noor tasauke dan yadda yayi maganan in a sexy tone ya bala'in saukar mata da mutuwar jiki, yau shine ke bata haquri, anya ba imposter bane, Basamude ne ke cewa bazai kara ba, tabb za'ayi ruwa da kankara da alama. Wani irin sanyi yaji azuciyarsa, yanzu abu daya ya rage mai, shine maganan zuwa date, he's not sure kozata amince amma gara ya jarraba yagani. Hannu Noor tasa ta banbare hannunsa dake rike da kugunta,gabadaya jikinta sai kamshin turarensa yake gawani kasalan datake ji a jikinnata. Ledojin dayasiyo wannan kayan ya dauko ya mika mata sannan yace" later in the evening, get ready we're going somewhere" kai kawai ta gyada alamar toh sannan ta bude kofar tafita dagudu. Tana fita ta tsaya abakin kofar da wasu yan mintuna tana sauke ajiyar zuciya, meyasa takasa nuna masa fushinta da kuma rashin yarda da inda yace zasutafi, duk muzuran dataso masa sai takasa. Ga wani kwarjinin da ya mata lokaci guda. Kayanta ta shinshina taji duk kamshin daddadan turarensa yake. Dakinta ta bude ta shiga sannan ta aje kayan kan gado ta zauna har yanzu jikinta ba kwari, bata taba shiga irin wannan yanayin ba, bama tasan yadda zatayi explaining abinda takeji,kamshin turarensa shi yafi shige mata kwakwalwa, kamshi ne irin mai sanyaya zuciya ba mai hayaniya ba. Tunda tabar dakin jikinsa ba kwari, ga mararsa data daure gamm, toilet yashiga ya sakar wa kansa ruwan sanyi, kusan ten minutes kafin ya fito da towel a kugunsa, gaban dressing mirror yatsaya yana karewa kansa kallo, ahankali ya furta"Angon Noor "murmushi yayi kafin yadau mai yafara shafawa, shiryawa yayi cikin gajeren wando da rigarsa yayi zaman sa adaki tunda yasan akwai baki agidan.

Wuraren karfe biyu su Anty Jamila suka tafi,kafin sutafi saida tabawa Noor wasu turaruka da gumba,tunma kafin su tafi mutuniyar taku tafara hambula gumbarta hankalinta kwance, dariya kawai Anty Jamila takemata saboda tasan ranan kin dillanci na nan zuwa,lokacinne idonta zai raina fata inta shiga hannun Oga Basamude.


Kamar yadda ya fada mata karfe takwas na dare ta dau wankar lafayar ta, tayi matuqar kyau kamar wata amarya,kafarta sanye yake da takalmi half cover baki, handbag dinta shima baki da digon silver ajikinshi, sarka tasanya mai kyau da walwali silver colour, saiga matar Basamude tamkar wata shining armour. Bayan tagama shiri tazauna abakin gado tana jiran kiransa.

Basamude fa angama shiri cikin suit white colour, na cikin sa kuma black color da black tie, sosai yayi wani irin shu'umin kyau mai tafiya da imanin mutum, agogonsa na diamond White colour yasanya a tsintsiyar hannunsa, takalminsa toms black colour kirar company din Gucci, ba karamin hadewa yayi ba abun ba'a magana.Wayarsa ya dauko ya fito sannan ya knocking kofar dakinta, tsayuwa yayi har lokacin data fito, ko kyaftawa bayayi sai kallonta yake kamar zai hadiye ta, itako kunyar yadda ya tsareta da ido ne ya kamata, har tsawon minti hudu kafin ya excusing dinta tawuce shikuma ya take mata baya. Mercedes dinsa fara mai kyau ya budemata ta shiga shima ya zagaya ya shiga sannan ya tada motar suka bar gidan. Itako Noor kallon ikon Allah kawai take, toh ina zasu da wannan tsakar daren, ko dai wurin masu yankan kai zai kaita(kai Noor😂😂), tanacikin wannan tunanin suka iso harabar wani babban restaurant mai azaban kyau, wurin nan ya hadu iya haduwa kuma daga ganinsa kasan masu hannu da shuni kadai ke iya zuwa wurin. Fitowa yayi sannan ya zagayo ya bude mata, hannu ya mika mata alamar ta mika masa nata, babu musu ta sanya karamin hannunta cikin nasa, wani irin shock sukaji alokaci guda. Manager din wurinne yazo yai musu iso cikin restaurant din, ba karamin haduwa cikin wurin yayi ba,dim light ne tako ina a wurin just perfect for a romantic date,slow music aka playing inda ko ina a wurin yayi shuru babu surutan mutane. Wani VIP space aka kaisu inda Aryan ya making reservation dinsa kenan, dan kar wadda zai damesu. Noor sai ido, ba karamin burgeta wurin yayi ba. Kujera ya ja mata sannan ta zauna shima ya zagaya ya zauna yana facing dinta. Waiters uku ne suka shigo da trays na different dishes da beverages. Serving dinsu sukayi sannan su ka fice, kunya duk ya rufe Noor on a normal day ma kenan bata iya cin abinci agabansa balle kuma yanzu, daya lura cewa kunyarsa takeji saiya matso da kujerarsa dab da nata, fork yasa ya debi steak meat ya nufa bakinta,kallonsa tayi ya daga mata girarsa,da sauri ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, " haaa" ya fada tare da matsowa da fork din daidai bakinta. Ahankali ta bude bakinta ya tsoma naman aciki,tana cikin taunawa ta shaqe, da sauri ya dau ruwa a cup ya kai bakinta,saida ya make sure ta sha sosai kafin ya cire. Batawani ci abincin ba dan dama ba wani yunwa takeji ba, shima ba wani ci yayi ba dan ahalin yanzu abincinta kadai ke masa dadi. Wani button ya danna akan table din, within two minutes waiters dinnan suka shigo suka clearing abincin gaba daya. Tasowa yayi ya matso kusa da ita sannan ya tsuguna akasa, zaro ido tayi tana kallonsa, yo abun mamaki ba dole ba, itafa har yanzu taki yarda da abinda idonta ke ganr mata, amma dai bari taga iya gudun ruwansa. Wani karamin box ya fidda daga aljuhun suit dinsa, ahankali ya bude box din, wani farin haske ne ya fito daga ciki, wani diamond ring ne mai azaban kyau anrubuta kalamar N ajikinsa, hannunta na dama ya kamo sannan ya cire zoban yasa a ring finger dinta, sosai ya zauna akan yatsar hannunnata. "Nuwairahhh" ya furta ahankali cikin sugar rada har saida tsigar jikinta ya mike,murza hannunta yakeyi ahankali kafin yakara cewa" I'm sorry for all I did to you knowing and unknowingly, bazan kara ba, pls forgive me" ko kallonsa takasayi saboda wani kunya daya rufeta, yau Basamude ne ke furta wannan kalaman? Anya ba wani tarko yake shirya mata ba? Da kyar ta iya gyada kanta alaman ta yafe masa, still baki gamsu da amsarta ba yace" are you sure? Kin yafemin"?kai takara gyada masa, kamar an sauke masa wani dutse a zuciyarsa, murmushi yayi har saida dimples dinta suka lotsa gefe biyu,mikewa yayi sannan ya mikar da ita, ba zato ba tsammani taji ya rungumeta sosai akirjinsa,wani dadi yakeji har cikin ransa ba kadan ba. Dago habarta yayi yana kallon cikin idanunta, lumshe idanun nata tayi ahankali ta kara budesu, kallonsa ya maida kan cute lips dinta, kara lumshe idanunsa tayi da karfi dan batasan me zai biyo baya ba, aiko kamar tasani yaji saukar tattausar labbansa kan nata,lips dinta na kasa yakamo ahankali yafara sucking cikeda kwarewa,Sam taki bude bakinta balls yasamu chance din zura harshensa aciki, ya dau kusan five minutes kafin ya raba bakinsa da nata, kallon labban yakeyi yadda ya jike da danshin saliva dinsa. Duk ya kashemata gabobin jikinta. Murmushin jin dadi tayi kafin yace" mutafi ko"? Gyada kai tayi, handbag dinta dake kan table din ya dauka sannan ya kamo hannunta suka fito daga wurin, hankalin mutane sai ya koma Kansu,sun burge yawancin mutane a wurin, kana kallonsu kaga perfect match made in heaven. Kamar dazu yanzu ma shiya bude mata kofar motar ta shige sannan shima ya zagaya ya shiga. Ahanya kuwa sai sakin murmushi yakeyi time to time. Itako Noor abun duniya ya isheta,Allah Allah take yakoma gida dan gaba daya ta rasa nutsuwarta. Koda suka iso gida bata jira ya bude mata ba, ta sauko da sauri ta shige ciki, dakinta ta shiga tafara rage kayan jikinta ta shiga bathroom. Da ruwan zafi sosai tayi wanka dan wani sanyi sanyi takeji acikin jikinta,bayan ta gama ta saura dan karamin towel blue colour iya cinyarta ta fito, tama mance kofar dakinta abude tabarshi, hairdryer dinta ta jona sannan tafara blow drying dinshi,karar dryer dinne ya hanata jin shigowarsa. Handbag dinta ta baro a motarsa shiya kawo mata, shima har yayi wanka ya

Please Login or Register in order to submit comment